Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata dan tana san makarantar ne da wallahi baxata ba haka ta kira yah nasir ya kaita sun sha hira nanma yake fada mata kwanaki mami bataji dadi ba tai ta mita tace xata je ko da daddare ne.




Yana zaune yana cin abinci ta zauna kusa dashi baiko dago ba balle yasan da ita tace yah lpy yace daman yah Nasir yace mun mami bataji dadi ba shi ne nace dan Allah ko xaka temaka ka kaini daga nan inasan inje sabuwar kofa wato asalin gidan iyayenta ce miki akai ni direbanki ne eyyi tai shuru to ba inda zan kaiki bakuma xakije ba batace uffanba sai hawaye kawai da take yafi minti uku yana kallonta yaja tsaki shirya muje tasaki murmushi nagode yaya tai daki.


Tayi shigarta dingin bingil material ce pink ta amsheta sosai,ta fito falo sai kamshi take yi shi har ya saba da cin abinci mai dadi da kallon kwalliyar kallo daya yai mata ya dauke idonsa yana gaba tana biye da shi.



A can gidan mami hira suka sha ita da yan uwanta ji take kamar karsu tafi jin zata gida yasa mami hada mata tsara sosai dan kai musu.


Acan sabuwar kofa ma dai sun taba fira dayake in kadauke shakuwa irinta jini basu wani saba ba kannenta ma bakuwa suke daukanta mamanta tace ina dai kuna zaman lpy tai dariya eh mama to Allah ya dawwamar bata ce uffan ba dan kunya yawwa inasan fada miki nasani Hajiya Aisha uwa ce agunki anman kisani Aliyu danta ne dole saikinyi hankula da kai mata kararsa ko sukarsa kinji ko diyata tai dariya to mama tare ma muke dashi babanta dake kan tabarma yna cin tuwo yace jaji ja'ira bakya bakya cewa yashigo wallahi baba nace yashigo yaki ya mike hara haje yana ganinsa ya durkusa yana gaisheshi haba Ali se kace wani bako yai dariya to muje mama na ganinsa tace dan nema wato surukuta kame damu kenan ai da kanka tsaye kake shigowa yai dariya yana sosa keya ananma sun sha fira sai goma suka koma goda.....


✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾
*Ummusulym*
*F.A.Ya'u*

Dan ci gaba duba b
fayau9.blogspot. Com



⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
⚜⚜⚜⚜
⚜⚜
*AMRATU*




*page 45➰50*
*Na*
*Ummulsulaym*
*Da*
*F.A Ya'u*

fayau9blogspot.com
fayau26.wordpress.com


*Short and brief story*



*We Dedicated this page to Xee Yabour,Husnarh(my hussy)Miss Xoxo,Miss Mjay,Miss Gorgeous, Memxiey,Tuartah Aberdah(Taurah😜),Also Noor Luv you so much kwando-kwando😜😘😘😘*




Suna komawa gida lkcin ta gaji sosai da yake sun cika cikin su bata wani kalla kitchen ba tayi shigewata can bacci ya fara daukanta taji rankwsmashi ta tsakiyar kanta wani azababben zafi ya ratsata cikin magagin bacci tace haba wannan wane irin wulaqancine mutun yana cikin bacci sa aso a tasheshi...bata qarisa ba taji a murda bakinta tare da jan mata kunne keh tashi ai da sauri ta mitsika ido data tuna abinda tace batasan sanda gumi ya keto mata ba a ranta tana cewan lallai kashina ya bushe,yaci gama keh ni kk wa rashin kunya tabb yau jiki xaiyi tsami yaja mata kunne Wanda saida ta durqushe qasa ya qara jah da qarfi sannan yace dan wulaqanci ke na sane da kullum da daddare kafin in kwanta sai nasha ruwan Lipton Amman yau tunda kin rainani kk yi shigewarki gani dan iska kinyi shigewarki ba xaki dafa ba ko inyi duk abinda xanyi yana mgn ne hannunsa riqe da kunnanta cikin kuka tashe Allah Yaya Aliyu baccine bansan sanda ya kamani ba kawai gajiyane nayi yace "eyye wato kinma gaji ni kike cewa kin gaji ni nace ki kirkiro tafiyar ina seda nace bazaki ba kika sakan kuka ?" Tayi shuru toh ynxun muje ki hada maxa ki kawo minti biyar in ya wuce double punishment 😑aikam har kitchen ya rakata sannan ya sakar mata kunne ya tunkudata.
Aranta tace Allah yah Ali mugune dan dai ruwan tea tunda nai bacci ai ya dafa ahaka tana tsaye har ya tafasa kanta ke mata wani irin ciwo sakamakon tsoratar datai da ya rankwasheta haka ta daure ta kai masa.


✨✨✨✨✨✨✨


Yana sana'ar tasa wato danne dannen laptop ta kawo saida yaja aji sannan ya daka mata tsawa tare da cewan da yake kin rainani koh dole ki yi mini tsaye akai saina amsa tunda ga sa'anki yana mgn jiki na rawa ta ijiye sannan sum sum ta tafi daki ta haye gado saida tayi kukanta 😭ma ishi sannan barci ya kwasheta.


✨✨✨✨✨✨✨


Da safe da xaxxabi ta tashi sbd a daddafe tayi sallah subhi sannan ta koma ta kwanta sbd jin kanta wani irin sarawa da yake yi


✨✨✨✨✨✨✨


Safiya lkcin tashi bacci yy domin Six take tashi tayi aiki da girki sannan ta shirya xuwa makaranta Aliyu ya kaita yau yajita shuru baiji alamun ana girki a kitchen ko wani alamun movement dinta yace "Ah lallai yarinyar nan wuya yy qwari amman xanyi mgninta sbd wulakanci sai munyi latti"
Ya dai xauna shuru shuru bb alamun ta ya tashi da niyyar yaje yaci mutuncin ta yana qiyasta abinda xaiyi mata a ransa yana xuwa yy turus ya tsaya dalilin hangota da yy can quryar gado da qaton blanket sai rawan sanyi takeyi
*Tuartah yar sa idoπŸ‘bata bari ya qariso ganin me ya samu Amrah ba har tayi saurin sako kai nai saurin turata baya to yar sa'ido ina ruwank 😜*


✨✨✨✨✨✨✨


A fusace ya yaye blanket din da niyar fara fadan da yasaba yadda ya ganta a dunkule tana rawar dari yasa shi fadin subhanallah ya dagota tai saurin janye jikinta yaja tsaki ke tun yaushe ne baki da lpy tai shuru koda yake ma ace mutun bashi da sana'a sai kuka ba dole jikinsa ya gaza ya fara cuta ba ya mike gami da ficewa.


✨✨✨✨✨✨✨

Ita dai tana kwance yadda ya barta ko motsawa ta kasa yi ya shigo rike da tea mai kauri da ya hada mata gefe guda kuma yana rike da magani ya dagota ahankula yake bata harta shanye ya bata maganin saida yai jan ido sannan ta iya sha aikuwa tana sha tayo amansa ajikinsa takaici ya kamashi ya mike gami dayin waje da tsumma ya shigo ya goge gun tas itama ya goge mata jikinta data bata sannan ya dauko mop ya goge gun ya kamata zuwa toilet da zunmar wanke mata jikinta data bata aiko yana kokarin xuba ruwan taga dai dagaske yake ta noke zan wanke ya tabe baki gami dayin waje.

✨✨✨✨✨✨✨

Karnin da yaji dakin nayi yasashi feshe shi da turare nan da nan kamshi ya bai baye ko ina data fito yace bara na kira doctor tace yah kabar na warke hararar da ya watsa mata yasata yin shuru kan doctor yaxo ya kammala girki dayake tun yana gida ya iya komai dan mami dan sun kasance maxa hakan besata kasa sanyasu aikin gida ba.
Koda doctor yaxo yace ai gajiya ce kawai ba wani abu ba ta dan huta ya rubuta mata magani gami da tafiya aranar yini Ali yai yana mata hidima komai na gidan shi yai ita dai binsa kawai take da ido.


✨✨✨✨✨✨✨

Yah na shirya ta fada ya dan kalleta harta fada yace kin shirya me sch mana ya cigaba da abinda yake bai ce mata komi ba ta kuma daurewa yah nafa shirya zan makara adan fusace ya dago ke wai bakisan ciwon kanki bane na fuskanci zaman gidanne bakiso inba haka ba mutun bai da lpy yace sai yaje makaranta tace cikin raunanniyar murya wallahi yaya na warke kuma ganinai banyi reporting ba kar ayi attendance ko test eh kice karatu yafi lpyar ki to ba inda zaki tai rau rau da fuska zata sa kuka yace karki fara nafada miki batun yauba inda abinda yafi ban haushi dake to wannan kukanne ki koma daki ki kwanta kuma nashigo naga kina kuka Allah nida kene.

✨✨✨✨✨✨✨

Sai da tai bacci ta tashi ta tuna da maryam kawarta da sauri ta dauki wayarta dan kiranta ta fada mata bata da lpy ko dan ta sanar sai dai wayar bata shiga gashi number dinta kawai take da dan da ita kawai suka saba sosai taja tsaki itama dai maryam matsala ce wallahi ta fada gami da saukowa daga gadon toilet din dakin tashiga tai wanka gami da dauro alwala dan lokacin azahar yayi sai da tai sallah sannan ta fito da niyar dafa abinci.

✨✨✨✨✨✨✨

Ga mamakinta yauma kamar kullun tana fitowa falo komai tas kamshi kawai ke tashi wato yah Ali ya gyare gidan tas tai kitchen da zummar dora abinci ta akan tukunyar taga ya dora takarda da rubutu kamar haka _your breakfast in the dinning_ tai murmushi gami dayin waje komai yayi tana ci tana murmushi lokaci lokaci tana tubawa da yanayin Yayan nata.


✨✨✨✨✨✨

Jikinta yai sauki batajin komai dan yanxu tana riga yah Alin tashi ta kammala komai anman taga alamar har yanxu bai ga damar barinta taje sch ba hakan yasa yau tai niyar zuwa ta sameshi yana zaune yana kallo tazo ta zauna ko kallon inda take bai ba tace yah sannu da gida bai amsaba ta riga ta saba da halinsa tace yah dan Allah kaga fa na warke gobe ka barni naje sch pls yadda tai maganar yaso bashi dariya ya daure kije zanyi tunani pls yah to shikenan ki shirya tunda naga kin dena kuka tai murmushi gami da far da ido nagode yaya tai ciki.

✨✨✨✨✨✨✨

Ai kuwa a sch tasha ciwon baki bataxo ba kwana biyu anyi test hankalinta ya tashi dataji malamin dayai dan shi inbaka da test co direct aikuwa akan maryan ta hakke ita dai maryam hakuri ta dinga bata tace network ne ita wayarta kullun akunne take ita ce ma ankirata akashe.

✨✨✨✨✨✨

Dan Allah maryam in mungama lecture dinnan zaki rakani muje inroki malaminnan ko zai min test din ke nifa tsoronsa nakeji inji maryam pls kawas zainab dake gabansu tadan juyo kunsanfa halinsa kudena surutu karku jaza mn masifa kan tai shuru sukaji yace Amra Muhd Nasir stand up pls Amra ta kwalalo ido nashiga uku ina wannan mutumin yasanni Maryam tace ki tashi watakil yaga surutun da muke cikin Amra ya turu ruwa........

✨✨✨✨✨✨


*Loves u Fans especially ummusulym and F.A.Ya'u group members*


✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾
*Ummusulym*
*F.A.Ya'u*



[1/6, 8:45 PM] Fadima A. Ya'u(F.A.Ya'u)😘: ⚜⚜⚜⚜⚜⚜
⚜⚜⚜⚜
⚜⚜
⚜



*Amratu*


*50-55*


*Na*

*Ummusulym*

*Da*

*F.A.Ya'u*

fayaublogspot.com
Fayau26.wordpress.com


Who is Amra nace jin ya fadi haka yasata dan colling down tunda ta gano be santa ba maryam ta taba ta ki tashi karyai fushi ko bataxo bane tai saurin mikewa gani sir yadan kalleta au da kina ma gabana kikai min shiru koda yake ai naga tun daxu firar ku kawai kuke sorry sir tace any way u are deceiving ur self not me kinga ba ma wannan ba ya gijin ya fada tai saurin kallonsa Yayanki yaxo ya samemu yace baki da lpy nai test ki shirya gobe xan baki make up baiji ta cewarta ba yai ficewarsa dan daman ya gama lecture dinsa ana ficewa ta fada jikin maryan tana murna kai anman naji dadi da tuni co direct tai dariya mantawa nai ban fada miki ba ai tun randa bakixo ba yayanki me kawoki wataran yaxo ni nama kaishi office din Hod tai dariya aranta tace yah Ali kenan miji nane ta fada a hankula what maryam tace da ita ita kanta batasan sanda ta furta miji nane ba kunya duk ta rufeta.

✨✨✨✨✨✨✨

Maryam ta riketa da gaske kike kina da aure tai dariya eh zance ne be tada zance ba tun kanna shigo nakeda aure kuma da gaske shine mujinki ta daga mata kai alamar eh kai anman kinyi dace wallahi ko yai dace ba suka sa dariya Allah ki yadda dani samin sa a miji ba karamin dace bane kinga ni mubar batunsa awwo kishi kike ko tai dariya πŸ˜ƒ kawai.

✨✨✨✨✨✨✨

Waiko ina yayan nan naki Nasir tai dariya kwayi kwa gama ai tuni na ganoku kuna wani kunbiya kunbiya shima tunda ya kyallara ya ganki ya hanani sukuni ganin ta rafkota yasata sauya zancen da wani ke yar gata ce Amra ko ta fada eh mana ko ina kikai yayu na biye dake ga mijinki me sanki aranta ta kuma mai maitawa gamijina me sona tai dariya kawai.

✨✨✨✨✨✨✨

Koda ta koma gida ta kammala komai ta zauna dan kallo anman ina tunanin Yah aliyunta ya cikata shi kawai take ganowa yayin da yake goge mata jiki lokacin da bata da lpy ita kadai taketa sakin murmuahi musanman idan ta tuno lokacin da yake fada.

✨✨✨✨✨✨✨

Yana zaune yana kallo ta zo ta zauna a kujerar datake kusa dashi tace yah sannu da gida yaya yawwa yace batare da ya kalleta ba ya ciga ba da abinda yake can ya dago ko da wani abunne a'a daman cewa xanyi na gama abincin na kaima dinning ok nagode wani dadi ya cikata yau yace ya gode ji take kamar yai mata wata gaga ruwar kyautakyauta.

✨✨✨✨✨✨✨

Yana ci tana kallonsa jefi jefi tana sakin murmushi shiko gogon nata ko ajikinsa dan bema san tanai ba yadan jiyo jin ajikinsa kamar ana kallonsa tai saurin dauke kanta yaso fuskantar wani abu ya tabe baki gami da ci gaba da cin abincinsa dan baya gajiya da cin abincin yarinyar mami tai mata horo wajen iya girki ganin zai ganota yasata mikewa tai daki.

✨✨✨✨✨✨✨

Yadda suke zaune ba yabo ba fallasa fada dai yaki dewa yayinda ita kuma taki dena shagwaba abinda ke bashi haushi da ita dan ko ayau ta hadu da mami sai tayi abinda be saniba jikinta ya saba tana iya kokarinta wajen san ta dena.

✨✨✨✨✨✨✨

Kai Abbakar ka cika natsala daga can daya barin bataji me akace va taji dai yayan nata yace to shikenan sai kaganmu ya kashe wayar ganin goma tayi wato time din baccinta yasata mikewa da zummar yin daki ke ya ce taja ta tsaya gobe ki shirya zamu gidan Abbakar to yaya tace tai ciki.

✨✨✨✨✨✨✨

Washe gari ta shirya tsaf tai kyau sosai ta fito baya falon tai dakinsa da alama alokacin ya fito daga wanka yana goge jikinsa kunya duk ta kamata ganinsa dagashi sai tawul tai niyar juyawa ya tsai da ita ina kuma xaki gani nai kana shiryawa yaja tsaki matsalarsa da yarinyat tafiye gida danci ok fadi me ya kawoki daman cema xanyi na shirya yadan kalleta ke na fuskance ki gabaki daya bakisan zaman gida wato danace zamu unguwa ai shikenan farin cikinki yaxo zaki shirya da wuri tasaki murmushiπŸ˜ƒ kawai tai waje dan ta rasa me zatace ganewa ne beba ita ba unguwar takeso ba face fita dashi din dan ko bakomai in sunje gu baya shurun da yake mata agida zagewa yake ayi fira tare dashi ita ayanxu ba abinda takesan ji kamar muryarsa koda fadane shiyasa inta tarasa yadda zatai yai mgn take tsokanoshi yaita fada 😑tashige daki tai ta dariya.πŸ˜‚

✨✨✨✨✨✨✨

Yai kyau shima cikin shigar shaddarsa blue komai yaji inji matasan yanxu yai mata kyau a ido jitake kamar karta dena kallonsa tadai basar sai ayanxu yadan kalleta muje ko tai saurin yin gaba yaja ya tsaya ke me kike nufi ne tadan tsaya gami dabkallonsa kina nufin da wannan shigar zaki fita takalli kansa me tayi bansani ba jeki ki sauya matar aure ce fake yah naga kai zaka kaimu ka dawo damu ya daga mata kuma naga kinga ni atsarina matata hijab xata sa ta turo baki anman ko bakomai taji dadi tunda dai ya dauketa matarsa tai ciki.
Tafito sanye da hijab shi bega abinda ya sauya ba yaja tsaki suka tafi.

✨✨✨✨✨✨✨

Acan gidan Abbakar ansha fira da korafi kan Aliyun be kyauta ba ace tunda sukai aure ya kasa kai matar aagaisa mita kam yashata da yake sun saba da matar irin masu rahan nance tai tamasa tsiya eh kayi aure ka gujemu yace ke kuwa ba dole ba cewa nai ba huta da gori nima dai wane gori inkaga ka huta dashi sai kun aje mn babies kunya duk ta cika amra fuskantar hakan yasata janta zuwa ciki aiko tun tana sun sunkewa harta ware suka sha fira irinta gari dan Amra irin mutanannan ce da baka taba jin sirrinsu sai dare suka baro gida tare da jibgin alkairi daga Amina matar Abbakar.

✨✨✨✨✨✨✨

A hanya yake tambayar ta mene babu agidan tace aranta gida akwai komi saidai ginshikin gidanne babu afili tace akwai komi kifi da tumatir ne babu a jifato ya tsaya har ta fito da zummar binsa ko me ya tuna ohoo yace koma ki jirani.

✨✨✨✨✨✨✨

Da suka koma gida ta kaimasa tea dinsa tai dakinta wanka ta shiga tai wankanta gami da dauro alwala sunyi isha acan dan haka shafa'i da wuturi tai tafada gado dan tagaji sosai gashi gobe monday tanada lectute 8.

✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾
*Ummusulym*
*F.A.Ya'u*
[1/7, 3:44 PM] Fadima A. Ya'u(F.A.Ya'u)😘: ⚜⚜⚜⚜⚜⚜
⚜⚜⚜⚜
⚜⚜
⚜


*Amratu*


*55-60*


*Na*


*Ummusulym*


*Da*


*F.A.Ya'u*





*In Dedication to Halima Dangado(Dangadoriasis)😘😘*


fayau9.blogspot.com
Fayau2626.wordpress.com

Da wurwuri ta tashi ta kammala komai dan tanasan yau tashiga sch da wuri karfe bakwai dai dai ta fito ga mamakinta Yah Alin bai nan tai dakins sai takar da ta gani kan gadon da alama ita ya barma ta dauka abinda ta gani shine _Nashiga baki tashi ba jiya ban fada miki ba anturamu kaduna a gun aiki yau zan dawo ki kijira nace wani agida yaxo ya kaiki sch_ har ga Allah har ranta taji ba dadi tace Allah ya dawo dakai lpy aranta tai falo ko karyawa ta kasayi sai a flask ta zuba tana jiran me zuwa kaitan.

✨✨✨✨✨✨✨


Tadan russuna ta gaidashi Yah nasir ina kwana yaki amsawa shima yafan russuna kanwarmu ina kwana ta turo baki kai yaya nafa ce bana so nima nace ki dena gaishe ni kinki kefa matar yaya na ce Allah zanyi fishi dakai to ayi hakuri baxan kuma kaso ka makara yai murmushi bansan da zuwanba seda naga yaya sulaiman zaixo yace zaizo kai kine nace yabarshi na kaiki tai dariya kaji dashi dai yadan kalleta me xanji dashi tai darita ni muje ina makara.

✨✨✨✨✨✨✨


Ahanya yake mata maganar maryam tasa dariya ahaf ai nasani me kika sani ohoo gashi data fara wari mun faraji kinga ni bafa wasa nake ba pls ya za'ai ko number dinta ki ban tadan daga kai alamar tunani any way zanyi tunani haba aunty Amra ta tsuke fuska to wallahi zaka sanya infasa to nadena kanwarmu ta bude motar gami da lekawa inkaje ka gaida mami dan Allah kace wanda zaizo dauka na yaxo da wuri to yace tanxu number dinfa kabari zan tambayeta to shikenan se najiki.


✨✨✨✨✨✨✨


Bayan sun fito daga lecture Aisha taxo pls maryam yunwa nameji zoki rakani village Amra tace af kinga na mance naxo da abinci inxaki ci me zai hana yadda nakejin kudinnan nawa suka saka dariya dayake abincin da dan yawa tare suka ci su ukun Aisha sarkin jama'a ta mike ina zuwa tai gun dataga wasu na fira.


✨✨✨✨✨✨✨


Amra ta kalli maryam ban fada miki ba inajinki ai yau mutumin naki ne ya kawo ni tsaf ta gane wa take nufi ta basar wa kenan tadan kalleta ana so ana kaiwa kasu pls wa kike nufi ban gane ba waye inbanda Yaya Nasir tadan ja tsaki yaushe ta zama mutumina ohooo kya tambayeni kinga daman cewa yai inbashi contact dinki nace ai ankusa bikinki ta fadi haka ne dan ganin yadda zatai what inji uban...tai saurin rufe baki haba Amra yazaki min haka ke kika kusa bikin nawa aiko ankusa nasamu kama Nasir butsewa zanyi kaji yar newa to cewa nai zanmaki mgn abinda kika ce ynx zance ya kwantar da hankalinsa kema kina ciki haba ke kuma karki bada ni mana bama haka suka sa dariya vaki daya.


✨✨✨✨✨✨✨


Koda aka tashi Nasir ne yazo daukan Amrar sai da ya takura mata ta kira masa maryam dan ita tayi faculty din History dan dauko kanwarta da yake ita take driving aiko awayar tasha tsiya takusa minti goma bataxoba ta koma gefe dan kar yajita ke banfa san wulakanci yaysn nawa ma sai anja masa aji tai dariya yi hakuri ganinan.


✨✨✨✨✨✨✨


Anya kuwa kin kirata wallahi na kirata yaya tace kanwar tata ce bata fito ba ok ban wayar na kirata kan tace wani abu ya faketa ya kwace wayar yasa number din awayar tasa yana kokarin kira ta karaso Amra na kallonsu sai wani shassharewa Maryam take kasa kasa take musu dariya dan kar yagano wani abu.

✨✨✨✨✨✨✨


A gida gabaki daya ta kasa bacci duda bata iya wuce 10 sai gata har 11 idonta tan gararas sai 12 ya shigo gidan ga mamakinsa tana zaune ta rafka ta gumi bakuma kallo take ba dan ita din ba gwanar sa bace yazauna wash ya fada duda yai sallama bataji ba wash din data ji ne ya firgita ta tai saurin dagowa atsorace yasaki murmushi matsora ciya kawai tai dariya lah yaya sannu da zuwa yawwa ya fada ban ruwa ta mike jiki na rawa tai gun fridge yakar ba yasha tai dinning area ta hado masa abinci sai da ya fara ci ta mike gami da gada masa ruwa nakai maka toilet tadago yana murmushi me ya hanaki bacci kamar tacd rashinka ta daure tsoro to ynx na dawo jeki ki kwanta gobe da sch nagode Allah yai albarka amin ta fada gami dayin dakinta har bacci ya dauketa tana tunawa da dagowar dayai cike da murmushi fuskarsa maganarsa ke mata yawo aka to ynx na dawo jeki ki kwanta Allah yayi albarka.

✨✨✨✨✨✨✨


Da safe da wuri ta tashi ta gama komai tai makaranta A sch maryam ke mitar wallahi Amra baki da mutunci jiyafa kinso badani tai dariya tunda ban badake dinda ai shi kenan Allah da gaske nake inkina dariyar nan sai inna kalloki se inji nima kamar in sheke da darita kai dan Allah me yasa baki sheqe dinba mtseeew taja tsaki gami dayin gaba.


✨✨✨✨✨✨✨


Amra tabi bayanta ayi hakuri haba sis bafa ma haka dake ni ki kyaleni dole tasata dariya harta tsaya baki fadan ya kukai ba tadan tsuke fuska sirrinmu ne aha lallai masoya haka zaki ce eh haka zance to dai kiyi ahankula se inki baki shi ko sannu babarsa tasa dariya.


✨✨✨✨✨✨✨


Toma wai ke banda abinki Amratu ai ke zaki girmamani yayanki nake aute hoooo maryam Allah ya shiryeki wato ma harkin daura muku aure ahtoo ya ranki fari tas tace to bari yazo zaki sha mamaki tai aji tana dariya maryam tabita da sauri me zaki ce masa ah ohoo ki bari inyazo kyaji tai tai tafada mata taki.


✨✨✨✨✨✨✨


Agida suna zaune suna cin abinci ita abincin ma bawani ci takeba shi kawai take kallo wayarsa dake can kan kujera ta hau ruri yace mikon wayar can ta mike da hanzari bata duba wake kiranba dan kar kiran ya tsinke ta kawo masa yadan kalli screen din waya yawani saki murmushi kafin ta kara akunnensa taji yace Aminci agareki yake masoyita wani tukikin bakin ciki yazo mata wuya bataji me akace ba daga daya barin sai murmushi dataga yasaki tare da kara narke murya tare da naki afusa ce ta tashi tabar gun hartana faduwa dan ita kadai tasan me takeji aranta ya juyo ya kalleta ya tabe baki alamar i don't care yaci gaba da wayarsa......

✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾
*Ummusulym*
*F.A.Ya'u*

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
⚜⚜⚜⚜⚜
⚜⚜
⚜



*Amratu*


*60-65*


*Na*


*Ummusulym*

*Da*

*F.A.Ya'u*






fayau9.blogspot.com
Fayau26.wordpress.com





Daki ta shige ta bugo kofar da karfi tana shiga kuka ya kwace mata ta jingina ajikin

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment