Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

in dubashi .

Cikin damuwa Hajiya tace," ni kaina wallahi abun na bani mamaki amma yanzu kije Allah dai yasa lafiya .

Amsawa tayi da Ameen , daga bisani ta tashi dan shiryawa, tana shiryawa ta tafi .

Tana dosawa kofar gidan taji gabanta yayi mugun faduwa Wanda tarasa dalilin hakan.

Da sallama dauke a bakinta tashiga cikin gidan .

Kasancewar tunkafin tazo boka yasanar ma da *HATSABIBIYA* zuwanta hakan yasa tayi saurin zama a fallo dan tarbarta da salan rashin mutunci.

Sanye take cikin wasu irin kaya , wanda dashi da babu duk daya ne .

Cikin matukar mamaki suraiyya take kallanta ,ganinta ba karamin daure mata kai yayi ba .

Da sauri tace," baiwar Allah waye ke? naganki a irin wannan shigar , saikace matar gidan , kodayake ai ko matan gidan ma bazasuyi irin shigar nan ba .

Tashi tayi tanufo inda suraiyya take tana karkada jiki ta daga hannu ta kifeta da mari , rai a bace tace,"barikiji in fada miki, na fara tarbarki da mari ne sabida inaso ki koyi yanda ake magana da mutane , kingane , da farko cikin girmamawa yakamata ki min magana ba kimuun magana ba tamkar sa,arki ba , ko kinsan waye nii???.

Wata shu,umar dariya tasa tace," *HATSABIBIYA* kenan ,sunana hastsabibbiya mai tarwatsa farin cikin ma aurata , kuma matar gidan Alhaji musa, kingane koh ..???

Cikin tsoro da matukar mamaki suraiyya take kallanta , muryarta na rawa tace," kika mare..kasa karasa maganar tayi tsabar mamaki dayagama kamata.

Ganin Alhaji musa ne yasa suraiyya saurin zuwa gurinshi tace," yaya lafiya naganka haka kamar ba kai ba meyasa meka haka ciwo kayi ??, meyasa bakazuwa ganin Hajiya kullum cikin damuwa take , na rashin zuwanka , ina Anti Maryam da Anti Zainab ,da yara kuma waye wannan da take ikirarin matarkace ita,??.

Duk wani innan tambayoyin ta jefomishi ne lokaci guda inda yatsaya kamar mutun mutumi tana jira yaji abun da *HATSABIBBIYA* zata bashi umarni yayi .

Kallanta yayi amma yakasa cewa komai illa jiran umarnin *HATSABIBIYA* dayakeyi .

Kallanshi suraiyya tayi tace ," YAYA kayi shuru kamun magana mana kayi magana .

Kallanta tayi tace," ya miki magana ko yanzu zai miki.
Hade rai tayi tace, " wallahi ko kallanra naga kayi zaka gamu dani , kujirani ina zuwa .

Da sauri *HATSABIBBIYA* tashiga dakin dan daukko bulala.

Cikin rashin fahimta suraiyya tace," YAYA kamun magana , meke faruwa dakaine , kayi magana kayi shuru .

Shuru yayi baice komai ba kanshi a kasa kamar Mara gaskiya .

Fitowa tayi da katuwar bulala ta mikama Alhaji musa tace," yanzu yanzu inaso kafitar Mun da yarinyar nan daga gidanan bayan ka zaneta da bulalar nan .

Ba musu ya karba yafara shaudamata , ihu suraiyya takeyi tanafadin ,me menamaka YAYA mena maka, bashiri ta kwasa da gudu ta bar gidan a rikice, gudun kar ya illatata .

Da gudu ta shiga fallan ta tarar da Hajiya zaune tana lazumi.

A rikice Hajiya ta kalleta tace," suraiyya lafiya me yafaru meya sameki??.

kuka suraiyya ta kara fashewa dashi a rikice tace" Hajiya !! Hajiya wallahi ba lafiya ba lafiya a gidan yaya, Hajiya kitaso kitaso muje ki gani da idanki , Hajiya bazan iya miki bayanin komai ba bazan iyaba kizo dai kawai ki gani da idanki .

Cikin rashin fahimta Hajiya tace," in je fa kikace kimun bayani meke faruwa??, gashi kamar naga shatan duka a jikinki .

Da kyar Suraiyya ta saita nutsuwarta tace," Hajiya da kinzo munje kin gani wallahi ni bazan iya miki bayani ba yaya ne .

Rai a bace Hajiya tace," wai kinata yaya ne yayane in zo muje , me yayan ya miki kuma bakimun bayani ba kice iinzo muje , ki nutsu kimun bayani .

Nan suraiyya tadan hadiyi yawu ta gyara zama ta nutsu tace," Hajiya aure yaya yayi , kuma matarshi ce tasashi haka kawai yadinga zaneni da bulala banmusu komai ba , dakyar na iya gudowa a gidan .

Cikin matukar kullewar kai Hajiya tace, ke banasan shashanshi banza kinutsu kimun bayani kinsan ni banasan shirme ko , maza ki nutsu ki fadamun .

Wallahi tallahi Hajiya ba karya nake miki ba , nan suraiyya takwashe duk yanda sukayi tafadawa Hajiya .

Salati Hajiya tasa tamarasa me zatace , in banda zufa datake karyomata .

Cikin hanzari tace," tashi muje gidan in gani da idona .

Zaro ido suraiyya tayi tace, " tab Hajiya ni wallahi bazanje ba inje tasa yakara dukana , haka kawai , wallahi tsoron zuwa nake.

Kallanta Hajiya tayi tace," bakida hankali ne a gabana zasu kara dukanki , tashi ni kishirya mutafi .

Nan ta tashi , suka shirya suka nufi gidan Alhaji musa.............


*DOMIN JIN CIGABAN LITTAFIN HATSABIBIYAR KU BIYA NAIRA DARI BIYU 200 KACAL 👌👌A WANAN ACCOUNT NUMBERN 1400337156 AISHATU MUHAMMAD KABEER ACCESS BANK SAI NAJI KU*
*Muje zuwa*


*comments*
*share*
*like*


*By mum Fu'ad*✍️✍️✍️

*🧛🏿‍♀️HATSABIBBIYAR MACE*🧛🏿‍♀️


*Mallakin*👉...

*Zaynerb Muhammad kabeer*.

*(Mum fu'ad*)


*Marubuciyar*✍️✍️✍️

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺
*And now*👇

*HATSABIBBIYAR MACE*

*Banyarda a canzamin labari ta wata siga ba , ba tare da izinina ba.*

*( A true life story*)

*Littafin ba kagaggen labari bane da gaske yafaru*

*Wanan labarin yasha bambam da sauran novels ,dan yazone da wani salo ,sannan akwai darasi iri_iri a cikin shi , kuma zai zama izina ga mata masu irin halayen , kudai kubiyoni kusha karatu*

*Asha karatu lafiya*


*duk wacca ta karanta bata biyaba Allah ya isa, kuma banyarda a fitarmun da littafina ba wacca tayi hakan banyafeba*.


*Sadaukarwa ga my three sisters.*

*Maryam Muhammad kabeer*
*Aisha Muhammad kabeer*
*Ummisalma Muhammad kabeer*

*Ina Alfahari da ku yan uwana*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

*PAGE0️⃣9️⃣➡️🔟*

*SISTERS KU TAYANI JAJE WALLAHI NAYI TYPING KUSAN SIX PAGES WHATSAPP DINA YAYI RESTORE DUK YA GOGE😢😢😢*


*_WANDA YA KARANTA BAI BIYABA BAN YAFE BA KUMA WA INDA SUKA BIYA BANYARDA KU_* *_FITARMUN DA LITTAFI BA IN KUKAYI HAKAN BANYAFEBA GASKIYA_*

Kai tsaye gidan Hajiya da suraiyya suka nufa .

Da sallama Hajiya ta shiga gidan , ganin yanda take zaune hakimce a kujera cikin shigarta maras kyau tana taunar jingum tadaura daya akan daya .

Nuni suraiyya tamata da hannu tace," Hajiya itace fa ita nake fadamiki .

Ganita haka yasa gaban Hajiya yafadi cikin ranta takefadin", waye wanan wacce Annobace wanan .

Wani kallon banza ta jefi Hajiya dashi tana karkada jiki tace," mst miye haka kinshigo ba tareda izinina ba kina karema mutum kallo , wai tukunnama waye ke??.
Waya baki damar shigowa kai tsaye bani amsa ina jinki .

Gurinta ta karasa Hajiya ta kalleta sama da kasa tace," waye ke,??, me kikazoyi me ya kawoki gidan dana fadamun inajinki .

Tashi tayi daga zaunan datakeyi ta tabe baki tafara zagaye Hajiya tana yatsine fuska kamar taga saban kashi tanfadin , hummm da Alama kece Uwar miji na ko ?, dan ko ba,a fadaba naga kama , ke wace irin kidahumace zaki shigo mun gida ba tareda izinina ba ??.

Hannuta Hajiya tarike ta juyo da ita gabanta ta juyo da fuskarta ta daga hannu ta tsinketa da mari .

A firgice ta dago ta kalleta tana huci tace," bura uba ni kika mara kinsan wa kika Mara kuwa?? lallai yau zakisan kin mareni .

Hajiya na huci a zafafe take fadin in har ke bakida mutunci bakida tarbiyya ni zan koya miki hankali dan ubanki ni Sa,arkice zaki dinga fadamun magana .


Cikin matukar daga murya Hajiya tace," wai waye ke??!!!! wayeke !!?? daga ina kike har naji kina ikirarin dana mijinkine tun wuri kifita a rayuwar mu kifita a rayuwar d'ana daga ina kike daga ina kikazo bamusanki ba bamusan daga inda kike ba kinshigo ,zaki lalata Gidan ma,auratan dasuke zaune shekara da shekaru cikin jin dadi , me kikeso damu miye kudirinki akanmu ??.

Wata shu,umar dariya tasa tace," hummm kinaso in fada miki??.
Gyada kai Hajiya tayi Alamar ehh .

Murya Takara ji ta daki dodon kunenta ,muryar da ita kadai takeji( bokanta kenan) Tanafadin," _ki kifeta da mari wanan umarnina ne sanan ki sa danta yayi mata cin mutunci ya koreta , muryar takarasa maganar tana shekewa da dariya_.

Tanadaina jin muryar Hatsabibiya ta kife Hajiya da mari tana fadin dan ubanki an fada miki ni kanwar lasace da zaki mareni , wallahi sai kinyi danasanin zuwanki gidana , yanzu barin kira miki dan naki zakisha mamaki .

Hajiya suman tsaye takusan yi cikin ranta tana aiyya na cewa," lallai wanan akwai abun da ta taka tabbas .

Suraiyya da take gefe duk tsoro ya kamata tayi sauriin zuwa dan riketa .

Kuka Hajiya tasa tace, " suraiyya suraiyya akwai matsala .

Ganin Alhaji musa ya fito yasa Hajiya zuwa gurinshi da Sauri tace," musa musa meke faruwa waye wanan yanaga duk ka lalace meke faruwa musa me yahanaka zuwa kuma waye wanan datake ikirarin matarkace ??.

Kuka Hajiya tasa tace," musa kaga rashin mutuncin datamun kuwa, musa raban da Amarenj har a manta amma yau wata ta mareni ?? Miye Alakarka da ita kuma me ta taka , miye dalilinka na barinta ta zauma a gidanka ?inajinka kabani Amsa .

Shuru musa yayi yana tsaye kamar mutum mutumi .

Tsawa Hajiya ta dakamai tace," kamun bayani kamun bayani musa tafada da kakkausar murya .

Wata shu,umar dariya tasa tace," humm Ai bazai miki magana ba bar sai na bshi izini ko kina musu ne In gwada miki ?.

Wani taswa ta daka mishi tace," nabaka minti dayawa wanan matar tafitamun a gida in ba haka ba sai ranka yabaci .

Jiki na rawa ya nufo gurin Hajiya yace," Hajiya kifita kifita yanzu dan Allah.

Kuka Hajiya takara fashewa dashi murya dashe tace ," musa yau ni kake kora a gidanka musa nii nii !!! na tabbata musa ba kanka daya ba a haiyyacinka kake ba Gaskiya.

Akan wanan tsinanniyar matar kake korata musa nice fa nicefa

Hade rai yayi yace," ni Gaskiya kaina daya yaza kicemun ba kaina daya ba kifita kawai nace miki .
Kuma karki ka aibanta matata yauwa, in ba hakaba zanmiki rashin mutunci .

Ni musa ni zakayi ma rashin mutunci??.

Kuka sossai Hajiya takeyi ,suraiyya ma kuka tasa da Sauri tazo ta rike Hajiya ganin Hajiyan kamar zata fadi tana kuka tana fadin," mutafi mutafi Hajiya muje gida kar ciwanki ya tashi .

Dakyar suraiyya ta lallaba Hajiya tariketa suka bar Gidan banda kuka ba abun da sukeyi .



Ko da suka isa Gidan Hajiya tagumi tayi banda hawaye dake zuba a idanta babu abun da take .

Abinci suraiyya takawo mata tace," Hajiya ga Abinci kici dan Allah wanan tunanin bashi zai mana maganan wanan damuwa ba , amma ni kaina ina mamakin abun da wanan matar ta aikata ko me take takama dashi ohoo.

Hajiya kuwa tama kasa magana balle kuma taci abinci .

Cikin ranta take tambayar kanta cewa waye wanan matar daga ina take daga ina tazo me yahadata da danta , ganin cewa bata da amsa yasa ta numfasa tace ," suraiyya kirawomin sauran yaran gaba dayansu suzo dole in fadamusu wanan gagarumar matsalar data tunkaro mu.

Nan suraiyya ta shiga kiran wayoyinsu .


Cikin kankanin lokaci lokaci gaba dayansu suka zo , Alhaji mansur ,shine babban d'a a gidan sai Anti kubra itace ta biyu sai shi Alhaji musan shine na uku sai Habib shine na hudu sai Khalid shine na biyar sai kuma Autarsu suraiyya itace ta shida, su shida 'yan yan Alhaji Abdullahi mai dan kunne da kuma Hajiya Rabi,atu Abdullahi mai dan kunne, iyalan da suke cikin farin ciki tsawan shekaru masu yawa , dan takaitacen tarihin gidan Hajiya Rabi,atu kenan .

Cikin tashin suka CE Hajiya lafiya kikayi mana Kiran gaggawa haka meke faruwa ??.

Kokarin magana Hajiya tayi amma Kuka ya kubcewa mata .

fadin irin tashin hankalin dasuka Shiga
bata lokaci ne domin kuwa raban dasuga mahaifiyarsu na kuka Gaskiya sun manta .

Anti kubra CE tace," Autar Hajiya meke faruwa ki fada mana dan Allah Hajiya menen meyasameki me yafaru tafada a kidime ???.

Nan Hajiya tadan tsagaita kukan da take tace," dan uwanku ne yake cikin tashin hankalin da kwakwalwa bazai iya dauka ba , kukane yake San kubcemata ,nan tadan ja numfashinta ta kalli Suraiyya dake zaune tayi tagumi tace," suraiyya fadamusu .

Shuru suraiyya tayi dan itama kukan ne kesan kubcemata amma ta daure .

Cikin zakuwa sukace kimana bayani mana kinbarmu a cikin duhu .

Jiki a sanyaye suraiyya tace," toh.

Nan tafara musu bayan duk abun da yafaru a Gidan Alhaji musa.

Gaba dayansu zufa ce ke karyo musu cikin tsananin tashin hankali , Anti kubra tace," ke wanan labari da kika bamu da gaske ne??.

Wallahi Anti da gaske ne ai a gaban Hajiya akayi hakan .

Numfasawa Hajiya tayi tace,, tabbas duk abun da suraiyyatu ta fadi gaskiyane ni kaina da ba a gabana akayi ba ko kuma da bani akayi wa da bazan yarda ba .

Rawa muryarta tafarayi tana fadin ni dinan musa ya kora korar rashin mutunci , bayan Marin da matar ta tsinkamun , wallahi kaina ya daure kaina ya daure bansan meke faruwa ba nasan bayin kanshi bane nasani nasani ,kukane yaci karfinta, jin ta Ambaci Mari yasa a tare suka had a baki suka ce,"Mari!!!! .

Eh Mari, marina tayi , cikin zafin rai Habib yace kan uba kai!!! ina bazamu yarda ba ko wacece sai taci ubanta sai ta gane kuranta .

Kuka Hajiya tasa nan suka cigaba da bata hakuri .

Cikin tsantsan bacin rai da bakinci , Alhaji mansur cikin inda _inda yake fadin wai wai wacece ita? nifa kaina ya kulle , ni Nama rasa me zance me ta take takama dashi dan ubanta har zata mareki , yanzu yanzu zanje gidan sai na koya mata hankali, ni wallahi danaga bana ganinshi baya zuwa guna ni nadauka tafiya yayi baya kirana a waya Ashe yana can cikin matsanancin hali , amma ki kwantar da hankalinki Hajiya komai zai daidaita inshallahu , barin je gidan.

Habib da Khalid ne sukace eh muma zamu biki zamuje muga wacece ita metake takama dashi wallahi sai ta gane kuranta .

Ai nima tare zamu tafi dan kuwa sai naje naga wacece Anti kubra tafada rai a abace .

Cikin sanyin murya Hajiya tace," kunga karkuje kuyi wani tashin hankaki mubi abun a sannu dan nasan musa baya cikin haiyyacinshi , karkuje gidan kuyi hayaniya dan Allah , in kunga Alamar zata muku rashin mutunci kiyi maza kudawo bance Ku aikata komai ba kunji koh ??.

Toh suka CE suka tashi dan tafiya .
Kalan suraiyya Anti kubra tati tace," Autar Hajiya bazaki bimu bane?? .

Langwabar dakai suraiyya tayi tace," tab bazanje ba kinga dukan dayamun ne sai kun dawo .

Duk da suna cikin damuwa yannda suraiyya tayi maganar sai da yasasu Murmusawa gaba dayansu , suka nufi gidan .

Suna shiga suka tarar da Alhaji musa zaune yanayi mata tausa , ita ko tana hakimce a kujera .

Eh lallai Abun da su Hajiya sukafadi gaskiyane ko hakan kadai da nagani yasa na tabbatar da maganar suraiyya da Hajiya Anti kubra tafada cikeda mamaki , karasa gunta tayi tana karemata .

A fusace ta mike tace," kai nashiga uku wai miye hakane baza kubarni in huta ba wallahi tun wuri kuficemun a gidan kafin ranku yabaci .

A zafafe Alhaji mansur yace kee wacece ke?? Me kikazoyi nan daga ina kike waya kawoki gidanan ??.

Shuru tayi tana hararare _harare , cikin masifa Khalid yace," baza ki fada ba sai na miki dan banzan duka.

Wata shu,umar dariya tasa tace," hummm ni zaku daka , wani kallo ta jefa ma Alhaji musa dakanshi yake a sunkuye tace," kaji wai zasudakene , ni zanshiga ciki zan barka dasu karka bari in dawo in tarar suna gidanan , tafada cikin isa hade da iko , kuma sai kafadamusu waye nii ta karasa hade da shekewa da dariya tanufi saki tana tafiya tana juyi da harara ........

*hummm muje zuwa, wanan kadan kenan*

*_zakukiji Gobe inshallahu innasamu damama pages biyu zaku samu inshallahu_*


*SISTERS NAYI TYPING DA YAWA DAN INDINGA MUKU POSTING KULLUM AMMA YA GOGE , AMMA YANZUNMA ZANYI KOKARIN HAKAN INSHALLAHU*


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment