Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta sameta zaune tana lazumi kwance ya tayi kan gadon ta tana yar wake wake, Inna na gama sallah ta kalleta tace "yau baki kwanta a dakin nan ba in bakiyi wanka ba kinji ki kuwa yanda kike tsami, banza ta mata kamar bata abunda ta fada ba taci gaba da wakar ta, Inna ganin da tayi in bayi da gaske ba bazatayi wankan ba, ji kake dum! Inna ta ta kai mata duka a tsakiyan baya, wani irin ihu ta tsake tana cewa "wanyo Allah Inna ta karya min baya na shiga uku na lalace, Baffa ne yay saurin fita daga dakin shi ya kara so dakin yana cewa "keee! Fatu waye ta b'aki kike zunduma ihu haka?" Inna da ta tsake baki tana kallonta tace "bar yarinyar da iya shege dan nace ta fita tayi wanka kawai shene take wannan ihun yaushe rabon ta da tay wanka a gidan yau kusan sati biyu ake nema fa, ku yaushe sai dai ta lallaye kafarta ta shafa mai"..Fatu dake kuka ne tace "Baffa yau fa da zamu gidan mai gari nayi kuskuri ma fa ynzu kuma ni sanyi nake ji wlh, Baffa yace "tom shikenan gobe ki tabbatar kinyi wanka"tom Baffa insha Allah zanyi, jingina kai kawai Baffa yay ya fita daga dakin Inna dai sai masifa take zubawa akan Baffa ne yake goya mata baya take kin wankan, shidai baice komai ya wuce dakin sa"...

Washe gari da Asuba da k'yar Inna ta tashi Fatu daga bacci tayi Sallah wai ita a barta ta gaji jikinta duka tsami yake mata, Inna tace "indai baza kiyi wanka ba kad'an kika fara ji wata rana sai kin kasa tashi ma gaba daya. Taga alama idan batayi wankan nan ba Inna zata bazata a gari, tashi tay ta dauki bokati ta dibi ruwa rabin bokitin ta shiga ban daki dashi, tana shiga bata fi mintina goma ba ta fito, Inna dake kokarin dama kuko ne ta kalleta daga sama har kasa tace" har kin jiko kin fito Kanan?" Turu baki gaba tay tace "hba Inna kamar wani kayan wanki, ba maraba ba da kayan wankin ae duba fa kiga yanda kika tada dutti a jikinki ae gwara ace bakiyi wankan ba, wucewa daki tayi tana gunguni mutun in bai yi a damesa idan yay kuma ace dutti ya tado, tana shiga ta shafa mai tasa kulli tasa sanda ta gama zana fuskar ta da bakin gazal sannan ta dauki janbaki j'a a bakinta kamar zai digo kasa sabar jin da yay kallon fuskar a madubi tayi tace "kai yau dinan nayi kyau sosai wlh, tashi tay ta dauki doguwar rigar ta tasa ta daura dan kwalinta ta fita waje, tana fita tace "Inna ya kika ganni yanda nayi kyau" Inna dai aikin gaban ta take bata ce mata ko sannu ba, daukar madaran ta wanda ya saura jiya tay ta hada shayi ta zauna tana sha.. yaro ne ya shigo gidan yace "me gare na neman su ."mikewa Fatu tay tace "me kuma ya faru kira da sassafe haka?" Idan mukaje zaki ji koma mene Inna tace tana dauko mayafin ta tayi, tasa Fatu a gaba suka wuce gidan me gari" suna isah zaurin gidan suka sameshi zaune, zama sukayi bayan sun gasa me gari yace "wa ennan nan ne suka kawo karan jikar ki, kallon su Inna tay tace "sai gashi ban gane suba" matar tace "idan baki gane ni ba ae jikarki ta ganeni. Fatu dai tunda suka isah ta kalle yarinyar da suka mata dukane jiya suka debi Gyada tane, aranta tace"
Dani kuke zancen. Me gari ya kalli Fatu dake zaune tana wasa yay yace "keee! Fatu kinsan wannan yarinyar da Maman ta?" Turu baki gaba tay tace "ni ban taba ganin suba inba yau ba, yarinyar ne tace "wlh karya take itane jiya suka min duka ita da saude suka debar min Gyada ae kuka Fatu tsa tana cewa "Allah ya isa ban yafeba ni da ban tab'a ganin fuskar ki sai yau zakimin sharri, nifa jiya ko fita banyi ba ina gida zazzabi ya kamani zaki zo kina min sharri don kawai kun raina ni, ran Inna ne ya baci tace "kaga ko me gari sharri suke son ma jikata. Matar ne tay saurin cewa"in mun mata sharri ribar me zamu samu laifi dai ita tay don haka sai anbiya ni kudin geda ta dna jinyar yata da nayi wayen ne baisan ta da shegen rashin kunya da hankali. Kara sautin kukan ta Fatu tayi harda kwanciya a wajen tana kuka kamar ranta zai fito waje, kara sautin kukan ta Fatu tay kukan da ba hawaye, numfashi me gari yay yace "ban tara ku anan don kuzu kuna min fad'a ba yanzu dai tunda abun ya zama haka ke Jummai keda yarki kuyi hakuri ko koma gidan idan kahan ta kara faruwa zamu dauki munmunan mataki akan ta, Inna kema kiyi hakuri amma ki dinga jawa jikarki kunne idan aka sake kawo min Karan ta anan wajen sai na dauki mataki akan, Inna tace "insha Allah hakan ma bazata faruba, ta fada tare da mikewa ita da Fatu da tay tsit kamar ba ita take rusa uban kuka dazu ba. Tace "Inna nidai zan wuce gidan su Saude na ganta ko lafiya bata fito ba, Inna tace "sai kin dawo, wucewa tay Inna ma tayi haryar gidah"..
***************

Saif ne ya gama shirya wansa tsab cikin wando da riga na jeans masu kyau gaske, yana tsaye gaban wrdp yana kara sa hada kayan shi domin karfe 10:00am jirginsu zai tashi zuwa Najeria, ji kawai yay an rungumesa ta baya, sanin wanda zata iyayin hakan ne ya sashe tureta gefe yana cewa "baki da hankali ne?" Baki ganin aiki nake ne?" Ruky da Ranta ya fara baci ne tace "haba baby don kawai na rungume ka shine zaka tureni toh ma ina zaka da kake hada kayan ka haka?" Bai ce mata komai ba sanda ya kara sa hada kayan shi duka kafin yace "tafiya zanyi idan ba abunda zaki dauka to zan rufe gida na" sake baki tayi tana kallonsa aranta kuwa cewa take ina kuma zashi kar dai ace gida Nigeria zai koma?" Kamar yasan abunda take tunani kenan yace "eh komawa zanyi daman aiki ne ya kawoni koma na gama zan tafi, ya fada tare da jan a kwatinsa ya fita daga bedroom din , binshi tay a baya tana cewa"toh ya kake son nayi niku ma?" Bayan kasan sbd kai ne nake garin nan amma tun da nazo ma ba wani kulawa dani kayi ba, yanzu kuma kace tafiya zakayi ae sai dai mutafi tare" sanda ya sauko parlon kafin yace "wai ke wace irin mace ce da bata da zuciya nace maki niba son ki nake ba kar ki sake shiga sab gata idan kuwa kika dameni toh sai ranki ya baci, ranta ne ya baci zuciyar ta ta fara tafasa tace...!


Maman Khalid✍️
👧🏻 MIJIN YARINYA👧🏻

Story and written

Fatima Zahra (Maman Khalid)

ELEGANT ONLINE WRITINS

Page 6

____Tace "Baba na kayi kyau cikin manyan kayan nan sosai "murmushi yayi yace" thank you Momy" gaba dayan su suka nufi dining area zama sukayi Momy ne yau tayi serving dinsu kafin nan itama tayi nata ta zauna suka faraci, tunda suka fara cin abinci ba wanda yayi mgn har suka gama, suna gama cin abincin Daddy ya kalle a gogon hannun sa ganin har karfe 10;00 tayi ne ya sashi yace "idan kun gama shiryawan mutafi sbd k'auyen a koi shi da dan nisa , jakar kayan ta SONA ta dauka Momy ta musu Addu'a suka fito daga parlon harda Momy ta musu rakiya har parking space tare da musu Addu'ar sare hanya, shiga motar sukayi Daddy a baya SONA a gaba ita da Saif dake drive din motar, hon yay mai gadi ya bud'e musu get din suka fice daga gidan"...

________
Ta bangaren Ruky kuwa sabon waya Iman ya tsaya mata suka dawo gd wunin ranan bata yi shi cikin walwala ba wannan ma tana kukarin danne fushen ta kar Iman ya fuskan ci halin da take ciki...Domin Ruky ta kasance irin matan nan ne da basu iya danne b'acin rai su ko kad'an indai ka mata abunda ranta ya baci akai itama sai ta rama bata da tawakkali ko kadan"

Har dare bata tsake sosai ba, ganin kamar tana cikin damuwa ne yasa Iman janta suka fito yawo suna dawowa kuwa ya fara romance dinta da haka ta samu ta sake ranta amma da gudirin insha Allah gobe itama a Nigeria zata kwanna tunda akoi yar Uwar ta tana Aure a can ta saki ranta sosai suka more daren su cikin farin ciki...

Washe gari ta riga Iman tashi don haka ta wuce bathroom tayi wanka ta fito ta shirya daukar handbags dinta da key din motar tar ta fice daga gidan...

Inda ake yankar ticket ta wuce ta yanki ticket din tafiya Nigeria" direct gidan su ta wuce tana isah ta danna wa mai gadi hon, da sauri ya tashe kasan cewar sa yasan hon din motar ta, bud'e mata get din yayi ta shigo, tana parking cikin gida ta wuce part din Anty Yusra ta shige tana shiga parlour ta sameta zaune cikin daya daga cikin kaya tantun kujerun parlou tana lasar wayar ta da hannu daya, dayan kuma tana ri'ke da karamin cup tana sha.. ko sallama batayi ba tazo zata shige ta kenan, Anty Yusra tace "ke Rukayya baki san yanda ake sallama bane zaki shigowa mutane kai tsaye haka?" Kallon kin raina min wayo ta mata tare da cewa "keeeee! Matar nan ki fita daga idona na rufe ba ruwanki da shigowa ko nayi sallama ko kar nayi sallama wannan ruwa ne ba naki ba, don haka banason sa ido mutun da gidan Yaya yan sa bazai yi abunda yake so sai an wani taku ra masa,tana fad'ar haka ta shige cikin bedroom dinta"...

Girgiza kanta tayi tace " Allah ya shirye ku yaran zamani sai Addu'a"

Tana shiga direct gaban wrdp dinta ta tsaya budeshi tayi ta dauki akwatin ta fara zuba kayan ta a ciki sanda ta dauki duk abunda zata amfani dashi duka sanda ta gama ta rufe a kwatin ta wuce toilet ta sake yin wanka ta fito ta shirya cikin riga da skirt na a tampa sai k'amshi take zubawa fuskar ta dauke da make up mai shegen kyau, daka aganta sai dauka mutumiyar kirki ce wlh..

A kwatin ta ta janyo ta fita dashi parlon, ajiye a kwatin tayi ta wuce dining area ta jawo kujeran ta zauna ta dibi abinci ta fara ci sanda taci mai isar ta kafin ta dawo parlon ta zauna kan kujera tana jiran Yayan ta ya sauko sbd tasan baya fita office da wuri...

Ai kuwa bata dad'e da zama ba ya sauko shida Anty Yusra, kallon a kwatin yayi yace "wanan kuma daga ina?" Ruky dake zaune ne ta hada kafa daya kan daya ne ta mike tare da cewa "ina kwana Yaya" lafiya kalau Rukayya me ya faru kwana biyu baki kwana a gida?" Tace "wlh Yaya aikin ne ya mana yawa a office shiyasa bana samun lokacin da wowa yanzu haka ma Najeria aka turani wani aikin

"Najeria kuma Rukayya?"

Eh Yaya amma a gidan Anty Amina zan sauka"

Okay shekenan yanzu zaki tafi ko sai anjuma?" Eh yanzu karfe 10:00 jirgin zai tashi. Okay zan tura miki kudi ta account dinki wata kila zaki iya bukatar sa, murmushi tayi tace "thank u so much my brother Allah ya kara arziki da girma" shima murmushi yayi yace " Allah ya bada sa'a Allah ya kaiku lafiya, Amin ta amsa masa dashi tana jan a kwatin ta fita daga parlon...

Anty Yusra ce tace "haba sweetheart ya zaka bar yarinya nan ta tafi Najeria ita kadai ba tare da ka tambatar da gaske take ko akasin haka,kana ganin fa yau kwanan ta biyu bata dawo gidan nan ta kwana ba, tana dawowa kuma ta had'a kayan ta tace tafiya zatayi" numfashi yaja yace "kina nufin ba aiki take yi ba kenan wani abun daban take aika tawa kenan?" Tace "a'a ina dai nufin ka dinga sa mata Ido sosai da abunda take" kice zargin ta kike Kawai ba abunda kika iya sai sawa yarinyar nan ido, insha Allah ma ba abunda kike zargin ta dashi bane take" ganin abun zai jawo mgn tsaka nin su ne yasa ta sanja zancen mgn nar da wata..."

Tana fita daga gidan, direct gida Iman ta wuce tana parking ta shige cikin parlon, bata samesa a parlon ba hakan ya sata shigewa bedroom din, tana shiga ta ganshi gaban dressing mirror yana shafar mai, kara tsawa tayi ta karbi mai din ta fara shafa mishi, ta cikin madubin yake kare mata kallo daga tsama har kasa kafin yace "wanan wankan duka ina zakije haka?" Tace "tafiya ce ta kama ni" tafiya kuma a ina?" Najeria kasan akoi yan uwana a can tom akoi wacce ta rasu shine my brother ya turani gai suwar rasuwan, karfe 10:00 jirgin mu zai tashi"
Juyuwa yayi yace "da gaske kike ko dai wasa kike min?" Hmmm sweet kenan ka tab'a ganin na maka mgn nar wasa ne?" Yanzu ma sallama nazo muyi domin tafiya zanyi, dan Jim yayi na wasu mintina kafin yace "okay Allah ya kaiki lafiya, da Amin ta amsa mishe tana shafa mishi mai din tsanda ta gama ya mikewa tare da daukar kayan sa ya shirya sab kafin ya bude wani dorowa ya dibi kudi masu yawan gaske ya sanya mata cikin bags dinta" yana cewa " yaushe zaki dawo?" Uhmmm sai kayi kewata zan dawo"
Murmushi Yayi yace " uhmm ai ni ko yanzu ma banso ki fasa tafiyar ba, muje muyi breakfast sai na rakaki airport din ko" murmushi kawai tayi ya kama hannuta ya manna mata kiss akai suka fito parlon, dining area suka wuce zama sukayi suka fara cin abinci Ruky dai bata ci sosai ba sbd taci dazun, Suna gamawa suka fita daga parlour lokacin har 9:30 yayi direct airport kafin jirginsu ya tashi sanda suka tab'a romance na sallama kafin ta fita ta shiga jirgin har suka tashi kafin yabar wajen da kewar ta domin a iya matan da yake nema ba wance take masa yanda yake so kamar ta shiyasa yake sonta"...

**************************
Tunda suka dauki hanya SONA ce ki hira da Daddy batun kauye tana cewa "ita gaskiya tana son kauye sosai, Daddy kuwa sai murmushi yake yana bata yan da labarin kauye yake...Saif dake Drive yana jinsu ji yake kamar ya make ta wato kara zuga Daddy take don yace so dinga zuwa wanan shegeb k'auyen da ko hanyar kirki bata dashi"
Shi dai bai ce musu komai ba har suka isa k'auyen WANGARA k'auyen dake gefe da garin kano.. kwatan ce Daddy yayi ta masa har suka isah kofar gidan, ai kuwa suna tsayawa yara suka fara taruwa suna kallon su wayen ne zasu fito daga cikin motar, Daddy da SONA ne suka fara fita daga matar suka shiga cikin gida, Baffa dake zaune a zaure ne ya tare su cikin murna da farin ciki, cikin gidan suka shiga Inna dake zaune kan tabur ma tana tunanin ina Fatu ta shiga tun da ta aiketa da safe bata dawo ba gashi har rana tayi sosai... Tunanin ta tsayawa yayi lokacin da taji sallamar su Daddy, da sauri ta d'ago da kanta tana cewa "kamar muryar AMINU na nakeji Ko?" Dariya gaba dayan su sukayi Daddy yace "eh Inna ni dinne... Ai farin ciki gun Inna ba'a mgn dauko ta burma a cikin daki tayi ta shinfida musu suka zauna, SONA dake tsaye ta turu baki gaba tace "wato ma Inna baki kalleni ba sai Daddy" Inna tace "haba dai kawas ai ke na fara gani kafin kowa zoki zauna kusa dani, murmushi tayi ta karaso itama ta zauna a tabur mar da Inna take zaune akai"...

"Saif kuwa Sanda ya gera parking din motar kafin ya fito, shima ya shiga cikin gidan"

Shiga cikin gidan yayi da sallama abakin sa, amsa masa sallamar sukayi Inna wa nake gani kamar mijina ,Murmushi kawai yay ya kara so ya zauna a kan tabur mar gefen Baffa, kafin yace "eh nidin ne yar tsohuwa ai na zata idanun naki sun dai gani ashe dai da lafiyar su har yanzu" washe baki tayi tace "kaji ja'irin yaro idona ai yafi naka lafiya wlh, gaishe ta yayi ta amsa masa cikin farin ciki da wasa irin nasu na kakan ni, gaishe da Baffa ma yayi ya amsa masa, Inna ta kawo musu ruwa da abinci harda da men miyar fura Mai kyau ta ajiye musu a gaban su, Daddy da Baffa kam bayan sun gaisa suka wuce zaune gidan a can SONA ta kai musu abinci da ruwa da furan duka.."

Fatu da tunda ta fita ta kai aike gidan su Saude zama tayi suka fara ta wasan da Saude sanda taji cikin ta na qugen yunwa ne tace "gaskiya yunwa nake ji wlh kamar naci babu yanzu tashi mu tafi gida nasan Inna ta gama abinci sai muci"
Tom Saude ta amsa tashi suka fita daga gidan a hanyar su na zuwane suka hadura da Garba, Garba yace "Fatu wlh yanzu nan naga wasu mutane sun zu gurin Baffa kin gansu kuwa da wani katon Mota suka zo dashi, Fatu tace "da gaske kake ko kuma karya kake min?" Wlh da gaske nake idan kin koma zaki gani yana fad'an haka ya wuce a'bunsa"
Saude tace "kai da gaske ne fa, muyi sauri kar ayi bamu Fatu ta fad'a, ai kuwa run tumar na kare suka sai gida, suna isa kofar gida suka ga wata dalleliyar mota na tsaye, Fatu tace "ashe da gaske yake"
Shiga cikin gidan sukayi ko sallama babu Fatu na cewa "Inna yau kuwa su wayen suka zo naga mota a waje?" Domin bata kula ma da SONA dake zaune tana kallonta ba, Inna tace "baki mukayi baki gansu bane?"juyawa tayi ta Kalli SONA data kura mata ido tana kallonta, kallon tay daga sama har kasa tace "yan birni sannun ku da zuwa" murmushi SONA tayi tace "yaewa yar Kanwar mu, kara sawa kusa da Saif tayi dake zaune yana lasar wayar sa bai ma san ta kara sa kusa dashi ba, tace "Kai Malam bakajin ina muku sannu da zuwa ne ko dai kurma be Inna?" Jin wani irin tsami da doyi da yake jine ya tsashi daga da kansa ganin meke wari haka hada ido sukayi da Fatu tsaye gaban sa tana kare masa kallo, a hankali yace "me yake wari hakane matar naji gidan ta dauki wani kalan wari da tsami haka?" Daman haka kuke fama da wari a k'auyen nan?" Inna dai dariyar k'asa k'asa tayi domin tasan bai waci matsowar da Fatu tayi kusa da shine yaji tsamin jikinta" Fatu tace" kan uban can ni.....!

👯‍♀️🔥Toh fa ga Fatu ga Saif koya zasu kare, ko dai ko biyoni da ruwan comments❤️

Comments and share fisabilillah

👧🏻 MIJIN YARINYA 👧🏻

Story and written

by Fatima Zahra (Maman Khalid)

ELEGANT ONLINE WRITERs 📚

Bismillahir rahmanin Rahim


*ALHAMDULILLAH ALLAH YAYI DAWOWA NA LAFIYA, INA GODIYA GA MASOYA NA, SOSAI DA SOSAI MASU KIRA DA WAEN DA SUKA KIRA BAN SAMU DAMAR DAUKA BA INA KARA GDY DA SOYAYYAR DA KUKA NUNAMIN,I LOVE U SO MUCH MY FAN'S*

(Not edited)


Page7


___ Fatu tace" kan uban can ni dinne nake wari?" Jin abunda ta fada ne ya sashe dago da kansa yana kallon tsabar rashin kunyan dake da mum  kwanyar ta"
Inna ce tace "haba Fatu baki ga baki ne ba?" Bana son sakarci maza wuce ki bani waje" Turu baki gaba Fatu Tay bata ce komai ta wuce dakin su Saude ta mara mata baya, suna shiga dakin ta zauna bakin gadon ta tana kunkuni wai yau har ita wani zai zaga akan wanka ai abunda bazai yuba kenan, tashi tay ta fara zagaye dakin, Saude dake zaune itama abakin gadon ta  kalleta tace "tab! Lailai wlh wannan mutumin yayi mugun rai na miki wayu wlh, tab nikan kinji abunda ya fada miki kuwa?"  Hmmm kawai Fatu ta furta taci gaba da zagayen dakin tana tunanin wani irin abune zata mishi wanda zai tsata ta huce akan abunda ya mata.ta dade tana tsafa da marwa kafin tayi wata muguwar murmushi ta zauna kafin tace "dauko mana abincin nan muci kar yunwa ta illa tani"
Tashi Saude tayi ta kawo musu abincin suka fara ci,sanda suka gaba kafin suka fito waje, suna fita basu tsameshi ba sai Inna da SONA da suke zaune suna hiran su ta kaka da jika"kallon Fatu SONA tayi tace "Fatu ba mgn ne?" Murmushi kawai tay ta zauna a gefin su amma bata ce komai ba, Inna ce tace "haba Fatu na miyen ne ya tsame ki naga sai had'a min fuska kike?" Turu da karamin bakin ta gaba tayi tace"fushe nake dake tunda dai kina jin wanan mutumin yana zagina ke kuma harda goya meshi baya, sbd kinga sun kawo miki Madarar ta birni, sai washe mishi baki kike" da kuwa Inna ta mata yare da cewa" shidin Yaya n kine ai kuma madaran ai kema za kisha,
Dariya SONA tayi tace"Fatu da Inna akoi drama"

Saif kuwa bayan Fatu ta shiga daki ne ya dubi Inna yace "wace mara kunyan ce wannan?"yarinya ne ba hankali kamar shedaniya"
Had'a fuska Inna tayi tace "idan ita shedaniya ce kai ma shedanin ne kenan domin ita din kanwar kace" kanwata fa kike ce fa Inna?"eh da mai k'a dauka?" Nifa bana son iskancin banza dana wofi daga zuwan ka kafara tsokanar ta ahakan har ku iya zaman inuwa daya don haka daga yau karta kara shigar tsapgar ta ehee" cike da mamaki yake kallon Inna kafin ya yace"Allah baki hkr matar"sai lokacin Inna tadan Yi murmushi tace" kamar ka damu da matar taka yaushe rabon ka da garin nan tun kana zanin goye, sai kuma lokacin da uwar ka AISHA tazo kuka kwana, lokacin gaka da kukan tsiya abu kadan kuka sai shar ban majinan da kake"ai kuwa dariya SONA ta kyalkele dashi tace" da gaske Inna  don Allah bani labarin Yaya  ya akayi"
Inna tace "kai 'yarnan ai baki sani ba lokacin da yake yaro a 'koi shi da kashin banza banza wlh abu kad'an ya tsake miki zawo ajiki, tsuliyar sa baya hutawa kamar famfo,dariya SONA ta fashe dashi har tace"da gaske Inna?" Hmm! ke dai bari kawai 'yar nan ai in fad'a miki....ai Saif bai bari ta kai gayin mgn ba ya mikewa tare da cewa"haba Inna yaushe nazo gunki da har kike bata wani lbr n sherme,kudai tsonfi ba abunda kuka iya sai bada lbr shirben banza dana wufe yana fadar haka ya fice daga wurin da haushen SONA ma data ce ta bata lbr n"
Inna kuwa lbr taci gaba da bawa SONA har lokacin da su Fatu suka fito daga dakin suka ci gaba da hira"....

Da d'an dare bayan sunyi Sallah i'sha Fatu da SONA sukaci abinci tare domin har sun fara tsabawa,suna gamawa Fatu ta mike tare daukar babban bokiti ta cika shi da ruwa da k'yar ta dauke she zuwa ta ajiye ta dawo da kinsu ta dauki tsoson wankan ta wanda ta boyeshi tun randa Inna ta tsaya mata, a cewar ta bazata iya goge jikinta dashi ba salon jikinta ya dinga mata zafi, dauka tayi ta tana fad'an har mu za'a gwadawa tsafta ta wuce ban dakin dashi.ta jima tana goge jikinta da tsoson sanda taji jikinta ya fara mata zafi kafin ta bari ta zuba ruwa ta fito, ji tay jikinta ko ta ina iska na shigar ta har wani lumshe idanu take domin wani irin bacci daya zo mata,sai dai kuwa yau baza tayi bacci ba domin da abunda ta gudurta a ranta, shiga dakin su tayi ta shirya cikin wata doguwar riga faran TAs ta fito ta sami

Please Login or Register in order to submit comment