Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

k'araso d'aya daga cikin su yace "ya haka friend ka barsu suka wuce salin alin" juyowa yayi Yana watsa mai wani mugun kallo da idanuwansa wadda cike suke da jaraba da muryar sa irin ta gaggun y'an iska yace "kai kana zaton na hakura sai tasan kowani waye tayi babban kuskure da har ta d'aga hannu ta mare ni ko tsoho na na manta rabon daya sa hannu ya mare ni bare ni saina wargaza rayuwa ta saina aa rayuwarta cikin k'unciiiiiiii😳............✍️












*FATEEMAH RABI'U Ce (ZAHRA ROYAL STAR)*🥰✍️✍️✍️✍️








Comment and share Fisabilillahi🥰🙏




















*🐍🐉 FANSAR MACIJIYA🐍🐉*








MALLAKIN


*©FATEEMAH RABI'U*
*(ZAHRAH ROYAL STAR)*


















*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*




Marubuciyar :


*1-RAYUWA*

*2-WATA RANA SAI LABARI*


*3-ASMA'U (MA'U)*


*4- SA'ADAHTU*


*5-YAZDAD*


*6-MAHAIFINA NE SILAR KOMAI*


*7-RUHI BIYU*


*NOW*


*FANSAR MACIJIYA*






*GA MASU BUK'ATAR NAH TALLAH TA MASU HAJAR SU A BOOK D'IN NAH ZASU BIYA ₦500 . KACAL KU TUNTUB'I WANNAN NUMBER NAWA 08130479973.*
















*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم*




PAGE7️⃣➡️8️⃣






___________________✍️ da gama maganar ta ta maida dubanta akan macijin da aka turo mata dumin wai ya kasheta wata shu'umar dariya tayi girgiza ta farayi jikinta ya fara rikid'a yana zama na macijiya gaba d'aya ta zama wata narkekeyar macijiya gadan-gadan macijin ya nufuta cikin fushi itama ta nufesa,




Wata irin guguwace ta tashi fad'a suke suna sarar juna gani tayi zai wahalar da ita danda nan ta zama rabinta macijiya rabinta mutum nannad'osa tayi da jelarta ta yarb'asa a cikin k'ayoyi nan take macijin ya mutu,


Wata shegiyar dariya ta kece da ita tana cewa "ni zaka turowa wannan k'aramin alhakin wadda tsafinsa baikai da ya rink'a zamowa mutum ba inahhh kayi kuskure D'an macijiya ganin zuwa gare kahhh"


Bacewa tayi bata sauka a ko ina ba sai a kogon D'an macijiya zaune yake kawai yaga an wurgo mai macijinsa wadda ya aika,


Da sauri ya mik'e abin busar maciji ne rataye a wiyansa kallon-kallo suke ganin abun busar da yake sasu bacci da maida su asalin suffar su ta macijzai juyawa zaitai nufin tabar wajan, ai da sauri ya fara busar iya k'arfin sa


Tsayawa tayi tana dod'e kunwanta da iya k'arfin ta wata uwar k'ara ta kwallah tana zubewa k'asa "inahhh ka bari karkai min haka ka daina wannan busar nacehhh" ta fad'a da k'arfi,


Shi kuwa D'an macijiya bai fasa busar ba abinda bai gaza y'an mintoci ba ta zama asalinta na macijiya tayi lagwas bata iya komai,.


Da sauri yasa hannu ya d'auketa ya sata cikin wani d'an keji ya rufe yana murmushin nasara,




Gama artabunsa da macijiya su Aliyu sukai sallama ganinsu yayi ko wannan su da tshin hankali a fuskar sa zasuyi magana ya dakatar dasu da cewa "nasan tunda na ganku a haka tabbas tayi galaba akan mai taurin kan nan" (Kamal kenan), su dukan su dakai suka amsa mai inda dawowarsu kenan daga kaisa makwancinsa na gsky,




Cike da alhilin abun D'an macijiya ya k'ara da cewa "tabbas na jajanta muku kuna cikin uk'uba da kaidin MACIJIYA sai dai taimako d'aya ne zan baku shine ku tabbata wannan d'an hannun dana sanya muku ku tabbatar yana hannayenku a koda yaushe karku bari ya sub'oce maku" cike da gamsuwa da tsananin tashin hankali suka d'aga mai kai kwata-kwata baiyi gigin sanar dasu cewa macijiyar tana hannunsa ba dan suna iya cewa a fiddota a kashe ta sai dai kash wannan macijiya ko busar ba wani nasa take a jikinta ba yanzu haka ta sake ta dandai tana cikin abinda bazata iya fitowa ba,




Bayan kwana biyu sun d'an samu kwanciyar hankali jin ba wadda ya k'ara mutuwa a cikinsu,




D'an macijiya ne yaje cikin dajin d'ebo wani sassak'e dawowarsa ya nufi wajan daya kulle macijiyar nan zuciyar sa ce ta buga kamar zata fito girjinsa ji kake diff dumm diff dumm cike da tashin hankali yake kallon abinda ya kulleta a bud'e babu ita babu alamar ta,


Juyowar da zaiyi ya hange ta zaune a suffar mutum ta hard'e k'afa d'aya kan d'aya cike da izza tace "kayi kuskure baka son wace ni ba da har kasa kanka cikin wannan lamarin da bakai gigin shugowarka gona ta bahhh" ta ida da macin rain abinda yayi mata shima,




Cikin dagiya yace "bazaki tab'a cin nasara ba in...... Katse sa tayi a tsawace da cewa "har kai waye dazai dakatar dani?" Gama maganar ta zau juya ya d'akko abin busa da saurin d'aya wuce misali ta girgiza jikinta ta zama sharb'eb'iyar macijiya bai aune ba ta kai mai sara a agarar k'afarsa,


Zubewa wajan yayi dai-dai ya d'akko abin busar fad'uwa abin busar yayi D'an macijiya ya fad'i yana shure-shuren mutuwa dan ita dafinta tana sama shi nan take ake mutuwa saboda hatsarinsa tashi tayi tana murmushin mugunta tana matsawa kusa dashi ta kece da wata irin dariyar data girgiza kogon gaba d'aya sai kuma ta turb'une fuska tana kai dubanta kan D'an macijiya dake futar da kunfa na dafin maciji idanuwansa sun kakkafe jikinsa ya saddare kamar yadda ya shekara da mutuwa ga kalar jikinsa ta zama kalar dafin macijiyar tace "lallai ka jama kanka mutuwa wannan shine kad'an daga cikin duk wadda zai rink'a shigowa gona tahhhh" murmushi take mai cike da zallar mugunta tana bacewa daga kogon...........










****************** Sai nasa rayuwar ta cikin kunci" ai da sauri friend d'in sa suka fara mai kirare,


Bayan su Rayha sun shiga rom d'insu wadda yake a tsaftattace zaunawa sukai duk a gajiye Ikilima na kallonsu cike da tausayawa dan tasan tabbas Abdallah bazai bar wannan abun ba Rayha ta tashi tsaye tana nufar window tana zage labole d'an zaro ido tayi ganin wata gatuwar kuka kusa da window d'in da sauri ta waigo tace "amma Ikilima wannan kukar fa? Baki ganin akwai matsala kuwa" Ikilima tace "babu wata matsala mutum nawa suka zauna a d'akin kamin mu ba abinda ke cikinta na cutarwa naji ana cewa ta d'ad'e gaskiya shekaru da yawa" Aamah tace "Ahh ai daga ganinta kam" ita dai Rayha bata k'ara magana ba abinci suka ci sana suka kwanta a b'angaran Rayha kuwa wani mafarki ta fara mai cike da rikitarwa, Washe gari haka shi suku-suku bayan sun shirya suka nufi cikin makaranta da yake duk gurin lectures su d'aya duk abinda suke karanta saiya zamanto d'aya ne,




Zaune su Abdallah suke ta hanyar da dole sai kabi ta wajan zaka hall d'in lectures sai zuk'ar sugari suke,


Ikilima kuwa ganin su wajan yasa da sauri ta matso jikin Rayha tace "please Rayha kinga mutananchan ba mutumci ne dasu ba dan Allah mu wuce salin alin karki tanka masu" ita kuwa Aamah tunda ta hangosu tsoro ya k'ara shigarta,




Rayha kuwa tabe baki tayi dai-dai sunzo gifta su cike dajan magana Abdallah dake gaf da ita yana shan sigari ya daddage ya fesu mata hayakin akan fuskarta da sauri ta dod'e hancinta tana tari sosae kamar zata shid'e da sauri Ikilima ta zasu suka bar wajan Aamah kuwa kuka ta fara waje suka samu suka zauna har yanzu Rayha tari take ba k'ak'k'autawa cike da tausayin ta Aamah matsa ta samu ruwa tana bata sha tayi tana jan wani irin numfashi kamar wadda ta suma idanunta sunyi jawur tana sauke numshin wahalahh.........✍️














*FATEEMAH RABI'U CE (ZAHRA ROYAL STAR)*🥰✍️✍️✍️










Comment and share Fisabilillahi🥰🙏
















*🐍🐉 FANSAR MACIJIYA🐍🐉*








MALLAKIN


*©FATEEMAH RABI'U*
*(ZAHRAH ROYAL STAR)*


















*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*




Marubuciyar :


*1-RAYUWA*

*2-WATA RANA SAI LABARI*


*3-ASMA'U (MA'U)*


*4- SA'ADAHTU*


*5-YAZDAD*


*6-MAHAIFINA NE SILAR KOMAI*


*7-RUHI BIYU*


*NOW*


*FANSAR MACIJIYA*






*GA MASU BUK'ATAR NAH TALLAH TA MASU HAJAR SU A BOOK D'IN NAH ZASU BIYA ₦500 . KACAL KU TUNTUB'I WANNAN NUMBER NAWA 08130479973.*
















*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم*




PAGE9️⃣➡️🔟






___________________✍️ Tashin hankalin da ba'a sa masa rana wayewar gari su Aliyu suka samu labarin mutuwar D'an macijiya, lallai sun shiga tashin hankali wadda baki bazai fad'e shi ba,




Tabbas suna cikin matsala babba yanzu saura wadda suka rage Mustapha, Sulaiman, Aliyu, Jamil, saira su hudu lallai suna cikin tsaka mai wuya wadda yake basu taimakon shima ta halaka shi,




Zaune suke wajan gaisuwa kai daka kalle fusk'okinsu kasan sunfi koya shiga rud'u da tashin hankali kwana biyu sunji shuru ashe tana nan tana shirinta shin wane irin lefi sukai mata haka dahar take masu d'auke d'ai-d'ai,




Da gyar suka bar wajan gaisuwar inda kowa yana k'ara jaddada ma d'an uwansa cewa yafa kula da d'an hannun da D'an macijiya ya basu lallai sun tuna kamar wasiyya ce yake masu kamar yasan zai tafi yabarsu cikin wannan duniyar mai cike da rud'u da tashin hankali kullum cikin zullumi suke basu san wane yanayi zatazo masu ba,




Zaune matar Jamil take taci uban gayu ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya d'agowar da zatai tayi arba da mace tsaye kanta tayi gayo wadda yace uban nata, da sauri ta tashi zunbur cike da d'an kishi-kishi tace "wace ke ke tsayama taya akai kika shigo cikin gida nah eyee?" Ta idasa maganar tana b'alla mata wata uwar harara dakatar da ita tayi budurwar tana ware manyan idanuwanta bud'ar bakinta sai cewa tayi "ke ba matar Jamil bace?" Matar Jamil tace "kamar ya matar sace mana ji wata tabbayar reni" budurwar ta k'ara gyara tsayowarta da wani pictures babba a hannunta ta juya bayansa tace "to nima ai matarsa ce" Matar Jamil kuwa saddarewa tayi cike mamaki tace "anya kina da hankali kuwa kizo gida na da mijina kuma kice wai mijina mijinki ne" ta idasa maganar tana mata wani kallon banza,




Murmushi budurwar tayi tace "nima haka zalika bansan wata matarsa ba inba niba amma nuna min shirdar cewa ke matarsa ce" cike da tsananin mamaki na wannan baiwar Allah tace "ki shigo har cikin gidan Jamil kiga ni ni matarsa kuma kice in nuna miki shaida amma tsama ai inada pictures d'in bikinmu"ta ida maganar tana juyawa ta bud'e wata dorowa dake cikin porlon ta zaro wani abu mai kamar littafi cike yake da pictures d'in bikin nasu ta wurga mata shi,


D'auka tayi tana wani munafikin murmushi tukan ta mik'o mata taga dukkan abinda ke ciki ajiyewa tayi sana itama ta mik'a mata nata tace "nima ga nawa shaidar sunana *AMREETA*" da sauri matar Jamil ta amsa kallon pictures d'in take cike da tsananin mamaki da bugawar zuciya lallai kuwa ga hoto nan tana gani da mijinta da wata innalillahi wa'inna ilaihir raju'un kawai take mai-maitawa,


Zata k'ara magana kenan Jamil ya shigo kallon sa take cike da tsananin mamakinsa shi kuwa Amreeta yake ma kallon rashin sani ita kuwa matarsa ganin kallon da yake ma Amreeta gani tayi kamar na Soyayya ne da sauri ta matsa kusa dashi tana hawaye tace "Jamil dama yaudara ta kake ne ban sani ba?" Ta idasa maganar tana cin kwalar rigarsa cike da mamaki yake kallon ta yace "ban gane ba" tana kuka ta k'ara cewa "dama ya za'ai ka gane gata nan cewa tayi wai matarka ce" da sauri ya waiga yana kallon Amreeta kallo irin na tuhuma da rashin yarda,


Ita kuwa Amreeta ko gezau batai ba ba alamar tsoro a idanuwanta saima tsayowa ta k'ara gyarawa tana aika mai da wani munafikin murmushi, juyowa yayi wajan matar sa yace "nifa ban ma santa ba ke ina kika sanni da har zaki ce waike matata ce?" Ya idasa maganar yana kallon Amreeta ita kuwa Amreeta takowa tayi cike kissa ta shafa fuskar sa tace "haba hubbyyy kodai kana tsoron matarka ne in...... Tukan ta ida matar Jamil ta k'ara fashewa da kuka tana k'ara ruk'unk'umeshi ita kuwa Amreeta D'an hannunsa take kallo ganin ya kusa cikewa wani irin shu'umin murmushi ta saki kallon su take yadda ta had'a husuma wani irin dad'i take ji basuyi aune ba d'an hannun sa ya tsinke ya wargaje a k'asa,




Da sauri ya saki matar tasa yana furta "kin gani ko kinsan halin da muke ciki jibi kin katsi min abin kariyar kinji dad'i ai " wata irin dariya sukaji an b'ab'b'ak'ewa da ita da sauri suka waiga gaba d'aya cike da tsananin tsoro da bugawar zuciya suka za baya ganin Amreeta ta zama wata narkekeyar macijiya har wani huce take baitai wani sanya ba ta tashi sama kamar kububuwa bata saukar da sarinta a ko ina ba sai akan Jamil tsakiyar goshinsa nan take ya zube yana shure-shuren mutuwa kalar jikinsa ta fara chanzawa kunfa na fitowa daga bakinsa,


Amreeta kuwa wata dariyar ta sake shek'ewa da ita har kujerin porlon na girgiza tace "lallai sunana Amreeta lallai sai naga bayanku d'aya bayan d'aya lallai kunyi kuskuren shigowa rayuwa ta hhhhhhhh" ta idasa maganar da wata mahaukaciyar dariya da sai tasa d'an Adam fisari a wando ta bace kamar ba'ai wanzuwarta a wajanba matar Jamil kuwa ganin mijinta a saddare babu alamar rai a jikinsa girgiza kai ta farayi tana ja da baya dod'e kunwanta tayi tana tana kwala wata uwar k'ara ta zube a k'asa sumammiya.........












***************** Da sauri Aamah tace "Rayha kina lafiya?" D'aga mata kai tayi kawai dan zuciyar ta cike take sa tsanar Abdallah,




Ikilima tace "kin gani ko wallahi basuda kirki duk makarantar nan an sansu Allah dai ya rabaki da shirrinsu" tashi sukai suka shiga lecture Rayha kuwa kwata-kwata lecture ma ba wani ganewa take ba saboda damuwa koda aka tashi tare suka dawo d'akinsu,




Cike da damuwa Aamah tace "bari naje na sayo miki magani naga kamar kanki na ciwo" Rayha tace "ai kuwa kaina nad'an ciwo" fita Aamah tayi dan sayo magani Ikilima kuwa abinci ta d'ora masu sana ta shiga wanka,




Rayha kuwa jan numshi tayi tana d'agowa idonta bai sauka a ko ina ba sai a kan window d'in d'akin da sauri ta tashi tana ja da baya bakinta ya kasa furta koda kallama d'aya saka makon tozali da tayi da kan mutum sauran gaggar jikin kuwa ta maciji ne Bijay kenan bayan dubun nan shekaru ya fito daga kogon
Da aka gindaya mai sharidd'in bazai fito ba harsar wannan zamanin da za'ayo matarsa kuma gashi ta bayyana garesa Rayha kamarsu d'aya da matarsa kallon ta yake cike da k'aunar ta da kuma kewarta na tsawon shekaru masu tarin yawa,




Ita kuwa Rayha tunda take bata tab'a ganin tashin hankali irin na yauba maciji da kan mutum anya kuwa bata zareba hawaye take zuciyar ta na wata irin bugawa diff dumm dumm diff kamar zata faso k'irjin ta fito saboda tsananin tsoro numfashinta ne ya fara d'aukewa tana shirin suma ganin haka yasa Bijay gangarowa domin shigowa d'akin nufin ya rarrashe ta ganin yana nufo wajanta runtse idanuwanta tayi tana tsala wata uwar k'ara ta zube a sume............✍️












*FATEEMAH RABI'U CE (ZAHRA ROYAL STAR)*🥰✍️✍️










Comment and share Fisabilillahi🥰🙏




















*🐍🐉 FANSAR MACIJIYA🐍🐉*








MALLAKIN


*©FATEEMAH RABI'U*
*(ZAHRAH ROYAL STAR)*


















*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*




Marubuciyar :


*1-RAYUWA*

*2-WATA RANA SAI LABARI*


*3-ASMA'U (MA'U)*


*4- SA'ADAHTU*


*5-YAZDAD*


*6-MAHAIFINA NE SILAR KOMAI*


*7-RUHI BIYU*


*NOW*


*FANSAR MACIJIYA*






*GA MASU BUK'ATAR NAH TALLAH TA MASU HAJAR SU A BOOK D'IN NAH ZASU BIYA ₦500 . KACAL KU TUNTUB'I WANNAN NUMBER NAWA 08130479973.*
















*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم*






PAGE1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣










___________________✍️Su Mustapha kuwa dajin labarin mutuwar abokinsu ba k'ara min tashin hankali suka sake shiga ba dan kuwa Mustapha rungume d'ansa yayi yana durzar kuka shi kansa Al'ameen yana kallon Abbeensa yana hawaye duk da k'aramin yaro ne ya fahimci cewa Abbeensa yana cikin damuwa,




Matar Jamil kuwa tunda ta farka take sanbatu kamar zararra dan har aka kai Jamin bata sani ba ai saida aka dan ganta ta da asibiti inda Matar Sulaiman sosai ta shiga tashin hankali kullum dama cikinsa suke,




Mustapha da Sulaiman da Aliyu zaune suke sunyi jigum-jigum d'ago kyawawan idanuwansa Aliyu yayi a hankali cike da rauni yace "lallai chan baya munyi babban kuskure gashi abin yazo yana son shafe tarihin mu" ya ida maganar cike da rauni duk da ya kasan ko d'aya abinda friend d'in sa suka aikata ba hannunsa a ciki sai dai kash ai yana wajan akai abin,


Su duka suka shiga tariyo abinda suka aikata chan baya wadda ya jaza masu rashin kwanciyar hankali da dana sani wadda bazai musaltu ba.




*WAIWAYE*




Lallai su Aliyu sun taso basa jin magana ko kad'an duk da sun kasance marayu dole tasa aka sallame su daga gidan marayun dan kuwa rukuninsu su TAKWAS kowa ya sansu a gidan marayun sai dai missa babin abinda yasa aka koresu gidan marayun ya kasance maza da mata ne sai dai b'angaran mata daban na maza daban a gidan marayun anyi wata yarinya kyakkyawar gaske mai suna *Khausar* tana nutsuwa sosai bata shiga harkar kowa rayuwarta kawae take tun Khausar na k'arama Amreeta ke tare da ita (Macijiya kenan) sai dai ita kanta Amreeta bata san Macijiya bace dan kuwa tun tana k'arama ta taba ceton Amreeta time d'in itama Amreeta k'arama ce akwai lokacin da Khausar ta fito domin zuwa islamiyar dake cikin gidan marayun ta hangi wata y'ar Macijiya y'ar k'arama da ita dutse ya danne ta sai nishi take saboda wahalar da tasha da sauri Khausar ba tsoron komai ta matsa kusa ta d'auke dutsan tana sa hannu ta d'auki macijiyar luf kuwa macijiyar tayi a hannun Khausar ita kuwa cike da rashin tsoronta ta ajiye ta a k'asa tana shafa bayan Macijiyar tana mai juyawa dan barin wajan,




K'awayen tane taci karo dasu suna zare ido cike da mamaki d'aya daga cikin su tace "kai kai Khausar baki tsoron ta sareki ne?" Kama hannun su tayi suka fara tafiya dan suma y'an yara ne tace "bakwa ganin itama k'arama ce babu abinda zatai min" ta idasa maganar suna k'arasawa islamiyar.




Ita kuwa Amreeta da barinsu wajan ta rikid'e ta zama mutum dama zo wajanne da kanta ta d'orama kanta dutsin tana so ta gwada cewa shin akwai wadda zai iya taimakonta,




Cike da k'aunar Khausar a zuciyar ta lallai zata kasance tare da Khausar a matsayin k'awarta,




To dayin wannan abu indai Khausar zata wuce islamiya saita rink'a ganin y'ar yarinyar mai kyan gaske wadda ita kad'ai ke ganinta ita kuwa Khausar kamar ana ce mata taje wajanta haka zata matsa wajanta tun basu kai da saboba har suka saba dan har bata lokaci take wajan zuwa islamiya mlm yayita fad'a kan cewa mi yasa yanzu bata son karatu ne ita dai sai dai tayi shuru dan bata da bakin cewa komai,




Kamar kullum ma zaune suke ita da Amreeta tace "zanyi kewarki Khausar" tana mata wani irin kallo na kamar bazata k'ara ganinta ba cikr da tsinkewar zuciya da sanyin jiki da sauri Khausar ta kalle tace "wannan kallonfa kamar na bankwana to tukun ma ina zaki je ne" cike da kewar da xatayi tata tace "Khausar kamar yadda kika sani ni ba mutum bace kamar ke sana bawai yarinya bace kamar ke duk da yanzu kinkai shekara 13 kawai ina zo miki a yarinya ne domin kiji dad'in ma'amula dani yanzu haka zan koma chan wani jeji wadda muke rayuwa da mijina wadda yayi tafiya tsawon shekaru tabbas zan dad'e ban waiwaye ki ba" ta idasa maganar tana fashewa da kuka mai rauni da tsanin k'aunar Khausar d'in ita kanta Khausar matsawa tayi ta rungume ta tana hawaye tabbas zatai kewarta yanzu tana ganinta kamar wata y'ar uwar ta kuma danginta share mata hawaye tayi ta k'ara cewa "amma karki damu zan dawo gare ki komin daran dad'ewa" haka sukai ban kwana haka Amreeta ta tashi tafiya tana tafiya tana waigen Khausar ji take kamar bazata dawo ta sameta ba.




Bayan Shekaru hudu tabbas yanzu Khausar ta fidda rai da dawowar Amreetar ta yanzu Khausar ta zama budurwa ta k'ara kyau komai na halittun jikinta ya k'ara bayyana tafe take kanta a k'asa cike da nutsuwa tazo gifta wa dai-dai su Mustapha na shirin wucewa layi suke daga alama a shaye suke banda Aliyu dashi bai bugu sosai ba,


Cike da tsanin tsoro take kallon su ganin Kamal yana nufo wajan ta yana cewa "kai gayu kunga wata y'ar sakas dama gidan nan akwai zuk'a-zuk'an mata haka su dukansu har wani lashi baki suke Haidar ne da yaji abar girmarsa har wani tashi take zaboda zalama yace "kai Abokai bazan iya hakura ba ko d'akko mana ita muje cikin jeji da ita" dama ga duhun magaruba ya gabatu wajan ba kowa shi kuwa Aliyu a time d'in harya bingire da bacci danshi maganin mura ya sha,




A kuwa haka suka sungume sai cikin jeji da ita tana kuka tana magiya amma ina shed'an ya buga masu ganga haka baiwar Allah tana ji tana gani suka rabata da mutumcinta na y'a mace cikinsu ba wadda baiyi anfani da ita ba haka suka tashi suka barta a yashe a wajan tana kuka mai tsayawa a rai ko numfashin kirki bata iyayi ga sanyin dare ga wani irin tsoro daya k'ara shigarta kuka take tana anbatar "Amreeta ina kika barni ki dawo gare ni" wannan ciwon abun da sukai mata yasa zuciyar ta bugawa dan ko safiya bata kai ba tace ga garinku nan




A dai-dai wannan lokacin kuma Amreeta na zaune da mijinta zuciyar ta ce ke bugawa diff dumm diff da mugun k'arfi cike da damuwa da ruwan hawaye da take jin ya cika mata ido tace "mijina please ka barni naje wajan masoyiyata Khausar ina ji a jikina akwai matsala kaji dan Allah" ta ida maganar tana fashemai da kuka sauke ajiyar zuciya yayi yace "nima bank'i ta taki amma dai shikenan nan tare zamuje ki shirya" cike da tsanin murna ta rungume mijin nata,




Washe gari gidan marayun suka tashi da tashin hankali wadda bazai musaltu ba ganin gawar Khausar basu wani bincike ba sun d'auka wani abun ya sameta har yayi ajalinta suka sallace ta suka kaita gidanta na gaskiya k'awayen sunsha kuka kamar ba gobe,




Inda su Kamal kuwa ko a jikinsu saima wani shak'iyancin da saka sake b'ullowa dashi inda Aliyu daya ji labari yayi masu fad'a sosai amma sai ma tashi sukai suka rabo dashi,






Amreeta kuwa tunda suka isu wajan gidan marayun dan a suffar mutune sukazo sai da suka bi k'a'ida kana suka shiga inda sukaga gidan duk a hargitse kamar ba lau ba nan Amreeta ta k'ara shiga rud'o da tashin hankali da gyar suka samu wata yarinya suke tabbayar ta cewa ina Khausar yarinyar kuwa kuka ta fashe dashi tana cewa Khausar ta rasu Amreeta kuwa jin maganar tayi kamar saukar aradu saman kanta gani tayi duniyar na juyya mata da sauri mijinta chan nesa da wajan mutane ya zaunar da ita yana share mata hawaye runtse idanuwanta tayi komai na rayuwar da Khausar tayi ba ita saida ta gani da sauri ta bud'e idanuwanta tana tashi tsaye tana cewa "inahhh bazai yuwuba wallahi bazaki mutu a banza ba inahhh wallahi wallahi sai sun san ke suka tab'a tabbas kun tab'o abinda yafi k'arfin ku" da sauri mijinta ya jawota jikinsa yana aikin rarrashi maciji ya zama yana kwantawa jikinta cike da tausayin matar tasa zata shafa jikinsa kenan taji harbin bindiga cike da tsanin tashin hankali jin mijinta ya fad'o jikinta da suffar sa ta maciji alamar ba rai a tare dashi shafu jikinsa tayi inda harbin ya sameshi innalillahi wa'inna ilaihir raju'un wacce irin k'addara ce ta same ta haka girgiza kanta take ta rasa shin kuka zatai ko kuwa,




Ba kowa bane yayi wannan harbin sai Haidar tafe suke suna zagaye su duka suka ci karo da wata mace da maciji kanta kamar zai kai mata sari bai wani tsaya ba ya fiddo bindiga dan har ita garesu ya saita macijin nan sai dai sukaji harbi da sauri Aliyu ya jasu suka bar wajan cike da tashin hankali Aliyu yace "wai ku bakwa tunani ne in zaku aikata abu" da sauri Kamal yace "haba Aliyu baka ganin maciji ne kanta zai sareta" da d'an fad'a yace "kai baka da hankali kaida ka kallesu kasan ba mutane bane kasan

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment