Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, sai ma wani irin kallo da take masa hawaye na sauka a kumatunta tafi jin tausayinsa akan kanta."


Kallo guda ya yi masa ya sha jinin jikinsa idan ba mahaifinta ba to wani shak'i'ki ne a gurin ta saboda yanayin kammani da ya gani a fuskokinsu.



Da yake mutum ne mai kyauta sai yasa hannu cikin aljihu ya d'auko dari biyu ya bashi domin shi duk a tunaninsa abinda yake bukata kenan.''


Girgiza kansa ya yi kafin ya ce." Ina zaka kai min mata ta?"

Maganar ta dinga yi masa amsa kuwwa! a kunne "Ina zaka kai min matata? ya sake maimaita maganar, itama ta tsorata da jin furucinsa hawayen idonta ya bushe ta dinga kallonsa gabanta na dukan uku-uku!


"Kai ba na son hauka! kar'bi nan ka matsa ka bani guri." abinda ya fad'a masa kenan ya sake mi'ka masa gudar dari biyun.



'Kin 'karba ya yi maganar dai ita ya sake maimaitawa "Ina zaka kai min mata ta?"


Cikin fad'uwar gaba ya ce." Don Ubanki waye wannan maukacin! meye hadin ki dashi.?


Da yake da 'karfi ya yi maganar yasa da sauri ta ce." Ba mahaukaci bane sunansa Baban-Baba a 'karkashin waccan motar yake kwana Baba Asabe tana bashi abinci."


Ya ce." Okey shiyasa kuka k'ulla soyayya a tsakaninku.? ido ta tsura masa tana auna maganarsa. Ya buga mata muguwar tsawa! da fadin." Ba zaki bani amsa ba.? ta ce." Ba soyayya muke ba Allah ne kawai ya hada jininmu nake tausayin........Ya wanke fuskarta da wani azababen mari! yana huci! ya ce." Ni zaki mayar mutumin banza ko? wannan d'an iskan mutumin ban yarda dashi ba kina tausayinsa shi zai iya cutar dake saboda haka aure zanyi miki, kai kuma ka saurare ni da kyau."

Ya tsura masa idanunsa dake cike da tsantsar b'acin ran marin da yayi wa yarinya ya ji ciwon hakan har cikin ransa.

Cikin isa ya cigaba da cewa." Wannan yarinyar tafi 'karfinka ba zan baka auranta ba domin ba ka da komai! mahaukaci kawai." yana kai k'arshen maganar ya ja hannunta suka shiga motar da ta tsaya a gabansu.

Ya jima a tsaye a bakin titin yana nazari da tunani akan al'amarin, can kuma na ga ya tsallaka titin ya bi wata hanya ya mi'ke......


*****

"Ranka ya dad'e ina sauraranka. d'aya daga cikin yaransa ke wannan maganar yayin da yake tsugune a gabansa.

Ya ajiye jaridar dake hanunsa a nutse ya ce." Sule kai ne kasan gari sosai kasan wata unguwa Ja'in a cikin garin nan.?"


Yayi jim na minti biyu kafin ya ce." Eh ranka ya dade ina dai jin sunan unguwar amma ban ta'ba shigar ta ba amma wani lokaci muna bi ta hanyar tare da kai idan za muje babbban kamfanin ka na sumunti dake sharad'a."


Ya ce." To ai ta kwana gidan sau'ki tunda ka san hanyar wani aiki za kayi min akan wani mutumi ina so kayi min binkice sosai a kansa.


Ya ce." To ranka ya dad'e babu damuwa ya sunan mutumin?" shuru yayi na minti biyu, sunansa Jamilu idan bai manta ba domin can da dadewa ya taba bugun cikin yarinyar ta fada masa sunansa da kuma unguwar da yake zaune.

"Sunansa Jamilu amma akwai wani suna da jama'a ke kiransa ya kwanta min a rai amma hakan ba zai zama matsala tunda mutumin sananne ne a cikin unguwar binkice a kansa ba zai yi wahala ba."


Ya ce." To babu damuwa ranka ya dade insha Allah zanyi k'okari sanin wanene mutumin domin kawo maka cikakken labari a kansa."

Ya ce." To Allah ya taimaka ina tsumayinka daga nan zuwa gobe da safe.

Ya mike da fadin." Insha Allah ranka ya dade .'' da sauri ya nufi parking spece ya fito da mota domin cika umarnin maigidan nasa.


Na jima ina kallonsa ina hango nagarta da dattijantaka a tare dashi, cikakken mutum ne kamili a zahiri da bad'ini domin yanda yake tafiyar da rayuwarsa a nutse shine zai tabbatar maka da cewa ya san abinda yake.



Da wuri ya dawo gidan, ya umarci Jamila cewa ta shirya da sauri kada magariba tayi ta je ta kira masa Shahida maza su zo tare yana nemanta.

Tunda Talatu ta ji haka ta san da wata a kasa. sai ta bishi dakin ta same shi a kishingide yana zan can zucci.

Gefan sa ta zauna da fadin." Na ga ka aika a kira maka wannan yarinyar a jikina na ji ruwa baya tsami banza."


Ya kalle ta na second biyu kafin ya ja tsaki da fadin." A nan ki ka fi kauri gulma da tsugudidi dube ki don Allah kamar ba mace ba, wannan tufafin na jikinki idan ban mance ba yau kwanansa hudu a jikinki."

Hannu ta daga masa da fadin." Ya isa kada ka ci min mutunci, shin da kake wannan maganar ka siya min sabulun wanka ko omon wanki ne."?

Shuru yayi mata banda hararar ta babu abinda yake.

Tace." Da fatan dai yarinyar nan ba gidan nan za ta dawo da zama ba domin wallahi ba zan iya rike ta ba nima naji da nawa."
Tsakaninta da Allah take maganar.

Ya gyara zamansa da fadin." Aure zanyi mata itama ta huta da wannan cin mutuncin naki."


Tabe baki tayi kafin ta ce." Au ashe ta samu mijin aure amma babu labari."


Ya ce." Wannan mutumin ne da yake bina bashi zan bashi kyauta a madadin kudinsa, kin san yarinyar nakasashiya ce za'a sha wahala kafin a samu mai auranta shiyasa na yanke shawarar aura mata Saminu tunda dai shi din ma kansa d'aya da rabi ne.

Farin ciki ya cika zuciyar Talatu, babban burinta a duniya a ce Shahida ta wulakanta, a maimakon ta nuna masa kuskuran abinda yake shirin aikatawa sai ta cigaba da karfafa masa gwiwa cewa hakan da yayi daidai ne, domin shi yake da iko da 'yarsa.


Cikin wannan halin Shahida da Jamila su kayi sallama a gidan.

Talatu ta fito daga daki tana washe baki, abin mamaki cikin sakin fuska ta amsa gaisuwarta, ita kanta Shahidan abin ya bata mamaki mutuka.


Durkushe take a gabansa gabanta in banda faduwa babu abinda yake, tun kafin yayi mata magana ta karanci komai a fuskarsa, labarin gizo baya wuce na koki saura kwana uku wa'adin da ya bata ya cika, wasu zafafan hawaye suka shiga tsere a saman fuskarta.


Fuska a murtuke ya daka mata tsawa! da fadin.'' Ba kuka na ce kiyi min ba Shahida ki saurare ni da kyau! kina jina ko."? ya k'arashe maganar da karfin gaske wanda har sai da su Talatu su ka ji sautin muryarsa.


"Ina fatan baki mance magana ta dake ta karshe ba."?


Murya na rawa da yanayin maganarta ta ce." Ban man ce ba Baba."

Ya ce." Wa ki ka tsayar a matsayin wanda za ki aura."?

Kai tsaye ta ce." Babu kowa."

Ya jima yana kallonta kafin ya ce." To ba zaki mayar da ni mutumin banza ba, kina yawo godai-godai a gari ni ba shashashan uba bane, tunda kin kasa tsayar da mijin aure ni a matsayi na na wanda ya haife ki zan aurar dake ga wanda ya cancanta, saboda haka ki zauna cikin shiri ki kuma shedawa kakarki cewa nayi miki miji zan had'a ku tare da Hadiza na aurar daku a lokaci guda."


Wani irin kuka ne ya k'wace mata murya a sarke ta ke fadin." Baba ka da kayi min haka mana kayi min adalci ka sake bani dama a karo na biyu insha Allahu zan fito da wanda na keso."


Kafin ma yayi magana Talatu ta bankad'o dakin ta shigo domin duk abinda ke faruwa suna ji ita da yaranta, ta ce." Wa ne irin adalci ki ke so ayi miki ? ai ki godewa Allah tunda har ki ka samu wannan bawan Allah ya amince da cewar zai aure ki a matsayin ki na muskiniya, ki daina daukar kanki cikakkiyar mutum kamar kowa."


Maganganun Talatu sunyi mata zafi sosai! a shari'ance ma sunyi tsauri da yawa, jahili ne kadai ya ke bambamce jinsin mutum wanda Allah ya hallita mai lafiya ko mara lafiya, duk wata hallita da Allah yayi akwai manufa kuma ba don baya sonka ya hallicce ka hakan ba, shi ya fi so ya gan ka a hakan ne.


Da k'yar ta iya yunkurawa ta tashi. hanyar fita kawai ta nufa hannunta kunshe a bakinta kukan da take dannewa ya'ki dannuwa sai fita yake hawaye kuwa a saman fuskarta sai tsare suke.


A bakin titi adaidaita sahu ya sauke ta, yanayin tashin hankalin da take ciki ya sanya ba ta lura dashi ba, yana daga can tsallaken da jarkar ruwa a hannunsa zai je ya samu ruwan alwalwa a tuka-tuka! shi ya gan ta a firgice! hankalinsa kuma ya tashi ainun! ganin yanda take kuka! ya bi ta da kallo lokacin da take karya kwanar layin gidansu, sai da ta k'urewa ganinsa sa'an nan ya tsallaka titin cikin damuwa ya nufi in da tuka-tukar take yana tunanin abinda ya ke damunta.


Cikin matsanancin tashin hankali da damuwa ta shiga gidan, kai tsaye rugume kakar tayi tana rera wani irin kuka mai tsuma zuciya! duk da ta kasance nakasashiya ba zata so ayi mata irin wannan auran ba, gabadaya al'amarin bai kwanta mata a rai ba wannan shine dalilin da yake sanya ta zubda hawaye.

Baba Asabe ta rike ta suka shiga daki a tare, ita kuwa Saliha ko a jikinta ta'be bakinta ma tayi ta cigaba da aikin gabanta.


Da kyar Baban ta rarrasheta ta dora da fadin." Dama tun da naga wannan kiran na gaggawa na san akwai abinda zai faru, Jamilu ba shi da kirki ko kadan kiyi shuru ki fada min abunda sukayi miki."


Tasa hannu ta goge hawayen dake gudana a saman fuskarta, ido jawur! ta kalle ta da fadin." Wai aure zai yi min ."


Baban ta zuba mata ido cike da mamakin maganar

"Aure kamar yaya ."? ta sake tambayarta domin jin cikakken bayani.


Murya na rawa da yanayin maganarta ta fara sheda mata hukuncin da baban nata ya yanke a kanta cewa lallai zai had'a ta aure da wanda yayi ra'ayi.


Baba Asabe tayi tsalle ta dire! ta fara surfa bala'i ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, ta ce." Wato yanzu ne zai nuna iko a kanki saboda bashi da kunya an gama yi masa wahala kin girma kin zama mutum shine zai shigo da wannan maganar to wallahi bai isa ba mutukar ina raye ba za'ayi wannan auran ba."

Kawu Musa ya shigo gidan ya riski maganar ya zauna Baban tana sake jadadda masa cewa Jamilu bai isa ba yayi kadan sai dai duk in da za su shiga su shiga amma ba zata bari ba.


Ya ce." Baba musulunci ne ya bada damar hakan, ai budurwa ce mahaifinta na da ikon za'ba mata mijin aure bazawara ce kadai ke da 'yancin za'bar mijin da take ra'ayi, saboda haka babu ruwanki, ki cire kanki daga wannan maganar."


Ta ce." Ka san Allah ba zan lamunta ba, domin dai yarinyar nan ba ta da cikakkiyar lafiya to ba zan bari garin san zuciyarsa ya aura mata bara gurbi ba, a jikina nake jin akwai dalilinsa na aikata wannan abu."


Ya ce." To shikkenan yanzu abinda za'ayi shine zanyi binkice akan lamarin idan ya kasance shi wanda ake so ayi auran dashi mutumin kirki ne ya tara duk abubuwan da ake da bukata haka akeso, amma idan akwai mishkila a tare dashi nima ba zan bayar da goyon bayan tabbatuwar al'amarin ba."


Ta ce." Eh hakan yayi na baka wuka da nama kayi min binkice akan shi Jamilun da kuma dalilin da yasa yake so ya aura mata wanda ba ta so."


Ya mike da fadin." In sha Allahu zanyi kokarin gano yanda al'amarin yake.


A daran ranar Shahida ba ta iya rintsawa ba sallar dare ta kwana ta nayi tana kuka da rokon Allah yayi mata za'bi na alkairi a cikin ranta take jin za ta iya auran Baban-baba akan dai ta auri mutumin da mahaifinta yake kokarin aura mata, tun bata ganshi ba take masa wata irin tsana!

Da yamma tana daki a kwance tana tunanin rayuwarta ta tsinkayi muryar yaro." Wai ana sallama da Shahida in ji Saminu Abbatuwa."

Gabanta yayi mummunan faduwa! Baba Asabe ta harari yaron a fusace! ta ce." Ka je ka ce bata nan."

Yaron ya juya ya fita yana dariya! daman ya san za'a rina, tunda mutumin ya aiko shi gidan zuciyarsa ke raya masa cewa ba zai samu ganin budurwar da yake so ba duba da irin hallitarsa da tarin munin da Allah yayi masa.


A she bata hakura hijab ta zura a wuyanta ta kama hanyar fita tana surutai akan al'amarin, so take ta ga mutumin tayi masa cin mutunci!


Shirgegen mutum ta gani da katon ciki a tsaye a kofar gidan nata.

Ta kalli tafkekekiyar kafarsa da dunduniyar take waje sakamakon takalmin da yayi masa kad'an farce zako-zako kafafun sunyi wata irin daud'a da kaushi da faso abin babu kyawun gani!

Ta kalli sumulmulallan kansa da fuskarsa dake zuba uban kyalli 'kwayar idonsa jajawur gasu cike da kwantsa da alama dai yana da matsalar ido.

Hankalinta bai tashi ba sai da ya wangale bakinsa yana dariya babu ha'koran sama dana kasa sai turame a gefe da gefe! mummunan wawulo ne dashi! ya zube har kasa yana gaisheta.

Gefe ta matsa gabanta na dukan uku-uku! lallai Jamilu bashi da mutunci ina yarinya kankanuwa kamar Shahida za ta kai wannan katoton mutumin.


Ta gaza furta komai sai kallonsa take tana tunanin yanda zata bullowa al'amarin.


''Baba Asabe Ina wuni." Maganarsa ta dawo da ita hayyacinta.

Ta amsa "Lafiya lau kai ne kake sallama da Shahida."?

Ya ce." Eh ni ne sunana Saminu Abbatuwa ina sana'ar siyar da dabbobi a kasuwar Abbatuwa dake cikin wannan gari namu mai albarka."


Ta girgiza kai da mamaki a tattare da ita ta ce." Waye ya turo ka gurin Shahida? ko kuma kai ka ganta ka ga kana so."?


Yayi shuru yana nazarin maganar, fuskarsa ta sauya da bacin rai! ashe hujaj bai daidaita komai ba amma yasa shi zuwa domin a ci masa mutumci.

Ta sake maimaita masa tambayarta ta farko "Shin turo ka akayi ko kuma kai ka ga yarinyar kake so."?


Ya ce." Mahaifinta ne ya fansar min da ita a madadin kudin da nake bin sa."


Gabanta yayi wani irin fad'uwa! dama tasan ruwa baya tsami banza!


Ta kalle shi rai! a 'bace ta ce." To ka koma ka sheda masa cewa ni Asabe yayi 'karya bai isa ba ya sanya yarinya a caca na Shiriya zuwa kotun koli dashi a kan wannan al'amarin."

Ya sa hannu ya sharce gumin dake saman goshinsa ya kalle ta da mummunar fuska ya ce .'' Dama ba ni na nema ba shine yayi min kyautar ta a madadin kudin da nake bin sa kimanin dubu dari uku da hamsin saboda ya kasa biya na, don haka yanzu daga nan gidansa na nufa domin muyi wacce za muyi."


Ta ce." Wannan kuma ya rage naku." gida ta shige tana bambami da mamakin al'amarin.



Dawowarsa kenan daga kasuwa Saminu yayi masa dirar mikiya.

Tunda ya fito ya ga yanayin fuskarsa ya tabbatar da cewa lallai akwai matsala ya bude baki kenan zai yi magana ya katse shi ta hanyar fadin......
[4/19, 10:28 AM] Bintu: Unguwar giginyu.
Shukura cikin matsatsun kaya ta fito da wani 'karamin mayafi a kafad'arta wanda dashi gwara babu. hannunta rike da mukkulin mota tare da handbag tana wani irin k'amshi mai fizgar hankali. Shukura karatun low ta yi yanzu haka ta kammala, tana ta fafutukar aiki, mahaifinta ya ce ba da yawunsa ba, domin dai babban burinsa bai wuce a ce ya aurar da ita, duba da yanda ta kai munzalin auran, bayan haka kuma tana aikata abubuwa marasa kyau irin wanda ba ya so, hakan kuma baya rasa nasaba da sanya hannun uwarta akan dukkanin abunda take.

Ganinsa a zaune a gurin hutarsa ya sanya jikinta ya yi sanyi sai ta hau duru-duru! ya kalle ta tun daga kasa har sama! yanayin fuskarsa ya sauya da 'bacin rai!

Yarinyar na so ta zubar masa da mutunci a gari domin ya jima yana hana ta shigar kaya irin wannan amma taki ta daina a kullum burinta ta fitar da tsaraicin ta waje.

Cikin 'bacin rai ya ce ." Shukura ba kya jin magana ko?

A sanyaye ta ce." Daddy kayi hakuri don Allah."

Ya daga mata hannu da fadin." Koma cikin gida."

Sai ta fashe da kuka da fadin "Daddy kayi hakuri ka bar ni don Allah." A shagwabe take maganar.

Ya duba a gogon dake d'aure a hannunsa shida da rabi na yamma daf ake da a kira sallar magariba.


Ya ce." Ina za ki ji? Hanci ta ja da fadin" Bikin 'kawata a can karkasara."


Girgiza kansa ya yi da fadin ." Ki koma gida babu in da za ki je." yanda ya fadi maganar babu wasa ya sanya ta juya a guje! tana kuka!


Ta zube a jikin kakar uban tana gursheken kuka. Hajiya Saude hankalinta ya tashi a duniya ta tsani 'bacin ran yarinyar dalili ita kad'ai ce babu wasu. shiyasa take lallabata. ta dinga rarrashinta kan tayi shuru ta fada mata abinda yake faruwa


Ta ce." Daddy ne ya ha na ni zuwa kuma kin fi kowa sanin yanda nake da Samira 'kawata ce sosai ai bai kamata Daddy ya hana ni zuwa bikinta ba.


Ta ce." Aikuwa bai kamata ba wallahi, shiyasa wani lokacin bana son zamansa a gida saboda yana matsanta miki da yawa bari ya shigo na ji dalilinsa.

Tana rufe baki ya shigo da niyyar d'aura alwala. ta dakatar shi ta hanyar kiran sunansa "Alhaji Habu."

Ya amsa tare da tsayawa yana sauraranta. "Meye dalilin da ya sa zaka hana yarinyar nan zuwa bikin 'Kawarta kana fa matsantawa yarinyar nan Alhaji Habu."


Babu wasa a fuskrasa ya ce." Hajiya wane irin biki ne wannan ? wanda sai magariba za ayi shi, to ba zan lamunci wannan shashanci ba, bayan haka kuma dubi sutturar da take jikinta tuntuni na hana ta sanya dinkuna irin wannan amma taki ta dai na wannan dalilin ya sanya na hana ta zuwa kowane irin biki ta hakura dashi tunda ba ta jin magana."


Ta kwantar da kai da fadin." Ai ba za ayi haka ba yarinyar nan Samira 'kawarta ce tare su ka yi karatu ya kamata ace Shukura ta halarci bikinta kayi hakuri ka bar ta taje ba don halinta ba sai dai ni nake nema mata alfarma."


Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." To shikkenan amma ta sanja kaya lallai kuma ki sanya hijabi a jikinki kafin ki fita."

Da sauri ta daga kanta da fadin." Insha Allah Na gode Daddy." ba tare da yace komai ba ya bar gurin.


Kamar gaske ta fito da k'aton hijab har k'asa tayi wa hajiyar sallama ta fita, tana shiga mota ta cire hijab din tana jan tsaki ! karamin mayafin dake ciki jakarta ta fito dashi ta rataya a kafad'arta sannan ta kunnar motar fige ta da karfin gaske ta fita daga gidan, kai tsaye rijiyar zaki ta nufa gidan Hajiya Zaliha domin sunyi waya da Mamanta ta ce ta sameta a gidan domin itama ba ta jima da sauka a garin ba.


****
Tashin hankali kenan! tun a bakin titi a ka tare shi aka sheda masa abinda yake faruwa, bai gazgata ba sai da ya karya kwanar layin gidan ya ga zahiri! tun daga nesa yake hango jama'a cike a kofar gidansa ga katakwaye da katifu da sauran abubuwan amfaninsu nan a watse a gurin, tonan silili Saminu ya zo yayi a gidan bayan fitarsa yasa zaratan Samari suka dinga watso musu kayan su waje, Hadiza da sauran 'yan uwanta sai kuka suke, ita kuwa Talatu tana zaune a kofar wani gida abin duniya ya dame ta, ma'kota da 'yan uwanta sai bata baki suke, Saminu yasa k'aton kwado (dan mukkuli) ya kulle gidan yayi tafiyarsa.


Hujaj tunda yake bai ta'ba tozarta irin yau ba, ya rasa da wane ido zai kalli Jama'ar dake gurin, kawai sai ya huce! fushinsa akan Shahida ya dinga gaura mata mari yana fadin." Kin ga irin abinda ki ka janyo min ko? kin ga tozarcin da ki ka janyo min ko."? ya dinga kwashe ta da mari yana haurinta da kafarsa har sai da ta durkushe a gurin tana wani irin kuka! da kyar aka janye shi daga gurin ana bashi hakuri.

Malam Habu makocinsa ya ja shi gefe yana bashi baki da fadin ." Haba Alhaji Jamilu ka nutsu mana ita kuma wannan yarinyar da kake dukanta meye laifinta da zaka huce fushinka a kanta dama tuntuni nake fada maka ka gyara kuskuranka saboda irin wannan rana to yanzu ga abunda ya faru."


Ya cire hular dake kansa yana firfita da ita ya ce." Malam Habu wallahi ban taba tunanin Saminu zai yi min wannan tozarcin ba, amma babu komai tsinanniyar yarinyar can ce ta janyo min domin da ta amince da bukata ta da tuni haka ba ta faru ba kamar ni a ce an tozartani irin haka.''

Malam Habu Ya ce." Yanzu dai mu bar wannan maganar insha Allahu komai zai daidaita, akwai daki da rumfa a cikin gidana zan baka aro ka shiga ka zauna kafin mu ga abunda Allah zai yi."

Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke da fadin ." Na gode sosai Malam Habu Allah ya saka da alkairi." Ya ce." Babu komai bari yanzu nasa yara su kwashe kayan su shiga dasu Allah ya kiyaye faruwar hakan anan gaba .''

Ya amsa da "Ameen yana bin gurin da kallo, manya da yara sun cika sunyi dafifi a gurin kowa na tofa albarkacin bakinsa.


****
"Ranka ya dade wallahi na dauka binkicen da ka sanya ni zai bani matsala sai gashi cikin hukuncin Allah komai ya zo da sau'ki don lokacin dana shiga Unguwar ban sha wahalar sanin waye Alhaji Jamilu ba."

Zamansa ya gyara a nutse ya ce." Sule nima nayi farin ciki da haka ina fatan zan samu kyakykyawan labari daga gare ka."


Fuskarsa ta sauya da alhani da kuma jajantawa. Ya ce." Yallabai al'amarin mutumin dai babu arziki babu kuma kima da mutunci.''

"Ina sauraranka." Ya fada tare da mayar da hankalinsa gare shi.


Cikin rashin jin dadin abubuwan da ya gani da idonsa ya shiga warware masa abunda ya faru ya kuma dora da bashi labarin da ya samu daka bakunan mutane da sauran jama'ar dake makotaka dashi, domin ya tabbatar masa da gaskiyar binkicensa ya nuna masa hotonan da ya dauka a lokacin da yake ta zazzabgawa yarinyar mari ana ta bashi hakuri.


Ya karbi wayar yana duba hotonan ransa yayi masifar 'baci ganin yanda yake dukan yarinyar har da kafarsa, babu shakka wannan mutumin bashi da mutunci kuma bai san darajar dan adam ba, kuma jahilci shike da damunsa ba wani abu ba, hakika ya ji ciwon yanda ya ke tozarta yarinyar a gaban jama'a amma bai nuna hakan a fuskarsa ba, ya mika masa wayar da fadin." Goge hotonan daga wayarka."

Da sauri ya goge gabadaya kamar yanda ya umarce shi.

Ya kalle shi a nutse ya ce." Da safe idan Allah ya kai mu ka je ka nemi shi mutumin da yayi tozarcin domin jin cikkenan karin bayani daga gare shi, ina so ya tabbatar maka da iya adadin kudin da yake bi daga baya sai mu ga ya za'ayi ."


Ya ce." Insha Allahu zanyi kokarin ganin hakan ya tabbata."

Ya ce." Ma sha Allah ka tashi ka je kawai sai Allah ya kai mu goben ."

Ya mike yana godiya sannan yayi masa sallama ya tafi.


A daran ranar bai kwanta ba sai da yayi Istahara akan al'amarin, ya wayi gari da yarinyar a cikin ransa, yana tausaya mata sosai yana kuma so ya aure ta amma yana tunanin wani abu a cikin ransa, duk da hakan ba haramun bane amma yana ganin kamar yarinyar tayi masa 'kan'kanta da yawa idan anyi duba da matakin shekarunsa, yayi mata girma domin yana kallonta ne kamar 'yar sa Shukura

1 Comments On BA MAHAUKACI BANE Book 1
avatar
arfat-aliyu

12 months ago

Reply

Masha allh

Please Login or Register in order to submit comment