Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yarinya da ba ta kai ni ba, ta yi sallama cikin sassanyar muryarta ta shigo, hannuwanta duka biyu rike da ledoji, jikinta da fuskarta kamar an wanke a inji sumul-sumul da ita kamar tarwada abin sha’awa.
Gaba daya muka amsa mata banda Inna da ta juyo ta kalle ta, ta juya ta ci gaba da abinda take. Na mike da sauri na amshi ledojin hannunta ina yi mata sannu da zuwa, muka zauna bisa tabarma, sai zare ido take na rashin sabo.
Inna Rakiya ta ce, “Kamar Azizan Sa’idu, ‘yar wajen Hajiya Azumi, ina abokiyar tagwaitakar taki?” Ta ce, “Ba Aziza ba ce Iftihal ce, Aziza tana Porthearcourt”. Inna Dubu ta ce, “Ikon Allah, kamar taku ce har ta baci, wa zai iya banbance ku banda iyayen ku?” Ta yi murmushi da dan bakinta mai kyau.
Jin an ce diyar Baba Sa’idu ne sai na yi ta kallonta, nan da nan na ji ina kaunarta. Dan mai kaunarka, ai abin kaunar ka ne. da gani babu tambaya, ko daga yanayin fatar jikinta da irin kayan da take sanye dasu, tana kuma yanayi da Baba Sa’idu da irin Hausarshi ta Sokkotawa. Cikin murmushi na ce,
“Dama ke ce Iftihal?” Ta gyada kai tareda cewa,
“Wa ce ce Anti-Abu?”
Na kai duba na ga Innana wadda ko juyowa bata kara yi ba. Inna Rakiya ta zuba gyada da ruwan sha a babban kwano ta kawo mata tana nuna ni,
“Ita ce Zaynabu Abu, ‘yar’uwarki gata nan”.
Wani uban kallo da Inna ta juyo ta yarfa mata kadai ta san ta yi laifi, ta yi karambani, ta yi ba dai-dai ba. Amma ita din sai ta yi murmushi cikin bagararwa ta kara da cewa, “Ga Innar Abu nan tsugunna ki gaishe ta Iftihal”.
Ta kai gwiwoyinta kasa ta ce, “Inna ina wuni?” Sai da ta yi kamar ba za ta amsa ba, can dai ko me ta tuna? Ta daga mata hannunta na dama ba tare da ta juyo ba.
Banda dai ina tsoron Inna, da na tambayi Iftihal ina Baban yake? Sai na buge da ce da ita, “Ya Faruk yaushe ya ce zai zo ne?” Ta ce, “Ai sun tafi Bindawa shi da Ya Im, amma ina jin ya ce daga can nan zai taho, kullum yana zancen ki, yana cewa zai kawo mu wurin ki, koyaushe kuma sai ya yi tafiyarsa.
Yau ne da na ji Baba zai zo na ce zan biyo shi tunda Aziza ba ta nan, shine ya taho dani”.
Inna Dubu ta wanke min dattin raina da cewa da ita “To ina kika baro Baban?” Ta ce, “Yana zaure tare da Malam din nan gidan, amma ya ce komawa zai yi, nice zan kwana tare da Abu, idan zai koma jibi zai zo mu tafi”.
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Mafari kenan da wannan ya sayo min tsana mai tsanani a wurin Hajiyar su Hassan da iyalanta, sai da na gwammace dama Abba bai ji al’amarin ba. Tsakanin mace da mijinta sai Allah, bamu san ya a kai suka shirya ba, mun dai gansu kuma sun hade abinsu. Amma Mama ta ce take jin Imran (dan lelen Abba) ne ya yi waya ya ba Abban hakuri.

Na sha kimantawa raina ko ya Imran yake? Yadda abin ya bayyana a gareni shine, duk gidan kowa na son Imran, babba da yaro kowa bakin shi baya daina ambaton (Ya Im) kamar yadda na ji suna kiran sunan a takaice. Na san zai zamo mai kyawun sura kamar su Hassan, mai kyan hali kamar Baba Sa’idu. Tun ban ganshi ba na san dole ganinsa ya fi jin sa. Iftihal kan ce;
“A duniya ba mutum irin Yayana Abu!”.
Na tambayi kaina mai yasa shi din suke son sa, basa son kannensa su Hassan? Me yasa zai kasance na daban din, kamar yadda suke ikirari? Abubuwa da yawa kan sa a so mutum, muhimmi shine halayensa. A ganina ni ya dace in fadi cewa ba mutum irin Yayana Faruq amma ba su ba.
Na kan so Ya Faruq in kaunace shi, kauna irin ta su Iftihal ga Yayansu, saboda halayensa. Faruq mutum ne mai tsarge gaskiya komi dacinta, ko da hakan na nufin ya bata maka ne, hakan ba zai dame shi ba in har ya gaya maka ita wannan gaskiyar. Ba ya shiga abin da ba ruwan shi, baya da karya, baya da daukar duniya da zafi.
Babban abin da yake burge ni da shi shine, addininshi da gudun sabon Allah, a ko da yaushe yana kokarin fin karfin zuciyarshi a kan abinda take so, musamman idan ya fahimci wannan abun ba alhairi bane a gare shi.
Idan kuwa aka juya ta bangaren halitta, to su Faruq sune ‘maza’ da za a kira su da wannan sunan suyi gaggawar amsawa a ko ina. Ga tsayi ga zati, irin wadanda kowacce mace za ta yiwa kanta burin mallakar su.
Tunda na taso a rayuwata bani da abin tsoro irin MAGE, na tsani mage, ina tsoron mage tun ina mitsitsiyata. Idan na ga mage na kan firgita ne ko in kwalla kara. Idan kuwa ta hada yankwalallen jikinta da nawa, na kan suma ne ko in fita hayyacina, in yi ta firgita a yayin barci. Wannan dalilin ne yasa duk son kiwon mage da Malam ke yi ya hukura.
Rannan muna dawowa makaranta a motar yara (school bus), dama kullum sai an fara dauko su Hassan da suke da nisa, sannan a biyo ta makarantar mu a debo mu. Mun dauko hanyar gida Hassan ya ce, “Wai Rufa’i baka san magen gidan su Na’im ta haifi ‘ya’ya har guda goma ba? Suna nan baka gani ba in suna boxing abin sha’awa”.
Jauhar ya ce, “To su sammana man ko guda uku ne muyi kiwon su?” Rufa’i ya ce, “Ka ga ko Hajiya na son missa, don da tana da (Laura) da ta mutu ne ba ta sake samun wata ba”. Hassan ya juya ya ce da direba, “Maza kamin mu shiga gida juya kaimu gidan su Na’im”. Tuni Shehu direba ya cika aikinsa.
Ban san sanda na fashe da kuka ba na ce, “Don Allah don Annabi Hassan kada ku amso ‘yar mussan nan”. Rufa’i ya ce, “To ‘yar iko da gidan Uban wasu, idan Malam mai almajirai ne ya sayi gidan sai ki hana mu zuba mage”. Hassan ya ce, “Bar ‘yar banza, mai bakin baki irin na karuwai. Tunda an hana mu ce da ke BARAROJI to SADAKA-YALLAH ce???
Suka bude motar da kafa fut! Suka shige gidan mataimakin Abban su. Basu dade ba sai ga kowanne dauke da farar babyn mage, in ban da mazari ba abinda jikina yake. Suna shigowa suka watso su jikina. Da na kwalla wata azababbiyar kara sai da suka razana dukkansu, na mimmike ba ko kwakkwaran motsi balle kyakkyawan numfashi.
Iftihal tasa kuka ta ce, “Ai ga shi nan kun kashe ta, wallahi sai na fadi ma Abba”. Shi kansa Shehu direba ya tsorata, ya ja motar da gudu yana cewa, “Ku dai Hassan baku da kirki wallahi”.
Yana sanya hancin motar cikin gate din dai-dai lokacin da Faruq ya yi parking karamar Honda Prelude ta Imran, suka fito a tare, dukkaninsu sanye da kanyan NYSC, bakin Abia, zuwan su garin kenan.
Azizah ce ta fara fitowa daga motar a rude tana kiran “Ya Im!”. Shi ko Faruq ido yake warawa ya ga bullowar Abun shi, ya ga wane GIRMA da wane irin kyau ta kara, wane irin sauyin rayuwa ta samu a tsayin lokacin da ya yi bai ganta ba?
Kullum, cikin sabani suke, sau tari duk sanda suka zo Sokoton daga Abia, wanda kwata-kwata ma zuwan su uku cikin shekara daya, za su tarar su kuma anyi musu hutu suna Gwarzo, sanda suke Gwarzon su kuma sun dawo Sokoto abin dai kamar shiri, amma ya faru ne cikin ikon Allah. Kuma gareni sai ya zamanto rayuwa da su Iftihal ya debe min kewar Faruq din kusan kashi saba’in cikin dari.
Azizah ke fadin “Ya Im, su Hassan sun zubawa Anti Abu mage ta sume mana a motar”. Gaba daya Imran da Faruq suka yo motar, Imran ya riga Faruq dauko ni. Wannan shine karo na farko da ya daura idanun shi a kan Abun-Faruq, Abun-Baba Sa’id.
Maimakon ya yi sauri, tafiya yake dauke da ita a hannun shi tamkar wanda ya taka kaya, ko ko wanda kwai ya fashewa a ciki. Ganin irin tafiyar da yake yi ne ta marasa kuzari ya sanya Faruq karbe Abun daga hannunshi zuwa dakin Mama. A ransa yana cewa,
“Ashe Imran duk wannan physique nashi ragon maza ne, mace wannan kamar ‘yar shilla ya kasa daukar ta”.
Mama ce ta yayyafa min ruwa na farfado tana shafa kaina tana zagin su Hassan kaman ta ci babu. Farfadowa na yi ina makyarkyata, hawaye na tsiyaya ta gefen idona, fadi nake ina maimaitawa, “Mage ce fa a cikin jikina Mama”. Ta aza kaina bisa cinyarta ta ce, “Ba wata mage, sai ni sai Ya Faruq, gashi nan ya zo”. Ni ko na dage, “Gata nan fa a hannun su Hassan har guda uku wallahi….”
A ranar dai daga ni har Mama da su Imran babu wanda ya kwanta da wuri, don da na rufe ido barcin ya fara fizgana zan farka a firgice ina kiran mage. Washegari Imran ya tattara magen ya sanya a buhu ya ba Shehu direba ya ce ya mai da inda suka karbo. Ai kuwa a ranar su Hassan sun sha tafka da belt, sunyi kuka da majina, daman Imran ba daga nan ba (very-disciplined-brother).
Duk hakan bai ishe shi ba sai da ya sanya su duka cikin store ya kulle, ya hana masu aiki basu abinci tun safe har yamma. Hajiya Sa’a ba ta san me ake yi ba sai yamma lis ta dawo aiki. Ta yi murna da zuwan Imranan ta da kammaluwar bautar kasar sa, suka barke da hirar yaushe gamo irin na Da da Uwa a babban falon ta.
Ta nemi su Hassan ta aika su kawo mai lemu, ya ce, “Ai suna (store) ya kulle su”. Ta ce, “Dalili?” Ya yi kwafa cikin takaicin su da ya ki sakin sa har zuwa lokacin, ya ce, “Sun san yarinyar nan ‘yar Malam ba ta son mage suka watsa mata maguna ta suma, har yanzu ba ta san inda kanta yake ba”.
Ga mamakin shi sai ta buga tsaki ta ce, “Shine me? Gidan Uban su ta zo, ban ga dalilin da za ta takura su ba ta hana su yin abin da suke so. In ba ta son magen ta koma gidan Ubanta mana? Sallamamme kawai ka san me ake a cikin gidan ne? A kan Buzuwar nan aurena da ubanka ya kusa mutuwa, da sai dai ka dawo ka nemo ni a kauyenmu, in baka sani ba in gaya maka dalilin cewa da ya yi in tafi kenan kwanakin baya da na gaya maka a waya don sun ce da ita BARAROJI, ko ka bude min yara yanzu-yanzun nan ko in sabar maka wallahi”.
Ba musu Imran ya bude su Hassan domin dai shi mutum ne mai biyayya da baya saba umarnin iyayen shi ko ya ya ne. Ya samu Faruq a dakinsu yana cin abinci, ya zauna bakin gado ya dafe kai ya rasa abin da ke mai dadi, anjima kadan ya yi tsaki ya girgiza kai duk sai ya ba Faruq dariya.
Ya ce, “Kai Imran ya ya za ka yi when you become a father? (in ka zama uba) baka san sha’anin yara bane?” Imran ya sake yin tsakin ya ce, “Ni ba wannan ke damuna ba, maganganun Hajiya ne ban ji dadinsu ba, ban gane inda ta dosa ba. Ita fa babba ce, da ya dace ta dauki kowa nata ne a gidan nan, duk da dai na san ita mai nuna son ‘ya’yanta ne, amma saboda Allah su Hassan basu yi laifin da suka cancanci a hukunta su ba?”
Faruq ya dafa kafadunshi cikin murmushi “Common dear, don’t talk about this matter again, plz…” Shima sai ya share zancen bai kuma yin shi da Faruq din ba, to amma sai ya rika jin nauyin Faruq din ta yadda zai ga mahaifiyarshi a matsayin maras tunani, ga Faruq din shi bai dauki al’amarin wani serious ba ma.
Kwana biyu na warware case din mage ya wuce, sai dai cike nake da tunanin mene ne BARAROJI mene ne SADAKA-YALLAH?
Wannan tambaya ce da ta dade tana cina a rai, na kuma rasa wanda zan yi mawa, don haka da na ga abin ya fi karfin tunanina, dole na yakice shi karfi da yaji.

Imran dogo ne baki kakkaura, sai dai bai kai tsayin Faruq ba, amma ya fishi kauri da fadin kirji (physique), yana da kyakkyawar sura sosai, ya aje zagayayyen gashin baki dan siriri wanda ya tafi ya hade da kauraran zagayayyun lebban shi masu sulbi. Yana da hakora masu haske, jerarru kuma masu sheki. Komai nashi attractive wato mai daukar hankali ya dube su ko da bai yi niyya ba.
Kallon yanayin fatar jikinshi kadai ya isheka kimanta irin hutu da jin dadin da yake ciki, haka idanunshi za su nuna maka tsantsar ilimin da ke cikin su. Ba a fiya son mace mai kamun kai ta fiya sanya idanun ta sosai a kan maza irin Imran ba, domin ba wuya za a aikata zinar ido. Wanda kuma shi abin ya zo ne da halittar shi ba wai da gangan yake yi ba.
Yana da yawan amfani da karamin gilashi (medicated) ba don lalura ba sai don kara karkon idanu, haka nan Imran baka raba shi da cin biskit din nan na alkama (hob-nobs), yana da fada sosai kamar barkono, amma in ka fahimce shi ya fi ruwan sha saukin sha, raini ne baya so.
Shine babban da a ‘ya’yan Farfesa, sun haife shi a kasar England zamanin da shi Farfesa yake karatu, inda ya samu ilimin firamare da sakandire. Don haka ne in yana lallausar Turancin sa ba za ka so ya daina ba. Sai bayan haihuwar shi da kimanin shekaru goma, sannan aka haifi Hassan, Rufa’i ya biyo baya sannan Jauhar da dan karamin su Aliyu da Baban ya sanyawa sunan Malam Ali, suna kiran shi Haidar.
Sai da ya fara aiki a UDUS ne ya auri Azumi, wadda take basakkwata usul, kuma diyar wani abokin shi Farfesa a nan Sokoto wai shi Dr. Isma’ila Taura, ya ganta ne ranar ba da shaidar (Degree) ga daliban shekararsu da matsayin da ta fito da shi ne (best overall student in MBBS) na shekarar su baki daya.
Yana daukar lasifika abin da ya bude baki ya ce a filin taron shine, “Idan Azumi ba ta da aure shi V.C zai aure ta, wannan kawai shine kyautar da yake jin zai ba ta ya nuna kwazonta a duniya. Ba kuma tare da ya ganta ba, tsohuwa ce ko yarinya ce?”
Gaba daya filin taron rudewa ya yi da sowa, masu ihu na yi, masu kabbara na yi da sanyawa abun albarka. Babanta ne ya shige mai gaba ya ba shi auren ta. Ita kanta ta san ba karamar sa’a ta yi a rayuwar ta ba.
Imran da Faruk na tare tun daga farkon karatunsu na Jami’a, wato tun dawowar Faruq Sokoto, sun shaku sun kuma amince da juna, domin halayensu duk kusan daya ne, daman an ce wai sai hali ya zo daya ake abuta, wannan haka yake. Halayensu duk kusan daya ne, nutsuwar Imran daban take da ta sauran ‘ya’yan Farfesa, mutum ne da ya san ciwon kansa kwarai, yana adawa sosai da aqidun Malam Bature, yanayin rayuwar shi na Sokkotawan usli ne ziryan, hakan yanayin sutturarshi shadda ne, caftan ko babban riga a kullum, kai ka ce wani magidanci ne, da wuya ka ganshi da wani kaya ba shadda da hula ba, ra’ayinshi kenan.
Bayan kammala karatun su sun samu an yi posting din su gari daya yin bautar kasa, wato jahar Abia, duk da ba fanni daya suka yi karatu ba, shi Imran ‘civil engineer’ ne.
Sanda na kai aji hudu a sakandire duk wasu alamomin girma na ‘ya mace sun soma bayyana a jikina, da yake ban fara karatun sakandire da wuri ba, ni kaina na san na sauya wane shekarun baya. Abin nufi, halittar jiki da tsarin rayuwa. Zan iya kimanta shekaruna goma sha biyar a lokacin, mun yi sabo sosai da Imran duk da cewa ba zaman gidan suke ba suna fafutukar neman aiki.
Ba zan manta da yadda sunan “Abu” ya bace min a shekarar ba, ta dalilin Imran. Ya dauko mu ne daga makaranta yana tuki ina gaban mota, ya ce, “Shin wai ke ya sunan ki ne?” Na dube shi galala! Baki a bude ciki da mamakin wai duk kiran nan da ake Abu-Abu bai san sunana ba? Wannan ai rainin hankali ne, don haka na juyar da kai ban amsa ba.
Daga bayanmu Iftihal ta ce, “Kai Ya Im, da gaske baka san sunan ta ba?” Ya ce, “Gaskiya ban sani ba, na ji dai kuna cewa wani abu wai “ABU”, ni ko na san kyakkyawar yarinyar kamar wannan kallo daya za ayi mata a san ba sunanta Abu ba”.
Gaba daya suka tintsire da dariya, ni ko na yi murmushi kawai. Ya kafa mun ido kamin ya mai da hankalin shi a titi cikin son karantar karbar da na yiwa zancensa. Na kalli can wani gefen daban, cikin raina ina cewa, gaskiyan Iftihal ne, gaskiya ne ba mutun irin Yayan ta! Komi nashi mai ban sha’awa ne, hatta furucinsa. Azizah ta ce, “A school ma ba a ce da ita Abu sai Zainab”. Ya ce, “That is good, ZAYNAB, daga yau cikin ku kada wanda ya sake ce da ZAYNAB (ABU)”.
Wannan shine mafarin al’amarin. (Takori).

****

Na kwanta a daren nan ina maimaita kalmar “ZAYANB” da Imran ya ambata, na fadi ya fi cikin carbi, amma ban ji na fadi dai-dai ba irin yadda shi ya furta. Na yi tunanin abubuwan da suka faru a ranar tare da Imran na kasa mantawa. Idanuwanshi suka sanya zuciyata cikin wani sabon al’amari da ban taba tsintar kaina ciki ba. Na yi kokarin in yakice Imran a zuciyata na kasa, inda duk na juya shi ke zuwa cikin idanuna.
Na ji wasu sassa na jikina suna wani irin kaduwa da ban san na mene ne ba. Marana ya kulle tamau kamar zan yi fitsari, don haka na rarrafa zuwa (toilet) na yi ta kakalen fitsarin amma bai zubo ba. Na dawo daki na kwanta a dandaryar carpet, na ware fanka da A.C amma ban daina zufa ba.
Wannan al’amari ya tsoratani, domin wani al’amari ne sabo a gareni da ban taba tsintar kaina a ciki ba, ban kuma san ko mene ne ba. Hawaye ya zubo min ina kallon su Azizah dake ta barcinsu cikin kwanciyar hankali, na rasa abin da ke min dadi, na rasa mene ne shi wannan abun, haka na rasa me zan yi ya gusar min da wannan sabon abu da nake ji cikin jikina har kuma cikin kwakwalwata. Wannan shine mafarin shigar rayuwata cikin gararin da har yau take ciki, cikin halin bakin ciki da dakacen ina ma ba a haifeni ba.
Da ban hadu da Imran ba, watakila da rayuwata ta ci gaba da garawa a yadda take. Wato ba bakin ciki ba kuma farin ciki, sai godiyar Allah. Haduwata da Imran shine silar warwarewar al’amuran rayuwata da na Innana da suka shige min duhu, suke damun zuciyata tun ina kankanuwa. Har ila yau, Imran din ne sanadiyyar rushewar farin cikin rayuwata.
Wata zuciyar ta ce dani, wannan al’amari da ke neman samuna ba alheri bane a tare dani, don haka in nemi tsarin Allah. Wannan ita ce tarbiyyar da iyayena suka dora ni a kai, wato duk wani abu da ya fi karfin iyawa ta, ya fi karfin sani na, ya fi karfin kariyata to in nemi tsari da kariyar Allah, domin shine mai iko a kan komi.
Sai na mike ina layi na yi bayan gida, na dauro cikakkar alwala na yi (brush) na fito na suturce jikina na fara sallah, a cikin sujjada ta ina rokon Allah cikin yi masa kirari da ya yaye min wannan matsala da ya daura min a kan Imran, ya kawo sanadin da Imran din zai bar gidan gaba daya in huta.
Washegari na tashi da azumin tadauwa’i a bakina, kasancewar ranar Alhamis ce dama na kan yi azumi litinin da alhamis. Wallahi sai na ji ni sawai, kaman an yaye mani. Na yi ta yiwa Imran boyo cikin gidan har aka sha ruwa, gani nake kamar idan ya kalli kwayar idona zai karanto abin da ke damuna game da shi, wanda ya hana mani barci daren jiya. Wannan ya faru ne tun ina da shekaru sha biyar a duniya.
A daren Imran da Faruq na zaga gari cikin motar Imran din, Faruq ya ce,
“Yau tun safe ban ga Abu na ba, na shiga sassan Mama ya fi sau biyar ban ganta ba, ina cikin damuwa wallahi”.
Imran ya yi murmushin da shi kadai ya san dalili yin abin shi, amma bai ce komai ba.
Ya yi parking a wani katafaren shopping complex suka shiga tare, shi Faruq ya dauka biskit din nashi zai saya da baya rabo da saye. Don haka shi ya yi wani barin can daban yana saye-sayen shi. Kafin ya zagayo inda Imran yake, ya ganshi ya cika kwando taf da kayan shafa na mata (designers) yana jujjuya kwalbar turaren cool-water watau (Davidoff) a hannun shi, turare ne mai sanyin kamshi na ‘ya macen da ta san sirrin da ke cikin turare.
Sai daga baya ne ya dauki kayan shaving din shi da biskit din nashi na (Hob-Nobs) ya yi gaba ya bar Faruq da baki bude. Mamakin Faruq yaushe Imran ya yi budurwa bai sani ba? Ina ya je shi kadai ba tare da shi ba har suka hadun?
Imran S. Bindawa, tamkar ya san me Faruq din ke sakawa a ranshi, sai ya yi murmushi ya kanne mai idon shi daya cikin tsokana, ya ciza lebbanshi masu sulbi, ya matso dai-dai kunnenshi ya ce,
“Don’t be nervous mana (kada ka ji tsoro) ba kowa na sayawa ba face kanwata, ZAYNAB”.
Ya yi gaba ya barshi nan yana mai son convincing zuciyarshi ta yarda da abin da take ji, amma zuciyar ta ki yarda, karyatawa take da cewa, ba ZAINAB ya ce ba ZUBAIDA. Da Imran din bai yi gaba ya barshi ba, da ya ji irin hautsinawar da ‘ya’yan hanjin shi ke yi, da kukan da akuyar cikinsa ke yi. Ya kuma ga kallon firgicin da ya bishi da shi da gumin da ke ta yankowa daga kowanne sako a jikinshi.
Ya shiga gyada kai tamkar kadangare yana girgizawa, yana gayawa kanshi cikin lallashi cewa, ba da wani nufi Imran ya fadi kalaman shi ba, ba da wani nufi Imran zai yiwa Zainab kyauta ba, abin da yake kokarin fahimta ba shine ba. Zumunci ne kawai da alkhairi irin nasa, domin shi mutum ne mai alheri ga kowa ma ba Zaynab kadai ba.

Abinci ake ci bisa makeken dining din gidan, to amma me? Imran idanun shi kyar bisa kyakkyawar fuskar Zainab, tana kai lomar ta a nutse ba irin su Aziza ba hannu baka hannu kwarya. Idan tana tauna kumatunta duka biyu da tsakiyar habarta lotsawa suke ciki sosai. Komi nata a yangace amma naturally ba wai tana sane take yi ba, yana tafiya ne da halittar Ubangiji.
Sanye take da doguwar riga fara sol, ta matse dogon gashin kanta daga tsakiya da farin ribon ya sakko ya kwanta lamban bisa dogon wuyan ta kamar na barewa. Zainab a mike take sosai ga kuma alamun ‘mace’ dake neman bayyanuwa a jikin ta daga yanzu zuwa kowanne lokaci. Ya kasa cin abincin sai ko juya cokali cikin farfesu?
A bangarena, nima ba cin abincin nake yi ba, bugun da zuciyata ke yi a duk lokacin da na ga Ya Im, na yau har ya fi na kullum. Kaduwar da sassan jikina ke yi yanzu, wane na daren jiya. To a haka aka kare cin abincin ba tare da na ci wani abin kirki ba, haka tunda na dukar da kaina kasa ban dago ba. Idan akwai abin da nake son

Please Login or Register in order to submit comment