Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*🧛🏿‍♀️HATSABIBBIYAR MACE*🧛🏿‍♀️



*Mallakin* 👉...

*zaynerb Muhammad kabeer.*

( *mum fu'ad* )


*Marubuciyar*✍️✍️✍


*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺
*And now*👇

*HATSABIBBIYAR MACE*


*Ban yarda a canzamin labari ta wata siga ba, ba tare da izinina ba*.

*(A true life story*)

*Littafin ba kageggen labari bane da gaske yafaru*


*Wannan labarin yasha bamban da sauran novels , Dan yazone da wani irin salo, sannan akwai darasi iri_ iri a cikin shi , kuma zai zama izina ga mata masu irin halayen ,ku dai ku biyoni kusha karatu*

*Asha karatu lafiya*


*Matukar ina ganin comments sossai zai zama free amma in ba ,a comments zan mai da shi paid book*.


*sadaukarwa ga my three sisters*

*Maryam Muhammad kabeer*
*Aisha Muhammad kabeer*
*Ummisalma Muhammad kabeer*

*ina Alfahari da Ku yan uwa na*


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 0️⃣1️⃣➡️0️⃣2️⃣*

Wani irin bakin daji ne dauke da manya manya duwatsu , ciyayi da bishiyoyine ko ta ina , da kananan kudiddifai .

Banda kukan tsuntsaye da kwaɗina babu abun da ke tashi a gun .

Wata mata na hango tana kokarin shiga wani katoton kogo , babu Alamar tsoro ko firgici tattare da ita, da alama dai tasaba zuwa , tafiya ta dingayi har sai da naga ta tsaya a wani karamin kogo.

Ga mamaki , sai naga ta shige wanan kogon , wani irin kirari ta farayi , tana faɗin , " kaga matsiyaci tsinanne , ɗan wuta , Allah ya tsine maka Albarka , Allah ya hanaka Rahmar sa , makiri , me shan jinin bil adama, ta cigaba da kiraye kirayenta , bayan ta tube haihuwar uwarta , bako pant ajikinta tumbur tayi .

Wani irin murya najiyo , me daukeda kuwa da kururuwa da amo tana faɗin "keeeee *HATSABIBBIYA* matsiyaciya , kijira barin aiko , zambarutu zaizo ya tafi dakeee";matar;ce tace " toh ran tsinanne ya daɗe matsiyaci Wanda Allah ya tsinemai ina jiranka ."

Wata irin shu umar dariya wanan mutumin yasa yace" da kyau da kyau, *HATSABIBBIYA"* da muryarshi maras daɗin sauraro

Wata iska mai karfice ta taso , take matar ta 'bace bat .

Dim naji ta duro a wani katoton kogo, ko ina a rufe yake da fata , banda wari da hamani babu abun dake tashi a gun , da wani irin hayaƙi .

Can naga wata katuwar kwaryace a gefen kogon , tashi matar tayi , ta nufi Inda kwaryar take , ta ɗauka jini ne fam cikin kwaryar , deban jini ta farayi tana zuba ruwan a jikinta, tana sha , tana gamawa ,ta hauyin wani irin yare me wuyar ganewa ta nayi tana karkada jikinta , tana wani irin juya ido , kamar yar bori , can ta zauna ta bude kafafuwanta kamar yar kaciya

Wata irin dariya najiyo , " *innalillahi wa inna illaihir raju ,un hasbunallahu wani imal wakil*!!" Abin Dana iya furtawa kenan , tsabar ganin wanan halitta.

Wani irin hallitta ne ya baiyyana a cikin kogon , wani irin mutum ne a tub'e , baki wuluk kamar gawayi , ga idonshi kamar Jan garwashi , ga hakoranshi kamar kaca , bakin shi kuwa jaaaa ne wuluk kamar idonshi , gawani irin katan tunbi kamar zai fashe , kanshi katoto kamar katan dutse gashin kanshi jane , Azzakarinshi kuwa , ya kai zira in hannun koma yafi tsabar girma da tsayi
Tsayawa faɗan munin mutuminan da girmanshi bata lokaci ne , dan kuwa duk Wanda ya kalle shi bazai so ya kara kallan shi ba tsabar muni da girma.

Ga mamaki na wannan matar babu Alamar tsoro ko firgici ganin wannan hallitar.

Zama tayi kusa da wani katoton dutse , dutsen baƙi k'irin ne ba kyan gani .

Mutumin ne yace da wata irin muryar shi marar daɗin sauraro dan kuwa , in kaji muryar kiris ya rage ta fasa maka kunne , tsabar girman muryar da rashi da din ji .

Yace *" HATSABIBBIYA* harkin gama da wancan gidan kenan ??.."

Matar naji tace " kwarai kuwa, ran tsinanne ya daɗe , yanzu a duba min ina kuma zan fada .."?

Bokan ne yayi wata irin ƙara ya fara magana da Alama kirari ya keyi da yaranshi me wuyar ganewa.

Take wani Jan hayaƙi ya baiyyana , jim kadan sai ga wata hallita ta baiyyana , halittar dai bazaka kirashi da mutum ba dan kuwa ya sha bambam da mutane , magana bokan ya fara yace " kaje Ka duba wani gida ne yake da sa,a dan nan *HATSABIBBIYA* zata fada" , halittan ne ya girgiza kai yayi tsalle take ya ɓace bat .

Jim kadan sai gashi ya dawo , zuwa yayi ya daukko wata katuwar kwarya me daukeda jini a ciki, ɗaukan kwaryar yayi ya bugi cikin kwaryar da wani Abu .

Take wani katon gida ya baiyyana .
Wasu matane su biyu zaune a katoton falo suna ta hirarsu gwani Sha,awa da Alama dai Amarya da kishiyane , sai mijinsu dayake gefe suna zaune guri daya, sunata hirarsu .

Boka ne yace ma matar "ke leko kiga gidan nan yayi miki ??" Matar ta gama k'arema gidan kallo tsaf "tace ehh ya mun nan zan faɗa kenan ? Anan zan aikata *HATSABIBANCIN* koh ?"

Ta ƙara da cewa "gashi da Alama suna zaune cikin farin ciki , ni kuma na tsani in ga mutane suna farin ciki dole in shiga in tarwartsa farin cikin gidan ."

Nan boka yace " eh naga akwai sa,a amma in kika shiga sai kin aiko mana da jinin bil adama kuma a cikin gidan muke san Jinin ya fita , duk zamu rufe musu baki kuyi yanda kike so babu me ce miki komai "nan ya miƙa mata wata laya yace gashi da wanan zaki dinga amfani , kina Shiga kisa a ƙasa ki taka" matar tace " angama ran tsinanne ya Dade"

Nan boka yace " in kin fita kiyi ta tafiya zan aiko aljanin da zai dinga nuna miki hanya har ki isa gidan , in kin fita ki dinga rufe idanki kina budewe za kiga har kinzo gidan.

Matar tace '' toh Allah ya tsinemaka Ina godiya barinje sai markazu ya ziyarceni ".

Boka yace "shikenan tashi kije an sallameki ,barin sa a mai dake gida ."

Nan wata irin iska me karfi ta ziyarci gun kafin kace me wannan matar ta bace bat .


Ganinta nayi a wani katon gida , shiga ɗaki tayi ta buɗe wata wardrobe ta ɗebo wasu kaya marasa kyau tavsaka , zani ne da riga duk sun ji jiki sun yaiyyage sun Lallace , ta saka ta dauƙo wani silifas duk ya siɗe ta saka a wata jaka .

Ta saka ƙatan hijab ba tasa takalmin ba ɗauko wani flat shoe tayi tasa, ta fita.

Tafiya takeyi kamar ana kadata ana turata , can sai ta tsaya, a wani katon gida kamar an kafeta , taji murya me daukeda amoo ta doshi kunnanta tace" keeee *HATSABIBIYA* kishi ga ga gidananan" matar ba tace komai ba tayi saurin cire hijab din jikinta ta wurgar tayi saurin daukoo wannan sidadden silifas din ta saka , taɗan ƙara ya ga kayan jikinta , ta kutsa kai cikin gidan , ta daukoo wannan layan ta ta takata , ta shige gidan.

Matane su biyu amarya da kishiya gwanin ban sha'awa da mijinsu suna zaune suna ta hira haɗe da raha .

Nan wannan matar tayi sallama cikin muryar tausayi da .
Ta fara magana tace" Assalamu Alaikum" ta faɗa cikin muyar tausayi tace " ina wuninku ."

Nan duk kallo ya koma kanta, me gidan yace "mee baiwar Allah lafiya kika shigo mana gida haka .?"

Matar ta ƙarema mai gidan kalloo tace uhmm taimako nake nema .

Ga mamaki me gidan ya samu bakinshi da faɗin " toh toh shigo mana ".

Matan ma dukansu tashi sukayi su kace "shigo yar uwa ai dole a taimaka miki ko Dan irin halin da kike ciki."
Dariya matar tayi tace "na gode."

Da rawar jiki mijin yace "uhmmm!! Baiwar Allah me kikeso kick kuma ga dski kizaba duk Inda yayi miki , nanfa ta fara duba duben da'kunan , can ta nuna ɗakin mijinsu tace" "nan nakeso ".

Ga mamaki matan suke kallanta cikin ransu Suna aiyyana cewa akan me zata zabi dakin mijinsu , amma fur sunkasa ce mata komai sunma kasa magana , sai cewa sukayi "toh shikenan badamuwa."

Matar tace, "amma fa sai dai in zaku barmin mijinku ya dinga d'ebe mun kewa ,dan ban saba barci ni kadai ba " tana magana tana kashe murya kamar tsohuwar karuwa .

Matan suna so suyi mata magana amma Sam sun kasa cemata komai, sai binta da kallo da suke ...........

*Toh fa masu karatu Ku biyoni Dan jin cigaban . Hatsabibbiyar mace*


*Yawan Comments yawan typing*✍️✍️✍️✍️

*Comment*
*Share*
*Like*

*By mum fu'ad*✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*🧛🏿‍♀️HATSABIBBIYAR MACE*🧛🏿‍♀️


*Mallakin*👉...

*Zaynerb Muhammad kabeer*.

*(Mum fu'ad*)


*Marubuciyar*✍️✍️✍️

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺
*And now*👇

*HATSABIBBIYAR MACE*

*Banyarda a canzamin labari ta wata siga ba , ba tare da izinina ba.*

*( A true life story*)

*Littafin ba kagaggen labari bane da gaske yafaru*

*Wanan labarin yasha bambam da sauran novels ,dan yazone da wani salo ,sannan akwai darasi iri_iri a cikin shi , kuma zai zama izina ga mata masu irin halayen , kudai kubiyoni kusha karatu*

*Asha karatu lafiya*


*Matukar ina ganin comments sossai zai zama free amma in ba,a comments zan mai dashi paid book.*


*Sadaukarwa ga my three sisters.*

*Maryam Muhammad kabeer*
*Aisha Muhammad kabeer*
*Ummisalma Muhammad kabeer*

*Ina Alfahari da ku yan uwana*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

*PAGE 0️⃣3️⃣➡️0️⃣4️⃣*

Mamaki sossai matan sukeyi , amma sun kasa cewa komai .

Wani kallo matar tabi Matan dashi tace" ko kunada magana ne?? .

Da sauri Matan suka ce "uhmmm mu mun isa muyi magana! ai hakan da kikayi yayi daidai".

Wani shu,umin murmushi matar tayi , cikin ranta tana ayyana lallai aikin bokanta naci, bata taba aikin da ya lalace ba , Shiyasa take jinjina ma bokanta .

Da sauri mijin nasu yace" toh yanzu kishiga ki huta kiiyi wanka, kici abinci koh?.

Cikin isa da gadara da tsantsar fankama da tak'ama tace" ehh hakan yayi , amma yakamata kusan dokokina da ka idoji na da kuma sharud'a na,da abubuwan da nakeso da Wanda banaso .

Da Sauri mai gidan yace" eh hakan yayi , ni barin fita in siyo miki abubuwa da kike da bukata dakuma kayan sawa, ki fadamun me dame kikeso ??.

Nan tafara lissafomai duk abubuwan datake bukata tamkar tana aikan yaran aikinta .

Bayan tagama lissafamai ta kallo matan tace"Yanzu kuje ku fara shiryamun abun da zanci ,kuma inaso inyi wanka ,idan nafito sai Ku kawo min.

Da Sauri suka hada baki sukace "toh shikenan" .

Sun juya zasu tafi matar tace "kai !!kuzo !! .

Da sauri suka dawo, wani banzan kallo tamusu tace," Baku da hankalin da zaku tambayeni menake San ci ??.

Da Sauri sukace," ayya kiyi hakuri 'yar uwa Mum manta ne wallahi , fadi me kikesan ci ??

Iissafo abubuwan da zataci tafarayi tace,"inasan shinkafa jeloup da kuma stew da farar shinkafa ,sai farfesun kayan cikin , da kunun tsami , hakan is okay .

Da Sauri sukace" toh shikenan , bari mushiga kitchen din Mu girka .

Kallon mijin tayi sama da kasa tace" zaka iya tafiya, da Sauri yace "toh sai na dawo.
bata bashi ansa ba ta wuce abunta .

Dakin mijin tashiga ta hango rantsantsan toilet , nan tafada tayi wanka.
Bayan sun shigo kitchen din dana girka mata abincin .

Amaryar ce me suna maryam, maryam tace" Anti zainab " sunan uwar gidan kenan " zainab ta ansa tace " Na,am" nasan zakiyi magana ne akan wanan matar koh???.

Maryam tace " eh wallahi anti zainab , akan wanan matar kiduba daga zuwanta ki ga yanda take mana, bamusanta , bamusan daga inda tafito amma kiga yanda muke mata , kumama Abun mamakin anan shine, wai duk cikinmu munkasa mata magana ,duk abun da tace ,Sai dai muce toh .

Dan Allah kiyi magana kice baza mu taimaketa ba, ta tafi kawai.

"Hummm nima wallahi maryam ina mamakin hakan, abun na bani mamaki ....tana cikin magana ne taji wani irin jiri nadibarta tsigar jikinta na tashi .

Wani wawan mari Zainab ta zabgawa maryam , tace" dan ubanki bazan ce ta tafi ba ,in ke bakyasanta , toni inasanta , shasha kawai .

Mamaki sossai Maryam tayi da Marin da Antin ta zainab tayi mata tace"Anti !!!!! Kina cikin hayya cinki kuwa ??? Mena miki zaki mun irin wanan marin?? , Takara dacewa" Anti ko a da ,a baki taba mun ko kallan banza ba , amma yanzu sanadiyyar wata kin mareni , Anti anya kanki daya kuwa??? .

Wani marin takara sharara mata tace"kee!!! Maryam , tafada da kakkausar murya tace" in baki daina mun maganar matar nan ba wallahi bazan daina marinki ba , ke bakida hankali ne , baki da tausayi baki ga halin da take ciki bane , wawiya shashasha .


Abun da masu karatu basu sani ba shine" duk abun da ke faruwa tsakanin maryam da zainab , wannan kasun gumin bokan yatura Aljani maharaz , jin duk abun da suke fadi .

Sihirinsu yafi karfi a gun Zainab wato uwar gidan , amma kuma Maryam ,wato amaryar abun itama yayi tasiri akanta sai dai baikai Na zainab ba , shiko mijin shima asirin yaci sossai a kanshi sabida yanada dan sakaci wajan addu,a , maryam ce kawai mai dan addu,a Shiyasa itama abun baiyi tasiri sossai sossai akanta ba .

Shiyasa dazaran maryam tayi magana akan hatsabibiya ,wannan Aljanin shi ya Shiga jikan zainab ya tunzurata ta mari maryam.

Dan a lokacin da take magana ya dan shiga jikin ta shine dalilin Marin da tsawar da take ma maryam .

Maryam bata kara cewa komai ba tace" toh kiyi hakuri insha Allahu bazan kara magana ba kinji ???,toh kawai zainab tace.


Bayan tafito a wanka kira ta kwalla musu tace" kuna inaa!!! ,da Sauri suka fito a kitchen din dan jin muryarta .

Zainab tace,"kiyi hakuri, muna kitchen muna dafa miki abun da zakici , bamuji kiranki ba .

Wani tsawa ta dakamusu tace " Ku Baku da hankalin dazaku aji yemun kaya in saka koh??.

Da sauri zainab tace" ba yafita siyo miki kayan da zakisa , ba sai dai ko in daukko miki nawa sai kisaka kafin ya kawo miki naki koh?

Cikin isa da gadara hade takama da tunkaho , tace" , eh Ai nasan da cewa yatafi siyomin kayan .

Ki barshi kawai zan shiga dakin naki zan dauko da kaina in ne dakin zanje in dauko da kaina ???? nuna mun dakin "".


Da Sauri Zainab tace" ga dakinan, ta nuna tace" muje , sai ki zaba koh ??..

Wata harara ta banka mata tace" , dallah matsa ba kin nuna mun ba ki barshi zan daukko da kaina ,toh zainab tace," bari mukoma mukarasa girkin , bata ma kallesu ba , ta wuce abunta .

Dakin zainab tashiga tafara duba dubenta ,drowar ta bude ta dauko kayan da yamata , wani guntun bonshort ta daukko da wata yar have vest , tafita .

Dakin mjin ta Shiga ta saka kayan.
Fitowa tayi tana takun kasaita ta nufi kitchen din ta tarar dasu suna aikin dafa abincin tace" kun gama ne?.

Wani kallon mamaki duk suna bita da shi ganin shigar dayake jikinta.

Summa kasa ce mata komai sai kallo kawai da suke binta dashi .

Wani razanan tsawa ta daka musu tace , ubanme kuke kallo ina magana Baku ansa min ba kun tsaya kallo na , ko kuma sai Na koma nacanza wata shigar da tafi wanan , dan wallahi ba karamiin ai kina bane ehee,

Da Sauri suka,
,"ce A,a,kiyi hakuri munkusa inshallahu .

kallan sama da kasa ta musu takalli maryam da ta ambaci inshallahu tace" ke bana bukatar kice inshallahu kice toh kawai , daga yau kar ki kuskura ki kara anbatan Allah matukar inanan kinji koh?? .

Tabbb abun da maryam tace kenan ,nunfasawa tadanyi cikin girmamawa da sanyin muryar tace" toh dama ke ba musulma bace??, da za,a kice baza,a ambaci Allah ba .

Murmushin shu,umanci matar tayi tace" ke kam naga alama kamar kanji na rawa amma kuma zan gyara miki shi kiji koh? .

Kiyi hakuri bazan kara ba , maryam na fadin hakan tacigaba da aikinta .

Cikin gadara matar tace" idan kun gama kusameni a falo zan gin da ya muku sharruda na kunji koh? Toh sukace suka maida hankali dan cigaba da aikinsu .

Fallo. ta fito ta hakim ce a kan kujera , ta kunnan takamemen TV falon tana kallo .

Yarane su uku suka shigo da gudu daukeda sallama a bakinsu , sanye suke da uniform din school , da Alama dai yaran gidanne .

Babban Na mijjn zai kai shekara bakwai sai dayar mace ce za ta kai shekara biyar , sai karamar cikinsu za ta kai shekara uku da Rabi.

Matar da take hakimce a falo tace" Kai ,!!Kai!! Kai!!, miye nayin sallama zaku shigo gida , toh daga yanzu kar kukara yimun sallama kunjini koh ??.

Babban ne me suna Ibrahim Khalil yace" toh Anti wace kee, ,???.

Mari ta daukeshi dashi tace" kaje ka tambayi uwarka a kitchen zata maka bayanin ni waye.

Kuka yasa da gudu ya shige kitchen sauran yan uwan suka bi bayanshi .

Da kuka ya shigo kitchen yanufi gun mahaifiyarshi zainab , yace" mommy waye waccan matar a falo dan Na tambayeta nace " wace ita shine ta mareni .

Da sauri zainab tace" Toh kai wa yasa ka tambayeta ai gashi kamaru , karka kara tambayarta , itadin Antinku ce, kaji ,?? Gyada kanshi yayi yace" Antynmu kuma?, ta ina tazama Antynmu ?? bayan ban santa ba,?

Harara ta galla mushi tace" Khalil zan ci ubanka , banasan yawan magana kawuce kaja kananka ku je ku cire uniform , kuzo kuci abinci , toh yace" yaja hanun kanan nashi suka nufi dakinsu .

Wanan karan maryam batace komai ba illa mai da hankali da tayi wajan aikin da takeyi .

Bayan sun kammala abincin suka jerasu kan dinning table , isketa sukayi zauna tana taunar cingum tasaka kafa daya akan daya.

Kallam maryam zainab tayi tace" maryam " kije kice mata mungama, abincin, toh tace.

Gurin matar maryam tanufa , tanajin wani irin mugun faduwar gaba.

Dan rissinawa tayi a gabanta race" uhmm sannu da hutawa , dama Nazo na fada miki ne mungama abincin .

Ko kallo bata isheta ba balle tasamu damar da zata ansa mata.

Cikeda gadara tatashi tana karkada jiki kamar tsohuwar karuwa , ta nufi gurin dinning table din .

Zama tayi tafara bude kulolin abincin .
Tsaye sukayi suna kallanta , kamar wasu dogarai .
Wani shu,umin kallo tabisu dashi tace" kuna jiran in zuba abincin da kainane ne???.

Jikin su na rawa sukace " A,a" bari mu zuba

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment