Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a gefen Sarki, haushi taji dan ita bata son ganin sa ma dan ta tsani mutum marar tarbiyya, ta durƙusa gefen Mahaifinta, Sarki ya dafa kanta ya ce "Allah ya miki Albarka, wannan shine yariman Fallatu, yazo ganin ƴar uwarki ne to amma ya ganki ya ce ke yake so dan haka nan da sati biyu za'a muku aure da shi"


Ta ɗago fuska ta kalleshi yana yin murmushi kamar gonan auduga.




*_Daga yanzu dai free page ya ƙare duk mai buƙatan ci gaba zaibi hanyar da ya gani a sama_*






_*Mrs Aliyu ce*_



lιĸe
coммenт
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐A MASARAUTATA



NA
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)





_*Wannan labari na kuɗi ne Naira ɗari uku (300) ne kacal👌🏻 ga mai buƙatan ci gaba zai bi ta wannan hanya 👇🏻👇🏻👇*_


_Zaka/ki turo 300 ta wannan Account: *0019138715 Maimuna Isah stanbicIBTC* sai ki/ka turo min screenshort ta wannan number 09034313679_

_Ko katin MTN na 300 ta wannan Number 09034313679_






Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
BILKISU
A MASAURAUTATA




*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 11-12




Zata yi magana Sarki ya kuma shafan kanta ya ce "Ba sai kince komai tashi kije Allah ya miki Albarka"


Ta tashi ta miƙe tana fita a gurin ta fashe da kuka tana shiga ita ma ta faɗa jikin Sarauniya tana cewa "Ammy ki faɗa wa Sarki bana son sa Ƴar uwata ce take sonsa ni ina da wanda Nake so"




Sarauniya ta ce "Waye wanda kike so ɗin"


Ta ɗago ta ce "Ay kema kin san shi Umma Salman shi nake so"


Da Sauri Narsima ta tashi tana kuka ta ce "Munafuka dama can kin sa a ranki kina son Yariman Fallatu, duk kukan munafurci ne, kina ganin Wannan yaron kyakykyawan Yarima dama yaushe zaki ƙi dama son da kike wa Salman ɗin ma ƙarya ne dan kawai ki wulaƙanta mutane ne, yanzu kin samu Yarima, to bari kiji bake ba auren yarima kamar yadda kika rasa shi kema kin rasa shi kenan "



Sarauniya kan kallon ta ta ke har ta kai Aya sannan ta ce "Ke wa ce irin me baƙar zuciya ƙanwar taki, Wallahi idan kika yi wani gigi Sarki ya ce zai miki wani hukunci ba ruwana, ko da yake kinsan ba magana zanyi ba"



Ummu Salma ta ce "Ammi dan Allah kada ki bari nayi wannan auren dan bazan iya zama da shi ba"


Ta ce "Haƙuri zaki yi Ummuna kiyi mana biyayya zaki ga Alherin Abin kinji"


Ta girgiza kai ta ce "Ammi ko na rasa Salman bana son Yarima, saboda baida tarbiyya ko kaɗan dan Allah nidai ku min rai kada ku haɗa ni da shi"



Narsima ta ce "To Ammi ta ce bata so dole ku aura min shi mana ni ina sonsa"


Shiru Ammi tayi tana kallon yaran nata ta ce "To ku bari Maimartaba ya shigo sai ayi magana"



Shiru suka yi duka sai ajiyar zuciya da suke Narsima ko tana ta harare-harare.




Sai dare Sarki ya shigo Ummu Salma tana ɗaki har ta kwanta aka aiko Sarki na kiranta a falo, ta tashi ta bar abin da take yi Ta nufi Falon Sarki tana zuwa ta samu su Yakumbo (Wato sauran Matan Sarki) Da Sarauniyya sai Narsima da Yarima Anas. Gun Sarki tayi ya shafa kanta ya ce "Auta lafiyan ki kuwa naga idon ki haka "


Ta ce a hankali "Lafiya ta ƙalau "



Ya ce "To mun shirya za'ayi aurenki da Yariman Fallatu nan da Sati biyu"


Idonta ne ya cicciko da ƙwalla tayi sauri ta share ta ce "Ranka ya daɗe kumin haƙuri dan Allah bazan iya auren wannan mutumin ba, ku aura min wanda nake so "


Sarki ya ce "Me yasa baki son wannan ɗin"



Ta ce "Baida tarbiyya kuma ina da wanda nake so"


Sarki ya ce "Maganan wanda kike so bai taso ba haƙuri zaki yi rashin tarbiyya kuma kada ki damu da ita kinsan mutum ɗan Sarauta, kune ban ɗaura ku akan wannan turban ba, ban yadda ku raina wanda ya fiku ba"



Shiru tayi tana ƙara zubar da ƙwalla tana sharewa da bayan hannunta, jin muryan Narsima tayi ta ce "Ranka ya daɗe nice fa Babba ni ya dace da auren Yarima, kuma yaya zaka yi auren ta tana ƙasa da ni ni ka barni"


Ya ce "Saboda ita ya ce yana so, dama naso ya ce ke, amma tunda ita ya ce ay shikenan"


Ta ce "Ita fa tana da wanda take so Ka kyale ta ka aura mata bawan dama ay ita ɗin kalar bayi ce"


Sarki ya ce "Ke nifa bana son shashanci ku tashi kuje ku kwanta"


Suka tashi kowa yayi sassansa, Ummu Salma kan kwanciyarta tayi bata yi wani ishashshen barci ba.


Washe gari kuwa tana yin wanka ta miƙe sai gidan su Salman tana zuwa ta samu Umma na dama kunu, Umma zubo mata ta amsa tasha Salman ya fito daga ɗakinsa yana murmushi dan yaji yo muryan ta, Murmushinsa ya gimtse sakamakon garin fuskarta da yayi a kumbure ya isa gabata ya amshi kwaryan kunun ya ajiye gefe sannan ya mata wani irin kallo wanda ta gane tambayarta yake yi.



Ta buɗi baki kenan zata yi magana sai kuma ta fashe da kuka, Salman ya runtse idon sa dan jin kukan yake a cikin zuciyarsa, Umma ta kalle shi ta ce "Gimbiya a gidana take kuka, kai dan ubanka me ka mata dama ay na faɗa miki wannan bawa mungun iri ne idan dai kika ce zaki yi tarayya da shi haka zaiyi ta saki kuka, hala makirci ya haɗa miki"



Magananta ƙara dagula mata zuciya yayi dan haka ta tashi ta fita a gidan shi kuma ya bita, Ummi ma tana masa magana bai saurareta ba dan hankalinsa a tashe yake.


Tana zuwa ta zauna a inda suke zama tana share hawayen ta, shima ya zauna kusa da ita ya ce "Ina cikin masifa Gimbiya ki faɗa min me yasa ki kuka, nasan Sarki ya ce bazai aura miki ni ba ko"


Ta ɗako ta kalle shi ta ce "Wai zasu aura min Yariman Fallatu ne"


Lumshe ido yayi yayi ya buɗe su sunyi jajir jijiyoyin idonsa suka firfiti yayin da suka koma ja, tsoro ya kamata ya rike ta ya jijjga ta ya ce "Ba gun Gimbiya Narsima yazo ba"


Cikin kuka ta faɗa masa komai ya kuma riƙe damtsen hannunta ya kuma jijjigata ya ce "Shikenan sun raba mu, bazan iya rayuwa ba ke ba Ummu Salma"



Zamo hannunsa yayi tayi har ya kifa fuskarsa a kan cinyarta ya fara kuka, tsoro ne ya kamata dan tunda ta balaga bai taɓa riƙe koda hannunta, nan da nan jikinta ya fara rawa, jin jikinta na rawa yasa ya saketa ya miƙe ya zauna ya ce "Gimbiya ya zamuyi"


Ta ce "Ka tashi mu bar garin nan bazan iya zama a garin nan ba"


Ya girgiza kai ya ce "Duk yadda muke da son junan mu Ummu dole mu haƙura mu fawwalawa Allah komai "


Ta ce "Bazan iya ba, bazan iya auren kowa ba".


Ya ce "Kiyi haƙuri kiyi wa iyayenki biyayya, tashi kije kada su neme ki dan kinsan yanzu za'a saka mana ido sosai"



Ta ce "Salman har ankai lokacin da zaka fara korata"


Ya girgiza kai ya ce "Ba haka bane yanzu za'a na nemanki sosai"



Yana rufe baki saiga Yarima Anas ya na ganinsu ya matso ya ce "Kaidai baka da mutumci, yanzu dai kasan aure zata yi zata auri mutum mai daraja irin yariman Fallatu dan haka ka saurara lo da yake Da Yariman zan haɗa ku ya ci mata mutumci"


Gimbiya ta tashi ta kalli Salman ta ce "Shiga ciki dan bana son a wulaƙanta ka"


Ya miƙe Yarima Anas yajawo shi ya wanka masa mari Nan fa Ran Salman ya ɓaci ya juyo ya kalle shi kamar zai masa wani abu sai kuma ya fasa ya wuce cikin gida da sauri yana karanto Addu'a a cikin zuciyarsa, ita kan Gimbiya kuka tasa ta bishi ciki ta rungume shi baya tana kuka Yarima Anas ya bita har cikin gidan ya ɓanɓareta jikinsa ya kama hannunta, sannan ya kalli Umma da take shan kunu ya ce "Ki faɗa wa ɗanki ya fita harkan ƴata idan ba haka ba wata rana zaki tsinci gawansa"


Ta ce "Da hakan ma ka masa da yafi dan nima na gaji da masa magana baya ji, ti ni ba ruwana ka masa hukuncin da ya dace "


Cikin kuka Gimbiya ta ce "Ɗan naki za'a kashe, Salman matar nan bata sonka ina tunanin ba ita ta haife ka ba "


Ta ce "Ni na haife shi tunda baya ji idan akwai abin da yafi haka kisa ma a masa "


Gimbiya zata yi magana Salman ya ɗaga mata hannun yayin da kuma Yarima ya jata suka fita.


Suna fita Salman ya ce "Umma me na miki ne kika tsane ni haka na fara zargin ba ke kika haife ni ba, kamar yadda Gimbiya take zargi "


Ta ce " Zan tsine maka idan ka sake min irin wannan magana"



Shiru yayi ya tashi ya shiga ɗakinsa, yana tunani kala-kala a cikin zuciyarsa.


Duniyar ta musu zafi ko wannen su yana cikin ƙunci Gimbiya Ummu Salma kan tsaro aka saka mata an hanata zuwa gun Salman Kwata-kwata.


Masarauta kuwa sai Shirye-Shirye suke.


Yau saura kwana biyu yau kuma Dangin Ango Mata suka zo sawa Amarya Lalle akan idan sunzo washe gari sai a saka mata Lallen.


Masarautar ta cika sosai da jama'a Bayi ko sai aiki suke, Jama'ar masarautar Fallatu zasu wuce cikin gidan Sarki kenan wata mata ta hango Umman Salman ta waro ido ta ce "Rabi, me kike anan kuma"


Juyawa tayi taga Salman na kallon su yasa ta shige gida da sauri, ita kuma matar sai tabi ƴan uwanta tana ƙara kallon Salman.

Salman bin Umma yayi ya ce "Umma wacece wannan matar"


Ta ce "Fita ka bani guri "


Ya fita baice mata komai ba.


Bayan isowan su ne Yarima ya iso yana zuwa cikin gidan Sarki ya shiga, Fada yayi yasa aka saka masa kujera a gefen kujeran Sarki ya ce "aje a kira min Gimbiya Ummu Salman ace mata inji Sarki ne dan nasa baza ta zo ba in aka ce inji ne, dan yarinyar bata da kunya amma zan gyara mata zama lokacin da ta shiga Masarautar Fallatu, domin zan nuna mata Masarautar Famwa da Masarautar Fallatu ba ɗaya take da nawa masarautar ba, ita da ta taso ma ƙaramar masarauta irin Fomwa "


Ran Sarki ya ɓaci matuƙa, lalle yayi zaikai ƴarsa inda zata wulaƙanta, Lalle kuwa da ya bawa wannan yaro da baya ganin girman mutane gwara ya rasa Wannan Sarauta.


Yana cikin wannan tunani ne Ummu Salma tazo ta durƙusa Yarima ya taso yasa hannu zai kamata tayi sauri ta miƙe ya ce "Saura lokaci ƙalilan ki zama mata ta taho ki zauna gefe na"


Da sauri tayi gun Sarki ya tako zai yo gunta da sauri ta fita da gudu daga cikin fadan, Sarki ya mike ya ce "Ummu Salma ƴata ce dan haka na fasa wannan auren da kai kuma a ranan da nasa zan ɗaura mata aure da wanda take so wato Salman"



Yarima ya ce "Akan me"


Ya ce "Saboda baka cancanci mijin ƴata ba"

Yariman Fallatu ya ce "Lalle kuwa zaka rasa wannan sarautar taka"



Ya ce "A shirye nake saboda farin cikin ƴata"


Nan fa Yarima ya fita da jama'ar a lokacin ya koma garinsu.


Ummu Salma ko ɗaki ta koma tayi ta kuka har dare, ta kwanta barci amma barcin ya gagari idonta dan haka ta tashi ta fito taga harlokacin akwai jama'a sosai.




Cikin jama'a ta shiga ta samu tabar gidan Sarki tayi gidan su Salman.




Tana zuwa ƙofar gidan taga ya fito yana ganinta yaga ta rame sosai ta ce "Kazo mubar garin nan"


Shiru yayi cikin ziciyarsa yana tunani tabbas yayi niyyar barin gari to amma garskiya bazai iya tafiya da ita ba dan haka ya ce "Ummunah kiyi haƙuri kiyi wa iyayenki Addu'a kinji"


Kuka saka masa nan ya gara rarrashinta saida tayi shiru ya mata nasiha sannan ya rakata hanya ta tafi. Ya dawo ya shirya ba tare da sanin kowa ba yabar cikin masarautar.


Baza ta iya auren wannan mutumin ba dan haka gwara ta bar musu garin su, ta kwammace taje ta zama baiwa a wani gari akan taje ta auri mutumin da baisan mutuncin mahaifinta ba.


Ita ma cikin dabara ta fita daga cikin masarautar tayi cikin Daji...







_*Mrs Aliyu ce*_

An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__

lιĸe
coммenт
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment