Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaisa, kallonsa ya maida kan SONA dake kallonsa, suna had'a ido ta sun kuyar da k'anta, murmushi yay yace " ja jikin, alhamdulillah ta basa amsa a ta kaice"
Yace " masha Allah ki shirya Allura zan miki, da sauri ta dago da kanta sukayi ido biyu, marairai ce Fuska tayi tace " ni dai na samu sauki basai ammin wani Allura ba, na bar maka k'yauta"
Yana murmushi yace " no sai fa na miki"
Kukan shugub'a ta fashe dashi tace " ni dai wlh banaso"
Dariya yayi yace " okay kiyi hakuri sarkin shugub'a da wasa nake miki, murmushi tayi tace " wlh har naji dad'i"
Dariya su Momy sukayi Amma banda Saif dake lasar wayar sa"
Sallamar su yay a tare suka fito daman sun gama shiryawa, rakasu yayi har  Motar su,sanda yaga tafiyar su kafin ya koma ciki"

Direct gida suka wuce, suna parking dukan su suka shige cikin parlor, dai yayi da saukowar Daddy Yana murmushi yace " my daughter ya jikin?" Murmushi tay tace " alhamdulillah"
Masha Allah, gaishe shi Fatu tayi ya amsa cikin sakin fuska yana tambayarta ya jikin SONA tace" da sauki sosai"
toh Allah ya kara sauki ya kare na gaba" da amen suka amsa, tare da mikewa suka haura sama"
Daddy yace " wai son yaushe zaka fara aiki ne?"
Murmushi yay  yace "daga gobe insha Allah" toh Allah ya kaimu nidai bari na wuce office sai na dawo"
Momy tace " breakfast fa?" No karki damu zanyi a office" tace " please ka tsaya bari na had'a ma mai sauki"
Murmushi yayi yace " no akwai meeting da zauna yanzu" okay Allah ya bada sa'a"
Da amen ya amsa tare da ficewa daga parlor, mikewa tay itama ta haura sama"
Suna shiga bedroom Fatu ta fada toilet tay wanka ta fito ta shirya cikin dogowar riga ta atampa sai k'amshi take zubawa, kallo SONA tayi tace " kema kije ki zuba ruwa zakiji dad'i sosai, ni kuma bari naje naga me za'a mu hada breakfast"
Okay thank you so much dear"
Nifa malama ki dinga min yaren da nakeji ki daina min wanan yaren"
Murmushi tayi tace " toh shikenan kema ai zaki dinga ji kwanan nan, ngd sosai toh"
Murmushi k'awai ta fita daga dakin direct ta wuce bedroom din Momy, da sallama ta shiga, amsawa Momy tayi tace " my daughter" Fatu tace " me zamu girka?" Murmushi tay tace " muje kitchen muyi abu mai sauki tunda rana ya d'aga"
Wucewa kitchen din sukayi, ferfesu kaza sukayi sai kuma indo me da kwai, suna gamawa Fatu ta jera komai a dining, Momy tace " kima Yayan ku mgn da SONA su sauko" tom Momy, bedroom dinsu ta fara shiga tama SONA mgn kafin ta wuce na Saif, a hankali ta tura kofar parlor ta shiga da sallama, ba kowa a parlor hakan ya sata wucewa bedroom dinsa kai tsaye, turu kofar bedroom din tay ta shiga, a zaune ta kalleshi yana danna laptop dinsa,  dago da kansa yay jin an bude kofar anshigo ko sallama babu, suna hada ido ta wani dauke kanta, shikuma hada fuska yay yace " uban me kikazo min a daki ko sallama babu?"
Harara ta wurga masa tare da murgud'a masa baki tace " Momy ce tace na fad'ama ka fito kayi breakfast, shiyasa ka ganni inba haka ba mezan zo na maka"
Kallonta yay daga sama har k'asa yace " ke zonan"
Uban me zan maka, a fusace yace " ke har kin isah ina mgn kina mgn"
Tabe baki tayi tace " wanan dai ka ta d'ama ta fada tare da ficewa daga dakin, ai kuwa saurin mikewa yay yabi bayanta da sauri tana ko karin fita kenan ya....!

Share fisabilliah Habibaty 🥰
[1/21, 8:32 PM] +234 706 120 4735: 👧🏻 MIJIN YARINYA 👧🏻

Story and written

By Fatima Mrs Ahfat

ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚

Bismillahir rahmanin Rahim

Page 21

___________ Tana ko karin fita kenan yayi saurin kamuta ta fada jikinsa, yace " wa kikema ma rashin kunya ya fada tare da matse mata bakinta da karfi sanda tayi yar kara"
Da k'yar tace " don Allah Yaya kayi hakuri wlh tsubutar bakine, kasan bakin nawa baya iya yin shiru shiyasa, amma don Allah kayi hakuri muje kayi breakfast kar yunwa ta illa taka k'aji ko"
Tureta yay yace " idan kika sake min rashin kunya wlh sai na miki dukan tsiya"
Zaro ido tayi tace " k'ai k'ai Yaya duka fa Allah ya tsareni ai duka kam na wuce wannan ai yanzo"
Yace " me kikece ?" Ya fad'a tare da matsota"
Tace " a'a Yaya nidai kai abunda nace shine kanka naja shiyasa nake yinka, tana fad'ar haka tafice da gudu ta barshi, Shima binta yay suka fito parlor, kara sawa dining din tay tace " gashin fitowa" ta fada tareda zama kan kujera kusa da SONA domin harta fito"
Kara sawa shima yayi ya zauna suna hada ido da Fatu ya wani zabga mata harara, ta masa murmushi"
Suna gama cin abincin ya kalle Momy yace " Momy nasamo mata school din d'aya dace ta shiga insha Allah gobe sai SONA ta kaita"
Murmushi Momy tay tace " okay thank you my son"
Murmushi yay yana kallon Fatu dake kallonsa tana murmushi"
Shugub'e Fuska SONA tay tace " ni kuma Yaya?"
Eh ya fada atakaice"inaga ai idan ka kaita zaifi tunda kai kayi komai"
Harara ya wasa mata yace " idan ba zaki kaita ki bari, yana fad'ar haka ya mike ya bar wajen"
Binsa da kallo k'awai Momy tay tana murmushi,ta mike tare da cewa" karki manta baki sha maganin kiba SONA"
Okay Momy yanzu kuwa zansha"
mikewa Fatu tay ta tattara kwanukan abincin ta kai kitchen ta dawo SONA tace " sannu da aiki"
Murmushi tay tace " yawwa tashi muje kisha maganin ki naga alamun baki son shan magani"
Murmushi SONA tay tace " naga Alamun halinku d'aya da Yaya idan yasa mutun a gaba ya shiga uku"
Dariya Fatu tayi tace" rabani da wanna masifar"
Dariya gaba dayan sukayi suka haura sama"
****************Bangaren Ruky kuwa wani irin farin ciki ta tashi dashi cikin ranta domin Yau abunda ta dad'e tana nema zata sameshi"
Bayan sunyi waya da Saif yace mata zaizo la'asar ta mike daga kwanciyar da take ta bud'e wardrobe dinta ta fitoda wani doguwar riga ta lace me kyau, ta feshe shi da turaren da Boka ya bata tana murmushi ta ajiyeshi gefe"
Fitowa parlor tayi ta samu Anty na gyara wa su Addul takalmin su zasu tafi school, zama tay tace " sannu da aiki Anty"
Tabe baki tay tace " sai yau aka ga daman yimin sannu?"
Murmushi tay tace " ah ah Anty kiyi hakuri abun bai kai haka ba"
Bata ce komai ba taci gaba da gyara su, tana gama shiryasu ta musu addu'a driver ya fita dasu suna mata bye ² kallonta ta maida kan Ruky tace"
Uban me kike so naga kin min k'uri da ido?"
Murmushi tay domin yau dinnan tana cikin farin ciki kome zakace mata bazata damuba" tace " uhmm daman zanyi bako ne inason na masa girki"
Hmmm ba gaki ga kitchen dinba sai kiyi"
Eh toh daman dai ni dai ban iya girki ba shiyasa na tambayeki, tsaki Anty taja tace " ga ranan tazo ai abunda nake fada mikin kenan, kin girma baki san kin girma ba, kin kai 25 year amma ko rice baki iya girkawa sai dai a girka a baki"
Haba Anty ki taimakamin mana wlh girkin nada muhinman cine nayishi"
Mikewa Anty tayi daga zaunen da take tace " ni ba abunda zan miki kije zulai ta kwoya miki, ni aiki zan tafi" tana fad'ar haka ta haura sama"
Harara ta bita dashi tace " aikin banza girki dai sai nayi koma na cika burina"
Zulai! Zulai !! Zulai!!!" Ta kwalawa mata kira, jiki na mari zulai ta karoso tace " gani ranki ya dad'e"
Sanda ta harareta tace " ina son ki girka min joluf rice and pape chicken, nan da karfe 3 ki tabbatar kin gama"
Tom insha Allah cewar zulai"
Mikewa tay ta wuce bedroom dinta, tana shiga wayarta ta dauka ta kira Sumy bayan sun gaisa tace " yaune fa mutumin zai zo"
Wow da gaske?" Kice yau kuma kina da babban bako kenan?"
Tana murmushi tace " sosai kuwa gaskiya yau ina farin ciki mara misiltuwa"
Allah K'awata yaka mata ace nazo na tayaki farin Cikin yau dinan ,kinga nima sai mu gaisa dashi tunda ban taba ganin sab'a"
Dariya Ruky tay tace " hakane kuma fa k'awa, sai kinzo inanan ina jiranki"
Tom shikenan sai nazo"
Sallama sukayi ta kashe wayarta ta kwanta tanà jiran lkc yyi kawai ta shirya"
Sumy kuwa tana kashe wayar tace " hmmm bari naga idan dani yafi dacewa sai dai ki hakura, k'amar yanda kika jefa Yaya na cikin wani hali kema sai kin d'addani hakan"
************** Bangaren Saif kuwa bedroom dinsa ya koma yaci gaba da aikinsa domin Yana son ya gama komai yau, domin yana son ya fara aiki gobe, gashi goben karfe 9 yana da meeting din dazai shiga a'kan cigabar company nasu"
Shida gamawa har karfe 3 yana gamawa ya hada comai ya ajiye, toilet kawai ya fad'a, wanka yay tare da d'auro Alwala ya fito d'aure da towel, Jallabiya fari yasa yay Sallah la'asar"
Yana gamawa gaban dressing mirror ya tsaya tare da gyara suman kansa ya safa body lotion dinsa tare da feshe jikinsa body spray masu dad'in kamshi, wardrobe ya bude tare da dauko boxers,singlet, da wando jeans blue and white t_shirt wanda aka rubuta Handsome guy a jikin da blue color, ya sanya a jikinsa ba karamin k'yau yayi ba , agogo ya sanya tare da daukan white combs ya sanya, masha Allah saiya kara yin kyau sosai, jikinsa ya tsake bi da turarunruka masu k'amshi ya dauki wayoyinsa da key car dinsa ya fito, domin yana so d'aga gidan su Ruky ya wuce gun Hafiz,
Kicibus sukayi da Fatu d'atayi shirin tafiya islamiya"
Tana kallonsa sanda gabanta ya Fadi, bata san sanda tace " Yaya ina zakaje haka kayi wanan uban ado haka?"
Harara ya bita dashi yace " inda kika aikeni"
Tace " don Allah Yaya karka fita"
Wani irin kallo ya jefeta dashi yace " yaushe reni ta shiga tsakanin mu haka?"
Tace " ah wlh ba wani raini kawai dai inajin k'amar wani abu zai faru"
Tsaki yaja yace " aniyar ki ta biki, yana fad'ar haka ya fice daga parlor"
Girgiza kai k'awai tayi itama ta fice tana mamakin mesa tunda ta kalleshi gabanta ke fad'uwa"
Yana fita ya kira Ruky yace " gashinan zuwa"
Ruky data gama shirinta sab ta feshe jikinta turaren Boka tana jiran isowar sane tace " Sumy gashinan fa zuwa" murmushi tay tace " Allah kawo shi Lafiya naga wani irin guy ne kike rawan kafa akansa haka" dariya kawai tayi"
A bakin get din gidan yay hon da sauri me gad'i ya leka ganin shine ya tsashi bud'e masa get din da sauri ya shiga, parking yay ya fito daga motar gaisawa sukayi da me gad'i yace " tana ciki ne?" Eh tanan tace ka shigo inka karasa"
Murmushi kawai yay ya fara tafiya hankali gaban sa na fad'uwa k'amar ya koma haka yakeji Amma ya d'aure kawai ya shiga parlor da sallama, lokaci daya yaji wani irin shuuuu a cikin kan.......!


Mrs Ahfat ✍️

Comment and sharen fisabilliah Habibaty 🥰
[1/21, 8:32 PM] +234 706 120 4735: 👧🏻 *MIJIN YARINYA* 👧🏻

I just published "page 19" of my story "MIJIN YARINYA". https://www.wattpad.com/1179219048?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Asfats&wp_originator=NThwEb%2FTG8PMhMZYIlqw4PbgiQ72EDZuXFPUzABksO1sd0uGQZgR2ILFG%2FeY2Y0wyExBZ8QbpJwrecPkJcgNlv4CDnKkoXAxMeo%2FpVUOsWswSQlh2dnK1E3GOdroKdLm

Vote comment and share

*Story and written*

*By Fatima Msr Ahfat*

*ELEGANT ONLINE WRITERs* 📚

*Bismillahir rahmanin Rahim*

*Page 19*

__________________ Yace"  meya sameki kike kuka?" Cikin shenshekan kuka take nuna musa dakin su tana tace" SONA zata mutu Yaya
"What cewar Momy data fitoh daga bedroom dinta kenan taji abunda Fatu ta fada"
Da sauri suka haura saman duk kansu suna shiga dakin suka tsameta kwance kan bed dinta tana faman juyi,
Saurin kara sawa kan bed din Momy tay tace " what happen my daughter?"  Nuna mata maran ta tayi da hannu,  yaushe kika fara ciwon cikin?"kasa mgn tayi da sauri Momy tace " Babana dauko key mu kaita asibiti"
Okay ya fada tare da ficewa daga bedroom din, Fatu dai sai shenshekan kuka take, kallonta Momy tay tace " ki kwantar da hankalin ki ki daina kukan nan haka, zata samu lafiya ki mata addu'a kawai ki daina kukan nan"
girgiza kai  Fatu tayi suka fito parlor, Saif ne ya sauko da key direct parking space ya fito da wani black car suka shiga, binsu Fatu zatayi Momy tace " my daughter kiyi hakuri ki zauna yanzu zamu dawo kinji ko" daga kai tay kwalla cike a idanunta, jan motar yay suka bar gidan"
A hanya Momy ta fadawa Daddy suna kan hanya, yace " shima gashinan zuwa"
Suna parking da sauri suka fito da ita domin lkcn harta fita cikin hayyacinta, wasu nurse ne suka karbeta da sauri suka shiga da ita emergency room, don bata taimakon gaggawa, suna tsaye kofar emergency din babban doctor ya isa da tsauri ya shige room din, Alluran bacci ya fara mata kafin suka fara aikinsu, 30 minutes suka dauka, kafin suka fitar da ita zuwa wani room din, yayi dai² da isowar Daddy yace " meke damunta?" Karfin hali Momy tay tace " bamu sani ba yanzu aka fitoh da ita"
Okay bari naje office din doctor ya fada tare da wucewa, Momy ma wucewa dakin da aka kwantar da SONA tay,  a hankali daddy ya tura kofar office din da sallama ya shiga, wani kyakyawan saura yine  ya amsa mishi sallaman fuska tsake, zama sukayi bayan sun gaisa,  cikin damuwa Daddy yace " meke damun daughter na?"
Dan murmushi doctor Aliyu yayi yace " ka kwantar da hankalin  Alhaji ba wani masala sosai bane ke damunta" ajiyar zuciya Dad yay yace " okay ina jinka"
Abunda ke damunta ciwon cikine, koma ina ga duk wata tanayi idan period dinta yazu mata, wanan karon ne yazu da masala saka makon rashin shan ruwan ta batayi akai² shiyasa ta samu ciwon cikin yay yawa haka amma insha Allah komai zai zama normal"
Nunfarfashi Daddy ya sauke shi a tunanin sa wani babban masalane ke damunta, godiya yamasa ya fita daga office din ya koma room din da aka kwantar da ita, kallonshi Momy tay tace " meke damunta Alhaji?"
Zama yay ya fada mata komai,  numfashi taja tace "nima nayi tunanin hakan amma ganin yanda takeyi ne ya daga min hankali,
Toh Allah ya bata lafiya nidai bari na wuce gida kafin ta farka, okay Babana ku tafi tare kaga munbar Fatu ita kadai, ni zan zauna ta ita, don Allah ka kula da ita banda cin zali don na halinka"
Tsosa keyarsa yayi yana murmushi suka fita daga dakin,
Direct gida suka wuce, suna isah bayan sunyi parking Daddy ya wuce part dinsa, shikuma ya shiga babban parlor, Fatu ya gani zaune ta buga ta gume, tausayi ta bashi a hankali ya karasa inda take zaune ya cire ta gumin da tayi,  da sauri ta dago da idanunta tana kallonsa da kwallar data cika a cikin idanunta tana faman yin kuka, girgiza mata kai yayi yace " kukan fa name?" Tashi tayi ta
Rungumesa  tace "  Yaya inasu SONA Baku dawo tare dasu bane?"
Kokarin cireta daga jikinsa yake domin bazai iya jure rungumeshi da tayi ba, ita kuma kara shiga jikinsa take, da k'yar ya rabata da jikinsa yace " suna asibiti tama warke, kallonsa tay da dan murmushi a fuskar ta tace
"Da gaske Yaya?"
Eh na taba miki karya ne"
Toh mesa basu dawoba?" Ba'a sallamesu ba sai gobe acan zasu kwana"
Rike masa hannu tayi ta shugub'e Fuska tace " don Allah nima ka kaini mu kwana tare wlh hankalina bazai iya kwanciya ba ni kadai, don Allah Yaya"
Zuba mata idanu yayi yana kallon yanda take mgn a hankali kamar bata son yin maganar,
Yayaaaaaaa! ta sake kiran sunan sa tana lungub'e masa fuska tace " ba don niba ka kai ni don Allah"
Hada fuska yay yace " dare yayi ki bari sai gobe na kai ki"
D'iddire kafafunta ta farayi tana kukan shugub'a"
Tsayawa yay yana kallonta, a ransa yace " daman haka yarinyar nan take"
Murmushi yayi yace " toh naji zan kaiki sai ki daina kukan ko"
Wani gunguma ta masa tanà dariya tace " ngd sosai bari na dauko hijab dina mu tafi,
Haurawa sama tayi ta barshi tsaye yana kallonta, tana shigewa bedroom yaja numfashi tare da zama kan kujera"
Bata wuce 5 minutes ba ta fito hannunta dauke da wani karamin bags a hannunta tace " muje ko"
Kallonta yay daga sama har kasa kayan baccin ne ajikinta sai hijab din datasa iya guiwa"
Fuska d'aure yace "ba inda zanje in dai haka zaki tafi asibitin"
Kallon kanta tay tace " me kuma nayi?"
Je ki canja kayan nan idan zakije idan kuma bazaki tafi ba nayi tafiya ta"
Shugub'e Fuska tay tace " na canja me kuma?"
Mikewa yayi zai tafi da sauri ta taresa tace " don Allah ka zauna bari na canja mu tafi"
Bece komai ya koma ya zauna, da sauri ta koma bedroom din ta canja ta fito, tace " toh yanzu fa?" Kansa ya daga kan wayar sa da yake lasawa ya kalleta doguwar riga ce wanda ta k'arbi jikinta sosai, sai gelen kayan data yafa, bece komai ya ci gaba ta lasar wayar sa kafin yace " jeki dauko hijab dinki"
Cikin jin haushin sa ta koma dakin ta sanya hijab ta fito, tace " sai ka duba ai"
Kallonta yayi yaga ta wani hada rai murmushi yayi yace " idan baki saki fuskar kiba sai na fasa zuwan, murmushi ta sakar masa tace " kayi hakuri mu tafi don Allah"
Bece komai ba ya fita ta bishi a baya"
Parking space suka wuce, bude motar yayi ya shiga itama ta shiga suka bar gidan"
A hanya ya tsaya ya musu shopping suka wuce asibitin,
Suna isa direct dakin da aka kwantar da SONA suka shiga, Momy na kallonsu tace " dawowa kukayi?" Yace " eh itace ta masamin sai na kawota, murmushi kawai Momy tayi Fatu tace " ya jinkin?"
Alhamdulillah my daughter"
Murmushi ta zauna gefin SONA tana kallonta"
Sallama Saif ya musu ya wuce gida"

   Washe gari...!

Share fisabilliah Habibaty 🥰






An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment