Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da alamar kunya ko a Ido.. "A gayawa uwar ubanki me dattin talauci..." Hajiya mommy ta amshe da kundumoma na'eema manyan ashariya. Na'eema ta hade Rai tana kunkunai. "In ban aikaki kasashen wajen saro kayayyakin ba ubanki dake kabari zan aika ya saromin shigiya kawai! Yar bura uba, Nan dattin talauci ne ya kashe ubanki! shegiya Dan uban ubanki tashi ki barmin falona kuma gobennan ki shirya ki koma gidanki ,in mijinki yadawo ya taddaki gidansa,karki jamin yazo ya gayawa ubansa, tin uban be tafuka Wani Abu yazo ya tafuka a kansa, tinda azabar sonshi yakeyi kamar hauka.." cike dajin haushi da bakin ciki na'eema ta tashi ta bar falon ta cika fam ta batse, a rayuwarta ta tsani yarfi kuma mommy ta matsifar iya disga mutum a cikin friends dinta, ita kuma na'eema ga rashin kunya,ba tattausa harshe ko a kan uwa ne, a rayuwarta tana kaunar tafiye tafiyennan da takeyi , ko Dan pictures datakeyi tana nunawa duniya ta faso gari, uwa uba kuma tana facaka da kudi, ga yawon bude Ido tanayi tana ganin Yan Gayu da masu kudade. Hajiya wasila tace "wannan Karan kin matsawa yarinyarnan a kan seta koma gidan mijinta, bayan ke takema Amfani,saboda Allah fa yarinyar nan na Kokari ..." hajiya mommy tace "Eh nasani hajiya Amma ni tsorona kada yaronnan ya gaji ya gayawa mahaifinsa kinga de ko be mgna wata rana se yayi magana, ni shine kawai problem dina... " "Karki taba damuwa tinda kin riga kinsan hannunki..."cewar Hajiya najmu. Duk suka kyalkyake da dariya, hajiya nana ta nisa cikin nutsuwa domin duk tafisu nutsuwa da ilmi ita Dr ce, tace "Kawata gaskiya be kamata ace yarinyar Nan tayi wannan kibar ba Tari guda, alhalin ko haihuwar farko batayi ba,duba fa yadda tayi kiba duk gashi tafimu kiba, ke kanki uwarta tayi hudunki, mazan yanzu fa bawani So sukeyi mace tayi kiba ba, Nan da Nan seta narke inta cika kibarnan,.." Hajiya naja'atu ta amshe da "Ah Dr nana batta ta narka kibarta, yadda kowa ya kalleta zesan tana auran me kudi kuma babban soja Masu fada aji a Nigeria .." hajiya wasila ta amshe da "Wallahi kuwa a batta ta barbaza kibarta ...yooo taci tayi hani'an, uba kudi d'a kudi kaf dangi bana tsifa, a batta ta narka kibarta yadda zata kara bayyana a hajjajunta, Muma da kika ganmu Hana hajiya dande iya jikin kenan, Amma kiba ai kwarjini ce...." "Wannan de magana taku ce kune masu diya..."cewar hajiya rafi'ah, duk kaninsu duk suka murmusa .. hajiya nana ta rausayar da Kai tace "gaskiya de ni a ganina ya kamata ta rage,, kinga ita yarinya ce mu kuma mun manyanta a garemu kiba take kwarjini,ita Kam na'eema ai kunga yanzu take tashe, gashi Mijin nata shima yaro ne,gudun kada yaga wata yayi sha'awah mazann na yanzu se A hnkli daga haka se su jajibo maganar Aur..." "Aaahhhhhh kullll hajiya kulll da maganar Aurennan,, ke kinga alamar ni Rafi'ah ina raye za ayima diyata kishiya? Yooo ni Nan na da nake tsofai-tsofai Dani ma a Kanta ba Amin kishiya ba se ita datake yarinya danya a kaina... Allah kyauta, ya kade zancen kishiya,, ni wallahi wallahi a kan ama diyata kishiya kwara ni Amin kishiyari!'' rafi'ah ta fadi tana huci Kai kace kishiyar akayo mata ynzu. kaf kawayen nata seda suka juyo suka kalleta jin furucin datai na karshe. "Kinsan me kikace kuwa Aminiyata?'' cewar hajiya naja'atu baki sake. Hajiya rafi'ah dake girgizar kafafuwa cikin isa da takama da duniya tace "ina sane wallahi hajjaju. Sanin kankune a duniyar Nan kaf dinta na'eema kawai na mallaka a matsayin diyata, wlhi San da nake mata ko kaina ban masa wannan San, Sam banason abinda ze tabamin ita, kinga kuwa da ace an mata kishiya kwara ace ni akayima ita, nasan yadda zanyi da ita, itafa ga yarinta ga rashin wayau, uwa uba ba halinmu Daya da ita ba, ni ina iya kisan rayuka da yawa a kan mijina...Sam babu digon imani a zuciyata musammanma a kan kishiya,,kinga ita kuma na'eema akwai digon imani a zuciyarta bazata iya kashe kishiyarta ba,, ni Kam wlhi wlhi hajiya in akamin kishiya ko ban kasheta da makirci ba zan kasheta da hannayena, sede a wayi gari ta mutu, Kuna a rasa ta yaya ta mutu...wlhi duk abinda zan Aikatawa kishiyar da Akamin zan Aikata mafiynsa a kan kishiyar da Akama diyata,,'' kaf sukayi tsit suna nazarin kalaman Hajiya rafi'ah, Hajiya naja'atu tayi tsit Sam batasan kawarta tayi nisa ta wuce tunaninta har haka ba. tabbas kmr yadda tace Sam bata da digon imani. "Allah ma ya kyauta..." Cewar Hajiya naja'atu, datai mgnr Hadi da sauke ajiyar zuciyar da ita kadai tasan kona Menene. Kaf suka amshe da Amin hajiya nana ta zarce dacewa "Ai duk me tsautsayin data shigo muku a matsayin kishiya tini sunanta R.I.P...." "ai kwara Matacciyar da aka ga gawarta ta fita gata..." cewar Rafi'ah datai maganar zuciya da murya babu alamar imani dai-dai da kwayar zarra. "hmmmmm Allah de ya nisanta me tsautsayi..." cewar hajiya wasila suka amshe da Amin. "Hajiya mu gama muyi sallar la'asar se muje ki kaimu sabon shago muga didimar Arziki Musa albarka..." Cewar naja'atu, daman shago rafi'ah ta bude shine sukaxo gani dasa Albarka. Nan aka chanza Hira zuwa hirar sabon shagon hajiya Rafi'ahWadda liyafa keta kankama.

A bangaren Na'eema tanashiga dakinta tayi dealing number din Aminiyarta daya tal khadija, a Egypt dataje sarin kaya suka hadu da khadija rafi'u , suka kulla kawance gashi yanzu har sunyi 3yrs tare,. bugu daya khadija ta dauka. "Hajjaju da kanta uwar gidan Alhaji Aeezad,, yaushe kika dawo kasar?'' cewar khadija daga cikin wayar. Na'eema ta tabe baki tace "Jiya nadawo khadyn buba..." "Meyafaru Naji kamar bakya mood ?'' cewar khadija data fahimci na'eema bata mood a yanayin yadda ta amsa ta, da ace tana mood da yadda ta mata kirarinnan kyalkyalewa da dariya zatayi. Kmr na'eema na jira taja Wani dogon tsaki me shaddah da kisrah,kana tace "wallahi mommy ce ta bani mugun haushi...wai yau ni mommy kecewa in tattara in koma gidan Aeezad daga dawowata ko hutawa banyi ba, salon ya dawo ya maidani kamar dafaffen food me maggi..." Khadija ta kwashe da wata uwar dariya sbda karshen mgnr na'eema. "Yanzu meye abin dariya a Nan ?'' na'eema ta fadi a kule. Khadija ta tsagaita daga dariyarta tana fadin "am sorry kawai kece kk bani dariya da kikace wai ya maidaki kamar food...wlhi kawata rashin juriyarki tayi yawa, ke kawai matsalarki sex in namiji nasan sex in baki jure masa a hakan wlhi komi zaki masa bakya burgesa...." Na'eema ta amshe da "shi wannan ko gindin zan wanke in basa ya hada da gabansa su zama daya bazan burgesa ba wallahi,yadda kikasan mommy haka yake Sam ba ayi masa gwaninta., Kmr yadda de kikaga mommy ga yarfin tsiya,.." khady tace "Ohhh Wani na Nema Wani na gudu,, ni kinga wallahi Rabon da Alhajibuba yayi sex Dani yafi 2yrs shifa a rayuwarsa inde kudi na shigo masa ba ruwansa da maganar sex dinsa dani, kingade aurena dashi 4yrs tsaf zan iya kirga sau nawa ya kusanceni daga lokacin zuwa yanzu, kullum se yacemin beda lafiya shi yayi ayyuka ya gaji, gashi ko romances be iya ba, in Yana taba nonuwa ke kyace yaki akeyi ,kamar ze tsinkeminsu daga jikina, nifa da akan yayi wasa Dani kwara na hakura na fawwalawa ubangijina, na kallo sex video na hkra..tin abun na damuna har na hakura, ina Nan zan samarwa kaina solution danni ba dutse bace du-du-du shekaruna ashirin da uku, tinda mukayi Aure ko bari ban taba yiba,, to in takaice miki tinda yake kwanciya Dani a fari, be taba kaimin karo ba har in kawo sede inyi wasa da kaina in kawo Byn ya gama sex Dani...ganinan ba alamar ciki ,shi Alhaji inde da kudi to mgna ta kare a garesa, kudinsa sunfi masa iyalinsa daraja..." na'eema ta ciza yatsa tace "inama ace shine Aeezad..." "inama ace ni Aeezad dinne mijina..." Khady ta fadi a ranta domin mgnr bata faduwa a fili, ta jima tana mafarkai da dama a kan Aeezad mijin kawarta, taso ace daman a talaka ya fito da kudi ko nawa ne seta dinga biyansa domin ya dinga cinta, Amma Kash seya fito ame kudi ta yadda bata isa ta tunkari gabansa Kai tsare ba balle da wannan maganar. A zahiri Khadija tace "Hmmm ki bari kawai Na'eema Allah baya ba me wuka nama..." da wata manufa khady tayi mgnr Amma sam na'eema bata ankare ba, tace "Tabbas da nice ke yadda kike watayawannan ai danaji dadih dako tunanin Namiji bazan ba balle gabansa..." khady tayi humming kawai, ita ba bakuwar kudi bace, na'eema ce bakuwar kudi, iyayenta asalin masu kudi ne na fitar hankali kuma dattawa ne, mahaifinta shiya hadata da mijin da take aure, Alhaji buba shiya ganta yace yanaso Aminin mahaifinta ne, ya taba aure yanada yarinya Daya mahaifiyarta ta rasu tin yarinyar na 15yrs yarinyar sa'arh Khady ce yanzu haka tana kasar waje karatu, tinda khady ta Auri Alhaji buba bata samu abinda takeso ba a tattare dashi , ita Kuma gata jarababbiya tanada tsananin bukatuwa da d'ana miji. Haka take zaman hakuri da Alhaji buba saboda bata da yadda zatayi ,ba halin taje gidansu mahaifinta baze barta ba , domin shi babban mutum ne ga dattako bawai irin mutanen Nan bane da basu da girma sena rigunan jikinsu. "Yanzu yazanyi kawata? Wlhi Sam banasan komawa gidan Aeezad ynzu..." Cewar na'eema da abun ke damunta tinda Mommy tace ta koma gidan mijinta tashiga dimauta. "Toh in baki koma ba meye amfanin Auren? Kinga kawata wlhi mijinki nada hkri inba shiba a zamanin Nan ba wanda ze jure yawon da kikeyi zuwa kasa-kasa ba izinin mijinki...kowa yaji ai yasan ba izininsa kk tafiye tafiye, ina kirge fa tinda akayi Aurenki 1month kkyi a dakin mijinki kika cigaba da barin kasa-kasa sarowa mommy kaya, mijinki fa babban mutum ne kowa yasan ba a San ranshi ba,ynzu kuma ki dawo kina kyashin komawa meye problem dinki ne kawata? Sex kou?..'' na'eema ta amshe da ''After that shegen sa Aikin tsiya, kullum sena gyara masa room 2tyms, ga wankin toilet bayan uban gajiyar dayake taramin, dasafe inta masa aikace Aikace, ko maids dinafa baya fari su tinkaro part dinsa balle insasu gyara masa dakinsa..." Baki khady ta saki tace "gaskiya kawata kin cika San jiki, yanzu kawai wadannan sune problems dinki? Ke da maids kkeso su dinga gyara bed din da kuka kwanta?'' na'eema ta amshe da "Ehh mana kajiki ke kuma, ni me Aikinsa ce dazanta masa whla,,shifa Sam beso yaga kin zauna, ga shegiyar tsaftar tsiya a haka komi kkyi baki iya masa ba, ke kanki a kazanta yake kallonki..." "Tabdijan...yanzu inYa cire boxes dinsa wake wanke masa'?" "Waze wanke masafa khady? Shike wanke kayansa da kansa, ko nawa panties din ban wanke ba se nasa...tinda baze iya bawa maids Ko yasa a matching ai sede yasha whlrsa shi kadai,ke namiji fa kome kika masa baya gani kwara ma karkiyi..." khady tace "Hmmm Allah kyauta..." A zuciyarta tana hasaso inama ace itace ke Auren yaro karami me danyar kaciya tabbas dayasha lailaya, seta kara danyatasa tass, itafa dama za a dawo mata da baya da babu abinda zesa ta AUREN Alhaji buba NAMIJIN KUNAMA, bashi da dadih se azabar zafin harbi. "Gobe zanzo in kawo miki kayan gyara ki gyara jikinki kafin ki koma ko zaki samu sauki a bangaren sex din .." cewar khady. Badan na'eema taso ba tace "Okay se goben nagode best friend..." Daga haka sukayi sallahma.




Wannan book din na kudi ne, gamesan Namijn zuma da Namijin duniya se biya 1500, in kuma days kkeso zaki biya 1k 0542703718 Saadatu Abdullahi gT bank.

🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝
💖💖💖💖💖💖💖💖💖
*NAMIJIN ZUMA*
🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝
❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥
(Love and Romantic Story)

This book is 1k 08101626484

SAADATU BINTU ABDULLAHI (Writer of kyautar Allah)
Free page7
2month ya iyayi a garin Kano da kyar, Kai kace tsungulinsa, ba tare daya kammala Ayyukan gabansa ba yaji kawai so yakeyi ya tafi katsina, be san dalilin dayasa yakeso ya tafinba kawai de yaji yanaso ne ya dawo katsina. Jirgi yabi ya dawo garin katsina, daman sometimes shine kawai keson tafiya a mota in zeyi tafiye-tafiye yanada kebantaccen jirginsa,danma ynzu da rayuwa tayi tsada sace-sacen mutane yayi yawa musammanma hanyan abuja, shiyasa yake Hawa jirgin sometimes, Amma yafi kaunar tafiya a mota, sede in Nisan tafiyar yayi yawa, Kwata-kwata baya jure zaman mota sede awa biyu uku hudu biyar yake iya jurewa. Kasancewar be bar garin Kano da wuri, se after Azahar ya bar garin kanon, danma jirgine bawani jimawa ya sauka a babban Airport din dake garin katsina, already daman dreva dinsa da matakan tsaronsa suna airport din suna jiransa, Dan haka ba bata lokaci ya shiga mota aka nufo gidansa dashi,. Kallon hanya yakeyi Amma zuciyarsa na can ga tunani-tunani daban-daban, shide yasan Wani Abu na damunsa Amma ko za a kashesa besan mezece yana damunsa ba,. ''Ya Allah!'' ya fadi da sassanyar muryarsa tamkar busar sarewa, yakai hannu ya dafe saitin zuciyarsa Yana mejin bugunta da sauri da sauri. ''Ya Rabbih kayimin maganin boyayyiyar damunata..." Ya fadi a zuciyarsa, yayinda wayarsa ta dauki ringing ya duba yaga Daddynsa ne, girgiza Kai kawai yayi tinda ya bar garin daddy be kirasa ba, shima kuma Aeezad din be kirasa ba, abinda yasa shi Aeezad be kirasa ba sbda sometimes koya kirasa ba dagawa yakeyi ba, musammanma in Yana tare da hajiya mommy to ko ubanwa ze kirasa ba dagawa zeyi ba,. Yana niyar daukar wayar ta katse ya kirasa back bugu biyu daddyn ya daga. Sallahma Aeezad ya masa Hadi da gaidasa cikin girmamawa. Alhaji sunusi ya amsa cike da so da kaunar d'ansa tilo namiji, kana yace "Lafiya kwana biyu shiru ubana shirun yayi yawa ko ayyukan ne?'' a yadda yakewa Aeezad magana ya tabbatar masa da basa tare da rafi'ah domin da suna tare da wuya ya kirasa. "Alhamamdulillahi daddy kawai ayyukane sukamin yawa.." "tohh tohh ,,shikenan Allah yayi Albarka, Allah yasa ku gama da duniya lafiya, Ubangiji ya jikan mahaifiyarku me kaunata..." Alhaji sunusi ya karashe murya cikin rashin dadih. Cikin Wani yanayi shima Aeezad ya amsa da "Amin ya Rabbil izzatih daddy..." "Ya wajen Hafsatu da jikokina " Girgiza Kai kawai Aeezad yayi Wani takaici ya cika masa zuciya, ace suna the same state wai shida yake wani garin shi daddy ke tambaya Ya hafsat, mutum da yaransa seya buya ze kirasu a waya '' gaskiya rashin uwa ma jarabawa ce..." Aeezad ya fadi a zuciyarsa Sam kuma se yaji Wani takaici yayima Zuciyarsa dirar mikiya, ya tabbatar da sunada mahaifiya da hakan be faru ba, tabbas inka rasa uwa ka rasa rabin dadihn duniyarka. "duk lafiya Lau suke .." shine abinda Aeezad ya fadi a zahiri. "Masha Allahu a gaidasu Allah ya hanaku damuwa duniya da lahira .." "ga damuwar nan kanasa mana.. " Aeezad ya fadi a zuciya, besan mgnr ta fito fili daddy yaji ba, kawai sede yaji daddyn nacewa. "kuyi hkri wata rana se Labari, ba abinda yake dawwama..." A yadda yayi mgnr seya bawa Aeezad tausayi kawai ya furzar da iskar takaici da bakinci da tausan Mahaifin nasa gabaki daya. "Thanks daddy,Allah Kara lafiya..." shine abinda Aeezad ya fadi. Alhaji sunusi ya amsa da Amin daga haka sukayi sallahm. Aeezad ya ajiye wayar gefensa kawai Yana me tunano abubuwa da dama, shi da kansa yasan matsalolinsa sunada yawa,ga rashin uwa, ga mahaifinma da kadan yaso yafi kwara babu, ga na'eema itama matarsa da tini tazama kwara babu, Tako ina deshi babu dadih, mommynsa ce kawai inya tunata yakejin sanyi a ransa, a nan yake samun saukin wasu lamuran, da besan ina ze tsaya a damuwa ba. Da tunani tunani a ransa Aka isa gidansa dashi, wanda tin daga bakin get har zuwa cikin gidan abun kallo ne , duk iya gayunka in kazo gidan Aeezad dole ka zama Dan kauye, shi karshe ne a gayu da tsari. Tin kafin dreva ya karasa packing dinsa a packing space din gidan Aeezad ya kula da motar Na'eema wadda tafi Hawa a farfajiyar gidan, da wata motar ma da besan ta wacece ba,kirar Jeep, hakan yabawa Aeezad tabbacin na'eema tadawo gidan, haka kawai ya tsinci kansa da rashin farin ciki akasin da, da ace Dane da tini yanata murna a part dinta ze yada zango,ko wanka baze ba ze hauta daci, se ya sauke nauyin mararsa kana ze samu nutsuwar ko abinci yasamu yaci. Akasin yau, yanajin sha'awarh bawai beji ba,Amma sam be tunkari part dinta ha, ya tinkari nasa part din,. Direct a bedroom dinsa ya yada zango ba bata lokaci ya fad'a bathroom yayi wanka ya fito daure da Alwala ya shirya cikin kananun kaya na hutu, ba karamin amsar launin fatarsa kayan sukayi ba, dai-dai ana Kiran la'asar already daman ya dauro alwala lallausar takalminsa ya saka ya fito farfajiyar gidan ya nufa masallacin dake cikin gidan. Bayan sun idar da sallar ya fito daga masallaci hannunsa rike da counter Yana lazimi. Dai-dai Na'eema da khady sun fito ,na'eema zata rakata motar khadyn wadda zata tafi gidanta, domin ta d'an jima a gidan tin kafin Azahar tazo. Sukayi kicibus da Aeezad, kallo daya ya musu ya dauke idanuwansa A kansu yayi kamar ma be gansu ba, na'eema ta tabe baki ganin kallon dibar iskar dayayi musu daman shi haka yake Amma a daki ya dage yayita cin gindi, ya iya zunguri Kam kuma ya iya yarfi. khady ta kuresa da Ido a zuciya se wow wow kawai takeyi knr motar Ambulance! bata taba ganinsa da kananun kaya ba se yau, Ashe kyansa ya wuce tunanin khadyn bata sani ba se yau. "Tsarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci kyakyawan namiji me Asali(wato tsawo)..." Khady ta fadi a ranta seda ta sauke ajiyar zuciya, ko a Ido tasan guy dinnan zeyi dadih na matsifa, itafa wlhi da ace ze aureta tini zata kashe aurenta ta auresa koda ace beda ko sisi balle uwa uba ya tara qualities na fitar hankali, ga kudi ga kyau ga cikar haiba, ga asali (wato tsawo). "Ina wuni ranka ya dade...'' khady ta gaidasa cikin girmamawa dai-dai sun karaso daf-daf da junansu. "Lafiya Lau,,, ya iyali?'' Aeezad ya amsa a takaice Hadi da Tambayarta ya iyali sbda ya ganeta, yasanta a matsayin Aminiyar matarsa tin kafin ya Auri na'eemar. "Lafiya Lau Alhamamdulillahi...." Khady ta amsa, yayinda Wani irin sanyi da dadih me ni'ima ya ratsa khadyn tana bala'in San muryarsa tana narkar da ita over,, khady tayi murmushinn boye tabi bayansa da Ido yayinda tuni ya isa part dinsa, yanada sassarfa yanada sauri sosai kuma a hnkli yake tafiya. "Daman Yana Nan ne?"" Khady tayi tambayar taba dawo da akalarta ga na'eema wadda suke tafiya zuwa motar khady ita Kuma na'eema na danna wayarta a duniya na'eema bata rabin second bata danna waya ba, kullum wayarta na hannu tana chart a groups da friends dinta ko kuma tana kan tiktok tana kallo, ko toilet zata shiga da waya a hannunta. "Aah bayananfa inaga yanzu yadawo gaskiya,,," cewar na'eema datayi mgnr irin ko a jikinta dinnan, itade tasan tana kaunar Aeezad Amma sam wahalace ita bataso, shi kuma Aeezad nada sa Aiki, uwa uba kuma shegen San sex din tsiya, wanda dayayi dayasa mata ciwon jiki. "Amma shine baki gaidasa ba ko ki nuna murnarki a fili na dawowarsa..." khady ta fadi fuska dauke da mamakin hali irin na na'eema. Tabe baki na'eema tayi dai-dai suka iso bakin motar khady. "Murnar me zanyi danya dawo ? Daukarsa zan in goyasa a bayana in maidasa jariri..." cewar na'eema dake mgnr tana tabe baki. Khady tace "No but at least ai yakamata de ko gaidasa ne Kiyi...ke koni da raini yashiga tsakanina da mijina sbda rashin iya tabuka komi inya dawo daga tafiya ina tarairayarsa, sannan ina gaidasa cikin girmamawa,..." Cikin kosawa da mgnr na'eema ta amshe da "uhmmm kede khady da Allah kyale mutuminnan..ni wallahi zuwanki ma ya temakeni,nasan danya ganki ne ai da direct part dina zezo ya tasani da gafza,,jarababbe kawai!'' khady tace "Allah kyauta..." Tana me duba time, saboda mijinta na gari kuma baya barin fita shegen kullen tsiya ne dashi, in zata fita seya bata awannin da yakeso tayi, inko ta wuce awannin Nan se yayi fada sosai, in bayanan Sam baya barinta fita ,gashi ya cika gidan taf da matakan tsaro, in zasuje kasashen waje sede duk inda tasa kafa yana Nan ko kuma sakataransa na Nan kusa da ita , Sam bata sakewa, da ace ita kazar sake ce da Allah kadai yasan me zatayi. "ni zan wuce , nasan Alhajin Allah nacan yana duba time tin dazu,..." Khady ta fadi tana bude gidan baya tashiga domin daman dreva ne ya kawota.. "Alhajin Allah manya,, duk tsoronsa fa karkije a sosa miki inda shi be sosa miki .." cewar na'eema, khady ta kyalkyake da dariya Hadi da nunawa na'eema dreva din khadyn dake gaban motar Alamar tayi shiru karya jisu. "Afff...." Na'eema tace Hadi da rufe baki, khady takai mata dukan wasa sukayi Yar dariya, kana sukayi sallama dreva yaja khady suka fice a gidan, Na'eema ta juya zata koma part dinta, taga Aeezad ya fito daga part dinsa hannunsa rike da car key, ta kallesa taga shi ko kallonta ma beyi ba tamkar be ganta ba, ya nufa motarsa yashiga yaja da kansa ya fice a gidan. Na'eema ta daskare a tsaye ba karamin mamaki Aeezad ya bata ba yau, ganin yadda bebi ta kanta ba, mamaki ya tsaya mata a wuya wai yau Aeezad ne ze dawo ya iya fita ba tare Daya Addabeta da laguda ba. "Tafi nono fari " na'eema ta fadi Hadi da daga kafad'arta ta nufa part dinta.


5:pm tini ta gama girkin dare , daman girkin kadai takeyi a gidan shine aikinta, akwai ma'aikata kusan goma a gidan masu share-share da wanke wanke, kasancewar gidan nada tsananin girma kuma ga yawan part's,kullum se an gyara kowani part sbda baban Noor na yawan yin baki abokan Aikinsa. Zaune take a tamfatsetsen falon kasa, ita da yaran sunata bata labarai iri-iri wasu ta gane wasu kuma Sam bata ganewa,mahaifiyar yaran tana sama domin yau weekend ne ranar hutunta kenan, bata cika sakkowa kasa ba in ana weekend tafi zama a sama, Baban Noor kuma yana part dinsa. Kaman daga sama taji an turo kofar falon baki dauke da sallahma Kasa-kasa a natse, tin kafin yayi sallama tasan shine ya shigo sbda taji kamshin turarensa tin before ya bude kofar shigowa falon. zubo masa dara-daran idanuwanta masu kyau na fitar hankali Tayi se wani lumshewa idanuwan nata keyi cikin salon fisgar wanda ake kallo, ita haka idanuwanta suke, kullum cikin yauki suke. Maida kofar yayi ya kulle ya jingina bayansa da kofar shigowa falon, yana mejin zuciyarsa na Wani irin harbawa cikin hanzari, sbda zuro masa idon da tayi,, shima zuro mata dara-daran idanuwansa yayi narkakku sede basu Kai nata narkewa ba, sanye take da rigar zaman gida faraa sol me rodi-rodin d'awisu a gaban rigar cikin adon red-red, yayin datasa hula red a Kanta. Tamkar An kara masa matsifar dake damunsa haka yaji Nan da Nan yayi losing controlling, idanuwanta suka masa kisan gillah, kwata-kwata abinda yakeji bazeyu ya iya jurewa ba. "Wayyo Allah nah! Zuciyata namin zugi Me kunah!" Ya fadi Yana me dafe saitin zuciyarsa wadda ke barazanar fashewa daga ciki, Kawai seyaji wasu hawaye masu Azabar zafi tamkar ruwan Daya kusa tafasa suka wanke masa kyawawan kumatunansa, shi irin Mutanen

Please Login or Register in order to submit comment