Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cigaba da samun kulawa da mijinta da kuma mahaifiyarta, cikin ikon Allah cikinta ya shiga watan haihuwarsa, sai kuma lalura tayi yawa , yau da lafiya gobe babu, ta kai ta kawo har sai asibiti suka bata gado domin kula da ita da abinda ke cikinta, Allahu akbar ashe abokin tafiya ne, daran juma'a nakuda ta tashi, kafin asubah, ta haihu 'ya mace sai da babu rai! mahaifa kuma tayi gardama likitoci suka rufu akanta domin ceto rayuwarta, duk abinda Allah ya kaddara babu makawa, suna tsaka da taimaka mata mahaifar tayi sama, a take ta dinga wani irin nishi! idonta na rufewa da wata irin jijjiga, da kalmar shahada Allah ya dauki rayuwarta.

Sun shiga rudu mai tsanani mussaman mijinta da mahaifiyarta, bangaran Jamilu kuwa ko a jikinsa domin yanayin sa ma ya nuna kamar yana farin ciki da mutuwarta, domin koda yazo gaisuwa babu alhini a tattare dashi, kwalliya yayi sosai yana uban kamshin turare kamar sabon ango! komai na jikinsa mai tsada ne.


Wannan shine abunda ya faru a baya, Shahida ta cigaba da zama gurin Baba Asabe tana kula da ita ci da sha suttura harkar karatu da kula da lafiyarta duk Baba Asabe ta dauka. sana'a take sosai domin macace mai kamar maza.

Hujaj mantawa ma yake yana da wata 'ya a wani guri mutukar ya tuna da ita to yaje gidansu ne, mahaifiyarsa tayi masa maganarta, anan zai girba 'karya yace ai yana zuwa ya duba yarinyar har kudin abinci yana kaiwa, alhalin tun bayan haihuwarta bai sake zuwa gidan ba. gabadaya ya manta da ita, domin ko lokacin da Kawu Musa yaje kasuwa ya sameshi domin ya sheda masa lalurar yarinyar, sai da ya gama sauraransa tsaf sannan yasa hannu a aljihu ya dauko dubu daya ya bashi da fadin." Suyi hakuri insha Allahu zai zo ya dubata.''

Takaici yasa Kawu Musa ya fita daga shagon ba tare da ya karbi kudin ba.

Tun daga ranar Baba Asabe tayi al'kwarin cewa ta daina neman komai a hannunsa, za ta cigaba da kula da yarinyar da ikon Allah babu abinda zai gagare ta.
[4/19, 10:25 AM] Bintu: AIRPORT
babban filin tashi da saukan jirage na Malam Aminu dake Kano.
A hankali nake bin su da kallo sun jeru tsaf dasu cikin uniform gefen maza daban na mata daban, suna tsaye kowanne da 'yar jakarsa a hannu da alama screening ake musu kafin shiga cikin jirgin.
Na dinga ayyanawa a raina cewa wata shekarar insha Allahu dani cikin masu hauke farali. Ajiyar zuciya na sauke a hankali na gyara takardar da biron dake hannuna nayi saurin matsawa gefe jin horn na mota a dab dani.

Motar na zubawa ido tare da ayyana wani abu a raina.

Da sauri na kalli jiragen dake daukar fasinja. sunan mutumin dake bayan motar irinsa ne a jikin jiragen dake d'aukar fasinjan domin zuwa kasa mai tsarki.

'DANGASKE AIR LINE sunan dake tambare a jikin jiragen kenan.
'DANGASKE41 shine a rubuce a jikin hamshakiyar motar da tayi parking gefan da nake tsaye.

Ido na zura akan motar domin ganin wanda yake kokarin fitowa. kafarsa sanye cikin brown din takalmi mai gidan yatsa da kafar da takalmi duk abin kallo ne.

Ya fito bakinshi na dan motsi yanda na fahinta kamar addua yake. direban ya mayar da murfin motar ya rufe ya dan bashi hanya, kira kuma sai ya shigo wayarshi dake rike a hannunsa.

A sace nake kallonsa ina sake nazari a kansa. babu shakka shine hamshakin attajirin mutumin nan da sunansa ya mamaye ko'ina a fadin Najeria da ma kewayenta.

Yana sanye da milk din shadda 'yar gasken dinki tazarce rigar har kasa da aikin rumi a wuyan rigar kanshi sanye da brown din hula (dara) ya nad'e hular da farin hirami, hannunshi daure da wani irin agogon sarka white colour, a irin kallon kurrula irin nawa na fahimci cewa shi din ba yaro bane kamar dai yanda jama'ar gari suke maganarsa, babban mutum ne kamili mai shekarun da suka wuce arba'in, a kalla dai shekarunsa na haihuwa zasu kai hamsin da biyu zuwa da uku. da akwai tsalli-tsallin furfura a kwantaccen gashin da yake zagaye da bakinsa.

Yana wayar ina kallonshi tare da nazartarsa tabbas ya cika cikakken mutum mai kima da mutunci gami da daraja dan adam ko ga yanayin kalamansa a waya, a nutse babu baragada da hayaniya.

Escort dinshi uku suna tsaye a kusa dashi, sai kuma wata matashiyar budurwa dake d'an kama dashi kad'an a gefensa a tsaye sai zumbura baki take tana dauke kai tana sanye da jallabiya baka mai duwatsu tayi roling da pink din gale hannunta rike da wayoyinta da kuma handbang dinta.


Murmushi yayi ya dan gyara zaman gilashin dake sakaye da idonshi yace." Yanzu dai ni already ina airport tare da Shukura da Hajiya bana tsammanin kan wannan dalilin zan janye abinda nayi niyya saboda haka duk abinda ya dace ayi ina gari ko bana gari duk abinda kayi dai-dai ne Sule a cigaba da duk abinda aka saba kada a sauke min tukunya a gida
"

Shuru yayi na minti biyu kafin yace."Okey to hakan yayi Allah yasa albarka a ciki sai mun dawo." daga haka bai sake wata magana ba ya kashe wayar ya mayar da ita gaban aljihun rigar dake jikinsa.

Ya juya yana kallonsu a nutse yace."Ina Hajiya.?

Shukuran ce tayi magana. "Tana cikin mota wai kafafunta ke ciwo."

Girgiza kai yayi ya san za'a rina dama ko a gida ma kuka take da kafafun amma saboda rigima tace lallai sai taje aikin hajji tunda da iko to duk shekara ba za tayi fashin zuwa ba.

Hannu yasa ya bude motar gyangyadi take. sai abin ya bashi dariya yayi kadan kafin ya fara kiran sunanta.

Firgigit ta bude idonta tana kallonsa, da sauri tace." Wane irin baccin asara ne yake nema ya kwasheni a mota nida nake da niyyar zuwa gaban ma'aiki SAW."

'Kokarin fitowa take tana cigaba da surutai." Wannan kafa ita kadai ce damuwata a duniya amma Allah yayi min komai saboda haka babu abinda zan fasa na ibadah."

Duk wani bayani da k'auli da zai kawo mata ba zata yarda ba, shiyasa yaja bakinsa yayi shuru kawai yabi ra'ayin ta akan duk abinda takeso babban burinsa su rabu lafiya.

Yace." Ki zauna kada ki fama kafafun bari akawo keke a sanya ki a ciki.

"Wa za'asa a keke?" a tur'bune tayi maganar tana hararsa."

Shima ya gyara fuska babu wasa yace." Ke mana ko kin dauka idan mun isa can ma zaki iya d'awafi da kanki.?

Shuru tayi tana tunani. da kamar wuya wai gurguwa da auran nesa domin wani irin ciwo kafafun nata ke mata.

Ya d'an juya tare da kiran daya daga cikin Escort dinsa.

Ya risina cike da ladabi yana sauraransa.

"Adamu kaje ciki ka fito da keke za'a dora Hajia a kai."

Ya amsa da sauri cike da bin umarni ya bar gurin.

Ina nan tsaye a raka'be kamar wacce tayi wa sarki k'arya har wanda aka tura ya dauko keken ya dawo suka dora ta akan idona suka shige

Ban samu damar bin bayansu ba saboda akwai securities (masu tsaro) sai na dinga leken su ta tsakanin 'karafuna anan ne naga yanda ma'aikata da jama'a fasinjojin dake gurin ke bashi girma, fuskarsa ba 'boyayya bace idan akayi duba da yanda jaridu da gidajan television media ke nuna hotonanshi. Yanzu ma dai tunda ya shiga gurin masu daukar labarai sai d'aukar hotonshi suke da duk wani motsinsa. Cikin kamala da dattako yake dagawa jama'ar dake gurin hannu yana amsa gaisuwarsu fuskarsa a sake saboda daraja dan Adam har sai da ya cire farin gilashin dake sakaye da idonsa. wannan ya bawa gidan television din NTA dama daukar vedio sa lokacin ya juya da niyyar shiga wani kebantaccan jirgin da ya kasance na mussaman dashi da iyalinsa.

Kamar yanda mane ma labarai ke bin diddinginsa nima haka ban dauke idona ba har sai dana tabbatar da cewa sun shiga jirgin sannan na janye idona, gumin dake goshina na sharce kafin na sauke wata irin ajiyar zuciya, gaskiya na jinjinawa wannan mutumin da ace duk haka masu hali suke da sun ji dadi, ya zama koda yaushe a fadi alkairinka kafin a fadi sharrinka.

Wannan kenan

*****
Takwas na dare suka kawo wutar nepa cikin unguwar wanda jama'ar dake zaune a cikinta suka cire tsammanin samun wutar sakamakon faruwar matsalar data janyo shud'ewar wattani rabonsu da samun wutar lantarki.

Unguwar ta rikice da ihu! ba yara ba manya mata na cikin gida ma ihu! suke kananun yara sun fito waje sai ihu suke da fadin." NEPA!!.

Baba Asabe dake zaune a tsakiyar rumfa tana daura man gyada irin wanda take siyarwa, tafi kowa farin ciki da samuwar wutar dalilin sana'ar ta, bata samun lokacin daure-daure sai da daddare, fuskarta da fara'a tace." Allah ya taimake mu, jama'a mai za'ayi da duhu ko a kabari Allah yayi mana tsari dashi."
Saliha data fito daga uwar daki tace." Ameen dai ai Baba na fi kowa farin ciki kinga na huta wahalar kai waya ta gurin chaji." Tana maganar tana kokarin sanya wayar hannunta a chaji.

Tace." Aikuwa ai yaran nan sun cutar damu wallahi ace saboda tsabar mugunta da bushewar zuciya mutum abu ba shi ya aje ba kayan gwamnati amma sai abi dare a sace ko tsoro ba sayi watarana injin wutar ya tashi dasu, kai Allah dai ya shiryi yaran yanzu."

Ta amsa da "Ameen tana kokarin kunna Tv tace." Baba kin manta ai ba wannan ne na farko ba kusan sau uku 'barayi na bin dare su sace abubuwan dake da muhimmanci a transformer amma dai wannan karan naji ana cewa anyi kwamiti akwai kuma 'yan bijilanti da zasu sanya ido sosai."

Tana cigaba da abinda yake gabanta tace." Ai hakan shine abinda ya dace suyi dama can rashin hadin kai ne na cikin unguwa."

Shahida ce ta katse maganar da suke. rumfar ta shigo hannunta rike da plate da abinci a ciki.

Can gefe ta zauna babu walwala a fuskarta, kallo guda kayi mata zaka fahimci cewar akwai abinda ke damunta.

Ta kalleta da fadin." Akwai miya amma me yasa zaki sanya manja a cikin abinci, kina so wani ya shigo yaga kina cin fara da manja ya fita ya zage ni ko? dama kwana biyu naga sai nukufurci kike wai shin me akayi miki ne."?

Hawaye suka fara gudana a saman fuskarta. kawai sai ta ajiye cokalin ta kifa kanta tsakanin gwiwarta tana rusa kuka."


Ta bude baki kawai tana kallonta gabanta in banda faduwa babu abinda yake, rikon maraya akwai matsala babba.

Saliha taja tsaki da fadin." Baba don Allah ki kyaleta ke kike rarrashinta shiyasa ai take duk iskancin da takeso idan bata bukatar zama a gidan ba sai ta hada kayanta ta tafi gidan ubanta ba."
Duk da tana da matsalar kunne hakan bai hana ta jin irin kausasan maganganun da Salihan keyi a kanta ba, ta rasa me yasa Saliha bata kaunarta, tun suna yara take nuna mata kiyayya, bayan mahaifinta shine yasha nono ya bawa mahaifiyarta, amma kiyayya karara take nuna mata.

Baban tace." Saliha wace irin magana ce wannan? ba na san tashin hankali da neman fitina, saboda kina ganin tana da matsalar kunne shine kike cin mutumcinta a fakaice, kin fi kowa sanin halinta, duk sanda kike kure hakurinta to zan kyaleki da it........Ta katse ta da fadin." Ki kyaleta Baba ta cigaba da maganganu a kaina jikinta ne zai yi tsami yanzu yanzu." cikin dashewar murya take magana.

Baban tace." Magana dai ta wuce ke Saliha babu ruwanki da ita ki kama girmanki."

Tsaki taja ta gyara wayar ta dake chaji ta tashi ta bar gurin tana kunkuni."

Duk suka bi ta da kallon mamaki, Saliha sam bata da tarbiya wai a hakan ma gwara Shahidan tunda ita duk rintsi tana jin maganar kakar tasu.

Gurin yayi shuru sai tv dake aiki.

Kallonta tayi tana juya abincin har yanzu ta gagara saka loma daya a bakinta, da d'an 'karfi tayi maganar." Shahida sanja min tasha ki kai NTA KANO na saurari labarai."

Ajiyar zuciya ta sauke ta rarrafa ta isa gurin Tv fa fara kokarin sanja tashar Tv ce irin ta da sai shuuuuuu! take mutane ma basa fita sosai, a haka suke kallon.

Dai-dai lokacin da ta kai tashar NTA din yayi daidai da lokacin da aka haskoshi a filin jirgi yana gaisawa da mutane tare da cikakken bayani a kansa amma kuma da turaci ne.

Murya ta karo ita da Baba Asaben suka kurawa Tv ido suna ganinshi haza-haza domin tv ba clear saboda rashin Area mai kyau.

Baba Asabe tace." Shahida wannan mutumin ne mai taimakon mutane ko.?

A sanyaye ta daga kai da fadin." Shine wai suna bayani a kanshi zai je aikin hajji da tare kakarsa da kuma 'yarsa tilo guda daya."

Karaf tace." To bashi da mata aure ne.?

Itama tace." To ina zan sani Baba nima na dan tsinci wasu abubuwan ne ba komai na fahimta a kanshi ba, amma dai gaskiya ba zai rasa matar aure ba tunda ga budurwar 'yarsa nan."


Tace." Eh gaskiya kam amma kuma surutai marasa kyau suna yawo a kanshi jama'a da bin diddigi da ganin kwaf da yawa mutane nayi masa zargin auri saki wai a kalla ya auri mata sama da goma ya saki saboda yana da kudi."


Ta kalleta da fadin." Baba ki iya bakinki wallahi, na lura mutane ke kawo miki gulma iri-iri kada aji wannan maganar daga bakinki babu ruwanki."

'Yar dariya tayi tace." Yo 'yar nan ai maganar duniya bata 'buya, ko na fada ko ban fada ba, idan halinsa ne, Allah zai tona masa asiri watarana."

Tace." Eh duk da haka dai babu ruwanki wannan al'amari domin na san ki da magana watakila wasu na iya zuwa siyan abinci ki basu labarin da baki da tabbas akai, daga haka kuma sai al'amari ya lalace! sunanki yayi ta yawo gari."

Uffan ba tace ba, saboda ta san duk maganganun Shahidan akan hanya suke, sai kawai ta cigaba da abinda ke gabanta.

abincin take cusawa a bakinta tana had'iye wa da 'kyar! ita kadai ta san abinda ke damun ranta, kwana uku bata sanya shi a idonta ba, taje bakin kasuwar ya kai sau biyar bata ganin gilmawarsa, sai dai tarin tarkacensa a karkashin tsohowar motar da yake kwana, ko yana ina oho! wasu zafafan hawaye suka zubo mata a kumatu, tayi saurin gogewa! tana satar kallon in da take zaune, hada ido sukayi sai tayi saurin sunkuyar da kanta tana juya sauran abincin da ya rage da cokalin hannunta.


Ta ture bokitin man gyadan da ta gama daurawa, a nutse take kallonta kafin ta d'an bud'e murya yanda za taji tace." Shahida idan baki fada min damuwarki ba waye zaki fad'awa? duk halin da kike ciki na fahimta kwana biyu kamar baki da lafiya, shin ko dai wani abu yana damunki ne."?

Tasa hannu ta goge hawaye dake ta gudana a saman fuskarta, murya na rawa tace." Baba zuciya tana tausayin wannan mutumin na bakin kasuwa wallahi haka kawai nake tausaya masa, kullum dashi nake kwana dashi nake tashi a raina yau kwana uku kenan babu labarinsa sai dai tarkacensa a karkashin motar da yake kwanciya.''


Baba Asabe ta tsira mata ido cike da tsantsar mamaki tace." Baban- baba kike nufi.?

Kai ta daga.

Mamaki ya cika ta tace." Ke kuma meye damuwarki da mahaukaci Shahida kada fa garin tausayinki ki jefa kanki a wata musifa watakila ma ba mutum bane, aljani ne domun babu wanda ya san daga wace duniya ya fito."


Gabanta na faduwa tace." Wallahi mutum ne kamar kowa kuma ba mahaukaci bane, tunda yana sallah kuma baya doke-doke watakila damuwa ce ta mayar dashi haka."


Baba tace." To ai shikkenan yanzu wane irin taimako za'ayi masa."

Wani dadi ya ratsa zuciyarta, cike da farin ciki tace." Ki sanya masa kwano na abinci tun daga safe har dare, tunda Allah ya baki yanda za kiyi wallahi zaki samu lada."

Tace." To shikkenan zanyi yanda kikeso amma kada na kara ganin kin shiga damuwa a kansa, kuma kiyi kaffa-kaffa dashi tunda na lura baki da hankali."

Tana 'yar dariya tace." Baba kenan, Baban-baba ba zai cutar dani ba nayi imani da hakan, tunda na jima ina bashi sadaka kuma bai ta'ba yunkurin kawo min duka ba, sai dai yace ya gode."

Shuru kawai tayi mata ba wai dan bata da abun cewa ba, tsabar takaici ne ya isheta, yanzu yarinyar ta zama hukuma sai da rarrashi! za tayi kokarin ganin tayi mata duk abinda ta ke so.




Duk da Baba Asabe ta amince da abinda ta ke so hakan bai sanya ta kwantar da hankalinta ba, kullum cikin damuwa take duk saboda rashin sanin takameman gurin da mahaukacin ya sauya da zama, don ita duk a tunaninta tsokanar da yara ke masa ya sanya ya bar gurin, a rana ta kan je bakin kasuwar sau uku ko fiye da haka tayi ta dube-dube ko Allah zai sanya ta gan shi, babu shi babu dalilinsa sai tarin tarkacensa dake k'ar'kashin matacciyar mota (a kori kura) da yake kwanciya a 'karkashinta.

Da azumin arfa a bakinta daf da za'a sha ruwa ta faki ido ta fita daga gidan kai tsaye bakin kasuwar ta nufa.

Baba Asabe ta fito daga kicin da muburgi a hannunta, Saliha ce kad'ai a zaune a tsakar gidan tana had'a musu lemo, tace." Ina Shahida ita kuma sai tazo ta soya mana awara kada asha ruwa mu rasa abunda za musa a bakin salati."

Tabe bakinta tayi ta ce." Yanzu ta fita."

Cike da mamaki ta ce." Ta fita kamar yaya ina taje?"

Ta ce." To ni kya tambaye ni, nima ban sani ba, na san dai sa'i da lokaci tana fakar idonki ta fita."

Baba Asabe bata kawo mummunan abu a ranta ba, tafi tunanin cewa Shahidan bakin kasuwa take zuwa gurin mahaukacin data d'auki son duniya ta d'ora masa.

A fili ta ce." Allah yasa ya tafi kenan ba zai dawo ba domin kuwa na fara zargin mutumin nan idan ba aljani bane to babu shakka maye ne."
Ta d'aga labulan d'aki ta shiga tana cigaba da maganar da alama al'amarin yana damunta.


Yau ma ba sa'a domin kuwa gurin zaman nashi ma dabbobi (awakai) ne a kwance a gurin duk sunyi masa kashi ga ruwan saman da akayi jiya ya jika masa wasu kayan nasa, babu shi a gurin sai dabbobin da suka maye gurbinsa.

Wasu zafafan hawaye suka ciko idonta, ko'ina mutumin nan ya shiga? "Watakila ya mutu a wani guri." Zuciyarta ce ke raya mata hakan.

Ta girgiza kai gabanta na wani irin fad'uwa!

"Insha Allahu bai mutu ba."
Ta furta hakan a fili.

Da sauri tasa hannu ta goge hawayen da ya zubo ta kira wani yaro da hannunta.

Yaro yazo ya tsaya gabanta da ledar kankana da lemo a hannunsa da alama aikensa akayi kuma da azumi a bakinsa yana sauri ya isa gida yace." Gani."

A sanyaye tace." Don Allah ko kasan inda Baban-baba ya koma da zama?"

Cike da rashin fahimta yace." Waye Baban-baba?"

Ta nuna masa tsohuwar motar da fadin." Mutumin dake zama a waccan motar."
Ya kalli gurin da take nuna masa ya juyo da tsoro a tare dashi ya ce." Ni ma ban sani ba.'' bai jira jin abinda za tace ba yayi saurin barin gurin yana waiwayenta.

Ba ta ha'kura ba ta sake tarar wani yaron tana tambayarsa, yaron irin marasa kunyar nan ne, kawai sai ya fashe da dariya yana gwada irin maganarta ta kurame! "habbbaba! ya nu na ta da yatsa yana kyalkyala dariya ta bishi da kallo tausayin kanta da kanta ya lullubeta, wai shin ita din abar tausayi ce ko kuma Baban-baba?

Hawaye masu zafin gaske suka ciko idonta, tayi namijin k'okarin hanasu zuba, da saurin gaske ta bar gurin tana addua a zuciyarta.

Koda ta koma gidan ma 'bacin rai ne! don fad'a ta riska, Baba Asabe ta inda take shiga ba ta nan take fita ba har da cewa idan ba tayi a hankali ba to za ta kai ta asibitin dawanau a duba kwakwalwarta, to itama a lokacin da Baban ke fadin hakan ba taji haushi ba domin ta fara zargin kanta anya kuwa bata samu matsalar kwakwalwa ba.

Washe gari aka tashi da sallah, jama'a nata walwala da farin ciki mussaman wanda Allah ya hore wa abin layya ciki har da Baba Asabe domin babban (rago) na dubu sittin ta saya tayi layya dashi, wadatar zucci ne da ita tare da 'ko'karin faranta ran jikokinta dake gabanta.


Uku ga sallah ta shirya tsaf fuskarta babu walwala ta fito daga d'aki da hijab dinta a hannuta.

Baban ta kalleta da fadin." Kin shirya kenan? ai da nace Saliha ta shirya kuje tar.....Salihan ta katse ta da fadin." Ni babu in da zani bacci zanyi na huta, sannan kuma da yamma Kamalu zai zo muje gidan yayarsa ziyara." Kamalu shine saurayinta wanda akayi musu baiko.

Baban ta ce." Ayyo! to shikkenan Shahida kinji abinda ta ce."

Babu damuwa a tare da ita ta ce." Babu komai.'' Hanyar fita ta nufa da fadin." Sai na dawo."

Ta ce." Ki gaishe su ba dan halinsu ba, maganar naman sallah kuwa ba zan ce ki tafi musu dashi ba dalili na fi kowa sanin waye Jamilu da burgar tsiya yanzu idan baki take ba yana nan ya kayar da manyan shanu yana neman suna a unguwa."

Bata tsaya taji 'karshen maganar ba tayi saurin fita daga gidan, a ranta tana jin haushin irin cin mutuncin da Baban ke wa mahaifinta.


Ilai kuwa tana shiga gidan taga zahiri domin kaca-kaca ta samesu suna ta aikin suyar nama tare da daka dambu a k'aton turmi Hadiza ce mai wannan aikin.

Can gefe kuma ganda ce tare da kan sah! da rago a babbake akan buhu an shanya k'udaje sai tashi suke a gurin da wari mara dadi.

Jamila ce kawai ta amsa sallamarta tana fara'a tace." Aunty Shahida ashe kece dama kwana biyu kina raina."

Ta saki fuskarta da fadin." Nima saboda ke nazo gidan."

Hadiza ta kalleta da fadin." 'Yar iska bebiya kawai." da yake a hankali tayi maganar ba ta ji ba ta dai ga bakinta na motsi a lokacin da take maganar amma Talatun da sauran 'ya'yanta duk sun ji."

Babu wani 'kulli a cikin ranta ta ce."Talatu ina kwana anyi sallah lafiya?

A dakile ta amsa ta cigaba da juya zallar tsokar naman dake cike da kaskon suya.

Jamila ta shimfid'a mata tabarba tana zama ya shigo gidan fuskarsa a tur'bune!
kamar koda yaushe yana sanye da tsadaddiyar shadda wacce taji uban aiki irin na manyan mutane, hula da takalmi da agogo duka babu na banza kamshinsa kuwa tuni ya cika gidan.

Gabad'aya su kayi masa sannu da zuwa ya amsa babu walwala ya bud'e d'akinsa ya shiga babbar rigar ya cire ya rataye ya zauna kasan kafet zugum! da ka gani yana da damuwa.

Sallamarta ce ta katse tunaninsa, ya amsa yana bin ta da kallo har ta samu guri ta zauna tana sake gaishe shi.


Ya amsa yana mata wani irin kallo kafin yayi kwafa da fadin." Sai yau ki kayi ra'ayin zuwa gurin da nake?"

Shuru tayi tana wasa da yatsun hannunta.

Ya cigaba da cewa." Maganar aure ce ba kya so na yi miki shiyasa ki ka d'auke k'afarki daga gidan nan ko?"

Ta kalleshi da fadin." Baba aure nufin Allah ne idan lokaci yayi zanyi aur......ya katse ta, ta hanyar daga mata hannu da fadin." Ni zaki fadawa lokaci? zaman me kike kin zama uwar mata shekara ashirin kanwarki Hadiza saura wata shida bikinta ga Jamila nan itama nayi magana da yaron da yake son auranta mun tattauna da mahaifinsa, ke da kike babbarsu kina zaune to wannan itace magana ta karshe da zanyi miki wata biyu kacal na baki ki fito da mijin aure tunda kin kammala secondary kinyi saukar al'kur'ani to kuma me ake nema?"

Tana shashshekar kuka ta ce." Wallahi Baba tunda nake babu wanda ya ta'ba cewa yana sona, duk wanda yake so na yi aure ba kamar ni ba, na dai fi tunanin saboda lalurata maza suke gudu na."

Ya girgiza kai da fad'in.'' Mace bata kwantai matsalar ki ba zai hana ki auruwa ba, ki na da duk abinda ake

1 Comments On BA MAHAUKACI BANE Book 1
avatar
arfat-aliyu

12 months ago

Reply

Masha allh

Please Login or Register in order to submit comment