Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suyan naman suna, su Baba kuwa sai k'amshi kawai. Marne 'yan uwanta suka wuce da'ita wankan gida ba tare da sun nemi izinin Sada ba. Da yamma ya dawo daga aiki ya tarad d'akin a kulle. D'akin Baba ya shiga ya sameta a kwance.
"Baba ba lafiya ne?" Kallonshi tayi, taga duk ya sake sirancewa ga duhu da yayi. tace.
"Kaga irin matsalolin da nake guje maka kenan. Yanzu ka duba k'aninka yanda Harira take mishi biyayya. Har wanki take yi mishi, amma kai sai dai ka yi ma Marne wanki duk ranar lahadi, ni uwarka ina kallo, bak'in ciki saiya kasheni tukunna za ku ji dad'i ko? Babu komai." Shiru yayi kawai, shi kanshi yana mai nadamar auren Marne da yayi a rayuwarshi, kuma baisan me yasa baya iya taka mata burki ko tana fad'ama mahaifiyarshi magana ba. Shi kuwa ai babu irin d'iban albarka da bata mishi. Dan dai ya riga ya aureta ne kawai.
"Baba ki yi hak'uri ni kaina ina mai nadamar auren Marne da nayi wallahi. Yanzun ina su ka je, ko raka 'yan uwan nata ta yi ne?" Baba ta dubeshi tace.
"Au basu fad'a maka dama za su d'auketa wanka ba?" Da sauri ya d'ago yace.
"Wallahi babu abunda su ka ce mun Baba, tafiya da ita su ka yi?" Baki Baba ta tab'e.
"Ai kuwa sun tafi, ai yanzu sunfi rabi. Dan tun safe suka tafi. Ni dai abunda zan ce da kai shine. Ka dage da ibada domun ban yarda da matarnan taka ba, karka dinga sake baki kana kwana bacci, A'a rabi a gado, rabi goshinka a k'asa zai fi maka alkhairi. Nima zan sake zagewa da adda'a."
Sada jiki a mace ya isa k'ofar d'akinsu ya b'alle d'an makullin ya shiga. Tunani kawai ya shiga yi, ya cuci yaranshi daya zab'a musu uwa irin Marne mara tarbiyya da sanin ya kamata. Ya bi kyau da k'amshi, yanzu ga yanda abun ya zame mai. da yana da ikon sakin Marne daya yar da k'wallon mangwaro ya huta da k'uda. Amma ina sonta yana da tasiri matuk'a a xuchiyrmarshi.

KOSHOB'B'E
Da isar Marne cikin k'auyansu nan fa k'awayenta da jama'ar k'auyansu su kai ta zuwa mata barka. Kowa yana fad'in ta yi kyau sosai. Ta je ta tarad da k'annenta a gida. Ajidde itama tazo wanka gida da d'iyarta mace, sai Latifo kuma tana da tsowon ciki ta zo haihuwa, da yake a Mafa tayi auren nata. Ta ga k'annen nata duk sun lalace sun fita a haiyacinsu. tace.
"Waini cikinne yasa duk suka koma haka Ammi ko wani abunne?" Amminsu tace.
"Rashin dace ne kawai da mazaje, ke da kika dace ba gashi kinyi kyau ba, har kud'ad'en cefane ki ka dinga taramun. Kinga yanzu sai a duba miki d'an fili a siya miki ki adana abunki. Marne ta washe baki tace.
"Ammi kice in sake matsa lamba? Dan ba'a iya kud'in cefane na tsaya ba, ko kud'i ya shigo dashi gida sacewa nake yi, in b'oye a k'asan katifa, zan sake takurawa nan gaba in mallaki shanu. Ammi tace.
"Kin yi daidai Marne. Su kuwa shekara guda babu abunda su ka ajjiye.Haka su ka tawo gidan zik'au, kunsan uban naku malalacine nifa ke ciyar da kaina fa."
Haka rayuwa taci gaba da tafiya, Marne tana ta renon 'yarta Hauwa. Sada kuwa har yayi kumari a tafiyar marne harma ji yake yi dama ta yi zamanta. wasa_wasa sai da Marne tai wata takwas a gida sannan ranar Asabar da daddare sai ga su sun dawo gida, babu ko d'an rakiya daga ita sai jakar kayansu. Sada yayi murnar ganinta amma fa a daren da k'yar ta bashi hakkinshi sabida bai je ya dubosu ba.
Haka su ka ci gaba da gurgurawa. Wata Hud'u da dawowarta ta samu cikin Jamila. Rana d'aya wannan karon suka haihu da Harira, mata suka haifa dukka. Daga nan fa Haihuwa ta bud'e a gidan duk shekara sai Marne ta haihu. sai da ta haifi mata bakwai reras. Harira kuma yaranta maza hud'u mata biyu. A wannan lokacin yara sun cika gidan. Kullum a cikin rikici da Marne ake. Dan fa babu dama ta ji kukan yaranta sam. Sada kuma a lokacin sai dai ido tsakaninshi da Marne. Baba kuwa a kwance take tana fama da ciwon hawan jini. Ranar wata Alhamis tace ga garinku nan. Tun daga nan kan gida ya rabe. Domun dambe a tsakanin Marne da Harira kusan kullum ne. Da aka raba musu gadon Baba, Junaidu sai ya nemi gida kusa kusa ya siya, ya tattare kan iyalanshi suka tashi. Da yamma Sada ya dawo ya tarad Junaidu ya tashi, ba shiri ya fita yaje wajan Junaidun.
"Junaidu lafiyarka tun yanzu kan yaranmu zai soma rabewa ka sake gida ba tare da ka sanar dani ba. Junaidu yace.
"Na gaji da fitinar Marne ne Yaya, kullum a cikin rikici ake da'ita abun yai yawa ni na bar maka gidan da kake ciki duniya da lahira kuma dama da sunanka aka yi takaddar gidan shikenan, yara in Marne ta bari za su yi zumunci ai ƙila nan gaba in kowa ya mallaki hankalin kanshi, dan Marne ta gama lalata ma tarbiyyar yaranka, ina jiye musu ranar kuka, ranar dana sani. Sada ya shiga gida jiki a mace.
A lokacin ina da shekara goma sha biyu. Ina wanke wanke ya shigo.
"Sannu Abba da zuwa. Dubana yayi yace.
"Uwata ina gyatumar taku take?
"Tana ciki Abba. shiga ciki yayi.
"Yanzu Marne sabida rashin mutunci baki d'aukeni a bakin komai ba shine zan saka yara a makaranta ki ciresu ke?"
"Eh Sada na ciresu d'in yara dai nawa ne ni kuma nake ciyar da su, kai da ka lalata zuchiyarka da rashin nema, sai kace ba namiji ba shine zaka zo kana mun ihu aka. Lallai Sada ka rainani da yawa. Makaranta ba zasu sake zuwa ba.
"Toh sai me zasu dinga yi miki a gidan?" Shewa ta saka.
"In tusasu a gaba in ta kallan jarina mana." Sada yace.
"Jari kuma Marne?"
"kwarai kuwa jari mana Sada. Ai duk uwar da Allah ya azurtata da yara mata. wallahi ta huta, da ka haifi gwamna, gara ka haifi matar gwamna fa akace Sada. Kai dai bari su d'an tak'a kasha kallon motocin da za suita zuruftu a k'ofar gidannan dan wallahi ban haifa ma talaka yara ba. A take Abba ya soma tari yana nuna Ammi da hannu, harararshi kawai tayi. Fad'uwa k'asa yayi yafab. Nan kuma ta shiga kururuwar ihu. Dukkanmu muka fito mu ka yi cirko cirko.
"Hauwa kira mun junaidu maza Abbanku ya mutu. A guje na fita a gidan, ina shiga gidan Baffa na zube a k'asa ina kuka.
"Baffa Abbanmu ya mutu inji Amminmu." Hannuna ya kama muka koma gidan. A yashe ya tarad da Sada baya ko nunfashin arxiki. Ba'a tsaya wata wata ba sai asibiti. Da hanzari likitoci suka shiga da Abbana ciki. Ashe mutuwar b'arin jikice ta samu Abba a sakamakon bak'in ciki da Ammi take cusa mishi a zuchiyarshi.
Yasha jinya mai tsayin gaske, bazan manta ba a wulak'ance Abba ya mutu a cikin kashi da fitsari. tun safe ya mutu bamu sani ba, sai da daddare da Baffa ya shigo shine ya ganshi a mace." Ammi babu wani kuka da tayi. Muma dake akwai yarinta a tare da mu babu wani kuka da muka yi, sai kewar Abbanmu data dame mu. daga baya muka watsar.
BAYAN SHEKARA BIYAR
Zaune nake a gaban madubi ina kwalliya irinta yaran zamani. jikina sai tashin k'amshi yake yi. Na yi kyau sosai. Yarinyar Aminiyar Ammi ce ake Auranta. Kuma mune k'awayen Amarya. Yau za'ayi reseption ne. Sanye nake cikin shadda sky blue, da blue black a jiki. Sai gyalena ja, haka ma takalmina jane mai d'an karen tsini. Na fito a Shuwa sak. Bak'ina abun sone, kuma inaji dashi sosai, dirarriyar macece ni sosai. Mai cikar halitta, bak'ace ni wulik dan har shek'i nake yi. Amma abun mamakin duk inda na shiga sai an yabi bak'in nawa. A fuskata idanunane da hak'orana kawai farare. Lebb'na suna da kauri, amma bakin madaidaicine, bakine baƙina sitik irinna asalin shuwa arab, dan tun ina k'arama aka farfasamun bakin da allura, aka dinga shafa mun bak'in abu a bakin a haka ya warke. Wannan yana daga cikin Al'adar shuwa musamman mazauna k'auye. Domun a k'auye in yarinya ma bata da bak'in bakinnan bata auruwa. kuma za'a canfata. Ammi tayi mana mukam baki d'ayanmu. ina da k'iba ba sosai ba, kuma banda tsayi sosai. Gashina Bashi da yawa can can irinna shuwa, da kad'an tsayin gashina ya wuce wuyana. idanuna basu da girma sosai. Ammi tana kashe mana kud'i sosai. Wajan siyan mana sutura, da mayuka da sabulan gyaran fata iri iri, gashi duk bayan sati biyu saita kamamu tayi mana dulka, da dukkan dukkanmu.
"Ha'a Hauwa 'yar gayen Amminta. Kin fi su Jamila gaye fa. Ke na lura zaki kawo wani k'aton Alh ne gidannan. Kinyi kyau 'yar Albarka." Murmushi nayi sosai na farin ciki nace.
"Ammi ni kam zan tafi, bansan ko k'arfe nawa zan shigo ba." Dafani tayi tace.
"Ko kwana ya kama kiyi babu wani matsala Hauwa, ai zaki iya kula da kanki. Dad'i sosai naji. Nan na fice daga gida, zuwa gidansu Su Hasina Amarya. Na tarad dasu sun gama kintsawa tsab. Abokan Ango kawai ake jira. Suna zuwa kuwa muka tafi. A wajan taron bikinne Allah ya had'ani da Aminu. Ranar da bazata tab'a goguwa a cikin rayuwata ba kenan.

"Hauwa an dawo dake kenan, yaya jikin naki?" Muryar uwatale ce ta katseni a zurfin tunanin da nake ta faman ci. A sanyaye nace.
"Eh uwatale na dawo babu kowa a d'akin" Zama ta yi a bakin gadona tace.
"Mun tafi d'akin kiyon sana'a ne, muna fatan kema dakin ji sauk'i ki fara zuwa, daga nan kuma muka wuce dak'in koyon karatun addini." Kirjina sai nauyi yake sake yi mun, ji nake numfashina tamkar katsewa zaiyi. Uwatale ce ta duba laidar maganina taga ban sha ba. B'alla mun tayi tasa aka debo mata ruwa ta bani na sha.
"Nagode sosai uwatale, kuma na gode. Na kalli 'yan d'akin namu, wanda sai aikin sannu suke yi mun.
Idanuna na lumshe na sake lulawa tunanin sabon Aminuna, wanda ya soni so irinna gaskiya. Baccine yayi awon gaba dani, dan maganin hawan jini yana sa bacci sosai.


Mrs Bukhari ce


*TALLAH*
Ina kuke amare uwayen gida kai har ma da ƴan mata? Ko kun san Mrs Bukhari mai kayan ƙamshi, ai in dai batu na kayan ƙamshi gyaran jiki da na ɗaki to kai tsaye ku ne mi Badi'at domin gwana ce ta ko wanne fanni a ciki. "Wai ƙamshi kina nufin Badi'at dai marubuciyar nan tamu mai nishaɗantar da mu?"
"Tabbas Fati ita take magana, ai kin dai ji yadda ake magana a kai na, hatta me gidana ya jinjinawa Badi'at domin duk wani ƙamshi da zaki ji a jikina tare da gidana to daga ita ne, ke me kankat ma har gyara na nake yi domin gyaran aurena daga gareta ne, shi ya sa bana wasa da gyaran jikina da na gidana har kuke kirana da ƙamshi."
"Eh tabbas nima na jinjina mata, kuma zaki bani addireshinta domin nima na kwankwati wannan garaɓasa. Ko zaki iya faɗa mini abubuwan da take sayarwa.?"
"Bari na faɗa miki akwai...

Humra
Kulacca
Sudanese Humra
Kulacca ta gashi.
Turaren wuta ɗan gaske, iri daban daban.
Turaren mopping
Room freshner
Turaren turara kaya.
Turaren wuta na toilet
Sannan akwai ingantaccen maganin infection
Ina da magungunan mata, wanda zai gyara amarya da uwar gida.
Wanda zasu shiga daga ciki kuma
Akwai sabulun amare, da dilka ta amare, wanda zaisa amarya ta fito ta haska tas
Kabbasa
Setin kujerar tsugunno
Sannan inayin turaren wuta da kasko, da ashana wanda ake rabawa a taron biki ko suna.
Ina bayar da sari.

Ma sha Allahu to taya zan sameta domin mallakar nawa?

"Kai tsaye zaki mata magana ta whatsApp ko kiranta ta wannan number.

08179523215


*TALLAH*
A yau nazo muku da manya manyan magunguna domin gyaran Auranmu! Saboda yadda zamantakewarmu ta AURE keta kara tabarbarewa. Mata iyayenmu ku fito ku gyara jikinku , domin wallahi har Abadan macen da bata gyara bata isa ta hada kanta da mace me gyara ba har abadan! Mu gane yaku yan uwana mata, ma’aurata! wallahi gyara shine mace Akwai mata dayawa dasuka san magunguna na, a online Suna siya kuma Alhmdulillahi ba wadda ta siya bata dawo tamin godiya ba, Alhmdulillahi!Alhmdulillahi! Alhmdulillahi! Yawancin mata dayawa na nemana ta dayan sim dina sede nayi losing dinsa sede wannan shi yake Aiki 08104335144, A YAU NAZO MUKU DA MAGUNGUNA INGANCI DA IZININ UBANGIJI, WATO AINIFIN HADI Iri ~iri na MALLAKA D’ANA MIJI ALFARMAR ANNABI SAW, ina tabbatar muku da magunguna na babu shamaki base na tsaya bata lokaci a bayaniba zanso ku gwada dan tantance GASKIYA * Akwai cututtukan dake hana maganin mata aiki idan kinason sani ki tuntubeni ta wannan lambar 08104335144 wadannan cututtukan inhar kinadasu wallahi duk maganin daza kisha bazeyi Aiki ba, kuma bazaki taba fahimtar komiba a harkar dadih na magungunan mata.

*MUNADA MAGUNGUNA AVAILABLE KAMAR HAKA*👇🏽

*ingantaccen maganin infection *

Ingantaccen maganin basir

Ingantaccen maganin gyaran nono

Ingantaccen maganin gyaran hips

Ingantaccen maganin kara kiba kiyi dumur~mur dake

Ingantaccen maganin rage tumbi meyi tsakani da Allah

Ingantaccen maganin matsin farji mesa dadin farji ga azzakarin d’ana miji.

Ingantaccen MALLAKA TA DOMIN ALLAH (Bata harkoki) shine sunansa, hmmmm Wannan magani inada tabbaci a kansa shidin hadine kawai na mallakar d’ana miji akwai komi a cikinsa na mallaka hajiya ki gwada kisha mamaki Alfarmar Annabi SAW.

Se matsin (GAMADIDI) wannan matsi in kikayi amfani dashi har abadan abidina mijinki baze kawo a gaban wata ya mace ba in har ba gabanki bane wannan inada tabbaci a knsa 💯 kuma wadanda suka saya ma sun kara tabbatarmin da kyaunsa na mamaki.

Akwai zallan hadi na amarya

Akwai hadi na uwar gida sarautar mata wannan seat ne akwai komi a cikinsa.

Akwai ingantattun gumba iri iri kamar haka 👇🏽

Akwai gumbar Madara
Akwai gumba me rubutu 🤐
Akwai gumbar kankana
Akwai gumbar giginya (sa megida kuka)
Akwai ingantacciyar gumba me suna (BARIN MAKAUNIYA)
Akwai gumbar hasi
Akwai zallar gumba wadda ita ta rubutuce zallarta zaki ganta baka karki damu Aikin kawai zaki duba 😉
Akwai gumbar gero
Akwai gumbar ridi
Akwai gumbar garin gamadidi ita ta mallaka ce zallarta.🤐

Akwai tsumi iri iri sunansu sha yanzu magani yanzu 💯👇🏽

Akwai tsumin kankana
Akwai tsumin baure
Akwai tsumin rubutun Ayar Allah
Akwai tsumin kwakwa
Akwai tsumin giginya
Akwai tsumin GORON SUDAN (wannan special ne dan kudinsa ma daban yake)
Akwai ingantattun magunguna na tada shaawah kama daga na turawa har zuwa na Islamic wato namu na gangajiya. Akwaifa maganin maza madam na hausa dana turawa 😉 duk basuda side effects 👌

Akwai rubutun mallaka
Akwai zoben mallaka
Akwai hayakin mallaka
Akwai zani na mallaka
Akwai hadin ci da kaza
Akwai hadin yan shillah
(Muna dafa kaji da yan shillar ma dade sauran abubuwa da dama,)
Akwai dambun nama na mata wanda ke dauke da magungunan sirri na mata mesa tsantsi da laushi da ruwa a farjin mace 😉

Akwai magunguna na ban mamaki wadanda base na rubutasu ba saboda SIRRI 😉
Muna aika magungunan mu kasa kasa gari gari *UWAR GIDA KI GARZAYO QUEN SANAF Islamic chemist kise magunguna na ingantattun ne insha Allahu kin wuce takaicin d’ANA MIJI * direct to me 08104335144 muna sauraron masu shawarwari a kan zaman AURE insha Allahu, amma in knsan baki shirya siyan magungunan jima’i ba na mata ko na maza pls karki kirani.

_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*


_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*


_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿
[09/12, 19:49] Badi at: GAWURTATTU BIYAR
DAGA ALK'ALAMIN
BADI'AT IBRAHIM
MRS BUKHARI (B4B)

*ANGULU*
*DA*
*KAN ZABO*
15/16





Da wani irin farin ciki na wayi safiyar yau. Ashe dama haka soyayya take ne? Gaskiya ma'abotanta na morewa sosai. Tsakar gidanmu na fito dan a nan na jiyo hayaniyar jama'ar gidanmu. Ammi na gani a zaune a tabarma tana tsittsinka bank'ararrun kaji. Ga tea mai mugun kauri an had'a a k'aton jug. Hafsa tana bakin fanfo tana wanke kofuna, Jamila kuwa sai tsantsara kwalliya take yi. Maryam da Sameera kuma suna daga gefe can suna zuzzuba turarukan wuta a robobi wasu a kwalabe. Dan sana'ar Ammi kenan kuma sana'ar ta karb'eta. Kasuwar Kurmi ake kai mata wani babban shagon sai da turarukan mai. Ko na dubu nawa aka kai baya sati guda zasu kirata ana buk'atar kaya. Da wannan sana'ar take yi mana duk wata hidima. Aisha da Zainab kuwa suna gefen Ammi.
"Hauwa sai yanzu kika tashi ne?" Mik'a nayi ina hamma nace.
Wallahi Ammi, na jima ina waya ne jiya da daddare shiyasa banyi bacci da wuri ba. Zama nayi nace.
Wad'annan na gidan gonar fa Ammi daga ina?" Dariya muka saka dukkanmu Ammi tace.
"Hafsa ce Burina ya kusan cika a kanta. Jiya Allah ya had'ata da wani babban k'usa a wajan biki da kuka je. Shine fa ya saki aljihu yai mata siyayya, banda kud'in turare daya bata. Yau ma zai shigo gaisheni." Jijjiga kaina nayi a zuchiyata ina aiyana dama nice Hafsa dana more. Anya zan ma iya soyayya da Aminu kuwa?" Aminu fa talakane futuk mai na sama yaci balle ya ba na k'asa. Ni ina ganin nayi zab'en tumin dare. k'arar waya naji, abunda ya dawo dani a hayyacina kenan. Wata dalleliyar waya na gani a hannun Hafsa sai walk'iya take yi. Yawu na had'iye. Inaji Hafsa ta d'aga wayarnan tana wani lankwasa muryarta. Allah mai iko. Abunda nace a raina kenan.
"Ammi ce babu lafiya inaga bafa zaka samu damar ganina yau ba." Cewar Hafsa. Banji me gogan yace ba, na dai ji dariyarta ƙasa_ƙasa tana cewa.
"Toh Allah ya iso da kai lafiya." Ta ajjiye wayarta. Ammi tace.
"Yayi Hafsa, wallahi ke goyonace. Ai maxa irin gujjiyane su, kuma zuma ne su saida wuta. Gara mu yagi na yaga tun a waje, in in muka samu kika shige daga ciki ai kakarmu ta yanke saƙa. Me yace miki?" Fari Hafsa tayi tace.
"Baki ji yanda ya rud'e kamar gyatumarshi ce babu lafiya ba, cewa fa yayi gashi nan a hanyar zuwa ya duba ki, inta kama ma sai mu wuce asibiti wai. Shewa dukka suka saka. Ni kuwa nayi banza da kaina a zaune. Ina mamakin yarinya k'arama ta san takan kirsa irin tamu ta mata. Kiran wayata ne ya katseni. Aminu ke kirana. Gefe na koma.
Hello Aminu barka da safiya"
"Yauwa barka Hauwa Amma ya naji muryarki a b'ace, lafiya kuwa?" Baki na tab'e dan haushi ya soma bani, ni rabuwa da shi zan yi gaskiya.
Lafiya lau kawai Ammina ce bata da lafiya shine duk hankalina ya tashi. A gigice yace.
"Subuhanallahi, yaya jikin nata amma?" Nace.
Da sauk'i"
"Ki gaishe mun da ita da jiki, bari in barki sai na zo da daddare." Katse wayata nayi ina cizon yatsa. Ko yace zai zo ya dubata ma. duk da ciwon k'arya ne. k'wafa nayi, komawa nayi wajansu Ammi. Nan muka soma yagar kaji. Wayar Jamila ta soma kuka. Nan muka fashe mata da dariya.
Saurayinta ne mai kaji yake kiranta. A turb'une ta amsa.
"Hello" Ba mu ji mai yace mata ba, sai ji mu ka yi tace.
"Gani nan fitowa." karyawa taci gaba dayi har sai da ta gama tsab ta fita. Bata dawo ba sai da ledar kaji guda biyu manya manya, a gyare a fige. Gud'a Ammi ta saka tace.
"Haihuwa ta yi rana. Ƴaƴa mata jarine. Yafi duk wata hajar da me haja zai baza dancin riba. kai masha Allah, ya ga jan baki da hoda, yarinya fara mai diri." Hon d'in motar saurayin Hafsa ne ya katse Ammi.
"Hafsa maza je ki shigo dashi, ni kuma bari in kwanta. Hauwa d'akko mayafi da filo." Da sauri na d'akko mata. Ba shiri ta kwanta na rufeta. Yarane suka shigo da katon na ruwan Faro. da katon biyu na moltina. Sannan sai ga Alh da Hafsa sun shigo, wata dakakkiyar bazin ce a jikinshi. sai maik'o take yi. Duk girmanshi a gaban Ammi ya zube yana gaisheta. Nera dubu ashirin ya ajjiye a gabanta yai mana sallama. Hafsa data tashi shigowa da kayan mak'ulashe ta shigo. Wunin ranar sam saina kasa sukuni. Aminu ne yake ta kirana a waya. Agogon wayar na kalla k'arfe takwas na dare. Da kyar na d'aga wayar, ban iya cewa komai ba.
"Hauwa ina waje a k'ofar gidanku, kamar yanda ki kai mun kwatance." Wayar na kashe, na mik'e kwallin da Ammi ta had'a mana na musamman dan jan hankalin d'a namiji na ranbad'a a idanuna, dama hodar farin jini da jan hankalin ɗa namiji ita muke shafawa a koda yaushe. sannan na fita dan cikin kwalliya nake tsab.
Yana rab'e a jikin bangon gidanmu. Hafsa kuma tana zaune a bakin ƙofar motar Alhnta, shi kuma yana tsaye sai zuba yake yi mata. Jamila kuma tana zaune akan roba robar saurayinta mai kaji. Takaici duk ya cika ni. yanzu a dakali zamu zauna kenan, irin matsiyacin dana yayiɓoma kaina kenan? Bafa zata saɓu ba bindiga a ruwa. Fuu na wuce dakalin gidanmu na zauna, na bud'e Aminu da k'amshina mai janye hankalin mai shaƙa. Isowa yayi wajan ya zauna.
"Hauwa amma kamar an tab'amun ke ko?" K'inyin fara'a nayi, sai ma sake haɗe raina da nayi nace.
"Kaza nake ta son inci tun safe, ban samu ba har yanzu." Murmushi yayi mun yace.
"Kaza fa, ke bakya jin garinne Hauwa? Kaza fa dubu uku take, dubu uku ai garinta da nisa. Harararshi nayi, kaina na juya.
Kenan bazaka iya siya mun kaza ba ko Aminu, a haka ne zaka iya soyayya dani? Toh bari kaji duk wani fitowa da zanyi wajanka saika biya dan wallahi bazan yi fitowar banza, in sha sanyin banza ba. Kai nifa in bazaka iyaba kaje kawai." Iska ya busar a bakinshi, shiru yayi yana kallona k'ur, bagabaki d'aya hankalinshi na lura ya tashi. Da gaske Aminu ya zurfafani a zuchiyarshi sosai. sai naji ya d'an bani tausayi, amma dole in matse dan bazan iya zancen banza ba.
"Hauwa bari in fito in zaiyana miki koni waye tun yanzu. Domun na lura tafiyarmu kamar bazata yiwu ba, danni talakane, kuma aure ya kawoni ba shashanci ba.
Ni dai marayane, mahaifina ya rasu tun ina k'arami. Mu biyu mahaifiyarmu ta Haifa, dani da k'anwata Tahira. Nauyin gidanmu tun ina d'an shekara goma sha biyu ya hau kaina. hakanne yasa ban samu damar karatun boko can ba, iyakata faramare, amma nayi karatun addini madaidaici. Mu fulanin Adamawane, danginmu duk suna can. Ni ma aikacine a babban shagon sai da iskar gas, wanda yake kan titin mandawari, albashi nake d'auka duk sati. Hauwa wannan shine Aminu a tak'aice, ba da yaudara na zo ba, zan baki kulawa daidai k'arfina, zan kula da ke in sha Allah. Duk abunda kike so zanyi miki, kin amince dani ko kuma in yayyafama zuchiyata ruwan salama?" Tsintar kaina nayi da amincewa. Daga nan muka b'alle da hirar soyayya. Na saki jikina har da dariya. Da zan shiga gida ya kawo nera dubu biyu ya mik'o mun.
"Ga kud'in zancan ina fatan bai yi kad'an ba?" Hannu nasa na amsa.
Babu laifi dai, amma dan kad'an kam yayi." Murmushi yayi.
"Hauwa rigima.Zan tafi ni kam. Ki gaishe da Ammi da jiki. Sai gobe inna dawo, kya ban labarinki ko, dan sanin dawa nake taraiya. Sallama mukai da juna na shiga gida. Ammi na samu a tsakar gida, hannunta ta mik'o.
"Bani kud'in zancan, ko a haka kika bari ya tafi baki yago komai ba?
Dubu biyun na mik'a mata.
"Hauwa matsiyacine kika tsaya b'ata lokaci a kanshi, nera dubu biyu ya baki da zai tafi? Amman kin cika asararriya, ai ko kuɗin turaren da kika shafe jiki dashi bai biya ba, balle azo kan jan baki da hoda" Hafsa da ta shigo ta saki shewa tace.
"Bari kiga masu yi dan Allah Ammi.
Dubu goma ta mik'a ma Ammi. Tsaki nayi na shige ciki, baƙin cikin Hafsa yayi mun katutu sosai. Ba dan Aminu yayi mun ba da dole in yima Hafsa ƙarfa_ƙarfan Alh kota halin ƙaƙa ne"
Soyayyarmu sati biyu kenan da somata, kuma kullum Aminu yana xuwa zance, wataran ya bani dubu

Please Login or Register in order to submit comment