Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ο»Ώhttps://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*WASA DA SO* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*TRUE LIFE LOVE STORY*. _(Labarin Soyayyar Gaske)_

*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🀝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________


*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_.

*Writing by:*

*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_.

*Facebook Aisha Mohammed Sani*.


*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*.
_Duk kan godiya ta tabbata ga ubangiji madaukaki sarki. Gaskiya ina matukar farin ciki da fara sabon novel dina fatana Allah yasa ya ilmantar da al'uma tare da nishdantarwa, ina rokon Allah ya yafemin kurakuren da zan yi wayanda bansani ba. Alkhairan da ke ciki kuma ya isa ga al'umma su amfana tare da alfahari damu_.

*KAMAR YADDA KUKA GANI TUN FARKO WANNAN LABARIN BA KIRKIRARRE BA NE YAFARU DA GASKE NE SAI YAN WASU ABUBUWAN DA AKA GYARA DOMIN TAFIYARDA SHI A TSARI*.

_Sis faty fatymarh dauda wannan shafin naki ne ke kadai kiyi yadda kikeso dashi much luv dear mie😘_

*PAGE* 1
------------------------------------------------------------------------------------------


Wani dan Matashi ne yashigo tare da dan murmushinsa .

Yana zuwa ya dire kusa da yar uwarsa tare da ce wa, "Haba Sweery na kidan bani ruwa mana,ba ki ga agajiye na dawo ba ne?"

Budurwar tayi murmushi tare da gyara zama tukun ta ce, "Wai yaushe zaka bar kirana da sunan budurwayen ka ne? niko zan yi aure ma ance ma zan auri dan karya irinka ne?" takai karshen maganar tana kallonsa sama da kasa.

Shiko saurayin ko ajikinsa sai ma kara matsawa gareta da yayi ya na, "Yarinya kimin ladabi in rabaki da wannan kwamar VIVON taki in sai miki koda iphone 10 ce."


Maganar tasa ta mutukar bata dariya hakan yasa ta tashi tare da fadin, "Kan ka kasheni da karyar nan taka gwanda naje nadibo ma abincin na huta."

Wata dariya yayi tare da fadin, "Yauwa masoyiyata yi sauri kinsan sahib din naki ya kwaso yunwa awajen boll, jeki dawo ma nabaki labari yarinya."


Ta tafi tana, "Toh naji ina zuwa dai."

Tana zuwa bata jima ba ta ce, "Toh MESSI ko Ince Adamu gashi."

Tuni ya Bata rai , "kinga Wallahi zamuyi fada inkika kara ce min Adamu sai kace wani Kada?"

Hamida tasa dariya ta ce, "Yooo Inba Adamu ba me zance?,Messi dai ba sunanka bane bare kace."

Adam ya ce, "Eh dai naji din Amman ai haka ake kirana ko?, kinga ma ni bazan ci abincin nan ba wallahi,da kicemin Adamu ai gwanda kinmin kyakkyawan mari." yana fadin hakan ne yayin da yake tafiya.

Ita ko Hamida Ba abinda take banda dariya tana, "Yooo kai ka sani Adamu bara ma kaga nadauke abinci na nayi gaba."

Fita kawai yayi yana un'uni ko waigowa bai ba.


Hajiya ce ta shigo tana, "Toh anfara halin ko?"


Hamida tayi murmushi tana, "Umm Mama Ai Adam din ne sai ya kashe mutum azaune."

Mama tayi murmushi tace, "kwaji dashi dai tare na gankU."


Adam kuwa na fita yayi wajen Abokinsa mubarak .

Mubarak na ganinsa yafara, "Haba Alhaji na ya naganka haka ."

Adam ya tinsire da dariya sannan yace, "Wallahi Hamida ta rainani wai ni ta ke cewa Adamu?"

Yakara wata dariyar sannan yace, "Allah yarinyar nan ko ta rainani,umm ba ma wannan maganar ba ya zancen bikin nan ne kasan fa nariga nakai dinki dan zamuyi wuta agun wallahi,banaso yaran nan su rai namu."

Mubarak ya shekye da dariya yana, "Yoo ai nasan indai kana waje ba raini nidai damuwata musami fararen da zamuyi manni."


Adam ya dafa mubarak sannan yace, "Kai ko na Abulle akwai ka da son karanta ina zamuyi manni da wasu farare ai wallahi dolas zan samo mana."


Mubarak yayi wani tsalle yana, "Shiyasa nake sonka Alhaji na."

Adam ya ce, "Bari kawai,bara naje gida tukun dan inaso muje da hamida ko ta rage rainani."

Mubarak ya ce, "Toh sai naganka,kana Wuta Fa mutumina."

Adam banda kwanbo ba abinda yake yana tafiya kaman wani sarki dan ya huce dan sarki ma shi aganinsa.



*INDAI KUNASO NAGA RUWAN COMMENTS ZAKUGA RUWAN TYPING*.


URS PREETY XAYYEESHERTH.😘

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*WASA DA SO* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*TRUE LIFE LOVE STORY*. _(Labarin Soyayyar Gaske)_

*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🀝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________


*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_.

*Writing by:*

*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_.

*Facebook Aisha Mohammed Sani*.


*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*.
_Duk kan godiya ta tabbata ga ubangiji madaukaki sarki. Gaskiya ina matukar farin ciki da fara sabon novel dina fatana Allah yasa ya ilmantar da al'uma tare da nishdantarwa, ina rokon Allah ya yafemin kurakuren da zan yi wayanda bansani ba. Alkhairan da ke ciki kuma ya isa ga al'umma su amfana tare da alfahari damu_.

*KAMAR YADDA KUKA GANI TUN FARKO WANNAN LABARIN BA KIRKIRARRE BA NE YAFARU DA GASKE NE SAI YAN WASU ABUBUWAN DA AKA GYARA DOMIN TAFIYARDA SHI A TSARI*.


*PAGE*
------------------------------------------------------------------------------------------

_ASSALAM ALAIKAM YAN UWA MASOYANA DA LITTAFINA,INA MAI BAKU HAKURIN CEWA NA AJIYE ALKALAMIN RUBUTUNA SAI SABUWAR SHEKARA WATO JANAURY KENAN SABODA WASU YAN DALILE DA KUMA BIN UMARNIN HAKAN AGASKIYA NAJI DADIN YADDA WANNNAN LITTAFI YASAMU KARFUWA AWAJEN MUTANE DA DAMA FATAN ZAKU YI HAKURI KU TSUMAYENI HAR JANUARY INA MUKU ALBISHIR DA CEWA INSHA ALLAH DAYA GA WATAN JANUARY ZAN FARA SUBURBUDO MUKU SO DA WASA WANDA BAZAN NA JINKIRIN TYPE BA KUMA ZANYI ME YAWA YADDA ZAKU FI JIN DADIN KARANTAWA FATANA MUKASANCE TARE MASOYANA INA YINKU IRIN SOSE DINNAN LUV U OLL😘😘_

URS PREETY XAYYESHERTH

Share plsπŸ™πŸ™πŸ™
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation


🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍
*WASA DA SO* 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍

_{ Ganganci }_

*TRUE LIFE LOVE STORY*. _(Labarin Soyayyar Gaske)_

*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🀝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*OUR WEBSITE*πŸ‘‡πŸ½
http://Zamaniwriterssassociation.blogspot.com

*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_.

*Writing by:*

*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_.

*Facebook Aisha Mohammed Sani*.


*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*.
_Duk kan godiya ta tabbata ga ubangiji madaukaki sarki. Gaskiya ina matukar farin ciki da fara sabon novel dina fatana Allah yasa ya ilmantar da al'uma tare da nishdantarwa, ina rokon Allah ya yafemin kurakuren da zan yi wayanda bansani ba. Alkhairan da ke ciki kuma ya isa ga al'umma su amfana tare da alfahari damu_.

*KAMAR YADDA KUKA GANI TUN FARKO WANNAN LABARIN BA KIRKIRARRE BA NE YAFARU DA GASKE NE SAI YAN WASU ABUBUWAN DA AKA GYARA DOMIN TAFIYARDA SHI A TSARI*.

*LOvE MEssEGE*

_Let me write my love for you in the sand, so the water can wash it away and I can write it again and again and again. I love you like crazy._

*PAGE* 3,4
------------------------------------------------------------------------------------------


Ya na zuwa, sai ya ce,"Good Morning Habibbty."

Hamida ta yi murmushi ta ce, "Good Morning Yayana."

Adam ya ce, "Bara na tayaki girkin nan kinsan yau munada biki ina son mu gama komai da wuri."

Hamida ba ta ga Alamar wasa yau afuskar yayan nata ba duk da cewa tasan yan miskilancinsa ne suka motsa .

Ta ce, "Owk."

Ba mai wa wani magana kawai aikinsu su ke.

Sai da su ka kammala tsaf sannan Adam ya je ya yi wanka kan ya dawo dai dai lokacin da kowa ya halarta afalo.

Misalin karfe
Biyu dai dai Adam yashirya tare da zuwa wurin Hamida da dan murmushin sa na kasaita, "Sweetie kizo mu tafi ko."

Hamida ta ce, "Toh Yayan Swetie bari na sa kayan nagama
kwalliyar daman.

Alokacin da Adam da Hamida su ka fito tare da jerowa atare Kai kace su ne Ango Da Amaryar ba karamin kyau su ka yi ba .

Aunty ta ce, "Wooo ya'yana ko kune Angwayen ne?'

Adam ya ce, "Umm Aunty kenan bayan ni ta ki so na ma, balle ayi auren,yasin idan ta yi sake balarabiya zan aura."
Ya nuna Hamida lokacin da ya ke maganar .

Aunty da Mama me zasuyi banda dariya harda Hamida ma dariyar ta ke .

Aunty ta ce, "Allah ya shiryaka dai Adam."


Su na fita su ka hadu da Mubarak

Mubarak ya ce, "Wow masha Allah ai wannan ko amarya da angon ma iyakaci kenan."

Hamida ta yi murmushi shiko Adam ya ce, "Kai dalla mu ware lokaci ya kure fa."


Tuni su ka shige Mota Adam ke driving, Hamida ta koma baya shi kuma Mubarak a gefen mai zaman banza.

Sun isa dai dai lokacin da Amarya ta iso hakan yasa su ka jera abayansu daman Adam ne babban abokin ango.

Kusan mutanen wajen ba Amarya da ango su ke kallo ba gaba daya hankalinsu yakoma ga Adam Da Hamida.

Adam tafiyar kasaita kawai ya ke su na zuwa tsakiyar fili M.C ya tsayar dasu duka dole sai sun dan taka.

Hamida bata rawa kawai murmushi ta ke ta dan tsaya hakama Adam Amman shi yakan dan motsa jikinsa.

Anatawa Amare Hutuna da manni wasu ko Su Hamida su kewa domin sunfi basu sha'awa,mussaman ma lokacin da Adam ya cire chanji ya na ma Hamidan liki,sai ya ma ta ya kan dan yiwa su ango da amarya,hakan ya sa yan matan wajen su ka kara rikicewa kowacce awurin Addu"ah kawai ta ke dama ita tasamu wannan gwarzon namijin.


Yan Mata sai shishshigi su kewa Adam amman basar da su ya ke.

Hamida ko inbanda dariya ba abinda ta ke , "Haba Yaya Messi ga yan matan fa sun fara roshin."

Messi baya son raini kwata-Kwata hakan ya sa ya ba ta rai sannan ya ce, "Hamida." bai karasa maganar ba kawai ya yi shiru.

Ai ko tu ni Hamida Ta Nutsu Domin tasan halin yayanta lokacin wasa da ban haka kuma lokacin serious ayi serous kawai.


Sai da su ka shiga mota hanyar komawa gida sannan Adam ya dawo yadda yake,hakan bai sa hamida da Mubarak sun damu ba domin kuwa sunfi kowa sannin halin Adam, ya kan yi wasa in yaso amman in miskilancinsa ya tashi kai ka ce bai taba dariya ba.


"Yarinya kin ga yadda ake girmamani dai ko." cewar Adam.

Hamida murmushi ta yi sannan ta ce, "Haba yaya Adamu aiko nina marasa aikinyi."

"KUTT wai Adamunnan ba zai fita abakin bane? ko sai na fasa bakin? ,Oh nasani ma yasin kin yi abakin chocolate din ki na yau."

Da sauri Hamida ta rikwo hannunsa murya asanyaye ta ke ce wa, "Haba yaya messi na wasa fa na ke Kuma i promise bazan kara ba."

Murmushi kawai Adam yake Allah kadai yasan me ya ke kullawa azuciyar sa.

Chan ya ce, "Toh naji Ni barni na yi tukina kar muje mu bige mutane."


Mubarak kawai binsu da kallo ya ke abin nasu na matukar birgesa .


Su na isa gida Hamida ta shige da gudu ta na, "SWEETY ina jiran chocolate di na fa."

Adam ko kulata bai ba ya ja mota su ka kara gaba shi da Mubarak.


*WAYE ADAM*?

Adam da'ne ga Alhaji Rabi'u dan asalin garin sakoto wanda yakasance shine dansu na fari agun mahaifiyarsa Aisha,tare Da kishiyar mamansa zainab wadda ta ke da yarinya mace kimanin shekara 9 sunanta Khadija shi kuma Adam ya na shekara 23 ya kammala secondrynsa akasar waje hakan yasa da ya dawo basu kara nema masa makaranta da wuri ba, amma yanzu ansama mai makaranta A Birnin Kebbi zai karanci computer science .


*WACECE HAMIDA*?

Hamida ya'ce ga Alhaji Hamza kanin Alhaji Rabi'u wadda ta kasance ya daya tilo agun mahaifinta tare da mahaifiyarta Hajiya Maryam,Hamida ta na aji biyar na secondry, a duk sanda ta samu hutu ba inda ta ke zuwa sai gidan su Adam,domin kaf family sun fi sabawa da ju na,duk da cewa kusan kullum afada su ke amman basa iya juran rashin ganin juna.

*Cigaban labarin*

Adam nat a shirye-shiryen tafiya skul farin ciki ya ke mai hade da bakin ciki,farincikin zai tafi karatu da kuma bakin cikin zai bar Hamida kanwarsa,kuma aminiyarsa.

Hamida ma gaba daya ta kasa sukuni duk da ce wa ranar da za ta ko ma gida shima ranar zai tafi school gaba daya jikinsu ba walwala .


Adam ne ya fito da ga daki ya na, "Hameee tah ina ki ke ga chocolate dinki nan duka ni na gaji da ajiyar nan ."

Hamida ta tebe baki tare da fadin, "Umm umm yaya fa ni inyana guna shanyewa zan a ta ke wallahi,Yauwa daman inaso muje anguwa anjima kaga gobe ka na tafiya nima za akai ni gida."

"kyaji dashi dai." cewar Adam

Hamida ta ce, " please ka shirya,daga yau dai shikenan."

Wannan kalmar da Hamida ta fada ta taba zuciyar Adam ji ya ke kamar zai yi kuka hakan ya sa shi komawa dakinsa batare da waiwayo ba bare ya ma ta magana.

Ita ko bata lura da hakan ba ta tafi ta na miti, "Wai in yan miskilancin mutum yatashi ko magana ma ba iya yi bare ya danyi murmushi, Matarka in batasan halinka ba wallahi ta mutu da bakin ciki."


Misalin karfe hudu Adam ya fito cikin shigar kananin kaya,farar riga tare da bakin wando ba karamin kyau yayi ba,kamshin kawai ya ke tashi,mussaman da ya sa farin glass din sa ba a iya cewa komai sai MASHA ALLAH.

Dakin Hamida ya nufa tana zaune ta yi ta gumi.

Bai ce komai ba ya durkusa gabanta tare da riko hannayenta biyu
Ya ce, "Masoyiya ta abar Alfahari nah,baki san ce wa aduk sanda bakya cikin nishadi ji nake tamkar zuciyata zata fashe ba?,Shin ko kinsan kamar yadda kifi baya iya rayuwa batare da ruwa ba haka nima ban iya rayuwa batare da Hamee ta ba?,sonki yazama halina,jinin jikina farincikina,bazan rayuwa in babu ke ba yar uwata."


Tuni Hamida ta fara washe baki tana dariya.

Adam na ganin hakan ya ce, "Dalla chan matsamin da wasa na ke ina koya miki ne ki koyawa dan saurayinki."

Ya fara yi ma ta dariya tare da kara fadin, "yarinya taji kalamai ta rude Wallahi i pity you dilla jeki dauko hijabi mu tahi."

Hamida kawai harararsa ta ke dan ta kasa magana ma duk da ce wa ba yau kadai ya fara ma ta kalaman soyayya ba daga baya ya ce koya mata ya ke ko kuma ya na gwada yadda zai nawa matarsa ne.

Ba karamin birge Hamida ya ke ba aduk sanda yafara kwararo kalaman nan amman kash ba dan ita ya ke ba dan wata ya ke hakan yasa itama ta fara maida abun nasa shirme.


Tuni Hamida ta dauko hijabinta fari har kasa da nikaf dinta baki ta ce, "To yaya Romio Mutafi."

"Wooo lallai amaryata tasha kyau barakallahu fiki Habbibty."

Ko kulasa batai ba ta yi gaba abinta ya ce , "Ai kya tsaya muje nakara miki aji ko yarinya?.

"Ummm yaya please ka zo gidansu Amira fa zamu kuma kasan da nisa."

Adam ya shiga motar ya na, "Gidansu Amiro ne ba Amira ba in ki ka yi wasa yasin sai afasa zuwa."

Hamida ta ce, "Ah mai yayi zafi?, haba sweetyna muje ."

Adam ya ce, "Na ki wayon sai kince min ki na so nah."

Hamida ta ce, "Ohhh yaya inkaso rigima kafi tsohuwar mota tsiya,to I LOVE YOU."

Ya yi dariya tare da fadin , "Allah yataimakeki yarinya da kin rasa zuwa ko ina."


Su na zuwa gidan su Amira yayanta ya fito ba wadda ya ke kallo sai Hamida ya tsura ma ta ido.

Tun Adam na kawar da kai har sai da ya gaji ya ce, "Ohh nikam bawan Allah kaman kasamu TV."

Bakaramar kunya yayan Amira yaji ba amman duk da hakan ya kasa daina kallonta asace.

Da ga karshe dai Adam yaga kallon bana karewa ba ne tuni ya ce, "Hamida kizo mu tafi kinga mubarak na jira na."

Hamida ta ce, "Haba yaya please ko minti 20 fa bamuyi da zuwa ba."


Adam bai san lokacin da ya.....


*Comments and Share πŸ™*

*Urs Xayeesherth*😘

🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍
*WASA DA SO* 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍

_{ Ganganci }_

*TRUE LIFE LOVE STORY*. _(Labarin Soyayyar Gaske)_

*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🀝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________

*OUR WEBSITE* πŸ‘‡πŸ½

Www.zamaniwritersassociation.blogspot.com

*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_.

*Writing by:*

*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_.

*Facebook Aisha Mohammed Sani*.


*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*.
_Duk kan godiya ta tabbata ga ubangiji madaukaki sarki. Gaskiya ina matukar farin ciki da fara sabon novel dina fatana Allah yasa ya ilmantar da al'uma tare da nishdantarwa, ina rokon Allah ya yafemin kurakuren da zan yi wayanda bansani ba. Alkhairan da ke ciki kuma ya isa ga al'umma su amfana tare da alfahari damu_.

*KAMAR YADDA KUKA GANI TUN FARKO WANNAN LABARIN BA KIRKIRARRE BA NE YAFARU DA GASKE NE SAI YAN WASU ABUBUWAN DA AKA GYARA DOMIN TAFIYARDA SHI A TSARI*.

*LOvE MEssEGE*

_Let me write my love for you in the sand, so the water can wash it away and I can write it again and again and again. I love you like crazy._



Ya Mata wata tsawa ,wadda afirgice ta tashi,jikina rawa tayi guda ta na kuka sai mota.

Ya na shigowa ko kallonta bai ba ya figi motar sukabar gidan.

Ba inda suka nufa sai gida Hamida ko ba ri ya ga ma paking ba tai ba ta fita da gudu.

Bai kulata ba sai da ya ga ma paking dinsa sannnan ya shiga gidan,aiko ba kowa afalo hakan yasa ya hu ce dakinta direct domin yasan ta na chan,da sallamar sa ya shiga .

Hamida ta kwantar da kanta akan gado sautin kuka kawai ke tashi adakin.

Adam ya karasa gareta jiki asanyaye ya zauna agefen gadon,ya yi shiru na yan mintuna sannan ya ce, "Hamida ki sa ni banda niyar kunta ta miki ga ba daya arayuwata indai ba faranta miki ba ke kanki kinsan hakan,da ace zakisan zafin da nakeji azuciyata aduk sanda naganki kina zubar da hawaye da ko wani ya ce ki yi ba za ki yi ba,wallahi bazan iya juran ganin wani na kallonki ba kuma irin kallon da bai kamata ba,subhanallah bazan jure ba ko ma wa ye wallahi ki gafarceni."

Hamida ta da go tare da kara kurawa yayan nata ido ta ce, "yaya nasan da hakan amman kasan da ce wa ba abinda ya fi tadamin hankali irin ace Naga bacin ranka,ko da wanine ma yabatam banji dadi,ba re ace ni! HMM."


Adam ya yi murmushi ta re da fadin, "Haba Hamee tah ni rai na bai baci ba zafin zuciyane kawai,Oyaa smile kanwar yayanta Amaryar kanina da ban sansa ba."

Hamida ta ce, "Ummm kai kasan wani kani ni muje muyi sallah ka ga har an fito amasallaci."

, "Toh Ta sallah muje."

Dukansu suna dariya kaman basu ba sukaje sukayi sallah tare kuma su ka yi karatun al'qur'ani sannan sukayi sallar isha tukun aka hadu domin cin abincin dare.


Abba ne ya ce, "Ohh nikam daga gobe gidannan zai dai na dadi fa tun yanzu har nafara missing ya'ya nah."

Aunty, "Oh wa to mu ka manta damu ta yaranka ka ke ma."

Abba ya yi murmushi Sannan ya ce , "Ke ko kishin ma da ya'yanku za ku yi?"

Mama ta yi karaf ta ce , "Yoo tunda ana nuna mana banbanci ai dole muyi."

Adam ko da Hamida banda dariya ba abinda su ke domin suna son kallon dramar su Abba da su Mama kaman A Film.

Autace ta fara kuka ta na, "Nikam yaya zan bika please,wallahi bazan iya zama agidannan ba."ta kara maganar tana bubbuga kafa.

Adam ne ya durkusa gaban kanwar ta sa tare da rikwo hannunta yana, "Haba Yar beautyna nima fa banson rabuwa dake ko dan surutunki da hanani barcin da kike,toh amman yanzu kinaso na fasa siya miki irin motar Auntyne?"

Da Sauri Auta ta ce, "Tab Yaya ai wallahi sai ka siyamin tunda dai Abba ya ce wai shi sai na girma."

Adam ya ce, "Yauwa to kinga sai naje nayi karatun da zan sami aikin da zan siya miki."

Tuni auta ta goge hawayen fuskarta ta re da tashi tana, "Yaya gudnyt gobe ka tashe na rakaka domin inka siyamin motar nan inba su Abba barasu hau ba sai da su kalla."


Kowa afalon dariya kawai ya ke Abba ko azuciyarsa yana jin dadin sabon da ya'yansa su ka yi.


Alokacin ko wa ya watse aka nufi dakin barci.


Washe gari
Da sassafe Duk yan gidan su ka tashi kasan cewar yau Adam zai tafi birnin kebbi,Hamida kuma zata koma gida .


Dukansu sun shirya tsaf Har sunyi break sannan suka hadu amota daya domin raka adam tasha.

Kawai dauriya Adam ya ke amman zuciyarsa zafi ta ke wani sa'in yakanji kaman zata fashe.

Suna zuwa kuwa akasami motar birnin kebi da shirin tashi yanzu.

Urs xayyeesherth

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation


🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍
*WASA DA SO* 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍

_{ Ganganci }_

*TRUE LIFE LOVE STORY*. _(Labarin Soyayyar Gaske)_

*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🀝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________


*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_.

*Writing by:*

*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_.

*Facebook Aisha Mohammed Sani*.


*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*.
_Duk kan godiya ta tabbata ga ubangiji madaukaki sarki. Gaskiya ina matukar farin ciki da fara sabon novel dina fatana Allah yasa ya ilmantar da al'uma tare da nishdantarwa, ina rokon Allah ya yafemin kurakuren da zan yi wayanda bansani ba. Alkhairan da ke ciki kuma ya isa ga al'umma su amfana tare da alfahari damu_.

*KAMAR YADDA KUKA GANI TUN FARKO WANNAN LABARIN BA KIRKIRARRE BA NE YAFARU DA GASKE NE SAI YAN WASU ABUBUWAN DA AKA GYARA DOMIN TAFIYARDA SHI A TSARI*.


*LOvE MEssEGE*

_Sometimes I think we’ll never see each other, with oceans between us and the skies above us. But the more I stay in fear of losing you, the more my heart yearns for you. I miss you!_

*PAGE* 6

Adam ya shiga mota ya kasa waiwayo ya kalli Hamida ita ko sai dariya ta ke ta na, "Toh su Yaya Adam agaida yan matan makaranta banda wasa."

Alokacin motarsu ta tashi sannan su Abba su ka kai

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment