Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

meyasa zaki wareni daban a cikin ‘yan uwana? Laifi ta yi na hukuntata. ? Ta yi Kwafa kamar za ta kai masa duka, “Ita ta kusa da kai ba ta laifi ne ko me? Kada ka sake dukar min yara na gaya maka.? Bai bata amsa ba haka bata daina masifar ba, har sai da ta gaji ta juya abinta. Shi kuma ya kamo hannun Nasreen suka shiga mota. Wani wuri ya kaita © mai dauke da sanyi irin na korama. Tana zama ta shaki irin Kamshin da wurin yake yi, ta ce, “Deedina ina jin wani irin yanayi mai dadi a jikina. Dee da ba ka nan na yi ta kewar ka, amma kuma ina yi maka addu’a.? Sai da ya zauna bayan ya gama kallonta sannan ya ce, “Nima nayi kewarku ke da Nawfal kamar insa a kawo min ku, sai nayi tunanin karatun ku. Nasreen zaki iya tuna wanda ya watsa maki abu a idanu?? Hawaye suka gangaro fuskarta kamar daman tana jira ne, “Deena bansan waye ba. Ka bar maganar nan abinda Allah ya aiko kenan.? Jawota ya yi ta kwantar luf a Kirjinsa tana sakin Wani irin ajiyar zuciya. Hakan ya haifar da abubuwa masu girma da wahalar fassarawa a tsakanin su. Sultan kenan! Kowa kallonsa yake miskili mara son hayaniya, haka alamu sun nuna idan ya kama mai laifi baya sarara masu. Idan ka ganshi tare da Nasreen za ka iya rantsuwa ba Sultan dan sanda bane. A kunnenta yayi magana, “Kada ki damu, akwai zaman da zamu yi da abokaina akan wata matsala, don haka zanyiwa Dr. Aslaf magana, akan idanunki zai bamu shawarar Kasar da ya kamata mu tafi da ke sai a duba idanunki. Idan ba haka ba, waye zai aurar min Nasreen dina a haka?? Wani irin tafiya ta yi mai kama da tafiyar barci. Ga iska yana Kara kada su. Tana murmushi tana magana kamar wacce ta sha wani abin maye, “Deena, zan zauna tare da kai ba zan auri kowa ba.? Dagata ya yi saboda da gaske ya gane tana cikin wani yanayi. “Tashi muje Office dina.? Girgiza kai ta yi, “Ina son indauwama a nan wurin. Kamshin filawowin suna sanya min nishadi da sanyi a zuciyata, wanda rabon da in ji ? hakan na jima. Dee wani abu ke tsaya min a Kirji yana min zafi sosai, ko nasha ruwa baya wuce wa.? Wannan Karon tausayinta ya kama shi, Nasreen ta yi Karama da yawa da shiga irin wannan yanayin, “Ki dinga addu’a Nasreen kin ji? Mu je Office dina akwai abinda zan dauka.? Da isar su Office din, “yan sanda suka taso ° suna sara masa, shi dai yana rike da hannun Nasreen. Gaba daya mutane idanunsu akan Nasreen yake, wani ma cewa ya yi koda take makauniya zai iya aurenta inhar Oga zai ba su ita. A kujera ya ajiyeta, a lokacin ne kuma aka gaya masa wani case ya ce, a shigo da matar a gurguje. . ? Tana shigowa tana bayani bai dago daga abinda yake yi ba bare ya dubeta, “Yallabai mijina ne ya zaneni,? Yana rubutunsa ya ce, “Me kika yi masa har ya duke ki?? Ta share hawayenta ta ci-gaba da magana, “Ya musuluntar da ni ne, ya raba ni da kowa, ya ce min addinin musulunci shi ne addinin gaskiya, nasha wahala da iyayena har na rabu da su, na zabe shi da addininsa. Amma tunda na aure shi kullum sai ya yi min gori akan addininsa, kullum idan na yi kuskure sai ya ce min matsalar tubabbe kenan. Yallabai ina son a raba aurena da shi, zan koma addinina, ko dan inhuta da gorinsa da na ‘yan uwansa.? Tun bayan da ta ambaci ta koma addininta ya ajiye rubutun yana dubanta. Damuwa ce shimfide a fuskarsa. Har yaushe musulman mu za suyi hankali? A hakan wasu suke son jawo wadanda basa addininsu su dawo addinin su? Bai yi magana ba, har sai da ya gama nazari sannan ya ce ta fada inda za a ga miinta. Ta kwatanta ‘ya bada umamnin a je a kawo masa shi yanzu. Ya dubi matar ya ce, “Amma kafin in ce komai, daina daukar musulunci haka yake. Musulunci abu ne mai sauki da kuma dadi. Idan kina cikin musulunci zaki sami hanyoyin warwarewar matsalarki, wanda ina ganin baki bi hanyar bane shi ya sa kike dan samun matsala. Haka kuma mu a cikin addininmu akwai jarabawa, da Allah yake yiwa bayinsa. A Karkashin jarabawar nan zaki sami hanyar shiga Aljannah. Misali a cikin Alqur’ani akwai waraka a ciki. Ko malamin da ya musuluntar da ke bai gaya maki hakan ba?? Sunkuyar da kanta Kasa ta yi ta ce, ‘“Malamin ya yi min bayani. Amma bai gaya min musulmi zai lya yiwa wanda ya aro addininsa gori ba, haka bai gaya min akwai duka a cikin sharuddan aurenku ba. Ina zuwa Islamiyya har yau ban ji inda malaman ta ce ana gorin addini ba.? Sultan ya rintse ido yana kallon rubutun suna komawa kamar yashi. Saudat! Ita ta fado masa arai. Mahaifiyar Nasreen da Nawfal. Tasha gori akan addininmu amma kuma tana rike da mu. Hatta mahaifiyarsa har yau tana yi wa su Nasreen gori akan addinin da Saudat ta aro. Sultan ya girgiza kansa, “Hakane, haramun ne ma musulmi ya ci zarafin dan uwansa musulmi. A cikin addininku akwai na banza akwai na kirki, haka muma a cikin addinin mu, akwai irin hakan, Amma mu ba mu gorin addini, haka kuma ke kin fi shi rashin zunubi, saboda kin tuba kin musulunta. Addinin musulunci akwai dadi idan kika natsu a cikinsa. Dokokin mu basu da tsauri. Haka a KarKashin wannan auren da kike son a raba zaki shiga Aljannah. Haka ina son ki zuba ido ki gani, tun aduniya Allah zai saka maki, akan mijinki idan har da gaske yana zaluntarki. Shi Allah baya barin azzalumi. Kada zuciyarki ta yi rauni kawai dan namiji yana cuzguna maki, ki dauka irin taki jarabawar kenan. Idan Allah ya dubi zuciyarki ya tabbatar a wadace take da imani, da son addininsa, sai shi kuma ya saka maki. Kada ki ce wai sai kin ji dadi sannan zaki yabawa addinin musulunci.? A lokacin kuma aka shigo da Bala mijin Karima. A Kasa yasa ya zauna yana aika masa da mugun kallo mai cike da tsana. “Ka san wannan ko?? Ya nuna masa Karima da hannu. “Yallabai na santa matata ce, shekarun mu uku da aure da ita.? Sultan ya dinga jinjina yayi wuri ta fara fuskantar matsala, “Ta ce tana son a raba aurenku, saboda kana dukanta, don haka zan tura ku kotu, daga nan zaka amshi irin naka hukuncin.?

*Idan kina bukatar cigaban wannan littafin na RUBUTACCIYA da wasu guda biyu UMM ADIYYA by aziza Idris gombe da MISBAH by SA'ADATU WAZIRI GOMBE kiyiwa wannan number

🦚RUBUTACCIYA BOOK 1🦚*



CHAPTER 4



*BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*

*Wannan littafin na kudine idan kina bukata kiyi magana ta wannan number 09068032427*



A JIYA MUN TSAYA

Abbansa. ? A falon ya tara kowa yana faman kaiwa da komowa ransa a matuKar bace.,“Ya zama dole ku gaya min wanda ya aikata wa Nasreen wannan abin,:ko kuma in hada ku dukka in kulle.? Hajiya Salma da ba ta dauki lamarin zai yi irin wannan zafin ba, ta ware idanu, “Yanzu a kan wannan yarinyar za ka kulle su?? Alhaji Lukman ya Karaso har gabanta kamar zai dake ta, “Me ya sa kike cire kanki a cikin mutanen da zan dauki mataki a kansu? Ke ce mace ta farko da zan fara kiran “yan sanda su tafi da ke, su tuhumeki. Domin na fi zarginki,

ZAMU TASHI

sannan abinda yasa na hada da ‘yan aikin nan, saboda ban san aikin me suke yi da har za a yi wannan rashin hankalin wai a ce dukkanku babu wanda ya ji. Don haka idan kuka tsince ku a Police Station duk za ku yi bayani.? Yanzu Abban Sultan a kan yaran nan za ka zarge ni? Kana tunanin zan iya aikata wannan rashin mutuncin? Rashin imanina bai kai nan ba, duk abinda zan iya yi, ba zan iya kashe rayuwar idanun Nasrcen ba.? Kawai tasa kuka mai tsuma zuciya. A take nadama ya shige shi, haka kuma ya gaskata ba ita ba ce, to amma idan ba ita ba ce wace ce? Ta ya ya duk suna cikin gidan a ce an rasa gane wanda zai yi wa Nasreen hakan? A fusace ya fice daga gidan gabadaya. Kai tsaye gidan mahaifityarsa ya nufa ya zayyane mata komai. Hajiya Gwaggo ta dinga Salati tana Karawa. Cikin kuka take ambaton bala’i ga duk wanda ya aikata mata wannan mummunar aiki, Alhaji Lukman ya yi shiru yana sauraren addu’ar mahaifiyarsa haka kuma yana amsawa da Ameen. Yana sane da yadda mahaifiyarsa take Kaunar ‘yan biyun

tamKar jininta. Karfe ukun dare agogon bangon ya buga, a wannan lokaci Alhaji Lukman ne tsaye cikin dogon nazari. An dade ba a yi abinda ya tashi hankalinsa ba, kamar mutuwar idanun Nasreen. Yana kallon yadda dan uwanta ke riKe mata sanda idan za su je Makaranta. Hankalinsa yana Kara tashi ne idan ya tuna duk ranar da Sultan ya dawo, me Zai gaya masa akan amanar Nasreen? Sultan ya dauki burin duniyar nan ya dora a kan yaran, yana hango masu tarin ilimi a nan gaba. Musamman Nasreen da take: gaf da sauke Alqur’ani. Yarinyar ta taso da wani irin ilimi na ban mamaki, wanda ya sake sanya Kyashi a zuciyar Hajiya Salma. Haka abinda ke damun ta, Hafsat ta zama cikakkiyar budurwa amma babu ko mutum daya da ya taba zuwa da sunan yana sonta. Amma Nasreen sai dai idan ba a ganta ba, sai an ce “Tubarkallah masha Allah.? Wannan abu yana damun_ Hajiya Salma, shi ya sa ta yanke shawarar mayar da ita makauniya tun kafin wataran Haidar dinta ko Sultan din da kansa wani ya ce yana sonta. Idan ta tuna hakan takan yi rantsuwa da sai ta batar da ita a duniyar gabadaya. Abba ya sami Kaninsa kasancewar shi ne babba a gidansu don haka suka zauna da Baba Sani ya yi masa bayanin tunaninsa da kuma hukuncin da ya yanke. Baba Sani, Anti Iyami, da kuma Hajiya Gwaggo duk suka yi na’am da wannan shawarar nasa. Suna zazzaune a falo, wayarsa ta yi Kara, ya daga yana murmushi. Haidar ya dubi Hafsat suka tabe baki, domin har sun gane idan har mahaifinsu yana fara’a to dan gaban goshinsa ne ya kira shi. Bayan sun gaisa ne, Sultan ya tambayi dukkan mutanen gida, daga bisani ya ce a baiwa Nasreen wayar. Abba ya Kwala mata kira, ta fito tana harba sanda, “Na’am Abbana gani nan zuwa.? Za ta fadi Abba ya Kwala kira, ‘“Nasreen kada ki fadi. Tsaya kawai in Karaso.? | Mamaki ya kama Sultan. Ya kasa gane me Abbansa yake nufi da kada ta fadi? Bai ce komai ba har lokacin da ya ji sassanyar muryarta tana kwarara masa Sallama. “Nasreen kina cikin “kuna cikin Koshin lafiya ko? Na ji Abba yana cewa kada ki fadi me ya sa za ki fadi?? Shiru ta yi_ ta rasa me za ta ce masa, sai kawai ta gaida shi, ta fara ba shi labarin Islamiyyarsu. Ya ce, “Yi min karatunku na jiya in ji.? Nasreen ta gyara murya ta fara karatun da kaf dakin suka kafe ta da ido. Yadda take baiwa kowanne harafi hakkinsa ya isa ya sanya ka fi Kaunarta. Sultan da ke kwance ya sake mayar da kansa ya lumshe idanunsa, dama kansa wani irin ciwo yake yi masa ga gajiya ga shi yana son yin barci. Jin Kira’anta yasa ya sake samun natsuwa, yana lumshe idanunsa har barci ya yi awon gaba da shi. ? Nasreen tana saukewa ta shiga kiransa, “Dee.. Akwai gyara? Dee!? Ta cire wayar daga kunnensa, “Abbana duba ka gani ko ya kashe © wayar ne?? Abba ya karba yana sake duban Nasreen, ta burge shi Kwarai. Idan ya tuna rashin idanunta kuwa, sai ya ji kamar babu wanda ya kaishi zama cikin Kunci. Abba ya Kwalawa Nawfal ? kira, ya shigo da Sallamarsa, ya dube shi, ‘“‘Nawfal kama hannun Nasreen ku koma ciki.? Nasreen ta ta yi murmushi wanda gefen kumatunta suka lotsa ta ce, “A’a Abbana ni ma ina son in zauna a wurinku, ko ba zan iya kallo ba, zan ji sautin muryar talabijin din.? Abba yana sake al’ajabin Karfin tawakkali irin na Nasreen, kwata-kwata bata da damuwa da irin wannan jarabawa da Allah ya yi mata. Nawfal ya riKe mata sanda suka Karaso falon ta zauna a Kasa tana aikin murmushi. Tana jin nishadi ne a duk lokacin da ta tsinci muryar Sultan yana mata magana. Hafsat tana son yin tsaki tana tsoron Abbanta, don haka ta yi shiru kawai tana kallon Nasreen cike da haushi da tsana. Abba ya sake kiran Sultan ya rarumi wayar ya manna a kunne yana sake lumshe idanu. Abba ya ce, “SP tashi mu yi magana.? Babu musu Sultan ya tashi zaune tare da tattaro natsuwarsa ya zuba su a kan Abban. “Ina saurarenka Abba.? Sai da Alhaji Lukman ya saci kallon Hajiya Salma sannan ya ce, “Jiya na je gidan Hajiya Gwaggo, ka san mitarta kullum ba za ka yi aure ba? Sultan na zuba maka idanu inga iya gudun ruwanka sai dai baka da alamun raya sunnar manzon mu. Ga Kaninka nan shima har ya tasa. Hafsat kuwa ko yau miji ya fito za_ ta yi aurenta. Don haka kana babba kai ya kamata ka fara yin abu mai kyau wanda zai sa su yi koyi da kai. Na yi maka magana ko kana da yarinya amma sai kace min babu. Mahaifiyarka ta nuna min wata yarinyar Kawarta da suka so su hada aurenku, nayi irin nawa binciken ba za ku shirya da yarinyar ba. Na san abinda za ka iya zama da shi ka sami natsuwa, amma ba ‘yar Hajiya Ladidi ba. Don haka mun taru da ni da ‘yan’uwana mun yanke shawarar za ka auri yarinyar Alhaji Mamman da ke karatu a Rasha. Yarinyar tana da natsuwa da kamun kai. Na tabbata ba za ka yi da-na-sanin zabina ba. Za mu daura auren baka nan, amma kana dawowa za ka sami goron bikin zan adana maka koda kuwa ya bushe ne sai ka ci. Ina fatan amsar magana ta za ta kasance eh ne ba a’a ba?? Sultan da gabansa yake tsananta faduwa ya rasa me zai cewa mahaifinsa? Kawai ya tsinci bakinsa da furta, “Duk abinda ka yanke a kaina Abba dai-dai ne. Wannan ne amfanin haihuwar, idan har za ka iya sanya yaronka ya yi, za kuma ka iya hana shi ya hanu. Abba na kasa amincewa wata mace ne, a dalilin duk yawancin mata halayyarsu iri daya ce. Ka dubi duk irin zaman da kake da Umma, yau a kan taimako Umma ta watsar da lamarinmu, ta tsame ni daga cikin ‘yan’uwana, ta sa suna yi min kallon wani mugun mutum. Duk irin ilimin Umma da kuma girman tarbiyyar gidansu, amma Umma ta kasa karbar Kaddara. Abba abokin aikina Mahbub macen da take tsananin Kaunarsa taso ta kashe shi, abokina Ashrmnaaan matarsa ce take kawo masa maza a cikin gidansa, abokina Haisam, matarsa ce take aikata madigo a cikin dakin aurenta, dakin sunnah! Ba ta taba jin tsoron akwai ranar da Allah zai hukuntata ba. Abba ireiren wadannan matsalolin suna nan da yawan gaske, ta yadda idan ba rufe ido mutum zai yi ba, ba zai taba iya yin auren ba. Ina tsoron aure sosai Abba. Amma tunda ka amince nima na amince.? , Abba da ke aikin murmushi ya ce “Kowacce da irin halayyarta, zai yiwu Fatima Dan borno ce ta sa. jarumanta a hakan, ba lallai a same su da irin halin ba, idan ma ansamu za ka gaa yanzu haka sun shiryu, tun daga lokacin da ta furta Alhamdulillahi ta kammala. Daman haushin abun daya ne, mutum yana aikata kuskure ya kasa tuba ya koma ga Allah, irin wadannan mutanen su ake gudu a rayuwa. Amma duk wanda zai tuba irin tuban da Allah ke so, ai abin a gode wa Allah ne. Sunan yarinyar Fa’iza bayan daura auren zan sa ta kiraka ku gaisa.? Hajiya Salma ta mike a fusace ta tsaya masa a tsakiyar kai, “Wai Sultan dinne ka zauna da danginka suka bashi mata? In haifi yaro wasu su nuna min sun fi ni iko da shi? Me yasa a lokacin da zan haife shi baka kira danginka sun amshi nakudar da nayi ba? Ban yarda da wannan auren ba, dole zabina zai aura. Daman nasan kai kake sawa yaron nan yake raina ni.? Sultan yana sauraren hayaniyar mahaifiyarsa hakan yasa ya yi saurin kashewa ya rike kansa, “Ya rasa asalin dalilin da yasa bai yi na’am da wannan auren ba. Zuciyarsa tana gaya masa akwai wani abu da yake so amma kuma ya rasa menene? Nasreen ta duKar da kanta tana jin damuwa sosai. Ta fi danganta damuwarta da irin tijarar Umma. Shi kuwa Abba har ta gama maganarta bai ce mata komai ba. Dukkansu suka mike fuuu suka fice. Falon ya rage daga Abba sai su Nasreen. Ya dubi Nasreen ya _ ce, ‘“‘Nasreen ke ma zan iya aurar da ke a kowani irin lokaci.? Nasreen ta yi dariya har jerin haKoranta suka bayyana, “Abbana, duka-duka shekaruna sha shida a duniya. Ai ban isa aure ba, anti Hafsat ce ta isa aure da Yaya Haidar. Abbana na Kasa a yi auren Dee, sai mu koma gidansa da zama ko?? Abba ya ce, “Kwarai kuwa.? Nawfal ya ce, “Abba ni kuwa na isa aure ko?? Gaba daya suka yi dariya. Haka Abba ya zauna a cikin su suna ta hirar su. Idan ya tuna Sultan zai dawo ya sami Nasreen babu idanu, sal yaji damuwarsa ta ninku. , Yau juma’a a yau ne Abba ya shigo hannunsa dauke da goro yana aikin murmushi. Hajiya Salma tana zaune idanunta sun yi jazir saboda kuka. Ajiye mata goron ya yi ya shige ciki wajen Nasreen. Goron ya dan gutsura ya ce, Nasreen bude bakinki insa maki wani abu mai zaKin gaske a baki.? Babu musu ta bude bakin tana fara’a “Abbana har na Kosa ka sanya min.? Ta bude bakin ya sanya mata ballin goro. Ta rufe bakin tare da taunawa, “Abbana akwai zakin sosai. ? Ajiyar zuciya ya Kwace masa, ? “Wannan goron na daurin auren Daddynki ne. Kiyi masa addu’a.? Murmushi ya _ wadaci zuciyarta zuwa fuskarta, “Allah ya basu zaman lafiya Abbana. Ka bani waya infara yi masa albishir.? Babu musu ya zaro wayarsa ya mika mata, bayan ya danna kiran Sultan. Muryarta yaji cikin sanyi tana magana, “Ina tayaka mura Dee, Allah ya kade fitina. Yanzu na ci goron daurin aurenka.? Sultan ya danyi jimm.. Alamun abin bai yi masa dadi ba, daga baya kuma ya ce, “Har andaura? Zan kawo maki tukuicin fara gaya min da kika yi. Allah ya yi maku albarka.? Sama-sama suke magana, wanda ta fahimci yana cikin damuwa, dole ta hakura da hirar suka yi Sallama. “Abbana sai naji kamar Daddyna baiyi farin ciki da wannan auren ba. Abba me yasa baka barshi ya nemi matarsa ba? Ka bani matarsa a waya ingaya mata matsayina na “yarsa don ta fara gyara mana dakina da na Nawfal tunda can zamu koma da zama. Abba ya ce, “Idan bai yi farin ciki a yanzu © ba, na tabbata akwai ranar da dole zai yi farin cikin. Akwai ranar da zai gode min. Matarsa kuma ki bari ta kusa gama karatunta ta dawo, da zarar ta kammala sai ayi bikin tarewarta.? Nasreen ta langwabar da kanta ta ce, “Haka Allah ke ikonsa. Na ci burin ganin irin matar da Dee zai aura. Ashe ba zan iya ganinta ba, sai dai in ji muryarta. Allah ya kawo mana ita lafiya.? Abba ya rage murya ya ce, “Insha Allahu ba zaki dauwama a hakan ba. Ki kwantar da hankalinki kinji? Ina jiran dawowar Sultan ne a shirya a fita da ke Kasar”waje Bata ce komai ba, sai duKar da kai da ta yi, hakan yasa Abba saurin ficewa yana girgiza kansa. Yana ficewa Nasreen ta sunkuyar da kanta ta kama kuka sosai. Furucin da Umma da su Hafsat suke jifansu da shi yana sanya ta cikin damuwa da tashin hankali. Tasha kwatanta tambayar Abba sai kuma ta fasa. Nawfal ya shigo ya dafa guiwowinta, “Nasreen menene? Me ya saki kuka a ranar daurin auren Daddy? mene ne ke damunki bai kamata kiyi kuka a irin wannan ranar ba.? Nasreen ta lalubi hannun Nawfal ta rike tsam. “Nawfal! Umma ce take ce min mu ‘ya’yan shegu ne, haihuwar Karkashin gada. Me hakan ke nufi Nawfal? Ko dai ba mu da alaka da gidan Abba ne? Idan bamu da alaKa me yasa muke diban kama musamman da Umma? Abin yana damuna.? Nawfal ya yi dariya, “Shi ne kike kuka? Mu ba shegu ba ne, Abba ya gaya min bata son mu ne kawai, ba wai don mun yi mata wani abu ba. Kuma mahaifinmu da mahaifiyarmu sun rasu ne a dalilin hatsari. Daddy shi ya yi ta kulawa da mu ya rene mu. Kuma ai ba mu kadai take yi wa hakan ba, hatta Daddy Sultan ba ta bar shi ba, kuma kin ga ita ta haife shi. Ki daina damuwa kin ji ‘yar uwata?”? Ta gyada kanta kawai tana jin zuciyarta babu dadi. Karfe daya na dare, ya dawo gidan, a matuKar gajiye. Tsaye yake daga bakin tagar yana kallon yadda hadari ya hadu walKiya kawai ake yi. Idanunsa sun riga sun soye baya jin ko alamun barci. Yana tsintar kansa a cikin nishadi da kuma tunanin abubuwa masu mahimmanci a cikin rayuwarsa, sai dai yau akasin hakanne kwance a zuciyarsa. Yana son mahaifinsa fiye da kowa, bai taba yi masa musu ba, haka baya son yadda ya nuna masa Kauna a lokaci guda ya watsa masa Kasa a idanu, yasan yin hakan zai jawo mutanen cikin gidan su suyi masa dariya. Ya kasa amincewa kansa wai shi ango ne, akwai igiyoyin wata a kansa. Bai taba kawowa kansa yin aure yanzu haka ba. Akwai matsayin da yake kwadayin hawa wanda idan yana da aure a yanzu, zai dinga kaucewa zuwa kwasa-kwasan nan na Karin girma, Nasreen! Zuciyarsa ta ambata da Karfin gaske. Ya rasa dalilin da kwana biyu yake yawan ganin yarinyar a cikin farkinsa tana neman taimakonsa. Gaba daya ya ji garin ya fice masa a rai. Gida kawai yake hange. Sannu a hankali ya fice daga cikin dakin ya tsaya a bakin Kofa yana kallon yadda ruwan saman ke zuba a hankali, Nawfal da Nasreen kadai yake hange. A irin lokacin nan ne Nasreen da ke kwance a Katon gadonta ta lume cikin bargo sal juye-juye take yi tana jin ciwon kan, yana sake ratsa kanta. Duhun da take gani kadai a idanunta yana damunta, bare kuma wani Katon abu da yake tokare a Kirjinta wanda yaki wuce wa haka ta rasa menene. Da gaske take kewar Dee dinta, ta Kosa ta ganshi ya dawo. Bata Kaunar ci gaba da zama a tare da Umma ta Kosa matarsa ta tare, su koma gidansa. Tashi ta yi ta yaye bargon da ta rufa, ta dinga lalube har ta isa ga bandaki. Alwala ta yi ta dawo ta fara gabatar da nafifili. Ta jima tana yiwa Sultan addu’a kafin ta bude Qur’ani tana karanta Suratul Maryam cikin natsuwa da zakin muryarta. Da safe ta gama shirin zuwa Makaranta jikinta yafi na kullum yin sanyi, ta jiyo hayantya, hakan yasa ta yafito Nawfal ta ce su je falon. Nawfal ya kafe Umma da idanu da ta rike Abba tana kuka tana fadin sai ya saketa ta bar masa gidansa, ba za ta iya ba. Ya sa danta ya rainata, yanzu kuma saboda a nuna mata iyakanta aka yi masa aure. Ta nemi a gaya mata wacece matar idan da

Please Login or Register in order to submit comment