Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

halaka ka har da kai sai
kayi hattara.
Zuhairu ya cika da matukar mamakin najin labarin
abinda yake faruwa akan gimbiya Hasima tare da
gasgata maganar da Muzaffar ya sanar da shi. Saboda
abinda ya gani da idanunsa, sai dai lamarin baisa
Zuciyarsa ta karaya ga barin kaunar gimbiya Hasima ba,
sai ma ya ji ya kara bcgenta aransa ya kuma dauki alkawarin taimaka mata ya rabata da wannan shu'umin
matsafin iya kacin iyawarsa.
Ya dubi Muzaffar ya ce da shi "ldan har abinda ka
ambata ya tabbata gaskiya babu shakka na dauki
alkawarin kasancewa wanda za1 raba tsakanın gimbiya
Hasima da wannan shu'umin matsafi ko wanene shi, zan
sadaukar da rayuwata dan na taimaka mata takubuta
daga makircin wannan matsafi matukar ina raye."
Muzaffar ya sake dubansa cikin mamaki ya ce da
shi "Kaicon zuciyar da tamakance akan soyayya har take
neman kai ruhi da gangar jiki ga halaka. Ka sani cewa
rayukan mazaje da dama sun salwanta akan kaunar
gimbiya Hasima kamar yadda kai ma zaka halaka
matukar baka nisanta zuciyarka da begenta ba. Menene
dogaronka na tunkarar hamshakin matsafi da ya halaka
manyan jarumai ya'yan sarakuna da attajirai masu ji da
kansu akan gimbiya Hasima."
uhairu ya ce da shi "Kai dai bari ga ambaton irin
Wannan zance kada imaninka ya raurñana, cewa ni na
dogara ga Allah ubangijin musulunci, gareshi nake
neman taimako kuma nayi imani da cewa shi
mairinjayene akan kowane irin karfin tsafi da sihiri, dan
haka bazan taba zama mai rauni ba akan shakkar wani
mutum ma'abocin tsafi da sihiri, kuma da sannu zan
zama mai cimma nasara akan abinda na dauki alkawarı
akansa cikin yardar Allah."
Yana gama fadar maganar ya yiwa Muzaffar sallama
ya kada linzamin dokinsa ya wuce.
Muzaffar ya bishi da kallo har va bace sannan shima
ya saki nasa linzamin dokin ya ci gaba da tafiya ya zuwa
inda ya nufa. Da Zuhairu ya isa gida bai sanar da kakansa Marwan
abinda ya faru garcshi a ftarsa ta wannan rana ba, dan
gudun kada ya ce yarabu da gimbiya Hasima saboda
wannan da shu'umin matsafi, ya bar maganar aransa tare
da daukar alkawarin cewa idan har ya koma bakin
wannan lambu da gimbiya Hasima take zuwa, idan ya
ganta zai tunkareta ya sanar da ita yana kaunarta kodan
yaga wannan shu'umin matsafi da aka bashi labarinsa.
Bayan wasu kwanaki da faruwar wannan lamarı,
Zuhairu ya sake yin shiri ya nufi bakin wannan lambu da
gimbiya Hasima take zuwa da isarsa wajan ya tadda
gimbiya Hasima bata karaso ba, ya sauka daga kan
dokinsa ya daure shi, sannan ya koma inda ya saba zama
ya zauna yana jiran zuwanta.
Bai dade da zama ba sai ga gimbiya Hasima tare da
kuyangunta sun nufo bakin wannan lambu da take zuwa.
Zuhairu ya yi farin ciki da sake ganinta, yana dubansu
har suka iso bakin wannan lambun suka sauka daga kan
dawakansu sannan sai ya tashi ya tunkari inda suke dan
ya sanar da gimbiya Hasima abinda yake ransa na daga
begenta. Ko dan yaga wannan matsafi da aka bashi
labarin kamar yadda ya yi alkawarin aransa.
Tun da ya tunkari inda suke sai yaga sunja sun tsaya
suna dubansa a tsorace kamar wanda suka ga wani abin
cutarwa ya tunkaro inda suke.
Zuhairu bai karaya ba saboda sanin labarin da aka
bashi, ya isa garesu ya yi musu sallama kuyangin
gimbiya Hasima suka amsa masa ita bata yi masa
magana ba, ta ma kauda kai gabarin dubansa kamar
yadda tayi a waccen lokacin day a taimakesu.
Ya ci gaba da magana garcta yana nai ladin cewa
"Idan har nayi dace da zuwana garcki bai zama laifi ga
gimbiya ba, ina mika gaisuwata garcki cikin girmamawa
da martaba 'yar sarki jikan sarki abin bibiya da koyi a
fagen adalci ga sauran sarakunan duniya, nazo gareki ne
(dan neman yarda bisa ga begenki da yake zuciyata idan
kin aminta dani cikin lamarinki."
Yana fadar wannan magana sai yaga gimbiya
Hasima ta dago kanta da sauri ta dubeshi cikin yanayin
tsoro da razana, kamar wadda ya fada mata mummunan
kalami mafi munin ambato, amma bata yi masa magana
ba.
Kafin Zuhairu ya sake yi mata magana sai suka j
wata irin tsawa mai tsananin karfi tare da wani rugugi
mai hauhawa tamkar fadowar aradu ya gauraye wajan.
Kasa ta soma girgiza tana raurawa tamkar zata tsage su
nutse a cikinta su hallaka, iska mai tsananin karfi tare da
bakar guguwar nan mai fesar da wuta daga cikinta, irin
wadda Zuhairu ya gani a wancan karan ta keto daga
bangaren yamma ta nufo inda suke.
Zuhairu ya ji zoben dake hannunsa ya yi motsi
alamar wani matsafine ya tunkaro inda yake.
Bakar guguwar nan ta taso kan Zuhairu kamar zata
rufeshi ya halaka, da ganin haka sai gimbiya Hasima da
sauran kuyangun da suke tare da ita hankalinsu ya tashi,
suka shiga halin kidima da rudewa, shi kuwa Zuhairu
sai ya ci gaba da duban bakar guguwa dake tafe da
feshin wuta cikin jarumta da karfin zuciya, kuma yasan
wannan ba komai ba ne lace aikin tsafi da sihiri irinna
ma'abota shirka, wa'iyazubillah ya ce aransa yana duban
guguwar har ta karaso inda yake.
Da guguwar ta karaso bata rufe shi ba kamar yadda
ya yi zato sai yaga ta tsaya agabanza tayi tsiri sama tana
juyawa, sannan ta sake yo kasa har sai da talafa wajan
ya washe sai wani farin hayaki da ya tsaya a gaban
Zuhairu, suka sake jin wani karaji mai ban firgici daga
cikin hayakin, sannan suka ji anyi zagi da kalma mafi
munin ambato akan Zuhairu, aka ci gaba da yi masa
magana cikin kakkausar murya mai hauhawa da fadin
cewa.
"Kaicon rayuwarka da kusantar ajali sababin abinda
ka ambata na begen gimbiya Hasima, zai zama mafi
munin karshen garcka da mutuwar kaskanci akanka
saboda abinda ka ambata ka sani cewa gimbiya Hasima
mallakina ce. Kuma nayi alkawarin hallaka duk wani
namiji da ya kusanci inda take matukar ba mahaifinta
ka
ba, bare ya ambata yana kaunarta kamar yadda ka
ambata na rantsc da karfin tsafi da sihiri na sai na
halakashi kamar yadda na halaka wasu mazaje da dama
suboda begenta."
Zuhairu ya maida raddi ga inda yake jin maganar
cikin karfin zuciya da cewa.
"Da zanyi gani da mai ambato dake 6oye cikin aikin
sihiri, da kuwa nayi jahadin kawar da mushiriki
ma'abocin aikin tsafi daga doron kasa, wancenc kai kumna
ka bayyana gare ni ko kazama daga wanda suka 1sa
sufada aji ba masu boyuwa cikin aiki sihiri ba."
Yana fadar maganar sai ya sake jin wata tsawar mai
matukar razanarwa ta sake cika wajen sannan iskar da
take kadawa mai matukar karfi ta tsaya cak. daga cikin
farin hayakin nan dake tsaye a gabansa, sai yaga want
mutum ya bayyana ta cikinsa, katone kakkarfa babu...

DUK MAI BUKATAR AUDIO NA LITTAFIN SAI YA DANNA HOTON DAKE NAN KASA

https://youtu.be/YSYyhta02NI



BAKAR GUGUWA
littafi na daya 1
Na Marubuci Shehu Usman Muhd
Typing by Shuraih Usman
Part C
alamar tausayi ko imani a tare dashi. Yana sanye da
sutura irinta mashahuran matsata, hannunsa nadama
yana rike da 'yar kakramar sanda wadda akayiwa ado da
zinari na hagu kuma.yana rike da wani gora irin wanda
ya gani a hannu matsfiya Buniyatu, an zagaye bakin
goran da wasu gurayc da kambuna irinna aikin sihiri, ya
dubi Zuhairu ya ce da shi.
"Ahir
"Ahir dika da ambaton wadannan kalamai akan
wadda ya buwaya cikin aikin sihiri, nine matsafi
BAHALUL HAJARI BIN KAUWAS, mahaifina shine
sarkin bokaye da matsafa ma'abota bautar gumaka da ke
yammacin birnin Sinar, bayan rasuwar na gaj1 kashi
casa'in da tara na sirrin tsafi da sihirinsa yar uwata ta
gaji kashi daya, dan haka yau duniya babu wani masani
cikin alkaluman sihiri da yasan kashi goma cikin dari na
abinda na gada wajan mahaifina.
Sannan ina kaunar gimbiya Hasima ne da nufin ta
Zama matata saboda na yi bincike a cikin alkaluman
Sihirina bayanan sun tabbatar da cewa, babu wata mace
da ta kai ta kyau da cikar halitta a wannan zamani, don
haka na yi alkawarin aurenta ko ta wane irin hali, duk da
ita ta ce ba za ta auri ma'abocin tsafi da sihiri irina ba,
kuma na sha alwashin hallaka duk wanda ya kusanci
inda ta ke bare ya ambata yana kaunarta. Na halaka
mutane da dama a kanta wasu ma ba ta san da su ba
wucewa ta zo yi suka yaba kyawun surarta na halakasu,
kuma na yi rantsuwa da abin bautata tare da karfin tsafi
da sihirina sai na hallaka duk wanda ya ce yana kaunarta
ko wa ye shi, har zuwa ranar bayyanar wasu bayanal
Cikin alkaluman sihirina da zasu tabbatar da mallakar
Gimbiya Hasima garenı ta zama matata."
Da jin wannan bayani na matsafi Bahalu sai Zuhairu
ya gane cewa shi ne yayan Buniyatul Hajari da ta taba
uwa gareshi cikin halin aikin sihiri ta ce dashi tana
Kaunar sa da muradin ya aurcta.
Zuhairu ya sake madia masa raddi da cewa
"Kaiconka ya kai wannan fajirin mutum da irin
kalamanka masu munin ambato, zan yi ishara garcka da
zuwan karshen wannan ta'asa da zalunci da kake
aikatawa, idan har ba ka rabu da Gimbiya Hasima babu
shakka ajali zai gabata garcka sababin haduwar ka dani.
Bahalu ya fusata dajin maganar Zuhairu ya ce da shi
"Da ka yi sanin makoma da karshen wanda ya ambata
irin wannan kalamin gareni da ba ka yi sha'awar
ambatashi da bakinka ba, na yi rantsuwa da ni kaina
saina halaka ka da kisa mafi muni ta hanyar karfin tsafi
da sihirina."
Ya yi karaji da kururuwa mai karfi da ke tattare da
aikin sihiri, da jin ya yi amsa kuwwa da
hauhawa Kasa ta ti girgiza, ya juya sandar sihirin da ke
hannunsa nan takc ta rikida la zama shafceciy ar takobi
tana sheki kaifinta kamar zai zuba a kasa, ya taso kan
Zuhairu a fusace bakar guguwar nan ta biyo bayansa.
Zuhairu ya zare tasa takobin ya tareshi suka yi karon
battar karfe, takubbansu suna haduwa wata kakkarfar
iska ta yi jifa da Zuhairu har sai da ya tafi ya fadi a kasa,
Bahalu ya kai masa sara Zuhairu ya goce, sannan ya
mike cikın sauri da azama, shima ya kai masa nasa
saran, babu abin da ya tare kaifin takobin Zuhairu amma
amo mai
tana shiga jikin Bahalu sai va kece gida biyu sara
takobin ya wuce.
Suka ci gaba da fafataWa cikin mugun nufi na san halaka abokin karawa. Da matsafi Bahalu yaga ba zai
iva halaka Zuhairu ta hanyar karfi da jarumta ba sai ya
koma ga aikin sihiri da tsafinsa.
Ya yi karaji ya nuna Zuhairu da tafin hannunsa yana
surutai da sambatu irin na aikin sihiri, nan take wuta ta
kama ta taso kan Zuhairu za ta konashi, Zuhairu ya yi
tsalle da maujajawa ya goce wutar ta wuce ba ta samu
jikinsa ba, ya watso masa wzsu kibiyoyi irin na aikin
sihiri Zuhairu ya sanya takobin ya ya kade kibiyoyin
suka tafi suka zube a kasa wajen ya kama da wuta.
Matsafi Bahalu ya sake yin wani siddabarun cikia
alkaluman sihirinsa, nan take sai ga wani katon dutse
daga sama yana ci da wuta, ya mirgino ya nufo kan
Zuhairu zai danneshi ya halaka, Gimbiya Hasima ta
kwala kara mai tsananin karfi saboda razana, don ta sha
ganin da irin wannan sihirin ya hallaka wasu daga cikin
masoyan ta. Zuhairu ya ji hucin tahowar dutsen daga
samansa ya yi tsalle ya kauce dutsen, ya fadi a wajen ya
kama da wuta kasar wajen ta kone kurmus. Ta yi baki.
Bahalu ya fusata da ganin Zuhairu bai halaka ba, ya
sake yin wani siddabarun cikin alkaluman tsafinsa. Ya
sari kasa da takobin da take hannunsa, nan take kasar ta
rika darewa tana ruftawa da duk abin da yake kanta ta
nufo inda Zuhairu yake za ta rufta dashi ya halaka.
Zuhairu ya sake gocewa kasar ba ta rufta da shi ba.
Matsafi Bahalu ya sake yin wani karaji dake tare da
aikin sihiri, iska mai tsananin karfi tare da bakar
guguwar nan suka sake turnuke wajen. Bahalu ya biyo
ta cikin bakar guguwar ya taso kan Zuhairu zai
halakashi, idan ya yi karaji sai ka ga feshin wuta yana
zuba daga cikin guguwar saboda aikin sihiri.
Gimbiya Hasima ta sake kwala wata razananniyar
kara saboda firgita, don ta sha ganin a gabanta ya halaka
wasu daga cikin wanda suka ce suna kaunarta da irin
wannan aikin sihirin.
Kafin bakar guguwar ta isa kan Zuhairu sai ya yi
kabbara da madaukakiyar murya mai karfi, tare da
ambaton sunayen Ubangiji yana mai tasbihi gareshi dan
yin tawassali da neman kariya daga gareshi akan
wannan aikin sihiri. Guguwar tana karasowa gareshi ya
kai sara cikinta da dukkanin karfinsa, cikin sa'a ya samu
matsafi Bahalu a hannu kurtun sihirin da yake hannunsa
ya fashe. Bahalu ya yi wata razananniyar kara mai karfi
saboda azaba, guguwar da ta tunkaro Zuhairu ta koma
baya ta bace, sannan wajen ya washe Zuhairu ya duba
bai ga matsafi Bahalu ba ya shiga nemansa cikin taka-
tsantsan amma bai sake ganin ya bayyana gareshi ba.
Bayan wani lokaci sai ya ji maganar matsafi Bahalu
yana cewa dashi cikin kakkausar murya.
"Azaba ta tabbata gare ka ya kai wannan jarumi,..
dake nufin tozarci ga girman matsayina. Na yi rantsuwa
da taurari tare da karfin tsafi da sihiri sai na halakaka da
kisa mafi &askanci da azaba mai tsanani sababin abin da
ka aikata gareshi."
Zuhairu ya ce dashi "Babu razanarwa ko ban tsoro
ga wanda ya zama gajiyayye ma'abocin rauni da rashin
tasiri, kaicon wanda yake gudun ceton rai cikin tsoro da
firgita akan abin da ya sha alwashin ganin bayansa.
Wadai da mai alfaharin da ya zama kaskantacce abin
dogaronsa ya kasa tasirin bashi nasara, idan kana inkarin
abinda na ambata ka sake bayyana a gare ni, na rantse da'
wanda raina yake hannunsa sai na halakaka da shafe ruhinka daga doron kasa, kamar yadda ka halaka
wadanda ka samu nasara a kansu. Kake alfahari da
hakan.
Matsafi Bahalu ya bayyana cikin fushi amma nesa
da inda Zuhairu yake jini yana zuba a inda kaifin
takobin sa ya sareshi sannan kurtun sihirin da yake
hannunsa ya fashe, ya dubi Zuhairu ya ce da shi.
"Zai zama abin kaico gareni idan na bar wannan
waje ba tare da na hallaka ba, sai dai ya zama dole
gareni na koma ga bagırena don sake yin shiri a kanka,
sababin fashewar kurtun sihiri da yake hannuna, amma
ina mai sake yin rantsuwa da duk abinda nake yin
rantsuwa dashi, halaka za ta tabbata gare ka a duk sanda
na sake bayyana gareka. Sababin abinda ka aikata a
kaina.
Yana gama fadar wannan maganar sai suka ga ya
bace, sannan bakar guguwar nan da ya bayyanata
cikinta ta sake turnukewa ta yi tsiri sama, ta nuasa ta
nufi inda ta fito har ia bi iska ta bace. Duhun day a rufe
wajen ya washe komai ya koma yadda yake.
Da Zuhairu ya ga matsafi Bahalu ya tafi sai ya yi
ajiyar zuciya irin na jarumta sannan ya maida takobin sa,
ya juya wajen da Gimbiya Hasima da sauran kuyaginta
suke tsaye suna kallon abin da ya faru tsakaninsa da
mastafi Bahalu, suna hada ido da ita sai ta fashe da kuka
sannan ta soma yi masa magana cikin wata tattausar
murya mai ban tausayi ta ce da shi.
"Wannan shi ne abin da yake damuna a rayuwata ta
duniya, tun daga ranar da wannan matsafi ya ce yana
kaunata na rasa sukuni da farin ciki har ya zuwa yau,
babu shakka duk abin da ya fada haka yake wannan matsafi ya halaka jama'a da dama saboda ni tun daga
yayan sarakuna da manyan attajirai da suka ambata suna
neman aurena, har ta kai a yanzu babu wani namiji da ya
isa kusantar inda nake bare ya yi min magana matukar
ba mahaifina ba, har sai wannan shu'umin matsafi ya
halakashi, wannan ne ya sa ban yi maka magana ba barc
godiya a snada ka taba taimakona a farkon haduwata da
kai, don haka ina rokonka ka nisanta kanka da kusantar
inda nake matukar ba kana so wannan matsafi ya
halakaka ba kamar yadda ya halaka wasu mutanen a
baya.
Zuhairu ya ce da ita "Ka da ki zama mai raunin
zuciya da zai sa imaninki ya raunana, ki sani cewa tsafi
da sihiri shirka ce wadda ba ta tasiri akan gaskiya, wato
addinin Musulunci, kuma Allah yana tare da duk wanda
ya dogara dashi zai kuma kareshi daga sharri ma'abota
tsali da sihiri komai tasirin tsafin sa, garcshi na dogara
kasancewar shi mai rinjaye ne akan duk wani aikin
sihiri,.na samu labarin abinda yake faruwa gareki.game
da wannan shu'umin matsafi, wannans hi ne dalilin da
ya kawoni gareki har na ambata ina kaunarki dan na ga
kowane ne shi, kuma na dauki alkawarin cikin yardar
Allah sai na rabaki da wannan matsafi na kubutar da ke
daga halin da ki ke ciki.
Gimbiya Hasima ta sake cewa da shi "Ka yi hakuri
ya kai wannan bawan Allah, ba na so ka halaka a kaina
kamar yadda wasu da dama suka hallaka saboda ni."
Zuhairu ya ce da ita "Idan ya samu nasarar hallaka
wasu mazajen saboda ke a baya Allah ne ya kaddara
faruwar hakan a kansu, kuma wannan ba yana nufin
cewa ya fi kartin hukuncin Ubangiji ba, cikin yardar Allah ni zan žama sanadiyyar halakarsa matukar bai
rabu da ke ba. Daga kaina ba zai sake halaka wani ba."
Gimbiya Hasima ta yi shiru ba ta sake yin musu
akan maganarsa ba, bayan wani lokaci ta dago kanta ta
ce dashi, ya ya sunanka kuma ina labarin garinku da
abinda yake kawoka wannan waje.
Zuhairu ya ce "Sunana Zuhairu bin Safwan kuma na
kan zo wannan waje ne daga birnin SAMARAS dake
karkashin masarautar mahaifinki, ya sanar da ita
dukkanin labarinsa sannan suka yi sallama, ta kama
dokinta ta hau sauran kuyanginta suma suka kama nasu
dawakan suka hau suka yi masa sallama suka
hanyar komawa binrin Bahazum, sai da suka yi nisa
sannan shima ya kama nasa dokin ya hau ya nufi hanyar
kama
komawa gida.
Da isar Gimbiya Hasima gida ta sauka daga kan
dokinta, ba ta tsaya a ko ina ba sai cikin dakin
mahaifinta, ta shiga cikin matukar murna da farin ciki
ta sameshi a zaune cikin halin damuwa, saboda bakin
cikin halin da 'yarsa take ciki
Da shigowarta Sarki Shaiban ya ganta cikin murna
da farin ciki, abin da ya dade rabon da ya ga yarsa
Gimbiya Hasima a cikin irin wannan yanayi, tun daga
sanda matsafi Bahalu ya ambata yana kaunarta, ya mike
cikin sauri yana mai matukar mamaki tare da tambayarta
abin da ya sanyata wannan farin ciki.
(Gimbiya Hasima ta ce dashi "Ya kyautu gareni na yi
godiya ga Ubangijina Allah mabuwayi a bisa taimako da
rahamarsa da ya saukar gareni, ta kwashe labarin abinda
ya laruu gareta tsakanin matsafi Bahalu da jarumi Zuhairu, a bakin lambun da take zuwa ta sanar da
mahaifinta.
Ta ci gaba da cewaYa samu nasara akansa har sai
da matsafi Bahalu ya gudu da kansa dan neman tsira, ya
kuma dauki alkawarin taimakona da raba tsakanina da
wannan shu'umin matsafi cikin yardar Allah.
Sarki Shaiban ya yi matukar mamaki da al'ajabi na
jin wannan labari, tare da yabon jarumta da bajintar
jarumi Zuhairu, tare da farin cikin jin ccwar ya dauki
alkawarin zai taimakawa yarsa Gimbiya Hasima ya
rabata da wannan shu'umin matsafi,ya daga hannunsa ya
yiwa Allah godiya, sannan ya juya ya dubi Gimbiya
Hasima ya ce da ita.
"Hakika Allah bai saukar da cuta ba har sai da ya
saukar da maganinta, babu shakka na yi mafarki da
zuwan wani jarumi mahayin doki a cikin mafarkin nawa
na ga wannan jarumi vana yakar matsafi Bahalu har sai
da ya hallaka shi ya kubutar da ke daga halin da ki ke
ciki. Gashi ayanzu mafarkin nawa yana shirin
Zama
gaskiya. Lallai rahamar Ubangiji akan bayinsa tana da
yawa, ya sake yin godiya ga Allah, sannan ya ce da
Gimbiya Hasima.
"Idan kin koma bakin wannan lambu da ki ke zuwa
ki ka hadu da wannan jarumi ki ce masa ya zo birnin
Bahazum ni sarki Shaiban ina son ganinsa.
Gimbiya Hasima ta amsa masa da cewa za ta sanar
da Zuhairu abin da ya umarceta sannan ta tashi ta koma
cikin gida wajen mahaifiyarta.
Shi kuwa Zuhairu da ya koma gida bai sanar da
kowa abinda ya faru tsakaninsa da Gimbiya Hasima ba, ya ci gaba da harkokinsa kamar yadda ya saba.
Washe gari da yamma ya sake yin shiri ya tafi bakin
wannan lambu kamar yadda ya saba, yana zuwa ya
sauka daga kan dokinsa ya daureshi sannan ya koma
inda ya saba zama ya zauna.
Bai dade da zama ba sai ya hangi Gimbiya Hasima
tafe ta nufo inda yake, ya cika da mamakin ganinta ita
kadai ba tare da kuyanginta ba, kamar yadda ya saba
ganinta. Wani abu da ya kara bashi mamaki shi ne bai
ganta akan doki ba, kuma ya san ba zai yiwu ta taho
daga birninsu zuwa bakin wannan lambun da kafarta ba.
Zuhairu ya ci gaba da dubanta har ta karaso inda
yake tana mai yi masa murmushi, sai dai ya sake yin
mamaki da ya ga bata yi masa sallama ba, kamar yadda
yake a shari'ar Musuluci ga duk wanda ya zo ga dan
uwansa Musulmi. Sai ya ji ta ci gaba da yi masa magana
da cewa.
"Zuciyata na cike da farin cikin sake ganinka
masoyina, marhabin da 7uwanka abin. begena, cewa dai
ni na kasance mai ni imtuwa da kaunarka a raina tamkar
buguwar numfashi ga dukkan mai rai."
Duk da Zuhairu ya ji murya tare da ganin surar mai
yi masa magan tamkar ta Gimbiya Hasima, amma sai ya
ji yana kokonton tabbatar da cewa ita ce, ya ci gaba da
dubanta bai yi magana ba, zuciyarsa tana shakkar ace
Gimbiya Hasima ce, ya ji a jikinsa cewa akwai yaudara
a cikin lamarin don haka ya yi taika-tsantsan.
Ta sake matsowa gareshi tana mai yi masa magana
Cikin tattausar murya da cewa "Ya ya na ga ka yi shiru
ba ka yi magana ba, kuma ka ki sakin jikinka da ni
kamar kana cikin wani hali na damuwa."
Ta kai hannu za ta taba jikinsa a sannan ne ya ii
zoben da yake hannunsa ya yi motsi. alamar wani
ma'abocin sihiri ne ya kusanceshi, cikin sauri ya mike
daga inda yake zaune, ya zare takobin da take daure a
damararsa ya dubeta ya ce da ita.
Duk da jin murya da ganin sura irin ta Gimbiya
Hasima ban yi imani da cewa ke ce Gimbiya Hasima ta
gaskiya ba, don haka ki sanar dani wace ce ke kuma
daga wane jinsi ki ka kasance, idan ba haka ba kuma na
halakaki. Dan na ga akwai aikin sihiri irin na ma'abota
shirka da bata a cikin lamairnki."
alamar
wani
Matar nan dake tsaye a gabansa cikin surar Gimbiya
Hasima ta dubeshi ta bushe da dariya sannan lokaci
guda sai ta rikida daga wannan sura ta koma surarta ta
asali wato Buniyatul Hajri kanwar matsafi Bahalu dake
hallaka duk wanda ya ce yana kaunar Gimbiya Hasima.
Ta sake dubansa ta ce da shi.
Lallai ka yizurfi cikin begen Gimbiya Hasima yadda
har ka ke iya ganc cewa ba ita ba ce koda an suffantu da
irin surarta, da ni kake bege kamar yadda ka ke begenta
a zuciyarka babu shakka da na yi farin cikin da babu
wata halitta da ta taba yin kamarsa a duniya. Zai kyautu
gareka ka cire kaunarta daga zuciyarka dan ita yar Sarki
ce, mafi girman daraja daga 'ya'yan sarakunan duniya,
ba za ta auri wanda ba dan sarki kamar ta ba.
Zuhairu ya cc da ita "Ba zan so ki ba, ba zan aminta
da maganarki ba, kuma babu shiriya tsakanina da duk
wani mutum ma' abocin tsafi da sihiri a duk inda yake,
ina ma sake jaddada nasiha gareki ki gaggauta tuba
daga halin da ki ke ciki dan samun rahama, idan ba haka
ba kuma ki nisanta da inda nake ko kuma na salwantar


BAKAR GUGUWA
littafi na daya 1
Na Marubuci Shehu Usman Muhd
Typing by Shuraih Usman
Part D

da ruhinki da kaifin takobina."
Buniyatu ta sake yin dariya sannan ta ce da shi "Mai
ya haddasa irin wannan gaba da kiyayya tsakanina da
kai maosyina? Me Gimbiya Hasima ta fi ni da ka ke
matukar kaunarta har ka kasa amincewa ka so ni kamar
yadda ka ke sonta."
Zuhairu ya ce da ita "Shirka, tsafi da sihiri sune suka
haddasa gaba da kiyayya tsakanina da ke. Kuma ba zan
taba aminta da ke ba cikin wannan hali da ki ke ciki har
abada, ita kuma Gimbiya Hasima ta fi ki da daraja ta
addini da hasken Musulunci. Ta fi ki nasaba ta daukaka
da daraja, sannan ke najasace a bar ki kasancewar kina
halin bata
da tabewa, kuma za ki zama mafi munin
makoma idan ki ka mutu cikin halin da ki ke ciki a
yanzu."
Buniyatu ta fusata da jin maganar da ya fada, ta ce
da shi "Hakika ka zama mai muzanci da tozarta
matsayina akan wadda ka ke bege, na rantse da girman
darajar abin da na gada na sirrin tsafi da sihirin
mahaifina, ba don na yi alkawarin aurenka ba, kuma ba
na so ka shiga halin darnuwa daizai sa ka halaka nima na
rasaka ba, da sai na dauke Gimbiya Hasima na hallakar
da ita yadda ba za ka sake ganinta ba, har abada. To
amma ka sani na yi alkawarin aurenka ta kowane irin
hali, kuma ko ba ka amince ba sai ka zamo miji a gare
ni, har karshen rayuwarka, ba za ka auri Gimbiya
Hasima ba, ka yi saurare da zuwan abin da zai faru
garcka nan gaba a duk sanda na sake dawowa muka
hadu."
Tana gama fadar maganar a bace a fusace cikin
alkaluman sihirinta. ba tarc da ta saurari abinda Zuhairu zai sake cewa ba, da Zuhairu ya ga Buniyatu ta tafi sai
ya maida takobin sa sannan ya koma wajen da yake
zama ya zauna yana tunanin abinda ta ce cikin
kalamanta.
Bayan tafiyar Buniyatu ba da dadewa ba, sai ga
Gimbiya Hasima tare da kuyanginta sun iso bakin
wannan lambu, da zuwansu ba su shiga ciki lambun ba
kamar yadda ta saba sai Zuhairu ya ga sun tunkaro inda
yake zaune, suna zuwa Gimbiya da kanta ta yi masa
sallama Zuhairu ya amsa mata sannan ta ce dashi.
"Na zo gare ka nc domin na sanar da kai sakon
mahaifina sarki Shaiban ya ce na shaida maka ka zo
yana son ganinka a bisa ga taimakon da ka yi min."
Zuhairu ya dan yi shiru kamar yana tunani sannan ya
cc da Gimbiya Hasima to, ya tashi ya je ya kama
dokinsa ya hau, suka juya baki daya suka kama hanyar
komawa birnin Bahazum, suna tafe suna hira har suka
isa kofar shiga birnin.
Tun daga

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment