Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tuni muka Kara sauri sukuwa suna binmu har bakin gari wani uban dutsi da aka jefo ai sai ga idanuwa na wani dum! Naji dif! Naga duhu ya ziyarci idanuwa na wani zugi da radadi nakeji har tsakar kaina da karfi nace" wayyo Allahna Umma! Umma kina Ina umma bana gani!
Allah sarki dah da mahaifi sai Allah cikin takaici ta juyo umman tana kallonta,Wanda yayi dai'dai da lokacin da akayowa ummar jefa a kunne! Wani dum! Taji kunnuwan nata' tana kallon bakin taslima na magana amma batajin meh take cewa!
Ita kuwa kuka tasake Saki tace" wayyo Allahna ummana na makance umma idona a bude yake umma amma bana ganin ki umma duhu nake gani umma!!!!!!!!! Bana gani kitai makeni,
Matsowa tayi umman domin harga Allah batajin abunda taslimar ke fadi"kama hannunta tayi'tareda fadin taslima" Ina ganin bakin ki na magana amma kwata! Kwata banajin meh kike fadi banajin komai a kunnuwa na, sun jefe ni a kunne idan kina jina kizo mutafi karsu sake yimana lahani!!!

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ummana bakyaji na sai dai kina iya magana nashiga ukku sun kashe miki kunne kenan sun mayarda ke kurma, ni kuma sun kashemin ido sun mayarda ni makauniya wayyo Allahna!
Shirun dataji umma tayi yakara tabbatar mata da batajin ta,Wayyo Allahna nashiga ukkuna, ya *Allah Kai ne sheda* .................


still am in love with you my fans thank you, follow me!!!!!ΠΠΠΠΠΠΠΠ

Sai munhadu a book2 wato *ALLAH NE SHEDA 2* nagode masoya kucigaba da kasance Dani akoda yaushe taku har kullum"
ZAINAB ABUBAKAR SAFANA
xee'abu
Mrs'salihu Bamalli kaduna my luvly ustax.

GOLDEN'S WRITERS ASSOCIATION

Thank you for your shown love to me we are together fans.
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

ALLAH NE SHAIDA 2


ALHAMDULILLAHI NOW I WILL BE CONTINUE IN MY NOVEL ALLAH NE SHEDA 2,
Special tnx to my fans
Allah yabar xumunci daso da kauna.

GOLEN’S WRITERS ASSOCIATION

Dedicated to my sweet and dearling husby Bamalli ustax.
WRITING BY XEE’ABU SAFANA
MRS’SALIHU BAMALLI USTAX.



UMMA ta cigaba dajan hannun taslima ita kuwa kuka kawai take rusawa dakyal sukabar kauyen roni, suka hau motar jigawa,
Around 9pm suka shiga tasha babu kowa sai masu gadi wata rumfa dake chan gefe umma tajata suka tafi randar ruwan data gani a gefe ta bude tare da debo musu sukai alwala sallar magruba da isha sukayi suka cigaba da zama a gurin kowane da abunda yaje sakawa a zuciyarsa a haka sukaga safe, umma tace’ yanxu yah zamuyi gashi bamuda kowa ina zamuje sanin datayi umma batajin duk abunda zata fada hakan yasa tajawo hannun umma suka nufi inda taji wani kwandasta nata fadin Abuja! Abuja!!
Yana ganinsu yace” hajiya Abuja zakuje?
Eh chanxamu
Toku shiga yanxu motar zata tashi kushiga muje,
Babu bata lokaci motar ta cika suka wuce” sai a yanxu take ganin kamar tayi kuskuren cewa suje Abuja, to wama sukeda shi a abujan?

Doguwar tafiya sukai sannan suka isa garin Abuja inda kowa yasauka dole suma suka sauka, umma ce tace”taslima ga gurin siyarda abinci chan bari nasiyo mana, a’a umma muje tare to tace” tareda kama hannun taslimar da zummar su tsallaka titi.
Horn ake danna musu da karfi wanda ya gigita taslima ta fara kokaarin jawo hannun ummar ita kuwa umman inah! Batajin komai, ita kuwa datake jin horn din gashi bata gani basuyi aune ba motar tayi gaba dasu,

Da sauri matashiyar yarinyar ta fito wacce bazata wuce 16 years ba a rude ta nema taimakon mutane aka saka mata su a mota medical hospital ta nufa dasu aka karbesu emergency aka shiga dasu,
Duk wani abu daya kamata ayi tabiya akayi kiran mamanta taga yana shigowa wayanta da sauri ta daga tareda fadi”momma na akwai problem na kade wasu matane ina hanyar dawowa gida yanxu haka ina medical hospital.
Ayyah! Gani nan zuwa kijira ni”to saikin zo,

A lokacin da momma tazo yayi dai’dai da fitowar doctor dan haka office suka bias bayan ya zauna yake musu bayani,
Karku damu jikin nasu da sauki ita yarinyar ne sai zuwa gobe zata farfado, but dattijuwar kuma kanta ne yadan bugu but munmata dinki itama at any time zata iya farkawa, kuje gida kawai hajiya zansaka nurses su kulada su,
A’a doctor its not better’ momma kije gida ke nizan zauna nakwana dasu insha Allah tunda dama gobe weekend ne kinga bazanje school bad an haka kije, momma.
Ba musu tace” to dan haka ta wuce, bayanta koma gidane tasaka driver yakawo musu abinci da ruwan zafi,
Idonta biyu ko kadan babu alamar bacci a idonta umma ce ta fara farkawa da salati dasauri ta matso kusada umman tana mata sannu!
Cikin mamaki umma take kallonta domin jintana jin abunda take cewa ita kuwa sannu tacigaba dayiwa ummar tare da cewa”niceh na kade kuda mota sunana yusra dan ALLAH ku gafarce ni tsautsayi ne.

Ita kuwa umma farin cikin take da hamdalah domin jinta yadawo tanajin komai, dagama yusra kai tayi,
Tea ta hadawa umma mai kauri ta tayarda da ita tana bata ciki kulawa tsaf! Umma ta shanye tea din dan haka filet yusra ta dauka tareda zuba mata ferfesun kaza da dankali shima taci sosai sannan ta bata ruwa tasha, a haka suka kwana taslima kuwa sai safe ta farka, yusra c eta kira doctor bayan ya dubata yace” bawata matsala kuma babu abunda yasamu yaran dasuke a cikinta,

Lalube ta farayi tana kiran ummah! Da mamaki suke kallonta doctor yace” bata gani neh?
Eh umma tace”cikin kuka,
Da makantar aka haifeta ya tambaya?
A’a yau kwana biyu kenan da makancewar jefarta akayi a ido,
Yusra ta kalli doctor tace” doctor what is the solution now?

Daga kafada yayi yace”what do you went?

I went help her,
Ok go ahead ya fadi,
Kamar nawa kake ganin zasu isa ayi mata aiki?

Ehto tunda da wuri kike so ayimata zaki iya biyan dubu dari ukku da hamsin,


Ok so nake daga yau zuwa gobe kumata domin nanda ranar Monday nizan bar kasar nan abbana yana son inkuma Egypt da karatu kuma maybe this Monday zantafi dan haka inason ayi komai kafin intafi,

Ok,ya fadi tashi tayi tareda fadin zanje gida indawo zan dawo maka da kudinka kallon umma tayi tareda cewa” nixanje zandawo anjima za’a kawo muku breakfast yanxu Allah yakara sauki,”amin”


Bata wani jimaba ta dawo da kayan abinci bayan taje ta biya kudin aikin doctor yace”anjima da yamma zasuyi mata,


Da yamma aka shiga akayiwa taslima aikin ido doctor yace’ after 3days za’a cire mata, sosai umma kewa yusra godiya tace’ bakomai.

Ranar Monday tunda safe yusra tazo asibitin tayiwa su umma sallama ta wuce’ airport. Ta bawa doctor kudi kimanin dubu dari takwas tace’ ya basu,

Umma yasamu yabamawa tace” bawan Allah nayarda dakai kaje kasamar mana gida na daidai kudinmu nida yata muxauna bamuda kowa a Abuja, wallahi kataimake mu, nasan gidaje suna tsada a Abuja amma karufa mana asiri kamar yadda Allah yarufa maka, kallonta doctor yayi, sannan yace"to shikenan.


A ranar da aka cirewa taslima aikin idonta Umma tayi farin ciki sosai Wanda baya misaltuwa,
Doctor yasama Umma yai Mata bayanin ansamu gida amma Karami ne daki biyune ciki sai toilet da kitchen sai wani karamin shago a kofar gidan, yace idan anyi discharging dinsu zai kaisu.

Sosai Umma tayi farin ciki tare da godewa ubangiji, ta kuma godewa doctor sosai.
1week sukai a asibitin doctor ne ya daukesu yakaisu gidansu, Alhamdulillah domin yanxu taslima tana gani sai dai an yankar mata glass medical Wanda zata ringa sakawa idan zata shiga Rana,
A motarsa ya daukesu yakai su anguwar akwai mutane kowa harkar gaban sa yakeyi gwanin sha'awa parking yayi ya fito, sannan ya bude musu, key yasaka ya bude gidan karamin shagone a kofar gidan Wanda akwai kofa ta cikin gidan.
Dan karamin soro ke akwai tun daga zaure har tsakar gidan shafe yakeda siminti, tsakar gidan ma Karami ne, sai dakuna guda2 kowane yana dauke da kofa sai window, cikin dakunan kuwa duka tayils ne, bayin su a tsakar gidan yake shima shafe yakeda siminti gashida kyaure kuma a rufe yake,
Kitchen dinsu ma ansaka tayils a kasa sannan akwai kanta shima yana dauke da kyaure, gaskiya gidan ya burgesu godiya sukama doctor sosai domin sunsan gidan yafi karfin kudinsu, yadai siyar musu ne kawai.

A haka yai musu sallama ya tafi, zama taslima tayi a kasa taji sanyin tayils na ratsa ta tace" ummah! Mene ne abunyi?

Bangane abunyi be kamar ya?

Jakarta ta jawo Wanda take tara albashin ta a ciki ta zazzage duk yan dubu"dubu ne Masu yawan gaskiya domin bata taba kashe albashin ta,
Kirgawa tai kudin sun haura dubu dari hudu, dan haka ta dubi Umma tace" Umma Ina kudin kike Tarawa, irin Wanda antyna take bani Ina Kawo mini?
Gasu nan ta mika Mata wata Leda,
Umma tace" Ina tarasu ne idan kintashi aure inmiki kayan aure,
Dubawa tayi taga suna da yawa tace, Umma naga mun wuto wata kasuwa zanje inyo mana siyayya da kudin gurin ki, su kuma na wajena a ajiyesu bari inyi sauri zangane gurin bazan dade ba insha Allah.
Kallonta Umma tayi tareda fadin to saikin dawo, haka taja kafa da katon cikinta ta fita, ai kuwa tana fita taga wasu yara su ukku a kofar gidan maza biyu sai mace daya, gaisheta sukai ta amsa tare da tambayar su Dan Allah daga nan zuwa kasuwa babu nisa KO?

Eh macen tai saurin cewa tareda fadin" muje inraka ki,
OK nagode muje.
A kafa suka taka tafiya ta 10munites ta kaisu kasuwar inda babu abunda babu, a nanfa taslima ta fara siyan abubuwa komai saita ringaji da sauki ma, dariya yarinyar tayi tace" ai nan kasuwar komai sauki garesa shi yasa wasu kece Mata kasuwar yan'san banza.

Murmushi kawai taslima tayi" tukunyar girki ta sai musu guda ukku 3 sai murhu biyu, yarinyar tace' kinga risho nan mai biyu second new ne ki siya, ba musu tasiya, sai kasko na suya da ludayi nashan kunu Dana girki da spoons, filat'filat kwanoni duk dai wani abun amfani na talaka, tabarma tasai musu guda ukku manya 2 karama 1,

Yarinyar tajata sukaje gurin siyar da kayan kallo t.v tasiyo mai kyau da d.v.d duk second new itafa saukin kayan yafara bata tsoro kodai kayan sata ne, kettle na dafa ruwan zafi tasiya, sannan sai labulaye gaskiya ta kashe kudi sosai, sai katifu marassa yadi yan yanke manya ta yanko musu kudin data rage basu wuce dubu hamsin ba, buhun shinka tasiya sai taliya da masara, tayo cefanen abinci dai, yarinyar kuwa Mai shegen surutu ta nufi gurin gwanjo,,,,,,,lollz!

Dagawa ta dunga yi tana zabar t.shirt da rigada siket da dogayen riguna, tana wllh idan kika haihu wannan zasuyi miki kyau ki siya, kamota tayi tace' kinga zo muje inada kayan sawa ai.

Mota suka samu ta loda musu kayan har kofar gida yarinyar da kannenta suka dunga shiga da kayan cikin gida ko ummah tayi mamakin yawan kayan.
Bayan sungama ne taslima ta basu Dari biyar tace ita macen ta dauki Dari ukku sukuma tabasu dari'dari,
Godiya sukai sannan ta umarce su suje gida yamma tayi.

Ita dakanta ta shirya komai na gidan ta saka musu labulaye da katifu sannan tajera kayan kallo tasaka komai a inda yadace sannan ta nufi bayi ta dauro alwala tazo ta gabatar da sallah,
Zama tayi akan daddumar tana lazimi har akai isha'i tayi tacigaba da zama tana kai kukanta ga Allah, tana kallon Umma har lokacin da bacci yasace umman!

Allah sarki rayuwa dukkan su babu wanda ya nemi abinci a haka suka kwana,
Yarinyar nan makotan su ne sunanta saudat kannenta kuma murtala da Abdullahi mahaifiyar su tana da mutunci sosai duk sadda tagama abinci tana zubowa a kawo ma ummah kuma takan shigo su gaisa su kumayi fira.

ALLAH NE SHEDA 2
mrs"sweet dearling busby Salihu Bamalli on top
Xee"Abu"Safana

A bangaren tauhid kuwa bayan sungama wayada tauhida bacci ya kwashe sa washe gari around9 abbansa yakira sa yake fada masa yazo gida,
Lapiya ya tambaya abban yace" tauhid kasan ita rayuwa duk sonda kakewa mutum Allah yafika son bawan sa kuma dukkan mu bazamu dawwama a duniyar nan ba, sannan kasan na daga cikar ka musulmi kai imani da kaddara mai kyau KO sabanin haka, kuma komeh yadame ka cigaba da addu'a domin hadith ne ingantacce daga manzon Allah (s.a.w) yana fada mana addu'a'u huwal ibadah! Tauhid Ina mai baka hakuri Allah yayiwa tauhida rasuwa a Daren jiya.......!

Tsaye ya tashi cikin tsawa domin yama mance da mahaifin sa yake magana yace" whatttt!

Nasan kaji meh nace" Dan haka ka shirya kataho Nigeria,
Baisan sadda yasaki wayar yana dogon salati ba, jiyayi komai nasa ya tsaya masa da karfi yasaki kuka kamar wani karamin yaro sojojin dake gadin bakin kofar suka shigo domin suga mene ne?
Ganin ogan nasu yana kuka yasaka suka fara kallon juna cikeda mamaki da tsoro, bindiga ya dauka tareda sakin wani irin harbi asama Dan haka da sauri suka fita, shi kansa baisan halinda yake ciki ba, office din ogan shi ya nufa ya fada masa matarsa ta rasu yanaso yaje gida yanzu,

Kai tsaye ogan ya nuna rashin amincewar sa zai cigaba da magana tauhid yadaga masa hannu tareda ficewa baiko rufe kofar ba, jiri yaji yana kwasar sa dakyal yaje cikin gidansa yana kokarin shiga falo ya fadi!
Dasauri sojijin dake gadinsa suka sungume sa sai asibiti domin ceto rayuwar sa yashiga matsa nan cin hali harta kaiga ansaka masa oxygen sai da yayi kusan 2weeks a haka kafin yafara samun sauki watansa guda a hospital kafin ayi discharging nashi yana dawowa da kwana 2 ya shirya kayansa tsaf! Ya nufi office din ogansu gabaki daya ya bashi takarda yace" na'aje aikin soja har abada sir,

Yana fadin haka yakama gabansa sai airport dukda kiran da ogan yadinga masa amma inah zuviyar maza tayi zafi dan haka sai Nigeria saida yazo gida kuma damuwar tasake tasowa sabuwa da taimakon iyayen sa suka dunga rarrashin sa, but badai kagan sa yanxu yana fara'a ba kullum fuska a murtuke babu annuri ga rashin kuzari gashi baya zuwa ko'ina kullum yana gida, akullum tunanin tauhidar sa yakeyi yana kuma binta da addu'o'i.

Abba ne yasame sa yace" tauhid organ ku yakira ni yana bani hakuri in rarrasheka ka koma aiki domin kai mutum ne mai amfani a garesu.

Abba kace masa yayi hakuri bazan koma ba, ni nakeda amfani a gurin su amma ni yanxu rayuwata batamin wani amfani......

Tauhid Karna sakejin wannan kalmar a bakinka kaifa musulmi ne bai kamata ba ya kamata ka kiyaye harshen ka, kuma kasani zaman ka gida bashida amfani saima damuwa dazai kara dora maka Dan haka mungama magana dashi zaka koma aiki amma anan Nigeria sun kuma amince harsun gama komai zaka koma abuja da aiki insha Allahu kuma akwai yaron abokina yana nan zan hadaku mutum ne mai barkwan ci da iya zamada mutane sunan sa cpt.Adam Dan haka Kai hakuri end of this month zaka tafi abuja kacigaba da aiki.

A sanyaye yace"to Abba,
Yawwa Allah yai maka albarka"amin"

Bada son ransa ba ya tattara yakoma abuja anguwar dayake ta burgesa domin shi mutum ne mai son jama'a anguwar kuwa akwai mutane kuma akwai tsari da ban sha'awa ga makarantu boko da islamiya ga yawan massalatai, sannan daga nan gefe duk gidajen sojoji ne Wanda suke zagaye da babban get a takaice dai barrack ce sabuwa domin dayar wacce keda Dan nisa kadan gidajen sun cika shine aka musu wa'yannan kuma duk musulmai ne a cikin su, gidan sa jere da gidan cpt.adam a ranar dayaxo tun a ranar yagama fahimtar cpt.adam mutum ne mai barkwan ci da surutu, sai dare cpt.adam yashiga gida.
Tunda safe yaji Ana masa nocking a tunanin sa sojojin dake gadinsa ne wani dan yaro yagani wanda bazai wuce 9years ba ya gaishesa ya amsa, sannan yabashi bascket dinda ke dauke da breakfast yace'inji dadyn sa , dagani ya fahimci yaron adam ne Dan yaga Kama, godiya ya masa ya tafi yaron,

Satinsa daya da zuwa kullum cpt.adam suke Kawo masa breakfast sai kuma na dare domin na Rana yanaci a office,, cpt.adam ya matsa masa suje gidansa hardai rannan ya amince sukaje, a falo suka tarar da yar karamar yarinyar sa ta goye tanata kuka daukarta yayi tareda Fara kwalawa matar kira yana fada" fitowa tayi sanye da hijab tace" wallahi Ina sallah ne yi hakuri, ta fada tareda karbar yar'
Sai a lokacin ta lurada tauhid fara'a tasaki tana abban yasir wannan shine mejor" tauhid din?
Eh shine
Ayyah sannu zama tayi tareda gaishesa bayan sungama ta nufi kitchen ruwa ta Kawo masa da drinks with fruits, suna nan yaran cpt.adam suka dawo yasir da deen ita kuwa kitchen ta nufa haka suka sha fira bayanta kammala musu abinci, cpt.adam yafito ya taka masa harya shige gida yana kara fadawa cpt.adam yayi dacen mata gaskiya.
A haka sukaci gaba da rayuwa duk sadda yasama time yakanje gida yadubo su yadawo.

∆¶Π¶∆¶Π¶∆¶Π¶∆¶Π

Taslima kuwa ciki fa sai kara tsufa yakeyi mama(wato makociyar su mahaifiyar su saudat) tacewa"Umma yakamata ta Fara wata sana'a domin zaman a haka bazai yiwwu ba,
Dan haka Umma ta Fara dama koko da kosai da safe na siyarwa, Alhamdulillahi ana ciniki sosai taslima ke dama koko Umma ta soya kosai a cikin soron su suke siyarwa.

Sosai suka saki jiki suka cigaba da rayuwar su anan duk dare bayan magrub su saudat suna dauko littatafan suna islamiya suzo taslima ta biya musu, idan na boko ne kuma tana musu assignment da lesson.

Tunda watan haihuwar taslima yakama ita batama san haihuwar ce ba dama tauhida ce take kirga watannin cikin, ciwo ya isheta tafi sati a haka amma daurewa kawai takeyi, bata so Umma tagane hardai yau da abun yaci tura ta dunga nukurkuso Umma ta nemi taimakon maman saudat suka samu mota aka nufi asibiti da taslima lokacin harta fita hayya cinta, doctor ya fito da sauri ya nufosu yana fadin"
Munada bukatar Ku kawo kudi nanda awa daya zamuyi mata aiki yaran bazata iya haihuwar suba gashi daya harya koma Mata saitin zuciya Dan haka ku hanzarta Ku kawo dubu Dari da saba'in yanzu,
Dasauri ummah tadawo gida ta bude jakar taslima ta deba kudinta koma takai sai kuka take domin bataso tarasa tilon yarta.
Aiki aka shiga yimata da sauri umma kuwa alwala tayo ta tada sallar nafila tacigaba da jero addu'o'i.

Wajen 2hrs doctor yafito yana share gumi yace" congratulations anyi nasarar Ciro Mata yaranta biyu namiji da mace" kuma duk suna lapiya itada yaran, nurses suna gyara su idan sungama zasu kawo maku yaran ita kuma tana dakin Hutu!

Tun daga Umma har maman saudat hamdalah kawai sukewa ubangiji, ankawo masu yara manya kuma kyawa'wa kamar yaran larabawa, maman saudat tace" ikon Allah dukkan yaran babu mai kamada taslima to kodai sun biyo babansu ne,

Umma kuwa murmushin yake tayi tareda mayarda kwallan dake son zubo mata, tafiya maman saudat tayida yaran gida a inda ta musu wanka, sadda tadawo har taslima ta farka tasamu ta gyara jikinta,

Kullum maman saudat take musu hidima har saida taslima tai 1week suka sallame ta, ta koma gida sadda ta koma ta iske komai nata a dayan dakin maman saudat ta mayar Mata an gyara shi da dare kuma saudat kexuwa tayata kwana,

Ummah dake hawaye ta. dubi taslima tace" ki fadamin gaskiyar yaran nan waye ubansu kinga a baya ganin kinada ciki yasana daga miki kafa,
Saukowa tayi daga kan katifar ta duka tace" ummah na wallahi tallahi ban taba zina ba Umma wallahi cikin anty tauhida ne?
Cikin rashin fahimta ummar ta dubeta Dan haka tai mata bayanin komai, tadata Umma tayi tareda fadin" na yarda dake taslima nasan ki share hawayen ki Allah yasan taimako kikai kuma zai baki ladar zai

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment