Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bukka tana gyara d'aurin zaninta,Mamaki da furgici yasa Safiyya zubewa a wajen don k'afa funta sun kasa d'aukarta,Abu ta taho da gudu ta d'ago Safiyya suka kama ta fiya babu alamar boka babu dalilinsa a haka suka tafi har titi Safiyya tana uban tangad'i kamar y'ar maye nan kuwa tsabar wahala ce tsantsagwaro.



Yanke shawarar kai Safiyya gidanta ta yi duba da yadda boka ya yi wa Safiyya fata²,Sannan ta kirawo su Umma ta shaida musu ce wa Safiyya tana gidanta wai mai mashin ne ya kad'e ta ta suma.

Sun yadda sosai da Abu don shekara kusan Bakwai tana musu Aiki ba'a tab'a samun matsala ba har ta yi Aure,don haka suka d'unguma zuwa gidan Abu don duba d'iyar tasu.



Ni kuwa a lokacin muna d'aki nida Fatima Umma ta shigo tana fad'a mana da hanzari muka bisu, abun mamaki har da Yaya Deen shi da basu tab'a wata doguwar magana bq don jininsu bai had'u ba,don Aunty Safiyya bata da kunya ga turb'une fuska.


B'oye mamaki na na yi har muka shiga mota muka tafi dubota,Yaya Deen kuwa sai rawae jiki ya ke yi ba tare da ya kalleni ba tun da muka shiga motar,idan kuwa ada ne muddin muka fita unguwa koda dasu Umma ne haka zai juya glass d'in motar ya yi ta b'ingira dariya yana tsokana ta.



Da rawar jiki ya shiga d'akin tun kafin a yi mishi iso,Ita kuwa Abu k'ara k'arfafa mishi guiwa ta ke yi wajen ce wa"Ka shi ga can ciki tana k'urya saboda iska shiyyasa da aka shigo da ita na ce a kaita cen".


Wani malulun bak'in ciki ne ya ya tokareni alokacin dana ga Yaya Deen yana rik'e hannun Aunty Safiyya yana mata sannu ita kuwa sai wani kukan shagwab'a ta ke yi.

Fatima kuwa kallon Auntu Safiyya ta yi ganin duk k'afar ta jini ne,Ai kuwa da sauri Abu ta rufe k'ar Safiyyar don gudun kada asirinsu ya tonu,basu san tuni Fatima ta dad'e da gano abinda ya faru Da Safiyyar ba,don Allah ya yi wa Fatima baiwar gane duk wani mutun mara gaskiya don tana shigowa ta gane don baiwar Fatima tana da yawa.

Sai kuwa Yaya Deen ya ce"Umma mu tafi da ita gida don ta samu kulawa sosai don nan akwai zafi Sosai don bana son Matata ta shiga wani hali.




*Kuyi hakuri kunsan bani da lfy ne na samu Miscariage so shiyyasa na yi tyiping kad'an*.




*Ummu Maher*
Miss green ce.




Sai kuwa na jiyoshi
*JÂMÊÊLÊR*


Na💖
(Ummu Maher)Miss green💚
*MATAR BASH*💡

My
Wattpad:Rabiatu333




🟨8&9


Wani gumi ne ya shiga karyomin ta ko INA jin furucin Yaya Deen akan Yaya ta,ga wani kishi da naji yana Neman kassarani duk kuwa akan furucin da naji Yaya Deen ya yi ne,bayan mun koma gida kuwa hankali na ne ya nemi barin jikina yadda naga Yaya Deen yana lallab'a Aunty Safiyya har da ce mata dole a yi maganin zazzab'in nan saboda kar suyi aure ta na yi,don asatinnan zai kawo kud'in saka rana Dana komai kuma ba yaso bukin ya wuce wata 1kacal.


Fatima ce ta ringa tausar zuciya ta akan inyi hak'uri komai yayi farko yana da k'arshe, hakan ce kuwa ta faru dani domin a kaso 100 acikin son da na ke yiwa Yaya Deen sai naji bai fi kaso 40 ba,don arayuwa ta na tsani mutum mayaudari maci amana.

Ai kuwa kwana uku da faruwar wannan al'amari naje gaida Babanmu naji yana fad'awa Mamanmu CE wa,wai jiya Yaya Deen ya kai kud'in Aure har da nasaka rana kuma nan da wata 1 za'ayi bukin,duk da gabana ya fad'i sosai da jin maganar Amman ban nuna ba ko alamu.

"Fatima kinga cin amanar da akayi min ko?wai yaya ta uwa d'aya uba d'aya Amman ki duba kiga irin cin amanar da ta aikata a gareni ko?" Wallahi haryau ban San me na aikatawa Yaya Safiyya ba take nunamin muguwar tsana haka ba,a iya sanina ban tab'a k'inta ko muzanta mata ba,Amman ki duba kiga yadda ita kullum ta ke nema taci min mutunci,ta hanani farin ciki don ita ta samu farinciki.


"Kiyi hakuri Jamila tabbas Yayarki taci amanarki sai dai kiyi hakuri ki fawwalawa Allah shi zai shige miki gaba aduk inda kike,kuma Allah zai fito miki da Wanda yafi Yaya Deen da komai,nidai ina rok'onki da kada ki nunawa kowa sirrin dake cikin zuciyarki,yin hakan shi zaisa kibawa Yayarki kunya."


To da wannan dad'ad'an maganganun na Fatima ne zuciyata ta samu salama sosai don sai in kwana in yini banyi tunanin wani Yaya Deen ba,balle Yaya Safiya wacce ayanzu gaba ki d'aya ta zama busy saboda bikinta daya gabato,kullum suna yawo ita da Sabuwa narasa inda suke zuwa.


Yadda Yaya Deen ya shareni ya fita daga rayuwata nima kuwa hakance ta faru a nawa b'angaren don ko kallonshi yanzu ba na yi,don akwai ranarda suna zaune shida Yaya Safiyya suna zance naje wucewa,ko kallonsu banyi ba na fara tafiya zan wucesu,kawai sai naji muryar Yaya Safiyya tana cewa,ke Jamila wani irin iskanci ne muna zaune Zaki wuce ba tare da kin tsaya kin gaida Yaya Deen ba,ko kuwa shima mugun halin irin naki zaki gwada mai?.

Ban saurareta ba na k'ara kama hanya zan wuce tasha gabana tare da d'aga hannunta ta wanke ni da wani mahaukacin mari wanda sai Dana ga wucewar taurari ta masu haske,sannan ta nuna ni da ytsanta tace"daga yau sai yau duk ranar da kika k'ara wucewa muna zaune baki gaishe muba to wallahi na lahira ma yafi ki jin dad'i.


Zuciya tace ta tsinke na kalli Yaya Deen naga ko kallo ban ishe shi ba, wani malulun bak'in ciki ya tsaya min a k'ahon zuciyata,ban k'ara magana ba na shige cikin gida ina kuka,koda Mama ta tambayeni ban bata amsa ba kawai sai na fad'a d'akinmu INA kuka mai tsuma zuciya.



Fatima CE ta ringa rarrashi na,akan da na yi hak'uri kada kuma na sakata acikin raina har abin ya dameni,kuma idan nayi hak'uri ta kusa barin Gidan nan na dad'ewa ba.





<★>
Yau take ranar D'aurin Auren Yaya Safiyya da kuma Yaya Deen,idan ka gansu ko wannensu baki har kunne saboda murna,ya yinda ni kuma na ke cikin wani hali wani irin zazzab'i mai mugun zafi ne ya rufeni y'an buki sai sannu suke zubamin tare da tausayamin don ina shan wahala,Amman Yaya Safiyya ko kallon arzik'i ban isheta ba,saima kallon banza da take bina dashi.



K'anwar Mama nace ta fad'awa Mahaifiyarmu aka kirawo min Family doctor d'inmu don yazo ya dubani,bayan ya gama dubani ne ya bani magani sannan na yi bacci,har akayi dinner aka kai amarya ban San me ke faruwa ba,domin kuwa inata bacci Fatima na kusa dani tana kallona tare da tausayamin.


Sai k'arfe goma na dare na tashi,ina tashi Fatima ma ta tashi tana yimin sannu, abinci ta kawomin da ruwan tee harda maganina,sannan na tashi na rama sallolin da ake bina zuciyata tana yimin k'una yanzu shikkenan Aunty Safiyya ta Auri Yaya Deen?kuka ne naji ya kwace min Fatima ta ringa tausata har na samu na kwanta bacci.


*Bayan kwana biyu*

Itace kuma ranar da k'addarar Jamila ta soma.


"Jamila!Jamila!!da sauri na fito daga cikin d'aki har ina had'a hanya don amsa kiran umman tawa,a farlo na sameta da wani Abu a cikin kwali Wanda ban San ko meye ba.


" tashi ki shirya Fatima ta rakaki Gidan mami,don haka ake kiran Aunty Safiyya,ki kai mata wannan sak'on sannan ki tayata gyara kayan".

To nace sannan na tashi zuciyata babu dad'i,don araina ban tab'a kawo zanje Gidan Aunty Safiyya da wuri ba, na samu Fatima ta fito daga wanka tana waya da Lamir,saurayinta ne Wanda suka had'u da shi ranar bikin Aunty Safiyya abokin Yaya Deen ne.


Dariya nayi sannan na ce"Miss soyayya ta shi kiraka ni Gidan Aunty Safiyya,sauri tayi ta kashe wayar sannan ta ce"rufamin asiri yanzu Yaya Lamir ya CE min yana hanya sai dai idan ya tafi sai muje."

"A'ah gwara ba tafi kada dare yayi idan yazo kya mik'amin gaisuwa".




Kallon Gidan na farayi tun daga k'ofar gate d'in har ko'ina na Gidan, ina tuna ranar da Yaya Deen ya nunamin Gidan a wayarsa yana gayamin irin rayuwar da zamuyi a Gidan,wasu zafafan hawayene naji suna fito min har na shiga Gidan ban San na fito ba kawai sai ganina nayi a cikin Gidan.


Tunda ta taho Deen ya hangota tun daga nesa tana takunta mai tattare da nitsuwa acikinsa,ya rasa me yake yi mai dad'i aduk sanda yaga Jamila sai yaji wutar sonta tare da sha'awarta Amman baya jin zai iya Gaya mata kuma aduk sanda yaganta sai yaji bazai tab'a iya yi mata magana ba.


Ko kallonshi ban yi ba na yi shige wata ciki,sallama na ringayi a tsakiyar farlon babu Wanda ya amsa min,na shiga wani d'aki Wanda nake tunanin shine d'akin Aunty Safiyya,nanma babu kowa juyowar da zanyi kawai sai naga Yaya Deen daga shi sai boxer ajikinshi,hankalina ya tashi sosai na tsorata da ganin Yaya Deen a haka,ban sanda na bud'e baki zanyi ihu ba kawai saiya shek'amin wani Abu a hancina,daganan ban k'ara sanin inda nake ba...







Idan kin karanta don Allah kiyi share.👏🏻


Vote
Share
&
Comments
*_JÂMÊÊLÊR_*


Na💖
(Ummu Maher)Miss green💚
*MATAR BASH💡*

Follow me on watt pad
*Rabiatu333*




🟨10&11


Wannan ita ce rana mafi muni Dana fuskanta arayuwa ta,ranar da bazan tab'a mantawa da ita ba domin kuwa aranar ne Yaya Deen ya yimin fyed'e a gidansa kuma a d'akin Yaya ta Safiyya,kuka ne yaci k'arfin Jamila alokacin da take bawa K'awarta Jamila labarinta.


"Kiyi hak'uri Namesake komai yayi farko yana da k'arshe tun kafin ki k'arasamin labarinki tausayinki ya k'ara ninkuwa a zuciyata,Amman Yaya Deen bai kyautawa rayuwarsa ba".

" Hmm Jamila ki tsaya kiji k'arshen labarina domin kuwa haryanzu ban kai miki inda nakeson kaiwa ba,rayuwata cike ta da abin al'ajabi da ban mamaki,rashin tausayi,cin amana,tsantar yaudara.


Fatima tayi kuka ranar kamar ranta zai fita,saboda yadda na bata labarin yadda Yaya Deen ya b'atamin rayuwa,Naso na sanar da iyaye na abinda ya faru Amman tuno abinda zai faru nayi hak'uri, na danne abinda yake cikin zuciyata,na yi jinya ta a d'aki har na warke,tun daga wannan ranar ne na shiga cikin k'unci na rame na lalace duk akan fyed'e da Yaya Deen ya yi min.


Ana cikin haka ne fa na fara wani irin zazzab'in dare kullum sai na yi shi,ga tashin zuciya na shaidawa Fatima tace muje asibiti don ganin likita,har mukaje asibitin gabana yana fad'uwa don ban San me zai faru ba,ga wani irin fad'uwar gabar da na keji kiran sunan Allah na fara yi har sakamakon gwajin ya fito.


Shingin kad'an in fad'i jin mummunan labarin da Likitan yake fad'amin wai inada k'ara min ciki,harda rubutamin scanning.


Fatima ma kuka ta ke yi,don sai yanzu take Dana sanin b'oye maganar da sukayi ita da Aminiyarta Jamila,da k'er muka dawo gida dukkanin zuciyoyinmu kamar zasu fashe tsabar tunani da fargaba,muna shigowa Gidan da Yaya Deen muka fara cin karo alokacin da ya ke bud'ewa Aunty Safiyya mota,tana d'auke da d'an k'ara min cikinta daya fara fitowa,sai wani iyayi take koda ta hango mu nida Fatima muna tahowa saita k'ara shigewa jikin Yaya Deen tana wani shagwab'a.


Kallonsu nayi cikin wata kwalla da ta fara fitowa daga idanuwa na tausayin kaina,don na lura Yaya Deen ko tunanin abinda ya yimin ba yayi,ya yi k'ibarsa ya sake wani irin fari kamar bature ko balarabe,Fatima CE ta fara wucewa ko agaishesu ba ta yi ba,ta yi wucewarta nima hakan ne a nawa b'angaren don ko kallo basu isheniba,inajin Aunty Safiyya tana tsaki tare da zagina,ni kuwa ko juyowa ban yiba nabi bayan Fatima,don jin kaina na ke yi yana juyawa tsabar damuwa,ina shiga d'akinmu na mak'ale jikin bango sai sannan wasu zafafan hawaye suka zubomin,sai asannan Fatima ta shigo tare da Mamanta.


Gaba nane ya k'ara bugawa lokacin da na ji Maman Fatima tana yimin magana kamar haka.



"Yanzu Jamila meye amfanin b'oye wannan maganar da ki ka yi,ni banga abin buyewa acikin wannan maganar ba,yanzu wa gari ya waya da kin fad'amin idanma ba zaki iya gayawa Mamanki ba ai da sai ki gayamin in gaya mata".


Tunda ta fara yimin magana kuka kawai na ke yi don jin maganarta ta na ke yi kamar wata ta tsuniya don abinda ya faru ya Riga da ya faru don babu amfanin sake mai_mai ta ta.


" yanzu lokaci ya k'ure na gayawa iyayenki,Amman babu Wanda zai fitar dake sai Allah,sai Shamsudden don koma menene shine ya janyo miki shi,don haka dole ne yanzu ya Sani ba sai an b'ata lokaci ba kamar yadda ku kayi daga farko.




Haka kuwa a kayi Maman Fatima ta nemi alfarma wajen fad'awa Mamana CE wa zamu rakata unguwa, mama ta yi mana a dawo lfy.



Fatima ce ta kirawo mana shi don ta tambaye shi ko yana gida ne,ya ce eh yana gida yanzu ya dawo daga kai Safiyya asibiti,Fatima ta ce mai to gasunan Amman da zai yiyu ya zauna a babban falonsa na bak'i ummanta CE ta ke son yi mai magana akan maganar abokinshi da ya ke son shi,nan da nan ya bada ammuna yana mai sake godewa Allah daba maganar da ya yi tunani ba ce don haka ya tashi ya kashewa Safiyya Ac ba ki d'aya sannan ya fita,yana Fita Safiyya ta fito cikin sand'a_sand'a ta bishi haka kawai taji bata yadda da wannan maganar ba don ta gane da Mmn fatima ya ke waya.





Ummu Maher ce
_*🍇JÀMÈÈLÈR*_🍇


*💖NA*
_Ummu Maher(miss green💚🌱_

*MATAR BASH💡*

Follow me on wattpad
*Rabiatu333*




12🟨13

Sosai Umma ta yi nisa a maganar ta, tunkafin Ta k'arasa maganar da ta ke yi Yaya Deen Ya yi saurin ta shi tsaye yana muzurai k'asan zuciyarsa kuma tausayin Jamila ya ke ji Amman bazai iya zuba idanu yana ji yana gani ba mutuncinsa ya zube don haka cikin kakkausar Murya ya ce.



"Gaskiya ni bansan da wannan maganar ba don ni rabona da ita tun kafin bikinmu da Safiyya,Amman na yi mamakin jin wannan zancen don Jamila ta zubarwa da su Abba mutunci......



K'arya ka ke Yaya Deen,suka jiyo muryar Jamila tana faman kuka kamar iyayenta sun mutu,Wallahi tallahi Kaine kayi min ciki domin ban tab'a aikata b'arna ba Kaine kayi min fyed'e a ranar da nazo Gidan nan Mama ta aikoni kawowa Matarka sak'o."



Da k'er ta kai maganar tana numfarfashi,da sauri Umma ta rik'eta tana gaya mata maganganu masu kwantar da hankali,Fatima ma tana taya ta da sauri Umma ta ruk'o hannun Jamila suka fito daga gidan.




Da sauri Yaya Deen ya fito daga main farlonsa duk ya had'a gumi kana ganinsa kaga Mara gaskiya.


Safiyya da ke lab'e ta ji komai don haka ta share hawayen da suka zubo mata tana sauri don ta koma d'akinta,Muryar Deen ta ji a bayan ta yana kiranta,Cak ta tsaya awajen harya k'araso ya juyo da ita yana fuskantar ta.



"Yaya Deen da gaske ne Kaine ka yiwa Jamila ciki?".



A bazata maganar tazo masa don haka ya fara had'a gumi yana kaicon halinsa nason zuciya da cutar k'anwarsa mafi soyuwa a rayuwarsa.



Ni kuwa Ummu Maher Na ce so ko cuta.😏☹️



Da k'er ya had'e miyau d'in bakinsa wajen fara magana," Safiyya kinsan halina kinsan abinda zan Aikata wallahi ba nine na yi mata fyed'e ba,nima na yi mamakin irin sharrin da Umma ta yimin don dama matar bata kwanta min ba,tana da shishshigi sosai shiyyasa ban fiya shiga harkarta ba shiyyasa yanzu ta tsaneni tazomin da wannan zancen,Amman zanje har gida in San ta yadda zan Fara magana dasu Baba da Mama.


"Amman kafin nan inason yin magana da Jamila....."


"Wat wallahi baka isa kayi magana da Jamila ba su San yadda zasuyi wajen k'ara yi maka sharri to wallahi baza kaje ba,kuma tunda abin yazo da haka dole ne musan abinyi.



Deen da aikin asiri ya ke Kansa har yanzu don duk abinda Madam Safiyya ta tsara agidan shi a ke yi don har mutane sun fara gane yadda Deen ya zama mijin tace.


Dole yanzu Jamila tana shirya wani abin domin kuwa ni nasan ba zata zauna ta yi shiru haka ba,dole ta sanar da wannan maganar Amman nasan koda zatayi maganar to ba ayau ba sai zuwa gobe mu kuma a Daren nan zamu aikata duk wani shirinmu.




Sulolo Deen ya yi kamar wani wawa yana kallon Safiyya Jan hannunsa ta yi suka shiga d'aki.






Da k'er Umma ta shawo kan Jamila don ma Allah ya tai makesu da suka dawo Mama bata nan ta bada sak'o a gaya musu cewa taje dubiyar y'ar yayarta da ta haihu a kayi mata operation.




Baccin wahala ne ya yi awan gaba da ita Umma da Fatima suna kallon ta suna tausayawa rayuwarta don sun San Halin Jamila ba zata tab'a k'arya ba,Fatima CE ta k'ara shaidawa Ummanta cewar tabbas Deen d'in ya aikata haka duba da irin abubuwan da ya ringa yi mata tun kafin yayi Aure da yadda Auren ya koma kan Safiyya.



Sai dare sannan na tashi da wani irin mummunan mafarki wai wasu mutane suna bina.


Da alama mutanen Gidan sun da d'e da bacci abin mamaki koda na duba a gogo k'arfe 9 na dare ba wani dare ne yayi sosai ba.



Farlo na fito na zaunq har yanzu zuciyata babu dad'i Allah² na ke safiya ta yi don koma menene masu iya magana sunce ranar wanka ba'a b'oyen cibi.



Ruwa na gani kan fridge mai sanyi da alama kuma wanine ya d'auko bai samu damar sha ba har ya yi bacci,don haka na d'auko na kafa kai a gorar ruwan sai da na shanye ruwan tas sannan na ji wani irin jiri yana d'iba ta ban Ankara ba sai da naji na fad'i saman kujerar da ke farlon.






Deen da Safiyya suna d'auko Jamila suka fara tafiya akan titi suna sharara gudo,yadda Deen yasan gari shiyyasa kwata kwata baibi titi ba sai da sukayi nisa sosai,Y'an sanda kuwa masu patrol suka tsayar dasu don bin cike...








*MISS GREEN ce✍🏼*
_*🍇JÂMÊÊLÊR*_🍇


*💖NA*
_Ummu Maher(Miss green💚🌱_

*MATAR BASH💡*

Follow me on wattpad
*Rabiatu333*



14🟨15

.......A matuk'ar tsorace Deen da Safiyya suka kalli junansu ganin y'an sanda sunyi cirko cirko agabansu hanjin cikinsu ya kad'a,lokaci d'aya Wata irin zufa mai zafi ya fara karyowa ko wannensu,lokacin da y'an sandan suka lek'o su biyu ko wanne daga jikin windows d'in suna k'are musu kallo tare da nazartarsu.




Daga cen d'aya b'angaren wani d'an sanda Ya ce.

"Sir"
Da sauri suka juya suna kallonshi don jin me zaice.

"Sir ga wani mun kamashi da hudar iblis da daddaren yana Neman tsere da su" ya fad'i hakan yana numfashi don da alama ya sha wuya sannan ya kamasa,kuma da alama yaron d'an masu kud'i ne.


To fa ganin Y'an sandannan sun tafi wajen wancen me laifin sai kuwa su Deen da Safiyya suka saki murmushi tare da juya motar zuwa wata hanyar.


Sunyi tafiya me Nisan gaske a wannan Daren,ko tsoro ba sa ji kodon zuciyarsu ta k'ek'ashe ne oho?


Wani tafkeken ruwa naga sun nufa da alama ruwan ruwan me matuk'ar girma ne,don haka Deen ya fito Shida Safiyya suka d'auko Jamila a hankali har suka k'ara sa wannan tafkeken kogin suka jefar da ita saida suka wuwulata har sau uku yadda zata shiga ruwan sosai sannan suka cillata.


Da sauri suka shiga cikin motar suka bar wajen cikin sauri don kada wani ya kamasu.







Mlm Bashir ne a gefen babban wani ruwa yana aikinsu irin na Malamai Amman fa ba na tsibbo ba,wata baiwar Allah zai had'awa maganin Haihuwa,kuma da wata itaciya za'ayi aikin acikin ruwan take.


Koda yaga ba zai samu daga bakin ruwan ba kawai sai ya saka kayan ruwansa da ya ke sakawa aduk lokacin da zai yi irin wannan aikin.



Dube_dube ya ke acikin ruwan har Allah yasa ya sameta,sai dai me?Mutum ya ji yana tab'awa dai dai jikin Y'ar bishiyar da ke cikin ruwan.


Ya tsorata sosai Amman da yake a shirye yake,don Mlm Bashir baya wasa da addu'ah,don haka ya fara janyota har Allah yasa ya fito daga cikin ruwan.



Masha Allah!abinda Mlm Bashir kenan ya fad'a ganin kyakyawan budurwa,sai da ya kalli k'afafunta ne yaga jini na zuba sosai kodon da tana cikin ruwa ne oho?.

Da sauri ya saka ta acikin motarsa sannan yayi hanyar babban asibiti da ke jihar Bauchi,Suna shiga likitoci suka karb'eta hannu bibbiyu don sun San Mlm Bashir mutum ne Babba Wanda ajihar gaba kid'aya ake ji dashi don Mlm ne Wanda yasan takan magani kaka_kala.



Sai da aka samu kamar 1hr sannan suka fito mode d'insu gaba kud'aya ya canza.


Sun shaidawa Mlm MATAR tana da ciki,harma tayi b'ari sai dai har yanzu bata San inda kanta ya ke ba.


Dai dai nan Jamila ta fashe da wani irin kuka tana kallon namesake d'inta sannan ta ce in tak'aice miki sai da nayi kwana d'ai_d'ai har bakwai sannan nasan inda kaina ya ke.


Bayan na warke tsaf bisa kulawar likitoci da Matan Mlm don Mlm ya basu duka labarin abinda ya faru.


To tun daga nan na koma Gidan Mlm da zama,in tak'aice miki Jamila sai da nayi wata 1 agidan Mlm sannan na fara sakin jikina,don suna bani kulawa Sosai,don Amaryar Mlm macece mai matuk'ar kirki da Jan mutane ajiki.



"Kuma Jamila kin k'ara jin maganar gida kuwa?".


"Hmm".

"Tunda ganan ban k'ara jin labarin gidaba,sai dai har y'an gida ba,Amman ina matuk'ar jin tausayin halinda Masoyana zasu shiga musammam Mama,Baba,Fatima,da Ummanta".


Kuka sosai Jamila ta fashe da shi,Namesake d'inta na rarrashinta.




" Hmm Jamila kin gama naki labarin saura labarina domin idan kikaji nawa naki ba komai bane".





To sai Ku biyoni don jin labarin Jamila 2 itama.





*Miss green ce*
*_JÂMÊÊLÊR_*


Na💖
(Ummu Maher)Miss green💚
*MATAR BASH💡*

Follow me on watt pad
*Rabiatu333*




🟨10&11


Wannan ita ce rana mafi muni Dana fuskanta arayuwa ta,ranar da bazan tab'a mantawa da ita ba domin kuwa aranar ne Yaya Deen ya yimin fyed'e a gidansa kuma a d'akin Yaya ta Safiyya,kuka ne yaci k'arfin Jamila alokacin da take bawa K'awarta Jamila labarinta.


"Kiyi hak'uri Namesake komai yayi farko yana da k'arshe tun kafin ki k'arasamin labarinki tausayinki ya k'ara ninkuwa a zuciyata,Amman Yaya Deen bai kyautawa rayuwarsa ba".

" Hmm Jamila ki tsaya kiji k'arshen labarina domin kuwa haryanzu ban kai miki inda nakeson kaiwa ba,rayuwata cike ta da abin al'ajabi da ban mamaki,rashin tausayi,cin amana,tsantar yaudara.


Fatima tayi kuka ranar kamar ranta zai fita,saboda yadda na bata labarin yadda Yaya Deen ya b'atamin rayuwa,Naso na sanar da iyaye na abinda ya faru Amman tuno abinda zai faru nayi hak'uri, na danne abinda yake cikin zuciyata,na yi jinya ta a d'aki har na warke,tun daga wannan ranar ne na shiga cikin k'unci na rame na lalace duk akan fyed'e da Yaya Deen ya yi min.


Ana cikin haka ne fa na fara wani irin zazzab'in dare kullum sai na yi shi,ga tashin zuciya na shaidawa Fatima tace muje asibiti don ganin likita,har mukaje asibitin gabana yana fad'uwa don ban San me zai faru ba,ga wani irin fad'uwar gabar da na keji kiran sunan Allah na fara yi har sakamakon gwajin ya fito.


Shingin kad'an in fad'i jin mummunan labarin da Likitan yake fad'amin wai inada k'ara min ciki,harda rubutamin scanning.


Fatima ma kuka ta ke yi,don sai yanzu take Dana sanin b'oye maganar da sukayi ita da Aminiyarta Jamila,da k'er muka dawo gida dukkanin zuciyoyinmu kamar zasu fashe tsabar tunani da fargaba,muna shigowa Gidan da Yaya Deen muka fara cin karo alokacin da ya ke bud'ewa Aunty Safiyya mota,tana d'auke da d'an k'ara min cikinta daya fara fitowa,sai wani iyayi take koda ta hango mu nida Fatima muna tahowa saita k'ara shigewa jikin Yaya Deen tana wani shagwab'a.


Kallonsu nayi cikin wata kwalla da ta fara fitowa daga idanuwa na tausayin kaina,don na lura Yaya Deen ko tunanin abinda ya yimin ba yayi,ya yi k'ibarsa ya sake wani irin fari kamar bature ko balarabe,Fatima CE ta fara wucewa ko agaishesu ba ta yi ba,ta yi wucewarta nima hakan ne a nawa b'angaren don ko kallo basu isheniba,inajin Aunty Safiyya tana tsaki tare da zagina,ni kuwa ko juyowa ban yiba nabi bayan Fatima,don jin kaina na ke yi yana juyawa tsabar damuwa,ina shiga d'akinmu na mak'ale jikin bango sai sannan wasu zafafan

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment