Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana
hararar Abule."
"Oh ni Abu? Lalle idan ta karewa kare barin
haushi yake ya koma tunkuyi, na ga dai abin
rabo ne auran Mace da ciki. Ki gwada naki
salon mana mu gani, ai wani asirin baya ci
da turaren hayaki sai an had'a da yan
dabaru."
"Uban wa ke asiri da turare?" Nene ta faɗi a
fusace tana ture fai-fain tafasa gefe."
"A'a ai kinji matsalarki baki cin ribar
magana, yanzu mene na sakin na maguzawa
a wannan hirar? Ni kinga wucewata yin
abinda zai fisshe Ni. Ta faɗa tana mai
sunkutar bokitinta ta fada Makewayi.
Nene ta ciji yatsa tana mai tura baki gaba,
sai kuma idanuwanta suka sauka kan kayan
da Abule ke d'orawa saman yar katangar
bandakin ta langa-langa. Abin mamaki
harda wani tsohon dankwalin wata
atamfarta me fanteka da mati ya sa mata
tun a toshi. Har dai ta juya zata wuce, sai
kuma dai ta sake juyowa tana kallon
katangar zuciyarta na kiyastamata abinda
Abule ke yi da kaya haka. Nan fa
idanuwanta suka sake sauka kan wata
tsummar rigar Mati da tun yana Saurayi ta
sanshi da ita. Wani makirin murmushi ta
saki da ta gama hasaso abinda take zato. Ai
sai tayi gun 'yar katangar a hankali ta janye
kayan bata bar mata komai ba sai zanin da
zata yane jikinta.
Da sauri tayi ɗaki gurin Inna dake
gyangyadin shaiɗan na gabda Maghriba.
Itama Innan sai da ta firgita na ganin yarda
Nene ta fad'o Mata ba ko gafara dai.
"Lafiya Nene kika katsemin barci haka dan
rashin mutunta Uwar Miji?"
"Bari dai Inna, ai abinda na gani yau idan
ban sanar miki ba na cika ma-ci Amana, na
rantse miki da izifi sittin Abule cikin zani
gare ta. Idan baki yarda da batunnan ba
biyoni kofar Makewayin ki gani."
Inna ta watsa mata wani kallo she'ke'ke, sai
kuma ta mi'ke tana tura d'aurin kallabinta
gaba."
"Muje na gani." Ta fad'a tana yin gaba.
Abule da ta gama jika-jikan ta
mi'ke za ta mai da zannuwanta ta d'aure
yanda ta saba, ai sai ta tarar babu, ta d'auka
ko baya suka faɗa dan haka ta fito a sad'ad'e
tana Addu'ar Allah ya kau da idon Nene har
ta kwashe. Sai dai fa turus! Ta yi ganin Inna
da Nene tsaye tana sakar mata dariyar
Mugunta. Jiki na tsuma ta sunkuyar da
kanta 'kasa.
"Shegiya guntuwa me bakin hali, abinda ban
zaci gare ki ba sai gashi ya tabbata gunki.
Uwar wa ta koyamiki wanann kinibibin ko
dan ganin yar uwarki na da cikin? Inna ta
faɗi tana mai kai mata rankwashi a jikakken
kanta.
"A'a Inna lafiya kike bugurmin Abule" Mati
ya faɗa da shigowarsa kenan.
"Zaka rama mata ne? Sha-sha-sha kawai,
Matarka na cikin Zani dan sakarci ka kasa
gane wa."
Ya kwalalo ido yana dubanta, sai kuma ya
hau sosa kai yana noƙewa.
"A'a Inna ya za ai na sani, abinda rabon da
ayi abu tun watan shekaran jiya.
Ai sai Inna ta hau tafa hannu da Sallallami.
"Haka Auren ya mayarmin kai Mati sai
abinda Mace take so?Mene amfanin auren
idan ba za ka taki mace tamkar gona ba? Ya
kinan baƙar Munafuka sai kin faɗimin
abinda kike bawa dana da har kike juyashi
haka ko kuma ki tafi gidan Ubanki wallahi."
Ta faɗa tana jawo gashin Abule. Da sauri
Mati ya shiga tsakani yana faɗin "Sakarta
Inna."
Da dai Abule ta fito daga hannun Inna ai sai
tayi kan Nene dake ta sheka dariya a fusace
tana faɗin " Bazan fita Ni kaɗai ba sai da ke
bakar mujiya muga naki cikin mana in
gaske ne." Ta kai mata wawura.
Nene ta kankame jikinta tana ture Abule, ta
ɗaga hannu zatai naushi, Abule tayi nasarar
bankare hannun ta kuwa gatsa mata cizo a
hammata da dazunnan ta barbadawa
hammatar toka dan ta rage tsami, ai kuwa
bata ɗaga bakinta gurin nan ba sai da ta
cisge gashin hammatar Nene har jini yayi
tsartuwa.
Nene ta saki ihu tana dafe hammatarta.
Abule kuwa ta yi wuf! Ta fisgo zanin Nene
sai ga tullin tsummokara ɗaure a ciki. Wani
abin mamakin har da wani koren Gajeran
Wandon Mati da ya gaje shi tun gurin
ƙaninsa yasha doyin jakai da warin fitsari,
da Mati ya shafe shekara yana nemansa,
yau sai gashi a cikin Nene ɗaure...
*GIDAN MATI*
© BINGYEL FULANI & RUFAIDA OMAR
Inna ta hau tafa hannuwa tana salati iyakar
k'arfinta, kan ka ce me magulmatan
makwaftansu sun hau lek'e cike da al'ajabi.
"Yau na ga abinda ya fi karfina ni Uwar
biyu! Kai! Kai! Wallahi ba za ta sa6u ba,
Mati!"
Ta juya ga Mati wanda zufa ke ta
karyomasa, gabadaya ya susuce, daman ita
Abule ya san k'arya ce ta shukamasa
musamman da ya ji tana maidawa Delu irin
tuggun da ta shirya na iska, ita kuwa Nene
bai ta6a kawowa k'arya ta ke ba, a zatonsa
idan Abule ta ɓata rawarta da tsalle to yana
da mafaka a wajen Nene. Sai dai ashe
dukkansu taron na ayya ne.
"Eh dole ka rasa bakin magana mana! To
wallahi ba za ta sa6u ba! Ko ka k'ara aure ko
kuma ka saki kowace shegiya ta koma
akurkin ubanta. Za6i ya rage naka, yanzu na
ke son amsata."
Inna ta k'arashe tana gyara zaman siket
dinta na buje. Nene da Abule suka shiga
tashin hankali, kada fa su yi biyu babu.
"Kai nake sauraro ka tsayamin k'erere
kamar liman ya manta Fatiha."
Mati ya saci kallon Matansa, to da ya rasa
tafkekiyar gonar Inna da kuma gida ai ya
gwammace ya k'ara auren ya samu
haihuwa.
Ya mai da idanunsa kan Innarsa.
"Shikenan, ki nemo min mata."
Ai sai Inna ta rangad'a gud'a.
"Ayyiriririii! Haba ko kaifa, yanzu na
tabbatar da cewa kai jini na ne. Sai ka
shirya don kuwa yanzu za ka yi aure."
"To amma..."
"Amma me? Inna ta katseshi tana
harararsa.
"A'a wai dama gani na yi su biyun ma
mangalar jakai na biyu bata iya rikesu da
ita, shi ne nake tunanin kar ta ukun ta shigo
kuma idan ina cin abinci sau biyar a rana na
dawo sau uku."
"To batunu ƙiyama sarkin ci, in ce dai gidan
nan nawa ne?"
"Naki ne har ni d'inma." Ya faɗa yana dukar
da kai.
"To tunda ni zan ma auren mene na tunani?
Idan ta ciyarwa kake zan ƙarama akuya da
rago ka kiwa ta. Ina ce dai shi ke nan?" Ta
waigo ɓarin da su Abule ke tsaye.
"Ku kuma sai ku shirya don kuwa falleliyar
budurwa zan samar masa, ba irinku
zawarcin titi ba."
Bak'in ciki ya turnuk'e Nene da Abule.
Musamman Nene da ta tabbatar bata kai na
ta matancin ba, amman dai ai ita ce ta fari,
kuma ma ta toshe yanda ba za a gane ba,
don haka ta karkata baki.
"Allah na tuba ko dubu zai auro ba kamar ni
a zuciyarsa, ni ce dai Nenen Mati, kaf
k'auyennan an shai da soyayyarmu."
Inna ta bankamata harara kawai ta wuce
d'aki. Shi ma Mati da saurinsa ya fita ya hau
jakinsa ya fice. Abule ce ta saki shewa.
"Aikin banza wai bille a d'uwawu, duk dai
abinki bai sanya an fasa auroni ba, dad'in
abin ma ba abinda bansani ba. Ina ce da sa
hannun aljanu da 'yan bori a aurenki da shi
ko?"
Nene ta fusata, za ta kai mata bugu tuni
Abule ta nufi d'aki, ta mai da dubanta ga
masu lek'e.
"An yi asara munafukai da tsakar rana
babu ko kunya!"
Babu wacce ta tankamata acikinsu, ta
gama haukanta ta fad'a d'akinta.
BAYAN WATA BIYU
Ta faru ta k'are, duk wani shiri da gyare-
gyaren da ya dace a yi na zuwan Amaryar
Mati an kammala, amaryar ba wata bace
illah Faɗime d'iya ga aminiyar Inna, Ladidi.
Daidai da lefe Inna ce ta koma birni tare da
Ladidi suka haɗo. Abu kamar wasa dai aka
sanya biki sati biyu, duk irin borin Nene da
Abule bai sa an fasa ba, ganin babu Sarki sai
Allah ya sanya suka hak'ura.
An kawo Amarya lafiya lau da gud'a da
komai, cikin 'yan rakiyarta har da Shafa da
Delu.
Kwanan Amarya d'aya a gidan Inna ta
tattara ta koma birni da zummar sai nan da
sati biyu za ta k'ara lek'owa.
Nene na zaune ta tsefe kitsonta wanda
ya kusa shekara yayin da Abule ke kwance
saman tabarmar kaba tana jifanta da wak'e-
wak'en habaici tana ramawa suka tsinci
muryar Mati da Amaryarsa suna shek'a
uwar dariya, suka dubi juna da sauri kamar
wadanda aka mintsila suka nufi k'ofar d'akin
nata har suna bangaje juna, ƙarshe dai suka
nutsu suna lek'esu.
Amarya Faɗi ke kwance saman cinyar
Mati, shi kuma yana yagar tsire yana sa
mata a baki suna hirarsu cike da nishad'i.
Nene ta dafe kirjinta gami da had'iyar
yawu. Ba ta jira komai ba ta yi wuf ta shige
ganin haka Abule ta ja baya tana mai rike
ƙugu.
"Kan uban can! Wato Mati dama
amanarmu ku ke ci? To wallahi ba za ta
sa6u ba! Sai dai ayi raba daidai!"
Za ta d'auke ledar naman Faɗime ta cafke
hannunta ta mik'e tsaye.
Baki Nene ta saki ganin shigarta.
"Riga da wando a gidan nan? Jakar Uba!
Mati karuwar birni Innar ta auromaka ashe
banda labari?"
Harara Mati ya sakarmata bai ce komai ba
don wani sa'in yana shakkarta. Faɗi ta kauda
fuska gami da murgud'a bakinta da ya sha
jan baki.
"Ke Malama don Allah ki bar nan wallahi
warinki na tayarmin da zuciya. Ga dukkan
alamu dai ko wankan tsarki ba kya yi."
Ta saki hannunta.
"Kuma wallahi ki ka k'ara ta6a ledar nan sai
na miki ihun mahaukaciya. Ce miki akai Ni
haɗamammiya ce irinki? Ga naku kason can
a gefe dan bazan yarda Miji na ya tashi da
shanyayyen ɓarin jiki ba ranar gobe
ƙiyama."
Nene ta hau tafa hannu da shewa.
"Hehehe! Yau nake ganin bariki a gidan
nan, ashe kuwa yau wata za ta bi tsohon
najadu barzahu. Idan kin fasa kirana
mahaukaciya ba ki cika d'iyar Ladidi mai
siyar da kayan maye ba!"
Fad'in haka keda wuya, ta kai hannu za ta
d'auki ledar, Faɗime ta damk'i gashinta ta
mai da ta baya, tayi taga-taga za ta fadi
k'afar Mati dake ƙasa ya miƙe ta kwashe ta
sai gata Tim! A ƙasa tayi zaman 'yan bori.
Faɗi ta juya da Mini-minin idanuwanta ta
dubi Mati "Sannu Maigida bata dai jima
ciwo ba ko?"
Mati ya washe baki ya ce "Faɗi Amarya ina
gabanki ai bana jin ciwo."
Ta yi masa far! Da ido ta ce, "Mai gidana na
sha ce maka Timah zaka dinga kirana yarda
kawuna na birni ke faɗi.
Taɓɗijam! "Yau na ga sabon salo wai tafiya
bariki da Uwa" Cewar Abule daga bakin
ƙofa.
Amarya ta waigo ga Nene dake baje
ƙasa tana cije baki, "Ke kuma ki ci gaba da
shiga shirgi na, wallahi da ruwan sanyi zan
dafaki dan ban iya dambe tsakar gida ba,
balle na haifawar maigidana talauci, ku da
kuka saba kuje can ku ƙarata, ga tsiyarku
nan." Ta faɗa tana tura musu kasonsu na
tsire.
Muna zuwa.
MUN GA YABONKI YAKE GARKUWAR
MUNANA, MUNA GODIYA.
*GIDAN MATI*
©ƁINGYEL FULANI & RUFAIDA OMAR
"Maigidana Randar Zuciyata, Idan ka fita
kaje shagon Bakari Mai Ashana ka ce a baka
Makilin da Burushi." Mati ya washe baki
yana kallon kwalelen kanta da yasha zanen
shuku yana ta ƙamshin Karkar.
"Wani sabon Abinci ne muka samu
Amarya Timah?"
Ta yi far! Da ido "a'a kai dai jeka kawo za ka
ga abinda zan maka da shi."
"To shi ke nan, bari na yi wanka sai na fita
na siyomiki, kinsan tunda na sameki bana
iya fita banyi wanka ba.
Ta yi murmushi "Yauwa kama tunamin
abinda na ce zan nuna maka rannan, muje
Makewayin na maka kaga sai na cuɗamaka
baya ma."
Ta faɗa tana jawo hannunsa su fita. Fisgewa
ya yi yana nuna mata waje da baki, sai
kuma a hankali ya ce "Ki rufan asiri safiya
ce fa? Kinsan su Nene sun tashi kar ya zama
abinda zan kasa cin abinci yau."
"Haba Maigida Ni wallahi kanamin irin
wannan sai in dinga ganinka ragon maza,
ranar kwana nane fa, kuma baka shiga
haƙƙin kowa ba dan ka shiga Makewayi da
ni, Matarka ce ni, ba ta aro ba, ko ta titi,
kuma ko su ka shiga Makewayi da su ba
abinda zai dameni tunda na san aikin lada
ne.
Ya zare ido yana dubanta "Da gaske aikin
lada ne?"
"Kwarai kuwa, ai zaman Aure indai ba cuta
lada gare shi."
"Au to muje, amman dan Allah saɗaf-saɗaf
bana so Nene ko Abule su tsinkayi motsi
na.
"To shi ke nan muje" Ta faɗa tana me yin
gaba. Ruwa ta tuttula daga tulu a ɗan
kwatashin wankan na su, ta sunkutu ta yi
Banɗakin da shi, shi kuma Mati ya hau
kewaye tsakar gidan, da dai yaji kamar
babu motsi ko daga ɗakunansu, ai sai ya yi
wuf! Ya faɗa Makewayin.
Abule ta yi miƙa ba salati ba rufe baki, ta
miƙe tana mai riƙe mararta sakamakon
fitsarin da ya rike mata ita. A hankali ta fito
waje, ganin ba kowa ya sa ta tsugunna nan
gefen kwatamin tsakar gidan ta tsiyaya
abinta, ta wawwatsa ruwa ba ko cuɗawa ta
miƙe, za ta koma ɗaki ta jiyo kamar
kacaniya a Banɗaki, a zatonta Kajin
maƙotane ke kacaniya, sanin da ta yi sunsha
faɗawa wawakeken masansu azo a yi ta
hayaniya ya sa ta zari sanda da sauri ta yi
makewayin.
Sai dai fa turus! Ta yi tana sakin wani
razanannen Ihu ganin Mati zaune a dutse
daga shi sai gajeran wando, Amarya Timah
kuma duƙe saitin hammatar Mati da wani
ɗan ƙarfe a hannunta tana ta kwasar gashin
hammatar tana hura masa iska, shi kuma
yana dariya gami da fadin "Wai, ci gaba,
daɗi wallah."
A firgice Faɗi ta yada ɗan ƙarfen saboda
yadda ihun Abule ya kiɗimata, Abule kuwa
da ƙyar ta jawo sauran numfashinta tana
son daidai ta kanta, sai kuma ta ɗaga sanda
ba tai wata-wata ba ta saukewa Faɗi ita a
kafaɗarta.
"Sai na nakasaki baƙar mujiya me salon
karuwai kawai, dan Ubanki ce miki akai nan
bariki ne da zaki shiga wanka da Mijina, ko
kuwa ce miki akai ni ɗin zan yarda."
Ta sake ɗagawa za ta rafka mata Mati ya
riƙe sandan jiki na ɓari, "Karki kuma
dukanta, zan fa rama mata, ke Abule ki fa
fita idona da wanann jahilcin na ki, baki san
aikin lada ba ne take yi? Ba na son sakarci
fa." Ai sai ta yi baya tana kallon Mati sama
da ƙasa, kafin kuma ta rangwaɗa guɗa.
"Ahl lalle Mati yanzu na san ka ɗauru
tamau! a Minjaye, yanzu saboda wannan
me zubin botoramin kake cewa zaka dake
ni, Ni Abu? Da ka ce aikin Lada na ga dai
kwanana ya shiga daga sanda aka kira
assalatu."
"To na ji, yanzu dai wuce ki tafi haka ba zai
ƙarawa faruwa ba."
"Bazan tafi ba, Ni fa idan ba jini na fidda
mata ba bazan ji daidai ba."
"Haba Abu tawa, na ce kije dai, da daddare
zaki ji saƙo."
Ta ɓallawa Faɗime harara dake dafe da
kafaɗarta, ki sake gwadamana karuwanci
gidan nan ki gani, wallahi na lahira sai ya
fiki jin daɗi, shegiya da wani idonki kamar
tsaka ta saka kwai."
Af! Abu mai sauki, wai kura ta zo gidan
Maharbi, idan karuwancin ne ki gwada naki
mana mu gani, ai wallahi babu wata me
siffar Fanteka da ta isa ta hanani kula da
Mijina. Aikin lada ne yanzu na fara, wanann
sandar kuma bashi kika ci." Faɗi ta faɗa
tana murguda baki.
Sanin Mati ba zai barta ta sake taɓa Faɗi ba,
ya sa ta juya ɗakinta takaici fal ranta.
** ** **
Tun bayan da akayi cacar baki tsakanin
Abule da Fad'ime gidan ya k'ara kacamewa.
Tsakanin Abule da Nene sai ka rantse tun
da can kansu a had'e yake tsabar amincin da
suka k'ulla na munafunci. Koda suna cikin
habaice-habaicen su ne Fad'ime ta fito
tsakar gidan nan za su ɓige da shewa suna
watsamata bak'ak'en magana a fak'aice. Ko
kallon inda suke Fad'ime ba ta yi balle su
saka ran za ta tankamusu.
Ranar wata laraba wanda ya yi daidai da
cikar Inna kwanaki goma sha shida a birni,
Abule da Nene suna zaune a gaban d'akin
Abulen suna k'us-k'us tare da Shafa
makwafciyarsu. Shafa ke yi musu tallar
magungunan gyara na mata kala-kala. Ta
d'aga wani k'ullin gari tana fad'in.
"Kun ga wannan? Na rantse da daren
farkona da jikan Lamid'o yana da masifar
kyau. Ke wannan da ku ke gani sunansa 'Saki
Matar Uba'."
Nene da ke soshe-soshenta ta dubi Abule
suka yi wata iriyar shewa gami da cafkewa.
"Inda ranka ka sha kallo! Yo Allah na tuba
idan kura na magani ta yiwa kanta mana!"
Fad'in Abule.
"Atoh, taya ni gani! Wai Matar kwarto da
tallar maganin mata." Nene ta cafke.
Jin haka ya sanya Shafa kallonsu a fusace
kafin ta d'an kalli d'akin Fad'ime, ga dukkan
alamu batasan ma me suke yi ba. Ta maido
dubanta gare su cike da borin kunya ta ce.
"Oho dai, gwara ni akan ku, haka za ku
k'arata a borori."
Ta hau tattara komatsanta a sadda suka yo
mata ca! kowannensu da bak'ar maganar da
yake yarfamata. A daidai nan kuma Faɗi ta
fito daga ɗaki da gudu zuwa bakin
makwararar tsakar gida ta hau sheƙa amai
kamar ba gobe.
Nene ta miƙe ido waje tana tafa hannu,
yayin da Abule ta dafe kirji tana duban Faɗi
dake duƙe.
"Duka-Duka yau kwana nawane da Auren ni
Nene? Taya ni lissafi Abule.
Abule ta hau kasafta yatsun hannunta, sai
kuma ta zare ido waje.
"Duka-duka kwana goma sha bakwai kenan,
kar dai da ruɓaɓɓan kwai aka shigo?"
"Oh ni Nene, wannan wace irin haɗama ce
haka, ranar farko da rabon ciki kamar
marainiyar Karya? Ke kuma maƙaryaciya
kika cemin ba ai komai ba ranar jikin
tagarsu kika kwana?"
Abule ta ɓalla mata harara, "tuna dai, ke
kika cemin ranar da aka kawo ta jini take,
koma dai menene ni ban yarda da wannan
Salon ba, ban taɓajin cikin dake bayyana
kansa daidai da lissafin zuwan Amarya ba.
Sai dai idan da shi aka shi..." Nene ta yi
Wuf! Ta rufemata baki jin sallama kamar ta
Inna.
"Barta ta ƙarasa mana manyan Akuyoyi, ai
na dade tsaye ina sauraronku, wanda ya
gani dai shi ya ji kunya wai kallon fitsarin
makaho. Idan ba ku da kuke cikin ƙauye,
haihuwar ƙauye, renon ƙauye, auren
ƙauye, ina na taɓa ganin ana laɓewa
sabuwar Amarya? Kunyi asara wallahi Nene,
matsa ni na duba 'yar mutane, shashashai
masu wankin kai da ruwan daddawa, idan
ma da cikin ta shigo sai me? Na ce sai ƙaƙa?
Irin kune a jahannamar ma can ƙasan
wailun kuke. Sannu 'yarnan, sannu."
Inna ta k'arashe tana mai k'arasawa ga
Fad'ime wacce aman ya d'an lafawa.
Gefe guda ta ajiye akwatin kayanta, ta
yaye gyalenta ta dora saman akwatin kafin
ta tattare zaninta dinkin rafa siket. Ruwa ta
zubo a buta gami da mik'omata.
"Tayani duba Abule, toh wallahi ba za ta
saɓu ba bari Matin ya zo, ni ban yarda
wannan cikin nasa bane, ga dukkan alamu
dai mutum da abinsa ya zo, ai daman ni
nasan za'a rina, angama yawon ta zubar an
k'untso.."
"Ki ka k'ara magana a wajennan sai na
nunamaki ni ce nan na isa da Mijinki don
kuwa yana zuwa zan sanya ya sallamaki ga
tsohonki."
Nene ta yi d'if ta ja hannun Abule wacce
ranta ke ƙuna suka fad'a d'aka. Shafa kuma
da ke gefe kunne waje, tayi saɗaɗa ta fice
daga gidan.
"Mun shiga uku Abule, yanzu idan ta
tabbata matarnan juna biyu gareta ya za
mu yi?"
Fad'in Nene kenan yayinda gumi ke
tsirfomata. Abule wacce ta rasa bakin
magana tsabar bakin ciki da tashin hankali,
sai a lokacin ta iya bud'e bakinta ta ce.
"Hum, ni na rasa ma abin cewa wallahi."
Sallamar Mati ce a gidan ta katse su, suka
yi shiru suna sauraron yanda Inna ke
gayamasa rashin lafiyar Fad'ime da kuma
cewar Fad'imen na tunda ta zo ba ta ga
Al'adarta ba.
Muna zuwa
*GIDAN MATI*
BY BINGEL FULANI & RUFAIDA OMAR
Kamar wasa cikin Fad'ime ya tabbata, Inna
har Asibitin K'auyen ta mik'a ta tare da
Abule da Nene wadanda suka tik'e akan sai
sun bisu sun ji da kunnuwansu. Itama Innar
ba ta yi gigin hanasu ba don ta fi so su ji
abinda zai hana su bacci.
Ranar kam sun riga su yin gaba, zagi da
tsinuwa ba irin wanda Fad'ime da Inna basu
sha ba.
Tun daga wannan lokacin kuma sai sabon
tashin hankali da makirci ya k'ara ɓallewa a
gidan. Akwai ranar da Nene ta shigo da
Kuliya cikin gidan, sanin cewa Faɗime ba ta
so. Hakanan ta lallaɓa ta d'ora mata ita bisa
gadonta tana cikin barci. Allah ne ya tsare
da kwallayenta na jere basu zubo bisanta
ba, saboda yadda ta dinga razana tana bige-
bige a ɗakin. Ƙarshe dai Inna ta cece ta da
fitsari ya fiddo ta, ta juyo motsi ɓarin
Faɗimen. Shi kuwa Mati yana can ya saki
gañɗa ɗakin Abule. Sai washegari ne Inna
ta sanar masa, karshe dai ta yi maganin
abin da cewa duk wacce ta k'ara kawo wani
Abu gidan ko da Ɓera ne, ko ta jefi Faɗime
ko Mati da bak'ar magana to a bakin
aurenta. Da wannan aka samu bakinsu ya
rufu suka koma rara gefe, ƙarshe dai Nene
ta tattara ta tafi wani ƙauye bikin kanwar
kishiyar matar babanta.
Inna zaune gefen Fad'ime tana lalla6ata
ta samu ta ci kwad'on Zogalen da ta
had'amata, ita kuwa Abule tana tankad'e
Garin Tuwo tana wak'e-wak'en habaici.
Fitowar Nene daga bayan gida ya sanya suka
bita da kallo. Tayi daurin k'irji da tsohon
zanin da ta ci 'yanmatancinta da shi duk a
huje, k'asan duk ya rarake har idan ka zura
hannu a 6uli guda zai ta6o mazaunanta.
Fatarnan kallo daya za ka yi mishi kasan
akwai nakiyayyar d'aud'a da bai kammala
fita ba, jikinta kuwa babu alamar ya wanku.
Sai kyalli takeyi da nason datti da hamami
dake tashi.
"Ke jik'ar Maduga, wai wankan da ruwan
Taɓo ki ka yi shi ne?" Cewar Inna.
Juyowa ta yi ta mata murmushi, sai kuma
ta yi gaba tana murzo wata naɗaɗɗiyar
dauɗa a wuyanta.
"Ah'ah Nene magana fa nake miki." Fasa
ɗaga labulen kabar ta ta yi ta juyo tana
kallon Innar, sai kuma ta haɗe mata
hannuwa biyu tana roko alamun ta kyale ta.
"Uhm! Sabon salo, wai gemu a kafaɗa,
halan da kika je bikin rashin magana kika
koyo? To ai gaba ta kai mu, tuntub'en me
carbi" Inna ta faɗa tana riƙe hab'a.
Ganin haka ya sa Abule ture
tankaɗen gefe, ta mike zuwa dakin Nene.
Da shigarta ta same ta tsaye tana jan Jagira
a girarta me kama da ta Tunku. Ai sai ta yi
turus! Da mamaki tana ƙare mata kallo
daga ƙasa zuwa sama. Ta sha Atamfa koriya
fatau, da dinkin rigarta irin na Lema, wani
abin mamakin har kallabin irin na atamfar
ne, ba wai wari da wari ba. Kwalliya dai irin
wacce ko da tana Amarya ba ta taɓa yinta
ba. Sai ƙamshin man kadanya ke tashi da ta
mulkawa jikinta.
"Wannan kallon fa? Ban fa san irin kakannin
ki ba?" Ta faɗa tana kaɗawa Abule hannu
ganin yarda ta ƙame.
"A'a mamaki kawai nake, tunanina ko dai
ƙanwar Nene aka musaya mana.
"Uhm! Kibar mamaki, kawai nasihar da
Innata tamin kan zaman duniya da ƙiyama
nake ta tunanowa yau."
"Anya kuwa Nene? Ke din ce kike tuna
wanda ya mutu? Abokin kuka ai ba a
ɓoyemasa mutuwa. Ki faɗamin abinda ya
faru dake kika saki makaman haka? Ko duk
tsoron kar Innar Mati ta kora ki gida ne?"
Ai sai ta gundumo ashar tana me ture
ɗaurin kallabin da ta dade tana murd'ashi
dan ya yi kyau gefe. "Ni wallahi har kin
ɓatamin rai, tsohuwar banzar can zan ji
tsoro? To Talle Bodara ce ta ba ni maganin
Ɓari, sharuɗɗan cikar maganin shi ne ko
daka Ni Uwar Miji za ta yi kar na sake na
tanka ta. Kin ganshi a bakin Masai ake
barbaɗashi."
Ta karashe gami da bankad'a k'asan
katifarta, wani k'ulli ta fiddo a bak'ar leda ta
nunamata.
Abule ta washe baki don tsabar farinciki.
Ganin babu damar ihu ya sanya ta kaiwa
Nene runguma sai dai tun kan ta k'ara sa
had'a jikinta da na ta ta yi baya da sauri
tsabar tashin da Nene ke yi kamar mai
warin k'ashi.
"Dagaske ki ke yi?"
Nene ta ta6e bakinta.
"Ni idan na fad'i abu na fi son ki yarda, zan
miki k'arya ne? Nan da ki ke ganina ba ta
wasa bace ba. Bari ki gani, wuyarta dai
Fad'ime ta tsugunna saman Masai, ko
kwad'o ne a cikinta sai ya fad'o.
Jin haka suka saki shewa gami da cafkewa,
sai kuma da sauri suka rufe baki.
"Um kinga bari na je kafin wannan
Tsohowar karuwar birnin ta ankara."
Dariya Nene ta yi.
"Ai mukam Allah Ya had'amu da suruka."
Suka dara sannan Abule ta fice.
***
Shiru-shiru ciki zai zube anjima, gobe, bai
zube ba. Ko ciwon kai Fad'ime ba ta yi ba
ballantana a kai ga ciki.
Ganin haka Abule ta yanke gwada ta ta
sa'ar ko za'a dace. Nene ta ba ta goyon baya
d'ari bisa d'ari, da wannan ta shirya tafiyar
kwana daya da sunan ziyartar jikar abokiyar
kakarta.
Dawowarta akayi sa'a babu kowa sai Nene
a gidan da ke faman zazzaga bala'i ta
katanga tare da Delu wai Akuyar Delun ta
shigo ta cinyemata shanyar da ta yi ta
k'anzo.
Ganin Abule ba k'aramin dadi ta ji ba,
itace har da rungumarta tana tsalle, da ace
akwai mutane a gidan da sun sha mamaki.
Bayan sun k'ule a d'akin Abule ne ta hau
bata labarin abinda ta samo.
"Ba k'aramar wuya na sha ba in fad'amaki.
Ban ta6a rawar 'yan bori ba amma shege
la'antaccen bokannan sai da ya sanyani yi.
Amma tunda kwalliya za ta biya kud'in
sabulu da sauk'i. Bari ki gani."
Ta ɓalle ɓarin zaninta ta fiddo k'ullin
magani har biyu ta nunawa Nene.
"Ya ce na kwa6a lalle da garin na d'aurawa
Inna a k'afa don rufe bakinta. Shi kuma
wannan."
Ta nuna d'ayan,
"A had'a Lemon Zobarodo a sanyawa
Fad'ime a ciki ta shanye."
Shiru ya biyo baya kafin Nene ta jinjina
kai.
"Tabd'ijam! Aiki ja! Yanzu banda abinki ina
mu ina iya haka? Ni kinga banda kwaɗa
zobo da kuli ba abinda na sani kansa, sai
yau da na ji ana lemonsa, kema kuma na
san

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment