Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nemi kwano ki zuba shinkafa da miya in kinje gidan kwaci, ke da 'ya'yan naki." Tahira tana kuka ta fita a cikin gidan, a cikin tashin hankali take a gidan aure, duk bayanta a farfashe suke, kullum sai Tasi'u ya daketa,ga aman giya da yake yi mata, wani sa'in har fitsarin kwance ya ke yi mata."

"Hafsa wai shin me yake faruwa ne, kink'i cemun komai nifa kin barni a duhu. Cikin kukan fitar haiyaci Hafsa tace ma d'an sahu.
"Malam ka fara kaimu D'anladi na sidi. Daga nan sai mu wuce kasuwa, daga k'arshe ka sauke mu a jacara." Mai d'an sahu ya amsa mata da "Toh" Jamila a cikin tashin hankali da rikici take mai tarin yawa, zuchiyarta cike da nadamar rayuwa, bata san ma ta ina zata soma rok'on afuwar mijinta ba, domun yayi hak'uri da'ita sosai. Hafsa kuwa ajjiyar zuchiya take ta faman saukewa. Babu mai cewa da wani wani abun. A haka har suka isa anguwarsu Hafsa.
"Ki jirani a nan, yara kawai zan kwaso sai in zo mu wuce."
Fita tayi ta shige get d'in gidan nata. A farfajiyar gidan ta ga Alh yana kai kawo. Bata ko bi ta kanshi ba, ta yi shigewarta ciki. Kai tsaye zuwa d'akin yaranta. Jaka ta bud'e ta soma loda kayan yaranta. Bata d'iba duka ba. cikin d'akinta ta koma ta tattare 'yan kadarorinta. Ta had'e kan suturunta. A harzuk'e ya shigo.
"Hafsa wayata na fito nema tun tuni, yara suka ce mun kin fita da'ita bani wayata nace. A zabure ta d'ago idanunta a bushe. Dan ji take yi zata iya kasheshi kowa ya huta, abunda zai faru ya dad'e bai faru ba.
"Auwal na gama zama a gidanka, aurenmu ya k'are, k'azami wanda ya d'auki fasik'anci a matsayin ado. Toh kasani abunda kuka jima kuna shukawa ya fito, kuma in kayi yunk'urin k'in sakina wallahi saina yi ma bankad'ar da sai fita ya gagareka. Jakarta ta zuge ta ciro wayar tashi, ta lalubo mishi abunda ta gani ta haska mishi. Bai iya ce mata komai ba, sai kallonta yake yi kawai, zufa duk ta gama wankeshi tsab. A sanyaye yace.
"Hafsa ki yarda dani ba laifina bane. Zan yi miki cikakken bayanin da zaki fahimta." cije baki ta yi kawai tace.
"Takaddata nake so, in ba hakaba narantse da Allah kasheka zanyi a cikin gidannan, saidai a kasheni, ko kuma in je in taradda 'yar uwata a kurkuku, d'an bura uba mara mutunci." Dubanta yayi yace.
"Na sakeki saki d'aya. Amma fa ki sani babu inda zaki tafi mun da yara suna gidan ubansu. Dariya tayi, dukda xuchiyarta ta tsinke sosai, har kuka yaso ya xo mata, dannewa tayi kawai.
"Auwal kenan, ka kaini kotu sai su baka yaran naka, Amma ni ba shegiya bace dazan bar maka yara a hannunka. Fuu ta fita a d'akin ta fitar da kayansu tas, sannan ta dawo ta tusa kan yaranta. Har bakin D'an sahun ya je, ya rik'e k'arfen d'an sahun yace.
"Ki daure ki bar yarannan a gidansu shine gatansu, kar abun kunyar daya faru a gidanku ya shafesu.
"Kaci bura ubanka, kai da abun kunyar, abun kunya har ya wuce na kanka. Mai d'an sahu ja mu tafi. Jamila kuwa da mamaki take kallonsu, gani take yi abun tamkar almara. Mai d'an sahu ya jasu zuwa kasuwa. Xinarenta na gado ta siyar, suka wuce jacara.

Aminu
Sai bayan isha ya shiga gida, su Zara'u kam sun jima da yin bacci, Mardiyya ce idanunta biyu, yanzu ta gama tsinke alaiyawon miyar masa.
"Ka dawo?"
"Nadawo Dada, yau munsha zurga zurga ni da Saminu. Mun kammala komai, zuwa gobe zamu bud'e sana'a, Saminu zai rik'a saida su lemo da ayaba. Dada tace.
"Masha Allah Abun yayi kyau. Mardiyya ta fita zuwa d'akko ma Abbanta abinci bayan ta yi mai sannu da zuwa.Tuwon masara miyar kuka, ta ajjiye a gabanshi da ruwan sha, dana wanke hannu. Sai ta fita tsakar gida gyara shinkafar tuwo.
"Dada, dama Saminu ne ya zo mun da wata magana akan ita Mardiyya, tunda maneminta iyayenshi sunk'i amincewa da auran. Wai shi yana son ita Mardiyyan. Kinji fa abunda yake tafiya." Dada ta jinjina sosai tace.
"Toh Saminu yayi k'ok'ari sosai Aminu. Amma yanda za'a k'arke da Farida shine abun dubawa. Sannan zumuncin Mardiyya da Murja ka iya lalacewa. Sai dai in a ka yi duba da irin abun kunyar daya b'ullo a gidansu Hauwa, toh fa yaron mutunci ba lallai bane ya fito neman auren Mardiyya iyayenshi su amince mishi ba. Al'amarin yana da nauyi. Aminu yace.
"Hakane duk tunane tunanennan nima su naita tattaunawa a raina, amma abunda yafi shine mu yi istikara dukkanmu, Allah ya zab'ar mana abunda yafi zama alkairi shine kawai. Dada tace.
"Ameen, 'yar uwarka ma da kuka ta bar gidannan yau, sha'anin aure yanzu ya dawo abun tsoro, maza suna kukan mata, matanma kukan mazan su ke yi. Mu iyaye an barmu da kuka ta kota ina. Ga hawan jinina ma ina tunanin ya tashi, sakamakon wannan fitina data kunno, zanje asibiti gobe. Aminu ya cije leb'enshi dan shi halin da yake ciki yafi gaban a tsaya bayani ma. Shuru su ka yi kowa na zancen zuchi. Tuwon ya d'an cakala ya rufe.
"Aff masu jere fa sun zo an gama komai ras, waje yayi kyau.Kai ta adda'a Allah yasa Lubabatu ta kawo haske da canji a cikin rayuwarka.
"Ameen" Kawai yace, ya mik'e tare da yi ma Dada sallama.

KURMAWA
HAUWA
Wajajen k'arfe taran dare na farka, Uwatale tana sallah a lokacin, sauran abokan aikina suna daga kwance suke tab'a hirarsu cike da raha. Murmushi nayi daga kwancen da nake. Ahankali na mik'e zaune, ina jin wani irin jiri na d'ebeni daga zaunen. A daddafe na mik'e, sai a wannan lokacin suka lura dani.
"Hauwa Kin farka, Sannu ya jikin?"
"Da sauk'i nagode." Band'akin na shiga, nai fitsari, sannan na d'auro alwala. A zaune na gabatar da sallolin da ake bina. Sallama na yi musu, nan muka shiga gaisawa d'aya bayan d'aya, kowa na gabatarmun da kanshi. Naji dad'in had'uwata da su.
Abincina Uwatale ta bud'e ta mik'omun, tuwone miyar kuka. Ahankali na soma ci, a halin da nake babu wani dad'i da nake buk'ata. Kama daga na rayuwa har xuwa na d'and'ano. Ban iya cinye abincinba. Ruwa na sha na koma gadona na lullub'a
Awa d'aya. Ko wacce ta yi baccinta bandani, ina tuno gidana, da gadona na alfarma. Ina baje Aminu na yi mun tausa. Murmushi nayi.
Allah Sarki Aminu.

KOMAWA LABARI
mune masu hada hadar raba abinci a wajan biki, sabida mune na kusa kusa da amarya. Da kyar muka samu muka zauna ni da k'awata Zalika.
"Kai Zalika nagaji sosai da sosai. nifa ban fiye son aikin wahala ba." Daga bayanmu muka ji wata murya ta amsa da cewa.
"Aikin wahala bai kamaceki ba ai, domun ko jikinki ya nuna zallan hutunki." Juyawa mu ka yi ni da Zalika dan ganin mai maganar. Samari biyu muka gani a tsaye, sun sanya komai nasu iri d'aya. Kaftanne a jikinsu na farin bowel me kyau, duk da ba mai tsada bane, amma ya amshesu duba da yanda ya haska su, jar hular dara ce a kawununsu, da jan takalmi wanda kudinshi bazai wuci nera dubu uku ba. sai k'amshin turare mai mugun arha suke ta faman yi. Aminu na zuba ma idanu take sai naji ya burgeni gashi da sakin fuska.
"Kun bamu izinin zama ?" Cewar Saminu. Zalika tace.
"Bismillah kuna iyawa" Zama su ka yi, Aminu ya fuskanceni da kyau yace."
"Sunana Aminu, ina zaune a anguwar galadanci, kuma ina aiki a shagon sai da iskar gas dake kan titin mandawari. Kefa yaya Sunanki." Aminu ya burgeni sosai, kuma inajin zan iya soyayya da shi, duk da dai hamshak'in mai kud'i nake son Aure, amma a lokacin ni ban tab'a bama wani saurayi dama ba, sai nake jin zan soma ta kan Aminu kafin in samu miji daidai da abunda Ammina take buk'atar mu kawo mata.
Sunana Hauwa, ina zaune a Jacara."
"Masha Allah Hauwa, nayi farin cikin had'uwa dake. da fatan zan samu matsuguni a zuchiyarki, ko yayane a d'an karani, duk da nasan ban isa ba?" Murmushi nayi nace.
"Aminu kenan, da bazan baka dama ba da bazan ma saurareka ba balle har kaji sunana dama inda nake da zama ba. Mace allurace cikin ruwa, in ka biya allonka saika wanke, in wanda ya fika k'arfin hadda kuma ya kasaka karka ga laifina." Dariya muka sanya baki d'aya. Aminu ya k'arb'i number wayata, da aka tashi kuma ya ciro nera dubu d'aya ya bani in saka kati. Da ga nan mu ka yi sallama akan jibi zan ganshi. A gajiye tulus muka dawo gida, wata mota mai nunfashi na gani a k'ofar gidanmu. Da mamaki na k'araso wajan. Hafsa ce jingine a jikin motar tana tad'i da wani babban mutun, kai da ganin motar hawanshi, da suturar daya keta. Kasan kud'i ya zauna. Sum_sum na shiga ciki jikina a mace ina cizon yatsa. Har nake tunanin anya banyi gaggawar bama Aminu dama ba kuwa?" Amma da yake Aminu gwanin iya kalamai masu sanyi ne. A daren bai barni a waya ba sai da ya tabbatar ya cusa sonshi a xuchiyata da k'arfin tsiya, dan gudun karya tsaya kallon ruwa kwad'o yai mishi k'afa. Da mafarkai barkatar na kwanta, ina Allah Allah gari ya waye, domun daga Aminu har ni mun k'agu gari ya waye dan muga junanmu. sab'ani da daya ce mun sai zuwa jibi zai zo.


MRS BUKHARI

*TALLAH*
Ina kuke amare uwayen gida kai har ma da ƴan mata? Ko kun san Mrs Bukhari mai kayan ƙamshi, ai in dai batu na kayan ƙamshi gyaran jiki da na ɗaki to kai tsaye ku ne mi Badi'at domin gwana ce ta ko wanne fanni a ciki. "Wai ƙamshi kina nufin Badi'at dai marubuciyar nan tamu mai nishaɗantar da mu?"
"Tabbas Fati ita take magana, ai kin dai ji yadda ake magana a kai na, hatta me gidana ya jinjinawa Badi'at domin duk wani ƙamshi da zaki ji a jikina tare da gidana to daga ita ne, ke me kankat ma har gyara na nake yi domin gyaran aurena daga gareta ne, shi ya sa bana wasa da gyaran jikina da na gidana har kuke kirana da ƙamshi."
"Eh tabbas nima na jinjina mata, kuma zaki bani addireshinta domin nima na kwankwati wannan garaɓasa. Ko zaki iya faɗa mini abubuwan da take sayarwa.?"
"Bari na faɗa miki akwai...

Humra
Kulacca
Sudanese Humra
Kulacca ta gashi.
Turaren wuta ɗan gaske, iri daban daban.
Turaren mopping
Room freshner
Turaren turara kaya.
Turaren wuta na toilet
Sannan akwai ingantaccen maganin infection
Ina da magungunan mata, wanda zai gyara amarya da uwar gida.
Wanda zasu shiga daga ciki kuma
Akwai sabulun amare, da dilka ta amare, wanda zaisa amarya ta fito ta haska tas
Kabbasa
Setin kujerar tsugunno
Sannan inayin turaren wuta da kasko, da ashana wanda ake rabawa a taron biki ko suna.
Ina bayar da sari.

Ma sha Allahu to taya zan sameta domin mallakar nawa?

"Kai tsaye zaki mata magana ta whatsApp ko kiranta ta wannan number.

08179523215


*TALLAH*
A yau nazo muku da manya manyan magunguna domin gyaran Auranmu! Saboda yadda zamantakewarmu ta AURE keta kara tabarbarewa. Mata iyayenmu ku fito ku gyara jikinku , domin wallahi har Abadan macen da bata gyara bata isa ta hada kanta da mace me gyara ba har abadan! Mu gane yaku yan uwana mata, ma’aurata! wallahi gyara shine mace Akwai mata dayawa dasuka san magunguna na, a online Suna siya kuma Alhmdulillahi ba wadda ta siya bata dawo tamin godiya ba, Alhmdulillahi!Alhmdulillahi! Alhmdulillahi! Yawancin mata dayawa na nemana ta dayan sim dina sede nayi losing dinsa sede wannan shi yake Aiki 08104335144, A YAU NAZO MUKU DA MAGUNGUNA INGANCI DA IZININ UBANGIJI, WATO AINIFIN HADI Iri ~iri na MALLAKA D’ANA MIJI ALFARMAR ANNABI SAW, ina tabbatar muku da magunguna na babu shamaki base na tsaya bata lokaci a bayaniba zanso ku gwada dan tantance GASKIYA * Akwai cututtukan dake hana maganin mata aiki idan kinason sani ki tuntubeni ta wannan lambar 08104335144 wadannan cututtukan inhar kinadasu wallahi duk maganin daza kisha bazeyi Aiki ba, kuma bazaki taba fahimtar komiba a harkar dadih na magungunan mata.

*MUNADA MAGUNGUNA AVAILABLE KAMAR HAKA*👇🏽

*ingantaccen maganin infection *

Ingantaccen maganin basir

Ingantaccen maganin gyaran nono

Ingantaccen maganin gyaran hips

Ingantaccen maganin kara kiba kiyi dumur~mur dake

Ingantaccen maganin rage tumbi meyi tsakani da Allah

Ingantaccen maganin matsin farji mesa dadin farji ga azzakarin d’ana miji.

Ingantaccen MALLAKA TA DOMIN ALLAH (Bata harkoki) shine sunansa, hmmmm Wannan magani inada tabbaci a kansa shidin hadine kawai na mallakar d’ana miji akwai komi a cikinsa na mallaka hajiya ki gwada kisha mamaki Alfarmar Annabi SAW.

Se matsin (GAMADIDI) wannan matsi in kikayi amfani dashi har abadan abidina mijinki baze kawo a gaban wata ya mace ba in har ba gabanki bane wannan inada tabbaci a knsa 💯 kuma wadanda suka saya ma sun kara tabbatarmin da kyaunsa na mamaki.

Akwai zallan hadi na amarya

Akwai hadi na uwar gida sarautar mata wannan seat ne akwai komi a cikinsa.

Akwai ingantattun gumba iri iri kamar haka 👇🏽

Akwai gumbar Madara
Akwai gumba me rubutu 🤐
Akwai gumbar kankana
Akwai gumbar giginya (sa megida kuka)
Akwai ingantacciyar gumba me suna (BARIN MAKAUNIYA)
Akwai gumbar hasi
Akwai zallar gumba wadda ita ta rubutuce zallarta zaki ganta baka karki damu Aikin kawai zaki duba 😉
Akwai gumbar gero
Akwai gumbar ridi
Akwai gumbar garin gamadidi ita ta mallaka ce zallarta.🤐

Akwai tsumi iri iri sunansu sha yanzu magani yanzu 💯👇🏽

Akwai tsumin kankana
Akwai tsumin baure
Akwai tsumin rubutun Ayar Allah
Akwai tsumin kwakwa
Akwai tsumin giginya
Akwai tsumin GORON SUDAN (wannan special ne dan kudinsa ma daban yake)
Akwai ingantattun magunguna na tada shaawah kama daga na turawa har zuwa na Islamic wato namu na gangajiya. Akwaifa maganin maza madam na hausa dana turawa 😉 duk basuda side effects 👌

Akwai rubutun mallaka
Akwai zoben mallaka
Akwai hayakin mallaka
Akwai zani na mallaka
Akwai hadin ci da kaza
Akwai hadin yan shillah
(Muna dafa kaji da yan shillar ma dade sauran abubuwa da dama,)
Akwai dambun nama na mata wanda ke dauke da magungunan sirri na mata mesa tsantsi da laushi da ruwa a farjin mace 😉

Akwai magunguna na ban mamaki wadanda base na rubutasu ba saboda SIRRI 😉
Muna aika magungunan mu kasa kasa gari gari *UWAR GIDA KI GARZAYO QUEN SANAF Islamic chemist kise magunguna na ingantattun ne insha Allahu kin wuce takaicin d’ANA MIJI * direct to me 08104335144 muna sauraron masu shawarwari a kan zaman AURE insha Allahu, amma in knsan baki shirya siyan magungunan jima’i ba na mata ko na maza pls karki kirani.

_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*


_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*


_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿
[09/12, 19:49] Badi at: GAWURTATTU BIYAR
DAGA ALK'ALAMIN
BADI'AT IBRAHIM
MRS BUKHARI (B4B)

*ANGULU*
*DA*
*KAN ZABO*
17/18






"Assalamu Alaikum, maman Hewa kina ciki?" Maman Hewa tana daga d'aki tana turare d'akinta da turarukan k'amshi tace.
"waye shigo" Dada ta bud'e labulen da sallama ta shiga. Bata tab'a shigowa gidan ba, dan ba dad'ewa su ka yi da dawowa ba, 'yarta d'aya ce mace me suna Hewa. D'akin yaji kayan alatu sosai. Dada ta nemi kuri ta zauna a ranta tace.
"Shuwa gidan k'amshi kenan. Kaima Allah ya baka Aminu" Maman Hewa ce ta fito daga d'aki da fara'a suka gaisa da Dada. Ta tsaɓa ado tamkar zata je gidan biki ko suna. Dada tace mata.
"Dama nazo ne in miki wasu 'yan tambayoyi a game da al'adun auren shuwa. Da farko dai bari in soma da sadakinsu. Yana kaiwa nawa?" Maman Hewa tace.
"Toh Dada k'arfi k'arfine abun, kamar dai mu talakawa haka, sadakin daga dubu d'ari uku, d'ari hud'u har zuwa bakwai. Kuma da sisin gwal ake biya, wannan wajibine, duk cikakken shuwa da sisin gwal ake biyan sadakinsu. Daga sisin gwal uku, huɗu, biyar, goma sha biyu ne ƙarshe. Masu sukuni kuwa har million hudu, million goma ana biya sadaki, Dada har Million ashirin ana biya ya danganta da ƙarfi. Dangin amarya kuma gaskiya zasu narka mata kaya sosai. Akwai kayan uwar miji da akeyi har da katifa, da kafet na ɗaki, su kulolin cin abinci, abubbuwa da dama, shi kanshi kayan uwa kuɗi ake narkawa sosai. Al'adun da yawa gaskiya. Wannan dalilinne shuwa basa auren talaka, sai ake fassaramu da kwaɗayi, ba kwaɗayi bane talaka bazai iya bane. Akwai kashe kud'i." Dada ta yi shiru tana nazari, can kuma tace.
"Tom shikenan nagode sosai." Sallama ta yi mata ta fita. shagon k'ofar gidan nasu inda nanne d'akin Aminu. Dada ta shiga da sallama. Aminu ya amsa mata a hankali.
"Ina Saminun?" Dada ta tambaya bayan ta zauna.
"Ya shiga cikin gida, zai kama ruwa."
"Aminu har ga Allah banason wannan 'yar shuwan, ni hankalina bai kwanta da'ita ba. Ka ga mun jima muna wannan maganar dani da ku. Toh amma gudun kar in rasaka, kuma itama yarinyar tana sonka. Toh bazan tauye ku ba. Na Amince Allah yasa albarka." Murna ce ta cika zuchiyar Aminu fal. A haka Saminu ya dawo ya samu aminin nashi.
"Toh Saminu na tambayo mak'ociyarmu 'yar shuwa. Ashe dai haka ake biyan wannan sadaki, wai harda masu bada million ashirin abu kamar hauka. Naga yaronnan yayi zurfi a son yarinyar. dan haka na amince muku. Zan kuma je k'auye, a cikin shanun gado in gani ko guda biyu a siyar, ya samu ya aureta kowa ya huta." Murna su ka yi sosai da sosai. Washe gari Dada ta tafi gida. kwana hud'u tayi suka dawo ita da k'anin mahaifin Aminu, su ka had'u da mahaifin Saminu, ranar da aka yanke musu gobe ne, sun shirya zasu je da yamma."

Hauwa
wayar gari nayi cikin fad'uwar gaba da fargabar rasa Aminuna. Hak'ik'a ina son kud'i, kuma ina son auren mai kud'i. Amma son Aminu yaci k'arfina har nake ganin in zan samu Aminu zan zubar da makaman yak'i, in aureshi in ci duniyata da tsinke. na kasa walwala sam. Ammi ta yi mun tambayar duniya kan meke damuna. Ni dai da Ba komai nake amsa ta.
Tunda Aminu ya tafi bai d'aga waya ya kirani ba. Koda na kira wayarshi da safe dan in jaddada mishi yaune fa. Sai naji wayar a kashe. Hakan ya tsurad dani sosai."
Da daddare muna zaune a tsakar gida, sai ga sallamar Baffa Junaidu. Sannu da zuwa mu ka yi mishi, duk muka tarwatse.
"Marne na zo ne akan iyayen samarin yarannan da kika turosu maganar sadaki da tsaida rana. Sisin gwal biyar kamar yanda kika yanke. Gasu sun samu, Alh Auwal kuma guda sha biyu ya kawo. Marne kiji tsoron Allah yarannan siyar dasu zaki yi ne da irin wannan dukiya. Albarka ai itace kan gaba a aure ba tulin sadaki ba. Sannan kinsa musu wata d'aya ca su kai dake duk sun gama shiryawa koko yaya nine dai uban yarannan duniya da lahira. Kwatsam sai jin sallama na dinga yi a zauren gidana, wannan wanne irin ɗumasariya ne?"
"Hmm jibeka Junaidu me jiya ta yi ma bare yau. Dan kaga na baka girma anje kai sadaki gidanka har shine ka samu zarafin ci mun fuska?. Tunda wan naka ya mutu mai ka tab'a yi mana daga ni har yaran da kake ikrarin kai ubansune? Ko Sada bai isa nunan yatsa ba kai ka sani."
"Yaran da baki nuna musu girmana ba balle su san mutuncina. Ubansuma baki nuna musu su dinga yi mishi adda'a ba. Ranar fa Sada yazo yana faɗamun a titi ya haɗu da Hafsa amma kawar da kai tayi tamkar ba ɗan uwanta ba. Yanzu dacewa kenan, in yarannan basu yi zumunci dasu Sada ba dawa kike so suyi zumuncin to? Mu biyu rak iyayenmu suka haifa.To Ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta Marne. Sisinan gwal d'in ya zube mata a gabanta ya fice. Yana magana"
"In banda fitina ina Sada ina wannan mata, gata kamar basamudiya, ga rashin tarbiyya, sanda aka kawota ko sallah bata yi. Itace aka auro a matsayin uwar ƴaƴa. Ba dole aga aikin jahilci ba.
Gud'a ta shiga yi.
"Aiyiririiiiii Yarana sunyi kasuwa, Junaidu sai dai ka mutu. Irina sunfi ƙarfin aurenka sai dai irinsu Harira ai. Jin guɗarnanne yasa muka fito a guje dukkanmu.
"Ammi sun biya sadakinne?" na tambayeta a ɗarare.
"Sun biya sadaki, sun yi rabin aiki, inaga aje dasu d'in kawai ku auresu. Amma in ina raye babu wacce zatai kuka a gidan aure, zan shiga in fita a tsumaku, da sihirtattun itatuwan mata, ta yanda tasirinku zai baku damar mallakar mazajenku. Dan haka nan da sati biyu zamu tafi koshob'b'e duk wani gyara acan za'ai muku shi. Ku sanar da su kud'in gyaran jiki nera dubu d'ari d'ari, ke kuma Hafsa sai abunda Alh ya bayar."
Kwanan farin ciki nayi, inata kiran wayar Aminu a kashe, sai washe gari da daddare kawai yaro ya shigo kirana wai inji Aminu.
A jingine a bangon gidanmu ya tsaya.
"Aminu ka sanyani a cikin damuwa, tun ranar daka tafi ka barni a mawuyacin hali ban kuma ji daga gareka ba. Murmushi yayi mun. Sai naga Aminu ya sake yi mun mugun kyau a cikin darennan. Har nake jin lallai nayi dace. A lokacin Aminu bai wuce shekara Ashirin da biyar ba, ni kuma shekaruna duka duka Ashirinne . Amma Aminu yana da nutsuwa da kamala, gashi da tunani irinna manya.
"Hauwa ki yi hak'uri wayarce aka sace, kuma na kwanta jinya shi yasa baki jini ba."
Subuhanallah, jinya kuma? Muje dakali mu zauna Aminu.
Ina gaba Aminu na bina a baya har zuwa kan dakalin.
"Ciwon sonki ne ya kwantar dani a daren da muka bar gidanku da Saminu. Hauwa ina sonki fiye da tunaninki fa. Ina jira lokacine in nuna miki tsantsar son da nake yi miki. Na shinfid'a miki wata rayuwa mai kyau a gidana. Murmushi nayi ina kallonshi, Sonshi na k'aruwa a xuchiyaya.
"Aminu, nima ina sonka sosai. Kuma ina farin cikin mallakar juna da muka kusan yi. Amma dai bazaka had'a sonda kake mun da wata mace ba dai ko?" Dariya yayi kawai yace.
"Cikakken namijin da ya san kanshi, da irin halittar da Allah subuhanahu wata ala yai mishi. Bazai ma budurwar da zai aura romon baka irin wannan ba. Ni a ganina masu amsa tambayarnan da cewa eh bazasu yi ba. Ni na d'aukesu mak'aryata, mayaudara kuma Hauwa. Ni a tsarina bana yaudara." Rai na b'ata bance dashi komai ba. Shima shiru yayi yana kallona yana sake mun murmushi.
"Aminu zaka ba da kud'in gyaran jiki bisa al'ada, domun nanda sati biyu zamu tafi k'auyanmu, sai satin bikin zamu dawo."
"Toh nawa ne Hauwa? Ai mun gyara da kyau Hauwa."
Dubu d'ari ne kacal ba yawa."
"Dubu d'arinne ba yawa Hauwa, wannan wanne irin gyaran jiki za'ai miki haka Hauwa, a injin za'a saki?.
Haba Aminu dad'ina da kai ka fiye mammak'o da yawa akan komai sai ka nuna gazawarka. Kallonta kawai yayi yace.
"zan bayar. Zan nemi gidan haya kafin lokacin, sabida in kai ki kije ki ga gidan ki? Dariya na sakar mishi, shima ya mayarmun da martani.
Hakan yayi Aminu gaskiya.
Sallama Aminu yai mun dan baya doguwar hira.

Aminu
Ta b'angarensu sai shirye shiryen akwatuna suke ta faman yi. Akwati biyar da k'yar suka cika da karo karon dangi suka samu aka kammala komai. Tahira k'anwarshi ita aka wakilta ta sai komai. Aminu ya kai Hauwa gidajen haya da dama. Amma ko wanne sai ta ce bai yi mata ba.

HAUWA
Aminu nifa bari in fito maka a mutum irin gidajen da fa kake kaini ba su yi mun ba.
Ni gida mai get nake so, mai d'akuna biyu da falo, kuma ya zamana akwai bayan gida da kitchen a ciki, anguwa me kyau kuma."
"Haba Hauwa waike baki da tausayine? Gidan da kike magana a kai fa, hayarshi sai ya haure dubu hamsin. Haba ina zan dinga samun dubu hamsin ina biyan haya ga ciyarwa."
Dakata Aminu nifa sai a fasa aurennan fa. In dai bazaka iya kama mun irin hayar da nake so ba."
"Saime Hauwa a fasa d'in. Ku dawo mun da kud'ina mana kiga in bazan samu wata matar ba." Fuuu ya tashi ya barni a dakalin gidanmu. Fuu nima na shige gida. washe gari kuwa muka

Please Login or Register in order to submit comment