Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

itama kanta macijiyar ce suna zaune ne kawai" cike da kuma tashin hankali suka ce"yanzu ya zamuyi" sauke ajiyar zuciya yayi yace "tabbas kwana biyun nan kun aikata babban kuskure dama tuni an kuremu daga gidan nan dan haka kawai mubar wannan nahiyar kawai" ai kuwa da gama wannan maganar ko kayansu basu d'auka ba suka fice daga gidan gaba d'aya ma suka bar garin daga nan gidan marayun ba'a sake jin d'oriyar suba.




A wajan Amreeta kuwa d'aukar mijinta tayi mata sauke shi ko ina ba sai dajin da suke rayuwa zuciyar ta saboda da tsanin k'unci da b'acin rai ta kasa kukan ma mijina da ya koma mutum ta matsa kusa da gawar sa ta bud'e idanuwansa duk abinda ya faru a idanuwan mijinta ta gani da sauri ta tashi zunbur cike da tsananin mamaki again wani irin uban ihu ta buga wadda har yasa dajin amsawa sai kuma ta zube a k'asa tana rushewa da kuka tana k'ank'ame gawar mijinta magani take cike da tsananin d'aukar *FANSA* "lallai kunyi kuskure shigowarku rayuwa tahh ni zaku raba da abinda nafi so har guda biyu shin mi suka tarewa rayuwarku lallai ba d'aya daga cikin ku dazan bari a raye ta idasa tana fashewa da wani kukan zuciyar ta zafi kamar ta had'e ta mutu..............












***************** Tunda yaga ta sume ya ganka da sauri ya dafa kanta duk wani tsoro koh shakku ya cire mata shi san ya bace wajan,




Ita kuwa Ikilima jin ihun Rayha yasa ta fito ban d'aki da sauri ganinta tayi tana bacci hankali kwance cike da mamaki take kallon ta to kodai ba ita bace ne taji ihun ta kauda maganar tayi ta cigaba da abinda take,




Chan saiga Aamah ta dawo ranta a bace da sauri Ikilima tace "ya dai Aamah?" D'an tsaki Aamah taja tace "bari kedai fita ta na gamu da wa'inchan shashashun wai suna min gargad'in cewa sai sun illata Rayha" cike da tsoro. Ikilima tace kin gani koh wallahi zasu iya nidai Allah ya rabata dasu lafiya kawai" cike da sanyin jiki Aamah ta amsa da "Amin" kawai,




Ganin cewa har yanzu Rayha bata tashi ba yasa suka zuba abinci suka ci,




A wajan Rayha kuwa wani irin rikitaccin mafarki take wai gata a wani zami ni daya shud'e tana rayuwa da wannan wadda taga kansa kawai suna Soyayya mai tsayawa a zuciya ya kan ce mata "kin dawo gareni nine mijinki" tana cikin wannan mafarkin ta tashi a firgice da sauri su Ikilima suka matsa wajanta dafe take da kanta da take jin kamar zai rabe gida biyu da sauri Aamah tace "kanne ko? ga magani kisha" amsa kawai tayi tasha wanka tayi ta fito tana zaunawa da zaman ta d'aga kan da zaitai taga Bijay a dai wajan tagar yana mata wani irin kallo na k'auna a yanzu kuwa kallonsa take ba wani tsoro ko fargaba itama dai kamar kallon Soyayya take mai da kallon kamar ta tab'a rayuwa dashi,




Ikilima nata mata magana amma bata jiba hankalin ta baya wajan kwata-kwata Aamah kuwa ganin inda take kallo tana murmushi cike da mamaki tabi wajan da kallo sai dai mi..........✍️
















*FATEEMAH RABI'U CE (ZAHRA ROYAL STAR)*🥰✍️✍️














Comment and share Fisabilillahi🥰🙏


















*🐍🐉 FANSAR MACIJIYA🐍🐉*








MALLAKIN


*©FATEEMAH RABI'U*
*(ZAHRAH ROYAL STAR)*


















*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*




Marubuciyar :


*1-RAYUWA*

*2-WATA RANA SAI LABARI*


*3-ASMA'U (MA'U)*


*4- SA'ADAHTU*


*5-YAZDAD*


*6-MAHAIFINA NE SILAR KOMAI*


*7-RUHI BIYU*


*NOW*


*FANSAR MACIJIYA*






*GA MASU BUK'ATAR NAH TALLAH TA MASU HAJAR SU A BOOK D'IN NAH ZASU BIYA ₦500 . KACAL KU TUNTUB'I WANNAN NUMBER NAWA 08130479973.*
















*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم*






PAGE1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣






_________________✍️ Zuciyar Amreeta yadda kasan zata fito daga k'irjinta saboda tsananin hucen da take tundaga wannan lokacin Amreeta zuciyar ta bushe tsanin mugunta da d'aukar fansa,




Tunanin su Haidar sun tserema abinda suka aikata wadda saida sukayi abinda suka fara tara iyali nanfa nadama da dana sani ta fara zuwar musu sai dai kash lokaci ya riga da ya gure masu dan kuwa duk abinda suke ciki da duk abinda suke Amreeta tana sane dasu babu inda zasuje domin tsere mata domin kuwa tayi masu dabaibayin da duk inda suka shiga a fad'in duniyar nan bazasu goje mata ba sai dai in mutuwa sukai kamin tayi sana diyar tasu mutuwar.




Sauke ajiyar zuciya sukai su duka sun gama tunano abinda suka aikata chan baya tabbas saka makone suke gani,




Aliyu ne ya fara tashi yabar wajan dan bakinsa ya kasa furta komai da shigarsa gida wayarsa tayi k'ara dubawa yayi sunan wata budurwarsa ya gani wadda yake burin aura wadda ita ta nace mai tana matuk'ar sonsa,


Koda ya d'au wayar gaisawa sukai inda take mai ta'aziyya cewa zatazo har inda suke tayi masu gaisuwa sai dai ya hanata zuwa kan cewa basai tazo ba, sai dai bata bashi amsa ba sukai sallama.




Washe gari bayan anyi addu'a mutane sun watse Aliyu zaune yana cin abinci tusawa kawai yake amma ba wani dad'insa yake jiba ji yayi an turo k'ofar parlo an shigo da sauri ya d'aga kansa Aliya idanuwansa sukai tozali da ita a zuciyar sa kowa mamakin ta yake shin baya ce karta zoba, d'an tsaki yaja yana k'ara kallon taci wani uban gayu sai wani yauk'i take takowa tayi har gaban sa sana ta zauna kujerar dake kallon tasa cikin karya murya tace "dear sorry nazo ban sanar da kai ba ya hakuri" d'an yatsine baki yayi ya amsa chan ciki,




Ita kuwa cike da sonsa ta tashi ta k'ara matsowa kusa dashi lemon dake gabansa ta d'auka ta d'an kai bakinta d'an miyan dake bakinta ta tsirta ciki cike da kissa ta tako d'an shafa fuskarsa tayi gwarewa yayi ya fara tari idonsa yayi ja da sauri ya hankad'eta da cewa "ba nace miki bana so kina tab'a ni ke daina in ba haka ba kinsan hukuncin dazan yanke" yana magana yana tarin da sosai ya sark'esa da sauri ta tashi tana mik'a mai lemon da cewa "sorry dear amsa kasha naga ka gware" amsa yayi har yakai bakinsa sai kuma ya fasa d'an matsawa yayi chan kawai ya samu kansa da zubar da lemon ita kuwa bata lura ba ganin ya dawo da abin ba komai wani murmushin cin nasara tayi tana zama kan kojerar dake fesin d'in wani madubu dake parlon irin na kwalliyar parlo haka babba ne sosai sai wani yauk'i take tana rangwad'a shi kuwa Aliyu kamar ance ya matsa ta cikin madubin ta cikin madubin ya hangeta mi zai gani zuciyarsa ce ta buga da mahaukacin k'arfi kansa na sarawa cike da tsananin tashin hankali ya waigo inta take zaune tana latsa waya mutum yake gani a zaune a idanuwansa sai dai akasin haka a madubi k'ara waigawa yayi ta cikin madubin *MACIJIYA* Yake gani zaune innalillahi wa'inna ilaihir raju'un kawai yake mai-maitawa cike da tsananin bugawar zuciya ya dawo ya zauna d'an cire tsoro yayi yana d'an tabbayar ta wasu abubuwa akan aihin Aliyarsa ga mamakinsa komi amsa dai dai take basa lallai ya shaida wannan macijiyar ba k'aramar hatsabibiya bace cike da kissa da yaudara ta d'an tashi tana zagaye parlon ganin har yanzu dafin data samai a lemo bai fara kamasa ba mamaki take can ta hango inda ya zubar da lemo zaro ido tayi cike da mamaki dan har wajan ya chanza kala ya koma bulu shar tunani ta farayi ya gano ta kenan tabbas dole ta sake shiri bace wa tayi daga gidan kwata-kwata shi kuwa juyowar da zaiyi ya nemata ya rasa wata irin ajiyar zuciya ya sauke da yanzu ya mutu koh? Da yanzu wani zanchan ake ba wannan ba "kai Allah na gode ma" ya idasa maganar yana dafe zuciyar sa da har yanzu take cike da tsananin tsoro.




A wajan Amreeta kuwa ranta in yayi dubu ya b'aci har wani huce take na b'acin rai cike da wata irin murya mai cike da tsananin kuwwa tace "inahhh wallahi bazai yuwuba dole na sake shiri bazaku tab'a tsallake kaidi na ba in kunsan wata ai baku san wata bahhhhhhh" ta idasa maganar da k'arfi har bishiyoyin dajin na girgiza...............














***************** Aamah kuwa ganin inda take kallo tana murmushi cike da mamaki tabi wajan da kallo sai dai mi, ita bata ga komai ba cike da tsananin mamaki ta k'ara waigowa Sai dai har yanzu wajan take kalla tana murmushi mai k'ara ma fuskarta kyawu,




Ikilima ma wajan takai dubanta itama dai window take gani bata ga komai ba da d'an mamaki Ikilima ta fara girgiza ta tana kiran sunanta da d'an firgice ta dawo hayyacinta tana dafe kanta,




Ikilima tace "Rayha anya lafiyar k'alau kuwa shin mima kike kallo a wajan window?" Aamah itama tace "ashe kema kin gani har wani fa murmushi take irin tana tare da masoyinta d'in nan" da sauri Rayha ta kai mata duka kawucewa tayi tana dariya nan suka shashantar da abinda suka cigaba da fira.




Washe gari bayan sun fito daga lecture tsaye suke su uku yamma tayi sosai ga gari yayi duhu hadari ya gaggami daka kalle hadarin kasan ko da yaushe ruwa na iya sakkowa,




Da sauri suke tafiya domin isa rom d'insu suna cikin tafiya kawai sukaji mutum ya tsaya a gabansu cike da mamaki Rayha ke d'agowa idonta bai sauka a ko ina ba sai akan Abdallah dake layin giya sai wasu surutai yake marassa dad'in ji amai ya kwararo mata a kan jikinta mai warin giya da tsananin wari da sauri ta dod'e hancinta hawaye na b'alla mata su Aamah kuwa tsananin tsoro ya hanasu motsawa,




Ita kuwa Rayha cike da tsanarsa ta d'aga hannu ta sharara mai mari lafiyayye har guda biyu da sauri Ikilima da duk ta rud'e ta jasu suka bar wajan shi kuwa Abdallah duk da cikin mayi yake saida ya wartsake idanuwansa saun kad'a sunyi jawur na tsananin bacin rai "Wardugu" ya kira wani abokinsa da sauri ya k'arasu wajan cike da tsananin b'acin rai yace "ku tabbatar kun sato min wachan yariyar kun kawo min ita kangon makarantar inda kowa bai shiga saita gane ni ta mara sai tayi dana sanin hakan da taimin" "an gama ya shugaba na" cewar Wardugu da wata bud'ad'iyar murya.






Da isarsu d'akinsu Rayha tana kuka mai cin rai ta shiga wanka zuciyar ta sai tsinke wa take tana bugawa ga wani fad'uwar gaba da take ji a wajan Aamah ma haka take ji fashewa tayi da kuka haka kawai ko taji saukin zuciyar ta ta rasa mike mata dad'i dan har waya sukai da Momy ita ma dai fad'uwar gaba da tsinkewar zuciya da sanyin jiki duk sun hanata sukuni,




Da sauri Ikilima ganin halin da suke ciki ta fara rarrashin su haka suka kwanta babu wani baccin kirki da suka yi


Washe gari haka suka tashi Aamah kuwa cewa tayi bazata lecture ba sai dai Rayha duk da abinda take ji duk duniyar ta sire mata haka ta shirya ita da Ikilima suka fita,


Ana cikin lecture kamar ance ma Rayha ta mik'e kawai ta fita daga wajan Ikilima na kallonta cike da tausayin ta a wajan Rayha kuwa tafiya take bata san inda take jefa k'afarta sai dai kawai taga dandazon in isaka a kanta kusan su hudu zuciyar tace ta sake bugawa da k'arfi kamin tayi wani yunk'uri suka shik'a mata wata farar huda gashi wajan ba kowa gashi dama babbar makaranta ce wani wajan ma ba shigarsa ake ba




Basu sauke ta a ko ina ba sai a wani tsohon waje dake cikin makarantar wadda an fara gyara wajan aka barsa zaune Abdallah yake yasha wani askin y'an iska ajemai ita sukai wata irin dariya ya shek'e da ita nuna masu hanya yayi kan su fita suma zasusha garabasar cike da murna zasu kwashi dad'i suka fice haka bawan Allah nan Abdallah baiji tausayin ta baiji kunyar Allah ba baiji cewa Allah na kallonsa ba ya tub'e kayan sa haihuwar uwarsa ya keta ma Rayha mutumcin ta yana gamawa da ita ya tashi yana tufa mata yawu yana kiran sauran Abokan sa su hudu yana tsaye yasa suka rink'a keta mata mutumci har wani dariya yake zuciyar sa ta bushi da tsananin mugun ta ita kuwa Rayha duk da ba cikin hayyacinta take ba hakan baisa ta rasa gane wani irin hali take ciki ba wasu irin hawaye masu d'umi ne suka shiga bin fuskar ta,


Aamah kuwa zuciyar ta ce ta kasa sukuni ta fito ta nufu cikin school d'in cin karo sukai da Ikilima da sauri Aamah tace "ina Rayha dan Allah?" Da sauri tace "bata dawo ba ai ana cikin lecture ta fita" wata irin bugawa zuciyar Aamah tayi bakinta ya kasa furta komai da sauri Ikilima ta jata suna dubawa ko Allah zaisa a ganta chan suka hange kamar d'an kunnan Rayha da sauri Aamah ta d'auka tana fashewa da kuka kamar ana tunkud'a ta wajan ta doshi wajan zuciyar ta na k'ara bugawa Ikilima na kiran ta cewa bafa zataje nanba babu wadda yake zuwa wajan amma ina bata ma jinta bare ta saurare ta ganin haka yasa Ikilima bin bayanta tana shiga wajan taga su Abdallah ga Rayharta kwace ba kaya da sauri ta nufi wajanta ta cire gyalanta ta rufe mata jiki rungume tayi tana fashewa da wani irin kuka numshinta ne ya d'auke ta zube a sume Ikilima ma na shigowa nan take ta zube ita ma sume Abdallah kuwa ko a jikinsa saima nufar k'ofar fita yayi shida y'an iskan Abokansa wata irin guguwace ta turnik'e wajan idanuwasu suka rufe bud'ewar da zasuji sukai tozali da wani irin narkeken maciji ba wadda hantar cikinsa bai kad'a ba a cikinsu ja da baya suka rink'a yi zasu ruga amma ina haka Bijay ya nannad'ossu su uku yayi masu sari lafiyayye nan take suka zube babu rai a tare dasu mutane ne suka fara shigowa wajan da hukumar makaranta jin ihu na fitowa daga wajan Abdallah kuwa da wani abokinsa da suka rage wani mai suna Shamsu ganin macijin ya nufu su gadan-gadan yasa su sume wa ba shiri jin motsin mutune yasa bijay bacewa yana wani irin kuka mai ban tausayi shikenan nan ya k'ara rasata a wannan karanma da k'afin yace "wallahi sai naga bayanku bazaku sha ba saina kasheku kai da kayi musabbabin abun saina gana ma azabar dasai ka gwammace mutuwa da rayuwa" yana kallon Abdallah cikin idanuwansa yana kallon duk abinda ya faru wata irin k'ara ya saki yana cewa "A'ahhh bazai yuwuba karkuyi mi yasa y'an Adam da yawansu basu tsoron Ubangiji ne" duk ya fita hayyacinsa kamar zararre............✍️


















*FATEEMAH RABI'U CE (ZAHRA ROYAL STAR)*🥰✍️✍️














Comment and share Fisabilillahi🥰🙏
























*🐍🐉 FANSAR MACIJIYA🐍🐉*








MALLAKIN


*©FATEEMAH RABI'U*
*(ZAHRAH ROYAL STAR)*


















*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*




Marubuciyar :


*1-RAYUWA*

*2-WATA RANA SAI LABARI*


*3-ASMA'U (MA'U)*


*4- SA'ADAHTU*


*5-YAZDAD*


*6-MAHAIFINA NE SILAR KOMAI*


*7-RUHI BIYU*


*NOW*


*FANSAR MACIJIYA*






*GA MASU BUK'ATAR NAH TALLAH TA MASU HAJAR SU A BOOK D'IN NAH ZASU BIYA ₦500 . KACAL KU TUNTUB'I WANNAN NUMBER NAWA 08130479973.*










*KU KYAUTATA WA MATA INJI MANZON ALLAH S.A.W*


Manzon Allah (SAW) yace: kuyi wasilcin alkhairi ga mata, domin ita mace an halicceta ne daga qashin haqarqari, wanda yafi karkata shine qashin haqarqari na sama, idan ka tafi domin ka miqar da shi sai ka karya shi, in ka barshi dai ba zai gushe ba yana nan a karkace, don haka kuyi wasilcin alkhairi ga mata".
Bukhary da Muslim🙏🙏












*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم*






PAGE1️⃣5️⃣➡️1️⃣6️⃣






__________________✍️ Amreeta wani murmushin mungunta tayi jin ta tuno wani shiri daban dariya tayi mai cike da zallar mugunta ta bace bat bata sauka a ko ina ba sai a gidan Sulaiman tsayawa tayi k'ofar gidan tana murmushin munguntar Shirin da tayi.




Shi kuwa Aliyu d'akko wayarsa yayi ya kira Aliya koda ta d'auka ya tabbaye ta da ina da ina taje yau cewa tayi duk yau bata fita ba abinfa ya k'ara bashi tsoro ta ina tasan Aliya (ni ko Zahra nace kaima Aliyu yo abu da ba mutum ba taya za'ai ta kasa sanin komai kuma).





Amreeta ta ko bacewa tayi ta sauka a d'akin matar Sulaiman ta juya baya tana sa kayan bacci dan dare ne wani murmushi tayi sana ta d'ora hannunta kan matar tasa nan take wani nannauyan bacci ya sure ta samun wani waje tayi ta b'oye ta inda ba wadda zai ganta sana ta rikid'e ta zama suffar matar Sulaiman komai da komai da kayan data sa sak ita babu wani mahaluk'in da zaice wai ba ita ba ce.






Cike da takunta najan hankali ta nufi d'akin Sulaiman yana zaune yana shan shayi dan Matar tasa bata dad'e da kawo mai ba.




Cike da kissa ta tak'o sai kuma ta d'an ja birki ganin d'an hannun nan wadda indai yana tare dashi bata ikon mashi komai.


Cike da kissa da kisisina irin ta mata ko nace ta gaggun y'an duniya ta taku wajansa tana turo baki irin na shagwaba nan girgiza ta farayi da jikinta duk wani albarkatun jikinta ya fara motsawa da sauri Sulaiman ya runtse idanuwansa ganin ta fara tada mai hankali da sauri yakai hannunsa nufin ya kamota gocewa tayi da sauri ya tashi wajan tashi bai lura ba dan hankalin sa naga matar sa abin gado yaja abin hannun ya watse a k'asa amma hakan baisa ya lura ba dan kuwa d'an hannun dama ba kama hannun su yayi ba irin mai saku-sakun nanne.




Ita kuwa cike da tsananin murna ta matso garesa tukan ya k'ara su tunda abinda yake mata shamaki dashi ya tsinke,




Turasa tayi kan gado tana d'anewa jikinsa wani irin kallo yake binta dashi ganin matar tasa ta k'aro wani salo na daban, bai aune ta had'e bakin su waje d'aya wani irin kiss take mai cike wani salo wadda yasa bai shirya ba ya rink'a had'e miyan da take zubamai ji yake kamar sweet ce yake tsotsa da wannan damar tayi anfani ta samai tafin ta na maciji,




Dai-dai wannan lokacin ta turesa daga jikinta da saurinsa ya rik'ota turesa tayi da k'arfin gaske fad'awa yayi kan gadon ya fara wani irin tari numfashinsa na tsark'ewa dariya Amreeta ta saki mai sauti tana zama ai nihin suffar ta tace "lallai zuciyata ta kusa samun salama na kusa k'arar daku a doran duniya tabbas *RUHI BIYU* Zai samu salama ruhin Amreeta da kuma mijina" ta idasa maganar tana fashewa da wani irin kuka zuciyar ta na sosuwa tunawa da wad'anda take so a rayuwarta amma babusu a duniya ita kanta duniyar bata mata dad'i.




Shi kuwa Sulaiman dake kakarin mutuwa kunfa na fita daga bakinsa magana yake so yayi amma ina numshinshi ya fisga rai yayi halinsa, Amreeta ko a jikinta ta juya wata irin girgiza tayi ta bace bat...........












***************** Hukumar makaranta ganin abinda ya faru sun girgiza ainun da gyar aka samu su Ikilima suka farka Ikilima kuka kawai take kamar ranta zai fita Aamah kuwa tunda ta farka ta zama kamar tab'ab'b'iya da sauri ta matsa wajan Rayha dake mik'o mata hannu ta farka hawaye ne kawai ke shatata a idonta rik'e hannunta tayi tana fashewa da kuka mai ban tausayi Rayha da gyar ta iya bud'e baki tace "Aamah ki yafe min nasan mutuwa zanyi rayuwata bata da wani anfani kicewa Momy ta yafe min in....... Da sauri Aamah dake kuka tana girgiza kai cike da fitar hayyaci tace "bazaki mutu ba kuma insha Allah, Allah bazai barsu ba yanzu kam nasan ba wani mataki da za'a iya d'auka a kansu dan ya kasance d'an wani amma Allah yana gani dan Allah ki daina fad'ar wannan maganar" tari Rayha keyi numshinta na fisga tana hawaye masu ciwo da rad'ad'in abinda akai mata wadda yanzu a k'asa Najeria indai ka kasance kai ba d'an kowa bane akai ma abu to babu wani mataki da ake d'auka saima aima abun rufa-rufa abar zancan gaba d'aya ina kuwa rayuwa zata ci gaba shuwa gabanni ba adalci kowa cikinsu kansa kawai ya sani sai iyalinsa,




Tace "kayya Aamah wannan rayuwar cike take da rud'u da abubuwan ban tsoro nikam nasan rayuwata ta k'are naji a jikina ki doba ki gani mutum nawa ya keta min haddi rayuwata bata wani anfani koda Allah baid'au raina ba kina ganin za iya rayuwa mai dad'i ne ina fata na zama mai k'arfin hali na rashina da zakiyi" ta ida maganar tarin na k'ara yawaita aman jini ta fara cikin tsananin tashin hankali wadda bazai musaltu ba garesu Aamah ta k'ara fashewa da wani marayan kuka tana k'ank'ame ta jin tana farta kalmar shahada jikinta ya saki lokaci guda da sauri Aamah ta fara girgiza kanta tana nunawa mutane cewa "bata mutu ba fa ku tasheta dan Allah Rayha karki min haka" kuka take magana kai da ka kalleta kasan bata cikin hayyacinta Ikilima kuwa kuka kawai take,




Hukumar makaranta kuwa su duka aka kwasa sai asibiti sai dai tun a san nan aka shaida mutuwar Rayha tuburar Aamah haukace masu tayi itafa Rayhanta bata mutum ba inda hukumar makaranta taji wadda yayi abin zaima sukayi gum da bakinsu inda sai dai kawai gwamnatin jihar tasa aka kalle makarantar gaba d'aya amma dan wani d'aukar mataki akan su Abdallah babu ma wadda ya taso da zancan.






A motar asibiti akasa gawar Rayha da Aamah da Ikilima da duk basu cikin hayyacinsu aka nufi gwabbe dasu.




A wajan Momy kuwa tun jiya take jin fad'uwar gabanta ya tsananta ga jikinta dake k'ara sanyi haka nan sai taga hawaye na tarowa a idanuwanta haka yasa take ta kiran su Aamah d'in amma bata shiga gaba d'aya wayoyin nasu nanfa hankalin ta ya k'ara tashi sosai duk bayan wasu mintuna sai ta gwada kiransu amma dai amsar d'aya ce bata shiga tabbas tashin hankalin da take ciki bazai musaltu ba dan kuwa numfashinta har sark'ewa yake k'arar moto taji irin ta asibiti ta tsaya a k'ofar gidan da sauri ta mik'e zuciyar ta na lugude diff dumm diff dumm dumm hawaye ne ya tsinke mata tunkan tasan mike faruwa,




Aamah ce ta b'alle murfin motar ta shiga cikin gidan da gudu tana shiga ta fad'a jikin Momy tana fashewa da sabon kuka Momy kuwa saddarewa tayi bakinta na b'ari tace "Aamah mi yasa mi y'ar uwarki ?" Ta jefa mata tabbayar kasa amsa mata tayi Ikilima ce ta shigo itama tana kuka to nan fa Momy hankalin ta ya k'ara tashi fiye da da, cike da kaushin murya tace "wai bada ke nake magana ba kiban amsa nace ko mutuwa tayi ku gaya min" gaba d'aya sun kasa furta koda kallama d'aya ce jin hayaniya a tsakar gidan da sauri Momy ta ture Aamah ta nufi waje da sauri Aamah ta bi bayanta ganin motar asibiti ta shigo har cikin gidan dan kuwa get ne kuma tsakar gidan akwai fad'i daskarewa tayi a wajan ganin ana fiddo da gawa lullub'e da farin mayafi (likkafani) bayani suke mata na k'arya da gaskiya suna ajiye gawar suka juya sukayi Tafiyar su Momy zuciyar ta cewa take ina ba Rayhanta bace ba ita bace bata mutum ba da kyar ta ja k'afa funta ta matsa kusa da gawar tashin hankalin da ba'a sa masa rana su duka Aamah Durk'ushewa sukai wajan gawar hannun Momy na kyarma ta kai hannunta akan gawar tana yaye abinda aka rufeta dashi saddare wa tayi tana zare ido wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga bin fuskar ta zuciyar ta na buguwa da mahaukacin k'arfi kawai saita rungume gawar tana fashe da wani irin kuka mai tab'a zuciyar duk wani mai imani Aamah ma kuka take har yanzu fuskarta ta kunbura tayi sumtun zaboda da tsananin kukan data sha mak'otansu ko ta ina shigowa suke da y'an uwa gida ya riki ce da koke-koke da kyar Aamah ta bari aka yiwa gawar Rayha wanka Momy kuwa Suman ta yafi biyu data farka taga Rayha ba rai saita sake suma har saida wani limami yashigo yayi mata wa'azi mai ratsa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment