Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni gani nake dukan ba zai shiga jikina ba ko da kuwa da bulalar karfe ne.
Ya ga ni ban ba da hakuri ba, karewa ma wani gefen daban nake kallo kai ka ce ba dani ake case din ba, kuma dama shine (discipline master) din makarantar baki daya, kowa ya san Malam GG watu Garba Gumel a wurin mugunta babu na biyun shi duk fadin makarantar.
Ya ce, “Su Azizah su koma su zauna, ni kuma in taso in biyo shi”. Ban yi musu ba na karkade rigata na bishi a baya, Iftihal ta biyo ni tana ta ba shi hakuri ya daka mata tsawa ya ce ta koma mazauninta, ya kuma sanya monitar ajin Suhaila ta yi mai gadinsu, idan suka fito ta kira shi a waya ta gaya masa.
Tafi-tafi ina bin shi kamar jela, ina gayawa kaina na cancanci a hora ni, wauta ce tun farko ta hanani gane Imran ai ba tsarana bane da zan kallafa zuciyata a kansa, don haka kome GG da Imran suka yi min dai-dain su ne.
Wani kazamin (student toilet) ya sani in wanke kana tafiya kana karo da busasshen kashi, zarni kuwa ba a magana. Hankalina ya tashi, na soma hawaye amma GG in ban da narka min zagi ba abin da yake.
Cewa yake, “So nake in ga matsayin ubanki a garin nan, in tabbatar da cikar ki ‘yar masu kudi. Allah yasa ‘Yar Aduwa ne ya haife ki, da kike wannan bunkasar. Kin ganni nan duk kyawun mace da farar fatarta ba ta burgeni, ko da kuwa ta hurul-eeni ce. Ko dai ta yi karatu ko in bautar da ita, bautar da uwarta da ubanta basu taba yi mata ba. Ke ni ko a aljannah bana fatan Allah ya hadani da mace, ba don komi ba sai don cewa ita ba komi bace face fitina a doron kasa, balle irin ku masu narka-narkan…….sai ku lalata mutum in ba ana wulakanta ku ba….”
Na daga idona a hanzarce da hawayena suka kafe karaf, na dubi GG din nan na ‘yan dakikai don ji nake kamar Imran ne yake gaya mun hakan. Ashe dalilin Ya Im kenan na wulakanta ni, kada in lalata shi? Dalilin shi kenan na gaya mun abin da zai bata mun rai in ji har abada bana son mu hada hanya? Sai na ji GG ya yi gaskiya, na shiga kada kai ina mai gasgata kowacce kalma dake fita bakinsa.
Na duka na soma ture busassun kashi da tsintsiya, da wani amai ya taho min gabagadi sai na kwararo shi a kafafun GG kore shar da shi kamar atini, don rabona da abinci tun na safiyar jiya. Ji nake kamar hanjina nake amayarwa.
Ya daka tsalle ya yi gefe yana kara zagina, ya ce, “Wallahi ba amai ba ko hantarki za ki amayar sai kin wanke toilet din nan fes, kamar tuwo na ya fadi in dauka, in ya so gobe a sallameni daga aikin gwamnati. Wannan ba abun damuwa bane ina da makekiyar gonar gado a Gumel, sai in koma gida in cimma sana’ar Uwa da Uba watau (noma)”.
Ya kira wasu dalibai da za su wuce ya ce su dauko mai kujera, ya girkata can gefe daga nesa ya zauna yasa hankici ya toshe hancinsa, lokaci guda kuma yana wanke kafarsa da ruwa a gwangwani da na kwararawa amai.
Haka ba yadda na iya na zage na wanke toilets dai-dai har guda shida, na kuma kwashe busasshen kashi na zuba a dustbin, sannan ya sani a gaba muka nufo ajinmu. Lokacin karfe sha biyu da rabi na rana ya rage awa daya a tashi. Na dauka shi kenan GG zai kyale ni, amma me? Ina sa kai zan shiga ajin ya juyo ya dakatar dani ya ce, “Haka za ki shiga musu aji kina warin kashi? Koma ki shanya kanki a rana har sai warin ya gushe tukunna, kneel down”.
Na koma cikin rana na zube gwiwoyina idanuna a rufe. Tsayin awa guda da rabi sannan aka kada kararrawar tashi. Su Azizah suka rugo da gudu suka rungume ni suna tattabani suna tambayar abin da ya yi mini, ban ce musu komi ba illa hawaye da nake ta sharewa ina fyace hancina da ya toshe don azaba, suka tabbatar ba za su ji kalma ko daya a bakina ba sai suka hakura suka kyale ni.
Muka zo gindin bishiyar dalbejiya inda muke tsayawa Shehu direba ya zo ya dauke mu, shiru-shiru bai zo ba har dalibai suka fara karewa. Su Azizah suka kulu matuka, ni kuwa ta kaina nake da kuguna da ya rike kamar zai balle saboda durkuson da na yi na awoyi da dama.
Sai misalin karfe uku na yamma sannan muka hango hancin motar Abba (Vanquish), muka shiga ware ido cike da mamakin yau Abba da kanshi ya zo daukar mu, to ina Shehun? Ashe dan duniyar ne ka janye da motar da Faruq a kujerar mai zaman banza.
Suka saki baki suna kallon ikon Allah, don ni har zuwa lokacin kaina a durkushe yake, tunda na yi musu kallo daya ban sake dagowa ba. Ya daka mana tsawar da ta firgitamu ya ce, “Da Allah malamai za ku shigo ne ko kuwa mu juya ku kwana a makarantar, ruwan wa? ‘Yan kauye kawai kun saki manyan bakunan ku kuna kallon mutane kamar baku taba shiga mota ba a duniya…”
Faruk ya katse shi da cewa, “Haba babban Yaya ayi musu a hankali man da me za su ji? Da yunwar dake damun su ko da shanya sun da aka yi kamar kayan wanki, ko-ko da fadan ka kamar barkono bayan basu suka kar zomon ba….?”
Ya ja tsaki “Tsut-tsut!” Kamar ya ci kansa don bala’i. Mu dai tuni mun nabba’a a bayan mota babu wadda tai magana, ya fizgi motar da gudun ta mai kamar na tashi sama, kan ka ce meye wannan sai gamu a gida.
Kamin mu fita Ya Faruq ya dubi Azizah ya ce, “Ya ya ne Azzy, na ga mutuniyar tawa ba yada take?” Azizah ta dan saki ranta ta jinjina kai ta ce, “Kai dai bari Ya Faruq, wani mugun malami ne Allah ya hadata da shi yau ya zane ta ya sata kneel down a cikin rana wajen awa daya wallahi”.
Iftihal ta ce, “Kai ina jin ba zane ta ya yi ba, wankin kashi ya sa ta. Baki ji ba yana cewa ya za ta shigo mana aji tana warin kashi?’ Haushin su ya ishe ni na bude motar fit na fice kamar guguwa, Faruq yana danne dariyar sa ya ce, “Asshah! Abu bai yi dadi ba, galleliyar yarinya kamar Abu na a ce an sata wankin kashi?”
Imran ya daga murya da karfi yadda zan jiyo yana cewa, “Ai madallah, kai madallah, wannan malami ya burgeni. Yanzu haka ba ta karatu sai SOYAYYAH! Ai ni wallahi ya yi min dai-dai, da zan ganshi da na sa Abba yasa an kara mai girma zuwa principal din F.G.C baki daya. Me ake da yaron da ba zai tsaya ya yi karatu ba?
Kuma ku shiga taitayinku wallahi don gobe insha Allahu zan je na neme shi mu kulla abota, in ba shi izinin duk wadda ta ki tsayawa ta yi karatu ya ba ta aikin kashi….” Ni dai ban juyo ba sai kuka nake, sai Faruq dake ta shan dariya kamar me. Su Iftihal duk a kumbure suntum suka fito cikin dana-sanin da basu gaya musu ba.
Wannan wulakancin da Imran ya yi mani, idan da zuciyata mai hankali ce da ya isa a ce ta saduda ta fidda shi a cikin ta da duk wani al’amari da ya shafe shi. Amma ina! Abu kullum kamar ana kara iza shi. Tun daga lokacin ya daina kaf-kaf din da yake dani ya koma treating dina yadda yake horas da su Azizah. Duk wani wasa da shakuwa dake tsakaninmu ya janye shi, kullum sai fada kamar Babana.
Kai ni ko Babana bai taba yi min bala’I da sababi irin na Imran ba, da abin da ya isa da wanda bai isa ba, haka takurar da yakewa su Azizah ya kara ninkata. Ya hana mu kallon talabijin balle kallon fina-finan India wai mun fara lalacewa. Su Azizah da basu san hawa ba basu san sauka ba mamakin su ya kasa boyuwa, suka kai karar shi wajen Abba kan ya takura mana ko music ya hana mu ji a radio wai duk a nan muke debo lalata. Ya sayo kasusuwan kira’ar Jabir ya rika sanyawa duk gidan.
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Na runtse idanuna da karfi, wani sanyi ya ratsa zuciyata tare da yin wata irin kakkarfar ajiyar zuciya, amma na kasa bude idon. Babu shakka Ya Im ya yi min bazata, ya shammace ni ya kuma gigita ni. Na rasa da idanun da zan bude in dubi su Azizah. Wata irin kunya da nauyin su da ban taba ji ba suka taru suka yi min mayafi, na bushe a zaunen da nake. Su Iftihal kan su bushewar suka yi, kamar sassakakkun gumaka. Cikin mu babu wanda ya san fitar shi, sai bude ido mu kai muka ganmu a cikin mota, direba ya ja, ko uffan babu wadda ta yi kokarin cewa a cikinmu.
Sai me? Mun fito break kenan muka ga motar Ya Im a kofar ofishin principal, aka aika in zo, wani irin kululuuu! Da cikina ya bayar ban san sanda na tsugunne a kasa ba na dafe cikina dake hargagi, ita kanta Iftihal a tsorace take, don dukkan mu munyi tsammanin karar Malaman mu ya kawo da Azizah ta ce suna bamu amsa.
Na shiga na tarar ashe ba a nan gizo ke sakar ba, zuwa ya yi a kan makarantar ta yi mun iyaka da su GG da ke cewa suna so na, domin ni matar shi ce an daura mana aure tuntuni. In ka kalli fuskar nan mai bam sha’awa ta Ya Im, ta juye gaba daya da harbadadden kishi zuwa na wani mutum daban mai zuciya da razanarwa.
Na yi hanzarin daga ido na dube shi, in tambaye shi dalilin shi na yi mun haka? Wata uwar harara da ya jefe ni da ita ba shiri na dukar da kaina kasa na mai da bakina na dinke na kasa cewa komai. Principal ya ba shi hakuri, ya kuma tabbatar mishi za a tsawatar don wannan dokar makaranta ce dama. Shi kuwa GG anyi neman duniya cikin makarantar ba a ganshi ba ya gudu, tunda ya ga motar Ya Im ya tsere don bai san yau da wacce ya zo ba.
Na cika na yi famfam na fito ina hada hanya saboda takaici, wai me Imran ke nufi dani ne? Ya hana mun kurbar ruwa a duniya ko me? Saboda kawai ina zaman cin arziki a gidansu?
Ya sanya ni cikin wani hali na matukar kunyar su Azizah, ban fita daga wannan ba ya zo ya lankaya min auren da Allah bai lankaya min ba. Inda na gode Allah daga Azizah har Iftihal babu wanda ta yi mun tambaya ko daya, domin dai su yara ne nutsattsu kuma wayayyu da basu faya mai da hankali a kan abin da bai shafe su ba.
Na dawo gida ina ta fushi, da dare kowa yana falo amma ni na kasa fita, gani nake kamar su Azizah za su fadawa kowa abin da ke tsakanina da Yayan su, na ji ni duk na zama wata bare mara gaskiya kuma munafuka, ban san sanda hawaye ya zubo min ba, nasa bayan hannuna ina sharewa duk da haka Imran na nan like a zuciyata, haka komi da yake yi bayan bani haushi illa wannan abu da ya yi mun cikin su Azizah da ya hanani kurbar ruwa cikin gidan gaba daya, duk da na san ba halayyarsu ba ce fadar abin da ba a tambaye su ba.
Shi din ne dai ya shigo Iftihal na biye da shi, ya ce, “Kin gani ko abin da na gaya miki, saboda na ce ina sonta a gabanku ta bi ta kuntatawa kanta ta hana kanta sakat, nima ta hana mini. Tunda na zo gidan nan Iftihal Antin nan naki ba ta barni na huta ba, sai garani take kamar gare-gare ko kuwa juyani ya waina a tanda. Ban san me take nufi ba, ban san me take so in mata ba da zai nuna ni Imran mai so da kaunar ta ne. na yi duk iya kokari na ta saurare ni ta kiya, wayar da na kawo dominta ta rufe ta toshe duk wata kafa da zan bi in nuna mata manufata ta alkhairi ce a tare da ita”.
Ya samu gefen gadon da nake zaune ya zauna, ya kai hannu ya dago habana ya ga yadda hawaye ke ta gudu, ya ce, “Jibi ki ga Iftihal, shin dama kaunar da kuke wa Anti-Abun na karya ne, da take shakkar ku? Saboda ni dai na san in dai so ne Zaynab na sona, ba tun yau ba, tun sanda ta fara kirgen dangi take sona balle yanzun? Dama so nake ku yi karatu kuma an kare, ba sai aure ba Iftihal?
Yau shekaru dai-dai har uku ina rainon Zaynab a cikin raina, ina addu’ar Allah ya bani tsawon ran da zan ga karewar karatun ku, in fiddo burin zuciyata na son mallakar ta. Ki taya ni rokon Zaynab ta amshi kokon bara ta ko na samu nutsuwa, ita ma ta samu damar karasa jarrabawar ta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Amma meye amfanin wannan hali da take neman jefa kanta?”
Na matsa can gefe na takure cike da wata sabuwar kunyar, kamar in daura hannu aka in ce “Wayyo Allah!” Iftihal ta yi tsaki ta ce, “Kema dai don Allah Anti Abu meye haka kike yi sai ka ce wata Illiterate (jahila), mu fa ba tun yau ba mun san Ya Im na son ki, har amanarki yake bamu in zai tafi to meye wannan mummuken da kike mana sai ka ce baki yarda damu ba? Kina tsammanin zamu so Ya Im ya auri wata fiye da ke ne? Kin yi kuskure. Ko ita Azizah da take yawan yi miki zancen Mami ina tabbatar miki don kawai ta ga hawayen ki ne da kukan da kike mana cikin dare, kin dauka barci muke?” Ta fita tana dariya.
Na juya na harari Ya Im da idanuwana da suka kada suka yi jawur, ya rausayar da kai cikin yi min wani lallausan kallo mai nuna yes, abin da yake fadi da wanda ‘yar’uwarshi ke fadi haka yake har zuciyarsu. Cikin kuka na ce, “Don Allah mai yasa ka yi mun haka? Ni da bakina kataba jin na ce ina son ka? Wannan ma ai sharri ne kuma wallahi sai Allah ya saka mini…..” Dariya na ba shi sosai.
Ya ce, “Kina bani mamaki Zaynab, abin da baki sani ba shine, duk wani motsinki a tafin hannuna yake. Kuma tun baki da wayo nake da wayo. Maganar kina sona ko bakya sona duk a barta, na ji ni nake son ki, kuma a yau na furta. Amincewar ki kawai nake nema ba wani abu daban ba, ina fatan ranar da kuka kare jarrabawa ranar ne za a daura mana aure, don ba zan koma ko ina ba Zaynab sai tare da ke a matsayin matata (by my side) Insha Allahu. Abin da ya wuce a bar shi a matsayin wanda ya wuce a fuskanci na gaba…..”
Na dago cikin murmushin takaici na katse shi da cewa, “Kana manta da wa kake magana Ya Im, ba da Mami bane da Zaynab ne. Ka shirya shiga uku ne da kake marmarin auren jarababbiya kamana?”
Da sauri kuma cikin murmushi ya ce, “Na shirya Zaynab, in ma sau goma-goma ne a rana duk za ayi miki, me ake da ‘yan mazan? Ke irin ki hudu ma idan ana ciki a rana a kuma haife za ku haife goma-goma a rana daya, in dai Imran ne mijin”.
Ya kanne min idonshi daya cikin zolaya yana murmushin sa mai girgiza zuciyana, na kyabe baki na ce, “Ban ga alama ba, wai Liman babu Mamu…”
Da sauri ya mike ya nufo ni yana kokarin cire riga ya ce, “Eye! Me kika ce Zaynab sake fadi ban ji sosai ba, bari in nuna miki ko waye Imranan nan da kike rainawa… wayon ki kadan ne haka maganganunki ko daya babu respect a cikin su. Ko da yake mantawa na yi ke din babbar mace ce ba karama ba, tunda tun kina karama babba ce, to babu laifi yau kin samu babban namijin da zai sa ki raina kanki….”
Na ga da gaske yake tubewar zai yi, sai ‘ya’yan hanjina suka hautsine, na koma lallashi na ce, “Haba don Allah Ya Im, idan Mama ta zo fa? Allah ni wasa nake….” Ya ce (yana kara dosoni) “Wannan ne kuma baki isa ba, tunda ba matse bakin ki na yi kika fadi abin da kika fada ba”.
Ya wancakalar da shirt din da ke jikinsa ya rage singileti fara sol. Na dauka da wasa yake ba cirewar zai ba, na cira kai a hankali na hango wani irin ingarman kirji lullube da muscles baibaye da lallausar gashi baki sidik nannade da gurayen karfi ta ko ina. Ban taba ganin babban mutun irin Imran ba, ban taba ganin Da namiji mai halittar GIRMA irin Imran ba.
Na tabbata duk abin da ya fadi babu kuskure a ciki, zai iya yin abin da ya fi hakan. Ubangiji da ya halicce shi ya iya halitta, ya kyautata halittarsa yadda ta zamo mabambanciya da ta sauran maza kwatankwacin sa. Kenan tsarki da GIRMA sun tabbata gare shi. Ganin ya nufo ni gadan-gadan yana shirin cafka ta, na ce, kafa! Me na ci ban baki ba! Zuwa cikin toilet na murza key sai karkarwa nake saboda tsabar kaduwa. Ina jiyo shi yana cewa, “Karyar banza cika bakin wofi, da ki tsaya mana ki ga aiki da cikawa, ki ga in ana haihuwa a gobe baki haifewa Abba dan jika a gidan nan gobe ba!” A raina na ce, “Allah ya tsare ni da haihuwar SHEGE!”
Ashe har ya fito ya shiga kunnensa, ya ce, “Na ji abin da kika ce Zaynab, ina mai tabbatar miki in baki amince da bukatata ba wato daura auren mu bayan kammala jarrabawar ki, za kuwa ki haifi SHEGEN! In yaso daga baya ayi mana auren mu rike abin mu ko ya kika gani?”
Zaynabu dai baki ya mutu, sai Uban mazari da jikina ke ta yi kamar wadda ta yi gamo. Ya yi dariya shi kadai yana fita daga dakin yana cewa, “Yarinya baki san Imrana ba, watakila sai a (foot-ball field) watau filin saka kwallo, ranar Innar taki, Abban naki da Ya Faruq din naki basu isa su kwace ki ba. Kuma in gaya miki ke karamar jarababbiya ce, su manyan jarababbun tsayawa suke a doka kwallon don a ga hazakar kowa, in ya so mai sa’a ya dauka, ba gudu suke suna neman mafaka ba alamar weakness (ragonta) kenan”.
Bani na fito ba sai da na ji muryoyin su Iftihal suna cigiyata a dakin za su kwanta, na kasa ko da shakar kwakkawaran numfashi don yanzu su Iftihal sun zame min surukai, na rasa yadda zan yi in iya hada ido da su. Sai na jiyo Iftihal na dariya tana gulmatawa Azizah, “Allah sarki Anti Abu! Ya Im ya takurata a gidan nan, Allah ni har tausayi take bani, dazu da muka shigo baki gani ba tana ta kuka abin tausayi, yanzu zaman falo ya gagareta tana tsoron ko zamu gayawa Mama ne”.
Azizah ta ce, “Ke rabu da ita, gulma ce ita ma tana son sa, baki san duk ranar da na yi zancen Mami da kuka take kwana ba? Gaskiya in suka yi sa’ar yin aure, they’ll make a perpect couple, domin sun dace da juna. Sai dai kin san ba karamin abu bane a ce Hajiya ta amince, yadda take son Ya Im da auren Mami, amma daga Abba ba za su samu matsala ba”.
Na ga dai in zan kwana cikin bayin nan su ba abin da ya dame su, ba kuma fita za suyi daga dakin ba hirarsu kawai suke. Karewa ma tare zamu kwana cikin dakin, to boyon har na yaushe zan yi? Sai na share ido na murje kunyar na fito, duk suka juyo suka dube ni kamin su kyalkyale min da dariyar su ta ‘yan biyu mai ban haushi. Ban ce musu komai ba na bi lafiyar gado na ja bargo har kaina. A sannan ne kowacce ta bi gadon ta suka kwanta suma.
Dakin nau gadaje ne na ‘silver’ kanana guda uku, nawa ne a farko sai na Iftihal sannan na Azizah. Can anjima Iftihal da ta fi makotaka dani ta kwaye bargon da ta rufe kanta iya wuyanta ta ce cikin rada yadda Azizah ba za ta ji ta ba, “Anti Abu don Allah in ce wani abu?’ Na dauka tsokanata za ta yi sai na sha mur na ce, “Ki rike abunki bana son ji”. Ta yi shiru, can ta ce, “Am serious, don Allah ya ya so yake? Ina nufin ya ya za ki iya kwatanta son Ya Im a zuciyarki?” (Tana murmushi mara amo).
Na lumshe ido na a hankali ina jin wata sabuwar kauna na ratsa zuciyata. Ni kaina na san son da nake ma Imran ba za ya kwatantu ba, ba shi da iyaka, kwakwalwata ba ta yi kaifin da za ta fahimce shi ba, harshena ba zai iya bayyna shi ba, domin ya fi yawan silin gashin kaina.
Ta tabbatar ba za ta ji kalma ko daya daga baki na ba, (shiru ma amsa ce, amma ga mai hankali), sai ta hakura ta juya ta kwanta.
Washegari ya kama asabar din karshen wata, kuma rana ce da muke sanitary watau kakkabe komi na dakin mu, mu fidda kaya masu datti mu cire yana, mu kintsa sif din mu. Wannan wani aiki ne da muka sanya kanmu bama son masu aiki suyi mana saboda baya gamsar damu.
Imran yayi sallama a dakin ya shigo, turaren da ya fesa na (Gucci-Rush) ya bakunci hancinmu. Na lumshe ido zuciyana na girgiza domin ba karamin kyau ya yi ba, cikin bakar shadda ghalila. Mu kuwa ko wanka ba muyi ba.
Ni sanye nake da doguwar rigar barci fara sol mai gajeran hannu, sai dai na daura zanen atamfa a kai, kaina babu kallabi, don haka murdaden gashin kaina ke dunkule cikin tufka guda a gadon bayana, rike da abin sharo yana ina sharowa. Su Azizah duk suka russuna suna gayas da shi, ya amsa yana cewa,
“Zance na zo Azizah, ina fatan ban yi sammako ba?” Kunya ta kama su duka, suka dukar da kai suna dariya kasa-kasa, ta ce, “Gaskiya ka yi sammako, Anti Abu ko wanka ba ta yi ba”.
Ya ce (idanun shi a kaina), “Kin san meye ne Azizah? In da kin san kyan da ta yi min a haka, da na ce ta daina wanka. Wannan Zaynabun dake tsaye gabana, ta fi mun duk matan duniya. Idan na daga ido na dubi wata mace, komi wankanta da kwalliyar ta sai in ganta kodaddiya a kan Zaynab dina.
Wanka da kwalliya ba su ke sawa a so mace ba, wannan daga Allah ne. Don haka in kina tunanin hakan ki daina. Ina tabbatar miki in Zaynab za ta shekara ba ta yi wanka ba, ba zan daina sonta ba, ba zan daina ganin ta a matsayin wadda ta fi kowacce mace a idanuna ba….” Dariya suka yi suna kokarin ficewa saboda su dai basu saba jin irin wadannan maganganun ba, balle kuma daga bakin da suke matukar girmamawa.
Ya ce, “Ku yi zaman ku ayi hirar da ku, watakila in ci arzikinku ta amshi kokon bara na, in kun tafi ko kallo na ba za ta yi ba. Ku taimaka ku tambaya min Zaynab, shin kalamanta masu tsada na sayarwa ne? Ko-ko kwalliyar da na yo mata ne bai burge ta ba in koma in sako?”
Suka sa dariya gaba dayansu, nima kaina ban san sanda na murmusa ba, still ban juyo ba na ci gaba da abin da nake, kamar in ce da shi shin ba yanzu ka gama cewa ba kwalliya ke sawa a so mutum ba?
Ya karaso ya amshi abin sharar a hannuna yana cewa, “Kawo nan in karasa miki ko kya zauna mu yi zance?” Ya dubeni cikin

Please Login or Register in order to submit comment