Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewar har ma ya fi mai kahon BUSA
A MUTU jarumtaka sai naji babu abinda nakeso sama
da na yi arba da shi kuma na gwada jarumtata akan
tasa, maimakon na fara jarrabawa akan nai kahon
Busa a mutu."
Koda Sarki Huraisu da Sabirat suka ji wannan
batu daga bakin Suzailat sai idanunsu suka zazzaro
suka kamu da tsananin tsoro.
Huraisu ya dakawa Suzaila tsawa ya ce, "Shin
baki da hankali ne za ki ce za ki tari sadaukin da babu
kamarsa a fadin duniya?"
Suzaila ta ce, "Ai tunda ya kasance mai hakuri da
gaskiya ko na tareshi da yaki ba zai cutar da ni ba. Ya
kai Abbana ka yi sani cewa idan har baka sa da ni a
cikin cikin wadannan mutane hudu ba da za su yi
wannan tafiya to fa sai jama'ar garin nan sun zageka
sun ce ka nuna son kai da rashin gaskiya saboda kowa
ya san cewa ni ce jaruma ta farko wacce ya kamata a
fara za6a tunda nafi kowa cancanta.
Ka tsaya ka yi nazari da tunani bisa wannan
gaskiya da na fada maka yanzu don kada ka aikata
abinda za ka zo ka yi nadama a kansa. Na barku
lafiya".
Koda gama fadin hakan sai gimbiya Suzaila ta
mike tsaye ta sumbaci goshin Sabirat sannan ta
Fice daga cikin dakin gaba daya.
Tana fita sai Sabirat ta dubi Sarki Huraisu cikin
tsananin damuwa kamar za ta fashe da kuka ta ce, "Ya
kai mijina ka yi sani cewa ina jiye maka tsoron ranar
da Suzaila za ta gano sirin da muke boye ma ta
dangane da yadda aka yi ka zamo Sarki.
Ina tabbatar maka da cewa idan ka hanata yin
wannan tafiya za ta gan0 wannan sirri da wurwuri,
haka kuma idan ka barta ma ta yi tafiyar in dai ta rayu
har izuwa karshen tafiyar to babu shakka za ta gano
wannan sirri don haka kana cikin tsaka mai wuya don
haka sai ka yi tunanin abinda zai fissheka.
Ni kam babu wata babbar rana ta bakin ciki a wajena wacce tafi ranar da Suzailat za ta gano wannan
Siirri."
Koda gama fadin hakan sai Sabirat ta fashe da
matsanaicin kuka, al'amarin da ya dugunzuma
hankalin Sarki Huraisu ke nan fiye da ko yaushe ya
rasa abinda ke masa dadi a duniya.
Nan dai ya shiga rarrashinta ya rinka gaya ma ta
maganganu masu tausasa zuciya har dai ya shawo
kanta ta daina kuka.
AA Misau ke magana
A CAN bangaren ragowar Sarakai kuwa, bayan
an watse đaga taron da aka yi a fada sai suka shiga
sabon taron sirri a cikin tsakiyar dare inda suka
taltauna akan batun bakon boka Kirishna wanda ya zo
daga kasar Hindu.
Kaso takwas daga cikin kaso goma na Sarakunan
sai suka nuna Cewa su sam basu gamsu ba da wannan
shawara da boka Kirishna ya kawo saboda sun gaji da
karyace-karyacen bokaye akan wannan al'amari.
Sai da aka shfe sa'a uku da rabi ana ta kacé-nace
sannan ka yanke shawarar cewa kowanne Sarki Zai
bayar da dakaru dubu arba'in a sirance bisa jagorancin
babban bokan kasarsu su tafi izuwa dajin Kirzufa
domin yiwa dajin taron dangi a rana guda a shafe duk
wani abu mai rai da yake cikinsa.
Nan take aka tsaida ranar da za a tara wadannan
dakaru kuma aka tabbatar da cewa dakarun za su hadu
ne a birnin Ihisar za su hadu. A takaice dai Sarki Jamal
ne jagoran wannan taro.
Wannan shi ne abinda ya faru a bimin Lairuf
bayan Sarakunan nahiyar gaba daya sun zaUna sun
tattauna bisa yadda za su sami mafita akan masifar
annoba ta jarumi mai kahon BUSA A MUTU.
A CAN dajin Kirzufa kuwa Muraisù da
mahaifiyarsa Husnaila sun ci gaba da rayuwarsu cikin
koshin, lafiya da kwanciyar hankali, amma tun daga
ranar da suka yi yaki da su Sarki Zaidur sai suka daura
darmarar baiwa juna horon yaki kuma suka rinka baiwa
jikinsu horo mai tsanani na yin gudu mai yawan gaske
babu hutawa har na tsawon kamar sa'a goma sha biyu
sannan idan suka fara yakar juna'suna kai sara da suka
nan mà sai su shafe sa'a bakwai suna yi.
A haka ne kullun jikinsu ya rinka'sabawa- da
jurewa wahalá da gajiya ya zamana cewa kullum
jarumtakarsu karuwa take. Su kansu sai suka rińka
mamakin al'amarin.
Abinda basu sani ba shỉ ne, simin yana daga cikin
dajin da suke zaune.
Sai da Muraisu da Husnaila suka kwana goma
sha bakwai a cikin wannan hali na baiwa kansu,
wannan horo su kansu sai da suka ji sauyi matuka a
jikinsu bisa wani irin gagarutnin karfi da suka ji ya
shiga cikin jikinsu tamkar za su iya yakar duniya gaba
dayanta su biyu.
A ranar kwana na góma sha bakwan ne da hantsi
bayan sun gama baiwa kanşu horon yakin kuma sun
záuna suna hutawa sai suka ji sukuwar dawakai ba
adadi sun durfafo cikin dajin.
Duk da cewa su Muraisu suna jin gagarumin
karfi a jikinsu sai da karar sawayen dawakan ta
firgitasu saboda ganin yadda kasar dajin gaba daya ta
kama girgiza.
Ba komai ne ya haddasa hakan ba face tsananin
yawan dakarun da suke bisa dawakai.
Küma tun daga nesa ana jiyo irin karlin gudun
da suke yi da karar kofaton dawakan.
Muraisu da Husnaila suka mike tsaye zumbur
suka ruga da gudu izuwa cikin kogon da suke rayuwa
suka debo makamansu na yaki. IHuraisu ya daga kansa
sama ya kurma wani uban ihu.
Faruwar hakan ke da wuya sai gaba dayan
dabbobin dajin suka rinka firfitowa daga cikin
ramukansu wadanda ke kan bishiyoyi suka sauko.
Wadanda ke cikin gabar kogi ma suka fito gaba
dayansu suka rugo da gudu suka iso inda Muraisu da
Husnaila ke tsaye a tsakiyar dajin rike da makamansu
na yaki sun yi wata irin tsayuwa ta manyan jarumai
wacce ke nuna tsantsar rashin tsoro da yarda da kai.
A dai-dai wannan lokacin su Muraisu suka hango
DANDAZON MAYAKAN da suka durfafosu masu
tsananin yawan gaske tamkar yakin duniya za a yi.
Amma wani abin mamaki da ya faru shi ne, ko
gezau Muraisu da Husnaila da dabbobin dajin ba su yi
ba, kawai sai suka tsaya cak a inda suke aka fara
kallon-kallo tun daga can nesa.
Lokacin da ya rage saura baifi taku hamsin ba
tsakanin rundunar mayakan da kuma ayarin
Muraisu, sai Muraisu da Husnaila suka daga
makamansu sama a lokaci guda kuma suka falfala da
azababben gudu suka durfafi abokan gaba.
AA Misau ke magana
Nan kuwa surna sauran dabbobi dajin sai suka
rufawa su Muraisu baya.
Koda rundunar mayakan suka hango su Muraisu
sun taso da gudu suma sai suka sakarwa dawakansu
Kaimi suka rinka kwalla ihu suna zumudin a hadu
domin su yi ta-more saboda ganin cewa yawansu da
karfin shirinsu na muggan makaman yakin da suke
rike da su gami da yarda da bokayensu bisa sa'ar da
suka basu suna ganin cewa lallai babu abinda zai
hanasu samun nasara a yau.
Ai kuwa ana haduwa a tsakiya sai aka kacame da
azabbaben yaki wanda baki bai isa ya iya fasaltashi ba.
Ihu, kururuwa da gurnanin mutane da dabbobi ya cika
dodon kunne. Kura ta tashi ta turnuke sama da kasa.
Nan fa kasuwar cinikin rai ta fara kankama sai
gashi jini ya fara tsartuwa, feshi da malala a sama da
kasa tamkar ruwan samansa ake yi, wani kuma tamkar
daga cikin kasar yake tsattsafowa kai kace idaniyar
ruwa ce ta balle.
Sassan jikin bil'adama kuwa ya rinka shawagi a
sararin samaniya tamkar iska ce ke yawo da takardu.
Wani lokacin idan dabba ta wangame bakinta ta
daka tsalle sai dai ka ga ta hadiye kan mutum ta
gutsure kan tamkar an sa takobo an sareshi.
Wani babban abin mamaki shi ne, su kansu
dabbobin na dajin Kirzufa wannan karon sun koyi
dabarun yaki matuka sun san yadda suke kaucewa sara
de suka. Kai hatta harbin kibiyoyi ma kaủce musu suke
tamkar an basu horo na musamman kan hakan
Wohoho! Wuya ba a sama ta ranaa, ita
masita idan ta taho babu abinda yake iya dakatar da ita
face Allah.
Tun da aka fara warnan azababben yaki kó
alamar nasara babu a 6arigaren wannan runduna ta
dakerun teron dangi, domin ko dabba daya jal basu
sami damar kashewa ba, amma sun yiwa wadansu
dabbobin raunika da yawa.
Sai ka ga gashi an sari dabba ko an soketa jini na
zuba amma naci tana mai ci gaba da yaki babu alamar
Jigata a tare da ita.
Jarumi Muraisu da Husnaila kuwa duk inda suka
sa gabansu sai dai ka ga maza na zubeva kasa ratata
tamkar ana sassabe a gona, kuma ko yaushe dada kara
samun kuzari suke da karfi maimakon su gaji.
Nan dai su Muraisu suka zamewa dakaron
alakakai kuma annoba.
Koda aka shafe sa'a biyar ana wannan gumurzu
sai dakarun TARON DANGI suka ja da baya gaba
dayansu sakamakon ganin irin mummunar 6arnar da
aka yi musu saboda du sa'adda suka dubi kas
gawarwakin 'yan uwan da na dawakansu suke gani.
Ai kuwa suna ja da baya sai Muraisu da Husnaila
ma suka ja da bayan, dabbobin din ma sai suka yi
koyi da su. A sannan ne aka tsaya ana kallon-kallo.
A wannan lokaci ne dakarun taron dangin suka firgita
ainun domin sun fahimci cewa an kashe kaso daya
cikin kaso ukunsu. Nan take fiye da rabinsu suka
yunkura za su kada dawakansu su juya da baya don su
gudu sai. wani barde mai kirar sadaukai wanda ya
kasance shi ne mataimakin Sarkin Yakin Sarki Jamal
wanda ake kira da suna BULMAZU ya daka musu
tsawa ya ce, "Duk wanda ya yi kokarin gudu ni da
kaina zan kure masa gudu na kashe shi.
Shin kun manta ne cewa duk wanda ya shigo
dajin nan ba isa ya fita a raye ba face ya kashe duk
wata halitta mai rai da ke cikinsa? To ku sani cewa
bamu da wani zabi wanda ya fi mu yaki wadannan
takadiran mutane biyu kuma mu kashe wadannan
dabbobi nasu gaba daya".
Koda gama fadin hakan sai Bulmazu ya daga
takobinsa sama yana mai kwarara uban ihu wanda ke
firgita maza a filin daga sannan ya sake sakarwa
dokinsa kaimi ya yi kan su Muraisu. A lokacin ne
sauran dakarun taron dangi suka taso aka sake kaurewa
da sabon gumurzu.
Har ya zamana cewa tsakanin Muraisu da
Bulmazu bai wuce taku biyar ba Muraisu ko motsawa
bai yi ba daga inda yake isaye kuma ko kadan babu
alamar tsoro a fuskarsa, kawai jira yake Bulmazu ya
karaso.

Nima anan zan dakata sai wani lokaci kuma
AA Misau ke magana
WhatsApp group

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30QBUSA A MUTU
Littafi Na Biyar (5)
Part C

Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau ke Magana

Barkanmu da wannan lokaci dafatan kuna lafiya ya ku jama ar wannan gida Mai AlbarkA

Ba zato ba tsanmani sai kawai aka ga Muraisu
ya daka tsalle sama.
Kafin Bulrmazu ya sake
kawowa Muraisu wani harin tuni
gadon bayan dokin Bulmazu.
A saman Bulmazu ya kawowa
mummunan saraa wuya da nufin ya fille masa kai.
Cikin bakin zaffn narna Muraisu ya sunkuyar da
kansa kas amma duk da hakan sai da kaifin balkin
takobin ya zabtare wani bangare daga cikin gashin kan
Muraisu.
Nan take muraisu ya gigarawa Bulmazu takobi a
makogwaronsa.
Gudan jini ne ya bullutso daga cikin wuyan,
jijiyoyi kuma suka kama feshin wani jinin.
Da karfin tsiya Muraisu ya karasa yanke kan
Bulmazu ya daga kan sama yana mai ihu da kururuwa.
Al'amarin da ya karya lagon dakarun taron
dangin ke nan suka karaya ainun.
Duk da sun san cewa ba a fita daga dajin Kirzufa
sai suka kara juyawa da baya a guje don su tsira da
rayuwarsu amma sai Muraisu da Husnaila da kuma
sauran dabbobin dajin suka rinka kure musu gudu suna
rafkesu.
Saí da aka shafe sa'a biyar ana rafke wadannan
dakaru sannan suka kare saboda yawansu.
A wannan lokaci ne Mủraisu, lusnaila da
Dabbobin suka gaiji likis suka kwanta a kas suna huci
Kamar ransu zai fita".

Koda Muraisu ya dagokansa ya dubi
gawarwakin dakarun taron dangi ya ga dukkaninsu fa
mutane ne irinsa sai nan take nadama ta zo masa kuma
Ya kamu da tsananin tausayinsu.
Kawai sai idanunsa suka ciko da kwallah.
hawaye ya fara sartu bisa kumatunsa.
Yana juyawa bayan sa ne ya yi arba da
mahaifiyar sa . Koda ta ga hawaye na zuba a idanunsa
sai ta cika da tsananin mamaki.
Cikin sanyin jiki ta taso daga inda take kwance ta
iso daf da shi suka fuskanci juna sannan ta ce, Ya
kai dana namijin duniya, kuma Sarkin gobe a birnin
Lairuf, mene ne ya saka kake zubar da hawaye haka
alhalin gashi mun sami gagarumar nasara akan
makiyanmu?"
Sa'adda Muraisu yaji wannan tambaya sai yasa
hannu ya share hawayensa sannan ya dubeta ya ce,
"Ya ke Ummina ki yi sani cewa ba komai ne ya sani
zubar da wannan hawaye ba face tsananin tausayin
wacannan mutane da muka kashe.
Ki tuna fa cewa suma suna da iyali.
Wani yana da iyaye, wani yana da mata da 'ya'ya
wani kuma 'yan uwa kadai gareshi. Ya ya iyalinsu za su kasance? Wane irin bakin ciki za su shiga idan suka
san sun mutu?"
Sa'adda Husnaila taji wannarn batu na Muraisu sai
ta murtuke fuska ta dubeshi a fusace ta ce, "Akan
wanne. dalili za ka ji tausayin wadanda basa jin
tausayinka kuma basa kaunarka?
Shin ka manta ne cewa wadannan mutane sune
suka kashe mahaifinka suka sa muka baro cikin garri
muka dawo rayuwar daji muka rasa daular da muke
ciki. "
Gama fadin hakan ke da wuya sai suka hango
wata damisa da ke tsaye tana numfarfashi, ta sulale
kasa ta baje tana kakarin mutuwa.
A dimauce Muraisu da Husnaila suka mike tsaye
zumbur suka ruga izuwa kan Damisar suka hau.
duddubata.
Nan take suka ga ashe gefen cikin damisar a bule
yake har hanjin cikinta ya fito.
Koda ganin haka sai Husnaila ta fashe da kuka
kuma ta sake dimaucewa ta mike zumbur za ta je ta
dauko maganin da za ta sawa damisar sai Muraisu yai
caraf ya ruko hannunta ya dubeta cikin alamun karayar
zuciya ya ce, "Ki yi hakuri ya ke Ummina ki yi sani
cewa lokaci ya kure wannan damisa mutuwa za ta yi."
Ai kuwa kafin Muraisu ya gama rufe bakinsa sai
Damisar tayi ajiyar numfashi na karshe ta sandare ya
zamana cewa komai na jikinta ya daina motsi.
AA Misau ke magana
Koda ganin haka sai Husnaila ta fada kan gawar
Damisar ta fashe da matsanaicin kuka tamkar wadda ta
rasa dan cikinta ko wani shakikinta.
Da kyar Muraisu ya ya bambarcta daga kan
gawar Damisar.
Nan take sauran Damisoshi suka taru a gaban 'yar
uwar tasu, wasu daga cikin suka kama tonon kasa har
sai da suka yi rami mai dan zurfi da fadi sannan suka
Janyo gawar yar uwar tasu izuwa cikin ramin suka
binneta.
Sai da aka shafe sa'a daya ana jimamin mutuwar
damisar sannan Husnaila da Muraisu suka mike tsaye
suka tafi izuwa cikin kogonsu suka zauna.
A sannan ne Husnaila ta lura da cewa akwai
kananan raunika a jikin Muraisu.
Cikin hanzari taje ta d'auko wani garin magani
wanda aka yi shi da busasshiyar saiwar wata bishiya ta
fara lika masa maganin a jikin raunikan.
Koda tazo kan wani rauni da ke gadon bayansa
sai tayi arba da wani zanen wuka mai nuna tambarin gidan sarautar binin Lairuf.
Al'amarin da ya jefata cikin tsananin mamaki ke
nan domin tunda ta haifi Muraisu ba ta taba ganin
wani hatimi a jikinsa ba sai yau, don haka sai ta daina
shafa masa maganin ta kurawa tambarin idanu kawai.
A sannan ne Muraisu ya yi gyaran murya ya ce,
"Ya ke Ummina me ya faru kika tsaya ga barin sa mini
maganin ?"
Koda jin wannan tambaya sai Husnaila ta yi
ajiyar zuciya ta ce, "Ya kai dana ka yi sani cewa wani
hatimi na gani a gadon bayanka wanda ban taba
ganinsa ba sai yau kuma shaidace mái nuna cewar kai
jinin sarautar birnin Lairuf ne".
Koda jin wannan batu sai nan take Muraisu ya
tuno da mafarkin da ya yi a daren jiya.
A zabure Muraisu ya juyo ya fuskanci Husnaila
ya ce, "Ya ke Ummina ki yi sani cewa jiya na yı
mafarki na yi gamo da wani gawrtaccen sadaukin
saurayi wanda ya fini karfi da jarumtaka ainun domin
duka daya ya yi min na yi sama kamar an cillani daga
cikin baka, tun a saman jini yai feshi daga cikin bakina
kuma na fado kasa a matukar galabaice. Kafin na
tsaye sai na ga wani Sarki mai kwarjini da cikar haiba
tsaye a gabana ya caba ado yana ta faman kyalkyala
mini dariya.
A hannun Sarkin akwai wata sandar mulki mai
siffar doki."
Koda jin wannan batu sai hankalin Husnaila ya
dugunzuma ainun domin itama irin wannan mafarki
tayi sak a jiya da daddare babu bambanci.
Koda Muraisu ya ga alamun damuwa karara alkan
fuskar Husnaila sai shima hankalinsa ya dugunzuma
ya dubeta ya ce, "Ya ke Ummina wai shin Mene ne
yake faruwa ne haka? Na ga kema kin shiga cikin halin
damuwa bisa wuanan mafarki da na baki labari?"
Husnaila tayi ajiyar zuciya sannan ta ce, "Ya kai
dana ka yi san cewa nima a jiya cikin barcina na yi
mafarki iri daya sak da naka mafarkin.
Ko shakka bana yi akwai wani mügun tanadi da
Sarki Huraisu an uwan mahaifinka ya yi mana.
Hakika hankalina ya tashi ina tsoron kada wani
mugun abu ya samcka ko ya samneni a nan gaba"
Koda jin wannan batu sai Muraisu ya cika da
mamaki ya ce, "Ya ke Ummina ya za a yi wani mugun
abu ya samemu alhalin muna zaune a cikin dajin
KIRZUFA inda babu wani mahaluki da ya isa ya shigo
ya fita a aye?"
Husnaila ta ce, "Shin ka manta nc cewa ba anan
tamu dauwama ba? da zarar fa ka gama busa kahon
Nan zamu yi shiri mu tafi izuwa birnin Lairuf domin ka
carbi karagar mulki a hannun azzalurnai Huraisu.
Abinda na ke so ka sani shi ne, a wannan lokaci ne
Barki Huraisu zai yi amfani da damarsa wajcn cutar da
Koda jin haka sai hraisu yayi ajiyar numfashi
ra ce, "Amma ai jarumin da aka nuna mini a cikin
Barcina ina yaki da shi anan cikin dajin Kirzufa ne ba
wai a can birnin Lairuf ba
Husnaila ta ce, "Ai shi mafarki wani abu
wanda ba lallai bane ya zama gaskiya.
To amma dai tunda ni da kai duk mun yi mafarki
iri daya a lokaci guda to lallai koda abin da muka gani
bại faru ba to tabbas sai makamancinsa ya faru.
Tabbas yanzu bamu da wani abin yi face mu ci
gaba da jjircewa wajen kefe baiwe kanmu homn yaki
kullum babu sassautawa domin mu yi shirin tunkarar
duk abinda zai zo mana.
Muraisu ya gyada kai sannan ya ce, "Hakika kinzo da bayani mafi cancanta
agaremu."
Wannar shi ne abinda ya faru a dajin Kirzufa
bayan an fafata kazamin yaki tsakanin su jarumi
Muraisu da dakarun taron dangi
AA Misau ke magana
A CAN birnin Lairuf kuwa, sai da aka kwana
goma sha hudu ana ta shirye-shiryen gagarumar tafiyar
da za a yi ta, bazama a cikin duniya domin neman
jaruni IMRAN.
A ranar kwana na goma sha uku ne Sarki Huraisu
ya yiwa gimbiya Suzaila albishir cewa ya amince ta
zama daya daga cikin mutane hudu da zai bayar domin
yin wannan tafiya ta neman jarumi Imran sadaukin da
zai shiga cikin dajin Kirzufa ya kamo mai kahon busa a mutu
Koda jin wannan albishir sai gimbiya Suzaila ta
kamu da tsananin farin ciki. Nan take ta fara shirye-
shiryen tafiya saboda doki da murna har dare ya yi ba
ta rintsa ba.
Makamanta na yaki kuwa sai da ta tanaji kala
goma sha daya. Bayan Suzaila ta gama shiri tsaf ta
shirya dukkan kayanta a gefe daya cikin turakarta sai
taje kan gadonta ta kwanta ta rintse idanunta domin
tayi barci, dama ta kashe fitilar dakin.
Koda ta rufe idanun na ta sai ta rinka ganin hoton
jarumin Imran wanda ya kasance kakkyawan saurayi
na gaban kwatance mai cikar kyawun sura, kwarjini da
haiba.
Nan take sai taji ta kamu da tsanánin kaunarsa
don haka sai tayi sauri ta bdue idanunta lokacin da
zuciyarta ta fara bugawa da karfi.
Al'amarin da ya matukar ba ta mamaki ke nan
domin a iya rayuwarta ba ta taba ganin saurayin da taji
ta kamu da sonsa ba sai Imran.
To wai shin ma akan wane dalili za ta kamu da
son mutumin da ba ta taba yin arba da shi ba a fili? Ai
kuwa dole ne na yi yaki da zuciyata na tursasata ta cire
so .0wanne da namiji a cikinta."
Haka dai Suzaila ta ci gaba da sakar zuci ta kulla
wannan ta kwance wancan har barci ya saceta ba ta
sani ba.
Kashe gari kuwa da safe bayan Suzaila tayi
kalaci sai tayi wanka ta kimtsa tayi gagarumar shigar
kayan yaki sannan ta nufi fada inda za ta iske ragowar
abokan ta fiya.
Tun daga nesa Suzaila ta hango fadar a cike
makil da dakarun tafiya. A can sama bisa kan gini mai
matattakala inda karagar mulki take, gaba dayan
se rakunan nahiyar ne a zazzaune har da mahaifinta
Sarki Huraisu. Sarki Imras ne kadai babu shi a wajen.
Suzaila ta ci gaba da tafiya har ta ratso ta cikin
mutancn da aka zaba don yin wannan tafiya tana
wucewa ta tsakiyarsu tana kallonsu da nazarinsu daya
Koda ta riski layin karshe ta iso kan gaba tayi
arba da wadensu mutane guda biyu tsaye cikin sahu
sai ta cika da tsananin mamaki.
Ba wadansu bane wad'annan mutane face yarima
Hasnalu da 'yar uwarsa gimbiya Lushaira dukkaninsu
sun yi shigar yaki.
Al'amarin da ya yi matukar baiwa gimbiya
Suzaila mamaki ke nan domin ba ta ga amfanin yin
wannan tafiyar ba tare da su tun da basu kasance
jarumai ba.
Kawai sai Suzaila taje ta tsaya kusa da Lushaira
ta dubeta suka yiwa juna dan guntun murmushi. Koda
yarima Hasnalu ma ya dubi Suzaila ya yi ma ta
murmushi sai ta maurtuke fuska ta daka masa harara.
Ba shiri ya kau da kansa ga barin kallata.
Faruwar hakan ke da wuya sai ga Sarki imras ya
shigc cikin fadar shima fuskarsa a murtuke ko kadan
babu annuri a cikínta.
Koda Sarki Huraisu ya hango Sarki Imras a cikin
wannan hali sai bankalinsa ya dugunzuma ya mike
tsaye daga kan karagarsa ya sauko kasan natattakalar
ya tareshi yana mai rike kafadunsa kuma ya
tambayeshi ya ce, "Ya kai abokina waye ya Gata maka
rai kå shigo cikin fadar nan tawa haka babu annuri
akan fuskarka?"
Koda jin wannan tambaya sai Sarki Imras ya
yiwa Sarki Huraisu rada a kun.
Nan take Sarki iuraisu ya kamu da tsananin fishi
ya juya a fusace ya yiwa gaba dayan Sarakunan da ke
fadar wani irin kallo wanda ya sa duk suka sha jinin
jikinsu kuma suka sunkui da kawuaansu kas cikin
alamun kunya da rashin gaskiya.
Nan dai Sarki Huraisu ya kama hannuh Sarki
Imras ya jashi izuwa can sama Suka Zauna tare akan
karagarsa tare sannan sai fuskar Sarki Huraisu ta juye
izuwa annuri ya mike tsaye ya dubi kowa da kowa ya
ce, "Ya ku 'yan uwa da abokan arziki, ku yi sani cewa
yau ne ranar da wakilanmu za su tafi neman jarumin
iya sadauki Imran wanda shi ne zai iya yi mana
AA Misau ke magana
maganin wannan.
annoba ta mutuwar ya'yayen Sarakunanmu
Duk wadannan mutane da kuke gani a tsaye a
tsakiyar fadar nan su ne wadnda aka zabo don yin
wannan iafiya.
Ni a 6angarena akwai 'yata gimbiya Suzaila
wacce kuka fi sani da Sarkin yakin birnin Lairuf sai
kuma Sarkin yakina na da, sại kuma tagwayen
sadaukai jarumi Shalaru da jarumi Halaru.
A 6angaren Sarki Imras kuwa akwai 'ya'yansa
guda biyu yarima Hasnalu da gimbiya Lushaira sai
kuma Sarkin yakinsa da mataimakinsa.
Kowanne Sarki anan shirna ya bayar da mnutane
hudu kamar yadda muma muka bayar.
Baya ga wadannan dalkaru mun sake ware.
wadansu dakaru guda dubu sittin kacal wadanda za
su yi musu rakiya.
Tunda akwai 'ya'yanmu a cikin wannan tatiya
dole nea ware kuyangi wadanda za su rinka yi musu
hi dima a cikin wannan tafiya, saboda haka kowanne
yarima ko gimbiya an ware masa kuyanga goma.
Muna sa ran cewa wadannan matafiya za su dawo
garemu cikin nasara a iokacın da ba zai wuce tsawon
shekara daya ba.
Da wannan furuci nake yiwa matafiyan
bankwana da fatan za su yi tafiyar lafiya su dawo
lafiya.
Idan akwai wani mai koráfi akan abinda na
fadi yanzu sai ya yi tun gabannin wadannan
matafiya su tafi."
Koda gama fadin hakan sai fadar gaba daya
tayi tsit! Aka rasa wanda zai ce kala.
Har Sarki Huraisu ya yunkura zai daga hannu
domin ya baiwa matafiyan umarni su tafi sai Sarki
Jamal yai gyaran murya kuma ya mike tsaye ya ce,
"Yana da magana".
Sarki Huraisu ya dubi Sarki Jamàl ya ce, "An yi
maka izini ka fadi korafinka".
Sarki Jamal ya sake yin gyaran murya a karo na
biyu sannan ya ce, "Ya kai wannan Sarki mai daraja
ni ina ganin cewa bai kamata mu dauki har tsawon
shekara guda ba muna jiran dawowar wadannan
dakaru saboda kafin cikar shekara gudan ba a san iya
adadin 'ya'yan Sarakan da za a rasa ba.
Kamata ya yi a baiwa matafiyan tsawon wata
uku kacal, idan har basu hadu da jarumi Imran ba
kawai su dawo gida."
Kafin Sarki Jamal ya gama rufe bakinsa tuni
Sarki Huraisu ya daka masa tsawa yana mai cewa,
"Wannan wacce irin maganar banza kake yi ne
haka?
To idan suka dawo bayan wata ukun basu sádu
da sadauki. Imran ba mene ne amfanin fitar tasu
kuma waye zai yi mana maganin wannan masifa?
Su.
Shi ke nan sai dai mu zuba ido muna gani a
ya'yayen namu su ci gaba da mutuwa har a karar da
Ka tsaya ka yi tunani ka gani yanzu fa ni da
Sarki Imras 'ya'yan namu muka bayar ayi wannan
tafiya mai hadari tare da su don kawai a kawo
karshen wannan masifa.
Shin ka san irin hadarin da ke cikin wannan
tafiya kuwa?"
Sarki Jamal ya kada kai cikin alamun sanyin
jiki da borin kunya.
Sarki Huraisu ya matso har izuwa gaban Sarki
Jamal ya tsaya daf da shi yadda suna iya jin
numfashin juna ya ce, "Kada ka yi zaton cewa duk
abinda kuke kullawa a sirrance bamu sani ba kai da
sauran sarakuna kun tashi dakaru masu yawan gaske
bisa jagorancin bokayenku kun turasu izuwa dajin
Kirzufa domin su kashe yaro mai Rahon BUSA A
MUTU.
To ka sani cewa gaba dayan dakarun naku da
bokayensu duk sun hallaka dayansu bai tsira da
rayuwarsa ba."
Koda jin wannan batu sai idanun Sarki Janal
suka zazzaro, hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye
da ko yaushe ya rasa abin da ke masa dadi. Saukinta
ma kamnar a cikin rada Sarki Huraisu ya yi masa
wannan jawabi babu wanda ya ji.
Nan take Sarki Jamal ya koma ya zauna,
sannan Sarki Huraisu ya yiwa matafiyan bankwana.
Bayan ya gama yi

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment