Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shekaru ashirin wannan gida yana nan kamar yadda yake a yanzu
.
Boka daulakaki shi ya gina wannan gida da karfin tsafinsa, yana zaune ne shi kadai, amma yana da mata da wani dansamai suna ihimuzussam ma yaro ne dan shekara goma da haihuwa
.
Babban dalilin daya sa boka daulakaki ya baro cikin kasar yamzin ya dawo kan wannan dutse shi ne .
Akwai wata rana da sarki badalaki yasa boka daulakaki yayi amfani da karfin bokancinsa ya tara masa wata dukiya mai tsananin yawa,
.
Shi kuwa boka daulakaki yaya nunar wa sarki cewar hakan ba zata taba yiwuwa ba, sai kuwa sa'insa ta shuraih Usman inkiya 99% kuduru a tsakaninsu har daga karshe sarki badalaki ya kori boka daulakaki daga cikin kasarsa
.
Ya kuma yi masa gargadi akan cewa bashi ba sake shigo masa kasa muddin bazai biya masa wannan bukata tasa ba, haka kuwa akayi, boka daulakaki yabar kasar yamzin , amma kafin yabar kasar ya dawo asaman wannan dutse daya gida wannan gida
.
Ya nemi alfarma a wurin sarki badalaki akan yabar iyalinsa suci gaba da rayuwa acikin kasarsa kasancewar shi kadai ne ya aikata masa wannan laifi, haka kuwa akayi
.
Bayan wasu yan shekaru sai sarki badalaki ya tsokano wani babban sarki mai girman sha'ani, wanda ake kira da suna sarki dawur ibni zaujainun.
.
Sarki dawur ya kasance tsara a cikin sarakunan duniya ,babu wanda bai san irin tsananin zalunci da rashin imaninsa ba , yana da runduna mai tsananin yawa masu zafin shuraih Usman inkiya shuraih 99% zafin nama da juriya a fagen yaki, sannan yana da eundunar bokaye wadanda suka shahara a duniya, atarihinsa ma ance duk inda yaje labarin wani hatsabibin boka daya gagara
Sai yaje wurinsa yabashi dukiya mai tarin yawa yazo ya zauna tare da shi.
.
Ran sarki dawur ya matukar baci ganin cewa yafi karfin sarki badalaki a kowanne fanni, don haka sai ya taho da rundunar yakinsa ya sauka a bayan kasar yamzin suka kacame da wani azababben yaki mai matukar tayar da hankali.
.
Wannan kazamin yaki da aka buga tsakanin sarki dawur da sarki badalaki sai ya kasance darki badalaki yayi dana sanin tsokano sarki dawur dayayi, akarshe sai da aka kashe shi da gaba dayan dakarunsa.
.
A karshe ma sai da sarki dawur ya shiga har kasar yamzin yana ta kashe mata da ka nanan yara sai ya zamo babu sauran mai numfashi a kasar face Shuraih Usman inkiya 99% ihimuzassam daya boye a wanin sako da basu ganshi ba.
.
Alokacin da wannan yaki ya kaure boka daulakaki baya nan yayi wata gagarumar tafiya lokacin daya dawoo ya tarar da cewa an rusa kasar yamzin kuma an kashe matarsa sai dan ne yayi saura , sai ransa ya yi matukar baci,
.
Take ya shirya ya tafi ga sarki dawur suka gwabza yaki mai tsanani, inda a karshe da kyar ya kwaci kansa, bayan kwanaki uku sai ya mutu agaban dansa ihimuzussam
.
Amma kafin ya mutu sai daya damkawa wa dansa jakar bokancinsa ya umarcesa daya gudu yabar kasar
Haka kuwa akayi , bayan shekaru shida ihumuzussam ya wanzu yana mai karanta duk wata takarda daya gani a cikin jakar bokancin mahaifinsa,
.
Daya kalleta sau daya sai kawai yaji ya hardace gaba dayanta, sannu a hankali, sai ihimuzzassam , ya zamo shuraih Usman inkiya 99% kasurgumin matsafi mai girman sha'anin da babu kamarsa a gaba dayan nahiyarsu
.
Da ihumuzussam ya fahimci ya samu wannan matsayi da daukak, sai ya kulla gaba da duk wani mahulukin dake zaluntar na kasa dashi,
Yana mai matukar jin haushi, da tafiya tayi tafiya sai ihimuzussum ya rika bi kasa kasa yana yakar azzalumai yahar sai da ya zamo cewa duk bokaye da matsafa suna boye kansu da fadar cewa su ba bokaye bane, izan su kayi gaba da gaba da ihumuzussam, shi kuwa sai yai wani tsafi duk inda ma'abocin tsafi yake kawai sai dai yaga ihumuzussam a gabansa, sannan ya halaka shi
.
Har ta kai babu wani mai ilimin bokanci da yai saura sai shi kawai a duniya
.
Tun daga ranar da ihimuzussam ya gama da bokaye da manyan sarakuna da takurawa na kasa da su, sai gaba dayan Shuraih Usman inkiya 99% mutane suka samu saukin zaluncin dara shin imani da ake nuna masu
.
Har ya zuwa lokacin da ihimuzzusam tsufa ya kamashi ya kasance baya iya zaga duniya domin ya kai agaji ga marasa karfi da ake zalunta
.
Saboda haka ne sai ihimuzzassum ya tattara gaba daya duk ilimin bokancinsa ya sana'anta wannan hatsabibin zobe na zinari yakai shi kogon darul yamzin anda ya riga ya san cewar koda bayan ransa babu wanda ya isa ya tunkari kogon bare yayi yunkurin mallakarsa komai hatsabibancinsa da shahararsa a duniya
.
Lokacin ihimuzussam ya mutu sai gaba dayan sarakunan duniya suka rika kokarin ganin sun mallake shi ya zama nasu saboda sanin cewa, duk wanda yake rike da wannan zoben dukkan mutane da aljanun duniya zasu zamo a karkashin ikonsa sai yadda yace za'yi
.
Hakika da yawa daga manyan sarakuna sun salwanta shuraih Usman inkiya 99% an gwabza kazamin yaki milyoyin mutane sun rasa rayuwarsu akan wannan hatsabibin zobe na zinari
.
Lokacin da zabbabu yazo nan a zancensa ,sai ya dubi huzainu yace da shi.
"Ya huzainu ka sani cewa kafin dawwara ya tafin yayi shirin zuwa kogon darul yamzin daukoo wannan zobe, sai da yahada wani tuggun da yayi sanadiyar rasa rayuwar mahaifina.
.
Wanda a wannan lokacin ina da shekaru goma sha biyar saboda haka sai aka danka min sarauta na ci gaba da kula da kasarmu har izuwa wannan lokaci da boka gayyar ya aiko da wayannan dakaru suka sato ni da niyyar su halaka ni,
.
Ka sani yakai huzainu a dai dai wannan lokacin dawwara yana kan hanyarsa ta zuwa kogon darul yamzin domin ya samu sa'ar dauko hatsabibin zoben zinari a kokarinsa na ya halaka duk wanda yake sarauta a kasar zayyar
.
Shuraih usman inkiya 99%. Koda zabbabu yazo nan a zancensa, sai gaba dayan kasar wurin ta dauki raurawa ta girgiza kamar zata kife, daga bisani kuma sai kasa taci gana da darewa wata guguwa mai tsananin karfin gaske ta ci daukar abu marar nauyi tana mai yin wurgi da dashi,
.
Bayan kamar kimanin dakika hamsin, sai komai ya daidaita , kawai sai ganin zuhaisa sukayi agabansu.
Zuhaisa ta kyalkyale da dariya tace da huzainu
.
"Hakika yakai huzainu kasani gani nazo a gareka cikin yanayi na ba zato da shammata. Kamar yadda na sha fada maka a baya, bani da wani makiyi a duniyan nan daya wuce kai, na tsani duk wani cigaban rayuwarka, kuma na dade da cin alwashin ganin ka daina numfashi.
.
Na zamo ni ce nayi sanadiyar mutuwarka, saboda haka ne nazo a .............
Toh jama'a sai fa anyi hakuri don fallen littafin na karke ya balle
.
Anan muka kawo karshen littafin RANA da WATA na daya sai kunjini a littafi na Biyu nan da kwana biyu
Marubucin yace
.
SHIN TSOHUWA SHAFHILA ZATA SAMU NASAR ISA KOGON DARUL YAMZIN KUWA?
.
A TSAKANIN ZUHAISA DA HUZAINU SHIN WAYE ZAI SAMU NASARAR KASHE DAN UWANSA
.
SHIN DAWWAR ZAI SAMU NASARAR DAUKO ZOBEN ZINARI A KOGON DARUL YAMZIN KUWA
.
INA LABARIN DAJIN MAYUN DA SU TSOHUWA SHAFHILA sUKA ShIGA?
.
SHIN ZASU TSIRA DA RANSU KUWA??
.
Domin jin karshen wannan littafi sai mu hadu a littafi na biyu,
Tare dani Shuraih Usman
Inkiya Shuraih 99%
Jagoran Typing
Mamallakin shafin hausaebooks
Da keffians News Teller
.
Kar dai ku sha'afa zaku iya download na wannan littafi zuwa kan wayoyinku ta hanyar ziyartarmu a shafinmu na yanar gizo gizo Hausaebooks
.
Sai kunzo
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment