Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasa kamar yadda ka yi mini bayani. Hakika a da na tsani Imhal fiye da komai da kowa a wannan duniya amma a yanzu ina kaunarsa kamar yadda nake kaunar farin cikina da naka.
Kafin gimbiya Lamirat ta gama rufe bakinta tuni sarki Gurzalu ya daka mata tsawa cikin tsananin fishi har yana bamberata da kafa ta fai kasa sannan ya ce, ashe kuwa ke ba jiina ba ce muddin za ki do wannan yaro. Akan wane dalıli ma za ki soshi kuma saboda me ya ki kasheki?
Ko da jin wadannan tambayoyi guda biyu sai Lamirat ta yi murmushi sannan ta mike zaune ta zauna akan kujera ta fuskanceshi ta ce ya kai Abbana ka yi sani cewa ba komai ne ya sa naji yanzu na kamu da son jarumi Imhal ba face ganin yadda na tsananta kiyayya a gareshi nake ta kokarin hallaka shi, ammna sai gashi shi ya sami damar kasheni har sau uku amma bai kasheni ba, sai nuna mini tsantsar soyayya ma da yayi.
A Lokacin daya gabza mini wawan naushin nạn a mukamikina sai da nayi dan gajeran suna. Ko da na farfado na ji ya dan shakeni a wuya kadan sai nayi yunkurin.na kwaci kaina, a sannan ne ya rikeni gam ya yi mini rada a kunne ya ce zai yi kamar ya murde mini wuya, don haka na zube kasa nayi kamar na mutu. Ba ni da wani zabi a wanna lokacin wanda yafi nayi abin da ya umarceni idan har bana son ka rasani. Tabbas idan ka rasani zaka shiga cikin mugun yanayi.

Zamu dakata a nan saikuma allah ya kaimu zamu ci gaba
AA Misau ke MaganaRIJIYA GABA DUBU
Littafi Na Hudu (4)
Part D.
Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau ke Magana

Marubucin yaci gaba da cewa

Tabbas idan ka rasani zaka shiga cikin mugun yanayi.
Wannan bayani da nayi maka shi ne amsoshin tambayar da ka yi mini guda biyu. Na san ba zan iya tilasta maka ba akan ka janye kiyayyarka akan jarumi Imhal ba, kuma gashi babu damar ka fita daga cikin wannan gasa to amma ina so ka sanı cewa daga yau na cire kiyayyar Imhal a cikin zuciyata bisa la'akari da rashin sanin takamaiman dalilin da kuma hujjar da ta cancanci na ki shi.
Na yi iyakar tunani da hange tun daga lokacin daka fara haduwa da Jarumi imhal kawo yanzu naga cewa idan ma gabarka da shi tana da asali to daga danginsa ne kuma bai kamata ka ci gaba da ita yanzu ba tunda shi bai yi maka komai ba. Sai dai kuma idan akwai wani 6oyayyen siri a cikin zuciyarka.
Kafin Lamirat ta rufe bakinta tuni Sarki Gurzalu ya shara mata mari. Saboda Karfin marin sai da ta fadi kasa, a lokacin ne nadama ta zowa sarki Gurzalu ya yi Sauri ya kama kafadunta ya tasheta tsaye, ya shiga bata hakuri domin tun daga lokacin da aka haifeta kawo iyanzu bai taba ko da shafar jikinta ba da nufin duka ba sai yau.
Kawai sai gimbiya Lamirat ta share hawayenta ta dubi sarki Gurzalu cikin
murmushi ta ce, babu komai ya Abbana ka je ka yanke duk irin hukunci da ka ga ya dace. Ka sna6i cewa daga yau babu wanda zai sake ganina a garin nan tunda kowa ya dauka cewa na mutu.
Ko da gama fadin hakan sai gimbiya Lamirat ta wuce izuwa cikin dakinta.
Kafin ta janyo kofar dakin ta rufe sai ta duni wata kuyanga dake zaune kusa da kofar dakin ta ce daga yanzu ke kadai ce kike da ikon ganina da shiga cikin đakina kuma idan kika bari wani ya san cewa ina raye a bakacin ranki.
Cikin rawar jiki kuyangar ta sunkui da kai ta ce, an gama ya shugabata.
Take gimbiya Lamirat ta janyo dakin ta rufe sannan taje ta kwanta akan
gado.
A sannan ne taji keyarta ta fara zogi, take ta tuno da ciwon da jarumi Imhal ya ji mata a lokacin da ya fyalleta da kafa tayi sama ta fado kasa ta kume. Cikin sauri ta mike tsaye ta cire dukkanin kayan yakin dake jikinta har ma da takalmanta, sannan ta cire kyallen da ta daure keyar ta ta da shi ta shiga kewaye.
Da kanta ta wanke ciwon sannan ta dawo falo ta sawa kanta magani, ta daure ciwon da sabon kyalle mai kyau sannan ta sha maganin kashe radadi da zogi ta sake kwanciya akan gado.
Ko da ta lumshe idanunta da nufin tayi barci sai barcin ya gagara domin ba komai ta rinka gani ba face fuskar jarumı Imhal a lokacin da ya kura mata idanu yana murmushi. Nan take Lamirat ta ji babu abin da take so sama da ganinsa yanzu take.
Sai kawai Lamirat ta mike tsaye zumbur ta nufi kofar fita daga cikin dakin.
Har ta kama marukin kofar dakin zata Janyo ta bude ta fita sai ta tuna cewa ai yanzu bata da ikon fita tun da kowa ya dauka cewar ta mutu.
Cikin tsananin takaici da bakin ciki gami da sanyin jiki ta koma kan gadon ta kwanta. Kawai sai ta ji wani irin hawaye mai zafi ya zubo mata saboda radadin soyayya a cikin zuciyarta.
Al'amarin da ya bata mamaki kenan domin a iya rayuwarta bata taba kamuwa da son wani da namijı ba, amma yau gashi saboda son da namijı da ya shigeta farat đaya har tana zubar da hawaye mai zafi saboda begensa da rashin ganinsa a kusa da ita.
Nan fa hankalin Lamirat ya dugunzuma ainun saboda tasan cewa har a
gama wannan gasa bata da ikon baiyana kanta a wajen jarumi Imhal tunda ba za ta bari ba a ga fuskarta ba.
Wannan shi ne abin da ya faru ga jaruma Lamirat bayan an gama gasar kambun jarumtaka a karo na uku tsakaninta da jarumi Imhal.

**** ***** ******

A can bangaren su sarki Taryan kuwa lokacin da suka shiga cikin turakarsa shi da gimbiya Shumaira sai suka zauna suka yi zugum suka rasa me ma zasu yi tsakanin farin ciki da bakin ciki, saboda ganin mutuwar gimbiya Lamirat.
Cikin alamun tsananin damuwa sarki Taryan ya dubi Shumaira ya ce, abin da nake so da ke shine kada mu kuskura mu nuna farin cikinmu akan wannan nasara da Jarumi Imhal ya samu duk da cewar mun sami ribar kudade masu đimbin yawa a cacar da na shiga kuma kema nasan cewa
kina farin ciki da mutuwar gimbiya Lamirat tunda itace kadai zata kawo miki cikas a cikin soyayyarki da shi.
Ko da jin wannan batu sai Shumaira ta yi murmushi ta ce, abin da ka fadi
gaskiya ne, to amma ni kaina na yi matukar bakin ciki bisa ganin yadda aka kashe 'yar sarki mai daraja haka a cikin wannan gasa.
Ko da Shumaira ta zo nan a zancenta sai hawaye ya zubo mata ta fashe da kuka. Da kyar ta budi baki ta ci gaba da magana ta ce, tabbas na ji wannan mutuwa matuka domin na shaku ainun da gimbiya Lamirat tunda tun muna yara muke kawance, tabbas zan dade ina alhinin rashinta.
Ko da gimbiya Lamrita ta zo nan a zancenta sai kawai taji sarki Taryan ya
kyalkyale da dariya.
Al'amarin daya matukar bata mamaki kenan ta kura masa idanu kawai ta kasa cewa komai, a sannan ne sarki Taryan ya zauna daf da ita kamo hannayenta ya rike ya dubeta cikin nutsuwa ya ce yake yata kiyi sani cewa mai aiki da hankali da tunani shike warware dukkannin wata matsala da kuma abinda ya shige wa mutum duhu, kai tsaye kiyi tunani da nazari tabbas jarumi imhal ya kamu da tsananin son Gimbiya Lamirat domin ko irin kalllon da yake mata ya isa ki tabbar da hakan, idan har son n gadkiya babu karya to babu yadda za ayi jarumi imhal ya iya kashe Gimbiya Lamirat da hannunsa, king kenan lallai akwai wani abu da suka shirya don haka ni bna yarda d cewar gimbiya Lamirat ta mutu ba, idan kuwa har ta mutun da gaske to dole ne ayi bikin binneta a matsayinta na yar babban sarki a gobe da safe ko kuma a tafi d ita can kasarsu, dan haka ya zama mana wajibi damusan hanyar da zamu bi mu bincika gawar dan mu tabbatar da hakan, kafin su bar yankin birninmu da gawar ta ko wane hali dan kada a rain mana hankali.
Sa'adda sarki Taryan yazo nan a zancensa sai hankalin Gimbiya Shumaira yq dungunzuma ainun ta cika da tsananin mamaki gami d wasi-wasi ta dubeshi cikin alamun matukar damuwa ta ce to yanzu ta yayazamu iya dub gawar Gimbiya Lamirat idan aka hadata da dakarun tsaro wadanda zasu yi mata rakiya izuwa can birninsu?
Koda jin wannan tambaya sai sarki Taryan yayi murmishi snna ya dafa kafar Shumaira ya ce ai maso abinka ya fika dabra, kuma hanyar kashe makahon kare yawa gareta, kedai kawai ki zuba idanu ki sha kallo, yanzu zan je na gana da Sarki Gurzalu omin nnji yadda yake son ayi binkin binne gawar yar tasa, amma dai nasan bazai binne a wannan birni namu ba sai dai yace a tafi da ita cqn birninsa, kuma lallai bazai iya bin gawar ba dole ne ya zauna har sai an kammala wannan gasa ta kambun jarumtaka.
Sarkin Taryan na gama fadin hka sai kawai ya mike ya fice daga cikin turakar tasa yq nufi bangaren da aka baiwa su sarki Gurzalu masauki, da isar Sarki Taryan bakin kofar sai ya iske kofar a bude, kai tsaye ya kunna kai ciki falon koda ya isa sai jikinsa yayi sanyi matuka sakamakon inda yayi arba da shi ba komai ya gani ba face sarki Gurzalu da dukkanin makarabansa zaune a kas bisa gwiywowinsu sun tasa gawar Gimbiya Lamirat aba suna zubar da hawaye.
Nan take shima Sarki Taryan idanunsa suka kada suka kama zubar da hawaye, ya karasa kusa da sarki Gurzalu ya rungumeshi yana kuka gmi da yi masa ta'aziyya, daga nan kuma sai ya mike ya karasa gaban gawar Lamirat yq tsugunna ya kuma surutai irin na wanda yqke bakin cikin mutuwarta, haka ne a cikin hikima ya sunkuyo da kansa daidai saitin hancinta ko zai ji fitar numfashinta amman sai yaji shiru, kai har sai da ya dora hannunsa a bisa kirjinta ko zai ji bugun zuciyarta amman nan ma shiru bai ji komai ba.
Al'amarin aya sa jikinsayayi sanyi sosai kenan, ya fara tunanin cewa lallai Gimbiya Lamirat mutuwar gaske ta yi, babu batun sihiri ko rainin hankali.
Bayan Sarki Taryan ya gama yan surutansa gami da yan koke kokensa ne akan gawar Gimbiya Lamirat sai ya mike tsaye ya koma kusa da sarki Gurzalu ya zauna daf da shi yadda kafadunsu na gugur na juna sannan ya ce ya kai Abokina hin yanzu me ka shirya akan binne gawar yarka, anan birnin za a binmeta ko kuma can birninka za a kai gawarta?
Koda jin wannan tambayar sai sarki Gurzalu ya dago da kansa a lokacin da hawaye ke faman zubowa daga cikin idanunsa ya dubi sarki Taryan ya ce bisa al'adar masarautarmu abin kuny ne jininmu yq mutu a binneshi a wani wajen da ban ba cikin yankin kasarmu ba, dan haka gobe lallai zansa jama'ata su dauki gawar Lamirat su tafi da ita, ni babban bakin ciki namq shine bazan samu damar halartar bikin binne yata guda daya jal a duniya ba, tunda dole ne na tsay na karasa wannan gasar ta kambun jarumtaka wacce nke ganin za a iya kammalata nna da kwanaki biyu kacal, tabbas nasan cewa jarumi imhal zai iyayin wasan gobe, kuma idan har yq samu nasara a wasan na gobe kaga kenan jibi za a yi wasn karshe wanda zai kara dani.
Koda sarki Gurzalu ya zo nnn a zancensa sai sarki Taryan ya jinjina kai yace tabbas maganarka gaskiya ce, dan haka yanzu sai dai mu zuba ido muga abinda zai faru a goben aboda babu tabbacin cewa jarumi imhal ne zai samu nasara.
Koda jin haka sai mmaaki ya kama sarki Gurzalu ya ce wai shin wane jarumi ne zai fafata da Jarumi imhal din a gobe?
Sarki Taryan yayi jiyar zuciya cikin alamun karaya ya ce ba wani bane face sadauki MarrasuBin Samdas, koda jin haka sai idanun sarki Gurzalu suka zazzaro ya firgita kuma ya cika da dunbin mamaki. Shidai sadauki Marrasu wani gawurtaccen jarumi ne wanda ya shahara a wancan karon da aka yi gasar kambun jarumtaka, ya zamana cewa ya gagari gaba daya jaruman gasar, kuma shi kwaf daya yake yi wa mutum ya gama da shi saboda tsananin afin namansa da karfin saransa gami da naushinsa. Sai da ya kafsa da jarumai 73 kuma yayi musu dukan farat daya suka sheka barzahu. Sarki Gurzalu ne kadai ya fafata da shi har tsawon rabin Sa'a, sai da sadauki marrasu yayi wa sarki Gurzalu rauni sau 13 yayi masa lagalaga har ya zamana cewa kowa ya cire wa sarki Gurzalu tsammanin rayuwa, amman ba zato ba tsammani cikin tsananin zafin nama sai aka ga sarki Gurzalu ya dafa kasa yayi sama kamar an harbo shi dag cikin baka, kafin marrasu ya kai wa sarki Gurzalu hari a lokacin aya daga kansa sama tuni Gurzalu ya zaro wata sharbebiyar takobi ya caka masa a makoshinsa ba tare da wani bata lokaci ba wannan wuka ta lume a cikin makoshin marrasu tana mai fasowa ta keyarsa, sai ga jini yana burbulowa daga keyarsa yana kwanya a kasa kamar idaniyar ruwace ta balle.
Nan take Marrasu ya sandare yana mai durkushewa kasa kai kace gunki ne shi ba mutum ba a wajen.
Koda ganin qbinda ya faru sai yan kallo suka hau shewa suka riga yiwa sarki Gurzalu jinjina, a wannan shekara sai da sarki Gurzalu ya samu kyaututtuka masu yawan gaske daga hannun sarakuna duniya wanda shi kansa bai san adadinsu ba, ya zamana cewa ya samu dukiyar da bai taba samun kamarta ba a rayuwarsa.
Sarki Taryan yayi murmishi ya ce ya kai Abokina nasan kayi mamaki bisa jin cewar sadauki marrasu ya sake dawowar wannan gasa ta jarumtaka alhalin ka kashe shi da hannunka gaban miliyoyin yan kallo, to ka sani cewa Marrasu bai mutu ba domin bayan an dauke gawarsa an tafi da ita daji da nufin a binneta sai kawai akaga akwai sauran numfashi a tattare da shi, nan da nan dakaru suka dawo da shi gari a guje, aka yi mani bushara da cewar bai mutu ba. Kod jin haka sai nasa likitoci suka sukufa akansa aka shiga ceto rayuwarsa, sai da Marrasu ya shafe wata tara a kwnace yana jinya, kamar ma bazai tsira da rayuwarsa ba sannan ya samu lafiya, har ya bude idanuwansa sannan ya bude baki a karon farko tsawon wata taran da yake kwance ya ce sai na dauki fansa akan sarki Gurzalu, sai nayi masa mummunan isan da ban taba yi ma waninsa ba.
Koda aka zo aka fada mani cewa sadauki Marrasu ya bude baki da idanu a wannan rana kuma ga abinda ya fada, sai na kamu da tsananin farin ciki ba dan komai ba sai dan sanin cewa jarumina ya dawo wanda yafi kawo mani kudi.
Tun daga wannan rana na boye cewa sadauki Marrasu na nan a raye bai mutu ba, kuma nasa aka rinka bashi kulawa ta musamman, amman fa hatta tafiya sai da aka koya masa.
Lokacin da Sadauki Marrasu ya gama warkewa sosai ya cigaba da baiwa kansahoron yaki dare da rana kawo izuwayanzu da aka fara wannan gasa bai huta ba daidai da rana daya, ina mai tabbatar maka da cewa inda za a samu jarumai irin ka guda uku su rufarwa sadauki Marrasu bazasu iya ganin bayansu ba, saboda karfin damtsensa da iya yakinsa sun ninka na da sau uku.
Koda jin wannan batu sai sarki Gurzalu ya gyada kai gami da dan guntun murmushi y ce ya kai abokina bana musu da dukkanin abinda ka fada, amman akwai wani abu da kake mantawa da shi, ni da jarumi imhal muna da tsananin naci, sa'a da kuma juriya dan haka samun nasara akna mu sai babban rabo, kai dai kawai ka zuba ido goben domin ba a sanin maci tuwo sai miya ta kare.
Koda gama fadin haka sai sarki Gurzalu ya fice daga cikin dakin ya nufi masaukinsa.
Kashegari kuwa tunda sassafe aka sanya gawar Gimbiya Lamirat a cikin wata akwatun katako, aka sanya a cikin keken doki aka kuma hada gawar da dakaru dubu biyar bisa jagorancin Sarkin yakin sarki Gurzalu suka fice daga cikin birnin na Misra.
A daidai wannan lokacin ne kuma aka fito da Jarumi imhal daga cikin dakin da ake tsare da shi, an gama shirya shi kuma an sanya masa kayan yaki, kuma an bashi takobi da garkuwa suna rike a hannunsa ya doshin hanyar da zata kaishi filin gasa. Koda Jarumi Imhal yaga akwatin gawa bisa keken doki, kuma kuma ga dakarun sarki Gurzalu sun yi mata rakiya sai hankalinsa ya dungunzuma ainun ya dubi daya daga cikin dakarun sarkin Gurzalu ya ce wannan kuma gawar waye za a tafi da ita birnin kisra?
Badakaren ya ce wace irin magana kake haka, shin har ka mnta ne cewa kaine ka kashe Gimbiya Lamirat a gasar da kuka yi jiya, ai gawarta ce waccan za a tafi da ita birnin kisra ayi bikin binneta.
Koda jin wanan batu sai idanun Jarumi imhal suka zazzaro ankalinsa yayi masifar tashi, kuma jikinsa ya kuma tsuma tunda shi a saninsa ya tabbar da cewa bai kasheta ba, shin yaya aka yi yanzu kuma aka ce masa ta mutu?
Koda ayyana haka sia kawai ya zabura da gudu yayi fitar burgu daga cikin dakarun dake zagaye da shi, yana mai falfalawa da azababben gudu ya nufi inda gawar Lamirat take...

SHIN ME JARUMI IMHAL YAKE NUFI DA YA FALFALA DA GUDU YA DOSHI RUNDUNAR DA KE TSARE DA GAWAR GIMBIYA LAMRITA

YAUSHE ZA A CIGABA DA WANNAN GASA TA KAMBUN JARUMTA

KUMA WAYE ZAI SAMI NASARAR LASHE GASAR KARSHE

Marubucin yace
Mu hadu a littafi na 5 don jin cigaban wannan labari daga Mai debe muku kewa a kullum a ko yaushe
Abdulaziz Sani M Gini

Saikuma ni
AA Misau ke Magana
Nake cewa Sai mun hadu a na gaba

Domin shiga WhatsApp group dinmu danna blue din rubutunnan👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment