Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wanda ya fara sanunta.Amma sai samu time ya zauna da ita dan su sasinta idan kudi take bukata ya bata danta rabu da shi.da wannan sakar zucin ya tsaya masallaci dan gabatar da sallar azuhur.



Tun bayan fitar shi Zulaihat take faman yin waya,ga dukkan alamu akan maganar mai gidan nata ne saboda yadda ta zage tana ruwan masifa da kakkausar murya take cewa "wallahi idan har baki rabu da mijina ba sai nayi maganinki,karuwar banza karuwar wofi irinku ne masu kwace mana maza mu muna cikin gida ku ko kuna kokarin tarwatsa rayuwar mu,munafika nadai fada maki idan har baki rabu da Habib ba sai Kinga abinda zai biyo baya"tana Kara kaushin muryarta.
A daidai wannan lokacin IHSAN tana cikin dakinsu ita da Su Hannatu,dukan su sunyi shiru suna sauraren badakalar dake wakana tsakanin IHSAN da Matar Habib.ganin ta katse call din tana jan dogon tsaki yasa dukan su sukayi galala suna kallanta.
Cikin jin haushi Hannatu ta ce "kiramin nomber Habib ki bani Ina so nayi magana da shi"
To shi ne sanadin Kiran da tayimai Yana cikin mota yayi switch off na wayan.
Kallon Hannatu tayi tana kwabe fuska "Kinga ya kashe wayan"

"Ok kyaleshi zaiga abinda zai biyo baya,tunda haka ya zaba,ita Kuma wannan masifafiyar matar tashi sai mun aje tarihi a cikin rayuwarta,Wanda Koda ta zo gabar mutuwane saita bada labarin mu"tana wani munafikin murmushi mai ma'noni da dama.

Ajiyar zuciya IHSAN ta sauke tana jin zuciyarta tana yimata zafi.haka Suka ci gaba da tattaunawa akan irin matakin da zasu dauka.niko jefoni waje sukayi suka sakama kofar key dan kar naji abinda suke fadaπŸ˜‚πŸ˜‚.duk kwakwata nayin labe dan na jiyo maku tuggun da suke kitsawa Amma abin ya gagara dan haka nayi nan πŸƒπŸƒπŸƒ.

*Sai mun hadu a next* *page Dan jin yadda zata* *kaya tsakanin* *zulaihat da Ihsan* .





✍️✍️✍️✍️✍️✍️


*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*







πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘.
[4/2, 11:24 PM] Hayat: πŸ—‘οΈπŸ—‘οΈ *ZAFIN KISHI* πŸ—‘οΈπŸ—‘οΈ

*short story*

*true life story*


*LABARI/RUBUTAWA*



*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*



*MARUBUCIYAR* πŸ“šπŸ–ŠοΈ
ka
🀦 *ZAMANINMU* 🀦

*AND NOW* πŸ‘‡


πŸ—‘οΈπŸ—‘οΈ *ZAFIN KISHI* πŸ—‘οΈπŸ—‘οΈ


________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}?kafjfd
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*



*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*




*DA* *SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN KAI* .



PAGE 2️⃣3οΈβƒ£βž‘οΈ2️⃣4️⃣


πŸ“Akalla an dauki tsawon sati daya ana faman fafatawa tsakanin IHSAN da zulaihat inda har takai ga Habib ya sani domin baya da kwana ukku Hannatu taje har office dinshi sunyi magana inda anan ne take sanar da shi irin wulakancin da zulaihat take shukawa Ihsan,Wanda baya da masaniyar hakan dan ita Zulaihat kin sanar da shi tayi a cewarta zata dauki mataki da kanta.Anan dai yaba su Hannatu hakuri akan faruwar lamarin,Kuma a ranar da yamma su Abbah Hasan kanin Baban shi Suka je gidan su Habiba Kai kudin neman auren Habib.cikin mutunci aka tarbesu inda aka saka ranar daurin aure nan da sati ukku masu zuwa idan Allah ya nuna Mana.

A lokacin Habib ya dawo gida karfe hudu na yamma saboda ayyuka da suka yi mai yawa.dan haka a gajiye ya karaso cikin gidan.
Direct bedroom dinshi ya wuce kayan jikin shi ya cire kafin ya nufi toilet. Zulaihat bata ji shigowar shi ba tana kitchen sai Nafisa da take kusa da ita tana yanka kabej da albasa.fitowa tayi tana leken window'n cikin falon jin har yanzu shiru mai gidan nata bai dawo ba.Mamaki ya kamata ganin motar shi a wurin parking,a zuciyarta ta ce "To ya'akayi banji shigowar shi ba"tana wucewa zuwa cikin dakin shi.ganin ba kowa a dakin yasa tadan matsa jikin kofar toilet din,tana jin motsin ruwa yasa ya gane tabbas ya dawo.dan haka ta fito mai da kayan da zai saka na shan iska,ta Kara gyara dakin kafin ta koma kitchen din tana sakar zuci .

Tunda ya fito daga wanka yaga dakin yadan canza,ganin an fito mai da kayan da zai saka ya gane ita ce ta shigo.

Cikin farinciki yake shiryawa,dukda wani baren na zuciyar shi Yana jin fargabar sanar da ita,saboda yasan tashin hankali ne ba kadan ba,ga rigimar Ihsan data dameshi akan sai dai ya aure su su biyu.shi wlh ya rasa me yake yimai dadi,saukin shi daya Maman shi da take karfa fa mai guywa akan sha'anin dukda ya boyemata tsakanin shi da Ihsan.da haka ya karasa shiryawa ya nufo falon.cikin takun sanyi ya karaso tsakiyar falon ganin ba kowa yasa ya juya akalar tafiyar shi zuwa kitchen din inda anan ne ya ji motsin mutane.

Daga bakin kofar ya tsaya Yana kallonta ganin yadda ta juya baya tana aikinta,gani yayi tayimai kyau duda yaga kaman tadan rame saboda jikinta ya dan saki.

Ji tayi kaman ana kallonta shiyasa tayi saurin jiyowa,ganin shi ne yasa ta sauke ajiyar zuciya tana cewa "Wallahi harka saka na tsorata,yi hakuri nasan kana jin yunwa yanzu zan kawo maka abinci wanna kawai zan sauke just give me two minutes "tana murmushi ganin yadda ya tsareta da ido.
Baice Mata komai ba ya juya zuwa wurin dinning dan jiranta.



"Wallahi baka isaba,ni zaka wulakanta a unguwar nan saboda baka dauke ni a matsayin uwarta ba shiyasa zaka yi abu ba tare da kayiman shawara ba"cewar Innajo da take ta faman kunfar baki.ita ko Habiba tana cikin dakinta inbanda kuka ba aikin da take faman yi,tunda Babanta ya sanar da ita saka ranar auren da kayan saka ranar daya shigo da su cikin gidan shida kanenshi to ta rasa abinda yake damunta kukan dadi ne na zata rabu da jarababbiyar Mata Babanta ko na zata auri mai Mata ne,Wanda tana da tabbacin Babanta yasan halin matar tunda a bakinshi ta ji labarin irin fadan matar Habib da *ZAFIN KISHIN* ta,dukda ya nusar da ita akan komeye tayi Mata tayi hakuri ta kasance mai biyayya ga mijinta da abokiyar zamanta.

Da haka Innajo ta gaji da kunfar bakin ta dauki gyalenta ta zagaya makotansu.shiko Malam baice komai ya kyaleta,Dan shi ba ma'abocin fada ne ba.

Sosai Habiba take kuka Dan ita ta sadakas a haka rayuwarta ta zo da wannan kaddarar,tana Addu'ar Allah ya bata ikon cinye jarabawar nan.




Zulaihat bata jimaba sai gata ta fito dauke da katon tray ta jera kayan abinci akai.a gaban shi ta aje tana yimai sannu.cikin sanyi ya amsa Yana ci gaba da danna wayar shi.
Jolop din shinkafar ta zuba mai da taji kabeji da nama,tana turamai gaban shi sai zobo data hada mai sanyi ta Cuba cikin wani dan karamin cup mai kyau.gani tayi baya da niyar ci yasa ta kalleshi tana cewa"ya kamata kaci abincin kada ya huce,kafin kaci gaba da magana da budurwar taka"tana yimai kallan nasan komai.
Da sauri ya kalleta Yana aje wayar "wa yace da budurwa nake yin waya,ke kullun baki da zancen da ya wuce zargina,to yanzu misali idan akace maki zan Kara aure ya zakiyi ?Yana tsareta da kallo.Amma abin mamaki gani yayi ta saka dariya sosai harda kyakyatawa tana tafa hannu.
Shiko cokalin da zai Kai bakinshi ya aje Yana kallon ikon Allah,Dan shi rabon da yaga tayi dariya kamar haka harya manta.gani yayi ta Kara yin kyau ga kolliyar da tayi ta amsheta tayi das da ita.dan yasan Zulaihat tafi Habiba kyau,dukda itama Habiba ba baya ba ce.

Cikin dariyar ta ce "Abban Arfat kana bani mamaki,Ai Koda baka fadamin ba to nasan komai zaka Kara aure ko?yau aka saka ranar aurenka kaida Habiba ko?Kai yanzu kana tunanin zan barka ka zauna da wata Mata bayan ni?to kasani Habib dakai da wacce zaka aura da Wanda zasu daura auren naku wallahi kunyi kuskure da duk Wanda kake tunanin ya tsaye maka akan maganar wannan auren to a sannu duk zanyi maganin ku"ta mike tsaye tana jan wani uban tsaki mtssssssss,Dan tuni ta dade da daina dariyar da take yi..
Fuuuuuuuuuuu ta wuce bedroom dinta tana karkada hifs.

Shiko tsabar mamakin kalamanta galala yayi ya saki Baki da hanci Yana kallonta harta shige,kafin ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi Yana jin faduwar gaba.shifa irin wannan tashin hankalin yake gudu shiyasa tun tuni ya kasa Kara aure.shi yanzu ya zaiyi ga Ihsan itama ta tasoshi a gaba da fitina.shikam ya godewa Allah Dole yasan abinyi tun kafin wata rigimar ta Kara kunno Kai.







tunda Ihsan ta ji Karan wayar ta tayi saurin yin picking ganin Wanda yake kiranta.da sauri ta mike tsaye tana cewa "what Hudu meye kake San sanar da ni haka marar dadin ji,Dan Allah kada kasa zuciyata ta harba,kayi gaggawar karyata kanka"tana safa da marwa a tsakiyar falon sai faman goge zufa take yi dukda iskan fankar da take kadawa.daidai Hannatu ta fito daga kitchen da cup a hannunta bata ankare ba kawai sai gani tayi Ihsan ta fadi kasa a sume........




✍️✍️✍️✍️✍️✍️


*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*



[4/5, 6:03 AM] Hayat: πŸ—‘οΈπŸ—‘οΈ *ZAFIN KISHI* πŸ—‘οΈπŸ—‘οΈ

*short story*

*true life story*

*LABARI/RUBUTAWA*


*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*


*MARUBUCIYAR* πŸ“šπŸ–ŠοΈ

🀦 *ZAMANINMU* 🀦

*AND NOW* πŸ‘‡


πŸ—‘οΈπŸ—‘οΈ *ZAFIN KISHI* πŸ—‘οΈπŸ—‘οΈ

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*



*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*



*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI*


PAGE 2️⃣5οΈβƒ£βž‘οΈ2️⃣6️⃣



πŸ“Da gudu Hannatu tayi kan Ihsan tana sakin cup din hannunta.cikin dimuwa ta fara girgiza ta tana Kiran sunanta "Ihsan!Ihsan!!" Amma shiru kake ji.da gudu ta dauko key din motar ta kasancewar sauran yan'mata duk sun fita sai su kadai a gidan.wurin mai gadin su ta leka ta nemi taimakon shi Dan su sakata cikin motar,saboda Hannatu big girl ce bata mu'amulla da kananun kwari sai manyan garin hakan yasa take fantamawa.ko gidan da suke ciki wani dan kasuwa ne ya bata shi.

Da taimakon gate man Suka sakata cikin motar taja da gudu zuwa wani karamin asibiti dake cikin unguwar.cikin gaggawa aka amshe su.drip aka daura Mata tare da yimata allurai.


Habib ya dade a wurin dinning a zaune Yana juya cokalin hannun shi.tsabar kaduwa ya kasa cin abincin,a karshe ma tashi yayi ya kwashi wayoyin shi ya bar gidan Dan yasan a wannan lokacin zulaihat ba zata saurare shi ba.direct gidan Mama ya nufa.



Har aka fara Kiran sallah Habiba tana faman aikin kuka,saida ta ji Babanta ya tsaya jikin kofar Yana cewa "Diyar Albarka tashi kiyi sallah kinji,insha Allah Koda bayan raina ne zaki ji dadin rayuwar ki,ki Kara hakuri kinji komai lokaci gare shi"Yana jin shima kaman zaiyi kukan.

Jin muryar mahaifin nata yasaka ta ta fito tana goge fuskarta.shima fita yayi dan zuwa masallaci,itama tayi alwala ta koma daki dan sauke farali.



Uwar gayya zulaihat tunda ta shige dakinta ta bar Habib anan,saita sakama kofar key tana jingina da jikin kofar.hannuwanta duka ta saka tana dafe kanta saboda wani mugun sarawa da taji Yana yimata.ko maganar data yiwa Habib karfin hali ne kawai tayi,sai yanzu take jin kaman zuciyar ta zata tarwatse,wato ba Ihsan ce zai aura ba wata ce daban.to dole zata dora binciken ta akan wannan yarinyar da take kokarin shiga tsakanin ta da mijinta.sai hawaye cur cur suke zuba daga idonta.jin Karan wayarta yasa ta mike cikin sanyi tana wucewa gaban mirror inda wayar take aje.ganin sunan Ikilima babbar aminiyar ta yasa tayi saurin yin picking tana fashewa da matsanancin kuka.

Ikilima Bata yi yunkurin hanata ba saima shiru da tayi tana sauraren kukan kawarta ta,Dan tasan ayi haka saboda ta fahimci kawarta ta ta fita *ZAFIN KISHI* sannan bata iya boyewa da danne zuciyar ta akan shi.

Ta dau tsawon lokaci tana rera kukanta kafin daga bisani ta tsagaita tana sauke ajiyar zuciya."nasan meke wakana kawata"cewar Ikilima da take baiwa yar jinjirar ta tsotsa Wanda basu dade da yin arba'in ba.taci gaba da cewa "kina jina Zulaihat ki kontar da hankalin ki,saboda yanzu duk matakin da zamu dauka tofa da an samu akasi yasan cewa kece,Amma idan kika nutsu sai musan meya kamata muyi"
Ajiyar zuciya ta Kara saukewa a karo na ba adadi ta amsa da "To zan gwada danne zuciyata kodan ganin nayi nasara"tana mikewa tsaye.
"Yauwa ko kefa,gobe kice mai zaki je gidan ku,Kinga daga nan saiki biyo mu tattauna yadda zamu bullowa lamarin ko?"cewar Ikilima .
Amsawa tayi da "shikenan"tana katse call din.aje wayar tayi tana Saba da marwa a tsakiyar dakinta tana jin zuciyarta kamar zata fashe saboda wani kululu da yake yimata yawo a kirjinta.



a hankali Ihsan ta fara bude idonta tana kallon pop din saman dakin.da Sauri Hannatu ta aje wayar dake hannunta ta matso jikin gadon tana "sannu kin tashi,Bari na Kira Doctor"ta fita zuwa office din shi.

Bata wani Jima ba suka shigo tare,Bayan ya cire Karin ruwan ya Kara yin checking dinta ya tabbatar ba wata matsala,saboda sanadin shork din da ta samu ne tayi doguwar suma.anan ta rubuta masu discharge da kudin da zasu biya.bayan Hannatu ta biya suka nufi gida.


Tun a Mota taci gaba da kuka,Hannatu saboda haushi daya kamata kasa yimata magana tayi .ta kyaleta tana ta sharbar kukanta.suna karasawa gidan ta wuce daki ita Kuma Hannatu ta zauna a Falo tana Kiran waya .
"Hello mutuniyar inaso gobe da karfe takwas na dare ki zo gidana inason ganinki,akwai wani babban aiki da zaki yiman maganar kudi Kuma kada kiji komai ko nawane zan biya ki"tana jingina kanta jikin kujerar.banji amsar da aka Bata tana amsa da cewa "nagode saina ganki".
Ajiyar zuciya ta sauke a fili ta furta "sorry Habib saika yi nadamar cin amanar Ihsan da kayi"....













✍️✍️✍️✍️✍️✍️


*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*












πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘.
[4/5, 6:03 AM] Hayat: πŸ—‘οΈπŸ—‘οΈ *ZAFIN KISHI* πŸ—‘οΈπŸ—‘οΈ

*short story*

*true life story*


*LABARI/RUBUTAWA*


*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*


*MARUBUCIYAR* πŸ“šπŸ–ŠοΈ


🀦 *ZAMANINMU* 🀦


*AND NOW* πŸ‘‡

πŸ—‘οΈπŸ—‘οΈ *ZAFIN KISHI* πŸ—‘οΈπŸ—‘οΈ

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*


*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*




*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN KAI* .


PAGE 2️⃣7οΈβƒ£βž‘οΈ2️⃣8️⃣



πŸ“Da dare Habib bai Kara bi takan Zulaihat ba,itama tunda ta shige daki bata Kara fitowa ba,Koda su Arfat suka dawo daga islamiyya sai Nafisa ta canza masu Kaya sukaci abinci bayan ta saka sunyi sallar.tunda ya konta zuciyar shi take faman sake-sake akan wannan lamarin,Amma ba yadda zaiyi face addu'ar Allah ya zaba abinda yafi alkhairi.haka zulaihat itama ta kwana da faman tunanin Wai ita ce Habib zaiyiwa kishiya duk irin kulawar da take bashi,Kai shiyasa akace wasu mazan Basu da tabbas.


A bangaren gidan su Ihsan har su Hannatu suka gama firarsu a falon da sauran yan'mata ,Amma Ihsan tana daki taki fitowa saboda tashin hankalin daya sameta.tana bisa katifa ta janyo wayarta tana Kiran Habib Cikin sa'a taji wayar tayi ringing Aiko da sauri ta tashi tana goge fuskarta.
"Hello Yanzu Habib ni zanyi ta kiranka kana kashe min waya?saboda kasan baka kyauta min ba ko?"tana Kara fashewa da kuka.

Sosai yaji tausayin ta ya kamashi,Dan yasan kowacece Ihsan,yasan tana mutuwar sanshi Amma akwai dalilan da yasa bazai aureta ba.
Cikin sanyin voice ya ce "sorry Ihsan yi hakuri kinji gobe mu hadu zamuyi magana zanyimaki bayanin duk yadda abin ya faru kinji"Yana gyada kanshi kaman Yana gabanta.

Share hawayen fuskarta tayi tace "to Dan Allah ka daina kasheman waya idan na Kira ka kaji"

"Tau insha Allah bazan Kara katsewa ba,kiyi hakuri kinji?".cewar Habib Yana gyara konciyar shi.

Da haka suka katse kiran dukan su suna sauke ajiyar zuciya.

Wani farinciki taji a ranta jin muryar shi da tayi.Amma dukda haka dole ta hukunta shi.saboda yaci amanar ta.
Fitowa tayi falon cikin takunta.dukansu su Hannatu suka juyo suna kallanta ganin yadda take murmushi.

"Hmmm ga dukkan alamu ya daga wayar dan fuskarki ta nuna haka"cewar Baby da take konce kan doguwar kujera.

Karasowa tayi ta zauna kusa da Hannatu tana dora kanta bisa kafadar Beby cikin fargaba ta ce "Kunsan inason Habib,Amma daga yau dole na fara yaki da zuciyata dan ganin na cireshi daga raina,Hannatu na amince da hukunci da za'ayimai kodan mu kafa tarihi a rayuwar zulaihat".tana yatsina fuska kamar mai jin wari.

Gaba dayan su suka saka shewa da tafi suna cewa "sai Ihsan,sai Ihsan"kafin sukayi shiru suna sauraren Hannatu da take cewa "ki kontar da Hankalinki kinsan abokin sweetyna Yana ta kwawar sanki,Kuma da gaske yake yi don haka insha Allah baza'a samu matsala ba"

Da haka Suka ci gaba da tattaunawa har wuraren karfe dayan dare kafin kowaccen su ta nemi wurin konciya.


A washe gari Habib ko break bai samu ba,Dan lokacin daya fito Babu kowa a falon ya duba babu alamar an hada break dan haka ko dakinta bai leka ba ya wucewar shi.

Bayan ya tashi ya wuce wani kayataccen wurin cin abinci acan suka hadu da Ihsan ya Kara bata hakuri,alart yayi Mata na kudi masu kauri kafin suka rabu,Amma ita dai Ihsan jinshi kawai take yi,ita kadai tasan abinda take ji a ranta.


Tun bayan fitar Habib itama Zulaihat ta dauki jakarta da mayafi tabar gidan direct gidan kawarta Ikilima ta nufa.dan neman mafita........












✍️✍️✍️✍️✍️✍️



*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*






πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘.
[4/5, 6:03 AM] Hayat: πŸ—‘οΈπŸ—‘οΈ *ZAFIN KISHI* πŸ—‘οΈπŸ—‘οΈ

*short story*


*true life story*


*LABARI/RUBUTAWA*


*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*


*MARUBUCIYAR* πŸ“šπŸ–ŠοΈ


🀦 *ZAMANINMU* 🀦


*AND NOW* πŸ‘‡


πŸ—‘οΈπŸ—‘οΈ *ZAFIN KISHI* πŸ—‘οΈπŸ—‘οΈ



________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*




*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*




*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN KAI* .






PAGE 2️⃣9οΈβƒ£βž‘οΈ3️⃣0️⃣



*BAYAN SATI BIYU*


πŸ“Haka rayuwar tayi ta tafiya a tsakanin wadanna nan mutane.Habiba na dokin ganin sauran sati buyi bikinta,ita ko zulaihat tana ta kokarin ganin ta lalata wannan auren.A bangaran Ihsan kuwa yanzu hankalinta ya konta domin ganin suna gab da yin nasara yanzu ta koma soyayya da abokin saurayin Hannatu mai suna Alhaji Bukhar.

Yanzu duk wata hidima da Zulaihat take yiwa Habib to ta daina a cewar ta tunda har kyautatawar da take yimai a baya bata hana shi Kara aure ba to itakam yanzu ta daina harkokin gabanta kawai take yi.abincima idan ta dafa saidai ya dauko da kanshi a kitchen,daya sanarwa da Mama cewa tayi ya kyaleta neman fitina take yi.Hakan yasa ya tattara ta ya watsata a kondon shara.


Ana sauran sati daya daurin auren shi da Habiba aka Kai kayan lefe Wanda kanwar shi Fatima Suka hado su,Kaya sunyi kyau sosai akwati guda takwas sai jakukkuna guda biyu,kama daga leshin,atamfa,laffaya, materials,dogayen riguna .da sauran tarkacen kayan kolliya.Uwar gida akwati hudu yayi Mata da naira dubu hamsin kudin dinki ne da sauran abinda zata bukata,Dan itama ya zuba Mata Kaya sosai.


Lokaci zuwa lokaci yakanje gidan su Habiba su gaisa tunda haryanzu taki sakin jiki da shi ballantana su saba.dan hakane idan yaje basu wata maganar kirki yake yimata sallama.


Har yanzu bata canza zani ba ga rayuwar zulaihat dan ranar daya kawo mata nata akwatina yaga ruwan tijara da wulakanci.cewa tayi ya dauke kayan shi bata so Dan ba tsirara take yawo ba.


Ranar kasa bacci tayi,saboda ita da kawar ta Ikilima sunbi malamai da bokayen Amma abin ya faskara,a karshe ma wani malami cemasu yayi "tabi a hankali akwai wani tashin hankali da zai bayyana a tsakanin ita da mijinta,Wanda zai iya zama silar rushewar farincikin su".ita dai wannan magana ta tsaya a kokon ranta,hakan yasa ta kasa samun sukuni duk da tana tunanin kilama karya yake yimata dukdan ya torata tane.



Ana sauran kwana bakwai daurin aure yaje yaba Habiba kudin dinki da sauran hidimar da zatayi saboda ya fahimci bata da wasu kawaye.sannan ya sanar da Malam kada ayi mata kayan daki yasaka an yi komai a gidan da za'a kaita.


Wani tashin hankali tunda Habib ya dawo da dare bacci ya gagareshi saboda wani matsanancin zazzafan y daya sauko mai sosai yake fama da jikin shi.bayan yasha maganin ya konta amma Ina abin ya faskara har wuraren karfe biyu na dare Daman shi kadai ne a dakin dan zulaihat ta dade da yin hijira daga dakin shi,Dan haka shi kadai yayi ta fama har goshin asuba kafin yaji zazzabin ya fara yin sauki.





πŸ—‘οΈπŸ—‘οΈ *ZAFIN KISHI* πŸ—‘οΈπŸ—‘οΈ

*short story*

*true life story*


*LABARI/RUBUTAWA*


*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*


*MARUBUCIYAR* πŸ“šπŸ–ŠοΈ


🀦 *ZAMANINMU* 🀦


*AND NOW* πŸ‘‡



πŸ—‘οΈπŸ—‘οΈ *ZAFIN KISHI* πŸ—‘οΈπŸ—‘οΈ



________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*




*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*




*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI* .




PAGE 3️⃣1οΈβƒ£βž‘οΈ3️⃣2️⃣




πŸ“Da kyar yayi alwala ya shimfida prayermate,anan yayi sallar dan jiyake bazai iya fita masallaci ba.
Bayan ya idar komawa yayi ya konta kafin gari ya waye,sai wuraren karfe takwas kafin ya farka,Amma dukda haka Yana jin sauran zazzabin da ciwon kai.samu yayi ya gabatar da Wonka ya saka wani Golding din yayi mai taushi,dinkin riga da wando ne ya amshi kalar fatar shi,sai fuskar shi da tayi fayau ta dan fada alamar Yana jin jiki.ko hula bai saka ba ya fita zuwa falo.


Zulaihat a lokacin tana kitchen tana ta kokarin ganin ta hada kayan break.bata San da fitowar shi ba.shiko jin motsi yasa ya dawo da baya Yana kallon kofar kitchen din.duk yinin jiya bai sakata a idon shi ba dan yanzu ko magana ta daina hada su.cikin jin haushi ya fice daga gidan bayan mai gadi ya bude mai gate.


Ta ji tashin motar shi,Amma kawai saita ci gaba da aikinta ita da Nafisa.


Gidan Mama ya fara biyawa,kafin ya nufi asibiti daman yayi waya da Doctor'n shi akan gashi nan zai shigo ya duba shi.dan yaji jiki sosai.






Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

1 Comments On ZAFIN KISHI
avatar
abasu-kala

10 months ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment