Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai tsadan shi wai a raina mana hankali ace kyauta ne aka dauki nauyin ta . Koda ba muyi boko ba ,ai muna da ilimin sanin Rayuwa. Kallon Su Lanti tayi tana Cewa" Lallai kun dade da manta Wacece Lanti , akan mijina zan iya yin komai Wallahi kun Sanni farin sani . Tabbas kun manta irin faɗa na ,don Ni bana cacan baki sai dai cika Aiki , a nawa tunanin a yanzu an girma ne shiyasa nayi Watsi da komai , ashe har yanzu da sauran Haukan Ƙuruciya akawunan mu duka . Bara ina zuwa ....! Tayi maganan tare da juyawa tana nufan Madafin su ( Kitchen) . Ganin haka yasa Jummai kallon Baba Zuwai da Sauran matan Gidan kamin Zuwai tace " Wai mene take shirin yi ne .? .

Cike da sassataccen Gwuwa Jummai tace baya ne zata dawo gaba ai . Motsin fitowan Lanti suka ji daga Madafi nan take Kowa ya kalli inda take tahowa hannun ta dauke da Guggun ice irin manyan iccen nan na jego yana ci da Wuta ,don alamu daga Murhu ta fito dashi , nufo su take kaman Boss wanda tabbas sun san a da baya haka suke faɗan su acikin gidan ,wannan ta dauko taɓarya wannan bakin Wuta wannan bokitin ƙarfe . Wani irin zurawa da Gudu Zuwai tayi nonon ta na dukan ɗaya tana shigewa cikin Ɗaki tare da rufo ƙofa . Haka suma suka Gudu suna yin ɗakunan su babu Wanda ya tsaya . Ku ƙananan yan matsiyata ne ,da kun sani ku tsaya Ni ban iya cacan baki ba ayi aiki a zahiri ne da jiki shine za'a sani .

**
A makarantar Hi Academy an gama tantace Amrah an kuma miƙata zuwa ga Malaman Ajin su Wato Aunty Jamaima wata inyamura nan igbo ce . Nufar Primary 2 tayi da Amrah tana shiga Class tana faɗin " Good morning Class.! Good morning Aunty.." Ɗaliban suka haɗa baki Wurin Gaishe da Aunty Jamima. Kallon Inda Amrah take tayi tana faɗin " Ga sabuwar Zuwa sunan ta Amrah Adaam Ɓaidu . Wow nice name.... your Welcome classmate ( Muna maki Barka da zuwa ) . Sam Amrah bata ji mai suke cewa ba , sai dai bin su da kallo da take yi , Anty Jamima ce tayi mata Wuri A second seat don kowani dalibi seat din shi ,shi kadai ne da wurin aje jaka da Lunching Box . Sabon Rayuwa take ganin kan ta a ciki ,a haka take kallon kowa na Ajin da Ɗaliban ke ta mata Murmushi irin na baƙuntan nan . Tun da Aunty Jamima ta fara masu karatun har ta gama Amrah bata san inda ta dosa ba , a haka ta fita wani malamin ya shigo shima yayi nasa . Third period na fita aka tashi break nan take Yaran Ajin suka nufo wurin zaman Amrah kowa na gabatar mata da kan shi da turanci ,ta ɗan fahimta abun da suke nufi Amma kuma ita dai Ba turancin nan take ji ba , hasali wannan shine karon ta na farko da ta fara shigowa Aji da makarantar baki ɗaya indai aka cire Allo .

Nurain Whare are we Going now.? . ( Ina zamuje yanzu Nurain). Nurain ne ya kalli Abokanan nasa yana Murmushin nan nasa don shi mutum ne mai fara'a sosai ga surutu . Please come and Excout me to Primary Section , Akwai wata sabuwar Ɗaliba da nake son Ganin ta before a koma break . Kallon sa David yayi yana cewa " New comer .? Kasan tane ? . A'a ban san ta ba , kawai dai a hanya na ganta ɗazu , komai nata Dariya yake bani , oya common guyz . Sanin Halin sa da in yace Abu dole a bi masa yasa su bin bayan su suna nufan Primary Section, tun daga Primary 5 suka fara shiga , suna shiga duka daliban suke tashi su Gaishe su suna fadin " Good morning seniors....Bai tsaya basu Amsa musamman idan yaga bai ga Wacce yazo nema ba sai ya fita ya faɗa wani Ajin . Nufa Primary 2 suka yi inda a bakin Windown Ajin ya tsaya yana Hango inda Ɗaliban Suka Rufe Amrah tsayawa Su David suka yi suna kallon yanda kowa ke gabatar ma Amrah da sunan sa tare da Son zama Abokin ta . Amma bata ce masu komai. I think she don't know how to speak in English . David yayi maganan yana kallon Nurain Wanda idanun sa ke acan Seat din da Amrah take . Eh Nima tunanin da nake yi kenan . Ihun Wata yarinya suka ji tana daka nawa Ɗaliban Tsawa tare da cewa " Ibeg You Are disturbing her (Kuna damun ta ) . i think this girl doesn't know how to speak in English so please just leave her alone . Kallon Marian suka yi wacce ta kasance Yoruba amma Musulma ce . Tsoron Marian ake ji a Class din don bata da kirki ga tsiya ,hakan yasa kowa kama bakin shi . Excuse me pls , ku bani Wuri . Tayi maganan tana zama a saman desk din da Amrah take . Cikin Harshen Hausa tace " Aunty Jamima tace mana sunan ki Amrah Adaam Ɓaidu Right.? So can we be friends, zakiyi ƙawa Dani ?. Kallon ta Amrah tayi tana watsa mata manyan idanun ta kamin ta gyaɗa mata kai alamun eh . No that's not good, Nima magana Zaki mun kaman yanda nayi Miki Amrah ,kin yarda muyi Ƙawance tare ?. Cikin Zazzaƙar Muryar ta mai cike da sanyi na haƙuri tace " Eh na Amince . Murmushi Marian tayi tana Kama Hannun Amrah tare da Ɗagawa sama tana ɗaga murya tare da cewa " yanzu yan Aji dani da Amrah Mun zama Ƙawaye. Chioma ce cike da jin Haushi tace " And SO What.? Se mene kuma , mun ji to . Tayi maganan cike da Tsiwa tana barin Ajin . Taɓe baki Marian tayi tana kallon Amrah tana cewa " Shekaruna 8 kefa?. Ni kuma Shekaruna 7. Murmushi Marian tayi tana kallon Gyefen littafin Amrah tare da duba rubutun nata Wanda ko sunan ta bata saka a littafin ba . Ɗan jimmm tayi kamin tace " baki taɓa shuga Makaranta bane .? Gyaɗa mata kai Amrah tayi ,wanda kamin Marian tayi magana Nana ta katse su tana cewa " But you are not suppose to be in primary 2 , kamata yayi akai ki primary 1 ai. It is your business.? Gulma da saka ido to Ɗauke ta ki kaita Primary 1 din idan akan ki take . Marian tayi maganan tana dalla ma Nana harara . Karan kada kararrawa ne yasa Amrah Juyawa tana kallon inda daliban ke shigowa da gudu ajin idanun ta ne ya sauka akan Window inda Nurain yake da Abokanan sa ,suma idanun su na akan ta . Murmushi yayi mata a zuciyar shi yana cewa " Ohh Duk maganan ma dana yi mata ɗazu bata jini Bama Ashe .? . Juyawa sukayi ba tare da yace mata komai ba suna koma Section din su .

2:30pm . (Closing hour).
Ana tashi Amrah ta fito ga yunwa dake cin ta ,don ko karyawa ba tayi ba , har jiri take gani , gashi tasan idan ta koma gidan ba Abinci za'a bata ba sai Tallah da zata Dauka na Awara . A farfajiyar makarantar daga masu shiga school Bus sai masu shiga moton gidan su wasu kuma manya irin yan SS suna tafiya a keken su . Hanyar ƙasa ta kama tana fara tafiya tare da kallon titi nan biyu ko wanne na wucewar manyan Abin hawa ne . Hi Amrah...!!!

Jin Muryar shi tayi Wanda cikin sauri ta juyo tana kallon Nurain a keken sa dake bayan ta yana murmushi. A daidaita zaki Hau ne na taran Miki .? Kallon sa tayi tana Girgiza kai alamun a'a . Ɗan kallon ta yayi yana ƙare mata kallo kamin yace " Ke scholarship ne aka dauke ki anan .? Eh . But me yasa bakya magana.? Kurr tayi masa da ido cike da Yarinta idanun ta na kawo ruwa tace " Idan ina magana Baba Zuwai duka na take yi... Shiiiii Don't cry please kar kiyi kuka , Ni ki rinƙa mun magana saboda baki ga nima ina Miki magana ba ?. Eh kana mun . Yauwa yanzu zo tanan na goya ki a keke na mu tafi..... Cike da Yarinta ta Wangale masa baki gyefe da gyefen Kuncin ta yana loɓa . Common Amrah yi sauri rana bai damunki.? Sam bata basa Amsa ba ta nufi inda Nurain yake da hannun sa ya Ɗagota yana Ɗaurata a gaban keken nasa yana fara tafiya da ita tare da bin Wani hanya wanda bata san wacce hanya bane don sun sauka a titi . Murmushi yayi yana kallon ta tare da cewa " Kinga tanan yafi sauƙin kaiwa Gida nan da nan zamu je gida. Da gaske ..? . Eh mana .! Ruwa ruwa zai sauko Kayi Gudu . Amrah tayi maganan tana kallon sama don a watan August ake nan da nan ruwa ya sauko ,don a wannan lokacin yayyafi aka fara . Dariya Nurain Yayi yana dakatawa da tuka keken yana cewa" Tsoron Ruwan kike ji.? Gyaɗa masa kai tayi tana cuno dan mitsulun bakin ta gaba na yarinta tana cewa " Idan ruwa ya duke Ni to da kayan zan kwana Baba Zuwai ba zata bari na cire ba a jiki na zai bushe ,Ni kuma ina jin Sanyi sosai . Wacece Baba Zuwai.? . Wangale masa baki tayi tana faɗin " Mama nace . Ɗan jim Nurain yayi kamin ya kafe ta da ido a zuciyar shi yana ayyana anya Mahaifiyar tace kuwa .? May be bata san Maman ta bane ko ta rasu . Ruwa ne da iska ya sauko a lokaci daya . Ihu Amrah ta fara sa masa tana faɗin " Shikenan da tsumammun kaya zan kwana , kuka take yi sosai wanda Ganin haka yasa Nurain saurin nufa Wani rumfan mai tsire ,don mutumin da Yamma yake fara fitowa . Amma kamin su kai tuni ruwan ya gama sauka a jikin su sun tsime sosai....... Ganin yanda take Kukan yasa shi ɗan murmushi cire da son kwantar mata da hankali yace " I'm sorry Amrah , Amrah kin ma san sunana kuwa.? . Goge Hawayen fuskar ta tayi tana cewa " A'a . Fuskar ta ya ɗan Tallabo yana cewa sunana Nurain... Kasa Furta sunan tayi da kyar ta ce" Nurry.................


```Tallah```
Assalamu alaikum jama'a yau gaku ga buxuwa empire

Dakinga wannan page din indai ke mace ce to wannan page din nakune mata iyayen gida

Mata kamar yanda kukasani nicedai *buxuwa empire* wanda nake kawo maku kalolin mallaka,farin jini,kiranye dadai sauran su

Hajiyata mijinki duk dafa'insa kixo nan inshallah zamuyi maki maganin sa inshallah

Mace mai zama da miji mara kyauta mai mako kitaho inshallah magana ta kare

Kina zaune da saurayi ana mashi mgnr yaturo sai su gudu ki taho inshallah

Mace mai fama da matsalar jinnu matar aure ko budurwa

Budurwar da akalla zata kai shekaru 25 bata taɓa saurayi ba ta kitaho da izinin Allah

Budurwa mai samari amma da yazo ana murna zuwa daya bazai sake dawowa ba lamarin dai Allah shi gyara

Masu bukatar kiranye ko farraku tana iya mun mgn ta wannan number kamar haka:08139762831

Kiranyen miji
Aiki da tumfafiya
Aiki da idon dabba wato kamar bita zai zai
Aiki kan shanu a soke shi a bishiya

Aiki da sokakken dabba amma dabban da aka yanka sai a samu laya kamar guda 313 a xiba shi a duk wata organ 🫀🫁 ta ciki da ta waje

Zamu saka wani a idonsa a ƙwaƙwalwa aciki sannan a saka a kogo Hajiya ta mijinki he is sorry 😐 Allah ina fadamaki ai baya da tacewa sai naki

Sannan ana mawa yammata irin shi amma na kiranye cikin kwanaki uku xaki gansa a kowani hali aure kawai yake so

Bana tausayin namiji fa inkinsan kina tausayin mijinki kinfiso yarinka azabtar dake a maikuwan yarinka maki kyauta soyayya dake da yara ki da yan uwanki ba

To inkinfiso komai ki zauna a baya to gaskiya kizauna bansan yanda zan maki ba domin nayi ma mijinki mallaka ko saurayi ko yaƙi ko yaso sai yabiki yamaki abinda kk so kuma kk bukatar

Mallakar zuciya mai allurai a baima kare mai bukatar tabini pc

Mai bukatar mallakar ko kiranyen bakin Ruwa tabini pc inshallah mgn yakare

Nidai nafiso acemun Hajiya inason 🤗 komai da min da mijina kamar kaza ......... Ya rinka mun kaza kaza

Please 🥺 ko kinbini pc kigayamun abunda kk so direct

Matan da kayan sallah wani baiwa shi ba
Sha'anin yan uwanki bai san wannan ba

Lamarin ki da wasu kananan hidimomin ki sodayawa baya biyamaki bukata

Kije wani gida kiga matan gidan nayin abunda baki isaba kice dame tafiki dashi ga abinda tafiki dashi din .....

Ga mata masu bukatar kayan da'a available suke cikin price mai saukin gaske inshallah da masu aiki aciki da marasa aiki
Duk wacce take buƙata tana iya mun mgn ta:08139762831
Muna godiya ga mata bakiɗaya masoya mu mun gode🙏🙏🙏🙏🥰🥰🥰🥰🥰😍😍🙏🙏🙏🙏

*NASRULLAH DATA SERVICES*

_Reach out all for all your cable subscriptions at very cool rate (Airtime data, Tv Subs, prepaid bills)at comfort at your home_

*MTN*
500MB ₦150
1GB ₦300
2GB ₦600
3GB ₦900
5GB ₦1500
10GB ₦2500

*GLO*
200MB ₦100
500MB ₦150
1GB ₦300
2GB ₦600
3GB ₦900
5GB ₦1500
10GB ₦2500


*AIRTEL*
500MB ₦200
1GB ₦350
2GB ₦700
3GB ₦1050
5GB ₦1750
10GB ₦3500

*9MOBILE*
500MB ₦150
1GB ₦300
2GB ₦600
3GB ₦900
5GB ₦1500
10GB ₦2500

*VALIDITY 30 DAYS*


*PAYMENT DATAILS*

ISHAQ NASIR
0778991869 | 7055852908
ACCESS BANK OPAY

*YOUR SATISFACTION IS CONCERN*

Follow this link to view our item on WhatsApp: https://wa.me/p/6501220559940694/2347055852908

*To kaman yanda na faɗa masu buƙatar na tallah ta masu hajar su a page ₦2000 ne idan kuma a Status ne ₦1000 kacal sai Kuyi mun magana ta WhatsApp number na 08081202932*


Mamanteddy 📚🧸
[7/25, 9:57 AM] Matar Mijin Ta: *🛖ƳAR TSAKAR GIDA🛖*
*Romance love and Sympathetic Story*


*Story and Written by Aisha Mamanteddy*

_Page 0 5_

*Littafin Ƴar Tsakar gida na kuɗi ne Regular payment ₦500 Vip payment ₦1000 Special payment ₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932... Idan VTU transfer ne sai ki tura ta Wannan number 09061466409*

Kallon Manyan idanun ta yayi yana ɗan yin ƙasa da kansa tare da kallon Ƙwayar idanun Amrah yana cewa " Mene kika ce.? . Cike da Sanyi don jikin ta ya ida mutuwa Ganin yanda tayi sharkaf a ruwan nan yau tasan Da tsumammun kaya zata Wuni har ta kwana ,hakan yasa ta yin laƙwaam takaicin Nurain ne yanzu take ji ,don idan da bata biyo sa ba Da hakan bai faru da ita ba a ganin ta . Cikin Nuna ka dameni tace " Nurry .! Dariya yayi mai fidda Sauti fararen hakoran sa na bayyana tare da Siririn Hushiryar sa . A dakyau. Suna mai daɗi . Ya ƙare maganan yana kallon ta tare da mata Murmushi . Cike da Rashin Sanin makaman zancen nasa ta juyar da kan ta gyefe tana kallon Ababan Hawan dake Wucewa gefi² ,don bata ƙara bi ta kansa ba bare tasan Mene yake yi . Ruwan ne ya ɗan fara Ɗaukewa wannan yasa Amrah murmushi tana leko da kanta ta Wajen Lange ² Rufin mai tsiren . A hankali ta ɗago da idanun ta sama tana kallon yanda ruwan ke saukowa ta saman Fale-falen Shagon ,wannan yasa ta cike da murmushi takai Hannun ta tana tarawa ruwan na zuba a tsakiyar taffan hannun ta . Tsayawa yayi yana kallon ta tare da murmushi kamin Nurain shima yakai hannun sa yana Daura Hannun ta a saman taffan hannun shi yana tarawa a tare da nashi . Waigowa tayi tana kallon sa a wannan karon dariya tayi masa tana cewa " Nurry Ruwan ya kusa ƙarewa muyi sauri muyi sauri fa kar ruwan ya dawo . Amrah ce tayi maganan cikin Sauri tana janye Hannun ta daga nashi tare da Fitowa daga Rumfar tana nufar inda keken Nurain yake . Bayan ta ya biyo yana Tahowa tare da Hawa yana dorata bisa cike da nishaɗi suke tafiyar don a yanzu ruwan ya dauke sai dai Ɗan yayyafi . Fuskokin su kawai zaka kallah ka tabbatar da suna jin daɗin kasancewar su a hakan .

Tafiya ce ta mintuna Goma sha biyar ya kasu zuwa ga layin su . Lokaci daya Fara'ar nata ya Ɗauke , Kirjin ta taji yana buga mata da ƙarfi tuno da Baba Zuwai da tayi . Nurry Sauke ki anan. Bakin sa yakai zuwa Saitin kunnen ta yana cewa " Ina ne Gidan ku anan da zan sauke ki .? . Nidai A'a ka sauke Ni idan ba Haka ba Zulai ta ganni a keken ka zata faɗa ma Baba Zuwai ne . Kallon Gyefen sa yayi yana kallon Gidan Mahaifin sa kamin yace " Ni kin ga gidan mu Amrah, Kema muje ki nuna mun gidan ku .A'a Nidai Ka sauke Ni anan zan maka kwatance daga nan . Tsayawa da keken nasa yayi yana kai bakin sa dai dai Kunnen ta sauka to . Cikin Sauri Amrah ta dure tana kallon sa tare da kama Ƙugun ta tana cewa " Naƙi na kwatanta maka Nurry . Tana faɗin haka ta Zura da gudu tana barin sa anan tsaye . Keee Kee Amrah..! Ina ma ta sauke shi lungun da zai kaita Gidan su tayi Saurin bi tana Dariya a ganin ta Wayo tayi masa. Murmushi Nurain yayi yana faɗin " Zan kama ki ai .

Komawa yayi yana nufa Gidan su tare da tsallaka karamar Titin . Gate Man ne ya kalli Nurain yana cewa " Nurain ka dawo ruwa ya duke ka. Wani irin kallo Nurain yayi masa yana kauda kai tare da kokarin shiga cikin gidan da keken sa . Bude baki Mai Gadin yayi zai kara masa magana cike da jaraba Nurain yace " Da ruwan ya buge Ni Magani zaka mun ne kome ne . Ibeg just open the door . Jikin Mai Gadin a sanyaye ya bude masa ƙofan gate din Nurain na shigewa daga ciki . Mama Nanny ce take tsaye a baranda tun saukar Ruwan take jirar tahowar Nurain don yau tasan babu lafiya . Ganin sa da tayi yasa ta Saurin tahowa a wannan yayyafin tana nufosa tare da kama shi tana Rungume shi jikin ta , Wani iliya mai Bama ma flowers ruwa yana amsan keken nasa . Ayya Sorry My Nurain ... gaskiya Ruwa n nan bai ƙyauta mana ba . Taho muje a sauya uniform din. Ba tare da ya tanka mata ba yabi bayan ta suna shigewa daga ciki .

**
Ɓangaren Amrah kuwa a zaure ta laɓe tana tsoron shiga cikin gidan , tun daga Zauren take jin Hayagagan Baba Zuwai tana cewa " To gidan Uban ta ta tsaya ko Uwan ta har karfe Uku Da kusan Rabi yau zanci Uban yarinyar nan Wallahi zata dawo ta same Ni . Jikin Amrah ne ya hau Rawa daga tsayen da take , idanun ta na fara Ambaliyar Ruwan Hawaye mai tattare da maraici da tsoro ga tashin hankali . Kaman daga sama ne ta jiyo Muryar Zulai wacce bata san ta fito ba tana cewa " Laa Baba Zuwai ga Shegiyar nan ta maƙale a zaure , bata son ta shigo ne don kar ta kai Miki Tallahn yayi kwantai . Laha'ila kunji baƙin hali irin na yarinyar nan aiko yau sai naci Uban ki . Baba Zuwai tayi maganan tana leko Zauren tare da kamo Amrah tana jawo ta zuwa cikin Tsakar gidan . Kuka Amrah ta fara tana faɗin " Don Allah Baba Zuwai kiyi Haƙuri wallahi Zani Tallahn Ruwan sama ne ya sa na fake a hanya . Wani irin kallo Baba Zuwai ta watsa mata tana daga hannun ta tare da fara Wanke Fuskar Amrah da Mari jikake tasss⁴ har sau hudu . Jummai ne ta miƙo mata Bulalan Inji tare da Cewa" A'a kar ki Wahalar da hannun ki ga Bulalan da zai shiga jikin ta ?. Amsan Bulalan Baba Zuwai tayi tana Wani irin dukan Amrah tamkar wacce take bugun baligar mace nan ko yarinya ce yar shekaru 7 . Tun Amrah na kuka har sai da bakin ta ya mutu . Sannan Baba Zuwai ta rabu da ita ,don tafi mintuna talatin tana dukan ta kaf cikin Gidan nan babu wanda ya fito Kwatar ta . Numfasawa Baba Zuwai tayi tana cewa " Dan uban ki kuma ki Ɗauki Tallahn Gyaɗan gashi can ,na ɗari Biyar da hamsin ne ,Naira daya ya ɓata sai naci Uban ki Wallahi . A hankali Amrah ke jan jikin ta , fuskar ta duk ya kumbura na tsaban Mari hannayen Ta duk sunyi shatin bulala suna zubda jini . Jan jikin ta tayi tana Ɗaukar Farantin gyaɗan tare da Ɗaurawa a saman kan ta . Idanun ta na ganin duhuwa Ga yunwa ga duka da tasha na mutuwa . Nufar Hanyar kofar gidan tayi tana tangaɗi kaman zata kife .

**
Zaune yake a saman Ƙayataccen Bed ɗin shi ,ƙafafun shi na akan jikin Mama Nanny wacce take ta matsa masa ƙafan a hankali tana basa labarai masu daɗi ,tamkar yanda mahaifiyar sa ke masa . Kallon Nurain nayi Da yake sanye cikin Kananun kaya Rigar jikin sa T.shirt Blue sai Wandon jikin sa Farin jeans mai ɗan yalwa bai takura shi ba . Sunan Labari Mama Nanny ke basa Amma sam baya ta kan ta idanun sa na akan laptop ɗin sa dayake playing Game . Saurin Kallon Nanny yayi yana kiran sunan ta da "Halima Ƙarfe nawa yanzu.? . Ɗaga idanun ta tayi tana kallon Agogon dake maƙale a bangon Bedroom din nasa kana tace "ƙarfe Huɗu da rabi . Ohhhh God . Saurin Miƙewa yayi yana Zura Room silipers din sa tare da cewa " Ina zuwa .? Ficewa yayi daga Dakin yana nufar Wajen Farfajiyar gidan,inda ya hango mai Gadi can zaune a Kujeran sa . Nufar inda yake yayi ,yayin da mai gadin yayi Saurin muskutawa yana Miƙewa tsaye tare da cewa " Barka da fitowa Nurain . Bude mun kofa ,ina kujeran nan naka ? , Kasa mun a waje zan zauna yau .! Cike da dan gajeren mamakin yau Shine zai zauna a waje. Yaron rainon turawa sam baya son hayaniya kullum yana daki yau shine zai zauna a waje . Murmushi yayi yana cewa " Ohk sir . Yanda suke basa Girma ka rantse babba ne nan kuwa yaro ne wanda a wannan lokacin baifi Shekaru 16 ba. Jiki na Rawa Gate man ya aje masa Robber chair tare da ja gyefe Nurain na zama . Mintinan sa baifi Uku da zama ba ya hango Ta dauke da farantin gyaɗa a bisa tsakiyar kan ta . Idanun ta na kallon Ƙasa . Jan jikin ta kawai take yi dagani kasan da Akwai Abin dake damunta . Idanun sa ya kafe a kanta na yan Daƙiƙu har ta zo ta gaban sa zata Wuce bata Gan shi ba don gaban ta kawai take kallo . Motsa Laɓɓansa yayi yana

Please Login or Register in order to submit comment