Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk sammak'al. Inna kuwa ba ta yanda
za ta amince waninmu ya d'auramata lalle.
Ina mafita?"
*GIDAN MATI*
BY BINGEL FULANI & RUFAIDA OMAR
"Ke dadina dake jahilci kwarankwatsa dubu,
haba ai ko karamin yaro ya san ruwa za a
shekama Zubo a zuba Sugar shi ke nan ya
zama lemo, batun lalle kuma kin manta
Inna da shegen san fadanci kamar matar
Bawan Sarki? Ai kawai kururuta mata kai
zakiyi har ta sake ta baki kafar ki kunsa. "
Nene ta yi shiru kamar mai nazari, sai
kuma ta gintse fuska ganin Fad'ime ta fito
zuwa makewayi. "Shegiya kai da wata
fuskarta kamar taunanniyar gyada, Allah
Abule yadda naki jinin Matar nan bank'i a
cemin karta fito raye daga makewayin nan,
ba ni zoban ki gani duka gidan zan had'a
idan ya so a na tan sai na juye maganin" Ta
fad'a tana wartar ledar zobon da Abule ta
riga ta siyo. "A'A hankali dai Nene d'an
kad'an ya ce a zuba saboda karfinsa." Ta
balla mata harara "Wallahi duka zan juye
idan za a sha giya asha ta dubu Abule!" Ta
fad'a tana mai ficewa daga d'akin. Kai tsaye
madafi tayi ta dauko kwanon sha ta juye
zobon, ta tuttulo ruwa daga tulu ta sheka
bisansa ta zuba Sukari wadatacce ta juya.
Nan da nan ta kasafta na kowa, na Inna ta
fara dauka dauka za ta kai mata, da shigarta
kuwa ta tarar ta tana gyangyadi dan haka ta
aje ta juya za ta fita. " Na shige su ni Uwar
Biyu, Nene me nake gani haka?" ta juyo da
sauri tana kallonta kafin kuma ta saki
murmushi. "Zobo ne muka samu tsaraba
daga Abule, shi ne na hadamana lemo da
shi na san ai kin sanshi a birni." Inna ta
balla mata harara tana turo kallabi goshi."
To ke ina kika taba ganin anyi zobo ba a
tace tikar ba? Wannan zobo za mu sha ko
roman zobo? Idan ba ku iya abu ba ku dinga
tambayata mana, ni nan da kuke gani na
bayan zobo durinkis (DRINKS)har mangwar
durinkis (MANGO DRINKS) Na iya, dan haka
ban san jahilci d'auki ki ta ce shi sai ki
kawon. Sum-sum Nene ta fice jin Inna ta
koma yaren 'yan sama jannati. Sake
gyarawa ta yi, tukun ta dauki na Fadime ta
kai mata daki, komawarta daki ke da wuya
Mati ya sawo kai Gidan. Kai tsaye dakin Fadi
ya yi yana doka sallama, fasa kai dan
karamin kwanon shan baki ta yi ta aje tana
amsa masa da murmushi kafin kuma ta
mike tana kokarin zare masa zungureriyar
hular da ke kansa. Ya shaki kamshinta da
yake so na Karkar dan haka ya washe baki
"ALLAH Amarya son ki nake kamar na
mutu" Ta yi murmushi tana rangwada
kwalelen kanta "A'A Maigidana mai ya kawo
mutuwa kuma, muna tare ai." "Hmm! Ba za
ki gane ba ne, idan kina kusa da ni ji nake
kamar numfashi... KYYYATTT...FYYTTATAT...
Ya dakata yana mai kakalo kaki, kafin kuma
ya dunkulo majinar yana mai furzo ta waje
da ba ta dire ko'ina ba sai cikin kwananshan
Fadime dake cike da zobo. Ita da shi suka
zubawa kwanon ido kafin kuma ta kwabe
fuska. "Haba Maigida na sha ce maka ka
dainamin tofe-tofe a bangon daki ko kasa,
wannan ko a kan titi ne ba abin so ba ne.
Yanzu kalli yadda ka haramtamin abinda
tunda na gani yawuna ke tsinkewa. " Ki
hakuri na mantane, yanzu bari na karbo
miki kasona sai ki sha." ya fada yana mai
daukan kwanon ya fice. Bisa randa ya tadda
wani kwanon rufe da Fai-Fai Dan haka ya
aje wancan ya dau wannan ya tafi. Nene da
ta shiga makewayi rage ciki tana fitowa tayo
inda ta ajje zobanta, ganinsa bude ya sata
doka ashar "Ko wane shegen ya budemin
oho, to idanma diba akai an sha wuta bal-
bal tunda nawa ne. Ta fada tana hararar
dakin Inna, kafin kuma ta daga kwanon ta
kwankwade tas! Har kakin Mati. Minti biyar
da sha cikinta ya yi wani irin juyi, jin kamar
ruwa da wani wari na binta ya sata lekawa
abin da ta gani na binta ratata ya sata doka
ihu tana dafe mazaunanta "Wayyo ni Mati!
Yoyon Kashi ya kamani.
Muna zuwa.
*GIDAN MATI*
©BINGYEL FULANI & RUFAIDA OMAR
Ihun Nene ya janyo hankalin mutan gidan,
gaba daya suka fito har da Abule wacce ta
gwaggwa6e a d'aka tana kwa6a lallen. Kan
kace me tuni Delu ta gyara zamanta jikin
garu tana lek'e, itama Shafa ba'a barta a
baya ba wajen ganewa idonta. Mati a rude
ya nufeta.
"Nene, lafi..."
Kii! Ya ja burki sakamakon wari da k'arar
sakin tusa da ya bugi kunnuwa da hancinsa.
Inna ta sanya salati.
"Me zan gani haka Nene? Wane irin
shashanci ne haka ki wuce Makewayi mana"
Nene dake ta kokarin danne mazaunanta da
hannu ta daddage ta ja numfashi sama tana
mai hade jikinta dan ta tsayar da gudawar,
ganin kamar an kara kunnu ta ya sa ta sakin
wani wawan ihun "Wallahi ba ta tsayawa, na
shiga uku ruwan jikina zai k'are. Kai Mati!
Kai mati zan mutu, za ta zuƙen jini" Ai sai
ta zabura ta danna a guje zuwa karshen
gidan abu na yoyo. Mati ya yi sauri ya bita
ganin ta zube gun, "Nene, nene, jin shiru ya
sa shi toshe hanci yana jijjagata, sai kuma
ya dago a tsorace yana duban Inna.
"Kamar fa ba ta numfashi Inna" "kai
kauce nan, wane irin ba ta numfashi matsa
ni ka ga na ba ta fastu aidi (First
Aid)shashasha ko dabarun lafiya baka iya ba
dake kanka ya cika da gashin jakai." "Um
Inna yanzu dai bata ba'a ake ba ki duba ta
kiga ni Aradun Allah Inna ba ta motsi"
Inna ta dan na masa harara, sai kuma ta
hau karewa Nene dake yashe kallo, ganin
har yanzu Abun na tuttulowa daga jikinta ya
sa ta kallo Mati "Tunda dai kai ne Mijinta
matso kusa daidai bakinta ka lalubo
harshenta ka gantsara mata cizo, shi ne zai
sa ta farfadowa yanzu" Mati ya kalli Inna da
ta kauda kai gefe tana jijjiga kafa kamar ba
ita ta fadi wannan zance ba, ya waiga ga
Abule dake matsar kwalla, ya dora idonsa
kan su Delu dake bisa katanga, ai sai ya hau
girgiza kai yana mai sharce gumi "Bazan iya
ba! Kwarankwatsa dubu Inna wannan zalunci
ne, ya zan ciji marar lafiya. Kuma sannan
wannan ai Yahudanci ne." ai sai inna ta
zabga salati tana mai fashewa da kuka Mati
ya ce mata Azzaluma, kafin kuma ta share
hawayen tana mai watsa ma masa dakuwa
"To ka tsaya jahilci Nenen ta mutu,
numfashin mutum na daukewa da minti
goma idan bai samu taimakon gaggawa ba
yake mutuwa"
Jin haka ya sa Mati yin wurin Nene da
sauri yana lalumar bakinta. Da dai ya zakulo
harshen ai sai ya gatsashi da karfi. Baya ya
yi yana ganin Nene ta yi wani irin cilla kafa.
Tana fadi a hankali " Na mutu Mati" cikin
magagi. Abule ta ƙara sautin kukanta "Inna
dan Allah mu kai ta gun kula da lafiyan da
kika kai Faɗime kwanaki" Mati ya kalle ta,
sai kuma ya yi waje da sauri. Ba daɗewa sai
ga shi da mai Baro. Abule ta taya shi kama
Nene aka dora ta bisansa. Suka ɗunguma
Asibitin ƙauye.
Bayan dube-duben da likitan ya yi
sakamako ya fita. Nene dai banda Maleria
ba abinda ke damunta. Likita duk
tambayoyin da ya yi sun tabbata ba abinda
ta ci na ɓata ciki tunda dai abincinsu guda
ne. Dan haka ya daura ma karin ruwa ya
rubutawa Mati O.R.S da Napkin na manya
aje a siyo mata. Ta kuma dinga daura
napkin din duk bayan sa'a biyu. Karshe ya
sallemusu da cewar su je Binni a duba ta da
kyau shi kam iya na sa ke nan. Da
komawarsu gida Abule ta yi wuf! Ta fada
ɗakin Nene tana sakayo kaba. Kallonta take
cike da tausayi ganin harta tsotse rana
guda.
"Ni Nene anya ba maganin fadi kika sha
ba? Na ganta sumul fa" Nene dake ji da
yoyon kashinta ta mike a hankali jiki na
rawa" Shi ne wlh a randa na tadda shi a
bude na sha, na shiga musanyamin ta yi
bakar muguwa wayyo ni. Mene makarin ki
taimake ni Abule" Abule ta dafe kirji ido
warwaje "Lalle dara ta ci gida Nene!
Makarin da wuya Nene, ba za mu iya ba, sai
kuma rushe da kuka."
Nene ta yi ruf da ciki tana numfarfashi.
"Ki fad'amin Abule, ko menene shi zan iya."
Jin haka Abule ta fyace majina ta soma
magana.
*GIDAN MATI*
©BINGYEL FULANI & RUFAIDA OMAR
Abule ta yi k'asa-k'asa da murya.
"Makarin shine a jik'a wandon kwarto a
shanye."
Nene ta zabura tayi zaman 'yan bori
wanda ya yi daidai da sullu6owar tusa ta
mai k'ara. Abule ta toshe hancinta, a
hankali Nene ta numfasa har da lumshe
idanu don ba k'aramin sassauci ta samu a
cikinta ba.
"Na shiga uku, yanzu ina zan ga kwar... Af!
Fad'uwa ta zo daidai da zama ai Abule, yo
bana manta ashe muna da su a kurkusa ba?
Ga Basharin Shafa?"
Abule wacce itama shaf ta mance da batun
Jik'an Lamid'on ta sauke ajiyar zuciya tana
mai jin zuciyarta wasai, babban abinda ya
sanyamata damuwa da lamarin ba komai
bane sai na tsoron kada ya kasance Nene
bata warke ba ta tonamata asiri mutan gari
su zageta. Ta daki cinyarta tana mai washe
rinannun hak'oranta.
"Kai Allah mungode maka, ai ni dinma kaf
tunanina bai je nan ba. Ko jiya da daddare
ya haurawa Kulu Gurguwa."
Suka saki shewa don Nene har ta hango
warakarta a sauk'ak'e.
"Kai Allah Ya k'arowa Bashari ilimin
kwartanci, wannan ai gaba ta kaini. Ashe
kwarto da ranarsa. (Kun ji jahilci!)"
Dariya suka k'ara kwashewa da ita.
A yammacin ranar Shafa na durkushe a
gaban murhu tana kokarin iza wuta ta
tsinkayi sallamar Nene da Abule. Da
mamaki ta dubesu kafin ta mike. Abule ta
ci burki anan tana k'arewa gidan Shafar
kallo domin rabonsu da shiga gidan har sun
mance. Daga can gefen garu ta hangi jerin
manyan duwatsu wanda ta taimakonsa ne
Shafa ke k'arewa cikin gidansu kallo. Ta6e
baki ta yi gami da bin sahun Nene da har ta
shige rumfar Shafar ba tare da ko neman
izni ba.
Shafa za ta yi magana Abule ta hanata ta
hanyar rik'o hannunta tanamata alamar ta
yi shiru gami da yi mata nuni da gidansu,
nan take ta fahimci ba su kaunar Fad'ime da
Inna su san da zuwansu. Ta gyara zaman
d'aure kirjinta suka shige ciki.
Nene ta washe baki.
"Shafa Shafa, Shafar Bashari, uwargida ran
gida! Kin tare gaba kin tare baya, turmin
tsakar gida sha lugude!"
"Wannan haka yake." Fad'in Abule tana
gyada kai kamar k'adangaruwa.
Shafa ta yamutsa fuska tana kallonsu d'ai-
d'ai.
"Halan dai Nene acan asibitin har allurar
mahaukata suka manta suka yi maki?"
Nene ta hau daure fuska za ta kwa6omata
mai zafi ganin haka yasa Abule saurin
tarewa.
"Kai Shafa, dad'ina da ke zolaya. Nene ai
taki ce, banda abinki ai makwafci ance ya fi
dan uwa, a baya ma rashin fahimta ne."
Dariya Shafa tayi gami da tafa hannuwa.
Nene da Abule suka dubi juna, dakyar dai
suka shawo kanta ta yarda zata sauraresu.
Nene ce ta soma magana bayan ta gyara
zaman nafkin dinta.
"Ki taimakeni Shafa ki bani aron wandon
Bashari."
Shafa ta fiddo idanu gami da dafe k'irji.
"Yau naga ta kaina! Nene me zakiyi da
wandon Basharina? Anya Nene ba ki samu
matsalar kwakwalwa ba? Au to na fahimta,
wato dai duk matattarar kwararar gudawar
da aka sanyamaki bai isheki ba sai kin had'a
da wandon Basharina? To mine amfanin na
Mati?"
Nene ta share zufa tana girgiza kai. Abule ta
cafke zancan.
"Kinga Shafa duk ba haka bane, wannan
maganar da za mu yi sirri ce, don Allah ki
rufamana asiri."
Shafa ta dan zubamasu idanu na 'yan
dak'ik'u kafin ta gyada kai don ba za ta bari
gulmarnan ta wuce ta ba.
"Ina jin ku."
Abule ta zayyanemata duk abinda ya faru
da kuma makarin asirin.
Shafa ta saki shewa har da tafa hannuwa.
"Yau abin namu ne! Oh ni matar na
Lamid'o!"
Saida ta basu wuya Nene harda matsar
kwalla sannan ta amince da sharad'in
Nenen za ta kyautarmata da tunkiyarta da
take kiwo. Ba musu Nene ta aminta
daganan ta mik'e ta fita zuwa d'akin
kwanansu ta hau lalube.
Jimawa kad'an sai ga ta rik'e da wani
tsohon wandon Bashari da ya gada gun
Lamid'o ta mik'amata.
"Gashinan, kuma kada ya kai gobe a
wajenki, ko ta katanga ki jehomin."
Nene ta hau godiya kafin kuma cikin lallami
ta ce.
"Ki taimakamin Shafa, ki bani sabon d'inki
mana."
"Cab! Ai idan kinga Bashari ya yi sabon
dinki to mutuwa akayi a danginsa don haka
ban bayarwa, idan ba kwa so ku k'ara gaba."
Ta k'ara he tana girgiza k'afa gami da
jefamusu tafin hannunta.
"A'a me ya yi zafi? Mu je Abule hakan ma
ya wadatar" " To karki manta dai ki jefon ta
katanga." Da komawarsu kuwa Abule ta
tarkata lallen ta watsar Masai, shi zaman
duniya dama rabo ne, idan ba ka da shi
kuwa za ka zo ne a banza ka koma a wofi.
Tuna hakan ya sa ta nutsuwa ta ma fita daga
batun Fadi. To haka ma ga Nene sai wayar
gari akai aka ganta sumul tamkar mai
bugun Iska. Itama ta mai da rayuwarta
shiru ta hanyar aro nutsuwar dole. Daga
bisa ni ta kulla Amintaka da Shafa ba ma ta
zaman gidan balle ta zubda hali. Bayan
watanni, ranar wata laraba wanda ya yi
daidai da kwanan Inna guda a birni ta je
hado kayan haihuwar fadi. Faɗimen ta tashi
da nakuda. Gidan daga Abule sai Nene dake
shirin fita.
Ta gyara zaman yafenta tana mai sauke
kabar shiga d'akinta. Ta juyo gami da duban
Abule, za ta yi magana kenan suka ji nishi
da salatin Fad'ime. Cikin hanzari suka dubi
juna.
"kinji abinda na ji?" Abule ta ya tsina
fuska" na ji mana kila abinne ya zo." "To ya
za ai ko mu dubu yar magaji... " Abule ta ƴi
saurin rufe mata baki. "Ke gafara, kinmanta
yanda ta musanya miki magani? To yaune
ranar ramuwa dan haka maza kwaɓe gyalen
nan ki dauka surfe mu yi yanzu dan karma
makota su jiyo bayan awa guda ma lekata."
Da sauri Nene ta aje gyalen ta juye hatsinta
a turmi suka hau dukansa ba ka jin karan
komi sai tunkwal-tunkwal.
Fadime cikin azaba haka ta rarrafo bakin
kofarta tana kiransu amman suka yi biriss
da ita. Har sai da suka bar jin muryarta
tukun suka zubda taɓaren suna ma su
nufarta. Ganin ruwa gefenta ya sa Nene
zare ido "Ke abu ai fayar ta fashe."
Abule ta karasa itama tana lek'e-lek'e, a
karshe suka kinkimi Fad'ime suka maidata
ciki. Haka suka kar6i haihuwar santalelan
d'anta suka yanke cibi. Nene dake rike da
jaririn wanda bai bar komai na Mati ba,
katon kan Fad'ime ya yo. Ta yiwa Abule ido
kafin ta fice zuwa d'akinta rike da jaririn
wanda ta cusawa yatsanta a bakinsa gudun
kada sautin kukansa ya ankarar da
gulmammun makwaftansu.
Abule ta dubi Fad'ime wacce ba k'aramin
k'aruwa ta samu ba wajen haihuwa sai
murk'ususu ta ke da alamar dai akwai
abinda ke damunta. A hankali ta sulale ta bi
bayan Nene. Idanu ta ware a tsorace ganin
Nene na kokarin sanya jaririn cikin kwali.
"Nene! Bakya tsoron asirinmu ya tonu?"
Nene ta harareta.
"Kinsan iyakar tsawon lokacin da na dauka
ina ajiyar kwalinnan? Ai bazan bari
damarnan ta kufcemin ba, yau dan kwal
ubannan sai kwanan daji."
Kafin Abule ta ce wani abu suka tsinkayi
sallamar Mati.
A razane suka dubi juna har Nene batasan
sadda ta cire yatsanta daga bakin jinjirin ba
ai kuwa ya canyara kuka.
"Lafiya Fad'i? Kin haihu ne?"
Mati dake jefowa Fad'insa tambayoyi ya
tsaya gami da saurin bin inda ya jiyo kukan
jaririn.
Duk kokarinsu na kada ya fahimci shirunsu
saida ya gane. Nan ya hau salallami, wani
wawan tsalle da ya doka sai gashinan gaban
Nene, ya kwasheta da mari kafin ya fiddo
jaririn daga kwali.
"Ka gantanan, yasin ba hannuna ciki! Yanzu
na shigo daga makwafta ina.." Fad'in Abule
yayinda Mati ya katseta da sauri.
"Dalla can rufemin baki kema bakar
munafuka! Wato kun yi shirin kashemin
mata da d'a ko?"
Sautin karar Fad'ime ya kid'imashi, a guje
ya fice zuwa d'akinta.
Kan kace me Shafa da Delu sun shigo
domin tun kukan jaririn na farko sun
tsinkaya saidai ba su k'ara ji ba sai yanzun
da Mati ke balbalin fad'a. Lek'owarsu suka
san abinda ke faruwa suka bazamo cikin
gidan.
Su ya bari a wajen Fad'ime yayinda ya fice
nemo abin hawa don mik'a Fad'ime asibiti.
Delu na gyara jaririn tana zubamusu
habaici Shafa na tayata. Su kam kowacce na
d'akinta sun k'unshe gaba daya a tsorace
suke da abinda zai biyo baya.
"Shegen, ashe d'agamin k'afa kawai ya ke."
Fad'in Nene a k'asa-k'asa tana shafa
kuncinta.
Mati na dawowa aka wuce kai Fad'ime ga
likita bayan ya kora Nene da Abule
gidajensu da shika (saki) d'ai-d'ai.
*GIDAN MATI*
©FULANI BINGYEL & RUFAIDA OMAR
BAYAN WATA GOMA
Rayuwa mika a gidansu Mati, abubuwa da
yawa sun faru ciki harda dawowarsu Nene
bayan sunyi Bikon Mati sau kusan goma.
Wanda Nene sai da ta koma yini a gona gun
Mati tsaban son ta koma dakinta. A rana sai
tai wanka sau hudu ko biyar. Goge hakora
kuwa masu sai da gawayin ƙauyen sai da
suka shaidata, haka ma masu Gishiri.
Saboda tsabar tsafta sai da ta koma yawo da
tsumma tana goge kafarta idan tai kura.
Wannan fa duk shawarar ƙawarta Shafa ce.
To haka ma ga Abule itama sosai ta nutsu
dan har dan abin kwalama take kaima Mati
gona. Musamman ma Kundun Kaza da ta
san yana so. Karshe dai ya mai dasu. A
daren Inna ta tarasu da ta ta nasihar ta
nunamusu laifinta ne tare da neman
gafararsu.
"Haba Inna, ta ina kika zama mai laifi? Mu
keda laifi mu yakamata mu nemi gafara."
Fad'in Nene kenan tana mai k'arashewa da
sheshshek'a.
Fuskar Inna cike da damuwa ta girgiza kai
bayan ta k'aremusu kallo gaba daya har
Matin tana mai shafa kan jikanta Atiku dake
saman cinyarta, ya sha billensa a goshi an
rambad'amasa kwalli yayinda fuskar ke ta
kyallin mai. Ta cigaba da magana.
"Um um Nene, bari fad'in haka, maganar
nan haka take. Abule da bakinta ta
sanarmin musabbin wannan rashin jituwar
a sadda take zuwa yawon biko, nayi
kuskuren ware wani kaso na dukiyata da
zummar bawa jikan Matina na farko, kai
kuma Mati bai kyautu ace kai da kake
Maigida ba kana nuna halin k'aranta, Abule
ta sanarmin da irin yanda ka sanyata k'aryar
ciki wanda tun daga ranar zaman lafiya ya
k'ara k'aranci a gidanka. To yanzu wannan
sai ya zama izna gareka, matuk'ar kana son
had'in kan iyalanka kada ka k'ara wannan
gangancin. Nima a karshe ina neman
gafarar..."
Da sauri duk suka tari numfashinta kowa na
kara neman gafararta, Nene da ke tashin
k'amshin turaren matan arewa ta rungumo
kafadar Abule dayan kuma ta rungumo
Fad'ime wacce farinciki ya cika don har
zuciyarta bata son fad'ace-fad'ace, washe
bakinta ta yi wanda ya sha durji da gawayi
ta ce.
"Yanzu mun zama tsintsiya mad'aurinmu
d'aya. Daga gareni Nenen Mati babu abinda
zai k'ara fitowa daga wurina."
Farinciki ya cikasu babu ma ya Mati wanda
har aiken kiss ya yi musu ta iska bayan ya
fakaici idon Inna, suka tuntsire da dariya
kuwa.
Cikin iko na Ubangiji kuwa tun daga ranar
babu hayaniyar da ta k'ara tada hankula a
GIDAN MATI, Nene a matsayinta na babba
ta ja girmanta da sauran mutuncinta da ya
rage, hakanan Fad'ime tana binsu sau da
k'afa, saida ya zamana rainon Tanimu ya
koma ga Nene, kai kace itace ta haifeshi.
Fad'ime me kawaici kuwa ta d'auke kanta
daga Atiku, muddin ba nono zai sha ba to fa
babu abinda k had'asu sai kwanciyar bacci.
Bangaren Mati shima kuma daidai
gwargwado yana kokarin yin adalci
tsakankaninsu. Wannan ya kwantarwa Inna
hankali.
SAUYIN RAYUWA
Gida ne wanda ya sha filasta madaidaici,
tsakar gidan an shafeshi da sumunti.
Dakuna ne jeras har hud'u sai falo babba
guda daya wanda daidai talakan k'auye ya
tsaru.
Nene ce ta fito daga d'akin dake jikin na
maigidannasu tare da Atiku da kanwarsa
Sa'a, ta cakare cikin atamfa mai kalar ruwan
masara, tana kokarin rufe k'ofar d'akinnata
bayan ta saki hannun Atiku ta ce.
"Wai mutanennan kuna so dai dare ya yi
mana ba mu tafi gidan bikinnan ba ko?
Abule! Kanwata!!"
Kusan a tare suka amsa gami da fitowa
daga d'akunansu sanye cikin atamfa
irinnata. Abule rik'e da d'iyarta da Allah Ya
bata wacce ko wata shida bata cika ba a
duniya yayinda Fad'ime ke goyon yaronta
na uku Sallau don Nene kam Allah bai bata
ba.
Nene ta washe baki.
"Inye, cakarewa. To ai ni har kun fini
kyau."
Suka dara.
"Wane mu?"
Fad'in Abule da ke saita zaninta. Suka rufe
ko'ina suka jera gidan Delu wacce ke aurar
da yanmatanta uku.
Kowa a gidan bikin ya yaba da shigarsu,
Shafa ita kanta ta yi kyau tamkar ba ita ba,
cikin hukuncin Allah mijinta Bashari ya
shiryu ya daina kwartanci, hakanan Delu
itama mijinta ya daina dukanta tun
watarana da diyarsu Bushira (wacce duk
cikin yaran ya fi kaunarta saboda
nutsuwarta) ta gwada d'aga hannu da
zummar ramawa uwarsu, wannan abu ya
dagamasa hankali ainun karshe dai ya
saduda bayan limamin garin ya shiga
lamarin ya mishi nasiha.
Karshe. Mu hadu a wani sabon Labarin na
mu mai suna BUDURWAR KURMA...
MUNA GODIYA

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment