Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

musu bayanin sallama sai
gimbiya Suzaila ta rugo gareshi suka rungume juna a
lokacin da hawaye ke zubo ma ta ta ce, "Ka
gafarceni ya kai Abbana ka yi sani cewa ban ta ba
nisanta da kai ba sai wannan lokaci kuma ba don ina
so kana so zamnu rabu ba sai domin wannan tafiya ta
zama wajibi tunda ita ce ruhin ceton rayuwar
dukkanin jama'ar da ke wannan nahiya tamu."
Sarki Huraisu ya numfasa a lokacin da shima
hawaye ya zubo masa ya ce, "Tabbas magan arka
gaskiya ce, shin yanzu kin yi sallama da
mahai fiyarki?"
Suzaila ta ce, "Na yi sallama da ita amma
yanzu haka ma tana nan a can kofar fadar nan a
tsaye tana jiran ta ga fitowarmu"
A can 6angaren Sarki Imras kuwa, bayan an sallami matafiyan sun fara kokarin fita daga cikin
fadar sai Sarki Imras ya kwalawa yarima Husnalu
kira shi kadai ba tAre da ya kirawo gimbiya Lushaira ba....

Nima kuma rashin jin ya kirani yasa zan
dakata anan saikuma wani lokaci
AA Misau ke magana
Dafatan kuna nan cikin koshin lafiya
Domin shiga whtsap group dinmu ga link nan a kasa
👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30QBUSA A MUTU
Littafi Na Biyar (5)
Part D

Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau ke Magana

Barkanmu Da wannan lokaci dafatan kuna lafiya ya ku Jama'ar wannann gida ina muku fatan Alkhairi

A lokacin Liushaira na tsaye daf da Hasnalu.
Koda Hasnalu yaji Sarki bai kira 'yar uwarsa ba sai
shi kadai sai kawai ya kamo hannun Lushaira ya ja
ta da gudu suka nufi inda Sarki Imras ke tsaye
Hasnalu ya yi hal:an ne don kada mutane su gano
cewa akwai wata matsala tsakanin gimbiya Lushaira
da mabaifinta.
itama Lushaira sai ta tafi ga Sarki Imras cikin
tsananin farin ciki suka rungumeshi gaba daya.
Koda Sarki Imras ya ji Lushaira a jikinsa sai
ransa ya baci, duk maganganun da yake son ya
gayawa Hasnalu sai ya fasa.
Haka dai ya yi musu bankwana ba a yadda yake
so ba kuma ya rakosu har kofar fada.
Anan ne su gimbiya Suzaila suka riski sauran
abckan tafiyarsu a tsaitsaye bisa Rakumà da
Dawakai kuma ga guzuri mai yawan gaske a tanada
akan Rakumai kuma kowanne Basarake da
Kuyanginsa guda goma sanye da tufafi mai launin
tutar birninsu suma duk suna bisu kan Rakuna.
Ba tare da bata lokaci ba aka hau kan dawakai
sannan aka kama hanya aka fice daga cikin birnin
Lairuf.
Sarki Imras da Sarki Huraisu na Lsaye a kofar
gidan sarautar suna hangen 'ya'yayensu har sai da
suka 6ace musu da gani sannan Sarki Imras yai
ajiyar zuciya ya dubi Sarki Huraisu ya ce, "Ya kai
abokina ka yi sani cewa wannan ita ce damarmu ta
biyun karshe wacce zamu iya ganin bayan
makiyanmu amma idan har su gimbiya Suzaila basu
hadu da sadauki Imran ba ya basu hadin kai anje
dajin Kirzufa an kashe 'yar uwata Husnaila da danta
Muraisu to muna cikin GABA TSINI, BAYA
SIYAKI."
Koda jin wannan batu sai Sarki Huraisu ya
numfasa ya ce, "Hakika na yarda da wannan bayani
naka to amma kai yanzu me ka gani a cikin
bincikenka bisa wannan tafiya amma kuma na ga
wani mummunan tashin hankali wanda zai biyo
bayan nasarar da aka samu.
Babu kokarin da ban yi ba akan na gano
kowanne irin tashin hankaline amma na kasa. Abin
da ya sa ban damu ba shi ne, koma wane irin tashin
hankali ne in dai mun kawar da Muraisu da Husnaila
ai mai sauki ne tunda fargabarsa ba ta kai tasu ba a
garemu, "
Koda jin haka sai Sarki Huraisu ya bushe da
dariyar farin ciki sannan ya ce, "Hakika ka zo da
magana mafi kyau da kwanciyar hankali a gareni.
Yanzu zamu zuba ido daga nan zuwa tsawon shekara
guda mu ga abinda zai biyo baya.
Wai shin ina son na tambayeka, mcne ne dalilin
da ya sa ka tura 'ya'yanka duk su biyun izuwa
wannan tafiya mnai hadarin gaske alhalin su kadai
gareka? Baka tsoron ka rasasu gaba daya?"
Lokacin da Sarki Imras yaji wannan tambaya
sai ya yi murmushi ya ce, "Dalilin da ya sa ka bar
yarka gimbiya Suzaila ta yi wannan tafiya shi ne
yasa nima na bar 'ya'yana suka tafi saboda bana son
su gano wani babban sirri da ke boye a karkashin
rayuwata.
Yanzu wane irin hukunci ya kamata mu
yankewa Sarki Jamal bisa laifin munafuntarmu gami
da hada kai da sauran sarakai don gudanar da abinda
suka ga dama ba tare da saninmu ba?"
Sarki Huraisu ya numfasa kuma ya dubi Sarki
Imras ido da ido ya ce, "Abokina ka sani cewa a
nahiyar nan gaba daya mun fi dukkan sarakunan nan
karfin mnulki, arziki da daukaka, saboda haka bai
kamata ace wasu Sarakai suna kawo mana matsala
ba a cikin harkokinmu.
Ina mai tabbatar maka da cewa koda bayan
mun kawar da wannan matsala wace ta addabemu
Sarki Jamal ba zai daina yi mana zagon kasa ba
saboda haka kamata ya yi mu kawar da shi daga kan
doron kasa gaba daya , kuma mu shiga kasar tasa na
Zabi wanda muke so ya ci gaba da tafiyar da mu."
Koda jin wannan batu sai Sarki imras ya hushe
da dariyar mugunta ya ce, "Da kyau abokina ka cika
abokin tafiya domin hazakarka da tunaninka duk iri
daya ne da nawa.
Wannan shi ne abında ya firu a birnin Lairuf
bayan an zabi Dakarun da za su tafi neman jarumi
Imran sadaukin da aka tabbalar da cewa shi kadai ne
zai zai shiga dajin Kirzufa ya kamo yaro mai kahon
BUSA A MUTU ko kuma ya kashe shi domin a huta
da fergabar mutuwar 'ya'yan Sarakai.
AL'AMARIN Su gimtya Suzaila kuwa,
lokecin da suka yi dan nisa ga barin cikin birnin
Lairuf sai suka rabu izuwa kaso hudu, wato runduna
hudu, kowacce runduna akwai shugabanta amma
bisa akasi sai ya zamana cewa yarima Hasnalu da
'yar uwarsa duk suna cikin rundunar gimbiya
Suwzaila.
Ba wai wani ne ya raba ayarin gaba daya ba da
hanunsa, kacici-kacici aka yi, duk rundunar da
mutum ya fada a lokacin da ake kacici-kacicin kawai
shi ke nan babu canji.
AA Misau ke magana
Hakika gimbiya Suzaika tayi
matukar bakin
Ciki da ya zamana cewa su yarimaHasnalu sun fado
cikin rundunarta amma da yake babu yadda za ta yi
sai ta hakura.
Nan take rundunar su Suzaila ta nufi yammaci,
sauran rundunonin kuma suka kasu gida uku, gabas,
kudu da arewa .
Sai da su gimbiya Suzaila suka shafe yini guda
suna tafiya basu yada zango ba, sai dai shan ruwa da
cin abinci ne kadai ke tsayar da su.
Duk tsawon wannan tafiya duk sa'adda Suzaila
ta waigo baya sai ta ga Hasnalu ya kura ma ta idanu
yana murmushi, al'amarin da ya fusatata ke nan
ainun ta ji ma ta tsaneshi gaba daya a rayuwarta
kuma ta kudurce a ranta cewar komai daren-dadewa
sai ta taka masa birki kuma ta cire masa soyayyarta
daga cikin zuciyarsa.
Daf da magariba ne suka iso bakin wata
korama. Kawai sai gimbiya Suzaila ta bayar. da
umarnin a tsaya a wajena yada zango.
Cikin tsananin farin ciki kowa ya sauko daga
kan abin hawansa aka daure dawakai da rakuma
suma aka basu abinci da ruwan sha, sannan aka
shiga kafa tantuna.
Gimbiya Husnaila na ta tantin dabam, tare da
kuyanginta suna yi ma ta hidima. Haka ma yarima
Hasnalu shima nasa tantin dabam kamar yadda
gimbiya Suzaila ma ta shiga cikin na ta tantin
kuyanginta suka yi ma ta wanka, sannan ta kwanta
akan shimfida mai taushi tana hutawa.
A dai-dai wannan lokaci ne ta fara gyan-gyadı
saboda 'yar gajiyar da ke jikinta. Daga can kuma sai
barci ya saccta gaba daya.
Faruwar hakan ke da wuya sai ga gimbiya
Lushaira ta shigo cikin tantin. Koda ganinta sai gaba
dayan kuyangin na Suzaila suka risina a gareta suka
kwashi gaisuwa.
A dai-dai wannan lokaci ne gimbiya Suzaila ta
fara sumbatun mafarki. Koda jin haka sai Lushaira ta
dubi kuyangin gaba dayansu ta yi musu inkiya da su
fice daga cikin Tantin.
Lushaira ta je daf da gimbiya Suzaila ta zauna
kuma ta kura ma ta idanu tana mai sauraron
sumbatun da take yi.
Kawai sai taji tana ta jero kalmomin soyayya
ga wani jarumin saurayi har take siffanta kyawunsa.
A cikin siffantashi ne Lushaira ta gane cewa ba
kowa bane wannan saurayi face sadauki Imran
wanda suka fito farautarsa.
Koda fahimtar haka sai hankalin Lushaira ya
dugunzuma ainun, take tausayin dan uwanta
Hasnalu ya turuketa saboda ta gane cewa SON
MASO WANI yake yi, wato KOSHIN WAHALA.
Abinda ya daure ma ta kai shi he, ya ya Suzaila
za ta fara soyàyya da muturnin da ba ta ta6a ganinsa
a'zahiri ba?
Kamar an ce da Suzaila tashi sai ta farka a
firgice tana mai kiran sunan sadauki Imran a fili
karara.
Koda ta bude idanủnta ta ga gimbiya Lushaira
zauhe a gabanta tana yi ma ta murmushi sai kunya ta
kamata sannah ta dubi ko ina a cikin tantin ta ga
babu ko mace daya daga cikin kuyanginta sai ta dubi
Lushaira cikin mamaki ta ce, "Ina kuyangina suke,
kuma nene ne ya kawoki nan cikin tantina?"
Sa'adda Lushaira taji wadannah tambayoyi sai
ta 'sake yin mufmushi ga Suzaila ta ce, "Ya ke
waninan yar Sarki jarumar jarumai ki yi sani cewa ba
komai ne ya kawoni nan cikin tántinki ba sai domin
BA Remi wata alfarnma guda daya a wajenki.
Dangane da kuyanginki kuwa ni ce na
sallamesu gabi dayansu saboda na shigo na iskeki
kina sumbatu na soyayya a cikin mafarkin na ki,
kuma abin kụnya ne kuyanginki su rinka jin ki kina
yin hakan".
Koda jin wannan batu sai Suzaila ta kamu da
tsananin kunyar Lushaira ta sunkui da kanta kas
kuma hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa, abinda
ke ma ta dadi. Daga can sai ta dago kante ohankali
s ta dubi Lushaira ta ce, "Wane irin sambatu kika ji
ALina yi a cikin barcina?"e asvot r s as
Lushaira ta ce, "Na ji kina anbaton sunan
6 sadauki Imran kuma kina ta zaiyana masa kalrno in
Hisoyayya tarmkar kun shafe shekar: a tare, kuina
kamar baki da warni masoyi wanda ya fishi a. doron
8t aves Ya ke Suzaila kina nufin ke nan: kin kamu da
8 tsananin son sadauki Imran tun gabannin ki ganshi a
zahiri? Kada ki 6oye mini komai tunda ciwon ya
mace na mace ne?"" st ấees n siie
Kodajin wannan bata sai jikin gimbiya Suzaila
ya yi sanyi ta dubi Lushaira a cikin nutsuwa ta ce,
a "Ya ke kawata ki yi sani cewa tun daga ranar da na fara jin labarin sadauki Imran na ji na kamu da
tsananin sonsa da begensa saboda ni a rayuwata ina
son jarumin da ya fini jaruntaka saboda shi kadai ne
mutumin da zai iya burgeni nà amsn
tas Haka kuma ina son mutumin da ya.fini kyau,
kuma ina son mutumin da zai iya yin abinda ni ba
bazan iya ba"'.
Koda jin wannan batu sai gimbiya Lushaira tayi
murmushi ta ce, "Ban ga laifinki ba domin ni na son
AA Misau ke magana
mutum mai ra'ayin kansa, kuma mại magana daya.
Amma ina son na baki wata shawara guda daya.
Shawarar kuwa ita ce, idan za ki so mutum
kawai ki soshi don son da zuciyarki ke yi masa da
kuma gamsuwa da shi a ranki, amma ba don kyansa
ko jarumtakarsa ba, saboda shi kyau yana iya
disashewa sakamakon tsufa ko sauyin rayuwa.
Haka kuma jaruntaka tana yankewa
sakamakon tsufa ko larura.
Alfarmar da na' zo nema a wajenki kuwa ita ce,
ina son kada ki kyahaci dan uwana Hasnalu a cikin
wannan tafiya kuma, kada ki wulakantashi saboda ni
na san cewa ya kamụ da tsananin kaunarki, idan kika
juya masa baya z ki iya jefa rayuwarsa cikin
mummunan hali.
A takaice dai abinda nake rokonki anan shi ne,
koda dai ba za ki nuna masa so ba, kuma ba ża ki
karbi soyayyarsa ba to kada ki wulakantashi.
Lallai ina mutuwar son dan uwana Hasnalu
fiye da yadda ma nake son kaina, idan kika gur6ata
rayuwarsa har abada ba zan iya yafe miki ba, Da
wannan furuci nakc yi miki sallama, sai da safe."
Koda gama wannan furuci sai Lushaira ta mike
tsayc ta fice daga cikin tantin gaba daya, ita kuwa
Suzaila sai ta bita da kallo cikin tsananin mamaki
tana juya al'amarin a cikin zuciyarta kawai.

Kashe gari da sassafe kowa ya tashi daga barci
aka kintsa sannan aka ci abinci. Bayan kowa ya
koshi ne aka cire tantuna aka dora kaya akan
Rakuma da Dawakai sannan aka ci gaba da tafiya.
Sai da aka shafe kwanaki bakwai ana ratsa
dazuzzuka iri-iri.
Ba a riski wani gari ba kuma duk inda aka
hadu da mugayen dabbobi ko 'yan fashi nan take ake
yi musu rubdugu a kashe na kashewa, masu gudu su
gudu saboda kasancewar jaruma Suzaila ce a kan
gaba ko yaushe.
Kwanci tashi, wannan runduna ta sami kwana
arba'in da daya tana tafiya sannan suka hangi wani
dan karamin kauye a gabansu da yammaci Sakaliya.
Har sun yi nufin su shiga cikin kauyen a sannan sai
kowa ya nuna cewar gwara dai a kafa sansani anan
daji a huta izuwa wayewar gari in ya so a shiga
kauyen da safe ido na ganin ido.
ls Suzaila ce kadai ba ta yi amanna da wannan
shawara ba ta ce, "Ya ya mu da mnuka shafe kwana
arba'in da daya muna tafiya a cikin dazuzzuka yanzu
kuma mun riski gari zaku ce mu yada zango a jeji?
Ai gwara mu shiga cikin wannan kauye yanzu a
wayi gari damu'
Koda jin haka sai kowa ya yi caa! A kanta ana
nuna rashin goyon baya, Yarima Hasnalu ne kadai
ya goyi da bayanta, al'amarin da ya fusata ta ke nan
ta hakura bisa dole tunda na rinjayesu su biyu.
Nan take aka kafa tantuna aka yada za go aka
fara shirye-shiryen abincin da za a ci.
Ana cikin wannan hali ne aka hango wani
mutum daga can nesa ya taho yana dogara sanda
yana tafiya da kyar. Mutumin na rataye da kwari da
baka, sannan fuskarsa gaba daya a cike take da
gemu, kasumba da saje tamkar tsohon da ya
Lanyanta a duniya amma da ya matso kusa da'su sai
suka ga tabbas saurayi ne ga dukkan alamu dai
wahalar duniya ce ta sa ya zama karnar tsoho.
Rigar jikinsa ta tsufa 'ainun, har ta fara
yayyagewa da kanta, sannan yana rike da wat
tsohon Akushi a hannuisa kai ka ce shi ya yankewa
Talauci cibiya.
Gaba dayan a jikinsa babu wani abu wanda
darajarsa za ta kai dinare daya face wani buzu na
fatar rago da ke rataye a bayansa a daure.
Wata kila dai buzun ne abin kwanciyarsa ko kuma
abinda yake shimfidawa ya zauna. Ko takalmi babu
a kafarsa, kuma da ganin kafar tasa ta sha wahalar
duniya saboda yawan tafiya har dunduniyar ta
tsattsage ta fara alamun faso.
Kallo daya mutum zai yiwa wannan Almajiri
ya san cewa duniya ba ta gabansa kuma idan mutum
mai kyankyami ne ma ba ria iya 'zama a kusa da shi
ba saboda tunanin zai iya vin warin gawasa.
A galabaice mutumin ya durfafo ina
su Suzaila yake yana tafe yana herfe kafafu kamayr
zai fadi yana sassarfa sabada tsaaanin gajiya gami
da yunwa da kishirwa.
Tur daga nesa kowa ya kura
masa idanunu, wasu na sai suka faie dora hannaye nasu
akan kufen takobinsu saboda basu yarda da shi ba,
jira suje kawai su ga ya yi wani motsi wanda basu
yarda da shi ba su fsr masa.
Idan ka dubi fuskar mutuninn baka iya shaida
irin kamanninsa saboda yawan gashin da ya lullube
fuska gaba deya idanunsa kaiai ake iya kalla a
gano cewa bai kasance tsoho ba amma ba Za a iva
banbancewa ba ya kasance muimuna ba ko
kyakkyawa, kavwai dai ya kasan ce talaka kuma
makiskanci wanda bashi a wani gata.
Da shigowar wannan Almajiri cikin sansarin su
gimbiya SuzailÉ™ sai ya fara bara yana mai cewa,
"Wa zai taimakeni da ruwa koda mukurwa daya ce,
waye zai taimakeni da abinci koda loma daya ne
Ubangiji ya biyashi.
Ya ku wadannan matafiya ku yi sani cewa yau
kwana na bakwai kenan rabona da na ci ko na sha. Sai
bilin-bituwa nake yi a cikin daji ni mafarauci ne
Kumma ko Kwaro ban sanu ba,"
Koda jin wannan batu daga bakin Almajirin sai
kowa ya bushe da dariya aka fara tunanin cewa lallai
Waninan Almajiri mahaukaci ne ko kuna dai
kwakwalwarsa ta tabu domin in ba wanda ya sami
tabin kwakwalwa ba ya za ai ya ce
Kwanansa
bakwai bai ci ba kuma bai sha ba amma yana raye?
Duk wanda Almajirin ýa dosa yana wannan
bara sai ya kyareshi ko ya koreshi. Wasu ma suka
rinka daga sanduna kamar za su koreshi.
Gimbiya Lushaira ce kadai ba ta kyari
Almajirin ba, kumna bata taimakeshi ba kawai dai ta
kura masa idanu tana mai jin tausayinsa.
Koda Almajirin yazo zai gifa ta gabanta yaga
tana yi masa kallon tausayi kuma ta kura masa idanu
cikin alamun tana yin wani nazari a kansa, sai ya yi
sauri ya sunkui da kansa kas ya wuce ta gabanta ba
tare da ya yi ma ta barar ba.
Kawai sai ya koma can gefe daya nesa da su
kadan ya zauna yana kallonsu kuma ya zuba ido ya
ga ko idan sun gama dafa abincin da suke shiryawa
Za su ji tausayinsa su san masa?
Haka dai Almajirin ya ci gaba da sauraron
tsammani yana ta faman zabga hamnaa gami da
hadiyar miyau a duk sa'adda ya dubi abinci ya ga
AA Misau ke magana
yana za6al6ala a cikin katuwar tukunyar da kuyangi
ke dafawa.
Bai gushe ba a cikin wannan hali har tsawon
rabin sa'a, sannan ne aka gama dafa abincin kuyangi
suka shiga raba abincin ana baiwa kowa.
Gimbiya Suzaila, Lushaira da yarima Hasnalu
cikin tantinsu aka kai musu na su abincin, sauran
dakaru, bayi da kuyangi kuwa kowa a bakin tantinsa
ya zauna ya kama cin abincinsa yana zabga loma
Suna kallon wannan Almajiri suna yi masa
murmushi da dariyar mugunta.
Wasu ma har daga battar ruwansu suke sama
suna shan ruwa, ruwan na zubewa kasa a banza.
Al'amarin da ya jefa wannan Almajiri cikin tsananin
takaici da bakin ciki ke nan, amma sai ya ki tashi ya bar wajen ya shiga cikin wannan karamin kauye da
ke gabansu domin ya yii bara.
Haka dai Almajirin nan ya ci gaba da jiran
tsammani ko wani daga cikin tawagar zai tausaya
masa ya taimaka masa amma shiru ya zamana cewa
kowa ya sude kwanonsa ko loma daya bai rage ba.
Kai da dai Almajirin nan ya tabbatar da cewa
wadannan matafiya basu da niyyar taimakonsa gashi
kuma yunwa ta isheshi ainun sai ya mike tsaye da
kyar ya zagaya bayan wani katon dutse.
Sai da ya shafe lokaci mai dan tsawo sannan ya fito
daga bayan dutsen ya dawo inda yake zaune ada.
A sannan ne ya ga gaba dayan matafiyan sun
shiga cikin tantinsu sun kwakkwanta domin su huta
gajıyar tafiya, wasu daga cikin dakaru ne kadai a
tsaitsaye suna gadi don tabbatar da tsaron sansanin.
Koda ganin haka sai Almajirin ya kishingida a
kasa kan kasa yana mai yin matashin kai da buzun
da ke rataye a bayansa.
Faruwar hakan ke da wuya kuwa sai barci ya
saceshi mai nauyi.
Kamar a mafarki sai wannan Almajiri ya ji ana
tashinsa daga barci. A firgice ya farka ya mike zaune
yana mai ambaton wata kalma.
Kawai sai ya yi arba da gimbiya Lushaira
tsugunnc a gabansa rike da akushin abincinta da
kuma ruwa a cikin tulu.
Kawai sai ta dubeshi cikin murmushi ta ce, "Ya
kai wannan mafarauci tashi ka kar6i abinci da ruwa
ka ci ka sha."
Koda jin wannan batu sai Almajirin ya cika da
tsananin mamaki ya dubeta ya ce, "Haba ya ke
wannan 'yar Sarki sboda me za ki hana kanki ci da
sha ki kawo mini alhalin ni ban kasance kowa ba
lace Almajiri mai neman abinci?"

Topah nima ganin wannan tausayi na GimbiyA lushaira yasa zan dakata anan saikuma wani lokaci idan Allah ya kaimu zamu ci gaba

AA Misau ke magana
Masu son shiga grp dinmu a whtsap ku danna wannan rubutun kasa
👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30QBUSA A MUTU
Littafi Na Biyar (5)
Part E
Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau ke Magana

Jama A Barkanmu Da Wannan lokaci Yaudai Insha Allah Zamu Kammala littafi na 5 Sannan Mu shiga Na 6 A Gaba

Koda jin 'wannan tambaya sai Lushaira ta cika da mamaki ta ce, "Kai kuwa ya ya aka yi Kasan ceWa ni 'yar sarkice?"
Almajiin ya yi dan guntun murmushi a garela
ya ce, "Haba, ai ido ba mudu bane armma ya san
kima.
Bisa ganin irin yanayin sutura dake jikinki kuma
Yadda na ga kuyangi .na shiga cikin tantinki, haka
kuma Dakaru suna tsaronki yasa na gane haka.
Wai shin ma ke menene dalilinki na taimakona har
kika ki cin abincin kika kawo mini?"
Koda jin wannan tambaya sai lushaira tayi
murniushi ta ce, "Ni ba zan baka amsAr tambayarka
ba sai bavan ka gama cinye yannan abinci da na
kawu maka ka sani nutsuwa".
Koda jin haka sai almajri ya yi murmushi. Ba
Tare da wata gardama va ya tsoma yan yatsunsa
guda uku rak a cikin abincin ya yi loma uku rak
sannan sai ya dauki ruwan tulun ya sha mukurwa
uku
Nan take ya yi gyatsa yana mai fadin wata
kalımar dai wadda Lushaira ba ta taba ji ba. Kawai
sai ya wanke hannunsa ya dubi Lushaira ya ce,
"Ubangiji ya yi miki sakayya da alharinSa Ni kam
na koshi kuma na gode bisa wannan taimako da kika
yi mini,"
Cikin tsananin mamaki Lushaira ta dubi
Almajirin ta ce, "Ya ya kai da ka kwana bakwai baka
ci ba, baka sha ba, yanzu za ka ci loma uku kacal ka
sha ruwa mukurwa uku kawai sannan ka ce ka
koshi?
Anya kuwa kai mutum ne? Ka gaya mini
gaskiya ko kai aljani ne.
Almajirin ya yi murmushi ya ce, "Tabbas ni
mutum ne kamarki, kuma haka yanayin cin abincina
yake.
Idan zan ci sama da loma uku amai zan yi,
domin zan yi cin haramun ne. Kuma inda zan sha
ruwa mukurwa uku to da cikina zai kulle saboda bai
saba da daukar ruwa sama da haka ba.
Ya ke wannan 'yar Sarki ma'abociyar kyau da
taimako, tunda har kin taimakeni nima kuwa zan
taimakeki.
Idan kuka shiga cikin wannan kauye da ke
gabanku gobe da safe kada ki ci ko shan komai.
Kada ki yarda ki zauna a ko ina face a cikin kasuwar
kauyen.
Kuma duk inda kike ki tabbatar da cewa kina
tare da dukkan 'yan uwanki. Kuma suma. ki hanesu
da duk abinda na haneki.
Da wannan furuci nake miki sallama Ni zan
Tashi na sake nauswa cikin dajin sai watarana idan muna da rabon sake haduwa
Koda gama fadin haka sai almajirin mike tsaye yana mai dogara sandarsa
Har ya juya yai gaba sai lushaira tace dakata
Almajirin ya tsaya cak a jnda yake, Lushaira ta
Shawo har gabansa Suka fuskançi juną sannan tace
Dazu kayi mini tambaya ban,baka amsa ba
saboda na ce sai ka gama cin abinci ka nutsu
tukunna.
Shis kana da, bukatar jin amsar tambayar
taka?
Almajrin ya girgiza kansa cikin murmushi: yan
ce, "Ai yanzu kuma ubangijina, ya,nųna mini amsar wannan tambaya da Nayi miki
Amsar kuwa itace kina da Tausayi da jin kai
sabanin sauran abokan tafiyarki.
ina mai yi miki albishir da cewa keçe kadai za
ki samu abinda kika fito nema
Koda gama fadin haka sai almajirin ya wuce
abinsa izuwa cikin daji ba tare da ya sake waigowa ba ko sau daya
Ita kuwa Lusihaira sai ta bishi da Kallo har ya bace mata ya zamana cewa almajirin ya 6ace 6at ta daina ganinsa.
AA Misau ke Magana
A sannan ne Lushaira ta mike tsaye ta shige
cikin tantinta ta kwanta.
Kashe gari da sassafe Lushaira ta shiga tantin
d'an uwanta yarima Hasnalu ta shaida masa cewa
kada ya kuskura ya ci ko ya sha wani abu a cikin
wannan kauye da za su shiga. Kuma kada ya zauna a
ko ina sai a kasuwa.
Bayan haka, duk inda yake ya tabbatar da cewa
yana tare da 'yan uwansa.
Koda jin wannan batu sai Hasnalu ya cika da
tsananin mamaki, ya ce, '"Ya ke 'yar uwata ke kuwa
mene ne dalilnki an fada min wannan batu?"
Nan take Lushaira ta zaiyane masa duk abinda
ya faru tsakaninta da wannan Almajiri a jiya da
daddare.
Koda jin haka sai yarima Hasnalu yai shiru
yana tunani da nazari a cikin zuciyarsa har izuwa
lokaci mai dan tsawo.
Daga can sai ya mike tsaye zumbur! Ya dubi
Lushaira ya ce, "Yanzu ina shi Almajirin yake?"
Lushaira ta ce, "Ai tun a jiya da daddaren da ya
gama cin abincin ya yi mini sallama ya tafi".
Cikin tsananin damuwa Hasnalu ya ce, "Shin
kin tambayeshi sunansa, kuma ya gaya miki inda ya
dosa daga nan?"
Lushaira ta gyada kai ta ce, "Ban tambayeshi
komai ba, amma ni kaina na yi matukar mamaki bisa
al'amarinsa da kuma wadannan kalmomi da naji
suna fita daga bakinsa masu yanayi da na irin
ma'abota adinin Musslunci".
Koda jiin hake sai hankalin Hasnalu ya
dugunzuma ainun fiye da ko yaushe ya ce"Ya yar
Uwata ki yi sani cewa kin yi babban kuskure da baki
tambayi .wannan Almajiri sunansa ba da inda yake
nifa Ina tabbatar miki da cewa wannan AImjiri shi
ne jarumi Imran wanda muka fito nema, jarumin da
si kadai ne zai íya zuwa dajin Kirzufa ya yaki mai
kahon BUSA À MUTU yayii Galaba a kansa ya yı
rnana magann wannan masifa da ta addabenu"
Koda jin wannan batu sai itama Lushaira
hankalinta ya dugunzuma ainun itama ta mike
zumbur! Ta fice da gudu daga cikin tantin, shima
Hasnalu sai ya bita da sauri, duk su biyun suka ruga
izuwa cikin daji suna nemnan Almajirin.
Sai da suka yi gabas da yamına, kudu da arewa
suna dube-dube anma ko duriyar Almajirin basu
gani ba. Bisa dole suka hakura suka koma can
sansaninsu inda suka iske tuni kowa ya gama
kimitsawa za a shiga wannan karamin kauye su
kawai ake jira.
AA Misau ke Magana
Tun daga nesa suka hango jaruma Suzaila bisa
dokinta ta kura musu idanu tana sauraren isowarsu.
Suna isowa daf da ita sai tå dubesu cikin
alamun danuwa ta ce, "Ina ku ka tafi muna ta
nemankü oamu ganku ba?"
A wannan lokaci gaba dayan abokan tafiyar na
tsaitsaye suna kallon Hasnalu da Lushaira suna
saurarOn amsar da za su bayar.
Cikin nutsuwa Hasnalu ya kwashe labarin duk
abinda ya faru tsakanin Almajirin nan da Lushaira
har izuwa lokacin da ya yi tafiyarsa.
Koda jin wannan batu sai ran jaruma Suzala ya
6aci, itama hankalinta ya dugunzuma ainun ta dubi
Lushaira da Hasnalu cikin fishi ta ce, "Tabbas kun yi
mana sakaki, na ji a jikina cewar wannan Almajiri
shi ne jarumi IMRAN wanda muka

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment