Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakin kofa masu tsaron kofar uk fara
duban Zuhairu cikin mamaki da al'ajabin ganinsa tare da
Gimbiya Hasima ba tare da ya hallaka ba, kamar aydda
suke da masaniyar cewa duk wani namiji da ya kusanci
inda takc sai wannan matsafin ya halaka shi, matukar ba
mahaifinta ba
Da suka shiga cikin birnin duk inda suka wucc sai
jama'ar gari su bi Zuhairu da kallo saboda ganin sa tare
da Gimbiya Hasima suna masu mamaki da ganin
wannan al'amari, shi kuwa Zuhairu bai damu da abinda
yake faruwa ba. suka ci gaba da tafiya har suka isa fadar
Sarki Shaiban
Bayan sun isa fadar Gimbiya da suaran kuyanginta suka shiga ciki, ta je ta sanar da mahaifinta sarki
Shaiban zuwan Zuhairu ta yi masa iSo. Sarki ya bada
umarmin Zuhairu ya shigo aka je aka shigo da shi har
cikin fadarsa. Tun da aka shigo da Zuhairu cikin fadar,
Sarki Shaiban ya dubeshi sai ya sake cika da matukar
mamaki saboda ganin shi ne jarumin da ya yi mafarki
dashi mahayin doki da ya yaki matsafi Bahalu ya
halakashi a cikin mafarkinsa, gashi yanzu ya ganshi a
zahiri kuma shi nc wanda ya dauki alkawarin taimaka
wa yarsa. Zuhairu ya kai gaisuwa gaban Sarki Shaiban,
Sarki ya amsa masa, aka yi masa ishara da wajen zama,
ya zauna suka kadaita daga shi sai Sarki a fadar sannan
Sarki Shaiban ya ce da shi.
"Labari ya isheni game da taimakon da ka yiwa 'yata
Gimbiya Hasima, tare da alkawarin da ka yi na kubutar
da ita daga halin da ta ke ciki, shi ya sa na umarceta
cewa idan ta koma inda ku ka hadu da ita ia sanar da kai
Cewa ina son ganinka."
Ya inganta na sake yin godiya ga Ubangijna bisa
baiwa da ni'imar da yake saukarwa akan bayin sa, don
kafin faruwar wannan lamari na yi ma farki da zuwan
wani jarumi mahayın doki da ya zo ya halaka wannan
shu'umin matsafi ya kubutar da 'yata daga halin da take
ciki, sannan a yanzu da aka shigo da kai fadata sai na ga
cewa babu shakka kaine jarumin da na yi mafarki dashi
ya halaka wannan matsafi, don haka nake mai
kyakkyawan zato na samun nasara nafarkina va zama
gaskiya.
Ba zamu zama masu yaw aita mamaki akan abin da
ya faru ba don buwayar Ubangiji da ikonsa ta wuce
haka. sai dai mu yawaita godiya gareshi da addu'ar neman nasara, kuma na yi maka alkawarin cewa
matukar ka raba 'yata Gimbiya Hasima da wannan
shu'umin matsafi da ya sanya rayuwara cikin kunci, to
kuwa zan baka aurenta tunda itama tana kaunar ka,
wannan shi ne dalilin da ya sa na ce ta sanar da kai ina
son ganinka, Allah ya yi maka albarka.
Zuhairu ya yi matukar farin ciki da jin wannan
bayani na sarki Shaiban saboda kaunar da yake yiwa
Gimbiya Hasima, ya yi masa godiya cikin girmamawa
Lare da tabbatar masa da alkawarin da ya dauka na
taimakawa
Bahalu.
ka,
Gimbiya
Hasima
akan sha'anin matsafi
Daga nan suka yi sallama da Sarki Shaiban Zuhairu
ya tashi ya fita daga fadar, ya koma wajen su Gimbiya
Hasima ya sanar da ita abinda ya faru tsakaninsa da
mahaifinta, Gimbiya Hasima ta yi matukar murna da
farin ciki, sannan ta sa aka kai Zuhairu wani daki na
hutawa, abin kawatawa da kayan ado nau'i daban-daban,
suka zauna suka yi hira irin ta masoya aka kawo masa
abin sha na 'ya'yan itatuwa na marmari dangin su tufa,
inibi da kayan ciye-ciye na karrama masoyi, Zuhairu ya
ci ya sha daga abin da aka kawo masa sannan suka yi
sallama a bayan gama hirarsu ya tashi ya fita, ya je ya
kama dokinsa ya hau, ya kama hanyar komawa gida.
Tun daga wannan lokaci Zuhairu ya ci gaba da
ziyartar Gimbiya Hasima cikin wannan lambu da take
zuwa a kowane yammaci suna hira, wani lokacin kuma
ya kan tafi har birnin Bahazum fadar mahaifinta ya
Ziyarceta a can su yi hirarsu irin ta ma'abota begen juna.
Sannan Zuhairu ya sanar da kakansa Marwan
dukkanin abinda yake faruwa game da soyayyarsa da Gimbiya Hasima, da yadda mahaifinta ya karbeshi da
martaba, kakan nasa dattijo Marwan ya yi mamaki da
wannan labari sannan ya gargadeshi cewa, ya guji shiga
abinda bai shafeshi ba, matukar ba taimako zai yi akan
dan uwansa Musulmi ba, sannan kada ya sake ya cire
Zoben da ke yatsansa ko kuma ya taka sahun wani
matsafi da ya taso masa da nufin halakashi a duk inda
yake, idan ya kiyaye wannan sharadi babu shakka zai
samu nasara akan kowane irin shu'umin matsafi komai
tasirin tsafi da sihirinsa.
Al-amarin matsafi Bahalu kuwa bayan da ya koma
bagiransa da suke zaune tare da 'yar uwarsa Buniyatu, a
cikin wasu manyan tsaunuka da suke nesa da Birnin
Sinar, tafiya ce mai nisa tsakanin inda suke da birnin
Bahazum, sai dai sukan yi tafiyar cikin alkaluman
sihirin rage nisan tafiya, su je bimin cikin kankanin
lokaci, kuma idan suka je yankin da birnin yake sukan
shafe kwanaki masu yawa wani lokacin ma har watanni
kafin su sake komawa bigirensu.
A sanda matsafi Bahalu ya fara kaunar Gimbiya
Hasima ya kan zauna kusa da birnin Bahazu cikin halin
6ata na alkaluman sihiri yana lura da duk wanda zai ce
yana kaunarta ya halakashi, kamar yadda ya halaka
'ya'yan sarakuna da dama.
Bayan matsafi Bahalu ya yi jinyar raunin da Zuhairu
ya ji masa a hannu tsawon kwanaki masu yawa har ya
warke, sannan sai ya sake yin shirin dan komawa birnin
Bahazum da nufin halaka Zuhairu yana mai tusatuwa da
abin da ya aikata gareshi
Ya tafi ga taskarsa ta ajiyar kayan sihiri da tsafi da ya gada a wajen mahaifinsa, ya budo, ya dauko wani
kurtun sihirin daga cikin taskar ya maida taskar ya rufe,
ya koma gaban wani farin dutse mai haske dake tsakivar
dakin ya fadi ya yi sujjada, sannan ya daga kurtun
sihirin ya girgiza shi yana mai surutai da sambatu irin no
aikin sihiri, wani farin hayaki ya soma fita daga cilkin
kurtun zuwa jikin farin dutsen, nan take sai ga zanen
siffar Zuhairu ya bayyana a jikin farin dutsen tamkar
madubi.
Matsafi Bahalu ya nuna wannan sura ta Zuhairu da
ta bayyana a jikin dutsen da tafin hannunsa, yana mai ci
gaba da ambaton wasu kalamai irin na aikin sihiri, da
nufin neman sa'a a kansa ya halakashi idan ya sake
komawa gare shi.
Yana cikin wannan hali na aikin sihiri sai ga 'yar
uwarsa Buniyatu ta shigo cikin kogon dutsen, ta dubi
jikin farin dutscn nan dake gaban matsafi Bahalu, sai ta
ga zanen surar masoyinta Zuhaira tamkar a jikin
madubi. Nan take. farin ciki ya lullubeta, ta gabata
gareshi tana mai yin yabo da begen wannan sura.
Da jin abinda ta ke cewa sai Bahalu ya da kata da
abin da ya ke yi, ya juyo ya yi mata magana da cewa
"Shin ko kin yi sani da wannan jarumi, da ki ke yabo da
ambaton kyawun surarsa."
Buniyatu ta amsawa yayanta matsafi Bahalu da cewa
"Babu shakka na yi sani da wannan jarima sunansa
Zuhairu bin Safuwan, yana zaune a birmin Samaras dake
karkashin masarautar birmin Bahazum, na kasance mai
bibiyar rayuwarsa cikin bege tun daga ranar da na fara
ganinsa, cikin wasu ranaku da na ziyarci yankin birnin
Bahazum, shi ne wanda zuciyata take bege da mafi kyawun ambato dan kasancewa tare dani, shi ne wanda
na kyautata ranisuwa a akan alkawarin aurcnsa duk da
ya nuna rashin amincewarsa akan muradina.
Matsafi Bahalu ya cc da ita "Ni kuma na kasance
mai nuna tsananin gaba da kiyayyata gareshi sababin
abinda ya aikata a kaina, ya kasance mai kaunar wata
'yar Sarki da nake so da muradin aurenta, na kuma yi
alkawarin halaka duk wanda ya ce yana kaunarta don ta
Zama mallakina duk da ta ce ba za ta auri ma'abocin tsafi
da sihiri irina ba.
Shi ne mutum na farko da ya taba daga makami a
kaina da nufin yin gogayya dani har ya fidda jini daga
jikina.
Shi ne wanda ya fasa daya daga cikin kurtun sihirin
da na gada a wajen mahaifinmu har karfin tsafi da
Sihirina ya raunana.
Wannan ne dalilin da ya sa na dauki alkawarin
halakashi dan yin ramuwa a kansa bisa ga abinda ya
aikata a kaina a duk sanda na sake komawa
Bahazum."
birnin
Buniyatu ta ce dashi "Ina mai neman afuwa gareka
kada ka halaka masoyina bisa ga abinda ya faru, cewa ni
na kasance mai yawan bege da kaunarsa gwargwadon
bugawar zuciya da fitar numfashina, kuma zai zama
abin kaico gareni da wanzuwa cikin kunci da bakin ciki
idan na rasa wannan jarumi ban ma san yadda makomar
rayuwata za ta kasance ba."
Bahalu ya ce da ita "A rayuwata bana afuwa kuma
bana fasa daukar iansa, ba an saurara ga duk wanda ya
daga makami gareni ba da nulin halakani har sai da naga
Dayansa, kuma bani da kaico akan kowane irin hali da rayuwarki za ta kasancc idan na halaka wannan jarumi,
Bakin alkalami ya riga ya bushe garcki don na yi
rantsuwa da ababen bautata tare da yin yanka garesu
akan hakan ba zan fasa abinda na yi niyya ba, sai ki yi
hakuri.
Buniyatu ta fusata da jin maganarsa ta ce dashi idan
kuwa har ka halaka masoyina kamar yadda ka ambata na
rantse da duk abinda nake yin rantsuwa dashi, sai na ie
na halaka Gimbiya Hasima 'yar Sarki Shaiban bin Yasar
da ka ke son ka halaka masoyina saboda ita."
Tana gama fadar maganar ta tashi cikin fushi ta fice
daga kogon dutsen ta bar shi, Bahalu bai damu da
maganarta ba, ya ci gaba da abin da ya ke yi na aikin
Sihiri, dan neman nasara a kan Zuhairu ya halakashi, duk
da cewa ya san Buniyatu za ta iya aikata abin da ta
ambata akan Gimbiya Hasima.
Bayan fitar Buniyatu daga kogon dutscn ta tafi ta
nuna ta rasa abinda yake yi mata dadi a duniva, ta shiga
tunanin maganganun da yayanta ya ambata na cewa sa
ya halaka masoyinta Zuhairu, damuwa ta yi mata yawa
har ta rasa abinda yake yi mata dadi, ta san cewa tun da
yayanta ya yi nufin halakashi to kuwa babu shakka
rayuwarsa tana cikin hadari, ta ji ta kamu da kewar son
ganinsa nan take ta tashi ta kama hanyar tafiya birnin
Samaras dan ta ga Zuhairu, duk da ta yi alkawarin cewa
ba za ta sakc zuwa gare shi ba har sai ranar da za ta
tabbatar da cikar burinta na aurensa ko da bai amince ba.
Ta yi tafiya mai nisa, a cikin alkaluman sihirin rage
nisan tafiya har ta iso birnin Samaras da tsakiyar dare
gari ya yi shiru babu motsin kowa. ta nufi gidansu Zuhairu kai tsayc ta shiga ta wuce har dakinsa, ta
sameshi a kwance yana barci a kan gadonsa ta tsaya a
gabansa tana dubansa cikin bege da kauna har tsawon
wani lokaci, shaukin sonsa ya kara ratsa Zuciyarta anan
ta sake daukar alkawarin cewa ba za ta bari yayanta ya
halaka masoyinta Zuhairu ba matukar tana raye, idan
kuwa ya samu nasarar halakashi ba da saninta ba, ko
kuma ya yi masa wani aikin sihiri na cutarwa to kuwa ta
yi alkawarin sai ta halaka Gimbiya Hasima 'yar Sarki
Shaiban dan ta rama.
Bayan ta gama wannan tunani na ta ne ta kai hannu
za ta shafi jikin Zuhairu saboda shaukin kaunar sa dake
kara ratsa zuciyarta.
Kafin hannun nata ya kai jikinsa sai zoben da ke dan
yatsan Zuhairu ya yi motsi da karfi, Zuhairu ya farka
daga barcin da yake yi saboda motsin da zoben ya yi
alamar wani matsafine ko ma'abocin aikin sihiri ya
kusanceshi, ya duba ko ina a cikin dakin bai ji motsin
komai. ba, bare ya ga wani abu ya yi shiru yana saurare
jikinsa ya bashi cewa akwai wanda ya shigo cikin dakin
duk da baya ganin komai, dan ya san cewa babu yadda
za a yi zobensa ya yi motsi ba tare da wani ma'abocin
aikin sihiri ya kusanceshi ba.
Ya tashi zaune ya yi addu'a sannan ya tafi ya dauko
takobinsa dake rataye a jikin bango da Buniyatu ta ga
haka sai ta ja da baya sannan ta juya ta fice daga dakin
cikin aikin sihiri yadda ba zai ji takun sawunta ba bare
ya ganta.
Bayan fitar Buniyatu sai Zuhairu ya ji kamar motsi a
Waje, ya bude kofar dakinsa cikin sauri ya fito. ya duba
bai ga kowa, ya sake jin kamar takun sahu an nufi wajen
DUK MAI BUKATAR AUDIO NA LITTAFIN SAI YA DANNA HOTON DAKE NAN KASA

https://youtu.be/YSYyhta02NI




BAKAR GUGUWA
littafi na daya 1
Na Marubuci Shehu Usman Muhd
Typing by Shuraih Usman
Part E

ka zama miji a gareni ta kowane irin hali, dan haka ba
zan diana kaunarka ba kamar yadda ba zan rabu da
abinda na gada a wajen mahaifina ba na sirTin tsafi da
sihiri.
Zuhairu ya ce da ita "Ke dai kina cikin rudani da
bata mabayyani, kasancewarki mai yin imani da
bayyanar wasu bayanai na alkaluman sihiri akan cikar
kudirinki, kuma cikin yardar Allah ba za ki taba cimma
kudirin naki ba, cewa ni na kasance mai dogarO dashi
akan ya kiyayeni daga duk wani sharri ma'abota tsafi da
sihiri irin ki."
Buniyatu ta ce da shi "Kaine rayuwar ka take cikin
tasku da razani na kusantar halaka, sababin alkawarin da
dan uwana ya dauka na halakaka, akan soyayyar
Gimbiya Hasima dake
kalamansa sun munana akan ambaton salwantar da
wanzuwa a tsakaninku,
rayuwarka cikin aikin sihirin da yake shiryawa a yanzu
dan zuwa gare ka, wannan ne dalilin da ya sa zuciyata ta
ka samun nutsuwa akan maganarsa. kuma na shiga halin
damuwa da begen son ganinka, don haka na taso na taho
garcka cikin wannan dare, na yi alkawarin bada kariya
garcka akan duk wani aikin tsafi da sihirinsa, kuma idan
har wani abin cutarwa na daga cikin sihirinsa ya sameka
to kuwa na yi alkawarin sai na halaka Gimbiya Hasima
yar sarki Shaiban bin Yasar da yake son cutar da
rayuwarka saboda ita.
Zuhairu ya fusata da jin maganarta ya maida mata
raddi da cewa.
Har ke kina da tasirin bada kariya ga wanda ya
dogara ga Allah cikin lamarinsa, ke kanki ba ki da ikon
Kare kanki daga duk abinda Allah ya hukunta zai faru garcki, kuma ina mai gargadinki da gargadi mai tsauri
kan cewa duk abinda ya faru ga Gimbiya Hasima na
rantsc da wanda raina yakc hannunsa sai na halakaki
daga ke har dan uwan naki na sharc ruhinku daga dogon
kasa.
Yana gama fadar maganar Buniyatu ba ta ko tanka
masa ba, ta bace cikin alkaluman sihirinta ta fice daga
gidan ta yi tafiyarta ta barshi, Zuhairu ya tafi ya koma
dakin sa ya yi addu'a ya kwanta yana tunanin maganar
da Buniyatu ta fada akan Gimbiya Hasima har barci ya
dauke shi.
Tun daga wannan rana da Buniyatu ta je wajen
Zuhairu ta sameshi a gida da tsakiyar dare, Zuhairu bai
sake ganinta ta bayyana gareshi ba, kuma babu wani abu
da ya faru gareshi na daga aikin sihiri daga yayanta
matsafi Bahalu da ya dauki alkawarin sai ya hallakashi.
Sannan Zuhairu bai sanar da Gimbiya Hasima
abinda
ya faru tsakaninsa da Buniyatu
ba, akan
alkawarin da ta dauka na cewa idan wani abu na
cutarwa ya same shi daga yayanta itama za ta maida
martani a kanta.
Al'amarin Gimbiya Hasima kuwa ta samu nutsuwa
da kwanciyar hankali, akan lamarin matsafi Bahalu, tun
tana fargaba da tsoron kada ya halaka Zuhairu kamar
yadda yake halaka duk wanda ya ce yana kaunarta, har
ta daina fargabar komai saboda ganin matsafi Bahalu bai
sake bayyana gareta ba, tun daga ranar da suka yi artabu
da Zuhairu ya fasa kurtun sihirin da yake hannunsa,
kuma ta daina yin munanan mafarke-mafarken da take
yi a kansa, tare da ganin ababen ban tsoro da firgitarwa dake sata zaran1 a duk sanda zai bayyana gareta.
Sukan hadu da Zuhairu a duk sanda ta ziyarci
wannan lambu da take zuwa tare da kuyanginta su yi
hira irinta ma'abota bege da kaunar juna har zuwa
faduwar rana, sannan Zuhairu ya yi mata rakiya, har
kofar shiga birninsu daga nan ya juya ya kama hanyar
kamawa gida.
Duk wannan abin da ya ke faruwa Buniyatu ta kan
kasahce tare da Zuhairu a duk inda yake. Saboda
alkawarin da ta dauka na bada kariya gareshi don kada
yayanta matsafi Bahalu ya halakashi kamar yádda ya sha
alwashi, sai dai ta kan yi nesa da Zuhairu yadda ba zai ji
motsinta ba, don ta san idan ta kusanceshi zai gane cewa
tana tare da shi saboda zoben dake yatsansa.
A duk sanda Zuhairu suke cikin lambu suna hira tare
da Gimbiya Hasima Buniyatu ta kan ji kishi da bakin
ciki kamar ta je ta halaka Gimbiya Hasima, sai dai ba ta
da ikon aikata hakan saboda sanin cewa idan ta halakata
babu shakka sai yayanta ya halaka Zuhairu, don haka ta
kan yi nisa da bakin lambun dan kada ta ji ko ta ga
abinda suke yi na soyayya da begen juna.
Wata rana daga cikin irin wadannan ranaku na
rayuwarsu, Gimbiya Hasima tare da Zuhairu suna zaune
cikin lambu suna hira, kuyanginta, sun basu waje suna
zantawa irin ta ma'abota begen juna, Gimbiya Hasima ta
caba ado da kayan ado mafi daraja da 'ya'yan Sarakuna
suke sanyawa, suna zaune akan wasu kuferu na alfarma
dake tsakanin wasu filawoyi da furanni masu kayatarwa
da kyan tsari, kamshin turaren wuta ya gauraye wajen
mafi dadin kamshi daga turaren almiski.
Buniyatu da ta kasance mai bibiyar Zuhairu a duk inda yake, ta yi nisa da bakin lambun ya zu wa cikin
wasu duwatsu dake bayan lambun dan kada ta riski hurar
da suke yi ta masoya saboda kishi.
Gimbiya Hasima ta dubi zoben nan dake dan yatsan
Zuhairu sannan ta ce dashi.
"Na dade ina muradin mallakar zoben nan na azurfa
dake hannunka, tun daga lokacin da na fara ganin sa tare
da kai, sai dai ban yi sani ba ko cewa ba irin zoben da za
ka bada kyautarsa gareni bane, kasancewar ko yana tare
da wani sirri na daga rayuwarka a tare da shi.
Zuhairu ya murza zoben sannan ya ce da ita "Hakika
wannan zobene ne mai daraja a gareni, kuma yana tare
da wani sirri da ya shafi rayuwata, don haka ba zan iya
bada kyautarsa gareki ba, kamar yadda wanda ya
mallakeshi gareni ya umarceni cewa kada na sake na
rabu da shi a duk inda nake cikin kowane irin hali."
Gimbiya 1Hasima ta ce da shi za ka iya bani shi ha
gani don na karewa irin kirarsa kallo, idan na koma
birnin Bahazum na sanya kwararrun makera su Kera min
irinsa."
"Zan iya baki ki gani." In ji Zuhairu ya cire zoben
daga dan yatsansa ya mika mata, Gimbiya Hasima ta
karba ta karewa zoben kallo na irin kyawun kirar da aka
yi masa, sannan sai ta sanya a dan yatsanta dan ta
gwada, zoben ya yi mata kyau matuka kamar saboda ita
aka kerashi, shi kansa Zuhairu sai da ya yi bege ga
kyawun zoben a jikin dan yatsanta, ya ji ba don
wasiyyar da aka yi masa ba cewa kada ya sake ya rabu
da zoben da kuwa ya bar mata 7obcn ta sanya a
hannunta.
Suna cikin wannan hali e kafin Gimbiya Hasima ta cire zoben daga hannunta ta bawa Zuhairu sai suka ii
wata irin kara mai tsananin karfi da rugugi mai ban
firgici kamar fadowar aradu ta cika wajen, kasa ta rika
girgiza tana raurawa kamar za ta tsage su rufta cikinta.
wani bakin gajimare ya taho daga gabas ya lullube
sararin samaniya tamkar hadari, gaba daya wajen ya yi
duhu mafi tsanani daga yankin duhun darc, rugugin da
suke ji ya ci gaba da hauhawa yana kara kusanto inda
suke har sai da suka daina jin komai sai shi, tamkar
kokon kawunansu zai fashe saboda tsananinsa.
Kuyangin Gimbiya Hasima suka razana suka rugo
inda su Zuhairu suke cikin firgici, ita kanta Gimbiya
Hasima sai da ta tsorata ta shiga halin rudani da kidima,
saboda ta san cewa matsafi Bahalu ne zai bayyana, cikin
wannan hali mafi munin yanayi daga alamomin
bayyanarsa.
Shi kuwa Zuhairu duk da ganin abinda yake faruwa
bai razana ba, sai ya mike tsaye yana duban wannan
yanayi cikin tsananin jarumta da karfin zuciya, kuma ya
san wannan ba komai bane face aikin sihiri da tsafi irin
na ma'abota shirka da tabewa, Wa iyazu billahi. Ya ce a
ransa, yana mai hasashen cewa matsafi Bahalu ne zai
sake bayyana garesu.
Bayan
Bayan wani lokaci sai suka hangi bakar guguwar
nan ta danno daga bangaren yamma, tare da iska mai
tsananin karfin, feshin wuta yana tartsatsi, da zubowa
daga cikin bakar guguwar. Kamar dai yadda matsafi
Bahalu ya ke yi idan zai bayyana.
Guguwar ta ci gaba da tahowa har sai da ta iso gaban
Luhairu sannan ta tsaya, aka sake yin tsawa da rugugin
radu mai tsananin karfi da ya zarce wanda suka ji da farko, wani farin haske ya keto daga cin bakar guguwar
daga cikin hasken sai ga Matsali G1Ziyanu ya bayyana
sanye da kaya irin na mashahuran matsafa, ma'abota
aikin sihiri, hannunsa na hagu yana rike da sandarsa ta
tsafi, na dama kuma yana rike da wani kurtun sihirin
bayan wanda Zuhairu ya fasa a wancan haduwar da suka
yi sanda suke fa fatawa a tsakaninsu.
Matsafi Bahalu ya dub Zuhairu cikin tsananin fushi
da fusatuwa ya ce da shi.
"Kaicon ranar dana-6ani marar amiani gareka, da za
ka hallaka sababin bijiréwa umarni da gargadin da na yi
garcka, akan ka rabu da Gimbiya Hasima amma ka ki ji.
Yau ne ranar da zan tabbatar da isa da karfin ikona a
kanka. Yau ne ranar da za ka tabbatar da tasirin tsafi da
sihiri da ka ke inkarinsa ya zarce tasirin duk wani abin
dogaronka.
"Yau ne ranar da za ka halaka da salwantar ruhinka
daga doron kasa ta hanyar kis amafi muni da ukuba mai
tsanani kafin fitar ranka. K uma yau ne ranar da na jima
ina sauraron zuwanta da alamomi zasu bayyana gareni
na mallakar Gimbiya Hasima ta zama matata, idan na
hallakaka zan dauketa na tafi da ita DAHRUL SABAR
dake lardin ASHTAR mu zauna tare da ita har abada,
fada ce da mahaifin yasa aka gina masa a wannan lardi
da babu wani mahaluki da ya isa zuwa inda take ya
shiga cikin ta idan ba mamallakinta ba, kuma shima
kafin ya kai ga tarewa a cikinta ya rasu, don haka ni ne
zan tare a cikinta tare da Gimbiya Hasima.
Zuhairu ya amsa da cewa kada ka zama mai alfahar
da bayyana abinda ba za ka iya aikatawa ba, cewa kai ka
kasance mai yawan alwashi da yawan rantse-rantse bisa ga abinda ka ke hasashen samun nasara a kansa, kuma
tun wancan lokacin har ya zuwa yanzu ababen bautarka
da ka ke yin rantsuwa da su sun kasa baka nasara bisa ga
tasirin tsafi da sihirinka.
Bahalu ya fusata da jin maganarsa ya yi karaji da
gunji dake tattare da aikin sihiri gaba ki daya wajen ya
yi amsa kuwwa da amo mai hauhawa, ya zaro wasu
kibiyoyi irin na aikin sihiri ya jefi Zuhairu da su, kafin
kibiyoyin sukai kansa sai wani farin haske ya ratso ya
shiga tsakaninsu,d aga cikin farin hasken sai ga
Buniyatu ta bayyana a gaban Zuhairu ta sanya wata
garkuwa ta kade kibiyoyin suka zube kasa, wajen da
kibiyoyin suka fadi ya kama da wuta kasar wajen ta
kone ta yi baki.
Bahalu ya fusata da ganin abinda ya faru ya dakawa
Buniyatu tsawa ya ce da ita, "Me ya sa ki ka kare abinda
na aikata cikin alkaluman sihirina da nufin halaka
wannan jarumi, ki sani cewa ba zan fasa abinda na yi
niyyar aikatawa ba, n: halaka wannan mutum ko ta
wane irin hali."
ga
Buniyatu ta ce da shi "Na yi rantsuwa da duk abinda
nake yin rantsuwa da shi ba zan bari ka halaka masoyina
ba, idan kuwa wani abu na cutarwa ya sameshi daga
garcka to kuwa sai na halaka Gimbiya Hasima wadda ka
ke son hallakashi saboda ita."
Matsafi Bahalu ya ce da ita "Idan kin zama mai bada
kariya a gareshi to kuwa ba za ki iya kubutar dashi daga
abinda na yi niyyar aikatawa a kansa ba, na yi rantsuwa
da tasirin tsafi da silhiri na tare da yanka ga ababen bauta
4 na kuma nemi sa'a daga garesu ina mai fatan samun
nasara a kansa.
Ya sake turawa Zuhairu wani aikin sihirin wuta ta vi
kansa za ta kama jikinsa ya kone, Buniyatu ta yi nata
surkullen ta tare wutar, nan take wutar ta mutu kafin ta
kai kan Zuhairu.



Ya sake jifansa da wani irin mashi na aikin sihiri ja
jawur dashi kamar karfen da aka curoshi daga wutar
makera, Buniyatu ta tura wata 1ska ma1 tsananin karfi ta
ture mashin ya tafi ya fada cikin wata korama dake
gudanawa a tsakiyar lambun, ruwan cikin koramar ya
kama tafasa saboda masifa nan take launin ruwan ya sauya
ya koma ja jawur kamar jini.
Matsafi Bahalu ya sake fusata da fushi mai tsanani ya
yi karaji da kururuwa mai matukar karfi, ya daki kasa da
sandar tsafin dake hannunsa, iska da bakar guguwa suka
turnuke suka rufe wajen har sai da su Zuhairu suka daina
ganin junansu, ya biyo ta cikin duhun bakar guguwar da
nufin halaka Zuhairu, Buniyatu ta tura wani farin haske
cikin bakar guguwar sai ga matsafi Bahalu ya bayyana
tana ganinshi, ya daga sandarsa ta tsafi dake hannunsa zai
makawa Zuhairu Buniyatu ta sanya hannunta ta ade
Sandar bai same shi ba.
Bahalu ya sake fusata ya kai mata sura cikin sa'a ya
fizge kurtun sihirin da yake hannunta, wanda a tare da
shi ne duk wani abu da ta gada na daga alkaluman sihiri
yake ciki, Buniyatu ta yi karaji da kururuwwa ma
tsananin karfi, saboda subucewar kurtun sihirin daga
hannunta zuwa hannun matsafi Bahalu.




Ku yi min afiuwa domin jin yadda za ta kasance
mu hadu a littafi na biyu.
Na ku har kullum mai fatan nishafantar da ku.
Shehu Usman Muhd
Littattafain Marubucin:
MAZAN FAMA
JARUMTA
BAJINTA
HARGITSI
GWAGWARMAYA
DAUKAR FANSA
BAKAR GUGUWA
JAHURUL KARNI
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment