Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi masa jana'iza, ita kuwa Murjanatu sai ta nufi shagon wani baduku, dattijo mai suna Baba Mustafa, domin dama dabi'arsa ce da an fito daga sallar subahi yake bude shagonsa.

Ta same shi a zaune cikin shagon, bayan ta yi masa sallama sun gaisa, sai ta ce da shi, "Baba Mustafa ina da wani aiki da nake so ka yi mini yanzu, amma da sharadi daya." Ta dauko dinari daya ta danka masa a hannu.

Ya yi sauri ya karbe yana murmushi, dama idonsa idon kudi kamar wuta da auduga ne, ya ce da ita, "Diyata, fadi abin da kike so na yi miki, ko menene idan dai zan iya yin sa, to zan yi miki shi duk da dai ban san ki ba, ban ma taba ganin ki ba."

Murjanatu ta ce da shi, "Jiya cikin dare barayi suka shiga gidanmu suka kashe mijina kuma suka sassara shi guntu-guntu. Ina so, a matsayinka na baduku, ka harhada gawarsa wuri daya ka dinke, yadda za a ji dadin yi masa jana'iza. Amma da sharadin zan rufe fuskarka da mayafi ta yadda ba za ka iya gane hanyar da muka bi zuwa gidan ba, kuma ba za ka iya gane gidan ba. Haka kuma idan ka gama zan sake rufe fuskarka na maido ka shagonka. Zan biya ka kudi mai yawa, ka yarda da wannan sharadi?"

Baba Mustafa ya ce ya amince. Murjanatu ta rufe masa fuska, ta ja hannunsa har suka isa gidan, ta bude kofa suka shiga ciki, ta ja shi har cikin dakin da gawar Kasim ta ke, sannan ta bude masa ido. Ta ce ya yi sauri ya hada shi masu jana'iza na nan zuwa. Nan take kuwa ba tare da bata lokaci ba Baba Mustafa ya dinke gawar Kasim wuri daya, kamar ba a taba sassara ta ba. Murjanatu ta ba shi kudi masu yawa, sannan ta rufe masa idanu ta mayar da shi shagonsa.

Aka yi jana'izar Kasim aka gama ba tare da kowa ya san gaskiyar abin da ya faru gare shi ba.

Su kuma barayin nan bayan kwana biyu suka koma maboyarsu, ga tsananin mamakinsu sai suka tarar da an dauke gawar mutumin da suka kashe, bayan wannan kuma an sake dibar musu dukiya. Cikin fushi, bakinsa na kumfa, babban yan fashin ya ce, "Ina rantsuwa da abin da zai kashe ni, hankali na ba zai kwanta ba har sai na nemo wanda ya gane sirrinmu, yana zuwa yana dibar mana dukiya, ko wane ne shi, kuma ko a ina ya ke cikin duniyar nan. Idan kuwa na same shi zan gana masa azabar da ba a taba yi wa wani abu mai rai irinta ba, kafin na kashe shi!"

*** *** ***

ZA MU CI GABA RANAR ALHAMIS DAI DAI WANNAN LOKACI, INSHA ALLAHU04. HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN

Bayan kwana biyu, barayi suka koma maboyarsu, ga tsananin mamakinsu sai suka tarar da an dauke gawar mutumin da suka kashe, bayan wannan kuma an sake dibar musu dukiya. Cikin fushi, bakinsa na kumfa, babban yan fashin ya ce, "Ina rantsuwa da abin da zai kashe ni, hankali na ba zai kwanta ba har sai na nemo wanda ya gane sirrinmu, yana zuwa yana dibar mana dukiya, ko wane ne shi, kuma ko a ina ya ke cikin duniyar nan. Idan kuwa na same shi zan gana masa azabar da ba a taba yi wa wani abu mai rai irinta ba, kafin na kashe shi!"

Ya ci gaba da cewa, "Ina so daya daga cikinku ya yi shiri irin na fatake, ya shiga cikin birni ya shako mana labari daga mutane, wata kila zai ji ana labarin wani mutum da aka kashe ta hanyar daddatsa jikinsa, ta haka za mu gane wanda ya zo nan ya dauke shi, kuma ya ke dibar mana dukiya."

Sai wani barawo daga cikinsu ya ce, "Ni zan tafi, kuma na yi alkawrin ba zan komo nan ba sai da cikakken labarin wannan mutum."
Babbansu ya ce, "Wannan aiki ne mai muhimmanci a wurinmu gaba daya, saboda haka idan har ka yi kuskuren da ka dawo nan ba tare da ka gano mana gidan wannan mutumin ba, to zan kashe ka."

Barawo ya ce ya yarda.

Ya yi shiri irin na matafiya, idan ka gan shi kamar wani mutumin kirki. Ya nufi birni. Ya iso cikin garin da sassafe. Da shigarsa cikin gari, sai ya hango wani mutum ya yi sammakon bude rumfarsa yana zaune a ciki. Da ya isa inda wannan mutumin ya ke, sai ya ga ashe dattijo ne, yana zaune yana dinkin takalmi. Ya yi mamakin wannan dattijo da yadda ya yi sammakon bude rumfarsa, bayan duk sauran rumfuna suna a rufe.

Barawo ya yi wa dattijo sallama. Bayan ya zauna sun gama gaisawa sai ya ce masa, "Baba, amma Allah ya hore maka kaifin ido, ta yaya kake iya gani cikin duhun safiyar nan har kake dinki, ga shi kuma ka tsufa?"

Dattijo ya ce, "Ga alama dai kai bako ne a wannan gari namu, idan ba haka ba waye bai sanni ba da kuma lakanin da ake yi mini na 'Baba Mustafa, dila mai idon zinari' ba. Tun ina dan shekara takwas na koyi wannan sana'a ta dinki daga mahaifina, kuma tun lokacin ita nake yi. Kai bari ma ka ji, saboda gwanancewata a dinki, har gawar mutum na taba hadawa na dinke ta wuri daya, bayan da barayi suka yi mata gunduwa-gunduwa, kuma a cikin daki mai duhu na yi wannan aiki."

Barawo ya bude baki cikin mamaki, ya ce a ransa, ga dukkan alamu na taki sa'a a kan wannan bincike da na fito yi, lalle ta hanyar dattijon nan zan sami abin da na fito nema. Ya dubi Baba Mustafa cikin mamaki ya ce, "Ka taba dinke gawar mutum fa ka ce? Kuma a cikin daki mai duhu? Wannan basira taka da yawa ta ke. Amma dai tun kana dan saurayinka ka yi wannan aiki ko?"

Baba Mustafa ya yi dariya ya ce, "Ba a yi kwana hudu da na yi wannan aiki ba. Wata rana ne, da sassafe kamar yanzu, wata yarinya.... Af! Na manta an rantsar da ni a kan cewa kada na yi wannan zance da kowa."

Da jin haka, sai barawo ya jawo jakarsa, ya bude ta sosai ta yadda Baba Mustafa zai iya ganin kudin da ke ciki. Ya lura da yadda Baba Mustafa ya yi ajiyar zuciya lokacin da ya ga kudin da ke makare a cikin jakar. Ya debo kudin ya ba shi, ya ce masa, "Karbi wannan ka fitar da kono a kan rantsuwar da ka yi, ina so ka fada mini wannan labari, kuma ka kai ni gidan da ka yi wannan aiki. Idan ka yi mini wannan, hakika zan biya ka da kudi mai yawan gaske."

Baba Mustafa ya ce, "Idan dai za ka biya ni ai sai na fada maka labarin duka." Barawo ya debo kudi mai yawa ya ba Baba Mustafa. Shi kuma ya fede masa biri har wutsiya.

Barawo ya ce, "Tashi mu je maza ka kai ni gidan, kafin mutane su fara fitowa zuwa wurin harkokinsu."

Baba Mustafa ya ce, "Ba ka ji labarin dai dai ba ne? Ai yarinyar rufe mini ido ta yi lokacin da za ta kai ni gidan, ba ta bude mini ido ba sai da muka shiga cikin dakin da gawar ta ke. Kuma ina gama aikin ta sake rufe mini ido, sai da muka zo nan sannan ta bude. Ba zan iya gane gidan ba, ko kalar fentinsa ban samu damar gani ba ballantana na ce zan iya shaida shi."

Barawo ya ce, "Ka yi amfani da hikimarka da basirarka mana, ni ma in rufe maka ido ka rika misalta hanyar da kuka bi a cikin zuciyarka har mu isa gidan. Ina tsammanin za ka iya yin wannan."

Baba Mustafa ya ce, "Kwarai kuwa zan iya, domin duk kwanar da muka bi zan iya kiyasta ta a cikin zuciyata. Kai bari ma ta wannan, har takun da muka yi kafin mu isa gidan da kuma bayan mun dawo na lissafe su kaf. Ba fa banza ake yi mini lakabi da dila ba yaro."

Suka tashi, barawo ya sami wani kyalle ya rufe idon Baba Mustafa. Suka shiga cikin gari. Bayan sun dan taba tafiya ta wani lokaci, sai suka iso gaban wani gida. Baba Mustafa ya tsaya, ya ce da barawon nan, "A dai dai nan ne na ji yarinyar nan ta bude kofar gida muka shiga daga ciki."

Barawo ya bude wa Baba Mustafa fuskarsa, ya ce, "Ka tabbata wannan gidan ne?" Baba Mustafa ya tabbatar masa da cewa ko shakka babu.

Barawo ya dubi gidan nan da kyau, da kalar fentinsa. Ga mamakinsa sai ya ga ai kusan duka gidajen unguwar kalar gininsu guda, kuma duk fentinsu kala guda ne. Sai lamarin ya daure masa kai, ya ga cewa idan ya koma ya fada wa 'yan uwansa ya gane gidan, idan suka zo cikin dare ba zai iya shaida gidan har ya nuna shi ba. Don haka sai ya bude jakarsa ya dauko wani bakin fenti da yayi amfani da shi wajen canja kamannunsa, ya zana wata 'yar alama a jikin kofar gidan, yadda idan suka dawo cikin dare zai gane gidan. Ya sallami Baba Mustafa ya koma rumfarsa. Shi kuma ya juya zuwa cikin daji wurin 'yan uwansa domin ya shaida musu cewa bukata ta biya.

***

ZA MU CI GABA RANAR ASABAR DAI DAI WANNAN LOKACI, INSHA ALLAH005. HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN

Al'adar garin ce idan mutum ya mutu, 'ya 'yansa ne za su gaji dukan dukiyarsa, idan kuwa ba shi da 'ya 'ya, to 'yan uwansa ne za su gaje shi, idan babu kuma sai matarsa ta gaje shi, idan ba shi da mata sai a saka dukiyarsa a baitulmali.

Bayan mutuwar Kasim, kasancewar ba shi da 'ya 'ya, sai Ali Baba ya gaji dukan dukiyarsa, da gidansa da kuma kuyangar nan tasa mai tsananin hikima, watau Murjanatu. Ali Baba ya kwashe dukan dukiyar da ya samu daga taskar 'yan fashin nan ya koma gidan Kasim tare da matarsa. Ita kuma matar Kasim ta koma gidan mahaifinta.

A cikin wannan halin ne barawon nan ya hilaci dattijo Baba Mustafa har ya kawo shi gidan da Ali Baba ya ke ciki da matarsa da kuyangarsa. Kuma ya yi wa gidan 'yar alama da bakin fenti yadda idan suka dawo cikin dare tare da sauran barayin za su yi saurin shaida gidan.

Bayan barawo ya koma wurin 'yan uwansa, cike da farin cikin gane gidan Ali Bab, ya shaida musu cewa bukata ta biya. Barayi suka yi murna da wannan labari. Babban su ya ce, "Kowa ya zauna cikin shiri, domin yau cikin dare za mu tafi mu kashe wannan mutum, sannan mu kwashe dukan dukiyar da muka samu a cikin gidansa." Barayi duka suka shirya suna jiran dare ya yi.

Ashe kuma bayan tafiyar barawo da Baba Mustafa daga kofar gidan Ali Baba, Murjanatu ta fito domin ta kai sako wani gida. Bayan ta dawo, har za ta shiga gida, sai ta kyalla ido ta ga an yi wata 'yar alama da bakin fenti a jikin kofar gidansu. Ta duba kofar makwabtansu ba ta ga irin wannan alama ba. Ta kuma duba wani gidan, ba ta ga wannan alama ba, ta sa hannu wai ta goge alamar, amma ta ki goguwa. Sai jikinta ya ba ta lalle wannan alama da aka zana a kofar gidansu akwai wata manufa a ciki, ruwa ba ya tsami banza.

Murjanatu ta shiga gida ta samo bakin fenti, ta bi dukkan kofofin gidajen makwabtansu ta yi musu irin 'yar alamar da ta gani a kofar gidansu. Ta ja bakinta ta tsuke, ba ta fada wa kowa ba.

A cikin daji kuwa, barayi sun shirya tsab domin tunkarar gidan Ali Baba, Da lokaci ya yi, suka shirya suka nufo gari. Da suka iso bakin gari, sai suka dakata sai da dare ya raba tsakiya, ba a jin motsin komai a cikin garin, sannan suka shiga.

Barawon da ya gane gidan yana gaba suna biye da shi har suka iso unguwar da gidan Ali Baba ya ke ciki. Da zuwansu, sai suka shiga haska fitulu a kofar gidajen domin gano gidan da barawo ya yi wa lamba. Can sai wani daga cikinsu ya ce, "Ga alamar nan a jikin kofar wancan gidan." Wani kuma ya ce, "A'a, ga gidan nan." Can sai kuma wani ya kyalla ido ya ga alamar a jikin kofar wani gidan dabam.

Da barayin nan suka duba da kyau, sai suka ga ashe duka gidajen unguwar an yi musu lamba. Sai shugaban 'yan fashi ya dubi barawon da suka aiko ya ce, "Sai ka nuna mana gidan da ka gano."

Barawo cikin kaduwa ya ce, "Wallahi ni gida guda na yi wa lamba, ban san me ke faruwa ba."

Shugaban barayi ya ce, "Wane ne daga cikinsu ka yi wa lamba?"

Barawo ya duba, ya kara dubawa, ya kasa gane gidan da Baba Mustafa ya nuna masa. Sai ya ce, "Wallahi ba zan iya shaida shi ba a halin yanzu."

Shugaban barayi ya fusata ya ce, "Ka san ba za ka iya gane gidan ba ka sa muka zo, muka yi wahalar banza, za mu koma a banza a wofi? Lalle hukunci zai hau kanka." Ya ba da umurni aka daure wannan barawo a kan dokinsa, suka kora shi suka nufi cikin daji, wurin maboyarsu.

Da suka isa wurin da dutse ya ke, suka bude shi suka shiga daga ciki. Shugaban 'yan fashi ya sa takobinsa ya dauke kan barawon nan da ya kasa gane gidan Ali Baba. Sannan ya juyo ga sauran barayi ya ce,"Wa zai faranta mini rai, ya shiga cikin gari ya gano mana gidan mutumin nan, ni kuwa in saka masa da abinda duk ya ke bukata?"

Duk barayin nan suka yi jim, can sai wani ya yunkuro daga cikinsu ya ce, "Ni zan tafi, kuma ba zan dawo ba sai na gano takamaiman gidan wannan mutumin, idan kuma ban gane ba na yarda a zartar da hukuncin kisa a kaina, kamar yadda aka yi wa na farko."

Barawo ya yi shiri, ya canja kamanninsa kamar wani mutumin kirki, ya nufi cikin gari. Da ya isa cikin gari, sai ya tasar wa rumfar Baba Mustafa, baduku. Ya same shi zaune yana dinkin wata jakar fata.

Barawo ya yi amfani da dabarar da abokinsa na farko ya yi, ya ja hankalin dattijo da kudi, har ya kai shi dai dai kofar gidan Ali Baba. Bayan da ya sallami dattijon, sai ya dauko jan fenti a cikin jakarsa, ya sami wani wuri a jikin gidan, wanda ba duka idon mutum zai yi saurin kaiwa ga wurin ba, ya yi 'yar alama wadda za ta sa ya gane gidan.

Bayan ya tafi, sai Murjanatu ta fito zuwa wurin da aka aike ta. Bayan ta dawo, kafin ta shiga gida sai kuwa idonta ya kai ga alamar da barawon nan ya yi da jan fenti. Ta tsaya tana tunanin shin wai me ake nufi da wadan nan alamomi da ake yi musu a jikin gida? Ta je ta samo kalar fentin, ta bi dukan gidajen makwabtansu ta yi musu irin wannan 'yar alamar. Ta shiga gida ba ta fada wa kowa ba.

Shi kuwa barawo da ya koma sai ya shaida wa shugabnsu cewa ya gane gidan, don haka su shirya da dare su shiga gari su kashe mai gidan sannan su kwashe dukan dukiyar da suka samu a cikin gidan.

Da lokaci ya yi, barayi suka shirya suka shiga cikin garin da dare, lokacin kuwa duk mutane kowa ya yi barci, suka tasar wa unguwar da Ali Baba ya ke da iyalinsa. Da isarsu sai shugabansu ya ce da barawon nan, "Maza nuna mana gidan mu aikata abin da ya kawo mu, mu juya kafin gari ya waye."

Barawo ya haska fitilarsa a jikin gida na farko, dai dai inda ya san ya yi alama, sai kuwa ga 'yar alamar da jan fenti. Har za su balle gidan su shiga, sai shugabansu ya ce, "Bari mu fara tabbatar wa da kanmu cewa wannan shi ne gidan da muke nema, kada a sami kuskuren da aka samu jiya, ku tafi ku haska sauran gidajen, idan babu wani gida mai irin wannan alama, to wannan shi ne gidan da muke nema."

Sauran barayi suka warwatsu cikin unguwar, duk gidan da suka haska fitilarsu sai su ga irin wannan alama a jiki. Suka zo suka fada wa shugabansu. Shugaban ya tambayi barawon ko zai iya gane gidan a cikin sauran gidajen da suke da alama iri daya? Barawo ya ce ba zai iya ba.

Suka koma maboyarsu. Shi ma wannan barawo aka zartar masa da hukuncin kisa. Da shugabansu ya ga cikin dan kankanin lokaci ya yi asarar mutum biyu daga cikin yaransa, sai ransa ya baci, ya yi fushi, fushi mai tsanani. Ya yi rantsuwa da abin da zai kashe shi cewa, shi da kansa zai shiga gari ya gane ainihin wannan gida da suke nema, wanda ya yi sanadiyyar rasa yaransa biyu. Lalle mai wannan gida zai dandana azaba mai tsanani kafin su kashe shi.

Washe gari shugaban barayi ya yi shiri da kansa ya shiga gari. Ya yi amfani da dabarar da barayin nan biyu suka yi amfani da ita, ta saye dattijo baduku, watau Baba Mustafa da kudi.

Da suka zo kofar gidan, shugaban barayi ya sallami dattijo. Ya dubi gidan da kyau tun daga kasa har bisa, ya yi murmushi ya ce a ransa, "Yaro dai yaro ne, in ba halin yarinta ba mene na abin yi wa wannan gida alama? Wannan makeken dutsen da ya ke kwance gab da kofar shiga gidan ai ya isa alamar da za a gane gidan, ko ba shi ba ma, waccan tsagawar da bangon gidan ya yi ita ma alama ce babba ta gane gidan." Ya sake yin murmushi, ya dubi gidan ya ce, "Mai gidan nan yau kwananka ya kare, Allah ya kai mu dare." Ya koma gun 'yan uwansa.

Da Murjanatu ta fito daga gida, bayan tafiyar shugaban barayi, ta tsaya ta duba jikin gidansu da kyau ko za ta ga wata sabuwar alama, amma ba ta gani ba. Ta ce a ranta, "Wata kila mai yi musu lamba a jikin gida ya gaji ya watsar, ko wane ne? Oho! Wata kila ma yara ne." Ta kama harakokin gabanta, ba ta koma kan batun ba.

***
Ga dukan alamu an kusa kashe BOSS. Ku biyo mu zuwa ranan alhamis dai dai wannan lokaci domin jin karshen wannan labari.

Naku: WAZIRI AKU

Ga dukan alamu an kusa kashe BOSS. Ku biyo mu06. HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN

Lokacin da shugaban barayi ya koma cikin daji
wajen 'yan uwansa, ya shaida musu cewa ya gane
gidan Ali Baba. Dabarar da za su yi sur kashe shi,
ba tare da sun ja hankalin jama'ar garin ba ita ce,
yana so su tafi inda suke boye dabbobinsu, su zo
da jakai goma sha tara, sannan su shiga cikin
kasuwar garin su siyo jakunkuna na fata, wadan da
ake dura wa mai, manya-manya wadan da mutum
zai iya shiga cikinsu, guda talatin da takwas.
Ya ci gaba da cewa, "Idan muka hada wadan nan
dabbobi da kuma jakunkunan dura mai, kowane
mutum daya zai shiga cikin jaka daya da
takobinsa, jaka dayar da za ta rage, zan dura man
girki a cikinta. Zan dora ku gaba daya a kan jakai,
duk mutum biyu jaki daya. Mutum na karshe zan
dora shi tare da jakar da take da mai. Ni kuma zan
yi shigar farke, na kora jakunan nan zuwa cikin
gari. Zan dakata har zuwa faduwar rana sannan
na shiga cikin gari, na je gidan mutumin na shaida
masa cewa ni farke ne, na kawo man girki ne, ga
shi dare ya yi ban samu shiga kasuwa ba. Ina so
ya taimaka mini da wurin da zan sauke kayana a
gidansa, idan gari ya waye sai na dauka na shiga
kasuwa."
Shugaban barayi ya ci gaba da cewa, "Na san
cewa zai yarda da bukatata. To, zan sauke ku na
bar ku a wajen. Idan na ji gari ya yi shiru, kowa ya
yi barci, zan zo na rika taba kowace jaka, duk
wanda ya ji na taba jakarsa to sai ya fito, lokaci
ya yi ke nan da za mu aikata abin da za mu
aikata. Mu kashe shi da iyalinsa duka, sannan mu
kwashe dukan dukiyar da take gidan, mu dora wa
dabbobin nan mu koro su mu dawo. Ina fatar kun
fahimce ni."
Sauran barayi suka ce sun fahimta. Ya rarraba su,
ya aika wasu su zo da jakai, sannan ya aika wasu
su tafi cikin gari su siyo jakunan dura mai da
kuma man da zai cika jaka daya. Duka suka tafi
neman abin da shugabansu ya umurce su da
samowa.
Bayan kwana biyu barayin nan suka gama shirinsu
tsaf. Kowane barawo ya shiga cikin jaka daya rike
da takobinsa. Da suka gama shiga gaba daya.
Shugaban barayi ya yi sadi da su a kan jakai, duk
jaki daya ya dauki barawo biyu a cikin jaka. Jaki
na karshe ya dauki barawo daya da jakar mai.
Shugaban barayi ya canja kamanninsa, ya yi shiga
kamar farke, ya kora jakai dauke da barayi suka
nufi cikin gari. Bayan tafiyar wani dan lokaci, suka
isa bakin gari, dab da rana za ta fadi. Da shigarsu
cikin gari, shugabn barayi ya kora dabbobin nan ya
nufi gidan Ali Baba da su. Yana isa kuwa ya yi
sa'a da Ali Baba ya dawo daga kasuwa, zai shiga
gida ke nan, barawo ya dakatar da shi.
Bayan sun gaisa, sai barawo ya ce wa Ali Baba,
"Ni farke ne, na zo da man girki ne domin kai wa
kasuwa na sayar, ga shi dare ya yi mini ban samu
shiga kasuwar ba, ko zan samu alfarmar masauki a
wurinka da kuma wurin da zan sauke kayana kafin
gobe da safe na shiga kasuwa?"
Ali Baba ya ce, "Wa zai ki bako? Ai bako rahama
ne. Babu komai, shigo da kayanka daga ciki ka
sauke kafin Allah ya kai mu gobe. Zan dawo na
nuna maka dakin da za ka kwana idan ka gama
sauke kayan." Barawo ya yi ta godiya, kamar
mutumin kirki. Ali Baba kuwa ya wuce cikin gida,
ya bar barawo ya na sauke kayansa a farfajiyar
gidan.

Da Ali Baba ya shiga cikin gida, sai ya fada wa
matarsa da kuyangarsa Murjanatu cewa ya yi
bako. Ya ce, "Farke ne ya zo da man girki zai kai
kasuwa ya siyar amma dare ya yi masa, don haka
zai kwana a nan gidan tare da kayansa zuwa gobe
da safe. Yanzu zan fita zuwa farfajiyar gidan mu
kara gaisawa da shi, a kai mini abinci na can, za
mu ci tare." Suka amsa masa da to. Ya fita.
Ko da ya fita ya tarar da shugaban barayi ya
gama sauke kayansa. Ali Baba ya nuna masa
dakin da zai kwana. Barawo ya kara yin godiya,
sannan ya ce wa Ali Baba yana so ya nuna masa
cikin gari domin bude ido, tun da shi bako ne. Ali
Baba ya ce masa to, amma ya dakata sai sun ci
abinci tukuna.
Murjanatu ta kawo musu abinci, har ta juya za ta
tafi sai Ali Baba ya ce da ita, "Idan mun gama cin
abinci za mu shiga cikin gari ni da bakona, akwai
kifi na nan na siyo, ina so ki soya mana shi kafin
mu dawo daga cikin gari." Murjantu ta amsa cikin
girmamawa, ta tafi.
Bayan Ali Baba da barawo sun gama cin abinci,
sai suka tashi suka nufi cikin gari. Ita kuma
kuyanga Murjanatu ta dauko kifi ta nufi dakin dafa
abinci domin soyawa kamar yadda aka umurce ta.

Bayan ta hura wuta, ta dora tasar suya, sai ta
jawo jakar da ake ajiye mai a ciki, sai ta ji ta
kwambar babu komai a ciki. Ashe ta manta sauran
man ne ta yi abinci da shi. Ga shi dare ya yi
ballantana a tafi kasuwa a siyo. Nan take sai ta
tuna, "Af! Shin bakon maigida mai ne ya zo da shi
domin siyarwa kasuwa ba? Bari na je wurin da ya
sauke man, na debo wanda zan soya musu kifin da
shi, alabashi idan maigida ya dawo sai in fada
masa, sai ya saye jakar man da na diba gaba
daya."
Ta dauki abin dibar mai ta nufi inda shugaban
barayi ya sauke kaya. Tana zuwa sai ta taba jakar
mai daya za ta bude, sai ta ji an ce, "Lokaci ya yi
ne?" Sai abin ya bata mamaki, nan da nan ta gane
abin da ake shirin kulla wa maigidanta, sai ta
canja murya kamar namiji ta ce, "Da saura!"
Ta nufi wata jakar za ta buda, sai ta ji an ce,
"Lokaci ya yi ne?" Ta kara canja murya ta ce, "Da
saura!" Sai da ta bi duka jakunkunan nan guda
talatin da bakwai, ta gane duka mutane ne a
cikinsu, sai guda daya ce

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment