Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ud kuma sai Shumaira ta tsuke fuska ta daina yin dariyar, sannan ta duneshi cikin nutsuwa da laranci ta ce Kwantar da hankalinka ya kai jarumin jarumai wanda zai karbi kambun jarumtaka daga hannun sarki Gurzalu ka yi sani cewa nima mutum ce kamar kai, nice dai Gimbiya Shumaira iya ga sarki Taryan na wannan birni wacce kake gank a filin gasa. Tabbas na yi amfani da karfin sihiri wajen shigowa wannan waje ammqn bisa taimakon wanda ya taimakeka a filin gasa ya ceci rayuwarka a lokacin da abokin da abokin karawar taka ya gazayi maka komai.
Koda jin wannan batu sai idanunjarumi imhal suka zazzaro yana mai gyyara zama cikin alamun tsananin mamaki ya ce To wai shin wane ne wannan mutumin wanda ya taimakenk kuma saboda me ya taimake ni, shin yana da watabukata ne a wajena?
Yayin da Shumaira taji wadannan tambayoyi sai ta girgiza kai ta ce Amsar wannan tambaya na wajenka cikin wannan dare. Da farko dai shi wanda ya taimake in yace na fada maka cewar shine dan uwanka na jini wanda yay saura a duniya amman yace ka yi hakuri ba zaka ganshi ba har sai bayan an kammala wannan gasa ta kambun jarumtaka.
Sannan y ce na sanar da kai cewa zai ci gba da iya kokarinka iyakar iyawarsa don ganin ya kareka daga sharrin makiyanku, kuma idna har kana son ka gnaa da shi to kaima kayi iya yinka wajen tabbatar cewar kaineka lashe wannangasa ta kambun jarumtakaanan birnin Misra. Magana ta karshe da xan yi maka ita ce tun aranar d idanunasuk yi arb dakai naji nakamu da tsananin kaunarka kuma nake fama da begenka dare da rana don haka ko kanasona ko baka sonasai na yi duk yaddazanyi dan gankn na mallake zuciyarka akan ka so ni feyw da dukkan wata ya mace a wannan duniya, da wannan furuci nake maka sallama ya tauraron zuciyata, sai mu hadu a filin gasa. Shumaira na gama fadin hkaa sai ta juya ta fice ta cikin wadannan sandunan karfen kamar yadda ruwa ke ratsa kasa.
Nanfa Imhal yq shiga kwala mata kira akan ta dawo ammna sai yaga dakarundake tsaron daki da yake ciki su kama kyalkyala masa dariya domin su a zatonsu y samu tabin hankali ne.
Koda ganin haka sai Jarumi Imhal ya koma ya kwnata abinsa a lokacin da kansa ya daure, wasiwasi gami da tunanuka suka cika masa zuciya; abu nafrako dai shine ji yayi wani irin farin ciki mara misaltuwa ya shiga ransa sakamakon jin cewar yanq da sauran dan uwa na jini a wannanduniya kumaya ji babu abinda ya ke so sama da yaga wannan dan uwana nasa da idonsa, kuma yanzu neya samu karfin gwiywar da yake gani cewar ta kowane hali sai ya samu nasarar lashe wannan gasa. Abu nabiyu da ya tayar masada hankali shine bqtun kalmomin oyayyar da gimbiya Shumaira ta yi masa wadanda suka jefashi cikin tsaka mai wuya tund shima yq lashi takobin sai ya samu soyayyar Gimbiya Lamirat ta owane hali, duk da kuwa yqsan a yanzu babu abinda ta tsana sama da shi, kuma gashi itama Gimbiya ta lashi irin wannan takobi. Wai shin wane ne zai samu biyan bukattarsa acikin su su uku? Tambayar da Jarumi Imhal ya yi wa kansa kenan kuma ya kasa fitar da amsarta, nan take kuma ya tuno da batun kurkukun Birnin Kisra dakuma rijiyar azaba wato rijiya gaba dubu da irin tsananin wahalar da ya sha a cikinta, kawak sai jikinsa ya kama tsuma zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone har bai san sa'adda da ya sake mikewa zaye zumbur ba yanamai take karyayyar kafarsa ba nan take iccen daya daure kafar suka kakkarye tare da zubewa kasa, nan fa ya kama zarya a cikin dakin tamkar bai taba karye wa ba.
Kawai sai ya kama sandunan dake jikin kofar dakin ya kama girgizasu yana kwala ihu mai tsananin karfi da razanarwa, dakarun dake tsaron shi kuwa tuni suka arce cikin hanzari suka yi cikin gidan sarautar domin kai rahoton abinda ke faruwa saboda suna gani a kodayushe Jarumi Imhal zai iya jijjige wannan kofa ya fito ya gudu.
Tuni a wannan lokaci labari ya riski Sarki Taryan ya garzayo da gudu izuwa dakin, dakaru da yawa na take masa baya. Sai dai koda ya iso sai ya iske Jarumi Imhal a tsaye kuma a nutse kamar bai aikata dukannin abinda akaje aka fada masa ba.
Cikin matukar mamaki Sarki Taryan ya dubi jarumi imhal ya ce da shi ya kai jarumin jarumai shin gaskiya ne kayi kokarin guduwa daga cikin wannan daki damuka sa aka tsareka?
Koda jin wannan tambaya sai Imhal yayi murmushi sannan ya suddar da kansa kasa sannan cikin biyayya ya ce Ya shugabana ai ba guduwa zanyi ba, kawai so nake na nuna cewa nasamu lafiya domin karayar dake jikin kafata ta warke, kuma inaso lallai gone da safe a cigaba da wannan gasa.
Koda in wannan batu sai mamaki da kuma farin ciki suka turnuke sarki Taryan, ya zura hannayensa cikin sandunan karfen yana mai dafa kafadar Imhal ya ce da kyau jarumina tunda aka fara wannan gasa da kai nine dan cacar da yafi kowa zuba kudi a kanka, kuma ga shi nasamu ribar da ban taba samun kamarta a rayuwata ba, koda kuwa a cikin harkokin kasuwancina, yanzu dai zan cigaba da zuba kudadena koda kuwa bazaka samu nasarar lashe wannan gasar ba, ina mai sanar da kai cewa idan ka fadi a wannan gasa tabbas arzikina sai ya raunana ainun, amman kuma idan ka lasheta to zan zamo attajirin da babu kamarsa a nahiyar nan gaba daya, Kuma na yi maka alkawarin cewa zan raba ribar dana samu kaso uku na dauki biyu na baka daya.
Koda jin wannan albishir sai Jarumi Imhal ya kamu da tsananin farin ciki gami da dimbin al'ajabi domin yana mamakin yadda aka yi ya hau tafarkin zama babban attajiri haka, a matsayinsa na mafaraucin daji da bai taba mallakar kudin da suka wuce dinare 1000 ba ma.
Nan dai sarki Taryan ya yi masa sallama sannan ya bada sanarwar ayi shelar ci gaba da gasar nan da gobe da safe.
Kafin gari ya waye tuni labari ya bazu a ko ina na cikin gari kama daga birni da kauyuka harma da sauran kasashen dake makwaftaka da su.
A lokacin da sarki Gurzalu da Gimbiya Lamirat suka ji cewar wai Jarumi Imhal ya warke daga karayar da ya yi a cikin kwana daya jal, kuma har ya yarda zai ci gaba da gas a gobe, sai suka rude kuma suka dimauce, ba su suka gaskata maganar ba sai da suka ji ta a bakin sarki Taryan da kansa. Ba komai ne ya dagula wa Gurzalu lissafi ba face kada ranar fafatawarsa da imhal ta zo ba tare da cikar kwana ukun da za a gano masa barawon kambun sihirinsa ba.
Lokacin da Gimbiya Lamirat ta lura da cewa hankalin mahaifinta ya dugunzuma ainun, sai ta dubeshi ta ce Ya kai mahaifina, ka kwantar da hankalinka domin na fada maka cewar ta ko wane hali sai imhal ya fadi a gobe saboda ina da tabbacin cewar jarumin da zasu fafata a gobe ya fishi jarumta da kuma sa'a.
Ko dajin haka sai Sarki Gurzalu yayi murmishi irin na manya ya ce Haba yake yata ina so kiyi sani cewa ni din nan nasan abinda ke baki sani ba, ina mai tabbatar maki da cewar babu wani jarumi wanda zai iya samun nasara akan jarumi Imhal a halin yanzu face ni komai karfinsa, iya yakinsa da kuma sa'arsa kuwa. Nasan kina shakka akan maganata amman ki zuba ido ki sha kallo domin gani ya kori ji, sai goben idanunki za su tantance wannan magana tawa, kada ki damu ya ke yata domin akwai wani boyayyen sirri gami da tanadin da na yi, duk da cewa bana tare da kambun sihiri na, ai duk wanda ya rigaka kwana dolene ya rigaka ta shi.
Sarki Gurzalu yana gama fadin haka sai kawai ya juya ya fice daga cikin dakin da suke zaune yana kyalkyala dariyar mugunta, nan ya bar gimbiya Lamirat tana mai binsa da kallo cikin matukar mamaki.
Kashe gari da safe lokacin da sarki Gurzalu ya farka daga bacci sai ya nemi Gimbiya Lamirat amman sai ya rasa, kawai sai yaga wata wasika data bar mashi. Cikin hanzari ya dauki wasikar tare da budeta. Ba komai ta rubuta a cikin wannan wasika ba face Mu hadu a filin gasa zaka sha mamaki.
Koda ganin wannan dan guntun bayani sai zuciyar sarki gurzalu ta buga da karfin gaske, ya kamu da tsananin tsoro gami da wasiwasi yana cewa anya kuwa ba Lamirat ba ce jaruma ta uku da za su fafata da Imhal a yau ba kuwa?
Koda ayyana haka sai kawai ya ruga cikin kewaye tare da fadawa, ko wanka bai tsaya yi ba ya tafi izuwa filin gasar.
Koda isarshi filin gasar sai ya iske ai yafi kowamakara a filin gasar, domin filin gasar ya gama dinkewa da jama'a babu masaka tsinke. Nan take dakaru suka buda mashi hanya da karfin tsiya sannan ya wuce ya isa inda su sarki Taryan ke zama wato wurin da aka tanadar wa sarakuna da kuma manyan attajirai.
Nan take ya tabbatar da cewar zarginsa ya zama gaskiya wato lallai Lamrita ce jarumar da za ta fafata da jarumi Imhal.
Tun daga nesa zuciyar sarki Gurzalu ta ci gaba da bugawa da karfi sakamakon rashin ganin gimbiya Lamirat zaune akan kujerarta.
Nan take bakin ciki ya turnuke sarki Gurzalu ya ce a ransa hakika wannan
yarinya bata da hankali, kuma kuruciya da wauta na damunta. In banda wauta, akan wane dalili zata tari jarumi Imhal alhalin ni kaina ina shakkarsa. Ta bar ganin cewa yanzu ta sami horon yaki da fada mai yawa wanda yafi nawa ai ba a nan take ba. Yanzu gashi bani da ikon tsayar da wannan gumurzu nasu tunda an gama shirya komai. Shi kenan na rasa 'yata, lallai sai na yiwa Imhal kisan gilla irin wanda ba a taba yin kamarsa ba.
Ko da sarki Gurzalu ya zo nan a cikin zancen zucinsa sai kwallar takaici ta cika masa idanu amma sai ya yi sauri ya goge idanun nasa don kada su sarki Taryan su gane halin da yake ciki, yaje ya zaune akan kujerar sa wacce ke daf da ta sarki Taryan suka dubi juna cikin murmushi sannan sarki Taryan ya ce da shi, ai nayi zaton ko ba zaka iya kallon wannan wasa ba tunda da 'yarka za a yi shi.
Gurzalu ya yi murmushi ya ce ai na yarda da 'yata don haka ba na shakkar
kallon wannan wasa, don nasan ba zata taba bani kunya ba kuma ai ko taje kasa bani da nadamar komai tunda wanda ya kaita kasan jarumi ne abin kwatance a duniya.

Zamu dakata a nan saikuma allah ya kaimu zamu ci gaba

AA Misau ke MaganaRIJIYA GABA DUBU
Littafi Na Hudu (4)
Part C
Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau ke

Ina yiwa Daukacin jama ar wannan gida barka da wannan lokaci dafatan kuna lafiya

Marubucin yaci gaba da cewa

komai tunda wanda ya kaita kasan jarumi ne abin kwatance a duniya.
Ko da jin wannan batu sai sarki Taryan ya gyada kai cikin nuna alamun gamsuwa sannan ya ce, gaskiya na yi matukar mamakin yadda akayi har Gimbiya ta shiga wannan muguwar gasa mai hadarin gaske a matsayinta na "yarka guda daya jal a duniya, alhalin kasan cewa wasa ne na kisa wanda ba sani kuma ba sabo. Dokar wasan da ka'idarta shi ne dole ne mutum ya kashe abokin gwaminsa.
Yanzu idan Lamrita ta sami nasarar kashe Imhal zata iya haduwa fa da kai kenan a zagaye na biyar kuma shi kenan sai ta kasheka ko kuma kai ka kasheta? Menene ribarku da ma'anar aikata hakan?
Ko da jin wannan tambaya sai jikin sarki Gurzalu ya yi sanyi, takaici ya dada kamashi ya ji kamar ya fashe da kuka, amma sai ya dake ya kawar da kansa ga barin kallon sarki Taryan ya zuba ido akan tsakiyar filin gasar.
Nan take mai gabatar da gasa ya fara da kiran sunan gwarzon jarumi wato Imhal. Ko da jin an ambaci sunansa sai filin gasar ya kaure da shewa gami da tafi tare da kade kade, kowa ya cika da mamaki kuma aka zuba ido aga ta yadda jarumi Imhal zai fito da karyayyiyar kafa don babu wanda ya yarda cewar kafar ta warke a kwana daya jal har ya sami damar takata kuma ya ci gaba da yin wannan gasa.
Ai kuwa sai ga jarum Imhal ya fito daga cikin dakin da jarumkan gasa ke
fitowa a cikin shigarsa ta yaki kuma yana taka kafafunsa da karfi cikin sauri tamkar bai taba samun karaya a kafar tasa ba.
Nan fa filin gasar ya dada kaurewa da ihu, shewa, kade kade da bushe bushe gami da kirari da jinjina ga jarumi Imhal, har ya iso tsakiyar filin yaja tunga, ba a saurara ba sai da aka buga gangar fara gasar sannan aka yi tsit tamkar mutuwa ta gifta.
A sannan ne kuma mai gabatarwa ya kirawo sunan gimbiya Lamita a matsayin abokiyar gwamin jarumi Imhal.
Ko da jin wannan suna sai kowa ya Cika da dumbin mamaki, aka sake yin shiru fiye da farko, sai ga gimbiya Lamirat ta fito sanye da bakaken tufafi
rike da takobi da garkuwa a hannunta, kuma ta rufe fuskarta da hular karfe, idanunta kadai ake gani. Hatta takalmin kafarta bakake ne na fata kuma dogayene iya guiwa.
Tunda aka fara wannan gasa kambun jarumta bisa tarihi ba a taba samun mace jarumar da ta shiga ba sai yau.
Ko da aka ga cewa Lamirat ta durfafi inda jarumi Imhal ke tsaye wato da gaske take, fadan zatayi sai aka kaure da shewa aka rinka yi mata tafi da jinjina.
Shi kuwa jarumi Imhal sai ya kura mata idanu kawai yana yi mata murmushi mai nuna tsantsar soyayya. Hatta gimbiya Shumaira dake zaune a cikin yan kallo sai da kishi ya turnuke ta sakamakon ganin irin kallon da jarumi Imhal ke yiwa Lamirat.
Kai tsaye Lamirat tà ci gaba da durfafar inda imhal ke isaye har sai da ta iso daf da shi yadda suna iya jin numfashin juna sannan ta dubeshi ta ce ya kai abokin gaba ina mai shawartarka da ka tsaya kayi yaki da ni bil hakki, yaki irin na abokan gaba, kada ka kuskura ka tausaya mini don kana sona domin ni rayuwarka kadai zan nema.
Sa'adda jarumi Imhal ya ji wannan batu sai ya yi murmushi ya ce, tabbas ba zan yi yaki da ke da wasa ba, amma kuma ba zan yi miki raunin da zai yi miki illa ba, kuma ba zan nemi rayuwarki ba. Shawarar da zan ba ki ita ce ki yi amfani da duk irin shawarar da zan baki a yayin da muke cikin wannan gumurzu idan har ba kya so ki mutu ki bar mahaifinki a cikin mummunar bakin cikin da zai iya zama sanadin ajalinsa.
Ko da Lamirat ta ji wannan batu sai ta murtuke fuskarta duk da cewar fuskar ta a rufe take cikin hular karfe ta ce, babu yadda za a yi makiyi yayi amfanı da shawarar makiyinsa. Ni da kai kowa ta sa ta fissheshi.
Ko da gama fadin hakan sai Gimbiya Lamirat ta ja da baya ta gyara tsayuwa, irin tsayuwar fara gumurzu.
Ba tare da 6ata lokaci ba aka buga tambarin fara fada, sai filin ya kaure da shewa a lokacin da Lamirat ta ruga izuwa kan Imhal suka kacame da
azababben yaki ya zamana cewa suna kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama, juriya da bajinta. Banda sautin haduwar takubbansu da na ihun yan kallo babu abin da kunne ke ji.
Sai da suka shafe sama da sa'a guda suna wannan bakin artabu amma dayansu bai samu nasarar ko da kwarzanar jikin dayan ba.
Al'amarin da ya sa 'yan kallo suka, kosa kenan đomin ya kamata ace a tsawon wannan lokaci ma an gama gasar amma sai gashi kamar ma yanzu aka fara.
A daidai wannan lokacin ne jaruman gasar suka ja da baya da kimanin tazarar taku uku uku, suka yi cirko cirko suna haki da kallon juna kamar zakaru. Ga shi dai duk Su biyun suna haki amma a jikinsu babu alamar gajiya saboda tsananin horon da suka samu.
Gaba daya mutanen dake cikin wannan filin gasa sunyi matukar mamakin irin karfin damtse gimbiya Lamirat da kuma iya yakinta to amma da suka tuna cewa ta kasance yar sarki Gurzalu sai suka ga cewa ai tasha a nono ne, don haka babu mamaki dan tayi wannan bajintar.
Kamar hadin baki sai gimbiya Lamirat da jarumi Imhal suka rugo da gudu izuwa kan juna a lokaci guda suka sake kacamewa da azababben yaki a karo na biyu amma wannan karon sai suka sauya salon fadan suka hada da naushi gami da bugun juna.
Abin da ya daurewa kowa kai shi ne kowannansu yana shanye naushi da bugun da ake yi masa tamkar jikinsu ba na jini da tsoka bane, nan da nan suka hadawa kansu jini da majina.
Ana cikin haka ne Lamirat ta shammaci jarumi Imhal ta doki kafarsa wacce ta karye jiya da karfin gaske. Saboda tsananin zafi da zogin da yaji bai san sa'adda ya kurma ihu ba kuma ya durkushe kasa bisa guiwarsa guda.
Damar da ta samu kenan ta kawo masa wawan sara a wuya. Cikin zafin
nama Imhal ya sunkuya ya kaucewa saran, takobin ta ta sari iska. Kafin ta juyo ta kawo masa wani harin tuni ya yi katantanwa a kasa ya fyali
kafafunta da kafarsa lafiyayyiyar, ai kuwa sai ji tayi tayi sama ba shiri ta fado kasa tim, kanta ya bugu da kasa, ta kasa mikewa da sauri.
Duk wanda yake wannan wuri yaga Cewa jarumi Imhal ya sami babbar dama a wannan lokaci da zai kaiwa Lamirat sara ko suka da takobinsa ya halakata amma sai ya ki. Kawai sai ya yunkura ya mike tsaye da kyar yana dingishi.
Ko da yay nufin taka kafar tasa sai ya ji ya kasa, take ya gane cewar sake
karyewa ya yi a kafar sakamakon dukan da Lamirat tayi masa. Kawai sai ya yi sauri ya kama rigar jikinsa ya tsargeta ya daure kafar tamau ya tsaya cak a inda yake yana mai dada gyara tsayuwarsa da jinjina
garkuwarsa yana kallon Lamirat kuma yana kallon jama'a yana sa ran ko yau ma za a taimaka masa a jeho masa itacen da zai gyara kafarsa amma sai ya ji shiru.
Gimbiya Lamirat ta mike tsaye tana nishi, ko da taji zogi da radadi yayi yawa a keyarta sai ta cire hular kwanon dake kanta ta shafo keyar, ai kuwa sai taji danshi a hannun nata tana dubawa taga jini mai dan yawa. Al'amarin da ya dugunzuma hankalinta kenan kuma ya fusata ta ainun domin a iya saninta babu wani jarumi da ya taba ji mata rauni babba haka ko da kuwa mahaifinta a duk sa'adda suke gumurzu.
Cikin sauri Lamirat ta cire wani kyalle da ta đaura a gashinta mai dauke da hatimin gidan sarautarsu ta daure raunin keyar ta ta don tsaida jini, sannan ta juyo ta fuskanci jarumi Imhal suka fara kallon kallo, kowannansu na nazarin ta yadda zai 6ullowa abokin gwaminsa.
Bayan kamar dakika arba'in suna yin wannan kallon kallo sai Lamrita ta sake rugowa izuwa kan Imhal suka kacame da sabon masifaffen yaki.
Shi dai Imhal a waje daya yake yaki bai motsa ko ina ba da taku daya amma ita Lamirat zagayashi take tana kai mashi sara da suka ta ko ina.
Babu abin da zai burge mutum sama da yadda Imhal ke kare duk hare haren da Lamirat take kai masa ta bayansa ba tare da ya waigo ba.
Al'amarin da ya yi matukar burge kowa kenan aka rinka yiwa Imhal tafi da
jinjina.
A daidai wannan lokaci ne Lamirat ta fuskanci cewar lallai kafar Imhal ta sake karyewa ba zai iya yin kyakkyawan motsi daga inda yake ba, saboda ta kurawa kafar idanu da kyau ta ga harma ta fara kumbura. Ko da ganin haka sai farin ciki ya turnuke Lamirat tayi dan guntu murmushi na farin ciki.
Nan fa ta ci gaba da kaiwa kafar tashari, kokarinta kawai shine ta lalata ta amma sai ta kasa taba kafar, saboda shima jarumi Imhal ya dage iya karfinsa waje kare kansa.
Ko da yaga ta dage iya karfinta tana son lallai ta lalata kafar tasa sai shima ya shammaceta ya gabza mata wawan naushi a mukamukinta na hagu. Take Lamirat tayi katantanwa sau uku a tsaye saboda karfin naushin, a lokacin da numfashinta ya d'auke ta sulale kasa.
Maimakon Imhal ya yi amfnai da takobinsa ya sareta sai ya yi jifa da
takobinsa ya shake Lamirat a wuya da hannunsa, amma a badini ba shaketa yayı ba jira kawai yake ta dawo cikin haiyacinta ya yi mata rada a kunne.
A daidai wannan lokaci ne gaba dayan jama'ar dake filin suka mimmike
tsaye, bakunansu a bude kawai suna jira su ga Imhal ya yi jifa da gawar Lamirat.
Shi kuwa sarki Gurzalu a wannan lokaci gabadayan jikinsa sai ya kama tsuma, idanunsa sun kada sunyi jawur saboda tsananin bakin ciki, kawai ji yake kamar ya zare takobinsa ya ruga izuwa cikin filin gasar ya ceci rayuwar yarsa amma sai ya kasa bai san sa'adda ya kama kujerar da yake zaune a kai ba da hannunsa guda ya matseta ba. Kasancewarsa sadauki kawai sai kujerar ta farfashe amma saboda hankalin kowa na kan jaruman gasa babu wanda ya ga barnar da ya yi.
Ko da Imhal ya ji Lamirat ta yunkura zata cire hannunsa daga wuyanta sai ya yi sauri ya yi mata rada a kunne. Faruwar hakan ke da wuya sai ya murđe mata wuya ya yi jifa da ita kasa, ko shurawa bata yi ba.
Nan fa filin ya kaure da shewa aka rinka yiwa jarumi Imhal jinjina. Duk da
cewa sarki Taryan ya san cewa ya sami riba mai dumbun yawa a wannan gasa sai ya kasa yin murnar komai domin hankalinsa ne ya dugunzuna ainun bisa ganin mutuwar yar abokinsa wato gimbiya Lamirat.
Shi kuwa sarki Gurzalu sai ya mike cikin tsananin sanyin jiki, hawaye nata kwarara daga cikin idanuwansa ya nufi cikin filin gasar ya isa inda Lamirat take kwance ya sunkuya ya cicci6eta. Yana daga kai ya hada idanu da jarumi Imhal, sai yaga yana yi masa murmushi.
Abin da ya kara fusatashi kenan ya ce a ransa ya mutum zai kashe mini yata guda daya jal a duniya kuma ya yi mini murmushin mugunta.
Nan take Gurzalu ya ji ya tsani Imhal fiye da koyaushe a rayuwarsa. Nan da nan ya rungume Lamirat a kirjinsa ya fice da ita daga cikin filin gasar.
Shi kuwa jarumi Imhal sai ya kasa motsawa daga inda yake, sai da aka zo aka daukeshi, likitoci suka bishi da gudu Izuwa cikin gidan sarautar domin su yiwa kafarsa magani.
Al'amarin sarki Gurzalu kuwa kai tsaye ya nufi cikin turakarsa dauke da yarsa Lamirat a matsayin gawa. Yana isa kuryar turakar sai ya janyo kofar ya rufe sannan ya kankame Lamirat a kirjinsa ya fashe da matsanancin kuka kamar ba zai daina ba har abada.
Yana cikin wannan hali ne kwatsam sai yaga Lamirat ta dago kai ta kalleshi tana murmushi. Saboda tsananin kaduwa bai san sa'adda ya saketa yana mai ja da baya ba. Sai da yaga ta kara matsowa gareshi ta kama hannunsa guda ta sumbata kamar yadda ta saba yi masa kullum da koyaushe sannan ya gamsu cewar lalali 'yarsa ce ba aljana ba ce.
Cikin tsananin mamaki sarki Gurzalu ya dubeta ya ce, ya ya aka yi kika sake rayuwa alhalin a gaban idanuna jarumi Imhal ya karya miki wuya ya yi jifa da gawar ki?
Koda jin wannan tambaya sai Gimbiya ta yi murmushi ta ce ai bai karya mini wuya ba, kawai ya nunawa 'yan kallo ne kamar ya karya mini wuyan
domin a dauka cewar kasheni ya yi. Ya kai Abbana kayi sani cewa a cikin wannan gumurzu da mukayi sau uku jarumi Imhal ya sami damar hallakani amma sai ya ki. Ba don komai ya kasa kasheni ba sai saboda ya kamu da tsananin sona tun a ranar da ya fara yin arba da ni.
Maganar gaskiya na shiga wannan gasa ne da nufin na kashe jarumi Imhal domin na kawo karshen fargabar dake Zuciyata dangane da hadarin rayuwarsa a garemu a doron

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment