Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

so kike nashigo cikin gidanba, kinsan nine d'angidan kekuwa haya kike. "K'yalk'yalewa tai da daria " kai ya Usee" tunda cikin raha take yasata fad'in haka, "Baki yaddaba kenan to natafi, dama Mama tanatamin tsiya, nazo kuma kinmin haka Nagode. "Laaah! Afuwa DanAllah, Ina zuwa takashe wayan. Tareda mik'ewa. Band'aki tai saurin fad'awa, Inna ko tahau fad'in, " Badai wanka zakiba, mutum yayo tattaki yazo amma sekin 6atamasa lokaci. Murmushi yai tareda shafa kwantaccen gashin bakinsa. Yasamu Bench daka gefe yazauna, kamin tafito. Afuwa plss makaranta, Kutaya mu addua plss Allah yabama Uncle lafiya.!!! ยฉ *Aneesa_Didi*๐Ÿผ๐Ÿ‰๐Ÿ˜œ [2/18, 10:48 AM] โ€ช+234 703 962 5239โ€ฌ: {21/11, 2:00PM, Didi} โ™ก *DUTSEN CIKIN RUWA* โ™ก *Na* *Haleema G Khaleel* *37-38* Da hanzarinta tafito daka toilet in, fuskarta fayau Hijabi kawai tasa tafita. Tun kafin ta k'araso murmushinsa yake mata maraba, ganin yayunta sun shigo gidan kunya kaman k'asa tabud'e tashige. "Tasowa Usman yayi sukai Musaba ha da yayunnata. Itama tagaidasu tawuce. "Nesa dashi tazauna bayan taimasa sallama. "Ai nazata bazaki futo ba, yace. "Hmm to ai kaine nasan ko zolayata kakiyi. "Au hakane ma abun? To yahak'uri ai gani. Fatan kazo lafiya? "Lafia lau, Queen, nasameku lafiya, yasu Innata dakowa na family? "Alhamdulillah kowa sunane lafiya ya,mutan gida? Ina yaya Yusra? "Kowa lpy tunda kika ganni, Ah tace mun kuna waya ai. Amma kink'ki yadda ku gaisa da Mama, gashi ita Sis Yusy har waya kukeyi. "Sunkuyi dakai tayi tana wasa da abun Hijab inta. K'arfin hali kawai tai tace "to zangaidata amma ba yanzuba, nasan yanxu saika kirata" Kede wannan kunyar naki keda zaki zama matar d'anta inhmm! "Hmm! To ai *kunya adon 'ya mace* (littafin My Feedo-Deedo). Hakane kinyi gaskiya shiyasa kike k'ara shiga raina Najata. "Harma nazama takan? Tafad'a tana karamar dariya. "Dariya ma kike to ai kinkusa zama, yad'an sha mur tareda fad'in "Naja'atu yau nazo da magana, dukda nasan anrigada anyi abaya, amma yanzun za akuma jaddadata. "Ganin datai yadan sha mur seta tattara duk nutsuwatta tana sauraransa, tinda taji ya ambaci sunanta tasan muhimmin abu zai fad'a. "Naja'atu yakira sunanta akaro na biyu, AURE nakeso, kinga niba yaro bane, lokaci yayi tinda nakusa kammala komai gameda karatuna course in da aka turamuma miyi saura wata uku mugama. To sonake dana dawo lokacin ayi Auran, koya kikace? "Nannauyan numfashi taja, tace "wannan maganar ai ba a hannuna takeba. Wurin manyana zaka, su zasusan abinyi. "Nasan da haka ai, amincewarki kawai nake nema. Inkin yarda sai ak'arasa magana. Ad'aura aure kinzama tawa. "Kasa cemasa komai tayi ta duk'ar da kanta tareda cewa "Allah yatabbatar da alkairy yashige gaba. Amma kuma. Ameen. Amma kuma me? Kifada kinji bazan cutarda keba kome kikeso ki fad'a kunyarnan arik'a rage ta kaman ba mijinkiba yace yana darawa. "Bawani abu bane, cigaba da karatuna kawai dama zance. Indai dan wannanne karki damu, karatu sekince ya isheki, keda zaki aure likitan mata, kinga sekina tayani nima ko nadubaki kidubani, batare da wani yagane miki miji ko angane min mata ba. "Dariyar da take 6oyewa saida tafito fili, wayarshi yazaro yashiga d'aukanta a hoto, bak'aramin kyau tamaiba jiyai kamar yajawota k'irjinsa koya samu sassaucin da azazzalar da zuciyarsa keyi akanta. Yai k'ura mata ido yana kallan kyakykyawar zagayayyar fuskarta. Komai kamar ita ta za6awa kanta. Ganin abin nasa nayau yasa tace masa inyaje gida yagaida su Mama da K'annanta. "Kawai dai kice korata kike, kingaji dani be ida rufe bakiba sega su Fawad sundawo daka Islamiyya, Salim da gudunsa yazo hannu yabashi suka gaisa, sauranma duk suka gaidashi suka wuce gida. "Aranta taji dad'in dawowarsu, koba komai yanzu zetafi dan yau ta fuskanci da zolaya yazo mata. Shima Usman ganin dawowarsu yatabbatar mai da lokaci yaja. Badan yasoba yai mata sallama, had'e da mik'a mata k'aramin buhun bagco daukeda Plantain, Kwakwan-manja, Kwakwa da Agushi. Mamaki tai tayi tace Haba danAllah kai kana Student hadda wani tsaraba, kaida za abama amma kaine mai kawowa? Cikin shagwa6ar data zamemata jiki hadda turo dan bakinta.(Maryam Speaker๐Ÿ˜œ) Usman kuwa galala yai yana kallanta, bak'i su dauwama a hakaba. Lallai Allah yasoshi daya had'ashi da kalan matar dayakeso, wadda komi tahad'a, "Sokike mukwana anan naga Alama,? Danai me kajika tace, toshikenan zanwa Mama waya nace 'Yarta ta rik'eni. "Nidai baruwana ban rik'eba, angode wannan kayan dukmu kad'ai. Allah yasaka da alkairi. kiran sallar magriba dole yasa sukai sallama, yana mai jaddada mata da kadata kashe wayanta. "Murmushi kawai tamasa tashige gida shima yatafi. "To bayan Sallar magriba sannan taiwa Inna bayanin kayan takarkasa tabawa kowa nasa, gudun k'ananun magana irin ta mutan gidan. Afuwa plss makaranta. ยฉ *Aneesa_Didi*๐Ÿผ๐Ÿ‰๐Ÿ˜œ [2/18, 10:48 AM] โ€ช+234 703 962 5239โ€ฌ: [24/11/16, 6:22PM] Didin Anee๐Ÿ˜ โ™ก *DUTSEN CIKIN RUWA.....*โ™ก *Na* *Haleema G Khaleel* *39-40* Cikin watannin da suka biyo baya Soyayya sike kaman yacinyeta yakeji, dama ita kunyarsa datake matuk'ar ji yake hanata maida masa da martanin irin zafafan kalaman dayake gaya mata. Saranar biki akai nanda sati shida. "Cin lokacin duk tabi tarame ga ciwan Inna yatashi jikin ya matsa mata, hakan yak'ara sanyayarwa da Naja'atu jiki. "Duk dare kafin su kwanta bacci se Innar tai amfani da wanna damar taita musu nasiha gameda rayuwa. Tak'ara had'awa da bata makamai na addu'a yadda zata bi da arun dazasu taimaketa a sabuwar rayuwar dazata shiga. "Ba abinda takeyi se kuka dazarar Innar tafara, gani take kaman wasiyya Innar take basu. "To ganin Innar tafara warwarewa yasa hankalin Naja'atu kwantawa tad'an fara walwala har take samun damar karanta wasu daka cikin littattafan da Innar tabata: *ZINAREN MA'AURATA*(MY ANEE๐Ÿ˜) *WASIYYATUL-UMMI* *ZAMANTAKEWAR MA'AURATA*(DIDIN-ANEE) Dawasu sauran littattafai dasuka shafi Rayuwar Aure da Tarbiyar Yara a Musulunci. Uwa tagari kenan. "Gyaran jiki da akema Amarya kuwa Innar ce da kanta take mata tun tana jin nauyi har tasaki jiki take gyara 'yarta duk abinda yadace takemata. Ana cikin turareta da Dukhan Usman yabugo mata waya, gata a lullu6e badaman d'aga wayan, dole samiha ta d'aga tasa mata a kunne, wata sassanyar dariya tasaki, meya gaya mata tace "nide baruwana a shagwa6ance, tama manta da Inna tana gurin, "mezan fad'ama to? Usman yace kina ina yanzu? "Ina gida Allah yasa lafiya? Naja'atu tafadi. "Yace to mekikeyi, kinmaci abinci kuwa? "Naci mana mikagan? "Nikam kinganni dangatan Mamata gyara miki ni take tayi. Tahad'an wani abu mai dad'i konazo nakamaki? "La la! nids banceba baruwana. Hhhhhh "Kinji ai ke kita kunya abundama kinkusa zama tawa, itadai shiru tamai yanatayi. Da abun ya ishetane tace ana kiranta. Bawani kiranki da ake zaki kashen waya dai? Usman yafad'a yana murmushi abinsa. Kinga nama san komi ai da akeyi inma kin 6oyen. Sema na fad'o miki basu ....... "Ai bata yadda yakai k'arshen zancenba takashe wayan tanata murmusawa. Inna kuwa tabita da kallo tana me addu'ar Allah yasa Farincikinsu yad'ore a zaman dazasiyi. Sunkuyar da kanta tayi ganin
irin kallon da Innar kebinta dashi. "Hada-hadar biki ta kankama, danma Amaryar tace it ba bidi'ar daza ai. Komi bisa tafarki za ayishi. Ana saura kwana uku afara biki dangi na nesa suka fara zuwa mutan getso da Gusauma ba abarsu abayaba. Anty husna itada Ummi farin zuwa, suka cigaba da shirye,shiryen biki. Ita dai Amarya duk tak'ara sanyayewa abincima se Inna ta matsa mata takeci, setakoma dama Kunun Alkama da Madara. Dukdan kada tai rama dayawa. Bayan daffaffiyar Madarar shanu safe da yamma, tun bata iya shanyewa harta hak'ura shiyasa jikinta yai lumi, fatarta tak'ara santsi da taushi. Se shek'i take irin na Amaren da suka sha gyara. "Ana i jibi d'aurin auren laraba dasassafe suka tafi k'unshi k'awatenta biyu Sady da Hafsa dan Nafisa a lokacin tayi nauyi. Juwairiyya Samiha harda Anty Husna suka tafi. Sun babbaje anata hira agidan lallen itakuwa seda taga anfara mata Jan lalle jikinta yakuma mutuwa ya tabbata takusa barin Inna da 'yan k'annanta jita hawaye masu d'umi sunabin kuncinta. Ganin haka itama Samiha tafara hawayen, Anty Husna kuwa mezatai inba dariyaba. Tahau yimada fad'an ai Aure shine DARAJAR MACE. Kumashi Katangane babu wani mahaluk'i dazai kamiki wargi matuk'ar girman nan ya hauki, Rigar mutunci tamiki lullu6i duk inda kika samu kanki za abaki girma da MARTABARKI(Ummi-Aishha) ta D'IYA MACE(Khadija Sidi). Taita mata ita kuwa tak'ara rushewa da kuka. Sauran kuwa sukai ta tsokanarta. " ```Ke kikacw kinaso Amarya dabaki so da ba abaki shiba``` sukaitayi suna dariya. "Meyi mata k'unshi kuwa dakatawa tai, tanata ganin ikon Allah. Wannan shagwa6a ta Amarya har ina.lalla6ata sukai tai shiru akagama mata lallen sannan suma akayiyyi musu. "Bayan la'asar suka dawo mutane dayawa sun zazzo anata aikace-aikace, shigowarsu tasa aka kaure da hayaniya masu gud'a nayi abokanan wasanta suna tsokananta, kowa da abinda zaice aikuwa meneman kuka anjefishi da kashin awaki(inji hausawa) aikuwa tasa kuka. Seda wata k'anwar Babansu tazo tajanyeta, suka k'yeleta. "Alhamis akaimata kamu irin na Al'ada, dayamma kuwa Walima akashirya Matan aure zallah se Ango da abokanansa. Kuzo kutayani ganin Amarya cikin shiga ta alfarma wata had'dd'iyar gown ce ajikinta gold colour da veil inta and'ora shi akan Top Knot inda akaimata jikinta rufe ruff light make-up aka mata ba k'aramin kyau taiba. Malam Auwal Muhamnad da Malam Nazifi sunyi fad'akarwa sosai akan Aure. Da matakan daza subi subi su mallake junansu. Ba Boka ba Malam musamman ga ita Amarya da sauran mata. Walima cikim tsari ba hayaniya akai lectures sosai kan Addini. Kafin magriba akai addu'o i da neman Albarka acikin Auren. Akatashi itade Amarya Murmushi kawai take. Sunda gida taga se had'a mata kayanta ake jikinta yak'ara mutuwa kamar anzare mata laka. Ranar jumu'a Takama 24 ga watan 10 dubban jama'a suka shaida d'aurin Auren *USMAN BELLO GALADIMA* da Matarshi *NAJA'ATU ABDUL-MU'IZ AUWAL* bayan Sallar Jumu'a bisa rangwamen sadaki. "Yinin biki aka zarce dayi bayan angwaye sunzo gaisuwar dangi akayiyyi hotuna. Amarya masha Allah kamar kasace ka gudu. Nikaina Didi ba k'aramin burgeni Amarya dashi kansa bikin yaiba. Lek'e nake tayi chan na hango su Haleema da Maman Ansar ansha anko. Sukuwa su Ukty yadda zasu Amshi take away suke. Nakallesu nace daga Take kuma se Away mukasa dariya dukanmu. "Kuka take kaman ranta zai fice, anata shiryata wankanma dak'yar tayi.wankan turaruka Anty Husna da yar Babansu suka mata nakaima dabanne Aka nad'eta da yalwataccen Mayafi, gurin Babansu aka kaita yaimata iya tashi Nasihar yahad'a mata da Al-Qur'an charbi da babbar Dadduma, shima jiyake kaman yasa kukan. Zagayawa da ita akai gurin sauran matan gidan suma sukasa Albarkacin bakinsu. Masu yada maganganu nayi kowa da abinda yadameshi. "Itadai Inna k'arfin hali kawai take, "Allah yasa kishiga a sa'a abinda ta iya furtawa kenan. Tai musu alamada hannu aka wuce da Amarya. Deedat ya k'ank'ameta shi bazata tafi tabashahiba dayawa cikin mutan gurin saida sukai k'walla. Aka tafi da Amarya gidanta dake Sharad'a. Gidan ya k'ayatar da mutane danba k'aramin dukiya dangi suka narka mataba. Kowa yataho akabar ta daga ita sai halinta. Semuce Allah ka d'anbaba mai k'uli-k'uli๐Ÿ˜œ Am so sry makaranta Abubuwan dayawa shiyasa baku ganin postn akai2. Inkomi ya gyaru zakunajina koda yaushe inasanku nima aduk inda kuke. Allah bar zuminci da k'aunar juna Luv u all๐Ÿ˜˜ ยฉ *Aneesa_Didi*๐Ÿผ๐Ÿ‰๐Ÿ˜œ [2/18, 10:48 AM] โ€ช+234 703 962 5239โ€ฌ: [25/11, 2:50PM] Didin Anee๐Ÿ˜ โ™ก *DUTSEN CIKIN RUWA.....*โ™ก *Na* *Haleema G Khaleel* *41-45* Abokanan Ango sukayo masa rakiya suka wuce bayan sunyi Addu'o i danemanmusu farinciki dazama lafiya mai d'orewa. Suka d'anyi ciye-ciyensu itadai akunyace tasha Ruwa shima danya matsamata ne. Usman ya Umarci Naja'atu data sake alwala, cikin toilet in d'akin tai Alwala. Sallar isha suka fara sannan suka d'ora da nafila yai musu Addu'a mai tsaho sannan yai mata tambayoyi gameda Addini, yak'ara mata haske har Wankan Janaba yakuma mata bayani dayadda take samuwa. Kanta a sunkuye yake tamata bayani, wani tai magana wani tai shiru. "Hannunta duka yakama, yajanyota jikinshi janye mayafin duka yayi yarungumeta tsam ajikinsa, dukda hakan bak'on abune agurinta jinta tai she is safe, zippin rigarta yasoma yana kuma cusa kanshi ajikinta cikin wani salo na soyayya dabata ta6a tunanin haka abin yakeba, nikam danaga lamarin yajuye abin yafi k'arfin ganina. Najuya nabasu guri. Kunsandai bakyau bincike balle su wannan daya zama sirrinsu. Asuba tagari couples. "Wayewar asabar, komi shiyayi mata, Addu'a kuwa tashata ba adadi takuma narkewa soyayya yake gwada mata wadda ba algus acikinta. Har sukai karin kumallan safe. nok'ewar da takene adan fusace yace "ai aikin gama yagama, abunda take kunyanma yagani tomiyai saura? Itadai murmushi kawai take tana k'ara sunkuyar dakai. Kujerar da take kai yadawo ganin ta mik'e yasashi janyota tafad'a kanshi. K'ok'arin zamewa take yak'ara k'ankamota. Zauna ma kiji abinda zaki fara ma shine indai ina gida bakida gurin zama daya wuce nan, yanuna mata jikinshi. Kinsan body contact yanada tasiri wurin shak'uwa da mararin juna ga ma'aurata. "Bugun k'ofar da akeyine yadakatar dasu, saurin mik'ewa tai daka jikinshi tayafa mayafi akan kayanta tanufi k'ofa danta bud'e, Abdullah ne da Shukra k'annan Usman mama ta aiko suka mata abincin Rana. Guri tabasu suka shiga falon gaisar da Yayan nasu sukai, itama suka gaidata tacikasu da kayan mak'ulashe. Shukra Autar mama dasaurin sabo duk inda Najan tayi tana biye da ita. Har Usman ke tsokanarta tayi 'yar zaman d'aki, murmushi tai tace " aikam danaji dad'i daza abarta ta zauna. Hararar wasa yabita da ita tareda fad'in "bakowa ma kink'i sakin jiki musha Luv inmu bare anka miki wannan mai surutun. Tace " aida Mama zata ban ita danaji dad'i. "Hmm! Bakisan yadda Mama da Shukra suke bane bame rabasu se makarantar data shiga amma da ko ina suna tare, har yanzunma. Bata yadda tazauna agidan kowa se Mama. Dakwai sanda mama suka tafi Dabinai aka kaisu gidan Sisto, har yamma basu dawoba data fara kuka, kowa seda yaji haushinta Sadiq da Anas sukai zamansu harsun kwanta amma Shukra seda akada da ita gida k'arfe 10 nadare. Tana ganin Mama shiru kikeji. Wai lallai kuwa naga ranar rabuwarsu da Mama. Allah sarki aikam dolene rabuwar ta fad'a tana rau-rau da ido. Laah! Nibance kiman kuka ba kingama natafi. Yafice daka kitchen in yana dariya. "Bak'i sukai tayi danginsa da nata danma ankakkamata abinci taita zuba musu faranfaran takar6i jama'ar. Tacikasu da kayan arziki. Washe garima haka sauran danginsu dabasu tafiba sukazo ganin idan amarya. "Anty Husna dasu Samiha se yamma suka tafi bayan sun gyaramata ko ina dasauran kayayyakin ta nagida, takuma ware wasu kayayyakin daza a rarraba harda wasu daka cikin kayan lefanta. suka turare mata gidan bayan anty Husna tasata tai wanka kwalliya sosai tasa tayi, dan yanzu bada bace dole sekina gyara ladabi da biyayya sannan zaki mallake mijinki atafin hannunki. Kud'an bamu guri tace dasu Samiha. Suka fita suna k'us-k'us batasan yaran zamani wasu sunmafi masu Auren sanin abubuwa ba. Tacigaba dabata tip da dabarun zama da miji. Da sirrikan dazasu k'aramata Ni'ima batareda tayi amfani da abunda zasu cutarda itaba wanda batasan dame akaiba. " *Sirrri na daya*:- kisamu kankana kiyayyanka kisa madara kinasha. " *Sirri na biyu*:- kisamu zogale ganyansa da cocomber kiyi blending insu sekisa zuma da madara zakisha mamaki. " *Sirri na uku*:- kwakwa dabino dankalin,hausa(kadan) farar shinkafa cukwi. Ki markada shiima kinashan ruwan. Inkinso kuma zaki iyayin na gari kina damawa da madara kinasha. " *Sirri na Hudu*:-kihadasu gero mazankwaila dabino farar shinkafa kwakwa busasshiya busasshen muruci kida kasu siyi gari. Seki zuba man habbatussauda kihadesu guri daya. Yazama gumba. " *Sirri na biyar*:-Man zaitun Man tafarnuwa Man Habbatussauda Miski kihadesu kina shafawa/insert.har maganin sanyi yikeyi. "Taita gayamata abubuwa tana rubutawa wanima intayi harshi zasuna sha kaman inzata dafa shayi tazuba Minannas da kirfa aciki kunasha tare tsafta dayadda zata tsaftace gida da jikinta turaren bayan kunne daban nagashi, na matse-matsi cibiya. Shikansa mijin tadinga tsaftaceshi da kayansa yadda bazai taba zamada daud'a ba balle ajiwani unwanted odour yana tashi daga jikinsu. Seda Anty Husna tacikata da abubuwan Alheri sannan suka tafi tanata kewarsu. "Alwala tai tazauna kan akira sallah tanata lazimi abinta. Alamun bud'a k'ofa taji da sallama yashigo cikin husky voice insa, sansanyan k'amshin turare yaji yabigi hancinsa wanda bazai tantance ainayi wasu iri bane. Tun alokacin tafara aiki da hud'bobin Anty Husna. Tasowa tai zuwa inda yake ganin kaya da ledoji fal a hannunsa tarusuna tamai sannu da zuwa takar6i kayan hannunsa janyota jikinsa yai yakuma jin wani k'amshi na musamman natashi. Eye ball to Eye ball suke kallan junansu yana mata wani sassanyan kallo da murmushi dashi kad'ai yasan ma'anarsu. "Kinyi kyau yace da ita. Tallafota tai tagefansa suka k'arasa cikin
falon, takai kayan inda yadace shikuma yai Alwala yatafi Masallaci. "Cikin kwanakin Amarcinsu kawai sukeyi, seda tai sati sannan yakaita gidansu tagaida Mama da Abbansu. Dabinai kuma seta k'ara kwana biyu zaikaita taga danginsu nacan. Yanata rawar kai agaban Maman itakuma duk yasa tatakure, Maman bata k'ara ganin rashin kunyaba saida suka gama abinci tazubamai waishi da Matarsa zaici. Taitamai tsiya kuwa, itadai Naja sai murmushi kawai take ta duk'ar sa kanta. Da Maman tagaji da shak'iyancin nasa tace itama tatafi gano nata Mijin. Bak'aramin burgeta sukaiba yadda suke abunsu faran-faran kamar ba Mahaifiyarshiba. Komansu a kammale ba raini in social life. Taji sunk'ara shiga ranta. Musamman mijinnata. Habeeb injita da fad'a dukdan karta ambaci sunanshi. Yayi-yayi da ita amma taki, irin abubuwan dasuke k'aramata Martaba da Daraja agurinsa Allah yai yawa dasu, banda zazzafar Soyayyar dayake mata wadda bazata misaltuba. Agidan suka wuni se dare sannan suka tafi tinda bawani nisa garesuba duk Unguwa d'aya ce. Kubiyo *Didin anee*๐Ÿ˜˜ danjin ya rayuwar Naja'atu zata kasance bayan Aurenta??? ยฉ *Aneesa_Didi*๐Ÿผ๐Ÿ‰๐Ÿ˜œ [2/18, 10:49 AM] โ€ช+234 703 962 5239โ€ฌ: Didin_Anee๐Ÿ˜ โ™ก *DUTSEN CIKIN RUWA.....*โ™ก *Na* *Haleema G Khaleel* *46-50* Da k'afa suka k'arasa gidan, shi yabud'e musu get in gidan tunda ba maigadi garesuba. Seda yakunna hasken gidan, Masallaci ya wuce dangabatar da Sallar Isha, ita kuma tashiga ciki, wanka tafarayi tagabatar da tata sallar, shafa tazaunayi rigar bacci tasa silk light blue, turare tafeshe jikinta dashi, kowana sak'o seda ta mulkeshi da nashi kalan turaren. Tahad'e gashin kanta da ribbon tareda d'ora hula aka. Jin shiru beshigoba yasata dawowa falon kallo takunna, Eternal Love take kalla a Ztv. Bata dad'e da zamaba taji Karan rufe k'ofa Alamun yadawo kenan, da d'an saurinta tataroshi, kayan hannunsa ta kar6a tai kitchen, tana wawwarewa yashigo kitchen in. Yatayata aje kowane abu agurinsa ita kuma tayayyanka fruits in dayashigo dashi, tin a kitchen in yahau shan kankanar datake yankawa, dataga haka ta d'auke plate in kankanar ta ajemai na lemo dasauran kayan fruits in. "Abun ma hakane? Yafad'a ashagwa6e kaman shine matar, ganin tayi blending in ragowar Kankanar, ido kawai yabita dashi tamarkad' kankanar tasa madara da zuma amemakon Sugar. A fridge tasa tagyara gurin suka fito atare daka kitchen in se murmusawa take ai kuwa ya hau fad'in. "Shifa beyadda da wannan murmushin da take ba, tafad'a masa metake shiryawa. Murmushin takumayi sannan tace "bakom muje nahad'ama ruwan wanka tinda ba abinci zamuciba. Tashige cikin d'akin tana dariya ganin yadda yabita da idanu kaman baisantaba. "Ruwan wanka ta had'a masa wankanma seda ta lalla6ashi yashiga. Wai yayi fushi tinda tak'i gayamasa metake shiryawa. Kayan bacci tafito mai dashi tafeshesu da turare, tak'ara kintsa d'akin dukda bawani datti yaiba se bada k'amshin freshner yake. Kallonta tacigaba dayi tanata farin ciki itama da Allah yabata miji irin Usman. Ganin yadda Sahiba da Ranveer suke zuba salon tasu soyayyan. "Kitchen tashiga, ta d'auko kankanar datai blending tayi sanyi, bame yawaba tazauna tanasha, d'an sanyi dayai yanabin jikinta harwani lumshe ido take, k'anshin turarensa kawai taji tabud'e manyan idanunta duka akansa, k'arasowa kujerar datake yayi yazauna jikinsa na gogar nata. D'ebowa tai zata kai bakinta yai saurin kai nasa bakin, "irin dad'in dakike sha kenan ashe, yafad'a yana lumshe narkakkun idanunsa. Sunkuyar dakai kawai tai murmushin de takuma, hannu yasa ya d'ago fuskar yahad'ata da tashi kowa nashak'ar numfashin d'an uwansa, yana mata wani sassanyan kallo dashi kad'ai yasan ma'anarsa. Cup in hannunta ya kar6a yana bata yanasha har suka shanye, seda yakalli News sukai brush yasunkuceta sukai d'akinsu. Tareda rufo k'ofa. Safiyar alkairi. "Kwance yake kaman bazai tashiba tinda yai bacci dagari yafara haske, bayan yagama yamutsa Naja atun Queen injishi da fad'a. Wayan tak'ara ringin akaro na uku, jin vivration in yayi yawa yasashi bud'a ido da kyar. Ganin a sch inda sukai ne yai saurin ansa wayar, "ok godiya nake prop, Allah yak'ara girma. Yamike yashiga band'aki already yasan tahad'a masa ruwan wanka ilai kuwa tarufe mai ruwan yasamu yayi daidai wanka. Wajen k'arfe goma yafuto, se kamshi gidan yake, yaduba ko ina batanan yai d'akinta. Sark'a take k'okarin sanyawa, ya kar6a yasa mata har d'ankunnen yak'arasa shiryata, tana tabinsa da kallo ire-iren abubuwannan dayake mata nakulawa da soyayya su suk'e k'ara mata k'aimi wajen yin duk wani abu datasan zai farantamai yasashi nishad'i da farinciki cikin d'an zaman dasukayi tare. So da K'aunarsa kuwa sun mamaye jini da jijiyoyinta, duk wani motsi da zatai da k'aunarsa take, Addu'arta kullum suzama cikin so da k'aunar junansu da farinciki mai yawa a rayuwarsu. "Rungumeta yai tabaya yad'ora ha6arshi a kafad'arta, suna kallon junansu ta madubin. "Queen Tunanin mekike kina tare dani? Idan muna tare bakida sauran damuwa a rayuwanki. Am always there for you. *Ina tare dake*(Meemee bea ta) cikin kowana yanayi *Komai Rintsi*(Hama Gee). Kikasace dani kowana hali samu da rashi, cuta da lafiya yafad'a yana k'ara rungumota kaman za a k'wace masa ita. "Hannayenta duka tasa tana shafo kansa, tahau rattabomai tsadaddun kalamai "kazama ni nazama kai mijina komai inzanyi dole saidakai. A kullum ina godiya ga Allah daya bani kai mai hak'uri da kawaici mijina takuma narkewa ajikinsa. Sund'au lokaci suna kallan junansu kowa na Sakar zuci sukasa dariya gaba d'ayansu yabata kiss a fore head inta, dak'yar yabari ta d'aura d'ankwalin suka fito dansuyi break fast. Agurguje yaci abincin, shima saida tai kaman zata masa kuka yazauna dakanta tabashi Oat ne yaji madara da Omylet, tanad'e mai Pan cake a foil da ginger drink aroba yatafi dasu. Dan idan yai irin fitar wurinnan baya dawowa da wuri, takanyi k'ok'arin yimai dabarun dabazai sa yaji yunwa dawuriba. Tinda ba abincin ko ina yake ciba. "A ranar ma kuwa se yamma yada gidan. Tana zaune itakad'ai se Radio data kunna, wak'an Nayi gamo ake tana tabin wak'ar dan tana santa(Miss zo6o๐Ÿ˜œ) kawai ganin mutum tai jitai anyi sama da ita tai saurin rintse ido, yai juyi sosai sannan ya ajeta. Neman kujera tai tai saurin zama gudun fad'uwa, seda ta maida numfashi ta iya cemai sannu da zuwa, kusada k'afarta yazauna yana "Addu'ar dakuke min a kullum ta k'ar6u anza6eni cikin wanda akai sponsoring inmu miyi masters a sch in damuka baro, dan haka kihau shiri dake za atafi. Dirowa kansa tai tarungumeshi tanata murna itama, jin bakinsa tai cikin nata tin tana tirjewa harta soma maidamai da martani ganin yana neman zarcewa yasata janye jikinta tai gefe sunata ajiye nannauyan numfashi. "Ruwa takamai yasha suk'a k'arasa maganar nanda wata biyu zasu tafi, kannan itama zata zaga dangi har gida zata tinda yau wata4 da zuwanta gidan bataje gidaba. Shiko yajajje gaidasu. Kafin magriba yatafi gida yagayawa Mamansu da Abbansu. Suji zancen suma. Sula kuwa samai Albarka dafatan samun Nasara arayuwarsu gaba d'aya. *Bayan Wata biyu* "Kafin lokacin seda tazazzaga dangi, dasukaje gida kuwa Inna kamar tacinyeta dan farin ciki ganin yadda 'yarta takuma cika da murjewa fata se shek'i take alamun hutu da kwanciyar hankali. Tawuni cir agida har mak'ota tazazzagaya. Gidan Yayarsa Yusra ma takar6esu hannu biyu-biyu sukai ta hira kamar sun saba. Tahado mata abubuwa dangin kayan k'amshi tinda su take siyarwa. "Daga getso suka ziyarci dangin mahaifinta, yacikasu da shatara ta arzik'i wanda basu sanshibama duk suka ganshi. Gusau suka wuce kwanansu biyu Anty husna kam tafi kowa farin cikin zuwansu. Tak'ara mata dabaru da sirrika irin na Mata masu aji. "Seda sukai kwana biyar dadawowa daga Gusau sukai shirin tafiya Dabinai. Suka k'ara kwanaki acan yadda dasunda se shirin tafiya. Taga karamci da mutuntaka irinnasu, taita godewa Allah daya had'ata da miji da danginsa masu so da k'aunarta da mutuntata. Tsaraba iri daban2 suka had'o su dashi taita kunya ganin ita bawani abun azo agani takai musuba. Turaruka sai k'ananun turamen atamfofi takai aka rarraba. Sukai ta farinciki dasa Albarka. "Tun ana sauran kwana5 sutafi kayansu sukai gaba a motar haya, se d'an abunda ba a rasaba, sunata

Please Login or Register in order to submit comment