Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kofar kuka take maras sauti tun tana tsaye harta kai kas saida tai mai isarta sannan taje ta wanke fuskarta bata koma takan abinci ba ta hau gado danyin bacci anman bacci yace shi bai shirya ba.

✨✨✨✨✨✨

Zaune ta tashi to ma wai mene naki na damuwa dan yayi waya da wata zuciyarta ta fada mata wani barin yace mata kardai fa kin kamu dasansa ina ta fada baso bane afili can ta mike tahau zirga zirga inba so bane to mene kishi ta kada kai wata zuciyar tace ai mijinki dole kiyu kishinsa alwala tadauro ta dauko alkur'ani dan karantawa ko taji dadi aranta.


✨✨✨✨✨✨✨


Washe ruwan shayi kawai ta dafa sai kwai data soya ko dakinsa bataje ba bslle yasamu matsayin gaidashi shikansa yai mamaki be kawo komai ransa ba ya fito tana zaune akujera tadan kalleshi fuskarta adaure ina kwana tace ya amsa batare da tunanin komai ba yaje dan karyawa.

✨✨✨✨✨✨✨

Bai ce komi ba ya ci abincinsa ya mike muje ko tabi bayansa ko amota tunda ta sunkuyar da kanta bata dago va sai da yace zaki iya fita ta fice batare da tace kala ba ya kada kai kawai ya tafi aransa yana cewa yau yan shaga bar suka motsa dan yaga babu abinda tai agidan yadda ya kwanta yabarshi haka ya tashi yaganshi.

✨✨✨✨✨✨✨

Sakawa take tana war warewa ta rasa me zatayi a sch ma a sabule ta wuni har aka tashi maryam nata tambayarta me yasameta sai dai tace batajin dadi ne jitake kamar taje ta fasa wayar tasa.

✨✨✨✨✨✨✨

Koda ta koma gida indomi ta dafa ko ci batai ba ta ajiye masa a dinning tai dakinta da ya dawo yai mamakin rashin ganinta a falo be kawo wani abu ba yaci abincinsa sannan har ya kwanta ya mike dan zuwa yaga me yasa bata fito ba dan hankalinsa ya kasa kwanciya.


✨✨✨✨✨✨✨


Tana jiyo bude kofar tai saurin kwanciya alamar bacci take batasan ya ganta va tace au dankin dafa indomi shine zaki koma yar buya dani ta bude idonta dayai jawur sabida kuka tace kaina ke ciwo sub hanallahi kinsha magani tace eh Allah ya sawwake ya fada gami dayin waje.

✨✨✨✨✨✨✨


Yanayin waje hawaye ya zubo mata wato shi bemasan me take ma fishi ba shi yadauka shirmenta kawai take kaico na ta fada.


✨✨✨✨✨✨✨


Dasafe ta fara wucewa tai dakinsa yana wanka wayarsa ta gani kan bed side drawer nan hankalinta ya bata ta dauka da sauri ta dauka number din mukli ta nemo tai niyar gogewa se ta fasa tasa ta black list ta shiga watsap tai blocking dinta tai ficewar ta dan ta fuskanci ita take kiransa shi kuma na biye mata.


✨✨✨✨✨✨✨


Fes tajejin ranta dan ji take kamar ta rabasu tunda inta kira bata shigoba ta turo message be shigo ba intana da tunani ta hakura shi kansa yai mamakin yadda ta sauya cikin fara'a suka gaisa abuncin a flask ya tafi dashi suka fuce.

✨✨✨✨✨✨✨

Yau gidan a cike yake dan kannenta na sabuwar kofa ne suka zo dadi ya cikata sai nan nan take dasu tun safe sukazo sai dare zasu tafi koda Aliyu ya dawo dashi sukai ta fira dan sunma fi sabawa dashi kan yayar tasu.

✨✨✨✨✨✨✨

Da zasu tafi ta basu turarurruka Aliyu yadauke su dan maidasu sai da ya biya ta Sahad yai musu tsaraba sannan ya wuce dasu gida acan gida mama take ta mita ku yanxu daga ziyara sai wahala yai dariya ina wahalar take mama au haka zaka ce to kuwa zasu dena zuwa ayi hakuri yazauna suka taba fira ya wuce gida.

✨✨✨✨✨✨✨

Allah maryam nayi fushi ta kalleta me kuma nayi ace baki taba zuwa gidana ba ko sau daya ayi hakuri kimin uxiri tadan harareta uxiri fa kika ce haba Amra tarefa muke karatunnan dake kina kallo a sch muke wuni da kefa taushe fa baje gida natafi yawo au zuwa gidan nawa ne yawo ba komai ta kada kai tai dariya ayi hakuri ba haka bake nufu ba zaki ganni tsulum kedai ki tanadi kayan dadi yaushe to sai randa Allah yayi taja tsaki kice kawai bazaki xo tai dariya nidai bance ba.

✨✨✨✨✨✨✨

Yaya mezan dafa yadanyi shuru kiyi kome ma kika ga yadace to yaya tace tai kitchen da yake yau ba aiki suna gida dan shi ba gwanin yawo bane innyaje gida ma mami cewa take ya dawo gidan matarsa koda ba fira sukeba anman sun saba zaman guri daya duda kowa kowa da abinda yake.


✨✨✨✨✨✨✨


Bawani abinci me wuya taiba danbun kuskus tai sai dan lemo tana jerawa a dinning taji kamar ana taba kofa ta basar dantaji kamar iska ce kawai ta cigaba da abinda take tsaf take tai kyau cikin pink din diguwar riga alamar dai bugun da gaske ne har Aliyu ya mike zai bude ta wuce shi bari na duba.


✨✨✨✨✨✨✨


Wa zata gani muklisa wato
tsohuwar budurwar Alin ce gabanta yai
mugun faduwa ta daure Aunty mukli kece eh bakiyi tsan mani ba ko tadanyi murmushi ba haka bane ok me gidan yana ciki kamar tace a'a tace eh basu jira karashen amsar ba sukai ciki tabi bayansu da kallo tana sake saken abu buwa da dama.....

✨✨✨✨✨✨



*One love to Fans no word to express our appreciation*😘😘





✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾
*Ummusulym*
*F.A.Ya'u*


⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
⚜⚜⚜⚜
⚜⚜
*AMRATU*



*Page 65➰70*
*Na*
*Ummulsulaym*
*Da*
*F.A Ya'u*


*Short and brief story*
fayau9.blogspot.com
Fayau26.WordPress.com


Iya yinta tai ta daure ta saki fukarta gami da bin bayansu yn zaune ya miqe fuskarsa cike da mamaki Mukli ta kalleshi bakai farin ciki ba ko me kika gani yace naga kana mama kine yadanyi murmushi no ba haka bane kawai banyi zaton ganin ki a 9ja ba ne tai far da ido kace haka mn tunda ka gujeni tafadi haka tana zama.

✨✨✨✨✨✨✨

Amra ta zo dauke da lemo ta ijiye musu kamin itama tasamu guri ta zauna tadaure Aunty mukli ina wuni ta amsa a sheke ga lemo ta fada mata dayar da suke tare ta dauka tana tsiyayawa kanta ko ba'ai mn tayi ba ai masha ita dai bata ce musu komai ba Ali ya dube ta kawo musu abinci ta mike gami dayin wajen abincin koda ta gama jere musu tai dakinta takaici fal ranta.


✨✨✨✨✨✨✨


Da zasu tafi ya leko dakinta zasu tafi kixo kuyi sallama kamar tace bazata zo dinba ta mike ta hado musu turare cikin fara'a tace gashi mungode mukli tace ki barshi bashi mukazo karba kawar tata ta karbe ni inaso bari na rakasu bai jira amsar ta va yai fucewarsa.

✨✨✨✨✨✨✨

Ai tundaga wannan lokacin mukli ta maida gidan gidan zuwanta tun Amra na haquri har tafara kaita bango taci aniyar inta sake zuwa sai tai mata rashin mutuncin da bazata qara sha'awar zuwar mata gida ba.

✨✨✨✨✨✨✨


Tana daki dan yanxu ta rage zama inda yake danshi dinma haushinsa take ji tajiyi alamar maganar mace ta fito aiko muklin ce yau ita kadai ce ga mamakinta dinning take shirin hawa wato wuyanta har ya isa yankan da zata zo mata gida ta nuna isa da sauri ta karasa lafiya ta fada bata kalleta ba ta cigaba da qoqarin zuba abincin ke dallah malama dake nake ta dago au ashefa dani kike Yah Ali yace sakko mukli ta zuba miki ta kalleshi wa ai wallahi bazata ci abincinnan ba ta tureta na fuskanci bakisan mutunci ba wace macen ce zata dinga baro gidan iyayenta tana tawowa gidan saurayinta inba mara mutunci da tarbiyya va what ni kike cewa banda tarbiyya eh anfada ko xakiyi wani abunne ta daga hannu zata mare ta Ali yai saurin rike hannunta ke kuma mene haka pls zoki tafi gansan rigima Aliyu ni kake kora a gidanka No ba haka bane muje waje yajata waje ba haka Amra ta so ba tai daki tana kuka.

✨✨✨✨✨✨✨

Misalin biyu na rana Ali bayanan tajiyo bugun qofa taci kukanta ta koshi idonta ya kada yai jawur tai toilet ta wanke fuskar taje ta bude wa zata gani maryam ce kawarta dadi ya cikata.

✨✨✨✨✨✨✨

Takalleta lafiyar ki kuwa batasan Sanda hawaye ya kwace mata ba kuka fa kuka kike Amra nida nasan haka zan ganki da banzo ba wallahi sukai ciki maryam tai ta bata baki da nasihohi Amra batasan fadon matsalar ta anman inbata fada ba bazata ji sanyi ba nan ta baima maryam labarin komi tundaga aurensu har kawo yau.

✨✨✨✨✨✨✨

Maryam taja ajiyar zuciya kin ban mama ki Amra sai kace ba mace ba ki zauna da namiji kullun kuna tare ki kasa sanya masa sanki har ki bari wata tazo har gida tana kokarin nuna miki isa dan kawai tana takamar ita yake so inda nice da tuni an fice gun dole ki tashi tsaye ba boka ba malan da salonmu na mata ki kafa taki jam'iyyar agunsa gami da ture ta kowacce mace Allah ko tsaya kallon ruwa nan tai tabata shawar wari ita sai alokacin ma taga baiken kanta mata mu kula wani lkci mu ke kwaron kanmu ban baki shawaran bin boka ko mallan ba domin wannan hanyar ita ke dulmiyar da mata da yawa na wannan xamanin,da wuya kuga namji na asiri sai dai Wanda bai amsa sunansa na maxaje ba,ki cire duk wata tsana,kunya ko girman kai ki bawa mijinki kulawa kiyi masa biyayya.

Sbd haka Amra ina mai shawartanki da ki kasance mai tsananin biyayya ga mijinki, ina tabbatar miki Allah xai da sa masa kaunarki domin dai ko ba komai hadisi yaxo daga manxon Allah (S.A.W)yana cewa.

"An halicci xukata a bisa son wanda ya kyautata masu da kin Wanda ya munana mata"

Idan kina kyautatawa mijinki ina mai tabbatar Miki sonki a kullum qaruwa xai dingayi,idan ke kuma yazama dole ki dena abinda baya so yadda kika ban labari tabbas Ali nasanki sedai be taka kara ya karya ba dole ke zaki tashi tsaye ki bunkasa sanki aransa ke burinki kullum ki bata masa rai toh tabbas bb shakka kullum sonki raguwa xai dinga yi a xuciyarsa,sbd haka 'yan uwa mata don Allah mu dage wurin kyautatawa maxa jenmu da jikinmu,da dukiyarmu,abin nufi da jikinmu shine tsabta,kula da gyaran jikinmu jan hnklin mijinki ta hanyar kwarkwasa domin kowacce mace ina tabbatar miki da jikinta jarintane muryanta jarinta ne,idonta jarinta ne.

Abun nufi kuwa da dukiyarmu shine siyan kyale-kyale da abubuwan gyaran jiki,turaruka da sauransu da kudin mu ba sai mun jira mijinmu ya saya mana ba kamar ynda wasu matan ke aikata hakan,domin da wadannan karuwa ke mallake mana maxa jenmu

Da fatan Amra xaki gane Allah ya baku xaman lfy kin ga lkci ya qure bari in tafi gida amman har ynxun ina shawartanki da ki qara dagewa da ibada,kuma komai ke tsakaninki da mijinki kikai kukanki gurin rabbi ixxati shine xai yaye miki,domin Allah shi yace Ku roqeni Xan amsa muku,Allah ya baki hqrin juriya na tafi sai mun hadu a skul Monday.
Suka rabu tanatai mata godiya dan tajibdadin zuwanta ko bakomai ta tunatar da ita abinda ta mance tabvas ita take da lefi kuma zata gyara ta fada aranta.









✨✨✨✨✨✨✨

Tunda ta tafi ta xauna tana tunanin mgnar da sukayi da qawarta tabbas Allah ya bata kaifin hnkl Allah ya bata ikon juriya.
Ta mike dan tunawa da ya kusa dawowa ko me ta tuna oho tasaki wani murmushi gami da yin dakinta.

*LoVes You Fans*

*Ummulsulaym*
*F.A Ya'u*
🖊🖊🖊🖊🖊



⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
⚜⚜⚜⚜
⚜⚜
*AMRATU*

fayau9.blogspot.com
Fayau26.wordpress.com

*Page 70-75*
*Na*
*Ummulsulaym*
*Da*
*F.A Ya'u*


*Short and brief story*


*Dedicated this luvly page to all Amratu fans mun gode sosai da qauna da kulawar da kk bawa wannan novel din Allah yabar mu tare luv yah😘*


Kwankwasar da taji ne yasa ta miqewa taje ta bude.

A tsaye yake,tayi masa sannu da xuwa ya qara murtuqe fuska sannan ya amsa ciki-ciki ya shige sashensa.

✨✨✨✨✨✨✨
Amrah tayi shuru tare da binsa da ido sannan ta shige nata dakin.

✨✨✨✨✨✨
Saida tayi wanka sannan ta tsala kwalliyarta cikin wasu shegun English wears coffee colour,ko dan kwali bb ta fita falo ta xauna tana duba jarida.
✨✨✨✨✨✨✨

Ya fito shima yy wanka yafi minti biyu yana kallonta,yana qiyasta abubuwa da dama a ransa,ita dai ko alamar dagowa bata yi ba sai can ta dago ta kalleshi murya qasa-qasa tace "abinci fa"

✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Fuska asake yace nagaji yau kawo mun nan ta mike yakuma binta da ido azahiri bawai yagajin bane kawai so yake yakare mata kallo duk inda tayi kuwa idonsa nakanta.

✨✨✨✨✨✨✨✨

Ta'aje masa taja gefe ta zauna yadan kalleta ki cika ladanki ki zuzzuba min ta zuzzuba masa ke bazaki ciba naci tun dazu tace oho ya fada ya kuma dagowa ya kalleta ya karatun lpy klau tace .

✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Kinsan me ya fada ta 'dago alamar tana jinsa duk kin sauya kin dena shagawa tadanyi murmushi oh my goodness tai saurin kallonsa yasakar mata murmyshi kinzama kurma ne

✨✨✨✨✨✨✨

Shuru tayi masa,
Ta mike yaya gobe da lecture bata jira amsarsa ba tai dakinta tana taku dai dai ya bita da ido yakasa aje cokalin ko zuba abincin abaki rufo kafar dakin ta datai ne yadawo dashi hankalinsa yasaki wata nannauyar ajiyar zuciya.

✨✨✨✨✨✨✨

Yarasa meyasa yarinyar duk ta sauya masa komai nata ynx burgeshi yake salon data dauka ne yakejin bazai iya daika ba wato salon shiru.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Ada farkon auransu yakan dawo da niyyar ci mata mutunci anman da yadawo sai yaji yakasa yayin da ayanxu yake da burin kawai yadawo yaganta sai dai girman kansa yasa yakasa nunawa.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Haka ya gama cin abincinsa har ya xauna jira bb alamun fito warta ya gaji ya shige dakinsa.

✨✨✨✨✨✨✨

Ranar Monday ya tafi aiki abubuwa da yawa suna jiransa a office sai qarfe sha daya ya dawo,Amra na kwance a babban falo tana duba littafinta domin takaicinsa ya fara isarta duk wata dabara tayi bb nasara,gashi ynxun ita da kanta ta gane ta fara sonsa domin kullum wutar sonsa ne take ruruwa a ranta.

✨✨✨✨✨✨✨

Ya turo qofa ya shugo,ta mike tana kallonsa shi kansa kallon nata yakeyi.

"Sannu da xuwa"

Fuskarta a hade tayi mgnar ta hada littafanta ta miqe ta wuce sashenta,ya bita da kallo.kayan baccine a jikinta sun amsheta riga da wandone.

Aliyu ya tabe baki ya shige sashensa.

✨✨✨✨✨✨✨

Tsananin takaici dajin haushinsa bai barta tayi bacci ba sai qarfe uku na dare bayan tayi nafilfilinta ta kwanta,don haka tunda tayi sallar asuba ta kwanta bama ta tunanin xuwa lectures a safiyar ranar sbd ynda take jin jikinta.

✨✨✨✨✨✨✨

Shi kuma oga Aliyu ya tashi da matsa kaicin xaxxabi a ranar domin ko yatsa baya iya motsawa sbd ynda jikinshi yakeyi.

✨✨✨✨✨✨

Amra ta fito da safe domin yin breakfast domin a xatonta oga ya tafi aiki har ta gama aikinta bata ga alamun ya fito ba wata xuciyar nacewa jeki duba lfy wata ta haneta dayin haka tadai fatattaki xuciyar ta nufi dakinsa tana daidai falonsa,taji kakarin amai alamun bb komai cikin mutun yana aman wahala a guje ta isa wurinshi ta taimaka masa ya tashi amman ina qarfin mace da Namiji ba daya ba kawai qarfin hali yasa,ya tashi dakyar sannan tasa masa filo a bayansa ynda xaiji dadin xaman tunda bb karfi sannan ta samu ta gyaran ko ina ta sanya turare yana kamshi ta iso gareshi Yayah Aliyu sannu ya daga mata gira alamun yawwa tace ina phone dinka a kira doctor yace da ita alamun da hannu ta duba drawer dinshi akwai mgni taje ta kawo sannan ta hada masa tea yasha ya danji qarfi a jikinsa sannan ta hada masa ruwan wanka ta taimake sa har qofan bayi kafin ya fito ta gyara,gadon ta dauko masa kaya marasa nauyi ya yi mata alamun. da hannu ya fito taxo ta taimaka masa ya qara so taje ta riqo hannunsa sannan suka iso gado tace ga kayanka nan na kawo kasa bara inje in dafa abinci in dawo.


Ta tafi tayo masa,girki mara nauyi daidai buqatar mara lfy amman jefi jefi tana xuwa dakin ta leko shi harta gama ta kawo dakyar taci shima don yaga bacin ranta sannan yasha mgninsa ya kwanta.

✨✨✨✨✨✨✨

Itama a dakin ta kwana akan kujera amman motsi kadan yy yana kan idonta.

✨✨✨✨✨✨✨


Da safe ta shiga kitchen ta hada breakfast sannan tayi hidima dashi.


✨✨✨✨✨✨✨


Tsawon kwana biyu yadan fara murmurewa a ranar da taga haka saita kwanta a dakinta amman xuciyarta na dakinsa

✨✨✨✨✨✨✨

A Daren Aliyu ya dade baiyi bacci ba yana ta xuba ido yaga Amra Amman shuru domin dan takaitaccen xaman da sukayi da Amra ya tsaya masa a rai,a haka yata juye juye a gado har bacci ya daukesa.

✨✨✨✨✨✨✨

Da,safe ma Allah Allah Aliyu yake yaga Amrah Amman shuru shuru lkc lkc ya kalli agogo har goma tayi bb Amrah bb alamarta sai misalin sha,daya yaji alaman turarenta nan da nan yai baya ya lumshe ido kai kace bacci yake yi tayi sallama ciki ciki ya amsa,ta nemi guri ta xauna tana gayar dashi sannan ta shige bayin dake dakin ta hada masa ruwan wanka yana shiga ta miqe xuwa kitchen ta shga fiddo da kayayyakin abincin data,shirya tun tashinta kamar irinsu kunun gyada,arish ball da sauransu lkci qanqani daki ya dume da kamshin turare dana abinci😝don haka idan ka shaqa sau daya ba xaka so fita ba,Aliyu na fitowa daga wanka daman ta riga ta fiddo masa,da kayan da xaisa a qofan bayin ya dogara yana bin Amrah da kallo kwalliya tayi na fitan hankali daman gata da kyau amman yau tafi ranan aurenta kyau cikin qarfin hali ya dubi daddumar cin abinci data shimfida da varieties din abinci iri iri yace duk wa yy wannan?tace ni kadai yace kai amman aiki yy yawa,bana son ganin mace na aiki da yawa,don haka idan kinyi man abinci guda daya ya gamsar.
Basai kinyi da,yawa ba.

Bata amsa ba illa lumsassun idanunta da tayi alamun gamsar dashi tsigar jikinsa ya tashi yarrrr kallo ya bita dashi ta miqe xata fita yace ki dawo muci abinci idan ba haka ba,sai kuma yy shuru.

✨✨✨✨✨✨


Cikin kwana kin da suka shude muguwar shaquwa ta shiga tsakanin Amra da Aliyu Wanda har yasa duk cikinsu idan basu ga juna ba basa jin dadi kuma bb kwanciyar hankali.

✨✨✨✨✨✨✨

Mummy taxoqara duba lfyar Aliyu tagan shi ya qara murmurewa abun gwanin mmki a ranta tayi farin ciki tare da addu'ar Allah ya hada,kansu.

✨✨✨✨✨✨✨

Suna cikin hira Amrah taxo ta dan kanga jikinta jikin mummy kamar koda yaushe tace mummynmu ina wuni?Mummy ta shaqi kamshin Amrah ta murmusa acikin murmushin take cewa lfy qlw Amrah ta saki mummy sannan ta nemi three sitter ta xauna suka cigaba da hira harda,Aliyu sannan tayi masu nasiha da xata tafi har mota suka rakata sannan driver yaja ta tafi.


✨✨✨✨✨✨✨


A dakin Amrah sallamar Aliyu yasan
Tayi saurin bude ido tare da Satan
Kallon sa,a kullum qara kyau yakeyi cikin sauri ta suri hijabinta d ke gefe tasa yadan saki murmushi yadda tayin ya bashi dariya wannance rana ta farko da Aliyu ya Shiga bedroom dinta domin iyakarsa falo yadan qariso daidai lkcin daya saki labulen rigar bacci qaramace a jikinta domin. Ko cinyarta bata gama rufewa ba hannuwar rigar siraraine inka cire rigar bb komai a jikinta banda shower cap daman qa'idar baccinta knan sai kamshine kawai ke tashi na dum dum dum a jikinta yadan kalli gafen dakin komai yy masa hatta turarenwutar data jona ajikin burner ya burgeshi a hankali ya taka ya isa gefen gadonta.Amrah ya kira sunanta a maqoshinta ta amsa....

✨✨✨✨✨✨

*Masu karatu kuyi hqr akan rashin jinmu da Baku yi kwana biyu ba*


✨✨✨✨✨✨✨
*Ummulsulaym 09039729270*

*F.A Ya'u 09028287218*

*For comment, correction or advice*
~Love you Fans~


⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
⚜⚜⚜⚜
⚜⚜
*AMRATU*



*Page 75-80*
*Na*
*Ummulsulaym*
*Da*
*F.A Ya'u*.



fayau9.blogspot.com
Fayau26.WordPress.com

*Dedicated this page to mah Luvly frnd Safiyyah H Aliyu Allah yabar so da qauna*


*Short and brief story*


Yadan jima yana kallonta kafun ta ce daman nashigo ne mudanyi fira naga ke kuma kamar bakya mara ko tai dariya no yaya kawai dai sai tayi shuru kawai dai na takura miki ko a'a wallahi to kawai dai me tadanyi murmushi gami dayin shuru any way tunda ba'a buka tata bari naje ya juya dan futa dasauri ta mike tabi vayansa haba yaya nifa bance katafiba to kinfada mn tanarkar da murya to pls kadawo ya dan kalleta sannan yace to muje.

Suka sha firarsu wadda rabbinta ta rayuwa ce sai ta karatun amra wadda ya fuskanci tafi santa hakan yasa yaketa jawota sai wajan shabiyu ya kalli agogo kai gaskiya na jima adakinnan vari naje ko ta rako har bakin kofa sai dasafe ya amsa Allah ya tashe mu lpy ta turo kofarta ta rufe.

Shoko gogon naku koda yakoma daki ai kasa bacci yai amrarsa kawai yake hangowa tana sakar masa lallausan murmushinta dakyar barawon yasace shi wato bacci.

Da safe tashirya tsaf dan tafiya sch shi kawai take jira yayin dashiko tai zamansa adakinsa yana sane yaki fito wa so yake tashigo dakin yayin da ita kamar tasan abinda ya tsara taki shiga tai zamanta a falo lecture din 10 gareta ta daga ido taga hat 9:00 ta zaro ido kyashin tashi take ta mika hannu ta daiko phone dinta yah sunan da ta sanya masa kenan ta danna saida ta katse be dauka ba akaro na ukunne ya dauka cikin muryar shagwaba tace yah pls kafito ina makara zai mgn takuma ce pls yaya ta kashe wayar ba haka yaso ba yadai daure ya fito.

Ita ko mukli ko da ta bar gidan Ali kasa tukin tai yau ita ce wata zata nuna ma iko akan Alin data ci buri akai kuma Ali yana kallonta ya kasa ce mata komai saima korarta da yai daga gidansa kuka ya kwace mata sai da tai me isarta sannan taja motarta zuwa gida.

Agida ma yini tai tana kuka ba abinda tane tunawa sai janta da Ali yai zuwa gun motarta ya turata pls kije gida zamuyi waya kinga nan gidanta ne bansan rikici ba abinda yafi bata mata rai irin cewar da yai nan gidan Amra ne data tuna sai kuka tun ana rarrashinta agidan da tambayar ta mene suka hakura suka kyaleta.

Amra nazaune tana rubutu duk kwakwalwarta tahau caji wani assignment aka basu a chemistry tayi tayi tayi ba idea wani abin takaici itace group leader gashi presentation assignment ne tashiga tunani sosai kallo ta kawai take gaban tan course dinsu tana baza ido yan group dinsu nata harararta batasan ma ya shigo ba sai jitai ansure ta atsorace ta dawo daga tunanin da take ya dire ta yana dariya matsoraci kawai tai dan murmushi lah yaya yaushe kashigo yai murmushi kinacan kina tunani harnaje daki na dawo sannu da zuwa tace yawwa ya fada atakai ce kawon abinci ta mike tai gun dinning ya dauki kayan karatun yana kallo tazo ta dure masa gashi ya aje yafara ci saida yaji ya koshi sannan yace wai tunanin me kike haka bakomai tace.

Kedai fadi gaskiya wallahi wani assignment aka bamu ya cajan kai nakasa gashi gobe zamuyi presentation ya mike ina zuwa ya wanko hannunsa sannan yakarba sai da ya koya mata sannan yace ta amsa gyara kadan yai mata sannan yace sauran rehearsal na gobe ya zauna as student and sauran kujeru ya tsara mata yadda zai komai ta gwada ya tafa mata sannan suka koma wata firar.



Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment