Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mata da Maza yawanci duk sun zubo mata idanu. Ahankali tafurta Mamace tarasu? Jikintane yahau rawa. Baban su kuwa tak'ofar gaba suka shigar da ita falon Abbansu Usman da mutane da dama a falon wasu daga ciki sunci kuka Yusra yayar Usman tana ganinta takuma sa kuka. Jitai wasu nafad'in "Mutuwa mai yankan k'auna kinga matarsa da tsohon ciki, jitai cikinnata yawani hautsuna har tana naman durk'ushewa. "Agaban gawar Usman d'in aka ajeta. Kwance yake amik'e anmasa sutura nannad'e da Likafani ankuma yafa zani akai. Idanuwanta takai kan mutanen falon kowa taga yananan har Innarsu cikin jimami da taraddadi y Suke, to bataga Mijinnataba. Hannu takai tana shafar jikin zanin da aka lullu6e gawar Usman dashi "Kiyi Hak'uri Naja'atu *Kullu nafsin za'iqatul maut/ kowane rai seya d'and'ana zafin mutuwa*.kowana lokaci takan iya riskarmu to Allah daya fimu sanshi yakar6i abunsa. "USMAN NE NE KO BABA? Abinda ta iya fad'i kenan dayawa agurin sunji tausayinta. Dan bakasafai zakaji ta ambaci *Usman* d'inba. Gaba d'aya iyayen suka matso kusa da ita suna banbaki da nasiha "tayi hak'uri da tawalkali wataran kowa in lokacinsa yayi seya amsa kiran Ubangijinsa. Karki tumami dan *Annabi S.A.W yace "Basa tare damu, #Masu marin fuskokinsu, #Da masu yaga Aljihunansu, #Da masu D'aga murya suna kira irin Na Jahiliyya. Ayayinda akai Mutuwa. @bukhari da muslim ne suka rawaito.* "Kiyi masa addu'a zaitafi gidansa nagaskiya muma wataren mune haka" Inji Maman Usman tana dafo bayan Najar. "Allah yai masa rahama yakyautata namu zuwan" abinda ta iya furtawa kenan. Dukkansu sunaji suna gani musamman Naja'atu da jinta take kamar kara cikimma tanemeshi tarasa haka aka fita da Usman d'in akai mai Sallah suk tafi kaishi zuwa kushewa. Semuce Allah yajik'an Muslim Umma. Ameen.!! @Team naja'atu kuzo mujewa Naja ta'aziyya gsky #sharar hawaye!!! Β© *Didi_sady*πŸΌπŸ‰πŸ˜œ [2/18, 10:49 AM] β€ͺ+234 703 962 5239‬: β™‘ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*β™‘ *Na* *Haleema G Khaleel* *71-75* ""Tunda aka fita dashi ta d'ora idanuwanta kan k'ofar, gani take kamar a mafarki. Lallai Rayuwa batada tabbas, yanzu kake Mutum yanzu zaka iya zama Gawa. Shiyasa ake so kazamto mai aikata Alkairi arayuwa kazauna da mutane lafiya yadda kobayan ranka Kyakykyawar Shaida zata rik'a binka. *Hak'ik'a duk Mutumin daya manta Allah to tabbas yana tareda Shaid'an*. Allah Yai mana muwafak'a. Ameen. Haka tazama kamar Mutum Mutumi, tana kafe aguri d'aya kamar gunki. Motsi ma kasawa tayi bare Kukan dataga dayawan mutan gurin nayi, wani irin d'imuwa tasamu kanta aciki, bugun da zuciyarta tayi hasseda taji Motsin abunda ke cikinta, kuka takeso tayi kota samu raguwar Nauyin da K'irjinta. Cikin kwanakin Naja'atu tazama komai sede aimata ko magana bayinta tacikaba. Abinci se anyi kamar anayi zataci shima kad'an. Tabi tarafke tayi wani bak'i se k'atotan ciki dake jikinta. Damuwace sosai tattare da ita. Agidan su Usman d'in take kwana. D'akin Maman suke kwana itada k'anwar Maman Yaya Yusra da 'ya'yanta se autar Maman. Bacci ma sede 6arawo ya d'auketa duk tabi tad'ashe tazama wata iri da ita. Daren ranar da Usman yai kwana uku darasuwa, Naja tana kwance dare yatsala tunanin rayuwar ta take harta gangaro kan zamantakewarsu da Usman cikin Aminci, Yarda, K'auna, Kulawa da Soyayyar junansu. Lokaci d'aya Allah yad'aukeshi daga cikinsu badan baya sanshiba, tatuno yadda yake san cikin jikinta tunkafin tahaifo shi irin burin daya d'ora akan abin dayake cikinnata. Kuka tasaka mai tsuma zuciyar mai sauraro, tin tanayi a 6oye har shashshek'arta tafito fili, Yaya Yusra dabata jima da komawa bacci ba, taji alamun kukanta tashitai tareda kunna fitilar wayarta tahaska kan gadon , jijjigar dataga jikin Naja'atun nayine yatabbatar mata da ita keyin kukan, gadon tanufa itama kamar jira take tasa nata kukan har Mama tashigo d'akin ganin suna kuka zuciyarta tak'ara tsinkewa, bata hanasu kukanba musamman Naja'atu dasukeso tayi kota samu ragin damuwar datake ciki. Batasan sanda itama hawaye yakecemata ba har wani nabin wani. Maman tai dauriya tai shiru Yaya Yusran ma, ita kuwa Naja'atu seda tai mai isarta Mama tatasheta tareda jingina ta ajikin pillow Ruwa tabata tasha sannan suka hau lallashi da nasiha tareda bata Misalai iri-iri na Rayuwa itadai jinsu kawai take. Cikin kwana bakwai darasuwar, sunsha bak'i daga 6angare daban-daban dayawa kuma sun mata ta'aziyya. Har 'yan gidansu dukda irin zaman doya da manjan dasuke. Zuwa lokacin ta kuma rama ba kad'an ba. Zagayayyar fuskarta tayi fayau da ita. Danna Inna kullum saitayi mata tofi cikin zam-zam tanasha, Addu'oi dadama take mata banda wanda tabata takeyi. Taga kuwa fa'idar hakan dan damuwar datake ciki taragu sosai. Tafauwalawa Ubangiji duk lamuran rayuwarta shiyasan miyake nufi dayai mata haka. Bata kuma rikicewa ba seda aka kawo kayan Usman ranar dayacika kwana takwas darasuwa, taga abubuwansa dayawa komai yananan shid'in ne babu yatafi inda ba'a dawowa. Aranarma tasha kuka wanda har zazza6i yasaukar mata. Kwananta goma gidansu Usman d'in. Alh Abdul-Mu'iz mahaifin su Naja'atu dakansa yanemi takoma gida dukda anriga anzama d'aya nanma gidane. Ganin irin damuwar dake tattare da ita, bayan hakama komai sai anmata. Hakan yasa sukace "zasu tafi da ita gida. Mama kuwa sotai abarta agurinsu har ta haihu. Kayanta duka aka kaimata gida tasha kuka harsu 'yan gidanma haka tatafi tana ganin kamar rabuwa sukai. Itada zuwa kuma se ikon Rabba. Danma zuriyar data shiga tsakaninsu in Allah yaraya abinda zata haifa. Har sukaje gida bata k'ara cewa k'alaba, dasukaje gidan nema bayan anfito da ita daga motar wasu daga cikin 'yan Mazan gidan dasuka tarar a harabar gidan suka k'ara yimata ta'aziyya. Da hawaye tashiga gida. D'akin Innar aka gyara mata bayan gadon dake d'akin, k'atuwar katifa baban yasaimata aka samata daka gefe daduk sauran kayanta aka shirya mata, kwanciya tai tanata maida numfashi. Tafad'a duniyar tunani har bacci yai awon gaba da ita. Zamanta agidan tun bayan dawowarta bayabo ba fallasa. Duk abinda takeso dai-dai gwargwado tanasamu. Matan gidan sunanan da halinsu, danma bakasafai take fita ba daga zuwa Asibiti dashima tafi zuwa dadare, se d'an atisayen datake zagaya cikin gidan. Ahaka har cikinta yashiga wata tara. Haihuwa yau ko gobe. Inna duk tatanadi kayan jego da ake buk'ata gamai haihuwa tashirya. Hatta kayan mai jegon duk tashirya sejiran Allah yasauketa lafiya. Zuwa lokacin Usman yayi kwana Arba'in harda d'oriya da rasuwa. Sosai take kewarsa, danma Inna tayi namijin k'ok'ari wajen hanata zuzzurfar tunani. Data fara zatai tabata hak'uri da nasiha harta samu tasaki jikinta. Maman Usman ma tana
yawon zuwa dubata banda aiken datake mata. Haka itama Yaya Yusra tana tafe da abubuwan arzik'i duk dan ragewa Naja'atun damuwa da kewar babban rashin datayi. Afuwa makaranta ankusa k'arka'arewa da yardar Allah. Β© *Didi_Sady*πŸΌπŸ‰πŸ˜œ [2/18, 10:50 AM] β€ͺ+234 703 962 5239‬: β™‘ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*β™‘ *Na* *Haleema G Khaleel* *76-80* ""Tun suna saran haihuwarta har EDD haihuwar yazo yawuce, ba abinda kedaminta se kumburin dajikinta yake gawani haske da d'ashewa daduk jikinta yayi. Wata safiya suka nufi Asibiti da ita dan tun cikin dare take abu guda, dak'yar ta iya Sallah asuba. Dan itama Sallar azaune take tunda cikinta yatsufa. Abincin da Inna takawo mata taga bata bud'a komaiba. Tana kishingid'e sefitar da numfashi take da k'yar duk tahad'a gumi. Inna ta tallafota tareda jinginata ajikin garun d'akin "Inna Bayana ciwo" Naja tafad'a dak'yar. "Subhanallah! Badai abinne yazoba? Ina zuwa" Innar tafad'a tafita daka d'akin. D'akin Mama Luba Uwargida tashiga tasanar mata "ko zatazo takai Naja'atun Asibiti tunda itace babba agidan. Bud'ar bakin Mama Luba secatai "Ita gaskiya bazata iya futaba dan bak'i zatai, yanzuma zaman jiransu take suna hanya." Inna mai sauk'in kai takuma cewa "dama dan kada abin yazama laifi shiyasa tazo tagaya mata dan abata girmanta na babba agidan... bata idasa rufe bakiba Mama Luba tace "kinga dan Allah banasan hayaniya kinzo kin gayamin tunda nace bazaniba a hak'ura mana". Sum-sum Innar tafita tana Addu'ar Allah yanuna mata ranarda mutan gidan zasu shirya. To yadda sukai da Mama Luba haka sukai da d'aya matar gidan wato Goggo Safiya ita cewa tai ma "Unguwa zataje taje takaita mana su innasune wasuke nema yakai musu. Ranar Inna ranta ya6aci sosai, dandai kawai batada dangi agarin za'ana yimata haka. Samiha tanemo a waya, suka rufewasu Fawad d'akin insun dawo tunda kowa zai iyaima kansa komai dama Deedat takeji inyada yaga batanan. A Napep suka tafi Asibitin ko Alh bata sanarwaba. To duk zaman awannin dasukai Naja'atu bata haihuba aranar. K'arshema dawowa gida sukai wajen Maghriba da aka tabbatar musu da cewa "ba haihuwar ceba. Haka Naja taita fama saida taikwana biyar ahaka. Zuwan da Maman Usman tayine suka yanke amaidata Asibiti.kar aje asamu matsala da abincikin ko ita uwar. Da wannan shawarar sukai amfani. Motar da Maman tazo da ita suka kaira Asibitin. Basu nemi kowaba dan ita kanta Maman d'an zuwan datake gidan tafahimci irin zaman dasuke agidan. Dandai su Naja'atun da Mahaifiyarsu sun maida komai ba komaiba sam abin baya damunsu dan dole wataran zasu dena ko duniya tabasu darasi. Lallai hausawa sunyi gaskiya dasukace *"DUTSEN CIKIN RUWA..BAISAN ANA RANA BA"*. Asibitin Nagari Hospital & meternity sukaje dan tun dawowarta Kano nan take zuwa. Tun rana da aka kaita Asibitin Naja'atu take abu guda Nak'uda sosai take likitan dake Dutyn Ranar yana kanta har dare lokacin tashinsa yai. Zuwa daren duk k'arfinta yabi yak'are Mama sai mulmula mata bayanta take. Dr nafeesa datake dutyn daren tana zuwa lavour room d'in taga yadda Naja'atun tayi cikin yabi yarairaye yai k'asa iya galabaita tayi bata haihuba. Kayan aiki aka had'a mata da taimakon wash Nurses suka shirya Naja'atun Dr Nafeesan dakanta taturata zuwa ```Theater room``` Emergency C.S zatai mata takadda tabasu sukai singning akai ciki da ita. Inna Addu'a take ta mata. Suna zaune jugun-jugun. Jiran tsammani har goma da rabi na dare. Dr Nafeesa kuwa suna kan Naja'atu itada Dr Moses da sauran nurses. Baby boy akafara cirowa sannan aka ciro 'yan mata guda biyu d'ayardai andenneta sosai acikin. Yara kamar mahaifinsu duk aka gyaresu sede wadda aka ciro ta k'arshen ita sam batai kuka ba. Dr nafeesa da Dr Moses suka rik'o 'ya'yan tareda wata Nurses suka kawasu Inna yaran. Se farinciki Mama cema tai k'arfin halin cewa Ina Maman tasu bata gama maganarba aka turota akan gado zuwa d'akin hutu aka shigaddasu duka da ragowar kayanta. Yaran annad'esu a showel harsu uku, Maman Usman kuka tasa sosai da ganin yaran, yau ga jinin Usman alokacin da Usman yabar duniya. Batareda hayaniya ba sukaita d'aukan yaran sud'au wannan su ajiya sud'au wancan. Maman Usman kuwa ga hawaye ga dariya duk afuskarta. Waya tasa tana tai musu Hotuna jitake kamar tamaidasu ciki sekace yanzu akafara haifa mata Jikoki. Inna har tausayinta taji. Se wajajen shabiyu suka bar asibitin akabar Inna da Samiha. Cikin daren yaran sekuka suke mace d'aya da namijin, d'ayar ko motsawa batai ba. Zam-zam Inna tasa dabino aciki taita basu suna sha, se jijjigasu suke seda sukai bacci suma suka runtsa dukansu. Da Asbah bayan sun idar da Sallah Dr Nafeesa tashigo dubasu dan dawuri zata wuce. Anan Inna taimata complaining kan d'ayar babyn sam batai Kukaba ko motsi bataiba. D'agata Dr tayi tak'ara jijjigata amma shiru overall d'in Jikinta tayaye duka tad'an d'ala mata, nanma shiru, tak'ara jijjigata ba alamun numfashi tace "I think so dama itace ak'arshe kuma biyun sundanneta dakuma galabaitar da mahaifiyarsu tayi yataka muhimmiyar rawa. Batazo da rai ba." Atafi da ita gida abunne. Allah yaraya sauran yabada masu albarka. "Haihuwar farine ko? Dr Nafi tafad'a tana kallan Inna tareda mik'a mata Jaririyar. Tai musu sallama tatafi idan incharge na safe sunzo zasu duba Naja'atun may b kafunnan ta farfad'o. Karfe 7 nasafe Maman Usman tazo hae har Yaya Yusra, lokacin sukaita bugawa dangi nakusa dana nesa waya. Suna sanar musu da haihuwar. Mik'o mata Matacciyar Jaririyar Inna tayi tace "wannan bata da rai kutafi da ita gida a bunneta". Allah sarki Mama tace "Allaj yai bame shan wuyar duniya bace." Can Sharad'an suka tafi da ita aka binneta inda aka kai mahaifinsu. Lokacin dasuka dawo har Alh dasu Sadiq a sannan Naja'atu ta farfad'o. Likitan daya karb'i dutyn safen shiyazo dubata yace "kar abari tai jijjinan motsi sosai, espcly kafarta sannan subata ruwa ko abinci mai ruwa-ruwa, banda abu mai k'ayau. Yafaffad'a musu duk irin abubuwan daza ai mata dawanda bazataiba. Dataimakon wata Nurse tai brush, aka bata shayi sannan suka gyarata. 'Ya'yan data haifa aka ajiye mata kusada ita sunsha wanka sai k'amshin turaren jarirai suke. Tana daka kwance 'ya'yan duk agabanta, kallansu taitayi cike da k'auna, wata soyayyar yaran taji tanabin kafofi da jinin jikinta. "Kamarsu d'aya dashi ko Yaya Yusra? Naja tace da Muryatta dabata gama warwarewaba, k'wallace tabiyo bayan maganar tata, itama Yaya Yusran sun bata tausayi sosai taji itama kamar tasa kukan, dandai kadata k'ara bata k'arfin gwiwar yin kukan yasata danne zuciyarta. Anan suka sanarmata uku tahaifa sedai d'ayar batazo da raiba. Zaro idanu tayi tace "duk acikina, lallai Iyayenmu sunsha d'awainiya damu. Kuma dole miyi Biyayya agaresu tahanyar dabata sa6awa mahalicci ba muddin munaso mu wanye lafiya a duniya. Alllah yasaka musu da d'umbin Alkairu yabiyasu da babban rabo. Allah yak'ara bamu ikon cigaba da faranta musu dayi musu biyayya bisa turbar Islama. Itakuma Allah yamata rahma yakyautata namu k'arshen. Duk mutan d'akin suka amsa da Ameen. Kwanansu biyar a Asibitin mai jego tawarware sosai, har tana shayarda yaran. Namijin mai hak'uri, macen kuwa rikici gareta. Danna Inna da Samiha basu gajiya da d'awainiya dasu ko kuka suke tana bacci ba kasafai suka fiya tashintaba. Inna takance "batta tai bacci tad'an samu hutu, ita kada'i tasan gumurzun datasha daga rainnan ciki har haihuwarsu." Dukda dai kowace mace da kalan nata abubuwan. Β© *Didi_Sady*πŸΌπŸ‰πŸ˜œ [2/18, 10:50 AM] β€ͺ+234 703 962 5239‬: β™‘ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*β™‘ *Na* *Haleema G Khaleel* *81-85* _Afuwa Makaranta wannan labari. Bajan rai bane kunsan d'an adam ajizi ne. Abubua sunyi yawa. Kwana biyu kuma banida lpy. Ga bukukuwa da aketayi a fam. In sha Allah before Jan 2017, zan kammala. Nagode da k'aunarku gareni aduk inda kuke._ ~~~Aran kwana bakwai da haihuwar aka sallamesu da rana. Duk wani kud'i da aka kashe tun farkon zuwansu Asibitin Baban Usman ne yabiya, dan cewa yai "Haryanzu da nauyinta akansu, dan haka duk abinda ake buk'ata yace "Agayamasa" Mama kuwa suka 6alle bakin aljihu akai komai cikin mutunci da girmamawa. Bare dasukaga anhaifar musu Tagwaye. Kayan barka sosai suka siya ranar dasuka koma aka bisu da tukwici dak'yar suka kar6a. Acewarsu "Ai yiwa kaine anriga anzama d'aya. Ranar suna kuwa bawani taro akai ba. Rad'in suna akai aka sawa Namijin sunan Usman itakuma macen aka samata Asma'ul Husna. Samiha tasa musu Hassan da Husna. 'Yan barka sukai tazuwa 'yan uwa da abokan arzik'i. Kayan barka iri-iri suka samu, wasuma sa shekara suna amfani dashi. Mejego tayi k'alau da ita. Dan jego mai kyau ake mata har sukai wata biyu. Yaran sunyi 6ul-6ul dasu, kamarsu da mahaifinsu se dad'a baiyana take. Ita kanta Naja'atun kamar ba ita ta haifesu ba, dan gyara sosai Inna da taimakon k'anwarta Aunty Husna sukai mata. Irin zugudan nan dayawan masu ciki keyi bayan haihuwa, basu bari tayiba. Tayi k'alau da ita. Sedai idan takalli yaran nata takanji tausayinsu natashi dazasi basuda mahaifi. Tak'udurce aranta bazata ta6a bari siyi Maraiciba. Duk yadda zatai takare Mutuncinsu zatai wanda bai kaucewa shari'a ba. Kuma ga kakannunsu da dangin mahaifinsu dasuke sansu da ji da k'aunarsu. *BAYAN SHEKARA HUD'U* Hangota nai cikin _Nagarta Shoping Complex_ d'auke da basket a hannunta. Deedat nagani yak'ara girma rik'e da hannun wasu yara masu kyau dabazasufi shekara uku da rabi ba. Mace da Namiji, kalan kayansu iri d'aya, sedai Bambanci na Mace da Namiji. Macen anmata kalba datasha Bead se reto suke ajikinta. Tsayawa tai wurin kayan k'amshin gida tanata duba irin wanda takeso. Domin ita ma'abociyar k'amshi tundaka najiki zuwa na d'aki hakama kyawawan 'yan biyun 'ya'yanta Hassan sa Husna. Naja'atu kenan matashiyar Bazawara, datun bayan rasuwar Mijinta bata sakeyin wani auren ba. Asalima catai ita tagama, seda mahaifanta suka tsaya tsayin daka da Addu'a da rok'on Allah tasaki ranta tadawo da walwalarta daduk wata mu'amala harta koma Makaranta da D.E daga level2 tafara har take shekarar k'arshe a course in ```Nursing and Nursing science```. Jitake
zata iya Aure ayanzu, kowaye yazo muddin yanada d'abi'a da mu'amala ta k'warai, kuma yakwanta mata tayi Na'am dashi da wanna tasamu tarufe bakin Iyayen nata. Ganin ana shirye-shiryen Auren Samiha da sauran k'annanta Mata, amma ita shiru. K'wace hannunsa Hassan yayi, daga hannun Deedat ganin Husna tayi gurin toys dandama tafishi wayo. Da gudunta nayara tayi gurin toys tagano 'yar tsana, Bangazar mutumin dataine yasata tsayawa. (Sanadi😻) Agogon daya d'aukane samfurin ```Dior``` yafad'i daka hannunsa har saida Glass in ya tsage. "Ya salam! Ya furta da _Husky voice_ insa mai amo. Irin yawan dayasha yana neman ```Wrist watch``` in besamuba se anan gashi yanzu kuma abinda yafaru ko biyan kud'inshi baiyiba, cikin jin haushi da takaici afuskarsa yad'ago zai mata masifar wata irin matace dabata tafiya a hankali? Tajamai wannan d'anyen aikin. Batasan irin wuyar dayasha yana abu guda naneman brand na Agogonba. 'Yar k'aramar yarinya kyakyawa idanuwansa sukai tozali dasu. Husna kam ganin yasha mur bashiri takama kunnuwanta tai kalar tausayi tace "Am sory Uncle" ai saurayin besan sanda ya murmusaba yaji yarinyar ta burgeshi sosai. Inama 'yar sace, tunano yadda Mahaifiyarsa babu abinda takeso irin yayi Aure, har matakaiga samun zuri'a. Shafa kanta yai yace mata "Be careful kinji Babyta next time kirik'a tafiya a nutse karkije kima wani irin tawa yadakeki, bama haka ba kada kiji ciwo kinji." D'aga kanta tayi alamun taji tace "Thank you Uncle" Matashin saurayin yace "Oya give me five" yabata hannunsa suka tafa sunata dariya. Hassan ganin ba a daki Husna ba, sunata dariya, shima yataho yana dariya dabaisan akan me ake ba. Da mamaki afuskarsa yake kallansu duka. Mik'amai hannu Hassan yayi da nufin su gaisa. Saurayin kuwa yakama d'an hannun Hassan suka gaisa. Tsugunawa yai dai-dai tsayinsu yace "U are identical 2wins?" Saboda tsananin kamanninsu yayi yawa. Yakuma fad'in "Am i right?" Yana cigaba da kallansu. Husna da surutu takuwa hau zuboshi "Mamynmu tace mu Triplet ne amma d'ayar tamutu ita bamugantaba. Dariya yahauyi sosai daya jima baiyi irin taba. Yace "Shikenan nikam nayi new friends yau, amma bansan sunankuba." Husna takuma cafe maganar tace "Mu 2wins in Mamynmune yanzu amma sunannu ni tanuna kanta sunana Husna Usman Bello Galadima, shukuma Hassan sunanshi Usman Usmab Bello Galadima, sunan Babanmu aka samai shine ake cemasa Hassan. Amma har yanzu Abban bai dawoba Mamy tace "Yayi tafiya inda ba a dawowa. Shiyasa bayanan. Kuma mu kullum baya d'aukomu a school, sukuwa su Farouk Abbansune yake zuwa d'aukansu." Tafad'a tareda kama hannun Hassan. Shima yace "Se Mamynmu ko Uncle." Sunbashi tausayi sosai, yafahimci komai wato Mahaifinsu yarasu basuda wayo ko ba a haifesuba. Kama hannayensu yai duka yace "Tare dawa kukazo gurin nan? Hassan yace "Da Mamy da Ya Deedat. Batasan munzo nanba dan tace mudena surutu inba Alkairi mutum zai fad'a ba yai shiru. Har Rok'o dayawoma tace. Ana sace mutum inyaje yawo inda baisaniba yadena ganin kowa har Mamanshi." Ko Husn Yafad'a yana kallan Husna. Surutun kuwa sukai tamasa yanata record dan sun birgeshi. hadda tambayarsu to in aka saceku yazakuyi. Zaro ido sukai suduka. Husna datafi wayo tace "semu kira Mamynmu awaya ko Uncle Isma'il da Ibrahim." Yace "To tayaya zaku kira?" Digit tahau fad'omasa yanata mamaki. Jiyai sunkuma shiga ransa, kamar yatafi dasu tunda duk yaji details insu har Adress in gidansu dana kakanninsu. Suka gayamai yaran masu d'ankaren surutu kamar sunci Kabarai. Ga wayo. Kuma ai shima 'ya'yansane. Tunda hausawa sunce *D'a nakowane* Tinanin dayai idan yatafi dasu Mahaifiyarsu yazatai dan ko ina take bazataji dad'i ba. Toma haka ake daka ganin Sarkin Fawa sai Miya tai zak'i Koshi bazaiso amai haka ba. Dankuwa sai inda k'arfinsa yak'are. Yace musu "Shi sunansa Uncle mai zane, daga yanzu yazama Uncle insu shima. Sukuma sun zama Friend d'insa. Suka tafa dukansu. Sunata mumma, yama manta da batun Agogonsa. Zagaye sukai tayi, yasai musu toys da chocolate, wafer,biscuit dayawa. Aikam yasha godiya gurinsu. Sukaje aka biya kud'in. Har waje yarakosu, kaya taganosu dasu nik'i-nik'i. Ita Husna ma jan kayan take. Nemansu take tayi har suka futo zasu shiga mota. Cogewa tai tana kallansu se muzurai suke. Β© *Aneesa_Didi*πŸΌπŸ‰πŸ˜œ [2/18, 10:50 AM] β€ͺ+234 703 962 5239‬: *β™‘DUTSEN CIKIN RUWA.....β™‘* *Na* *Haleema G Khaleel* *86-90* ~~~Yaran sunsan in Mamyn tasu tai shiru, tana kallansu sunyi laifi kenan. Tun basu fahimtaba, har suka gane me shirunta kenufi, dukansu suka saki kayan hannunsu suka kama kunnuwa atare sukace "Afuwa Mamy" ganin tayi shiru batace komaiba suka k'ara langa6ar dakai, kalar tausayi sukai sosai. Shigewa mota tai kamar zatatafi basu, da gudunsu suka taho har Hassan yakusa kifewa, "kayanfa wakuka barwa" Mamyn tasu tace, tana kuma kallansu, tasha mur. Suma d'if sukayi suka sunkuyar dakai. Bud'e motar tai atsawace tace "Kushige mutafi, zakusan kunje yawo daga zuwa daku harda rok'o, punishment zaku kwana kunayi, Abincima bazakucuba tunda bakujin magana. Ai bata k'arasa maganganunta ba suka shige motar dasauri suna kuka dukansu jin hukuncin daza amusu. Duk abinda yafaru yanadaka gurin k'ofar shiga _Complex_ in yana hangosu,"dukda baiga fuskartaba, hakan datai musu yanuna tanasan sukasance cikin tarbiya, ba kwad'ayi dasan abin duniya ba. Kayan dayasimusu suka bari, yazo yad'ibesu amotarshi yasa, yabar gurin shima ko siyayyar dayazoyi baiyiba. Direct gida yawuce. Mahaifiyarsu dasuke kira da Umma, tana zaune littafin *Garkuwar Musulmi* ne a hannunta tana dubawa, da Sallama yashiga falon. Ganinshi tai d'auke da kaya. "Sannu da gida Umma" yace tareda zama. Ummantasa tadubeshi da kulawa tace "Harka dawo ashema ba jimawa zakaiba, afitarba?" Ajiyar zuciya yasauke yace "Ah Umma d'an akasi akasamu a inda naje. Anan yakwashe komai yagayamata, dan itace abokiyar shawararsa tun yana k'arami, shi ko yawan abokanai bashida su. Ummansa itace kominsa, har _recording_in surutun di Hassan da Husna yakunna mata taji, na dariya tayi na tausayi ta jimanta, yad'ora dacewa "Shifa gaskiya seya bisu yakai musu kayan" yashige d'akinsa. Umman tasu tabishi da kallo aranta tana Addu'ar Allah yabashi mata tagari dazata kuladashi. Shima yai Auren koya dad'a samun nutsuwa arayuwarsa. Arc Sulaiman Tajuddin Kazaure shine sunansa. Mahaifinsa Alh Tajuddin Hafiz Kaxaure da mahaifiyarsu Hajiya Maryama. Asalinsu 'yan jihar Jigawane, Aurensu tunna Saurayi da Budurwa, Allah ya albarkacesu da 'ya'ya Hudu duk Maza, Muhammad Kabir shine Babba Barister ne mai zaman kansa, suna zaune a Abuja tareda Matarsa Farha da 'yayansu uku. K'aninsa Tasi'u shima da iyalansa su suna zaune a Kazauren inda yake aiki. Mebimsa Yusuf dabai dad'e da Aureba yatafi da Amaryarsa can Bony a Phorthacoat inda yasamu Aiki. K'araminsu shine Sulaiman matashi dabai haura shekara 30 ba, Archtecturing yakaranta a Jami'ar ```Kano University of Science and Technology dake Wudil ```A Kano . Zane zane da Allah yabashi baiwa da fasaha akan haka, Taswirar Gidaje da Ma'aikatu har mutane ma, yamaida kai sosai akan harkar tasa. Allah kuwa yasamai Nasibi acikinta. Hayarsa ake d'auka gari-gari wani sa'in har wasu K'asashe . K'ark'ashin kamfaninsu mai suna _"The Shariff Construction"_. Suna zaune a D'an Agundi G.R.A, dake Zoo road, sakamakon Aiki dayada da Mahaifinsu Ma'aikatar Ruwa ta Hadeja-Jam'are, reshen jihar Kano. Hajiya Maryama mace ce mai tsafta, kawaici dasanin yakamata, uwa uba rik'o da Addini. Ga zumincin 'yan uwa nakusa dana nesa, duk ta d'ora 'ya'yanta akan turbar hakan. Allah baibata haihuwa dayawaba, shiyasa takeso Sulaimanu in yai Aure yazauma kusa da ita. Kota rik'a ganin 'yan kufi-kufi akusada ita. Duk sauran 'ya'yannata da iyalansu sunmata nisa. Wannan kenan. Naja'atu dasuka koma gida ko kayan data siyo bata idasa ajewaba, takamo 'yan biyun nata Hassan da Husna "Kneel down & close your eyes" tace tana zare idanu. Bashiri sukayi atsorace bawanda yace uffan. Harta gama jera kayayyakin, ta adana komai inda yadace. Abinci tazubo dantaci, kasa cin abincin tai, dan tasaba yanzu tare dasu takecin Abincin. Abunka da Uwa da d'a tausayinsu yatasomata, janyosu tai duka tarungumesu tsam ajikinta kamar za'a k'wace matasu. Hak'uri suka bawa Mamyn tasu, taja musu warning sosai, suka fara cin Abincinsu cikeda ladabi dan duk takoyar dasu Ladubban ci dasha:- *Kaci da hannun dama* *kaci da Bismillah* *kaci Abinda ke gabanka* *kada kai Numfashi acikin kofi/k'waryar ruwan* *kada kashafi band'aki da hannunka* Ire irensu da neman yafiya yayinda kaima mutum badedaiba. Duk takoyardasu. Bayan sungama cin Abincin, aka hau labarai

Please Login or Register in order to submit comment