Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake wannan yarinya kin aikata manyan laifuka biyu a gareni. Na farko kin shigo wannan daji ba tare da izini na ba har kika shigo cikin turakata bata re da fargabar komai ba.
Na biyu kkuwa kin furta munanan kalamai masu nuna rauni da gazawa gareni. Lallai zaki dandana tsananin zalunci da ukubata ,
.
Kafin daga karshe na halakaki
..........
Anan zan dakata sai mun hadu a part e
ni dinne dai Shuraih Usman
In kiya shuraih 99%RANA DA WATA
Littafi na daya 1
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih 99%
Post:- Shuraih 99%
Part E

Koda ahakamul bainun yazo nan a zancensa sai ya nuna zuhaisa da sandar da ke hannunsa wani haske mai kamar walkiya ya fito da matsanancin gudu kamar an harba shi akwari da baka
.
Zuhaisa ta zare garkuwarta daga damararta ta yaki ta kare , amma saboda karfin tsafi ahakamu-bainun sai da zuhaisa ta gwaru da bangon dake kogon take kanta ya fashe har ta shafa ta ji jini
.
Al'amarin daya dugunzuma hankalinta kenan , kawai sai ta zare takobi ta tunkari boka ahakamul-bainun a cikin tsananin bacin rai da kunar zuciya , tana zuwa kusa dashi ta daka wani uban tsalle tare da kai masa wani gawurtaccen sara a saitin dokin wuyansa da niyyar ta sare masa kai ta halaka shi.
.
Lokacin da ta sare shi sai taji tamkar dutse ta sara ,amma saboda karfin saran sai da yayi baya taga-taga amma ya turje bai kai kasaba .
.
Ita kuwa zuhaisa sai da takobinta ta subuce ta fadi can nesa da ita boka ahakamul bainun ya bushe da dariya ya dade yana yi kamar bazai daina ba har tsawon dakika sittin sannan ya daure fuska kamar bai aba fara'a ba .
Take ya nuna ta da dan yatsansa manuniya, sai ya kuma nuna wani sashi na kogon dutsen
.
Nan take sai zuhaisa taji kawai ana gwarata aka'ina a cikin kogon ta sume
Boka ahakamaul bainun ya sake bushewa da dariya a karo nabiyu
.
Lokacin da zuhaisa ta farfado daga suman da tayi sai ya kasance ko hannunta bata iya dagawa ,
Al'amarin daya matukar tayar mata da hankali kenan, take sai tay duba zuwa ga boka ahakamul bainun tace da shi "hakika yakai wannan takadarin boka ahakamul bainun wannan al'amari da kayi gareni baya nuna kayi galaba da rinye a akaina saboda ka kasnace boka mai dogaro da bokanci,
.
Ni kuwa na kasance ina mai tsananin takama da karfin damtse . Ka sani cewa muddin muka gwabza yaki da takobi tsakani na dakai tabbas nasan ba zaka wanzu tsawon dakika sittin a gabana ba face nasa takobi na daddatsa ka Ia dai kaman yadda duk wanda yasanka a baya bazan shaida ka ba"
.
Yayin da boka ahakamul bainun yaji wannan batu sai ya sake bushewa da dariya irinta mugunta da zalunci, sannan yace da zuhaisa ido cikin ido "hakika na kasance boka mara tausayi,mugu kuma azzalumi, bana tausayawa kowa hatta mata da yara kana na muddin suka fado a hannuna, tabbas duk mahalukin daya raboni ni nake zama ajalinsa amma a bisa ga tsananin mamakina sai gashi na kin zamo mutum na farko dana kasa hallakawa farat daya
.
Kar dai ku manta kuna tare ne da Shuraih 99%
.
Haka nan sai naji a jiki na ba zan iya kasheki ba na kasnace ina jin wani abu yana min yawo a zuciyata, wannan dalili ne yasa na tsananta bincike a gareki,
.
Sai daga karshe na gano na kamu da tsananin sonki da kaunarki a zuciyata saboda tunda nake arayuwa ta ban taba gani ko jin labarin mace mai tsananin kyau da cikar halitta sama da ke ba .
.
Al'amarin daya hanani kashe ki farat daya a lokacin dana fara ganinki wannan dajin tun sa'adda kika fara kusanto inda nake
.
Koda boka ahakamul bainun yazo nan a zancensa sai ya nuna zuhaisa da dan yatsa, take sai dukkanin karfin jikinta ya dawo gareta har ta mike tsaye tayi taku biyu daga inda take .
.
Kuma a sannan ne ta dubi boka ahakamul bainun tana nazarinsa boka ahakamul bainun ya kasance kato ne gajere mummuna yana da katon kai kamar wani dutse, fuskarsa cike da take da farin gashi, kuma ya kasance baki ne sidik
.
Zuhaisa ta kuduri yaudara acikin zuciyarta muddin zata samu nasarar biyan bukatarta a gareshi, take sai ta dubeshi cikin kisisina tana mai cewa dashi "ya kai boka ahakamul-bainun ka sani cewa na samu labarinka acan baya wurin wasu mutane, suka sanar dani al'amarinka na yadda ka gagari manyan sadaukai da jaruman wannan nahiya , lamarin daya kwataitar dani kenan naci alwashin sai na kawo kaina a gareka, mu kasance tare domin biyan wata muhimmiyar buka tata"
.
Sa'adda zuhaisa tazo nan azancenta sai tayi murmushi irin wanda ke janye hankalin duk wanda yake kallonta .
.
Boka ahakamul bainun ya dada kwadaituwa da zuhaisa anan take ma sai ya bude baki galala yana kallonta ita kuwa ta fahimci haka sai ta matsa kusa da shi tana karairaya har tasa hannu ta shafa krjins.
.
Al'amarin daya sa boka ahakamul bainun kenan ya kurma ihu don dadi da shagaltuwa da wannan al'amari anan take ma sa ya budi baki yace da zuhaisa
.
"Yake wannan yarinya ma'abociyar kyawu da cikar halitta , maza sanar dani wace ce ke, daga ina kika fito da har kike neman hadin kaina akan wata bukata ta ki?"
.
Yayin da zuhaisa taji wannan batu sai ta sake kallon boka ahakamul bainun sannan ta soma da cewa " sunana zuhaisa bin zubgainu, mun kasance mu biyu ne ga mahaifiyarmu , un kafin a haifemu babanmu ya mutu, lokacin da aka haifemu ni da dan uwana mai suna huzainu sai ya kasance duk duniya bani da wani buri face naga na hallaka shi da kaina
.
Tun sa'addda muka girma nake ta faman farautar rayuwarsa domin ganin na
[Jama'a ayi hakuri don kuwa fallen wajen ya yage Shuraih 99%]
.
Bayan huzainu ya gama shiryawa sai kawai ya dane kan wani ingarmar dokinsa ya zabureshi ya faa tafiya har ya fito daga cikin kasarsu zaibalatu.
.
Yaci gana da tafiya yana wanda shi da kansa bai ma san inda ya nufa ba duk kauyuka da kananan garuwan dayake haduwa da akan hanyarsa sai ya shiga yana mai tambayar mutanen koda za'a sami wani wanda yasan inda take ko jin labari game da ita ,
.
Sannu a hankali har ya fita daga wannan nahiya tasu gaba daya ba tare daya samu wanda yasan komai akan mahaifiyarsa shafhila ba
.
Kwatsam ba zato ba tsammani sai huzainu yaga wani matashin saurayi yana yakar wata rundunar yaki da wani gawurtaccen jarumi yake jagoranta
.
Mayakan suna kokarin halaka wannan saurayi a halin gajiya saboda tsananin yawan mayakan da suka taru suna yakarsa shi kadai
.
Koda ganin haka sai huzaini ya kwadaitu daya taimaka ma wannan saurayi dake yakar wannan runduna . Nan take huzainu ya dakawa rundunar yakin wata tsawa da dukkanin karfinsa muryarsa
.
Lamarin daya sa kowa ya karkato da hankalinsa zuwa gareshi sai kawai huzainu ya zare takobinsa tare da kutsawa tsakiyar mayakan yana saransu da tsananin zuciya mai karfin gaske .
.
Koda ganin haka sai shima wananna saurayi yaji wani sabon karfi ya shige shi , take yaji kamar a sannan ne aka fara wannan yaki suka hadu su biyu suna masu farauce rayuwar duk mai tsautsayin daya fado a agabansu
.
Wohoho! Masu iya magana suna cewa mai son yayi kuka ne aka jefeshi da kashin awaki ,
Nan take wani sabon azababben yaki ya kacame a tsakaninsu huzainu ya wanzu yana mai tsananin farauce rayuwar wadannan mayaka , duk inda ya juya sai dai kaga yana tsarge mutane gida biyu haka nan shima wannan saurayi ya kasance sadauki ne mai karfin damtse da juriya , yana aikata mummunana kisa ga wadannan mayaka kamar yadda yaga huzainu yana aikatawa gare su
.
Cikin sa'a daya sai gashi sun halaka fiye da kaso biyu daga cikin kaso biyar na wadannan mayaka lokacin da wannan jarumi mai jagorantar runudunar ya fahimci wannan ta'asa ta huzainu da kuma wannan saurayi , sai ya fusata , nan take ya zare takobi tun ma daga nan inda yake zaune akan dokinsa yayi wata alkafura sai gashi yana juyi a sama sai gashi ya dira a bayan huzainu yasa takobinsa dake hannusa ya saro huzainu da dukkanin karfisa
.
Sai da kaifin takobi ya samu nasarar keta karfen dake bayan huzzainu yaji masa ciwo , har ya shige shi, jini yai tsartuwa a inda aka sareshi,
.
Take sai huzainu ya fado daga saman dokinsa saboda tsananin karfin saran da akayi masa bayan ya mike tsaye ne sai kawai ya juyo da baya da nufin yaga wanene yayi masa wannan sara haka cikin shammata da bazato lokacin da huzainu yaga ashe jarumin dake jagorantar wannan runduna ne
.
Take sai ransa ya baci fiye da sa'adda aka fara wannan gumurzu
.

Suka kurawa juna, idanu cikin nazari da jin motsin juna, lokaci daya suka yi kukan kura suka afkawa juna da sara da suka cikin tsananin zafin nama da jarumta
.
Sai da suka shafe fiye da rabin sa'a suna wannan azababben gumurzu ba tare da dayansu ya samu sa'ar raunata daya ba
.
Yauwa anan zan tsaya
Kuyi hakuri da yanayin posting din wlh bana samun lokaci ne
.
Naku akullum shuraih 99%
Friends kui hakrui yau ban yi posting da wuri ba
Wallahi bani da lafiyane
Yanzu ma na dan ji sauki ne shi isa na shigo
RANA DA WATA
Littafi na daya 1
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih 99%
Post:- Shuraih 99%
Part F

Bisa ga rashi sa'a sai huzainu ya taka gawar wani sadauki da aka kashe
Ya zame ya subuce tare da faduwa a kas takobinsa ta subuce daga hannunsa
.
Koda ganin haka sai jarumin yayi dariya irinta mugunta da zalunci, sai kawai ya daka wani uban tsalle da niyyar ya taushe huzainu yasa takobin dake hannunsa ya sare masa kai ya halaka shi
.
Huzainu yayi saurin yin alkafura da barin wannan waje , aikuwa sai wannan jarumin ya fada akan wannan gawa mashin da yakashe sadaukin , shima yayi ajalinsa
.
Koda sauran mayakan da suka rage suka ga huzainu ya samu nasarar kashe shugabansu sai kowannensu ya ranta ana kare
.
Suka tsere faruwar wannan al'amari ke da wuya sai waannan saurayi ya rugo a guke ya rungume huzainu yana mai masa jinjiana da bisa ga wannan nasara da ya samu . Ya kuma yi masa godiya bisa ga taimaka masa da yayi huzainu ya dubi saurayin yace da shi
.
[Ni dinne dai shuraih 99% ke cewa daku
"Yakai wannnan saurayi maza ka sanar dani labarinka da abinda yasa wadannan mayaka suka taru akanka da niyyar suyi maka kwab daya su halaka ka"
.
Koda wannan saurayi yaji wannan batu sai ya fara magana yana mai cewa .
.
"Su nana zabbabu ibini wargis, ni dan asalin kasar zayyar ne na gaji sarauta a wajen mahaifina sarki wargis . Wadannan mayaka da ka gani dawwara da boka gayyar ne suka turo su , suka sato ni bisa yaudara suka kawo ni wannan waje da nniyyar su halakani
.
Tsananin gaba da kiyayyar dake tsakani na da dawwara ya samo asaline tun mahaifina sarki wargis suna kanana shi da dawwara,
.
Wanda a wannan lokacin kakana sarki dakiru shine sarki a kasar zayyar , dawwara ya kasance dan riko ne ga sarki dakiru ya rikeshi amana yadda har da yawa daga mutanen kasar sun dauka cewa sarki dakiru shi ya haifeshi saboda tsananin soyayyar da ya nuna masa, ko wargis baya nuna mawa
.
Shuraih 99% ke cewa
Wata rana mahaifina wargis wata gagarumar tafiya ta kamashi , yai shirinsa tsaf ya gabata a gaban sarki dakiru bayan yayi gaisuwa ya fara magana da cewa
.
"Ya abbana ina mai neman izni a gareka daka amince min na ziyarci babban aminina jarumi abasul-saidanu da zaune acan kasar turkiyya , kasancewar ya dade yana zuwa har wannan kasa tamu yana ziyara ta,
.
Amma ni ko saau daya ban taba zuwa naga mahaifansa ba. Akan wannan daliline nake neman izininka ya mahaifina"
.
Koda sarki dakiru yaji wannan batu sai yayi murmushi yace da shi.
.
Kuna tare ne dai da shuraih 99%
"Maza ka shirya nayi maka izni kaje ka gano shi, har ma kace ina gaida shi.
Sannan kaje bital malika debi dukiya mai tsananin yawan gaske wanda zaya isheka sa'annan ka tafi da dakaru dari biyu suyi maka rakiya a wannan tafiya taka
.
Amma kuma shin ba da danuwanka dawwara zakuyi wannan tafiya ba ne?"
.
Yayin da wargis yaji wannan batu sai ya sake dukawa a gaban sarki yana cewa
.
"Ka sani ya kai abbana, lokacin dana tuntubi dawwara daa zancen tafiyar nan sai ya ke shaidamin cewa , bashi da lafiya baza ya iya raka ni ba a wannan tafiya tawa,
.
Sai dai yana maiyimani fatan alkhairi har naje na dawo
"Koda sarki dakiru yaji haka sai ya mike tsaye batare daya shirya ba jikinsa ya dauki kakkarwa gashin jikinsa ya mimmike ya dubi wargis yace dashi.
.
Shuraih 99% ke typing
.
"Kasan da cewa dawwara bashi da lafiya kayi shiru baka sanar dani ba tun farko?"
Batare da ya saurari komai daga bakin wargis ba ya fita daga fadar ya shige cikin gidan sarauta,
.
Da shigarsa bai zame ko'ina ba sai dakin dawwara ya tarar dashi kwance magashiyyan rai a hannun Allah
.
Tun daga wannan rana ne sarki dakiru ya kasnace yana makale da dawwara har ya kwashe kwanaki arba'in yana jiyyarsa.
.
Lokacin da aka sake kwashe wata daya ba tare da wargis ya dawo gida ba al'amarin da ya dami sarki da dawwara da duk mutanen kasar kenan
.
Sarki dakiru ya ya tashi yan aike suka je har kasar turkiyya suka samu jarumi abbasul-saidanu suka sanar dashi abunda yake faruwa. Jarumi abasul saidanu ya tabbatar musu da cear Wargis fa baizo wannan kasar ba.
.
Lokacin da wannan sako yazo kunnen sarki dakiru [shuraih 99% nedai har wayau]sai hankalinsa ya dada dugunzuma fiye da farko , sai kawai ya baza yan aike a dukkanin wannan nahiya tasu da sauran kasashen dake nesa dasu domin samo wani labari game da dansa wargis
.
Bayan watanni uku sai dakiru ya kwanta ciwon ajali , a haka sai da sake share kwanaki tara ciwo na cinsa , sannan ya mutu
.
Al'amarin daya jefa dawwara cikin tashin hankali da matsananciyar damuwa kenan, har ma akwai lokacin da dawwara yake yin ihu da kururuwa yana mai cewa "na bani na lalace , ayau na rasa gatana, shi kenan nayi sallama da duk wani jin dadi a duniya kaicona!!!"
.
Daga nan sai ya kama buga kansa da bango yana mai yin ihu da iface iface
.
Bayan mutuwar sarki dakiru sai manyan yan majalisar sarki dakiru suka yanke shawarar nada dawwara daya zamo sarki a garesu
.[Karfa ku manta kuna tare ne da shuraih 99%]
Tun da waragis haryanzu bai dawo gida ba, kuma sunga dawwara shi yafi kusanci da sarki tunda har a wani lokaci yafi nuna soyayyarsa akansa fiye da dansa waragis,
.
Haka kuwa akayi aka nada dawwara ya zama sarkin kasar zayyar
.
Kashe gari tunda safe fada ta cika ana ta fadanci sai ga wani mutum ya shigo fadar ya dika gaban sarki ya kwashi gaisuwa, sannan ya fara magana yana mai cewa
"Yakai sarki dawwara ina mai neman izni damu kebe ina da magana"
Nan take wani dokari ya daka masa tsawa da niyyar ya dakatar da shi bisa ga aniyarsa
.
Sai sarki dawwara ya umarci wannan mutum da su kebe din
Bayan sarki dawwara da wannan mutum sun koma inda babu wanda zai jiyo abinda zasu tattauna akai sai mutumin ya bushe [har ila yanzu dai nine nan Shuraih 99%] da dariya ya dade yanayi kamar bazai daina ba.
.
Sai dayayi mai isarsa sannan yayi tsagaita har ya dubi sarki dawwara yace dashi
"Hakika yakai sarki dawwara bukatarka ta biya , saura tawa bukatar ya rage, shin yanzu menene abunyi?"
Lokacin da sarki dawwara yaji wannan batu sai ya dubi mutumin yace da shi
"Ya boka gayyar , ka sani na riga na tanadar maka duk dukiyar da kake bukata, sannan zan nada ka daka zamo wazirina " koda boka gayyar yaji wannan batu sai ya sake kyalkyalewa da dariya yana mai kyakyatawa har zuwa wani lokaci mai dan tsawo.
.
Al'amarin wargis da dakarun dake tare dashi kuwa lokacin da suka yi nisa sosai suna tafiya ba dare ba rana kwatsam sai ga wata guguwa mai tsananin karfin gaske ta mamayesu,
.
Bayan [nidinn e dai Shuraih Usman inkiya shuraih 99%] wannan guguwa ta wuce sai kuwa wargis ya duba sama ko kasa babu abokan tafiyarsa, wannan al'amari ya daure masa kai zuwa can kuma sai boka gayyay ya bayyana kafin wargis ya zare takobi kawai sai boka gayyar ya huro masa wani farin haske bayyana tare da shiggewa a cikin hancin wargis.
.
Take sai wargis ya some sai boka gayyar ya bace yana mai kyakyata dariya
.
Daga nan wargis bai kara sanin halin da yake ciki ba , sai bayan shudewar dakika dari da hamsin , sai kawai ya samu kansa a wani katon gida na alfarma, yayi niyar tashi zaune ,sai yaji ya kasa koda motsa hannunsa,
.
Al'amarin daya sa hankalinsa ya dugunzuma kenan sai ya kasance yana mai sauraron abinda zai faru da shi
.
Bayan kimanin shudewar sa'a daya sai wargis ya rika jiyo wani kamshi yana dada kusantowa inda yake zuwa [shuraih usman A K A 99%] wani dan gajeren lokaci sai wata kyakkyawar budurwa ta bayyana gareshi cikin shiga ta kaya na alfarma, bayan ta samu wuri ta zauna sai ta dubeshi da murmushi sannan tace da shi
.
"Su nana zaitunal-abidina ka sani yakai wannan kyakkywar saurayi na tsintoka ne a cikin daji kana a halin galabita kuma ga dukkan alamu kana are da mutane ma'abota tsafi,
.
Wadanda sune suka yi maka mugun tanadi a kokarinsu na son su halaka ka , bisa ga kiyayewar ubangiji sai gani na bayyana a lokacin da kake neman taimako ta kowacce hanya .
Yakai wannan saurayi ka godewa Allah kasancewar yanzu ka dan fara samun sauki kana da dada warwarewa"
.
Yayin da wannan zaitunal- abidina tazo nan a zancenta sai wargis yaji wannan batu sai yai karfin halin ya fara magana yana mai cewa
.
Toh friends anan
Zan tsaya sai mun hadu bayan kwana biyu
Dafatan kuna jin dadin littafin
.
Shuraih Usman
Inkiya 99% mamallakin shafin hausaebooks da Keffians News Teller
RANA DA WATA
Littafi na daya 1
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih 99%
Post:- Shuraih 99%
Part G

"Yake zaitunal-abidina ,ina mai matukar godya a gareki a bisa wannan taimako da kika yi min , bazan taba mantawa da ke a agaba dayan tarihin rayuwata ba.
.
Kuma zan kasance tare da ke har izuwa lokacin da zan samu sauki na dada samun kwarin jikina sannan"
.
Zaitunal-abidina ta kasance ita kadaice zaune a wannan kasaitaccen gida gaba dayan iyayenta da duk danginta sun rasu,
Asalin zaitunal-abidina da mahaifanta yan asalin kasar zargayunu ne,
.
Yaki yaci kasar su aka kashe gaba dayan mutanen kasar,sai mahaifinta ne da mahaifiyarta da kuma ita a wannan lokacin tana karama bata iya sanin komai game da lamarin duniya
.
Tun daga wannan lokacin ne wargis ya kasance tare da zaitunal abidina har [shuraih 99% ke typingg
Tsawon shekara daya wanda wannan lokaci wargis ya wartsake garau, sai ya bukaci zaitunal-abidina da ta aure shi kasancewar ita kadaice yanzu tayi saura a gaba dayan danginsu
.
Haka kuwa wannan lamari ya kasance,wargis ya auri zaitunal-abidina, wanda a wannan lokacin wargis ya musulunta, sai da suka sake shafe shekaru biyu sannan wargis hankalinsa ya karkata ya zuwa tunanin mahaifinsa
.
Da dan uwansa Dawwara, shin ko a wane hali suke yanzu?,amsar daya kasa samu kenan a duk lokacin daya tuno da kasarsu zayyar,
.
Bisa dole, wargis ya bukaci zaitunal-abidina da suyi shiri suje kasarsa ta haihuwa domin yaga a wane hali mahaifinsa yake ciki da yan uwanda sa suke da babban abokinsa kuma dan uwansa suke
.
Shuraih usman inkiya 99% jagoran typing
.
Wata rana sarki dawwara yana zaune akan karagarsa ta mulki yana tafiyar da sha'anainsa yadda yaso,kwatsam! Sai ga wargis ya shigo a wannan fada koda ganinsa sai sarki dawwara yai saurin mikewa tsaye hankalinsa ya dugunzuma ,
.
Take jikinsa ya kama karkarwa wata zufa ta karyo masa. Amma sai ya wayance ya tari wargis yana mai nuna tsananin farin cikinsa game da dawowarsa a wannan lokaci da suke nemansa ruwa ajallo
.
Dukkanin mutanen gari babu wanda bai nuna farinciki da dawowarsa ba, sai ma aka balle da wata kwarya kwaryar liyafa ta murnar dawowar wargis gida a bisa jagorancin sarki dawwara,
.
Sai da aka share kwanaki hudu ana wannan liyafa ta karramawa, sannan aka lafa, kuma a wannan rana ne duk yan majalisar tsohon sarki suka hadu tare da cire sarki dawwara suka dora wargis kasancewar shine shuraih usman inkiya 99% dan sarki dakiru daya kamata ace ya gaji mahaifinsa
.
Daga cikin wadanda suka dage ala dole sai an cire sarki dawwara akwai wani matashi wanda suka dade tare da wargis wanda ake kira da Suna mudahir ibini muhutaru
.
Mudahir ya kasance masani ne sosai akan ilimim taurari, yana buga kasa yayi bincike akan kowane irin al'amari idan ya damu al'ummar kasarsu, kasancewar ya gaji mahaifinsa ne ta wannan fanni
.
Kuma dama tun kafin sarki dakiru ya mutu ya dade yana sanar da wargis cewa ya rike mudahir hannu biyu, kuma duk abinda ya sanar da shi yayi gaugawar amincewa da shi, sakamakon mahaifin mudahir ya rasa rayuwarsa.
.
Tun daga wannan lokacin wargis ya dada janyo mudahir ajikinsa yana mai tsananin kula da shi baya son wani abun da zai dameshi shuraih usman inkiya 99%
.
Mudahir shi ya zake akan lallai sai ancire dawwara daga sarki cikin dan kankanin lokaci haka, sannan ya bukaci sarki wargis da su kebe yana son su gana su biyu kawai. Mudahir ya dubi sarki wargis ya fara magana cikin nutsuwa yana mai cewa
.
"Ya sarki wargis, ka sani tunda nake da kai ban taba sanar da kai wani labari da zai tayar da hankalinka ba a gaba dayan tarayyarmu saboda haka nake so kayi nazari a kan abinda zan sanar dakai.
.
Dan uwanka dawwara yana da sa hannu wajen batanka na tsawon dogon lokaci, sannan yana da sa hannu cikin rasuwar mahaifinka sarki dakiru"
.
Yayin da sarki wargis yaji wannan batu , sai ya rikice ya dimauce,hankalinsa ya dugunzuma ba don mudahir ya kasance baya sa baki akan kowanne al'amari akasar ba, da to sai sarki wargis yace yayi masa karya a wannan shuraih usman inkiya shuraih 99% karon don haka sai sarki wargis ya tsananta bincike ya kuma gano lallai dawwara bashi da gaskiya , har ma sai da ya turke kansa
.
Al'amarin daya daurewa sarki wargis kai kenan , hankalinsa ya dugunzuma fiye da ko yaushe , anan take ya tsinewa dawwara ya kuma fada masa cewa babu wata dangantaka da zata sake hada su har abada, amma ba zai taba daukar wani mataki akansa ba
.
Lokacin da dawwara ya isa gida sai ya tattara dukkanin kayansa da iyalinsa ya bar kasar ba tare da sanin kowa ba yana fitowa daga kasar zayyar , sai ya tarar da boka gayyar yana jiran fitowansa ,
.
Koda boka gayyar yaga dawwara awannan lokaci sai ya tunstire da dariya yana mai kyakyatawa, sannan ya dubi dawwara ya ce dashi shuraih usman inkiya 99%
"Mugu shi ya san makwantar mugu"
Nan take boka gayyar ya kurma wani uban ihu, al'amarin daya matukar girgiza dawwara kenan ya dubi boka gayyar ya ce dahsi
.
"Ya boka gayyar shin ina dalilin wannan ihu naka da akayi a wannan lokaci?" Sa'adda boka gayyar yaji wannan tambaya daga bakin dawwara sai ya dube shi yace da shi.
.
"Hakika ya kai dawwara, ka sani akwai wata hanya ita kadaice zaka bi wannan bukata taka zata biya , kuma wannan hanya ta kasance mai tsananin wahalar gaske wadda zaka iya rasa rayuwarka ma akokarin ganin ka mallaki kasar zayyar ka zama sarki
.
Koda boka gayyar yazo nan a zancen sa sai dawwara yace da shi
"Wacce hanya ce wannan , shuraih usman inkiya 99% maza ka fada min ita na rantse da iyayena ba zan gaza ba wajen yin ko menene ake bukata ba"
Boka gayyar ya girgiza kai yace dahsi
.
"Muddin kana so ka zama kasaitaccem sarki da babu kamarsa a wannan nahiya , sai kaje can kogon darul yamzin dake acan karshen birnin sin,ka dauko wani hatsabibin zoben zinari da ke ajiye a dakin baccin dodanniya hujarnun-majnun
"
Koda dawwara yaji wannan batu sai ya kidime ,hankalinsa ya dugunzuma fiye da ko yaushe, sai kawai ya dubi boka gayyar yace da shi
.
"Koda na tsaya ban amince da zuwa dauko wannan zoben ba, nasan halaka zanyiabanza saboda bakin ciki da takaicin abinda sarki wargis yai min, yakai boka gayyar maza ka ka tsumani da tsumi irin naku na manyan bokaye,
.
Na rantse da iyayena sai naje kogon darul yamzin na dauko wannan zobe dyk rintsi da tsanani shuraih usman inkiya 99%

HATSABIBIN ZOBEN ZINARI

A can saman wani katon dutse dake bayan kasar yamfisu akwai wani katon gida akan wannan dutse, tun sama da

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment