Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Afeeyah sukai murnar jin haka kuma suka godewa Allah.


Kwanan mami uku a gidansu Zainab bata koma ba saboda tsoron haduwarta da daddy saiyau ta shirya taje asibiti gano Al'ameen.


Tana shiga dakin ta ganshi a zaune fati na gefenshi wata uwar harara ta wurga mata tana cewa.


"To sarkin kinibibi mahaifiyarsa tazo saiki fita ki bamu guri zanyi magana dashi kinzo kin gurbata mana zama kin zama ba'kar ashana fita nace me idanun mayu kosai kin lashe min tawa kuruwar nima kamar yadda kika lashe tasa mayya kawai". ?


Mikewa Fati tai cikin takaicin maganganun da mami ke fada mata ta fita waje tana share hawaye haduwa sukai da Sadiq ganin tana kuka yace.


"Zarah lafiya ina zakije ko wani abune ya samu Al'ameen din"?.


Kaita girgiza" babu komai gida zan tafi".


"Amma Zarah meyasa? ki bari sai dare mana".


"Mami tazo itace zata wuni a wajensa".

Kallon tsaf Sadiq ya mata haba shiyasa take kuka yasan da dalili.


"Ok muje na kaiki to"fita sukai domin ya mayar da ita yana kuma sake bata hakuri.


Page 35 to 36.
Fati na palor a zaune bayan Sadiq ya ajiyeta ita kadai tai shiru ta nutsa cikin tunani da mamakin wacce irin 'kiyayya mami ke mata abin ya wuce ma hankalinta.


Jin karar bude kofa yasa ta dago mami ta gani ta shigo jikinta ne ya soma rawa kamar taga hallaka.


Zama mami tai tana kallonta fuska babu wasa tace" ba wata tsiyar ta kawo niba na baki minti biyu ki shiga ki tattaro kayan daud'ar ki kibar gidann nan yadda kikai silar fitar Zainab to kema ya zama haramiyarki saidai ya auro wata yasa".


Hawaye suka gangarowa Fati da sauri ta goge tana juyawa ta shiga part dinta bata dade ba ta fito mami na zaune tana kad'a kafa ganin ta fito yasa ta mike tana sakata gaba da, tsinuwa suka fita harabar gidan.


Karbe key din gidan tai a hannun Fati sannan taiwa driver umarni cewa.


"Ga wannan bagidajiyar ta nuna maka hanyar kauyensu ka mayar da ita yau sai kwanan tabarma cikin 'kunci da zafi ba a.c sai ai ta fama da mafici daula kinyi bankwana da, ita".


Tana gama fadin haka ta shige motarta ta fice daga gidan Fati na kuka ta shiga mota bangare guda tana farin cikin barin masifar mami datai.


A ranar Al'ameen yabar asibitin Sadiq ne ya kaishi har gida sannan daya huta ya tafi nasa gidan.


Karfe goma daidai Al'ameen yace zai tafi gidansa tari mami batai masa ba balle ta nuna masa cewa ta koreta.

Tana kallonsa ya fice daga palon dariya tai tana cewa "hummm yaro man kaza ai kaida wannan shegiyar yarinyar har abada je ka dawo ina daidai dakai saika saketa".

Kamar an jefo Al'ameen haka mami ta ganshi murmushi tai tana dauke kanta daga saitinsa tace "a'a me kuma ya dawo dakai"?.


"Mami ina Zarah"?.

"Tambaye nidai baba tunda ajiyarta ka bani".


"Mami I know what u have done to my wife na roke ki daki fada min inda take me kikai mata".


"Ban sani ba zo ka rufe ni da duka saina fada maka inda na kaita".


"Dan Allah mami mubar wannan maganar ina key din gida na"?.


cikin gadara mami dake zaune tasa glass da laptop gabanta tana aiki tace".


"Wanne gida kake dashi daya wuce nan ai daga yau ka dawo gidan ku da zama zansa a gyara maka part dinka gobe".


"Meyasa mami bayan ga gida nacan da matata taya zan barta ita kadai na dawo nan".


"Allah ko sannu me mata karka batawa kanka lokaci na kora ta garinsu".

Wata irin juyowa Al'ameen yai yana kallon mami cikin tsananin mamaki yace mami kin kora ta garinsu saboda me"?.


"To babana matse ni saina fada maka dalili kuma ban yafe maka idan kaje wannan matsiyacin kauyen balle kace zaka dawo da ita yadda ka ci mutuncin Zainab ka wulakanta ta ka saketa haka itama nake so ka rubuta mata takardar saki uku ba maganar kome saidai ka auro wata".


Wata iriyar hajijiya ce ta debi Al'ameen da sauri ya zauna tare da dafe kanshi maida hankalinta mami tai akan aikin da take tana cewa".


"Kome zakai saika saketa bazan taba daukarta matsayin suruka taba".


Jin tafiya yasa ta dago ganin daddy ne tadan zaro ido tana fatan Allah yasa baiji zancen da suke da Al'ameen ba.


Shi kuwa ya riga ya gama jin komai muryarta nadan rawar rashin gaskiya domin tun ranar da ta daki Fati basu sake haduwa dashi ba saiyau tace.


"Sannu alhaji".


Banza yai da ita ya dauke mata wuta kamar baiji ba ya karasa inda Al'ameen ke zaune yana dago kansa.


Ganin hawaye a fuskarsa abinda ya manta yaushe rabon daya gani tun yana yaro saiyau cikin tsananin bacin rai da fushi ya juyo inda mami take yana kallonta yace.


"Yau tafaru ta kare Aisha kullum ina miki gargadi dajan kunne bakya dauka to yau zakiga sakamakon abubuwan da kike aikata min".


Part dinsa ya shiga mintuna biyu ya fito da takarda a hannunshi yana cilla mata cikin kakkausar murya yace".


"Ita kin bata minti biyu ni kuma minti daya na baki kada ki kuskura na fito na sameki kibar min gida na".


Mikar da Al'ameen yai yana shigar dashi part dinsa sannan ya fito ganinta zaune tana kuka yasa yace ki fita a gidan ko a hanya sai kiyi domin na gaji da ganinki".


Cikin kuka mami tace alhaji kayi hakuri bazan sakeba na tuba".

Kai ya girgiza ai Aisha bazan iya sake zama dake ba kina lalata min zumunci da hana zaman lafiya ya zaga ahli na".


"Wallahi alhaji kaban dama na karshe zan gyara hali na tun muna kuruciya banje gidan mu da sunan yaji ba saiyau naje da takardar saki wannan abun kunya har ina alhaji ka dubeni".


"Ai Aisha abinda ya dace dake na baki hukuncin ki kenan".

"Kayi hakuri kamin sutura alhaji zan gyara kuskure na namaka alkawari".


"Aisha bazan miki uziri ba a yanzu rayuwa ta bata bukatar ki na datse duk wata alaka dake tsakanin mu"'.


Cikin kalar tausayi mami ta durkusa gabansa tana masa magiya amma sam ya dauke kai daga saitin ta.


Mikewa tai ganin babu alamar zai karbi bada hakurinta tana kallonsa tace" na baka hakuri amma alhaji ka 'ki..............


Katse ta yai "ki barmin gidana bana son jin komai daga gare ki" bar mata falon yai .


Dole mami tahau tattara kayanta kamar yadda taiwa wata itama ta nufi gidansu cikin bakin ciki da kunyar yadda zata fuskanci mahaifanta.


Ranar kwana cur mami tai a zaune bata ko runtsa ba tana kuka har zazzabi da ciwon kai suka rufeta.


Washe gari ma haka ta wuni rim a kwance babu cin abinci babu shan ruwa ga fadan da tasha gurin dattijon mahaifinta.


Nadama iri iri babu wacce mami batai ba da dana sani domin a rayuwarta tana matukar son daddy kamar ranta.


Fati na zaune a kofar dakinsu tana gyarawa umman ta waken da za'ai abincin rana Saude ta fito daga dakin ganin Fati zaune yasa tace.


"Humm yan birni har dubun naku ta cika asirin da kukai musu ya karye ko kuma kinyi halin 'bera sun fatattako ki ko"?.


"Meye gaskiyar al'amarin fada min gashi zaki abin kunya ki haihu a gida tir da wannan abu ina tausaya miki domin zilamar uwarki dason zuciyarta ne ya jawo miki".


"Koma dai ba cikinsa bane shiyasa suka koro ki iye fada min naji domin yadda idonki yake a tsayen nan zaki iya aikata komai maganin son banzar ku kenan kunga kudi shine kuka rude saida kuka shiga jikinsu ai dama duk wanda yahau motar kwad'ayi yasan baida gurin sauka sai tashar wulakanci".


"Kiyi addu'a kada ki haihu su 'ki karbar d'an yan kauyen nan su samu abin gori kI shafawa danginku ba'kin fenti".


"Koda yake nasan me za'ayi zan taimake ki na karbo miki magani kawai kisha d'an ya mutu ko idan kin haifeshi ki sha'ke masa wuya bada sanin kowa ba kinji zan rufa miki asiri babu wanda zai sani amma kudin da kika sato musu daga can zamu raba idan kin yarda"?.



Ko dagowa Fati batai ta kalli Saude ba balle tayi tunanin zata bata, amsa kawai aikinta take".


Tsaki Saude tai ke dalla gafara don ma za'ai miki sutura shine kike min wani gani gani wato ke uwar dabaa lamba d'aya ko"?.


"Aiko kin shiga uku a gurina dan saina zaga kauyen nan na sanar dasu kinyo cikin shege a birni".

" ta fada tana saka hijab tare da rufo dakinta tai hanyar waje tana cewa" bari na fara daga makotan mu su tabawa da Aliyah" da kallo Fati ta bita tana share hawayen daya zubo mata".


Shigowar Salamatu ganinta haka yasa ta tambayeta" Fatima lafiya kike kuka? kiyi hakuri kaddararki kenan ki dage da addu'a babu abunda ya gagari ubangiji shine mai bayarwa,".


Kukan Fati ne ya fito fili cikin damuwa tace "umma ba laifin Al'ameen bane baisan ma na taho ba yana asibiti mami ce ta min komai".


"Duk da haka kinga ki kwantar da hankali komai yai farko wata rana zaiyi karshe idan Al'ameen mijin zaman kine zaki koma".


Kai Fati ta girgiza tace "nifa umma wannan ba shine matsala taba damuwa baba Saude yanzu tasa hijab ta fita wai seta zagaye garin nan tace ba wani aure danai cikin shege ne".


Kirji Salamatu ta dafe tana kallo Fati tace" ita Sauden ce tace haka? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Allah gamu gareka kaine gatan mu".


Fati data sauke ajiyar zuciya tace" amma umma ya kamata a dakatar da ita kinsan halin kauyen nan da kama abu ina tsoron sharrin su".


"Ya zamuyi Fatima waye zai iya dakatar da ita baban kune kuma baya nan sharrinta bazai tasiri ba domin muna da gaskiya ita kuma 'karyarta koda tayi fure bazatai 'ya'ya ba dan 'karya 'karya ce koda an lullubeta da sutura".


"Shikenan umma zan dage da addu'a Allah ya saukaka min abinda ke damu na yasa karshen wahala ta kenan".


"Yauwa Fatima haka nake son ji Allah ya miki albarka ya had'a ki da abinda zai zamo alkairi a rayuwarki".


"Ameen umma nagode da addu'arki da kyakkyawan fatan ki gareni" Fati ta fada cikin jin dadi.


Page 37 to 38
Bayan wata d'aya Mami na zaune a daki ta zuba uban tagumi naban tausayi ta rame tayi duhu saboda damuwa da rashin kwanciyar hankali.


Sallama wata mace tai tana cire nikaf din fuskarta ta zauna kusa da mami tana kallon ta tace .


"Haba Aisha kina rage yawan wannan tunanin da kike saikin dorawa kanki hawan jini garin wanke biyar a 'bata goma".


Numfashi me zafi mami ta fitar tana kallon 'kawar ta tace "humm Halima hawan jini kuma na nawa zai hauni saidai nasha magani taya damuwa ta zata kare alhaji ya'ki karbar bada hakuri na".


"Aisha kina ji ki kwantar da hankalinki Mustapha mutun ne me hakuri may be bango kika kaishi yadau zafi dake haka amma idan ya huce komai zai dawo daidai".


Jiki a, sanyaye mami tace "yanzu ba wannan ba da kikaje ya kukai dashi kinga alamar ya fara saukowa daga fushin da yake dani"?.


Kai Halima ta girgiza tace ""gaskiya ko fuskar da zamuyi maganar arziki ban samu ba karshe ma securities ne yasa suka fitar dani daga office din a wulakance kamar wacce naje maula".


"Amma nashiga uku Halima indai alhaji bai hakuri ya mayar dani ba banajin zan iya ci gaba da rayuwa ba tare dashi ba domin ina sonsa".


Gyara zama Halima tai "a'a karki ce haka ki sa a ranki zai hakura ya mayar dake amma dan Allah ki rage yawan damuwar nan zan sake komawa gurinsa nan da kwana biyu".


"Shikenan Halima na gode Allah ya saka miki da alkairi gaskiya ke 'kawa ta gari ce".


Daddy kam iya bango mami ta kaishi yama rufe babinta a rayuwarshi ya manta da wanzuwarta balle yai tunanin dawo da ita gidansa aiyukan sa kawai yasa gaba.


Wannan hakan dayai na nuna halin ko'in kula ba karamin tsorata mami yai ba ya firgita mata kwakwalwa ya ruda mata tunani ya juyar mata da hankalinta".



Har ciwo ya kama ta an kaita asibiti Sadiq na kula da ita sosai haka Al'ameen da Afeeyah kullum suna gurinta domin duk lalacewar uwa uwace.


Sunyi matukar damuwa da ciwonta daddy ya sani amma yayi banza ya nuna ko a jikinsa ita yanzu ba matarsa bace bata da wani nauyi akansa.



Haka ta 'karaci jinyarta ta shafe satika harta warke baiko le'ka asibitin da sunan ya dubata ba tayi kukan nadama da dana sani harta gaji.



Ganin halin da take ciki da yake mahaifinta mutum ne me hikima dattijon kirki me aiki da hankali da tunani ya kira daddy har gida.


Dole daddy yazo saboda yana matukar girmama tsohon yana ganin darajarsa cikin dabara da basira baba Ibrahim ya tarbi daddy da magana me dad'i.


Cikin fara'a dason gyara musu al'amarinsu ya soma tambayar daddy da kuma lafazi me kyau yake bashi hakuri da nuna bacin ransa akan halayyar mami.


Sannan ya kira ta yai mugun sa'ba mata ya kuma ce lallai ta aikata babban zunubi ta bawa daddy hakuri.


"Dama abinda take nema kenan wata silar daidaituwar su tazo dan haka da taga ta samu dama haka ta dage da kukanta sosai ta rika bashi hakuri da rantsuwar baza ta 'kara ba.


Saboda kunyar baba Ibrahim daddy ya karbi daba hakuri domin badan darajar saba shida Aisha saidai idan zance ya tashi tace da ta aure shi.


A ranar saboda zumudi mami taso binsa ta koma yace a'a sai satin sama zai turo driver yazo ya dauketa bataso hakan ba amma zuciyarta mamaye take da farin ciki.


Satin nan jinsa take kamar shekara ko baccin kirki batayi saidai tunanin daddy da mafarki komawa gidansa.


Lalle da kitso mekyau taje aka tsara mata tai fes da ita tasha sabon dandakeken dinki tayi kwalliya fada sosai baba Ibrahim ya sake mata sannan ta fito 'kawayenta biyu zasu rakata.


Halima da hajiya Maryama sai tsiya suke mata a mota har suka je gidan zama sukai saida daddy ya shigo sannan suka tafi.


Suna fita mami ta diro daga kan gado tana durkusawa a gaban daddy dake tsaye tare da rike kafafunsa hawaye na zuba a idonta ta soma magana.


"Alhaji dan girman Allah ka yafe min abinda nai maka nasan kayi hakuri da halina ina rokon ka kada ka gajiya nayi kuskure amma yanzu zan gyara ka yafe ni".


Daddy baiyi magana ba sai kallonta da yake ganin irin kallon da yake mata kuma bai tanka ba taci gaba domin tana son goge laifinta".



"Alhaji ka bani dama a karo na karshe ni kuma nayi maka alkawari zan gyara abubuwan dana 'bata maka fushinka a kaina barazana ce ga rayuwata ka yarda dani wallahi ina sonka kuma ina son ahlin ka na tuba kayi hakuri dan Allah".


Ta karasa maganar tana fashewa da kuka ganin har lokacin kallonta yake kila bai gamsu da abinda tace masa ba'.



Allah sarki zuciyar musulunci d'agota daddy yai daga durkushen da take saboda kada kafafunta suyi ciwo yana mikar da ita tsaye ya goge mata hawayen๐Ÿ˜‰๐Ÿ˜œ.


Muryarsa a daidai yace "shikenan Aisha ya wuce Allah ya yafe mana baki daya".


๐Ÿ‘‰ 39 to 40
Washe gari da safe suna zaune a palor Afeeyah ta fito da saurinta suna gaisawa tai hanyar fita.


Mami data bita da kallon yaushe rabo tace "Wai Afeeyah baki ganni bane ina zuwa haka? maimakon ki zauna mu wuni".


"Dan juyowa Afeeyah tai tana cewa "am mami kiyi hakuri saina dawo sauri nake domin mun fara jarrabawa".


"Ok shikenan to saikin dawo Allah ya bada sa'a".


"Amin Afeeyah tace tana fita.


Al'ameen dake kusa da Sadiq cikin tsokana yace" ni kuwa daddy ya batun auntyn nawa naji shiru har yanzu"?.


Cikin mamaki daddy yace "wacce irin aunty kuma kake nufi"?.


Kamar gaske Al'ameen ya gyara zama yana cewa "daddy aunty na mana dama gurinta zakaje ran nan amma bakace nazo nai maka rakiya ba"'.


Da sabon mamaki daddy ke kallonshi amma ganin yana kallon mami yasa ya fahimci tsokanar mamin yake.




Dan murmushi daddy yai yana mazewa kamar gaske yace" ayya sorry sorry Aminullahi auntyn ka tana lafiya ko jiya da mukai waya da ita tace na gaishe mata da autan ta".


Baki Sadiq ya bude yana kallonsu Al'ameen yaci gaba "daddy yaushe ne auren fatan an kusa domin nine zan mana anko mami wanne kallar atamfa ko less kike so"'.


Mami dake kallon Al'ameen jin shine me maganar a kara mata kishiya dukda tasan laifin tane itace tai sake jitai hawaye zasu zubo mata da sauri ta mayar dasu tana mikewa tabar palaon.


Daddy dahar lokacin yake murmushi yace "wato Al'ameen ashe kaima 'kafar baya ne๐Ÿ˜? gashi kasa maminka kishinta ya motsa zatai kuka".


"To ai daddy dama nasan haka zata faru kishin nata nake son gani dama manya ma suna kishi akan tsohon mijins.............


Rufe baki yai yana kallon daddy yace "sorry daddy ina nufin soyayya tsohuwar zuma tafi".


Kai daddy ya girgiza yana mikewa zai fita yace "Allah ya shirya min kai auta na nabiye maka kasa mata ta kuka".


Daddy na fita Sadiq kamar ana tsikarin shi yace" kai daddy dama aure zaiyi ban sani ba a ina ya samu lady"?.


Dariya ce ta kama Al'ameen yace "wato kaima kayi zaton da gaske ne ba wata lady dazai aura kawai shiri nane mami nake tsokana"'.



Sadiq yace "koda naji nidai nayi mamaki yanzu dai muje kamin rakiya yau tunda kana hutu" mikewa yai suka fita'.


Da dare lokacin da daddy ya dawo ganin Afeeyah a palor ya tambayeta.


"Daughter ina maminki"?.


Dagowa Afeeyah tai tana cewa "sannu da zuwa daddy mami tana part dinta batajin dadi zazzabi ke damunta".


"Ok bari muga" wucewa yai zuwa part dinta kwance ya sameta lullube da bargo yaye mata rufin yai yana kunna hasken dakin yace " Aisha".


Bude ido mami tai ganin dady tsaye yasa ta tashi zaune tana jingina bayanta da fuskar gadon.


Cikin alamar tambaya daddy yace "baki da lafiya"?.


Muryar mami na rawa cike da damuwa da tsananin kishi tace "alhaji da gaske ne abinda kunnuwa na sukaji dazu da safe aure zaka kara"?.


Kallonta daddy keyi haba yasan zafin kishin mami a kansa tun kafin ya aureta".


Mami da zuciyarta tai mata nauyi tace "alhaji kaban lokaci na gyara kuskure na idan kayo aure a wannan halin da muke ciki komai cakude min zaiyi dan Allah karka min kishiya".


"Aisha wai waye ya fada miki aure zan karo Al'ameen tsokanarki kawai yake amma ni banida ra'ayin zama da mata biyu karki damu komai ya wuce".


Sauke ajiyar zuciya mami tai tana cewa "amma sai naci 'kaniyar Al'ameen wato kakarsa ya mayar dani๐Ÿ™„".


"A'a karki taba min auta na babu ruwanki dashi idan ba haka ba muhau sama mu fad'o".


Dariya mami tai tana cewa "shikenan tunda abin son kaine".


Dan shiru tai kamar mai tunani zuwa can tace "alhaji gobe zanje garin ku".


Da mamaki sosai a fuskarsa yace" wai kina nufin kauye na"?.


"Eh ina son na gyara mu'amala ta da kowa sannan yarinyar nan Fatima nadau hakkinta zan bata hakuri kuma na taho da ita ta dawo dakin mijinta ta haihu".


"Dakyau Aisha kin kyauta kuma naji dadi na gode idan kinje da kwana biyu zamu biyo bayanki".


Kai mami ta jinjina tace "ina son atamfofi da kayan abinci na tafi dasu".


"Ok yayi zansa a kawo miki komai da kike bukata".

Page 41 to 42.
Washe gari haka mami tai sammako kamar kasar zata bari dan zumudi ba daddy ba hatta su Afeeyah mamaki ne ya kamasu.


Lokaci da mami taje Fati ta fara nema amma bata gidan taje wuni gidan kakannin ta na uwa.


Data dawo Salamatu ta sanar da ita mami na nemanta mamaki ne ya kamata amma tai burus bataje ba domin babu abinda zatai mata ko tace mata.


Kwanan mami biyu tana bin Fati tazo zasui magana amma harsu daddy suka zo garin Fati bata yarda sun hadu ba".


Gidan hajiya ma ta koma da zama gabadaya saboda bata son ganin mami.


Da kuka mami ta fadawa daddy Fati ta'ki sauraronta kwantar mata da hankali yai ta hanyar cewa zata hakura saita huce.


Su Sadiq na gidan hajiya sai jikin magriba Al'ameen da Fati suka fito saidai shima taki warewa ta masa magana wai tunda tazo gida bai biyo bayanta ba.


Ta danyi tafiya mai nisa ta waiga ta gano shi acan baya saitin dabar samarin anguwarsu yayi kneel down, komawa tai tana cewa "ka taso mana mutane fa suna kallon mu".


Komawa kalar tausayi yai yana miko mata hannu yace "bazan tashi ba saikin daga ni da kanki".


Zaro ido tai tana kallon yadda mutane suka zuro musu ido tace ",nidai ka tashi kona tafi".


"Allah Zarah bazan tashi ba saidai ki daga ni".


Ganin an kira sallah idan ta biyeshi zasu 'bata lokaci yasa dole ta mika masa hannu rikewa yai yana murmushi ya mike tsaya yana manna mata kiss yace.


"I love u my wife".


Kunya ce ta kamata tana kokarin zamewa daga jikinsa yaki sakinta ya rike mata hannu ya fara tafiya da ita dole ta bishi har cikin gidansu bai saketa ba saida yaji muryar ummanta.


Bayan sallar isha daddy yai kiran Fati dasu salamatu ya musu bayanin komai ya kuma basu hakuri.


Mami harda kukanta ta rike hannun Fati tana bata hakuri da mata magiya abinda bata taba yiba".


Saboda daddy da kuma Al'ameen yasa tilas Fati tai hakuri ta yafe mata jin daddy yace idan zasu tafi tare da Fati zasu wuce ta koma dakin mijinta.


Mikewa Fati tai tana kuka ta fita haduwa sukai da Al'ameen ganin tana kuka yasa ya riketa yana yin bangaren muntari baban su da ita.


Har daki yana goge mata hawayen yace "meke damunki"?.


Kaita girgiza tana cewa babu komai".


"Amma kike kuka? fada min damuwarki".


Ganin ya zauna yasa tace "ka zauna akan gadon baban mu"?.


Gira ya dage "eh madam to mene a ciki"?.


"Amma dai gadon surukin kane".


"To Zarah surukin nawa ba ubana bane"?.


"Duk da haka".


"Ok yayi to zo mu kwanta bacci nake ji".


Zaro ido tai "anan din? gaskiya a'a bazan kwana anan ba".


Juyawa tai zata fita ya dauketa yana dorata akan gadon yace "wannan daga baya kenan kwana kam sai kinyi".


Zatai magana ya rufe mata baki da nasa yana bata kiss mai d'umi wanda yasata sauke ajiyar zuciya.


Zuge zip din doguwar rigarta yana zura hannunsa ciki da sauri Fati ta kankameshi tana kwantar da kanta akan kirjinsa".


Da yake cikinta ya riga ya tsufa saita dabara yadan karkata ta ta gefe ya shigeta yana binta a hankali sakamakon yanayinta.

Page 43 to 44.
Washe gari tun kafin asuba tayi ya tasheta suka shirya anayin sallah suka wuce Abuja.


Da safe kowa yana zuba idon yaga ta inda zasu bullo amma shiru Sadiq daya shigo jin ana cewa ko suna gidan hajiya.


Yace ai yanzu kam Al'ameen yana Abuja domin gida suka tafi shida Zarah motarsa bata nan" mamaki ne ya kama kowa ganin basuyi sallama ba.


Kwana biyu da tafiyarsu daddy ma suka bi bayansu a ranar da suka koma suka tarar Fati na asibiti.


Dukka asibitin sukaje a lokacin Fati harta haihu ansamu baby boy farin ciki kamar basu taba jika ba sai akansa mami har mamaki ta bawa kowa ganin yadda take rawar jiki.


Da aka sallameta gida mami ta wuce da ita domin ta bata kulawa Afeeyah kam tana tare da babyn.


Kulawa sosai mami take bata kuma kusan kullum saita nemi yafiyarta bisa abinda tai mata tayi kas dakai ta bata hakuri, Fati kuma tana nuna mata cewa babu komai ya wuce ita mahaifiya ce a gareta.


Ranar suna baby yaci suna LABEEB sunan abokin Al'ameen wanda sukai makaranta tare.


Zainab na shigowa gidan da yake tunda ya saketa bata gari tana zuwa ta rungume mami tana kuka.


Cikin mamaki mami tace "ke lafiya kukaan me kike".


Zainab bata iya dakatar da kukan da take ba ta rike hannun mami tana cewa "mami da gaske ne abinda nake ji wannan yar kauyen ce ta haihu tare da Al'ameen ko mafarki nake kunne na baiji daidai ba"?.



Mami tace "wanne irin mafarki kuma Zainab? Bayan gashi kinga zahiri Allah ya azurta Al'ameen da samun d'a namiji ya sanya masa sunan abokin sa Labeeb".

A rude Zainab tace "dan Allah mami kisa baki ya mayar dani dakina wallahi zamuyi zaman lafiya nayi nadama ina son Al'ameen".


Kai mami ta girgiza "a'a Zainab da dayanzu ba daya bane kada kije ki sake gurbata musu zaman su Fatima Zarah ce ta dace da Al'ameen".


"Nima na dace dashi mami kalli ki gani ya zauna da yar kauye ma balle ni tashin birni nasan komai".


"Ai Zainab da kikasan komai sanin naki baiyi amfani ba tunda kika samu damar zama dashi bakija hankalinsa ba yanzu kam saidai nace kiyi hakuri duk abinda zai takura rayuwar Al'ameen bana kaunarsa".


"Mami me kike nufi kenan na hakura dashi"?.


"Eh abinda nake nufi kenan ki barshi yai rayuwa da matarsa itace za'binsa domin wancan karon

2 Comments On DAN MILLIONAIRE
avatar
zainab-ibrahim-8

9 months ago

Reply

Thank

avatar
zainab-ibrahim-8

9 months ago

Reply

Than

Please Login or Register in order to submit comment