Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sakawa ba yadan kontar da sumar shi duka ba Wai wani yawa ne da ita ba.plant shues ya saka marar nauyi ya fita daga cikin dakin.



Akan doguwar kujera ya tadda ita zaune tana faman aikin nata na dannan waya.sai a sannan ya tina da wayar shi daya manto bisa gado,Dan haka ya juya da baya,Yana dauka ya fita daga gidan Yana ji tana yimai magana ya shareta yayi wucewar shi.

Driver yaga ya dauko su Arfat daga isalamiyya Dan haka ya tsaya.suna hango shi suka fito da gudu suna oyoyo Abbah.

Da daddaya ya rings cabe su Yana daga su sama cikin farinci har ya dire su duka ukku.

"Abbah ka siyomana shawarma"Cewar Ahmed da shi ne babban cikin su.


Hannun shi ya kamo Yana cewa "ku Bari na dawo saina tahomaku da itaAmmafa da sharadi duk sai kin kawo haddar yau kafin kowa na bashi".
Yana yimashi murmushi.


Dukansu suka amsa da eh mun yada Abbahn mu.

Kansu ya shafa Yana saka masu albarka.
"Tau kuje a ciremaku uniforms din kuyi sallah kafin na dawo,dan yau ba zuwa masallaci a tare saboda acan zanyi salla ta". Yana daga masu hannu alamar bye- bye a lokacin har sunkai bakin kofar.


Da addu'a dauke a bakin shi Yana fara Jan motar mai gadi ya bude mai kofa ya fice daga gidan,a ranshi yana addu'ar Allah ya shirya zulaihat ta gane illar abinda take aikatawa tun kafin ta hallakar da su gaba dayan su.


Gab da magriba ya isa cikin asibitin,derect fakin ya nufa,Yana shiga yaga harta farka doctor Yana Kara dubata.sai a sannan ya tuna da bai siyo masu abinci ba dan shima Yana jin yunwar,Amma tashin hankalin da yake hangowa bazai barshi ya iya saka wani abu a bakin shi ba.


Kudi ya Kara ba wannan saurayin Yana umartar shi daya siyo masu abinci a wani gurin mafi kusa.


"A a ranka shi dade na dazuma daka bayar sun isa dan ba abinda aka bukata har yanzu"cewar saurayin Yana Dan dukawa alamar girmamawa.


"Ok Tau nagode jeka dawo"shi Kuma Yana zama kan kujerar dake kusa da gadon.

Bayan ya fita doctor yake Kara yimai nayani Kan "cewar ai yarinyar hawan jini take da akwai,Amma raunikan Basu da yawa,ta tsorata ne shiy saka ta doguwar suka"cewar doctor.

Godiya yayi mai Yana cewa "please Dan Allah ka samoman wacce zata dan zauna da ita kafin taji sauki na sadata da iyayenta,Dan wallahi ban santa na a hanyata ta komawa gida na kadeta ba tare Dana lura"Yana shafa Dan siririn hancin shi.


"Ok ba damuwa officer insha Allah zamu taimaka maka,saboda kaima mun sanka da taimakon Al'umma"cewar Doctor Yana fita daga room din.


Jim kadan ya dawo wata yarinya na biye da shi a baya."Yauwa wannan zata taimaka mata kafin muga yadda jikin nata yayi".cewar doctor.



Godiya yayi mai Yana Mika mai kudi aba yarinyar da zata kula da ita.ansa tayi tana yimashi godiya.


Bayan sun fita saurayin nan ya dawo hannun shi rike da ledojin takeaway da na ruwa da sauran kayan bukata.ajewa yayi Yana sanar mai da ya kawo.

A tare suka fito sai yarinyar da suka Bari danta taimaka mata.

Layin da ya dauko saurayin ya nufa,a daidai kofar gidan shi ya sauke shi,akan cewar zuwa da safe ya binciko mai gidan su yarinyar.da haka suka rabu ya dauki hanyar gidan shi zuciyar shi cinku she da tinanin irin matsalolin da suke addabar rayuwar shi.
















*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~* .



👏👏👏👏👏
[4/2, 6:17 AM] Hayat: 🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️

*short story*

*true life story*


*LABARI/RUBUTAWA*


*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*


*MARUBUCIYAR* 📚🖊️

🤦 *ZAMANINMU* 🤦


*AND NOW* 👇

🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️


________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*


*ALHAMDLILLAH NA* *DAWO DAGA HUTU* *LPY,INA ADDU'AR ALLAH* *YA KARAMANA* *LPY DA DA* *KONCIYAR* *HANKALI,ALLAH KASA* *ABINDA ZAN RUBUTA* *YA FADAKAR DA* *AL'UMMAR* *MUSULMI,KUSKUREN* *DAKE CIKI ALLAH KA* *YAFE MANA.*

*Masha* *Allah my fns* *zamu dora daga inda* *muka tsaya,Dan yanzu* *wasan ya fara* 🤣.



*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI* .



PAGE 9️⃣➡️1️⃣0️⃣

📝Da asubar farko ta farka zame jikinta tayi zuwa dakinta.alwala tayi kafin ta tayar da sallah.shiko saida aka tada kabbara kafin ya tashi da a gaggauce yayi alwala kafin ya nufi dakin su Ahmed.taddawa yayi mai aikin ta tayar da su sunyi alwala,Dan haka ya kama hannun su suka nufi masallacin cikin unguwar.zulaihat tana idarwa kitchen ta shiga dan hada kayan breakfast.karfe bakwai aka tafi da su Ahmed islamiyya.shiko yahau Shirin office kasancewar ranar laraba ne.yana gyara maballin ruganshi ta shigo dakin cikin kolliyar kananun Kaya wandon juens da teashet mai dogon hannu,sai Dan siririn mayafi data dora bisa kanta.karasa saka mai maballin tayi tana murmushi shima mayar mata yayi Yana kollan cikin idonta.hannunshi ta kama zuwa falo akan dinning area ta zaunar da shi tana zuba mai breakfast.kallonta kawai yake yi ganin yadda ta Kara kyau,shi harga Allah Banda larura mezai saka shi neman matan waje?Amma Yana Addu'ar Allah yasa ta daina halinta.baisan ta gama zubawa ba saida ya ji tana hura mai iskar bakinta a idonshi kafin ya dawo tunanin shi.da haka suka fara cin abincin harya karasa.ganin har karfe tara ta kusa.har bakin motar shi ta rako shi saida ta tabbatar ya fita kafin ta daina daga mai hannu ta wuce cikin gidan.

Shiko A S P Habib derect gidan Mama ya nufa, kasancewar bayan layin su ne yasa dandanan ya karasa.shiru ya ji gidan ganin Bata a falonta yasaka shi karasawa a kuryar dakin ya risketa Kan abin sallah ga kayan fruits a gaban ta.
"Assalamu Alaikum"cewar A S P Habib Yana karasawa kusa da ita.
A hankali ta juyo tana amsa sallamar ganin shi ne yasa ta ce "Habibu harka fito?"
"Eh Mama na fito,Ina kwana?"
"Lafiya Lau,ya iyalin naaku?"
"Duk suna lafiya,yaran sun tafi isalamiyya".
"To Masha Allah,Ina maganar da muka yi da Kai?"
Dan Kara sadda kanshi yayi,Yana jin faduwar gaba dan ya rasa amsar da zai bata.
"Da Kai nake Habibu ko banida amsa ne?"
"A a Mama Allah ya huci zuciyar ki,kidan karaman lokaci insha Allah a wannan karon baza'a sake samun matsala ba,zanyi kokarin ganin kin samu duk abinda kike so daga gareni"
"To Bari kaji na fadama wannan shi ne dama na karshe da zan baka idan ko ba haka ba zaka Sha mamakin hukuncin da zan dauka akan ka"tana cire glass din dake fuskarta.
Wata zufa ce ya ji ta karyo mai,hannun shi ya saka Yana gogewa cikin sanyi ya ce "insha Allah komai zai wuce,ki Kara hakuri ni kaina bana jin dadin abinda Zulaihat take aikatawa,Amma Insha Allah a wannan karon zan Bata mamaki"mikewa yayi "Bari na wuce office,idan akwai abinda kuke da bukata anjima da yamma zan dawo,saina taho maku da shi"
"A a muna da komai sai danyun kayan Miya da suka rage,Dan Naga kaman sun kusa karewa"cewar mama tana saka ayaba a bakinta.
"Tau zan kawo insha Allah"Yana fita daga gidan.a daidai bakin kofa ya gamu da Asabe mai yiwa mamanshi aiki.cikin girmamawa ta gaishe shi kafin ya fice daga gidan.

Office ya wuce har kusan karfe ukku Yana can kafin ya nufi gidan su Habiba Dan Kara duba jikinta,sannan ya tattauna da Babanta.

Bayan ya fita Mama ta sauke ajiyar zuciya tana jin tausayin danta Yana Kara ratsa jikinta,Dan ta fahimci kullin matsalar matar shi karuwa take yi ba raguwa ba.ga shi duk lokacin da yayi yunkurin Kara aure sai a samu matsala.karo ukku kenan ana saka ranar bikin shi ana fasawa.Daya yarinyar ta ce bata sanshi tun ana sauran sati biyu,saboda sunji labarin matar shi ta mallake shi sai abinda ta ce mai,ta biyun kuwa kawai an wayi gari ta rasa Wanda har yau an rasa sanadin mutuwar ta.duk iya binciken likitoci sun kasa ganowa,Dan Babu wani rauni ko wata alama da zata nuna kasheta akayi.hakan yasa suka hakura.cikon ta ukkun kuwa har saida aka saka Rana Diyar kanen Mama ce da yake a unguwar dosa,Bayan saka Rana da wata daya yarinyar kwatsam ciwon hauka ya sameta,Wanda tun daga lokacin ake faman neman magani har yaunzu ba'a dace ba.tun daga nan Mama take zargin akwai saka hannun matar shi a cikin wannan al'amarin.shiyasa ta dage da yimai addu'a,ta Kuma tsaye akan saiya Kara aure.Danta fahimci matar shi tana wahalar da shi,Kuma ta hana ya Kara aure.ajiyar zuciya ta Kara saukewa a karo na ba adadi tana goge hawayen da ta ji suna zubomata.dan ita abinda yafi bata takaici yadda Zulaihat ta rainata kwata-kwata bata girmamata,Dan ita a ganinta itace take saka Habibu Kara aure.ita ko wannan dalilin yasa ta kafe akan saiya Kara auren danta ga yadda zatayi da ita.da haka Asabe ta risketa tana wannan tunanin kayan break ta aje Mata kafin ta juya tana girgiza kanta.

Tun bayan fitar Habib daga gida zulaihat itama ta fita,sai yanzu karfe ukku take dawowa,Wanda ni kaina bansan inda taje ba.

A S P Habib kuwa gidan su Habiba ya wuce.a kofar gida ya iske Malam mahaifinta.wurin shi ya karasa a bisa tabarma cikin girmamawa suka gaisa "yaro ban wayeka ba dukda na ganka da Kaya irin na jami'an tsaro Allah yasa lafiya"cewar malam musa Yana sauraren shi Dan jin amsar da zai bashi.
"Eh Baba baka sanni ba,nine Wanda ranar na kawo Habiba.wallahi bisa tsautsayi na kadeta inata sauri Naga na koma gida.to a lokacin Dana zo Innajo taceman kana kasuwa,shiyasa na Kara dawowa Dan ganin ya jikin nata yake?"cewar A S P Habib Yana kar tonkwashe kafar shi.

"To to Alhamdlillah kwarai Habiba tayiman bayani,ba komai shi tsautsayi ai baya wuce ranar shi haka Allah ya kaddara saidai muyi fatan Allah ya kiyaye gaba.inji Malam.

"To nagode Baba Bari na karasa gida insha Allah zan Kara zagayowa"Yana mikewa tsaye.kudi ta ajemai kafin sukayi sallama ya wuce dukda dakyar ya amsa.

Zulaihat ce a kitchen tana ta kokarin ganin ta kammala girki kafin mai gidan nata ya Kara so.dan tasan yanzu Yana Kan hanya.a hankali ta kaga kular data zuba Miya a ciki wani kulli ne ta dauko daga cikin wata loka,koncewa tayi kafin ta barbada Dan kadan tana juya miyar sa spoon .kafin ta rufe tana mayar da maganin wurin data dauko shi.
A gajiye ya shigo gidan Dan haka da sauri ya dauki kayan shi Yana shiga cikin gidan.ko sallama baiyi ba jin motsi a kitchen yasaka shi bin hanyar abinda idon shi ya hango yasaka shi saurin komawa da baya Yana jin jiri Yana daukar shi.
Ita ko zulaihat ji tashi kaman hucin mutum a bayanta da sauri ta nufo jikin kofa ganin shi tayi dafe da kanshi Yana Jan numfashi.cikin bakinciki ya fara nunata da yatsa Yana cewa .............











✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*
[4/2, 6:17 AM] Hayat: 🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️


*short story*

*true life story*


*LABARI/RUBUTAWA*


*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*



*MARUBUCIYAR* 📚🖊️

🤦 *ZAMANINMU* 🤦


*AND NOW* 👇

🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*



*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*


*DA* *SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI* *JIN* *KAI* .



PAGE1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣



📝A ranar juma'a da safe kasancewar yara ba islamiyya,Kuma suna cikin hutun makarantar boko,hakan yasaka karfe shabiyu ya dawo daga office.lokacin da yayi Shirin zuwa masallaci suma Yaran an gama shirya su.har jikin motar zulaihat ta rakosu kafin ta koma cikin gidan dan cigaba da ayyuka ita da nafisa mai aikinta.
Cikin Nishadi Suka dauki hanyar masallaci.shadda ce maroum color a jikin shi dinkin manyan Kaya be,babbar rigar tasha aikin surfani mai color din zaren milk da ratsin baki a jiki.sai bakar hula da bakin cover shues daya dora.Ahmed da Arfat Suma kayan su iri daya da babbar riga irin ta yara da hulinan su.itako Khadija Abaya aka saka Mata pink color mai dan banzan kyau da tsada.sunyi Shar abinsu sai tashin kanshi suke yi.

Bayan idar da sallar juma'a derect gidan Mama ya nufa.tun kafin ya karasa parking a kofar gidan Suka fita cikin happy suka nufi cikin gidan suna kwana Kiran kaka!kaka! Gamu munzo barka da sallah.
Tana kuryar dakinta bisa abin sallah casbaha ce a hannunta tana lazimi ta jiyo muryar Yan jikokin nata.jitayi wani farinciki ya lullubeta .falo ta nufo Suma daidai sun karaso cikin falon.jikinta suka dane suna faman ture juna kowa Yana so ya jingina da jikinta.
Zama tayi tana cewa "Bari na zauna kada ku kayar da ni,bakwa jin magana idan baku zo ba bana jin dadi,Amma da zaran kunzo to bakina bazaiyi shiruba"tana rungume Khadija.
"A wallahi ku dagamin Mamata kada ku jimata ciwo"cewar Habib da yake bakin kofa yana kallonsu da murmushi dauke akan fuskar sa.
"A a Habibu tare kuke tafe kenan?,nayi tunanin direver ya kawo su"cewar Inna tana murmushi.
"Tare muka taho yau yini zasuyi maki,zakisha fama da rashin jinsu".
"To yazanyi idan basu zo ba bana jin dadi".
Asabe ta shigo tana kawo masu abinci.kasan kafet Suka sauko dukan su suka ci abincin, kasancewar daman haka sukeyi duk randa ya kawo yaran.

Habib shi ne bai bar gidan ba sai lokacin sallar la'asar,kafin yayi ma Mama sallama akan cewar da dare zai zo ya dauke su.yana fitowa wayar shi ta fara ringing.dubawa yayi Dan ganin Wanda yake Kiran shi.sosai yaji kirjin shi ya bada Dammmmmmm da karfi har saida jijiyoyin shi sukayi sanyi.sosai ya Kara ware eyes din shi akan fuskar wayar,A fili ya furta Ihisan ce yau take kirana,to meya faru ne?yake tambayar kanshi.harta katse bai daga ba saida wani Kiran ya Kara shigowa kafin yayi saurin yin picking.cikin sanyi ya ce "Hello Ihsan ya gida"Yana jingina da jikin motar.
Saida tayi shiru na wasu dakika kafin cikin gogaggiyar muryarta ta ce "wato da gaske bazaka neme ni ba ko?kaci moriyar ganga ka yada kauronta ko?to bari kaji ASP wallahi kodai ka aure ni ko Kuma duk matakin dana dauka akanka kaika jawo,gaskiyar maganar mutane da ake cewa kana tsoran matarka,na gano cewar tana aikata sihiri Dan kar ka karamata kishiya ko?to Bari kaji wallahi idan baka aure ni ba zanyi maganinku daga Kai har ita"mtssssssss taja wani dogon tsaki tana katse kiran.
Da karfi ya sauke ajiyar zuciya Yana Kara lumshe eyes din shi.shi wallahi harya manta da ita duk a tunanin shi bata cikin garin kaduna,Dan tun haduwar su ta karshe da sukayi fada akan maganar dole saiya aureta shi Kuma yace a a bazai iya aurenta ba,to shi ne sanadin rabuwar su saifa yau da take neman tayar mai da hankali.
Cikin azama ya shiga Motar ya bata wuta Yana mai barin cikin layin.

A kofar gidan su Habiba yayi parking,wani karamin masallaci ya gani kusa da gidan anan ya samu yayi alwala ya gabatar da sallar la'asar.kafin ya karasa kofar gidan.Wani yaro ya aika a kirata.yaran dawowa yayi yace Wai innajo tace inji waye ne?
"Kace inji ASP Habib ne"cewar Habib Yana Kara tsayawa jikin wata bishiya.

Ba bata lokaci Habiba suka fito tare da yaron daya aika.naira Hamsin ya ba yaron kafin ya dubi inda Habiba tayi tsaye.
"Baki iya sallama ne ba"da sauri ta ce "Assalamu Alaikum,Ina yini"tana Jan gefen hijaf dinta"
A gajarce ya amsa Yana cewa "Malam bayanan ne "
Cikin yin kasa da Kai ta ce "ya fita tun dazu,Amma nasan yanzu zai dawo dan zai fita da kayan Miya"cewar Habiba.
"Ok"kawai ya ce yana faman latsa wayar shi,wani sako ne yaga Ihsan ta Kara turo mai bai duba ba kawai ya kyaleta.
Dukan su shiru suka yi na wasu Yan dakiku kafin a hankali ta ce "zan shiga gida aiki nake yiwa Innajo"Dan ji tayi kafafunta sun fara yin sanyi saboda tsayuwar data Sha.
Bai tankata ba saima Kiran waya daya shiga faman yi.
Daga bayan su Malam yayi sallama.dukan su suka amsa sun juyawa bayan su.Habib kashe wayar yayi Yana amsar ledar da take a hannun malam.har zata shige cikin gidan malam ya ce "Anshi Habiba Kai ciki kafin na shigo"cikin ladabi ta duka ta amsa kafin ta wuce cikin gidan.
Mayar da hankalin shi yayi ga Habib bayan sun karasa gaisawa ya ce "Habibu Daman Ina son ganinka akan wani taimako da zaka yiman"cewar malam Yana yin kasa da kanshi.

Cikin jimami Habib ya ce "to malam Ina jinka,insha Allah zan taimaka maka da iya abinda Allah ya horeman"Dan shi harga Allah Yana da tausayi.

"Akan maganar Habiba ne,Dan Allah nace ko zaka taimaka na baka auren ta danta huta da wannan ukubar ta mai dakina?"Yana zubar da kollah.
Da sauri Habibu ya dago da kanshi Yana kallan tsohon,Amma ganin yadda babba da shi Amma hawaye ke zuba ta idon shi,sai yaji jikin shi duk yayi sanyi.a hankali ya motsa labban shi ya fara cewa.. .................















✍️✍️✍️✍️✍️✍️


*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*.
[4/2, 6:17 AM] Hayat: 🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️


*short story*


*true life story*


*LABARI/RUBUTAWA*


*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*


*MARUBUCIYAR* 📚 🖊️

🤦 *ZAMANINMU* 🤦


*AND NOW* 👇

🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️
________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*



*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* .




PAGE1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣


📝me..ne.ne kike zubawa a cikin abinci na?Hannun shi dafe da saitin zuciyar shi.cikin sauri ta karasa riko shi tana jin faduwar gaba kaddai ace mutumin nan ya ganta.cikin dakiya da nuna jarumta ta fara cewa "nifa gishiri ne naji kaman bai karasa ji a miyar ba,shi ne na Kara Dan kadan barima na dauko ka gani"ta zuya kichin din da sauri.lokar ta daga wani robar gishiri dauko tana nuna mai.sai a lokacin yaji hankalin shi ya konta.dukda bawai Yana zargin matar shi kamar yadda Mama take sanar mai ba,Amma Yana Addu'ar Allah yasa kada ta cutar da shi.
Saurke miyar tayi kafin suka karasa bedroom dinshi.ruwan wanka ta hadamai tare da taimaka mai ya fitar da uniforms din shi.tana ganin ya shige toilet ta sauke ajiyar zuciya tana goge goshinta jin wata Yar zufa tana feso Mata.A zuciyarta ta ce Allah ya taimake ni,yau da asirina ya tonu.

Bayan ya kimtsa ta gabatar mai da abinci.cikin yin Bismillah ya fara ci itako ta fita.
Yana cikin cin abincin yaji ringing din wayar shi dauka yayi ganin sunan Mama akan screen din wayar.bayan sun gaisa yake cewa gashi nan yanzu zai kawo kayan miyar,kafin ta katse wayar.
Key din motar shi ya dauka da wayan shi,cikin sauri ya fita.a bakin falo ya risketa da waya a hannunta ga dukkan alamu kirane take yi.nufoshi tayi tana tambayar "Abban Arfat Ina zaka je da yammacin nan"tana Shan gaban shi.a gajerce ya bata amsa"Mama take kirana zan kaimasu kayan Miya"Yana fita ya nufi parking space.bata rai tayi tana jin wani bakinciki Yana taso mata.cikin jin haushi ta ce "Yanzuma ba zata barshi ya huta ba,kullin tana faman neman shi,Kai nidai na bani da wannan mata"mtssssss taja tsaki tana zama Kan kujera.

Shiko A S P Habib Yana fita ya tsaya wurin masu kayan Miya ya ciyan masu dasu kabej,cocunver, carrots,da sauran kayan ganye.da haka ya karasa .

Yana shiga Asabe ta anshi kayan tana yimai sannu da zuwa.amsawa yayi Yana shiga cikin falon.A saman kujera ya risketa bayan ya kara gaisheta ya bata hakuri akan bai dawo akan lokaci ba.
"Ba komai Habibu kana kokari,Daman Aliya ce ta kirani tana bukatar jari zata fara Business kasan zaman hakanan ba dadi shi ne nace Bari na sanar maka"(Aliya kanwar shi ce )cewar Mama tana rage vollume din tv.
"To insha Allah zan bata,Amma Adan bani lokaci yanzu ba kudade sosai a hannuna"
"Tau Habibu kaima Allah ya baka masu yimaka"

Cikin sanyi ya amsa da "Amin ya Allah"
Daga haka ya mike sallama yayi Mata kafin ya fice daidai ana Kiran sallar magari ba.

A unguwar yayi sallah kafin ya nufi wata majalissar su gaba dakan da gidan shi gurin yake kasancewar duk abokanan shi ne nan yake zuwa suyi hira.tun shigar shi gurin suke janshi da cewar "ga mijin mace daya"wani a gefe da shi ne dan fari a cikin su ya ce "wallahi Habib sai na samo yarinyar da zata fi karfin wannan matar taka,Dan mun fahimci tsoron zulaihat kake yi shiyasa ka kasa Kara aure,kaga mu a cikin mu harda masu Mata ukku-ukku wasu bibbiyu.to ance dai mai Mata daya abokin gauro"gaba dayan su suka saka mai dariya.shima cikin tsokana irin ta abokai ya kallesu one by one ya ce "to naji ku biyu ne da ukku,ni duk randa na tashi karawa to guda ukku zan auro a rana daya kaga idan na hada data gida nayi hudu cif,Kuma daga su na rufe kofa"dariya Suka sakamai wasu na cewa bazai iyaba,wasu ko sunce su zasu hada kayan lefe.da haka sukayi ta hirar su irin ta abokai.anan sukayi sallar isha'i kafin ya wuce gida .suna tsoakanar shi da cewar madan tayi kiran mijin Hajiya .da haka suka rabu cikin Nishadi.

A Falo ya tadda ita da yara suna tilarwar karatun islamiyya.sunajin sallamar shi suka tashi da gudu suna yimai oyoyo.bayan ya gama gaisawa da su.Arfat ya ce "Abba mun dawo daga islamiyya bamu ganka ba"kallon yaranshi yayi cikin so da kaunar su Yana daukan Khadija ya ce "naje gidan Mama ne shiyasa baku ganni ba"
"Abba muma zaka kaimu?"cewar Khadija tana taba askin kanshi da babu hula.
"Insha Allah ranar juma'a daga masallaci zamu wuce ,ranar sai kuyi Mata yini ko?"
Cikin farinciki yaran suka amsa da "mungode Abban mu".dakin su suka wuce da litattafan su a hannun.

Cikin gajiya da san kasancewa da Matar tashi ya zauna kusa da ita Yana riko hannunta."Sweety ba sannu da zuwa"Yana kokarin Dora kanshi bisa kafadar ta.matsawa tayi tana turo baki,cikin jin haushi ta ce "to mezanyi maka ne?zargina fa kake yi akan zan cutar da Kai,shiyasa yanzu daka fita ka Dade baka dawo ba ko duk a gidan Mama kake?"

Cikin sanyi ya ce "common Zulaihat kiyi hakuri ya riga da ya wuce fa,bawai Ina zarginki ba bana so ne a samu matsala da zargi tsakanina da ke,Amma ni bana tunanin zaki cutar da ni,ki tuna tsawon shekaru sama sha ukku muna tare da ke"ruko hannunta yayi Suka nufi dakin shi,Yana Kara rarrashin ta.






✍️✍️✍️✍️✍️✍️


*~DAGA ALKALAMIN*~ *~AUTAH~*
[4/2, 6:17 AM] Hayat: 🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️

*short story*

*true life story*

*LABARI/RUBUTAWA*

*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*

*MARUBUCIYAR* 📚🖊️

🤦 *ZAMANINMU* 🤦

*AND NOW* 👇

🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*


*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*


*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI* .


PAGE 1️⃣9️⃣➡️2️⃣0️⃣


📝Habib tunda yaje majalissa ya kasa samun sukunu,domin ji yake yi kanshi Yana neman tarwatsewa saboda zafin daya dauka,Banda matsalar zulaihat ga wannan auren da ake kokarin kwakuba mai shi,uwa uba Kuma matsalar IHSAN dan yasan halinta Sarai idan har ta riga ta furta zatayi abu to ba makawa saita yishi.shikam ya godewa Allah,Amma Yana ta addu'ar neman zabin Allah a cikin wannan al'amarin.abokanshi ganin

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

1 Comments On ZAFIN KISHI
avatar
abasu-kala

11 months ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment