Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Meemi fad'a akan wulak'an ta d'an Adam ko don ina a matsayin y'ar uwarta mafi kusanci.

Ni kuwa daman nasan hakan zai faru don ba kowacce mace ba ce ta ke da b'oye Kishin ta don haka kuwa dole ne ta yi,Amman ni dai har zuciyata bana jin haushin ta ko kad'an don ni shi kanshi mijin ba sonshi na ke yi ba ballan tana inyi kishinsa don haka tuni daga shi har ita na tattarasu na watsar.


Umma ce kad'ai ta je ranar suna Amman babu yadda ba ta yi dani inje ba Amman na k'i k'arshe ma na lafe a gado na ce ba ni da lfy.


Ina kwance a kan gadona daga ni sai wata rigar bacci Red color gashin kaina duk ya barbazu akan gadon kamar wata ba India,k'arar shigowar mota naji Amman sai ban tashi ba don nasan Mlm ne ya dawo kuma watak'il wani abin zai d'auka don haka naci gaba da bacci na.


A cikin bacci na naji wani irin k'amshin turare Wanda k'amshinsa ba ya gushewa a cikin hancina da gangar jiki na baki 1,saurin ta shi na yi don tsabar tsoro gabana ne ya yi wani irin mugun tashi ganin Muta'z a kaina yana yimin wani irin mayen kallo kamar zai cinye ni.


Da Sauri na fara Neman blanket d'ina Amman baya kan gadon,kunya ta bi ta isheni kawai sai naga ya k'araso har inda nake ya lullub'amin a jiki na sannan ya yi min wata signal ya bi hanyar fita,tsayawa naga ya yi a bakin k'ofar sannan ya ce min"ki fito Hanan ta zo ganin ki don jiya ta dawo daga mkrnt......


Ai ban Bari ya k'ara sa ba na d'auko hijab d'ina na saka na wuce ta gabansa da Sauri don zumud'in ganin Hanan,shi kuwa tsayawa yayi a bakin k'ofar yana shak'ar daddad'an k'amshin da Mumtaz ta barmai,har zuciyarsa ya ke jin wani irin tsagwaran son Mumtaz har cikin zuciyar sa so na tsakani da Allah.


A farlo ya samesu sun rungume juna suna ta zuba surutu,ya watsowa Hanan wani kallo sannan ya ce"ke Hanan ki iya bakin ki don Da amarya ta ki ke magana ehee".

Dariya Hanan ta yi sannan ta ce"Kai gaskiya Yaya ka iya zab'e fa gata k'anwarka ga ta matarka kaga shikkenan ka had'a k'annenka a matsayin Matanka".

Nan dai Hanan ta ringa bani labari,shi kuwa Muta'z sai kallo na ya ke yi kamar zai cinye ni da naga ya matsamin sai na rik'e hannun Hanan na ce muje kitchen mu d'ora girki,sannan na juyo Amman na kasa kallon kwayar idonsa na ce"ka koma gida kaga yau suna zamuyi girki."


Zama naga ya k'ara yi sannan ya CE"Wow shikkenan kinga sai inci girkin amaryata".ya fad'i hakan ya na mannemin ido alamar yaji dad'in hakan.


Hanan sai dariya ta ke tana cewa Romio da Juliet kawai,ni kuwa naja hannunta muka shiga kitchen muka fara aikin mu gadan gadan,tunda suka fara girkin Muta'z yake kallon farlon kamar ya bisu ga wani k'amshi da ya faraji Wanda ya gama cika farlon.

Naman kai muka dafa Wanda ya gaji da k'amshi ,sai jallop d'in taliya Wanda Tasha green beans, da hanta,da kayan k'amshi sai coconut&pine apple jus.


Hanan ce ta fara jerawa a dining ni kuma ina gyara wajen da muka b'ata sai da na gama gyarawa tsab sannan nafito,na d'auka gaba d'aya ya tafi baya farlon Ashe yana nan ya hard'e k'afa 1 kan 1,kallo na ya ringa yi har na fara hawa kan step a hankali kamar me tausayin tsep d'in, Muta'z kuwa kamar wani soko sai kallo na ya ke yi Hanan ta kula da hakan sai dariya ta ke yi shi kuwa gogan besan ma meke faruwa.


Yana ganin Mumtaz ta hau sama ya fara cika cikinsa da d'a amun yana santi kamar wani yaro sai da yaci ya more sannan ya tashi yana masha Allah kace na more da amarya me iya girki.


A hankali na fara sakkowa akan step d'in ina sanye da wata doguwar Riga Arabian gown blue black kasan cewa ta fara sai ta haska ni sosai na nad'a belt d'in a kaina na saka plat show me kyau, ina danna wayata har na k'ara so Amman Muta'z besan na k'ara so ba don wani mugun kallo da ya ke bina dashi kamar zai cinye ni,ni kuwa na basar dashi na zauna ina cewa Hanan idan ta gama cin abincin zamuje gidansu Amal don su gaisa.


Saurin tashi Muta'z ya yi wai zai kaimu,Amman na ce mishi ya barshi ga gidansu nan kusa da namu Amman fafur ya CE wallahi sai ya rakani.


Haka kuwa akayi har gidansu Amal ya rakamu sai da yaga mun shiga sannan ya tsaya acikin motar ya ce mu shiga zai jiramu,ina matuk'ar mamakin kishin Muta'z kamar Wanda za'a saceni.


Amal ta yi matuk'ar jin dad'in zuwanmu,Mamansu ma sai nannan ta ke damu don yanzu sona ta ke kamar za ta goyani,ni kuwa a zuciyata oh Ashe dubiyarnan sai kana dashi a ke damawa da kai.





.....Fulani da kanta ta d'auko me yimin dilka da gyaran jiki ciki da waje,ai kuwa matar tasan abinda ta ke yi don irin matan sudawan nanne don haka ta zage awajen gyarani ciki da waje,gabana kuwa ko d'an yatsa bazai shiga ba tsabar gyara kuma an hana Muta'z zuwa gidanmu don har sai an kaini Gidan shi sannan zai ganni don haka Bak'aramun kwaruwa Muta'z ya yi ba don har ciwo sai da yayi,don Ni da kaina na tsara wannan don yadda na ke ada ma Muta'z yana k'ok'arin tab'a jikina ballan tana yanzu da komai nawa ya canza Wanda ya sanni ada yanzu ba zai gane ni ba.



Please kuyi hak'uri abubuwa ne suke yimin yawa shiyyasa bana tyiping da wuri✍🏻.




Ummu Maher CE
Vote
Share
And
Comments.
*_AKAN AIKI NA_*



Rubuta wa✍🏻
_(Ummu Maher)Miss green🍀_







_*Please don Allah kuyi hak'uri fans bana samun kawo muku labarin Jamila abubuwa ne suka yi yawa*_



_(The Wedding)_

💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼
To fa ranar muke jira yau gata tazooo,ranar bikin Muta'z da Mumtaz.



Page 76&77

Wani irin kyau me had'e da sirrika kala² Mumtaz ta yi kamar ka d'auke ta gaba d'aya,tun jiya na ke kuka don idan na tuna ayanzu haka na zama Matar Mumtaz ba k'ara min tashi hankali na ya ke yi ba,don gaba d'aya yanzu tsoron Mumtaz na ke yi don na dad'e da sanin ba k'ara min mugu bane.


Tun k'arfe 4 y'an d'aukar amarya suka zo muna ta kuka nida Amal,don tun safe muke kukan rabuwa ni da aminiyata Hajjo kuwa sai masifa ta ke Wai min isheta da kuka kamar wad'anda za'a yanka kukan ya yi yawa.


Hajjo CE ta shiryani da kanta da wata had'addiyar tamfa super me Golding ta yi kyau sosai sannan aka d'oramin wata lafiyayyiyar Lifaya fara Sol sai ratsin gold ajikinta aka fesheni da turare exsense ne k'amshin gaske.


Har aka gama shirin kuka na ke yi aka shigar dani babban farlon Mlm ya yi min nasiha sosai me ratsa jiki nan fa kuka na ya k'ara k'aruwa da k'er Mlm ya rarrasheni don shima kukan zuci ya ke yi.



Wata sabuwar mota muka shiga wadda Muta'z ya yimin kyautarta yau bayan d'aurin Aure motar sai k'elli ta ke yi.



Muna shiga Gidan Sarauta ya d'auka a ko ina bakajin komai sai tashin kid'a da tambura ta ko ina,Muta'z kuwa yana d'akinshi shida abokansa suna ta yimai tsiya Mijin Meemi da Mumtaz abin shi kanshi burgesa ya ke yi sosai.


Meemi kuwa tana sashenta lokacin da aka shigo da Mumtaz ji ta ke kamar ta kashe kanta tsabar kishi,Baby kuwa sai kuka ta ke yi baiwar Allah Amman tak'i kulata da ta dame ta ma har dungure mata kai ta yi ai kuwa ta ringa tsala kuka.

"Don ubanki ba ubanki bane ya janyomin wannan fitanar ba ina zaman zamana yarinya ta lik'ewa mijina ai kuwa duk sai sun gane kurensu don wallahi bazan yarda wacce mace ta had'a shimfid'a da mijina ba.


B'angaren Fulani aka fara kaini ta karb'eni hannu bibbiyu sannan ta kaimu b'angaren mai martaba shima ya yimin nasiha sosai ta zaman hak'uri agidan miji,sannan ya mik'omin wasu mukulli na kyautar wani Gidan shak'atawarsa Har kuka saida Hajjo ta yi na ganin irin kyautar da Mai Martaba ya yiwa jikarta ta dinga saka mai albarka.


Sashen Meemi aka nufa dani Amman muna zuwa Masu yi mata hidama wato bayinta suka CE mana ta fita,Hajjo kuwa cewa ta yi "Uban ta fita ba bata fita ba🥴wallahi sai tadawo munanan muna jiranta ko in shigo d'akin tafito ja'ira,da k'er aka bata hak'uri ta hak'ura ammanfa tana ta sababi.


Sashena aka kaini aka ce in shiga da bismillah,ai kuwa na shiga da addu'oi a bakina gwanin sha'awa,sai da na CE alhmdh don wani dad'i da nishad'i na dinga ji sosai.


Akan faffad'an gadona aka ajjeni Amal ta rungumeni tana ta kuka y'an kai Amarya suka fara watsewa daga ni sai Amal sai Hanan ita kuwa sai murna ta ke yi ta samu k'awa ni kuwa kaina yana cikin had'addiyar lifaya sai k'amshi na ke zubawa ana cikin haka mukaji ana bud'e k'ofa.

Da sauri Amal ta tashi tana share hawayenta,Muta'z ne shi kad'ai yasha wata d'anyar shadda fara Sol abin sha'awa kyaunsa da nutsuwarsa da haibarsa duka sun fito gwanin ban sha'awa.


Gyaran murya ya yi Amal da Hanan suka gaishesa sukayi mana sai da safe,anan naji hanjin ciki na sun kad'a K'uuuu tsabar tsoron Muta'z, shima ya fuskanci haka don haka ya zauna abakin gadon yana me godewa Allah akan kyautar mata da yayi masa.


Matsowa ya farayi ni kuma ina ja da baya don kunyarsa na ke ji ba kad'anba kawai sai naji ya kamo hannuna cikin nasa,yana shafawa ahankali da sauri na janye hannuna ina Jan zuciya.

Dariya ya yi sannan yace ina yiwa Allah godiya da ya kawo mu wannan rana Dana mallakeki a matsayin matata,sosai na juyo numfashinsa gab dani ya yaye min mayafina a hankali sannan ya CE"Masha Allah ina yiwa Allah godiya da ya bani wannan babbar kyau ta,Mumtaz da ban Aureki ban San yadda rayuwata zata zama ba sonki Allah ne ya d'arsa min shi a cikin zuciyata,ki bani dama in koya miki sona kuma in shayar dake dad'in da baki tab'a ji ba arayuwarki.





Ummu Maher CE
Vote
Share
And
Comments
*_AKAN AIKI NA_*

Rubutawa✍🏻₹₹₹₹₹

*_(Ûmmu Mâhér)Míss gréén☘️_*



Wannan shafin naku ne masoyana Allah yabarmu tare.


*Mmn Teddy*
*Y'ar Kaka*
*Nabila Dikko*
*Nabiha Aminu*
*Ruky Gawata(My suruka)*
*Hadiza Barau Gidan Iko*
*Amina M Baso*
*Ummu najma*
*Dr Amira*
*Khaltum Khanna*
*Zahra'uu Naseer Aliyu*
*Nersmer*
*Momin Shukura*




Page 78&79



Shiru na yi ina tunanin wannan wani irin farin ciki ya ke so ya saka ni,ni dai nasan babu wani farin cikin da zai iya saka ni saboda shi azzalumi ne mutumin da ya yi min fyed'e ta k'arfi Da yaji shine yanzu zai CE zai saka ni cikin farin ciki,ina cikin wannan tunanin na ji ya rik'e hannu na kamar zaiyi kuka ya Ce"Mumtaz ki yadda zan shayar da ke farin ciki Mara misaltuwa don haka yanzu ki tashi muyi sallah mu godewa Allah bisa wannan ni'ima da ya yi mana.





Addu'ah Yarima Muta'z ya dinga kwararuwa har mamaki ya bani daman ya iya addu'ah irin haka ban Sani ba,Ya kama goshina ya yi min addu'a.


Da kanshi yadinga shayar dani fresh milk tare da d'awisu wadda ta gasu da kyau k'amshi ya bad'e ko ina,ban San ina jin yunwa ba sai da naga abinda naci da yawa sosai.



"To ni baza a shayar dani ba a samu lada"?.

Maganar sa naji kamar a dodon kunnena don haka naji tsigar jiki na ta tashi sai na tsinci kaina a mai yimai murmushi na cuko hannuna da lomar D'awisu na saka mishi a baki,a kunya CE na fara ciyar dashi yana lumshe ido.

Zan saka mishi lumar k'arshe ya rik'e hannuna naga idanunsa gaba ki d'aya sun juye,ya rungumo ni kamar y'ar k'aramar yarinya sai bathroom,kunya da nadamar saurin saukowata daga dokin fushi ya dame ni,don kafin in farga ya rabani da komai nawa ya saka ni a komar wanka shima ya shugo.


Tunda nake ban tab'a jin Abu me dad'i irin Wanda Yarima Muta'z ya ke min ba,Lallai Allah ya yi gaskiya da ya CE muddin mace da namiji suka had'u to namijin su shaid'anne,kuma koma menene Aure dai ni'ima ne,don da zina CE ba zata yi armashi haka ba.


Gaba d'aya ya sake rungunoni zuwa kan faffad'an gadonmu Wanda ya gaji da had'uwa ya fara kawomin wasu zafafan kiss a cibiyata ban San sanda na manta da hanyar garinmu ba na saki jiki kamar y'ar hannu ina kawo wuta.



Ni kuwa Ummu Maher na rufo musu k'ofa na CE Yarima asha angonci lfy.



Sai da komai ya lafa sannan ya rungomin yana saka min albarka tare da fad'amin maganganun da sai da naji kunyarsu don tuni na manta da wani Abu da Muta'z ya yimin a baya kuma daga wannan Daren na gane Muta'z so ya ke yimin domin Allah ba don wani Abu ba.



Ranar kuwa Uwargida Meemi ko runtsawa ba tayi ba,don yadda ta kejin zuciyarta bata tunanin ayanzu Muta'z zai ko kalleta don yadda ya ke nan²da Mumtaz ga ta mai kyau, da koma ta CE ta fita komai don ta tsorata ita kanta da yadda Mumtaz ta yi kyau kamar ka d'auketa duk namijin da yasa ido akanta ba zai iya d'aukewa ba saboda ta tafi da ko wani irin sirrin kyau.


Kuka babu irin Wanda Meemi ba ta yi ba,Baby ma ta tashi jin uwarta na kuka ita ma ta fara ta ya ta,Amman da Ta ishe uwar da kuka Zane ta tayi don dole Baby ta yi kuka tana Jan zuciya,ta kalli yarinyar komai nata irin na mahaifinta sai taji gaba ki d'aya yarinyar tana bata mugun haushi.


Da kanshi ya gasa Mumtaz tana ta rufe ido saboda kunya,shi kuwa jinshi ya ke kamar wani sabo don yadda ya kejinshi cikin nishad'i da annushuwa.

"My Baby in k'ara round2 wallahi ban k'oshi ba?".


Da Sauri Mumtaz ta shammaceshi ta d'auki tawul d'inta ta fito da gudu suka fara y'ar tsere daga k'arshe dai suka fad'a kan gado suna mayarda numfashi a tsakaninsu,Muta'z ya kalli Mumtaz ya CE" My baby ina matuk'ar sonki da k'aunarki don Allah kada ki gujeni duk rintsi duk wuya",Mumtaz nasan kina sona duk da abinda na aikata miki Amman baki tona min asiri ba,kika rufamin asiri kinga kuwa ya zama dole in soki don ke matar rufin asiri CE.


Daga nan Muta'z ya k'ara yiwa Mumtaz,wayo suka fad'a duniyar maji dad'i.



Tare suka tashi daga bacci sukayi wanka suka shirya cikin shadda dark blue me kyau,yadda sukayi kyau kamar ka sacesu suka fito farlo a tare,angama jera musu komai akan dining,har Muta'z ya zauna sai kuma ya tashi ya CE"My love bari in dubo Uwar gida ina zuwa",da kallo na bishi ya yinda naji zuciya ta babu dad'i amman babu yadda za ta yi tunda matar sa CE.


Yana shiga sashen Meemi ya hango Baby a k'asa kan tile tana bacci ga shi idonta ya kumbura da alamu ma tashi kuka abinta.



Mamaki ne ya cika Muta'z yazo da Sauri ya rungumeta a k'irjinsa da alama d'umin ta keso ta kuma lafewa a jikinsa tare da sheshshak'ar kuka alamun ta dad'e tana kuka daga baya bacci ya d'auketa.


Ko kallonshi Meemi ba ta yi ba ta cigaba da Ku kanta kamar k'aramar yarinya ta kaici ne ya cika Muta'z, y CE"Ashe baki da hankali Meemi yanzu Y'ar tawa kika ajje a k'asan tiles,kin fi kowa sanin cewa ko magen gidanmu bata kwana akan tiles ballan tana y'ata ta cikina,How comes ki CE wai kishi kike,ko hauka?saboda yafi kama da hauka Amman ba laifinki bane ki yi komai a sannu".

yana kaiwa nan ya d'auki Baby ya fita da ita yana Jan tsaki kamar zai tashi sama,abinda yasa Meemi ta yiwa Muta'z haka saboda yana da masifar son y'ay'ansa shiyyasa ta yi masa haka,I ta kuwa yana fita ta saka mayafinta ta fita.






*Ummu Maher CE*
*_AKAN AIKI NA_*



Rubutawa✍🏻ঁঁঁঁঁঁঁঁঁঁঁঁঁঁ

_*(Ummu Mâhér)Miss gréén*☘️_





🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚


Pg 80


Tun daga wannan ranar ruk'on Baby ya dawo hannuna yarinyar ta saba dani sosai don ko bacci tare muke da Baby Uban ya yi ta fad'a mussaman idan yana Son harka in yi ta mai dariya da kansa zai d'auketa ya kaita d'akin ta.


Sannan an kawo min Barori har guda uku masu taya ni aiki,harma da Jakadiya aka kawo min, don babu yadda zanyi ne Amman kwata² masu AIKI basa cikin tsari na.



Tunda Meemi ta bar Gidan nan bata dawo ba,Ashe wajen Me Martaba takai k'ararshi Wai baya kwatanta mata adalci a tsakaninmu,lokacin da Me Martaba yaji ya kirawo Muta'z ya shaida masa duk abubuwan da Meemi ta fad'a mishi.


Sosai Muta'z ya ji haushin Meemi don ya tsani kai k'ara Amman babu yadda zaiyi Dole ya bawa Me Martaba hak'uri don a zauna lfy.

Ko da ta dawo Ma tashin hankali na yau daban na jib'i daban Amman duk da haka Muta'z baya shiga harkarta don ko yana b'angaren ta sai taga damar yimai magana,shi kuwa ya shigewarsa d'aki ya barta cikin zullumi,kuma har yau bata tambayi Baby ba don daman madara ake bata watanta uku ta daina bawa yarinyar nono Wai kada Nonon ta ya lalace shiyyasa ta daina ba ta,shima Muta'z ko zancen Baby baiyi mata ba ya saka mata ido kurum don shi zaman Baby awajan Mumtaz ya fiye mishi akan zama a wajen Meemi.


**** *** ****

"Wallahi tallahi Murat baka isa ka ce sai da ka aureni yanzu kuma zaka sakeni ba matuk'ar ka sakeni to tabbas asirinka zai tonu don bazan yarda ka cuceni ka CE kuma kai zaka zauna lfy ba ehe".

Meema bata San tun tuni Murat ya kwashe wannan CD d'in ba lokacin da ta saki jikinta dashi shi kuma a lokacin ya kwashesu duka ya k'una.


Shiru Murat ya yi yana kallon Meema sannan ya CE Meema ba zaki k'ara kwana a Gidan nan ba Meema kin cuceni kinci amanata duk kud'in Dana mallaka kin kwashesu saboda son zuciyarki Amman yanzu kina fad'a min kada in rabu dake saboda tonuwar asiri na,don haka na sakeki Saki 3.


Wani wawan ihu Meema ta yi ta zabura zata shak'e Murat ya yi kukan kura ya hankad'ata sannan ya nuna ta da yatsar sa ya CE" ki fitarmin agida tun kafin in saka ayi waje dake".

Ko da ta nemi ta yi mai gaddama don haka da kansa ya dinga janta har sai da fidda ta tak'arfi da yaji tana kuka tana ihu, don a rayuwarta tana matuk'ar son Murat.


Yana shigowa ya rufe get d'in ya zauna a farfajiyar Gidan yana jin zuciyarta tana yi masa zafi tabbas alhakin Muta'z ke bibiyarsa kuma tabbas bazai samu sukuni ba har sai ya nemi yafiyarsa,hak'ik'a hassada ga mai rabo taki CE,be yarda da wannan Karin maganar ba sai akanshi don Muta'z bai tab'a yimai Hassada ba Amman gashi kullum yana cigaba shi kuma yana dakushewa ya zamanto duk abinda yasa hannu to sai ya lalace.



Yana cikin wannan tunanin yaji horn d'in mota da sauri ya kallo bakin get d'in don yasan wannan tabbas horn d'in Muta'z ne.


Da sauri ya tashi ya bud'e mai yana me Matuk'ar jin kunyar kallon Muta'z don gani ya ke yi kamar Muta'z ya gane duk wani Abu da ya yi mai.


"Haba Murat yanzu ko ban nemaka ba kai ba zaka neme ni ba?".


Da sauri Murat ya rungume Muta'z yana kuka yana cewa" Muta'z ka yafemin don Allah idan baka yafemin ba bazan samu sa'ida ba har awajen Allah.


"Murat na yafe maka duniya da lahira,kuma bana son inji lefin da ka yi min na yafe maka Allah ya yafe mana baki d'aya.


Sosai Murat ya dad'a ganin girman Muta'z saboda lallai Muta'z ya cika mutum na gaskiya me yafewa magautansa.


Hira sosai suka shiga yi har Murat yana bashi labarin sakin da ya yi wa Meema da duk abinda ta yi mai babu Wanda ya b'oyewa Muta'z.

Daman Muta'z yasan za'a yi haka saboda yadda aka shirya Auren,dole Allah ya d'ebewa abin albarka.


*After 5 years*


..,....
Mumtaz na hango tana zaune da k'aton cikin ta haihuwa ko yau ko gobe,ta k'ara cika da kyau kana ganinta kasan Hutu ya zaunu ajikinta.


Wasu yara ne Twins wad'anda ba zasu wuce shekara uku ba mace da na miji sai kuma yayarsu Baby ta ruk'osu gwanin sha'awa.

Suka fad'o kanta suna mata sannu da gida. *After 5 years*


..,....
Mumtaz na hango tana zaune da k'aton cikin ta haihuwa ko yau ko gobe,ta k'ara cika da kyau kana ganinta kasan Hutu ya zaunu ajikinta.


Wasu yara ne Twins wad'anda ba zasu wuce shekara uku ba mace da na miji sai kuma yayarsu Baby ta ruk'osu gwanin sha'awa.

Suka fad'o kanta suna mata sannu da gida."Wash haba Murat kai kafi kowa rashin hankali so kake ka illata ni?".


" Haba Mmn Murat ayi hak'uri mun tuba".

Muta'z ne ya fad'i hakan lokacin da ya ke shigowa cikin farlon yasha kayan sarauta irin Wanda Y'ay'an Sarauta suke sakawa musamman y'ay'an gata.


"Har kun dawo daga hawan ne"?

" Eh madam mun dawo ya gida"?.


Nan muka cigaba da a tsakaninmu akwai shak'uwa sosai kuma bazaka tab'a cewa ba ni CE na haifi Baby ba,na d'auketa kamar Twins Murat da Meema asalin sunanta Khadija, sunan Meema wadda Allah ya yiwa rasuwa shekara 1,A sanadiyyar Haihuwa Allah ya yi mata rasuwa da d'an cikinta.


Kafin Meemi ta rasu mun zama 1 ni da ita domin duk wata k'iyayya ta daina da taga bana kula ta,shiyyasa muka zauna lfy.


Umma da Mlm sun dawo Gidan Sarauta,Hanan ta Auri Murat biyo bayan ruguntsumin da akayi don Da k'er Hanan ta Auri Murat,Amman a yanzu komai ya zama tarihi y'ar su 1 me Suna Mumtaz, takwara ta Hajjo ma tana nan tare damu Alhmdh ayanzu babu abinda zance da Allah sai godiya don ayanzu bani da wata matsala sai wadda ba arasa ba ita ma kuma ta zama dole kodon Allah ya jarraba ka.


Amal ta Auri wani abokin Muta'z shima likita ne kwararre Wanda a yanzu suna K'asar England ita da mijinta me suna Ahmad.



Meema ma ta yi Aure ta Auri wani me suna Alhaji K'asim matansa 4,Wanda a farko taji dad'in Aurensa Amman daga baya ya zamar da ita kamar jaka,zagi da wulak'anci yanzu ansallami ko wani me aiki agidan ita ta ke yi,Wanda tuni ta nemi yafiyar Muta'z duk da bata fad'a mai lefinta ba Amman ya yafe mata,ta nemi yafiyar Murat ma shima ya yafe mata.


Mumtaz ta sauka lfy ya yinda ta haifi d'a namiji me kamada Mutaz.


Hajiyan Mukhtar har gida tazo ta bawa Mumtaz hak'uri akan duk abubuwan da ta yi mata,don tun yanzu ta gane Illar Auren had'in da ta yiwa d'anta Mukhtar don yanzu Sakina da Uwarta ba k'aramin wahalar da Hajiya suke ba.


Duniya kenan shiyyasa aka ce makashinka yana tare da kai.



*TAMMAT BI HAMDULLAH/....*


*SUBHANAKHALLAHUMMA WABI HAMDI ASH'HADU ALLA ILAHA ILLA ANTA ASTAGHFIRUKA WA'ATUBU ILAIKA*



Anan na kawo k'arshen wannan littafi nawa me Suna AKAN AIKI NA,ina fatan y'an uwana zakuyi amfani da abinda muka karanta,saboda yana da kyau muringa karanta littafi badon soyayya ko wani Abu ba,a'ah mu ringa katantashi saboda d'auka darasi na rayuwa.



Wanda idan kun lura wannan labarin yana fad'akar damu akan illar Hassada da kuma cin amana.Sannan kuma yana nuna mana cewa yadda da k'addara Imani ne,kamar yadda mahaifin Mumtaz ya yarda dashi gashi daga baya ya yi arzik'i.


Masha Allah ina gaida masoyan wannan littafin baki d'aya musamman.



*KHALTUM KHANNA*
*DR AMIRA*
*MAMAN HUMAIRA*
*LUBABATU SULAIMAN*


Da dukkanin masoyanana Allah yabar zmnci Amin.



Taku har kullum Ummu Maher Miss green👌🏻££££չչչঊঊঊঊঈঈঈঐঔঔ

Masu jin yaran india su fassara🤣🤣🥴🥴✍🏻.

Sai kun jini a sabonLittafina me Suna
RAYUWARMU AYAU
&
MATA HUD'U.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu

Please Login or Register in order to submit comment