Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kurum ta ke dauke da
mai. Ta ciccibi jakar da take da mai, ta nufi dakin
girki.

Da isarta dakin girki, sai ta sauke tasar suyar kifi
ta dora babbar tukunya, ta juye man nan gaba
daya a cikin tukunyar. Ta tafasa man sosai har sai
da ya tafasa. Ta diba yadda za ta iya dauka, ta
dauki shantu ta tafi wurin barayin nan. Idan ta je
ga jaka sai ta tura shantu a ciki, ta dura
tafasasshen mai a cikin jakar, tun barawo na motsi
har sai ta ji ya yi shiru, ya mutu. Haka ta bi su
daya bayan daya, tana kashe su da tafasasshen
mai, har ta kashe su duka. Sannan ta soya kifin da
aka ce ta soya.
Lokacin da Ali Baba da shugaban barayi suka
dawo daga yawo cikin gari, Murjanatu ta kawo
musu kifi suka ci. Da suka gama suka yi sai-da-
safe da juna, barawo ya shige dakinsa, bai san
abin da ake ciki ba, shi ma Ali Baba ya shige cikin
gida.

Ita kuwa Murjanatu da ta shiga dakinta ta rufe
kofa, sai ta bude taga tana kallon abin da zai faru
a farfajiyar gidan idan shugaban barayi ya gane an
kashe masa mutane.

Can da dare ya tsala, gari kowa ya yi tsit, sai
Murjanatu ta ga shugaban barayi ya bude dakinsa
a hankali ya fito, ya nufi inda jakunkunan mai
suke. Ta ga ya taba daya, ya jira bai ji motsi ba.
Ya kara taba wata, babu motsi. Ya bi su gaba
daya ya taba, babu mai motsi. Sai ya bude daya,
domin ya ga ko barci ne ya dauke su. Sai
Murjanatu ta ga ya ja da baya cikin alamun jin
tsoro. Daga nan sai ta ga ya yi sauri ya nufi kofar
fita daga gidan, ya bude, ya arce.
Murjanatu ta mayar da tagar dakinta ta rufe, ta
tabbata cewa maigidanta ya tsallake wannan
tarko, sai dai ba ta san da wane shiri wancan
barawon da ya tsallake zai dawo ba, ko wane irin
tarko zai sake kafa wa Ali Baba? Ta kwanta kan
gadonta tana jiran gari ya waye ta fada wa Ali
Baba halin da ake ciki.
***

Bari na dakata a nan, don na ga wasu har sun gaji
da karatu. Idan Allah ya kai mu gobe

whatsapp number
0807105113807. HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN

Da gari ya waye, Ali Baba ya fito farfajiyar gidan
domin su gaisa da bakonsa, ga mamakinsa sai ya
ga kofar dakinsa a bude, babu bako babu
alamunsa, amma kuma ga dabbobinsa nan da
kuma hajarsa ta mai. Yana nan tsaye yana
mamakin inda bakonsa ya shiga, sai ga
kuyangarsa Murjanatu ta fito, ta durkusa ta gaishe
shi.
Ya tambaye ta, ko ta ji motsin bakonsa? Domin
tagar dakinta na kallon farfajiyar gidan ne, duk
wani motsi da za a yi a farfajiyar gidan Murjanatu
za ta iya ji daga cikin dakinta. Ta ce da Ali Baba,
"Maigida zo ka duba da idonka, ka kara yi wa
Allah godiya, da ya kubutar da kai." Ta ja shi har
zuwa wurin da jakunkunan mai suke, ta ce ya bude
daya da kansa ya ga abin mamaki.
Ali Baba ya bude jakar mai daya, sai ya ga mutum
a ciki, rike da takobi. Ya juya zai gudu cikin tsoro,
Murjanatu ta dakatar da shi. Ta ce, "Wannan
mutum da kake gani ba zai iya cutar da kai da
komai ba domin kuwa ba shi da rai. Mutum talatin
da bakwai ne, duk Allah ya ba ni nasarar kashe su
da tafasasshen mai." Ta kwashe labarin abin da ya
faru duka tun daga lokacin da ta ga ana yi wa
gidansu lamba, da kuma yadda ta zo dibar mai a
cikin hajar bako, ta gane mutane ne a ciki, da
yadda ta kona su da mai, da kuma yadda ta ga
shugaban barayi ya bude gida cikin dare ya arce,
da ya gano cewa an kashe masa mutane.
Ali Baba ya yi mamaki a kan hikima da kuma
dabara ta wannan yarinya, gayar mamaki. Ya gode
mata, godiya mai yawa, kuma ya yi mata abishir
da wata kyauta mai tsoka, amma bai fada mata ko
mene ne ba. Ya tura ta ta kira masa wani
bawansa mai suna Abdallah.
Da Abdallah ya zo, Ali Baba ya fada masa abin da
ke faruwa. Ya ce yana so su tafi lambun da ya ke
cikin gidan su gina katon rami mai fadi da zurfi,
wanda zai iya daukar barayin nan duka, su rufe su
ciki. Ali Baba ya taimaka wa bawansa Abdallah
suka gina katon rami, Allah ya taimake su akwai
danshi a cikin lambun, saboda haka ba su sha
wata wahala ba wurin haka ramin.
Suka rika ciccibo gawar barayin nan, daya bayan
daya, suna jefawa cikin ramin duk da jakunkunan
da suke ciki, har suka jefa su duka. Suka mayar da
kasa suka rufe. Ali Baba ya gargadi bawan nan,
duk da yake ya san amintacce ne, a kan kada ya
kuskura ya yi wannan zance da kowa a waje.
Jakan barayin nan kuwa, sai Ali Baba ya rika dibar
biyu, uku, yana tura Abdallah da su kasuwa yana
sayar masa, tunda ba wani amfani zai yi da su ba,
har suka kare.
Shugaban barayi kuwa da ya gudu daga gidan Ali
Baba, sai ya koma maboyarsu a cikin daji. Ba da
jimawa ba, kadaici da kuma tsoro suka lullube shi,
ya ji kwata-kwata ba zai iya zama shi kadai a
cikin daji ba. Saboda haka sai ya debi wani abu
daga cikin dukiyar nan, ya yi shiri kamar wani
bakon alhaji, ya koma cikin gari.
Da ya isa cikin gari sai ya tasar wa fada. Aka yi
masa iso gun Sarki, ya ce shi bako ne, sunansa
Koja Husaini, yana so ya zauna a cikin wannan
gari idan Sarki ya yarda, idan ma zai samu gida na
siyarwa, to zai siya ya zauna a ciki. Sarki ya sa
dillalai suka nemo wa Koja Husaini gida, aka yi
ciniki ya biya. Kwamfa! Ashe gidan kuma yana
makwaftaka ne da tsohon gidan Ali Baba wanda
ya tashi a ciki, ya koma gidan Kasim, wanda kuma
yanzu babban dansa ne, saurayi dan kimanin
shekaru ashirin da uku, a ciki.
Koja Husaini ya tare cikin sabon gidansa, lokaci-
lokaci kuma yakan koma maboyarsu ya debo wani
abu daga cikin dukiyarsu, wadda yanzu ta zama
mallakarsa shi kadai. Amma ya kan yi taka-tsan-
tsan duk lokacin da zai tafi, domin kada ya ja
hankalin mutane su fara zarginsa. Kullum
zuciyarsa cike take da tunanin hanyar da zai bi ya
kashe Ali Baba.
Sannu a hankali Koja Husaini ya fara sabawa da
makocinsa, dan Ali Baba, duk da yake ba sa'arsa
ba ne, har ta kai ga wani lokaci suna zaunawa su
yi ta hira a tsakaninsu.

Ana nan wata rana sai Ali Baba ya kawo wa dansa
ziyara a gida, a lokacin kuma Koja Husaini na
zaune a kofar gidansa, karkashin wata bishiya,
yana hutawa. Da ganinsa, nan take Koja Husaini
ya shaida shi. Ali Baba ya shige gidan dansa, bai
ko lura da wani mutum ba, ballantana ya lura da
ana kallonsa.
Bayan wani lokaci, Ali Baba ya fito daga gidan ya
yi tafiyarsa. Ba a dade ba kuma sai ga dansa ya
fito, da ya ga Koja Husaini zaune a kofar gidansa,
sai ya nufi can domin su yi hira. A cikin hirar tasu
ne Koja Husaini ya fahimci cewa wannan yaro,
wanda ya zama tamkar abokinsa a halin yanzu,
dan Ali Baba ne, babban makiyinsa a duniya. Don
haka sai ya raya a zuciyarsa, bari ya ja shi a jika,
wata kila ta sanadiyarsa zai cimma burinsa na
kashe Ali Baba.
Tun daga wannan rana sai alakar Koja Husaini da
Dan Ali Baba ta dauki sabon salo. Koyaushe Koja
Husaini ba ya da wani aboki da ya wuce Dan Ali
Baba, ya yi ta jan sa a jika har suka shaku da juna
suka zama tamkar abokai sa'o'in juna.
Ina ya Allah, babu ya Allah! Ana nan sai matar Ali
Baba ta haihu. Tun kafin ranar suna Ali Baba ya
shirya wata 'yar gajeruwar liyafa ta cikin gida,
watau iyalansa da barorinsa kawai. Da Dan Ali
Baba zai je wurin liyafar sai ya gayyaci babban
abokinsa, Koja Husaini, domin ya raka shi. Koja
Husaini ya yi matukar farin ciki a ransa, damar da
yake ta faman jira kwana da kwanaki yanzu ta
samu. Idan suka tafi, zai yi iyakar kokarinsa ya
kebe da Ali Baba wani wuri, inda babu kowa, ya
kashe shi ya gudu, lokacin da duk hankulan
iyalansa suke wurin liyafar. Sai ya dauki wata
sharbebiyar wuka ya sulle ta a cikin
rigarsa, suka
tafi.

Ko da suka isa gidan, komai ya kankama. Dan Ali
Baba ya gabatar da abokinsa ga mahaifinsa,
sannan suka sami wuri suka zauna. Duka-duka
wurin liyafar bai wuce mutum biyar zuwa shida ba;
Ali Baba da matarsa, Dan Ali Baba da abokinsa
Koja Husaini, Abdallah bawan Ali Baba, sai kuma
yarinya Murjanatu da take ta faman kawo kayan
ciye-ciye da shaye-shaye.
Murjanatu na cikin rarraba abinci ga mahalarta
liyafa har ta zo kan Koja Husaini. Tana ganinsa,
nan take kwakwalwarta, mai kama da kwamfuta, ta
gane shi. Shugaban barayin nan ne ya sake
dawowa. Tabbas wannan zuwan ma, akwai
manufar da ya zo da ita, ba liyafar ce ta kawo shi
ba. Ta kanne abin a cikin ranta, ba ta ce komai ba,
ba ta kuma nuna alamun komai ba, tana tunanin
hanyar da za ta yi maganin wannan barawo.
Bayan liyafa ta kankama, kowa ya fara motsa
bakinsa da abin da aka tanadar. Tuni kuma
Murjanatu ta gano wata dabara da za ta kashe
wannan barawo. Ta rada wa bawan nan Abdallah,
ya dauko dundufarsa ya fara kida ita kuma za ta
yi rawa, kamar yadda suke yi wa Ali Baba a duk
lokacin da yake bukatar nishadi. Abdalla ya jawo
dundufarsa ta kida, ya fara kadawa a hankali,
dama kuma gwanin kida ne, ita kuma Murjanatu ta
tashi ta fara taka rawa, abin gwanin ban sha'awa.
Al'adar garin ce, idan mace tana rawa a cikin
maza, ta kan rike wata 'yar karamar wuka a
hannunta. Idan ta yi rawa, ta yi juyi, sai ta zo
gaban mutum ta daga wukar nan kamar za ta
daka masa ita a zuciya, sai ta juya wukar ta daka
masa marikin wukar. Sai a yi tafi, a yi shewa, ta
haka ake gane namiji mai tsoro da kuma jarumi.

Duk kasar kowa ya san da wannan al'ada, hatta
Koja Husaini ya san da haka.
Saboda haka lokacin da Murjanatu za ta fara rawa,
sai ta dauko 'yar karamar wuka ta rike a
hannunta, tuni ta ayyana abin da za ta yi a cikin
ranta. Ta fara rawa tana juyi, ta zo kan mai kida,
Abdallah, ta daga wukar kamar za ta daba masa
ita, sai ta daba masa kotarta, aka yi tafi. Ta wuce
wurin Dan Ali Baba, ta yi kamar yadda ta yi wa
Abdallah, ta wuce. Ta je kan Shugaban barayi, ta
daga wukar nan, ta tattara iyakar karfinta a
hannunta mai wukar ta kirba masa ita a kahon
zuciya. Nan take barawo ya fadi kasa yana shure-
shure har ya mutu.

Ko da Ali Baba da dansa suka ga wannan danyen
aiki da Murjanatu ta aikata, wanda ba su san dalili
ba, sai suka taso mata, hankalinsu a tashe, suka
far mata da fada, don me za ta kashe bakon da
suka gayyato, laifin me ya yi mata. Murjanatu ta
dakatar da su, sannan ta bayyana musu ko wane
ne wannan bako, sannan ta ce musu, "Duk da yake
ban san manufar da ya shigo da ita wannan gida
ba, amma na tabbata manufarsa ba ta alheri ce
ba."
Da suka duba jikin shugaban barayi, sai suka
samu sharbebiyar wuka sulle a cikin rigarsa.
Wannan shi ne karo na biyu ke nan da Murjanatu
ta kubutar da rayuwar Ali Baba daga halaka.

Saboda haka yanzu ne zai sanar da ita albishirin
da ya boye mata a cikin zuciyzrsa, wanda kuma ya
taba furta mata.
Ali Baba ya dubi Murjanatu ya ce, "Daga yau na
'yanta ki, kin zama 'ya mai cikakken iko, kuma
idan kin yarda ina so ki amince da dana ya zama
mijinki." Sannan ya juya wurin dansa ya ce da shi,
"Ya kai dana, na san da cewa ba za ka ki
amincewa da zabina ba, ka amince na aura maka
Murjanatu domin na tabbata ta dace da kai, kuma
ba domin ita ba da wannan abokin naka ya sami
galaba a kaina, dama ya yi kokarin yin abota da
kai ne domin ya samu ya kashe ni. Na tabbata da
bukatarsa ta biya, kai ma ba zai bar ka ba. Don
haka wannan yarinya ita ce sanadiyar kubutarmu
gaba daya."

Murjanatu da Dan Ali Baba suka amince da
junansu. Bayan 'yan kwanaki aka daura musu aure,
aka sha biki aka watse, mutanen gari suka yi ta sa
albarka, a kan wannan karimci da Ali Baba ya yi
wa yarinya Murjanatu, ga ta baiwa amam ya
'yanta ta kuma ya aurar da ita ga dansa, da ma
yarinya ce mai ladabi. Duk mutanen gari babu
wanda ya san abin da ya faru.
Ali Baba bai kara komawa maboyar 'yan fashin nan
ba, domin yana gudun ya hadu da sauran barayin
nan biyu da bai san abin da ya same su ba. Da
aka shekara ya ga babu wata barazana da barayin
nan suka kara yi masa, ran nan sai ya shirya ya
faki idon mutane ya dare saman dokinsa, ya nufi
dajin. Ya debo dukiyar ya aza kan dokinsa ya hawo
ya dawo.
Haka Ali Baba ya ci gaba da zuwa dajin nan daga
lokaci zuwa lokaci, yana debo dukiyar da barayin
nan suka tara yana kawo wa gida, sai dai duk
lokacin da ya je yakan yi sauri ya diba ya dawo
don tsoron kada sauran barayin biyu su tarar da
shi. Ya ci gaba da yin haka tsawon shekaru, ya
kwashe dukiyar duka ya kawo gida, kuma yana ci
gaba da kasuwancinsa a kasuwa, don haka babu
wanda ya san sirrunsu. Ya zamana babu mai arziki
duk fadin kasar kamar Ali Baba.
Yayi zamansa shi da iyalinsa cikin jin dadi da
kwanciyar hankali, har mai rabawa ta zo ta raba
su.
=| KARSHE |=
***
Alhamdulillah! Wannan shi ne karshen hikayar Ali
Baba da Barayi Arba'in, wacce muka kwashe
tsawon makonni bakwai muna kawo muku.

wandàni yusuf abdullahi A jibaga,
na kawo muku.
SAIMUN HADU AWANI SABOÑ LÀBARIN,

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment