Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan tunanin a cikin ransa, ya yi tagumi. Wannan ranar ya tanadarwa Nasrcen dinsa, sai ga shi a lokaci guda Allah ya yi ikonsa, wanda babu wanda ya isa ya yi jayayya da yinsa. Shirin zuwa office ya fara, yana tunanin dole sai an samo ma’aikata sun yi masa gyaran gidansa domin har yanzu wari yakeyi sosai. Tashinta ya yi yace ta koma dakinta zai rufe Kofarsa. Ba ta yi mamakin rashin mutuncinsa ba, domin tuni ta fara haddace su. Tana dingishi ta fice.
Faruwar wannan lamari tsakanin Zakiyya da Sultan ya sanya mata wani irin sonsa, a cikin zuciyarta kamar ta mutu. Tana jin bata taba mu’amala da wani namijin da ya gigita tunaninta irin Sultan ba. Duk inda ake neman namiji mai mantar da mace damuwarta, Sultan ya hada abubuwan nan. Tana jin ko dukanta zai dinga yi kullum ba za ta rabu da shi ba. Haka ta raina iyawar Bilal duk yadda take yabonsa kuwa. Shi kuwa ya kasa farin ciki da irin sabon lamarin da ya shiga, abin ya kasa burge shi, haka shi bai san yadda budurwa take ba bare ya fahimci abinda Zakiyya ta yi. Yan sandan ya basu umarnin su samo masu aiki a tsaftace masa cikin gidansa, a fitar da dukkan abubuwan da suka lalace.. Jaridar da ya samu a cikin motar ya dauka yana dubawa. Gabansa ya fadi da ya ga hotonsa hade da na Zakiyya. Cikin sauri ya ware ya fara karantawa. Ya gigita iya gigita, don haka ya ce wa direba ya juya gidan. Yana fitowa daga mota ya dubi-~daya daga cikin ‘yan sandansa yana tambayarsa yaushe akayi wannan hirar? Cike da tsoron yadda ya ga yanayin Ubangidansa ya gaya masa komai. Sultan ya daga hannu ya wanke shi da mari, ya sake daga hagunsa ya dauke shi da mari yana huci. “Ashe baka san aikinka ba aka kawo min kai? Ashe idan kashe ni za a yi zaku iya ba barawon hanya? A cikin gidana zaku bar ‘yan jarida su shigo har falona? Wannan wani irin shirme ne� sandan ya ce, “Sorry sir! Mun so mu hana su, madam ta fito ta zage mu ta ce su shigo.� Sultan ya daka masa tsawa, “Ka yi min shiru bana son bayanin nan. Ita kuke yiwa aiki a gidan nan ko kuwa ni? Daga yau babu wata mace da za ta sake sa doka wani a cikin ku ya bi, ba tare da ya tuntubeni ba. Saboda kune sakarkaru har ayi wannan abun tsawon kwanaki babu wanda ya taba gaya min? A kan me?� Ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, za su iya rantsewa tunda suka fara aiki da shi, ko tsawa babu wanda ya taba yiwa, amma yanzu harda mari, lallai ankai shi Karshe kenan. A fusace ya taka ya shige dakin Zakiyya. Tana zaune tana waya tana bada labarin yadda suka kasance da Sultan, wanda karaf a kunnensa. A duniya ya tsani mace mara sirri, ji yake kamar ya shaketa ya huta. Tana ganinsa ta cire wayar tana zare idanu. “Ke ashe baki da hankah? Da izinin uban wa kika je kika yi hira da ‘yan jarida? A ina kika sami lambarsu da har kika gayyato min su cikin gidana?� Yadda ya harde hannayensa ya kafeta da idanu ta gane amsar kawai yake buKkata, ta ce, “Wata Kawata ce da ke aiki a gidan jarida, ta hada ni da su, shine suka zo. Kayi haKuri bansan zai bata maka rai ba.� Sultan mutum ne mai son


*Idan kina bukatar cigaban wannan littafin na RUBUTACCIYA da wasu guda biyu UMM ADIYYA by aziza Idris gombe da MISBAH by SA'ADATU WAZIRI GOMBE kiyiwa wannan number magana ta WhatsApp 09068032427*

🦚RUBUTACCIYA BOOK 1 KARSHE🦚*


CHAPTER 10



*BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*




A JIYA MUN TSAYA

sandan ya ce, “Sorry sir! Mun so mu hana su, madam ta fito ta zage mu ta ce su shigo.� Sultan ya daka masa tsawa, “Ka yi min shiru bana son bayanin nan. Ita kuke yiwa aiki a gidan nan ko kuwa ni? Daga yau babu wata mace da za ta sake sa doka wani a cikin ku ya bi, ba tare da ya tuntubeni ba. Saboda kune sakarkaru har ayi wannan abun tsawon kwanaki babu wanda ya taba gaya min? A kan me?� Ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, za su iya rantsewa tunda suka fara aiki da shi, ko tsawa babu wanda ya taba yiwa, amma yanzu harda mari, lallai ankai shi Karshe kenan. A fusace ya taka ya shige dakin Zakiyya. Tana zaune tana waya tana bada labarin yadda suka kasance da Sultan, wanda karaf a kunnensa. A duniya ya tsani mace mara sirri, ji yake kamar ya shaketa ya huta. Tana ganinsa ta cire wayar tana zare idanu. “Ke ashe baki da hankah? Da izinin uban wa kika je kika yi hira da ‘yan jarida? A ina kika sami lambarsu da har kika gayyato min su cikin gidana?� Yadda ya harde hannayensa ya kafeta da idanu ta gane amsar kawai yake buKkata, ta ce, “Wata Kawata ce da ke aiki a gidan jarida, ta hada ni da su, shine suka zo. Kayi haKuri bansan zai bata maka rai ba.� Sultan mutum ne mai son mutumin da

ZAMU TASHI

zai aikata kuskure ya kuma amsa ya aikata har ya bada hakuri. Don haka ya sassauto, “Ki kiyaye kanki, ki kiyaye mutuncinki, matar aure ce ke, bai kamata ace kin fito a haka a gidan jarida ba, kamar ba matar aure ba. Idan kin siya min mutunci kanki kika siyawa. Daga Karshe kada wani ya sake shigo min gida ba tare da izinina ba, yin hakan zai jawo maki tarin matsalar da baki taba tunani ba.� Ya juya abinsa cike da takaici. Ashmaan ya kira shi a waya, sun jima suna tattaunawa, sannan suka yi Sallama. Yana isa office yaga babu wani aikin kirki, ya shirya motar ‘yan sanda suka kama hanyar Kaduna. Nasreen tana zaune ta hada kai da wani abun, gaba daya ta yi baki, ta rame ta sauya daga Nasrcen din Sultan ta koma Nasrcen Kankia. Nawfal ya koma kamar mai sana’ar bola, haka duk inda ake meman dan uwa Nawfal ya wuce hakan. Hakika da babu Nawfal da rayuwar Nasrecn ya zama abar Kyama. A zaman su maza sun sha kawo mata farmaki, Nawfal ke tsayawa kai da fata wajen ganin ya kareta. A Kalla da zuwansu garin nan, sun yi sana’a yafi kala ashirin. Haka sun

kwana a wurare mabambanta, A yanzu haka ma Kosai ya siyo mata ya ajiye a gabanta tana ci, sai da ta gama sannan ta fara shan kokon, idanun Nawfal suka hasko masa hoton Sultan. Ya yi saurin dauka yana dubawa. Hotonsa ne tare da matarsa. Nawfal ya kafe su da idanu, ya gama karantawa yana al’ajabin irin wannan matsayin da Sultan ya samu, wanda a yanzu wane su su iya tunkarar gidansa? Bakinsa ya subuce ya ce, “Nasreen Deedinmu ya tare da matarsa yanzu ya zama A.I.G Kin ga yadda ya Kara kyau kuwa? Sai dai matar ko lullubi babu a jikinta.� Nasreen ta gigice iya gigicewa ta hau lalube, “Nawfal a ina ka gani? Ya zan yi in gani ni ma?� Bai dube ta ba ya ci gaba da duban jaridar Kosan, “A jarida na gani, wanda a ka Kunsa maki Kosai. Nasreen ke da ba idanu gareki ba ya za a yi ki iya gani?� Nasreen ta goce da kuka. Hakan yasa Nawfal ajiye jaridar ya kafeta da idanu ya rasa me zai ce mata kawai sai ya zuba mata idanunsa wanda shima hawayen ke zuba daga kwarmin idanunsa. A hankali ya fara magana, “Kin gani ko? Deedi ya fi Karfinmu a yanzu. Dole zamu ci gaba da zama a nan, domin gujewa abinda zai sa hankalinsa tashi. Na san soyayyar da zamu nuna masa kenan mu yi nesa da su. Ki kwantar da hankalinki akwai ranar da wahalar nan za ta zama labari.’� Muryar wani suka ji yana cewa, “Alhamdulillahi gasu can a lungun can.�
Nawfal duba Nasreen yace, “Mun shiga uku, waka gani waye?� , ne Mansur ya Karaso yana kwasar dariya, “Nasreen ni ne nan mijinki Mansur. Zuwa nayi insauya maku rayuwa inkuma ajiyeki ki zama matata.� Nawfal zai yi magana, wasu suka kama shi suka tura cikin mota, haka ita ma Nasreen din aka dauketa sai mota. Lalube ta shiga yi tana neman Nawfal, hakan yasa ya kama hannayenta, ta shafa fuskarsa zuwa kansa ta tabbatar da shi ne, don haka ta saki ajiyar zuciya. Ta riga ta sadakar mutuwa za ta yi, ta fi son idan za a kasheta Nawfal ya kasance yana kusa da ita. Sai da suka yi tafiya mai nisan gaske, kafin suka sauka a wani Kauye. A kuma Kofar wani gidan Kasa. Haka suka sauka suka shiga ciki Mansur ya umarci mutanansa da a shigar da su. Nawfal ya ce, “Dakata! Za mu iya shigar da kanmu ba sai wasu sun sake taba mu ba. Ya kamo hannun Nasreen suka shige ciki. Mansur ya nuna masu daki ya ce su shiga zuwa anjima zai zo. Haka suka shiga suka dunKule wuri guda daki komai sai ledan Kasa. Aka kawo musu abinci maradadi, haka suka tuttura suka sha ruwa
Mansur bai bata lokaci ba ya dawo hannunsa dauke da kwanon sha cike da fura yana isowa gabansu ya dubesu duba a tsanake sannan ya fara magana, “Na sha matuKar wahala wajen nemanki Nasreen. Hajiya Salma ta bani aiki akanki, domin in aureki in wahalar da ke, a lokaci guda kuma sai na ji ina son ki da gaske. Da naje gidanku sai Sultan ya watsa min Kasa a idanu, ya wulaKanta ni, ya shake ni yana neman ya kai ni inda ban shirya zuwansa ba. Ina cikin shirya wa Sultan kawai naji labarin Hajiya Salma tasa a sace ku saboda wasu dalilanta marasa tushe. A ranar da na sami labarin nan na yiwa Hajiya Salma gargadi akan duk abinda ya sameki ita ta siya da kudinta dan sai na fanshe bacin raina akanta. Hakan yasa ta tsorata ta gaya min inda aka kaiku. Daga Karshe take sanar min ashe kece matar da aka daura maki aure da Sultan. Bacewarki ya sa mahaifinsu gaya masu gaskiya, Sultan mijinki ne.� Nasreen da Nawfal suka ji dirar maganarsa kamar wani labari wanda ba zai taba faruwa ba. Ta gigice, ta shiga rudu, tana son ta Karyata shi domin Nawfal yaga jarida dauke da matarsa. Don haka ta girgiza kai tana kuka, “A’a ni ba matarsa ba ce, matarsa a yanzu haka tana gidansa.� Mansur ya kafe ta da ido, duk da ta lalace, amma har yanzu yana sonta, kuma da gaske yake ya shirya fuskantar kowacce irin matsala akanta. Zai jure koma menene yaga ya mallake ta. Girgiza kansa ya yi yana murmushi, “Ke ce matar Sultan ta farko, daga baya ne da aka yi ta jiran dawowarki aka ga shiru sai Hajiya Salma ta shiga ta fita ta mallake Abbanku, daga nan aka hada aurensa da Zakiyya ‘yar wajen Hajiya Ladidi, ba tare bada saninsa ba, sai ganin mata ya yi. Ya so ya ci musu ya Ki karbanta a matsayin mata, sai mahaifinsa ya yi masa nasiha, kasancewarsa mutum ne mai jin maganar mahaifinsa shi ne ya karbi Zakiyya a matsayin mata. Allah kadai ya sani ko suna zaman lafiya ko basa zaman lafiya. Amma tabbas ke matar aure ce, matar Sultan, Zakiyya ita ce matarsa ta biyu. Ni kuma ina son ki a yanzu haka, na shiryawa mutuwa akanki. Ki yi tunanin mafita, ina sonki babu idanun zan iya zama da ke. Zuwa anjima zan dawo in ji shawarar da kika yanke, ko aurena, ko kuma ki zama dadirona.� Mansur ya miqe ya fice, ya barsu cikin tashin hankali mara yankewa. Nasreen ta labubo hannun Nawfal ta ce, “Nawafal saita ni gabas don Allah.� Nawfal ya saita ta ta kai goshinta Kasa ta yi sujjada, “Allah na gode maka. Allah kai ne Allah, Allah ka bamu ikon bauta maka a bisa hanya madaidaiciya. Allah kai ka shirya wannna lamarin ka kawo min Karshensa. Allah na gode maka da ka amsa addu’ata a lokacin da ban za ta ba. Allah ka nuna min ranar da mijina zai dawo gareni.�
Farin ciki ya kama Nawfal ta yadda bakinsa ya kasa rufuwa. Haka ya shiryawa komawa ya damKawa Sultan matarsa. Ya kafe Nasreen da idanu yana kallon yadda take cikin farin ciki da annashuwa, wanda rabon da ya ga hakan tun suna gidan su Sultan. Daga baya kuma ya ga ta fara kuka tana magana cikin kuka, “Me muka yi wa Umma haka? Me yasa za ta sa rayuwar Abbanmu a cikin matsala? Duk Kokarin da Abba yake yi don yaga ya faranta mata sai da ta kai shi mahallaka? Me ya sa Deedi zai auri Zakiyya? Umma da kanta take siyo masifa tana kawowa cikin gidanta da sunan gyara? Rayuwar Abba a yanzu shi yafi bani tausayi. Yanzu tuntuni ni matar aure ce? Dama goron da Abba ya kawe min cikin farin ciki na daurin aurena ne? Me yasa Abba bai gaya min ba? Ina tafe da igiyar aure akaina ban sani ba? Allah ka sake hada idanuna da suke rufe da mijina ko da sau daya ne. Nawfal yanzu za ka daina nesanta ni da mijina? Yanzu ka amince son da nake yiwa Deedi a cikin jinina yake? Ka amince Allah ya riga ya hada jinin mu da su Umma? Abu daya ya rage mana shi ne mu gano su waye danginmu? A ina suke? Waye zai gano mana su? Deedi kadai yake da amsar wannan tambayar.�
Nawfal yasa hannu ya goge mata hawayen fuskarta, “Nasreen ba wannan ne a gaban mu ba, abinda ke gabanmu yafi Karfin wannan. Ta ya ya zamu iya rabuwa da mutumin da ya kira kansa da Mansur? Yanzu yafi Umma zama matsala a cikin rayuwar mu.�
Cak! Ta daina kukan, ta yi shiru kamar mai tunani, “Nawfal tunani ya Kare min, ban san ya zanyi ba. Mu ci gaba da addu’a kawai.� Dakin ya yi shiru Kowa da irin tunaninsa. A haka Mansur ya dawo ya same su, ya yi maganar duniya babu wanda ya iya ce masa ko zo ka c1 kanka. Sultan ya iso Kaduna cikin awannin da basu gaza biyu ba, ya wanzu a Kofar gidansu. Kallo daya ya yi wa gidan Nasreen ta fado masa a rai. Har ya juya ya ji muryar mahaifinsa yana masa sannu da zuwa. Ya dubi mahaifinsa sosai, a irin wannan lokacin kamata ya yi ace yana Office.
Tare suka shiga ciki suna rike da hannun juna. “Abba barka da gida.� Bai amsa ba, sai da ya dire shi a falon, sannan suka zauna. “Sultan idonka kenan?� Kafe hoton Nasreen ya yi da idanunsa har yanzu ba a cire hoton ba. “Abba ka yi haKuri na kasa . mance Nasreen. Abba komai ya sauya a rayuwar gidanmu abin yana ba ni tsoro. Ina Umma?� Abban ya dan yi shiru kafin ya ce, “Bana dan jin dadi ne shi ne na turata Office din taje ta sallami mutanen da suka yi Order tasa hannu.� Sultan ya girgiza kai yana al’ajabin yadda Umma za ta shiga harkar da ba nata ba. Haka kuma duk tsauri irin na Abba yau shi ne yake ba Umma izinin tafiya Office dinsa? Hafsat ta shigo ya kafeta da idanu, ta yi wani irin haske ta rame. “Barka da zuwa Yaya.� Murmushi ya yi ya mika mata hannu ta Karaso kusa da shi tana sunkuyar da kal, “Hafsat babu abinda ke damunki ko?� Girgiza kai ta yi tana sake duKar da kai. Sallamar Umma da Hajiya Ladidi yasa duk suka bi su da kallo. Hajiya Ladidi tana shigowa ta kwaye lullubnta tana satar kallon Abba. Ta jima tana kwadayin Alhaji Lukman a matsayin miji, amma bai taba kallonta ba. Sultan ya dan rankwafa ya gaida su, suka amsa cike da farin cikin ganinsa. Hajiya Ladidi ta ce, “Oh ashe kai ne a tafe? Shi ya sa muka ga garin hadari ya hadu. Ya su Zakiyyan? Ai mun ga � hira a jarida hira ta yi kyau sosai.� Sultan ya kauda kai kamar bai ji ba, ya dubi mahaifiyarsa ya ce, “Umma daga ina haka?� Tana shirin yin magana Haidar ya shigo yana sunkuyar da kai. Mamakinsa ya karu. Me yasa yaran basa son hada idanu da shi ne? Bayan sun � gaida shi ya dubi Haidar ya ce, “Haidar ka kammala karatunka me kuma kake jira?�
Ya dan sosa kai, “Har yanzu aikin bai fito bane.
Jinjina kansa ya yi, “Ka ba ni takardunka soja zan turaka. Zan ba Khamis shi zai yi maka komai.� Haidar baya son aikin soja, hankalinsa ya fi kwanciya a irin aikin Yayansa, amma kuma ba shi da yadda zai yi dole ya yi shiru kuwai. “Umma ki ba ni Hafsat intafi da ita Abuja.� Hafsat ta zaro idanu, yadda ta tsani takura idan ta koma gidansa ai ta shiga uku. “Ni dai Yaya nafi son nan.� Bai ce komai ba ya mayar da hankalinsa kan mahaifiyarsa da gaba daya ta sauya kamar ba ita ba. Umman ta daure fuska sosai, “Lafiya kake kallo na haka? Ni ka sanni Sarai na tsani irin kallon nan mai kama da na raini.� Murmushi yayi sannan ya dubi agogo, “Ya kamata in zo inkoma kada inyi yamma.� Abba ya girgiza kansa, “Babu inda za ka je, muna da bukatarka yau a gidan nan. Ka bari sai gobe sai ka koma.� Sultan bai zo da niyyar kwana ba, don haka ya fara zare agogonsa zuwa cire takalminsa. “Abinda kace ayi shi za a yi Abba. Idan ma kace in ajiye masu kakinsu indawo gida hakan zan aikata.� Abba ya ji dadin kalaman Sultan ba kamar su Haidar ba, da kullum suke yi masa rashin kunya. Zuwan Sultan ne yasa suke yi masa komai cikin girmamawa. Ya Kosa Hajiya Ladidi ta tafi, amma sai ta zauna a tsakiyarsu ta hana su motsawa. Hakan yasa ya dubi Abban ya ce, “‘Abbana zan je gidan Hajiya Gwaggo.� Abban ya mike yana satar kallon Hajiya Salma, “Muje nima na rabu da zuwa wurinta.� Sultan ya dan dakata yana kallon Abbansa. Bai iya yin magana ba, suka fito aka bude masu mota suka shiga. Sun fara tafiya ya dan waiwayo ya dubi Abba, “Yanzu Abba kana nufin Hajiya Gwaggon baka zuwa duba ta?� Abba ya hadiye yawu da Kyar ya ce, “Wato Sultan Hajiya Salma ta wuce duk yadda kake tunani. Ta kama komai ta yi kane-kane a kai. Yaran nan kada ka so kaga rashin kunyar da suke yi min. Ni na gaji watarana zaku iya nemana ku rasa.� Sultan ya yi shiru bai yi magana ba, gudun kada ‘yan sandansa su ji sirrin cikin gidan su. Hajiya Gwaggo tana jin murya ta tsaya kawai tana kallon su, kafin tai wuf ta shige cikin daki tana share
hawayenta. Abba ya durKusa a gabanta yana roKo. amma ko kallon sa ba ta yi_ ba. Sultan ya harde yana dubansu, har sai da ya tabbatar da ba za ta yi maganar da gaske ba, sannan ya shigo ya zauna kusa da ita. “Hajiya fushi kike da Abbana? Hajiya kin taba zama kinyi tunanin dalilin da zai sa danki ya gujeki bayan yafi kowa zumunci duk_ cikin ‘ya’yanki? Ashe danki ba zai iya shiga hatsari ki jawo shi jiki ki ji matsalarsa ba? Hajiya kin taba zama da danki kin ji matsalarsa? Mahaifina yana cikin wani halin da yake da buKatar addu’arki.� Sultan ya Karashe maganar idanunsa jazir, yana jin da zai iya zubar da hawaye babu shakka mahaifinsa zai fara yiwa kuka.� Hajiya ta dan sassauto ta dubi Sultan ta ce, “Sultan har gidansu naje a gabansa Hafsat da Haidar da uwarsu suka wulaKanta ni, amma ya kasa magana. Ban yi fushi ba, na sake dawowa haka suka sake cin mutuncina. Kai ba zan. taba mance wannan abun ba.� Sultan ya dan yi shiru kafin ya girgiza kansa, “Hajiya ki yi hakuri. Abba ya sauya daga Abban da muka sani shekaru talatin baya. Umma tana neman tasa Abba a wani hali. Hajiya kiyi wa Abba addu’a ta haka ne zai sami sassaucin abinda ke damunsa. Abinda yasa na tsani zuwa gida Hajiya kin sani, saboda su Nasreen. Da zarar na shigo sai zuciyata ta dinga gaya min zan gansu a kwance a daki. Hafsat kuma da Haidar ki zuba ido ki ga irin matakin da zan dauka akansu. Kin wuce mu tsaya muna kallon wasu su wulakanta mana ke, bare kuma mu da kanmu.� Haka ya yi ta ba ta baki har ta sauko ta kuma sawa Abba albarka, wanda yake jin kamar ansauke masa wani tarin kaya ne a kansa. Hajiya Gwaggo ta kawo masu_ tuwon shinkafa, suka ci kwano daya da mahaifinsa, sannan ‘suka bar gidan. A hanya suka wuce gidan Alhaji Mu’azzam, wanda ya fada harkar siyasa babu ji babu gani, kullum yana gidajen radio yana kumfar baki. Shi kansa ya ji dadin ganin Sultan har ya nemi taimakonsa akan abubuwan da yasa a yaba, Sultan ya nuna masa babu damuwa. Abin mamaki har suka dawo Hayjiya Ladidi tana nan a gidan, hakan yasa ya wuce dakinsa yana kallon yadda aka tsaftace dakin.
Shiru ya yi yana tuna ranar da ya kasance tare da Nasreen, wannan daren ya kasa Bace masa, haka sai da aka gaya masa matarsa ce ya tuna da irin murmushin da Abban ke jifarsu da shi a ranar da ya kamata ya yi masu fada. Rintse idanunsa ya yi, Ashmaan yana can yana bincike a kan mutuwar mahaifiyar su Nasrcen, ya Ki bari wai sai sun bayyana tukunna, kamar yadda suke tunani. Yana nan kwance ba barci yake yi ba, jira yake Hajiya Ladidi ta bar gidan ya ci mutuncin° Kannansa, domin abinda suka yi wa Hajiya Gwaggo ya tsaya masa a rai. Daga dakin yake jiyo surutai hakan yasa ya fito yana duban yadda Hafsat da Haidar suka hayayyakowa mahaifinsu, suna cewa yaje ya kwashe komai ya gayawa Sultan. Sultan ya kirawo ‘yan sandansa ya ce yana son su sauyawa Haidar kamanninsa. Ita kuma Hafsat ya zare belt ya dinga auna mata. Umma fa ta gigice, sai ta yi wurin da ake dukan Haidar da gudun gaske tana kuka, sai kuma ta koma tana zagin Sultan tana cewa idan bai daina dukan Hafsat ba za ta tsine masa. Ko kallon ta bai yi ba, hukunci kawai yake yi. Sai da Abbansa ya yi magana sannan ya dakata da dukan Hafsat ya kuma dakatar da dukan Haidar, wanda tuni ya zube a nan yana numfarfashi. Sultan ya dinga masifar da ya basu tsoro, ya botsare masu ya sauya kamar ba Sultan din da suka sani ba. Yana ji a ransa ba zai iya barin mahaifinsa a cikin gidan nan ba, kada watarana su kashe masa mahaifi su barshi da maraici. A take ya kira Khamis ya zayyane masa komai, Khamis ya ce, kawai ya turo shi Abujan shi zai yi maganinsa, kuma dole ya tafi aikin sojan nan. Don haka Hafsat kadai zai barwa Umma a gidan. Umma ta Karaso tana masifa ya dube ta duba sosai ya ce, “Umma zan dauke mahaifina daga gidan na rasa me ke masa dadi? Tunani ne fal a cikinsa. Ji ya yi ankwanta a bayansa, bai hanata ba, haka bai hantareta ba, kamar yadda zuciyarsa ke gaya masa, Haka ta shammace shi suka sake komawa wata duniyar. Shi dai ko dan bai saba bane? Idan ba haka ba, ya kasa jin wani abu mai kama da dadin kasancewarsa da ita. Amma kuma tana da Kima a idanunsa musamman da ta kama kanta. Barci take shaKa harda minshari, wannan abu ya sake daure
“masa kai. Minsharinta ya dame shi Kwarai domin ya tsani namiji ma mai minshari bare kuma mace,
Bubbuga ta yayi ta farka tana sake luma idanunta a
cikin nasa; Zakiyya wata irin jarababbiyar yarinya ce, wanda a farko ta yi masa kawaici amma a yanzu ba za ta iya ba, ya zama dole su sake komawa duniyar da suka fito. A idanunta ya fahimci

Please Login or Register in order to submit comment