Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake ɗan lallashin ta, akan ta janye zancen. Amma taƙi.



A lokacin kuwa Soyayyar su da Salman san ƙara girma take a zukatar junan su.




WANNAN KENAN






_*Mrs Aliyu ce*_



lιĸe
coммenт
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[6/19, 7:50 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐A MASARAUTATA



NA
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)





_*Wannan labari na kuɗi ne Naira ɗari uku (300) ne kacal👌🏻 ga mai buƙatan ci gaba zai bi ta wannan hanya 👇🏻👇🏻👇*_


_Zaka/ki turo 300 ta wannan Account: *0019138715 Maimuna Isah stanbicIBTC* sai ki/ka turo min screenshort ta wannan number 09034313679_

_Ko katin MTN na 300 ta wannan Number 09034313679_






Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
BILKISU
A MASAURAUTATA




*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Free Page 5-6




Ba'a raba hanta da jini, haka masoyan suke ji a jikinsu ba wanda zai iya raba su, ita Ummu Salma tana ji a jikinta zata iya guduwa saboda da Salman dan dai shine yake kwantar mata da hankali, amma taci Alwashin idan suka ce zasu aura mata wani ɗa Namiji ba Salman ba zata gudu, sai taji kuma dama ita ma a cikin bayi Allah ya yita da ta zauna da masoyinta, yanzu gashi saboda da wata Sarauta suna son su rabata da masoyinta wanda hakan zai iya sanadiyyar rabata da numfashinta.

Shi ɗin ma tunanin sa kenan taya zai iya rabuwa da Ummu Salmansa wanda yana ganin dole ne su rabu kasancewansa bawa, wai shin wani irin zuciya Allah ya bashi da har zata so yarinya mai matsayi irin Ummu Salma, ya sani Ummu Salma ba sa'ar auren sa bace kuma harda ita take taimakawa wajen sake haɓaka soyayyar ta a ransa. Yasan rayuwansa saura kwanaki kaɗan ya rage domin ya sani baza su bar masa Ummu Salma zasu aurar sa ita, shiko yana ji a jikin sa duk ranan da wani namiji ya samu nasaran ɗauke masa Ummu Salman sa mutuwa zaiyi bazai rayuba.

Yana daga kwance a cikin ɗakinsa yana wannan tunanin yaji Umma tana ƙwala masa kira kamar faɗuwan aradu da sauri ya miƙe, dama can ya saba da wannan kiran nata yana fitowa yaga Umma a durƙushe gaban Gimbiya Ummu Salma ita kuma Ummu Salma tana roƙonta da ta tashi ta zauna, amma taƙi, suna ganin sa, Ummu Salma ta miƙe tana murmushi tayi gunsa, shima murmushin yayi Umma ta miƙe ta kalle shi ta ce "Ran Gimbiya ya daɗe me zaki da wannan ƙasƙantaccen bawa ay ba tsaranki bane, idan kika tsaya wa wannan ay kinci baya, to idan ma ya aure ki me zai baki a matsayinki na ƴar Sarauta"


Taji haushin maganan ta amma ba yadda ta iya tunda ita ɗin mahaifiyar Masoyinta ne, Saidai murmushin ƙarfin hali ta yi ta ce "Ummu kenan kada ki manta nima baiwar Allah ce kamar ku, kuma ni ina son sa ne ba dan Sarauta ko wani Mulki na "

Umma ta ce "Ahh dama shawara ce kawai"


Salman kansa baiji daɗin maganan Umman sa ba, amma dan kada ya ɓata mata yasa ya ce da Gimbiya "Muje waje ko"


Suka fita suka samu Kuyanginta a waje su suka shimfiɗa musu abin zama suka zauna, suka fara hiransu cikin nishaɗi, sun manta da ƙalubalen dake gabansu. Jinshi yake kamar wani sarki ba abin da yake damun sa, ita ko ta manta da wani sarauta da mahaifinta yake da shi, ita dai tasan Gimbiya ce a cikin zuciyar Salman ɗinta.


Suna cikin Nishaɗin su kawai sai suka ga Gimbiya Narsima a gabansu tana musu wani mungun Kallo, Gimbiya Ummu Salma ta tashi tsaye ta ce "Ƴar uwata me ya kawo ki nan"


Hararanta tayi ta kalli Salman ta ce "Kai tashi daga kan shimfiɗar nan tunda ba na tsohon bane"


Ba musu ya tashi zai tafi ta ce "Na baka izinin tafiya ne"


Ya dawo ya durƙusa a gabanta Ta ce "Kai wani irin mai taurin kai ne me kake taƙama dashi da har zaka Soyayya da Ƙanwata"


Gimbiya Ummu Salma ta ce "Ƴar uwa ki ta kyale shi ya tafi, bana jin daɗin irin abin da kike masa ina son sa ina burin ya zama mijina saboda haka ki kyale"



Ta mata mungun kallo ta ce "Ki tafi gida bana son ganin ki a nan"



Ta matso kusa da ita ta ce A hankali "Ina kallon mutumcinki Ƴar uwata, kada ki bari mutumciki ya zube a gaban kuyanginmu, tun wuri ki Sallame shi"


Sa hannu Gimbiya Narsima tayi ta hankaɗa ta, da Sauri Salman ya miƙe Sai kuma Gimbiya Narsima ta masa wani kallo tuni ya koma ya durƙusa ta ce "Da me zaka kayi zaka tare ta, dama nasan ay kai ɗan iska ne, to bari kaji Sarauta sai ɗan sarauta baka isa kace zaka aureta ba "



Haushi ya kama Gimbiya Ummu Salma, tana ganin girmanta amma ita Ƴar uwar tata bata gani dan haka ta nuna ta da yatsa ta ce "Baki isa ki hana shi ya aure ni ba dan ba kece mai bada ni ba, ina baki girman ki naga alama bakya so saboda haka na ajiye girman mu zuba ni da ke"



Ta kalli Salman ta ce "Ka tashi ka shiga gida"

Ya miƙe zai fara tafiya Gimbiya Narsima ta ce "Kai sakaran ina ne na Sallame ka ne"


Ummu Salma ta ce "Kece sakarya dai ba shi ba"


Gimbiya Narsima ta ɗaga hannu zata mareta tuni Ummu Salma ta riƙe hannun ita kuma ta ɗa zata mare Narsiman tuni Salman ya riƙe hannun ta ya ce "Haba Gimbiya ba halinki bane haka ban yadda ki daki Ƴar uwarki a kaina ba, ko a kan menene ma ban yadda ba, kuka rashin kunya ba naki bane ki tafi gida kawai nikan bana son tashin hankali"


Zare hannunta tayi ta saki na Gimbiya ta fara tafiya shima ya shiga gida yana shiga Umma ta balbale sh da faɗa shidai yayi bata haƙuri.



Gimbiya Narsima ce ta shigo ta ce "Ka shirya karɓan tsatstsauran hukunci tunda a kanka Ƙanwata ta min rashin kunya"


Tana gama faɗa ta fita daga gidan.



Ummu Salma kuwa tana zuwa cikin gida ɗaki ta faɗa ta fara rera kuka kamar wanda aka ce Sarki ne ko Sarauniya suka mutu, ita baƙin cikin da har yayarta taja ta mata rashin kunya a gaban Kuyanginta, tana cikin kukan nata kuwa Gimbiya Narsima ta shigo tare da Yarima Anas ta ɗago jajayen idonta ta kalle su, Yarima ya ce "Yanzu abin da kika zaɓar wa kanki kenan kiyiwa ƴar uwarki rashin kunya saboda bawa, haba Ummu Salma me kike so ki zama ne"


Cikin kuka ta ce "Matar Salman! kuma ita ta jawo na mata hakan, me ya kaita gurinmu"



Gimbiya Narsima ta ce "Hmmm lalle asiri wannan bawa yana tasiri a kanki Ummu"


Yarima Anas ya ce "Lalle kuwa zan siyar dashi a wani garin da baki sani ba"


Ta ce "Nima ko zaku rasa ni kamar yadda na rasa shi dan ki zan gudu wank garin da ba wanda ya sani"


Zaiyi magana ta tashi fuuuu har tana buge Yarima tayi Sassan Ammy tana zuwa ta faɗa jikinta tasa kuka Ammy ta shafa kanta ta ce "Auta me ke faruwa "



Cikn kuka ta faɗa mata komai Ammi ta ce "Ohhh Auta baki bar wannan maganan ba ni ma fa gaskiya ban amince ki auri bawa, to da kike son aure yanzu ma, yanzu shekarunki nawa ne, ko ƴar uwarki Narsima bata wannan zancen, ga yaran Sarakuna Kala-kala me zaki da wani bawa"


Haushin maganar Mahaifiyar tata taji dan haka ta tashi a jikin ta ta koma gefe tana ajiyar zuciya.


Kusan a haka ta yini ko abinci ta kasa ci har zuwa dare.



Yana Karatun Al-qur'ani Mai girma yaji an shigo gidan ya leƙa ta taga mutane ya gani da bulala a hannun su, Umma ya gni gaban su ɗaya daga cikin su ya ce "Ina Ɗakin Salman"


Da sauri ta nuna musu shiko kafin su ƙaraso ya fito suna ganinsa suka fara zabga masa bulalan dokin da ke hannunsa, abin Mamaki mamakon Umman nasa taji tausayin sai cewa take ku ƙara masa dama baya ji"


Saida suka ga yayi lilis tukunna sannan suka kama shi suka fita da shi.


Washe gari Sassafe saiga Gimbiya Ummu Salma saida Ta gaida Umma sannan ta ce "Ina Salman"



Umma ta ce "Tun jiya wasu mutane suka zo suka tafi da shi suna ta dukansa"



Da sauri Ta fita kuyanginta suka bita a baya. Kai tsaye Fada tayi dan tasan yanzu haka Sarki ya fito Fada.






_*Mrs Aliyu ce*_



lιĸe
coммenт
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[6/20, 8:20 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐A MASARAUTATA



NA
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)





_*Wannan labari na kuɗi ne Naira ɗari uku (300) ne kacal👌🏻 ga mai buƙatan ci gaba zai bi ta wannan hanya 👇🏻👇🏻👇*_


_Zaka/ki turo 300 ta wannan Account: *0019138715 Maimuna Isah stanbicIBTC* sai ki/ka turo min screenshort ta wannan number 09034313679_

_Ko katin MTN na 300 ta wannan Number 09034313679_






Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
BILKISU
A MASAURAUTATA




*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Free Page 7-8




Tana zuwa ta samu mutane suna ta gaida sarki ita ɗin ma gaisheta ake tayi saidai ko amsa musu bata yiba taje gefen Sarki ta zauna yayin da Yarima yake gefen daman sa, yana kallon shigowanta yasan me ya kawo saidai baice komai ba. Sarki ya dubeta ya ce "Lafiya Auta"


Ta ce "Ranka ya daɗe Laifin me Salman yayi ake masa hukunci, har aka fitar da shi daga gidansu"




Sarki ya ce "Wa ya fitar da shi"


Ta ce "Ɗan uwana da ƴar uwata suka sa a fitar da shi"



Zufa ne ya karyo wa Yarima dan baiyi zaton Ummu Salma zata yi magana a gaban mutane ba, saida Sarki ma ya kalle shi cikin sa ya ɗuri ruwa dan baisan me zaice ba, ya ce "Me Yaron nan muku"


Ya yi ƙarfin hali ya ce "Bani bane Ranka ya daɗe Gimbiya Narsima ce tasa aka masa kama shi a kulle shi"



Sarki ya ce "To akan me, laifi ne yayi"


Ya ce "Eh laifi ya mata kan amma ban san laifin me yayi ba"


Sarki ya ɗan ɗaga Murya kaɗan ya ce "Aje a ce ina kiran Gimbiya Narsima yanzu"



Bayan an tafi kiran ta ne Yarima ya harari Gimbiya Ummu Salma, ita kuwa ta kauda kai.


Gimbiya na zuwa ta durƙusa ita ma a gaban Sarki ta ce "Ranka ya daɗe ance kana nema na"


Ya ce "Eh Me Bawan nan Salman ya miki kika sa aka fitar da shi daga gidan su"



Kai tsaye ta ce "Ranka ya daɗe So yake ya lalata ƴar uwata Ummu Salma"


Nan fa aka fara ƙananan maganganu a cikin fadan Sarki kuwa shiru yayi yana Kallon fuskarta yana son gano gaskiyar lamarin amma ya kasa ganowa Can ya ce "Lalle wannan Bawa da Tsaurin Ido yake, ya rasa wanda zaiyi lalata da ita sai ƴata ".



Ummu Salma kuwa kuka tasa ta ce "Kiji tsoron Allah ƴar uwata kisan zaki mutu, tunda nake da shi bai taɓa nuna min komai ba, kuma ma zama na dashi Alheri ne tunda nayi karatu tare dashi, wanda ka tambayi ƴar uwata ina takai a karatu"



Haushi ya kama Narsima akan Ƙanwarta ta ƙaryata a gaban mutanen da suke ƙasa da ita bata yi magana ba Sarki kuwa ya ce "Narsima kije kisa A zo min da Salman nan"



Tsoro ya sake kamata dan tasan Salman yana cikin mummunan yanayi. Ta miƙe ta fita, ita ko Ummu Salma tana zaune sai kuka take ita abin da tafi damunta shine Sharrin da Ƴar uwarta ta musu. Can sai ga Narsima tazo ta ce "Ranka ya daɗe Ya gudu ya bar cikin masarautar nan"


Gimbiya Ummu Salma ta miƙe ta ce "Salman ba inda zaije Wallahi, ki faɗa wa waɗanda suka ɓoye shi su dawo da shi"

Sarki ya ce "Narsima ki faɗa min gaskiya Ina kika kai shi, idan baki faɗa min ba kika bari na gano da kaina zan miki mummunan hukunci "


Shiru tayi tana Kallon Yarima Sarki ko da yaga haka ya kalli Yarima ya ce "Kaima zan hukunta ka na samu da sa hannunka a cikin wannan zalincin"


Ya ce "A'a ni bani a ciki "


Ya ce "Amma ay kasan komai me yasa baka hanata ba"


Shiru ya kuma yi ita ko Narsima ta miƙe Sarki ya ce "Ina zaki je"


Ta ce "Zanje nasa a ɗauko shi ne"

Bata wani jima ba sai gashi ta fito da ƙarti a bayanta sun ruƙo Salman jina-jina, Ummu Salma tana ganin sa ta kuma fashewa da wani sabon kukan, Sarki ya kalli yadda jikinsa yayi jina-jina sai ido kawai Ya ce "Me kayi suka maka wannan hukuncin "


Cikin ƙarfin hali ya ce "Ban sani ba ranka ya dade"


Ya ce "Faɗa min yadda aka yi"


Gimbiya Narsima zata yi Magana Sarki ya ce "Ban baki damar magana ba"


Salman ya ce "Ina kwance a ɗakina suka shigo har gidan mu suka fara dukana daga ƙarshe kuma suka tafi dani wani kogo mai duhu suka sani na kwana a nan sai yau da Sassafe Gimbiya Narsima da Yarima Anas suka zo, suka sa aka maida ni wani tsohon ɗaki waɗan nan ƙartin sukayi ta dukana, har na fita hayyacina, sai daga baya ne na dawo hayyacina"

Sarki ya ce "Duk wannan Hukuncin da suka maka sunce akan kana son lalata musu ƴar uwane wato Ummu Salma "


Hawaye ne ya zubo masa ya kalli Ummu Salma da take ta kuka zuciyar sa ba daɗi kamar yaje ya lallashe ta amma ba dama ya kuma goge hawayen ya ce "Wallahi koda zan lalata ƴar wani bazan taɓa lalata Ummu Salma ba, Allah shine shaidata sannan ita ma shaida ta ce"


Ya ce "To me yasa suka maka haka, ka faɗa min kada kaji komai"


Ya kalli Ummu Salma ya ce "Kayi haƙuri Ranka ya dade sun min haka ne saboda na kasance ina tare da ƴar uwarsu "



Ummu Salma ta ci gaba ta faɗi komai kuma ta ce "Ni kuma Wallahi har yanzu shi nake so"


Sarki ya ce "Tashi ka tafi gida ku kuma dole ku fuskani hukuncina"


Ya tashi ya fita yayi gida yana shiga ya samu Umma ta kalle shi ta ce "Sun ga dama sun sake ka, na faɗa maka ka rabu musu da ƴar su kaki Allah ya ƙara gobe ma ka sake ni da kaina zan faɗa"


Ya ce "Umma dan Allah ina danginmu ina mahaifina ki duba tunda muke nan baki taɓa nuna min kowa a matsayin ɗan uwana ko ɗan uwan Mahaifina ba, gashi ke kuma baki sona bakya nuna min ƙauna kamar yadda uwa take nunawa ɗanta, yanzu dubi jiya abin da kike faɗa ko tausayina bakya ji".






_Ayi haƙuri da wannan_


_*Mrs Aliyu ce*_



lιĸe
coммenт
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[6/21, 8:06 AM] Mim😘: _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐A MASARAUTATA



NA
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)





_*Wannan labari na kuɗi ne Naira ɗari uku (300) ne kacal👌🏻 ga mai buƙatan ci gaba zai bi ta wannan hanya 👇🏻👇🏻👇*_


_Zaka/ki turo 300 ta wannan Account: *0019138715 Maimuna Isah stanbicIBTC* sai ki/ka turo min screenshort ta wannan number 09034313679_

_Ko katin MTN na 300 ta wannan Number 09034313679_






Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
BILKISU
A MASAURAUTATA




*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Last Free Page 9-10





Kallon sa tayi ta yi sai da ya gama ta ce "To fitsararre ka gama ko, ka ga min rashin kunya sannan ka matse ni na faɗa maka"


Ya ce "Kiyi haƙuri Umma bawai naso in ɓata miki rai bane amma jiya kiga irin dukan da aka min ko tausayina baki ji a matsayina na ɗan cikin ki"



Ta kalle shi ta ce "To su kashe ka mana ina ruwana idan sun kashe ka ma ni zanfi samun iskan duniya"



Baiji daɗin maganarta ba saidai haka ya haƙura saboda ba yadda ya iya.



Gimbiya Ummu Salma da kanta ta kawo maza guda biyu ta ce su gasa masa jikinsa, sosai suka gasa masa jikinsa kuma yaji daɗin jikin nasa.


Sarki kuwa da kansa ya kulle Gimbiya Narsima a wani ɗakin duhu ga ƙura sannan ya ce bai yadda da kowa ba zai na bata abinci da kansa, haka yayi wa Yarima ma, kuma ya ce sai sunyi kwana uku a ciki waɗannan ɗakuna masu duhu da ƙura. Sunyi baƙin ciki matuƙa kuma sunci alwashin koran Salman daga Masarautar nan kowa ya huta.


Da yamma Sarki yasa aka kira Salman bayan yazo ya gaishe shi ya ce "To Salman sana'an me kake yi da kake son auren ƴata"



Shiru yayi can ya ce "Bani da wata sana'a ranka ya dade amma saidai ina ɗan buga-buga "

Sarki ya ce "Kayi haƙuri da abin da ya faru kuma na musu hukunci, abin da nake so da kai kuma ka haƙura da Ummu Salma domin bazan so ta aure ka baka da wata sana'a ba"



Sunkuyar da kai yayi Sarki ya ce "Tashi kaje "

Ya ɗago ya ce "Nagode ranka ya daɗe"


Ya fita gwiwa a sanyaye.



Haka Narsima da Yarima suka ci gaba da zama a wannan ɗakin har tsawon kwana uku Sarki ke kai musu abinci da kansa yaƙi kowa yana zuwa gurin, ranan da aka fito da su kuwa aka yi wa Narsima Albishirin kan cewa Yarima Fallatu zaizo ya dubata.


Garin Fallatu gari ne mai girman gaske wanda Garuruwa goma sha biyu suke ƙarƙashinsa cikin harda garin Fomwa, Sarkin garin Fallatu kuma shine babban Sarki sannan yana da ikon sauƙe ko wani Sarki idan yayi masa laifi.



To Ɗan sarkin ne zaizo duba Narsima ita murna sosai zata yi aure a Babban gari, kuma zata gudanar da sarauta duk inda take so idan mijinta ya zama sarki.


Wanka tayi kwalliya sosai tasa kaya irin na alfarma tasa Alkebba ta zauna jiran sa.


kafin ƙarasowansa kuwa anyi wa masarautar kwalliya na ƙin ƙarawa dokuna sunsha ado Fada ma tayi kyau sosai ansa bayi sunyi wanka suma sun saka kayansu mai dama-dam.


Sai yamma kuwa ya iso da mutanen sa, koda ya isa fadan kallon kowa yake kallon wulaƙanci, gaishe shi aka zo ana yi amma shi ko kaɗan bai gaida Sarki ba, Sarki bai nuna damuwarsa ba saboda dama ay shine a ƙasan uban sa ( Nikan Munari nace Wallahi bai isa ba ay aure yazo nema)



Daga baya aka kaishi ɗakin baƙi inda ɗakin ma aka masa kwalliya irin ta alfarma duk wanna saboda da zuwan sa, Zai shiga ɗakin Gimbiya Ummu Salma tazo wucewa zata je gun masoyinta ya ganta, ya aika a kirata, tana tafiya sai ji tayi ana cewa Ranki ya daɗe"


Ta juyo ya ce "Yarima Suhaib ne yake son ganin ki"


Ta ce "Wanene kuma me wannan sunan"


Ya ce "Ɗan Sarkin Fallatu "


Ta ɗan ja tsaki kamar baza ta je ba sai kuma ta juya tayi gaba ta isa ta shiga cikin Ɗakin ta durƙusa ta gaishe shi. Ya ce "Kin wuce kuma kinsan dan ke nazo nan garin amma idan badan haka ba bazan zo ba"


Ta girgiza kai ta ce "Bani bace yaya ta ce "Gimbiya Narsima tana nan zuwa gare ka"


Ya ce "Dama ku biyu kenan"


Ta ce "Eh ita ma yanzu zata zo gunka"


Tana magana ta tashi bata jira cewansa ba ta fita ta ci karo da Narsima zata je gunsa ta ce "Ke kuma me ya kaiki"


Kallon ta tayi ta galla mata harara dan yanzu ita kwata-kwata bata ganin girmanta ko kaɗan, Lalle badan inda zata je ba da ko sai ta mare ta gaban taron mutanen nan.



Shiga tayi da Sallama tana zuwa ta zauna a ɗaya daga cikin kujeran ta gaishe shi, ya amsa tunda ya amsa baice komai ba saida yaɗau lokaci sannan ya ce "Narsima kike kowa, zan faɗa miki wani abu da ya kamata ki sani, Cikin ƙananan garuruwan da suke ƙarƙashin garin mahaifina na zaga duk garuruwan dan neman matar aure, wannan garin naku ne na ƙarshe saidai kuma duk banga macen da ta min ba sai mace ɗaya tal, kinsan wacece kuwa? "


Ta girgiza kai amma zuciyar fal farin ciki dan tasan ita ce, saidai kuma aka samu akasin haka lokacin da ya buɗe bakinsa ya ce "Ƙanwarki da tazo nan kafin kizo ita nake so kuma ita tamin zan aura yanzu ki tashi kije ki kira min ita, mu zanta idan na koma za'a fara shirin bikinmu"


Bata ce komai ba ta tashi jiki a sanyaye ta fita waje, gidan su Salman ta wuce saboda tasan Gimbiya Ummu Salma tana can, ayko ta sameta suna ta hira cikin nishaɗi ta ce "To Malama dama nasan abin da kika je yi kenan gurin Yarima Suhaib, dan ya ce yana sonki ki raba mu saboda wannan ƙaƙantaccen bawan ya cusa miki hassada da baƙin hali to ya ce ke yake so kuma kada kice zaki murna da hakan dan yadda bazan auri Yariman Fallatu ba haka kema baza ki aure shi ba, in yaso kowa ya rasa. "


Ummu Salma kuwa ta miƙe ta ce "Kwantar da hankalin ki kije ki nemi soyayyar sa danni kwata-kwata tsarinsa ma bai min ba balle yasa ran zai same ni, kin sani sarai ina tare da Salman bazan taɓa auren wani banza irin Yarima Suhaib da bashi da tarbiyya ba"



Ta ce "Eh ay zaki ce haka mana tunda kina gaban sa, "



Tana gama faɗa ta wuce fuuuu. Salman da Ummu Salma suka dubi juna Salman ne ya fara magana ya ce "Gimbiya me yasa kika je gurinsa, shikenan yanzu ta tabbata zan rasa shi kenan"


Ta ce "Baza ka taɓa rasa ni ba, nima bazan rasa ka duk wuya duk daɗi ina tare da kai"




Ya ce "Yariman Fallatu fa yake son ki, kinga ko tunda ya furta yana sonki za'a bashi ke"


Ta miƙe ta ce "Dan Allah kabar wannan magana muyi wata magana, ba fata nake mana ba ko na rasa ka bazan taɓa auren marar tarbiyya irin Yarima Suhaib ba"


Hiran su suka ci gaba da yi amma shiko zuciyar sa a cunkushe take.



Da taga alamun yana cikin damuwa yasa ta ce "Barin tafi na barka amma abin da nake so da kai ka kwantar da hankalin ka ba mai raba ni da kai sai mutuwa. "





Tana zuwa gida ta samu Gimbiya Narsima tana ta kuka, Sarauniya ta ce "Ki je Fada Sarki na neman ki"


Ta koma ta wuce ta samu Fada ciki ta ratsa jama'a ta shiga ta samu Yarima suhaib yana zaine

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment