Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akan kowa ne harda baba baki bari ba, kinsan ma'anar su kuwa..... fauxie ta girgixa
kanta,

'masu shan jini ke sanya irin su, kinga Allah ya tsari baba ko.... Fauxie ta gyada Kai sai dai tayi
shiru tamkar wata Mai naxari, ta buďe baki xatayi mgn, Iman tace

'ďauko min wayana ďaki da hijab ďina kixo ki rakani maqota anyi rasuwa, ta tashi da sauri ta fice
bata jima ba sai gata ta dawo,

'Amma bada tedy xaki bini gidan gaisuwa ba ko? ta tunxuro baki kafin ta cillata Kan sofa, ta qagu
su fita tana son yawo a rayuwarta, fatyma ta tashi suka fice,

Gidan talakawa ne sosai masu buqata, sun rasa Mai gidan sai matar da ya bari da yara biyar, suna
dawowa Iman ta aika masu da buhun Shinkafa da dubu biyar akai, sosai sunji daďi kuma sunyi
godiya...

Tun lokacin da ta fahimci cikine da Ita take kaffa kaffa dashi tare da roqon Allah ya barmata shi,
shima Deedah Wannan Karon ya dage da addua yana son haihuwa....

Tafiya ta kamasu xuwa skt, inda xasuyi operation a wani gida, a motar haya suka tafi su uku ne sai
sauran passengers,

Akwai wani mutum dake cikin motar tunda ya shiga bashi da aiki sai xagin barayi shida na kusa
dashi, su Deedah na jinsa,

Driver ke tambayarsa meyasa kake xaginsu haka,

'bari driver basu min komai ba amma suna ban haushi, ai dana haifi barawo gwanda na haifi shege,

wai akwai hasararra uwa a duniya kamar wacce ta haifi barawo, sai da gaban Ahmed na faďi
xuciyarsa na bugawa tunowa da Inna, ya fakaici ido yana kallon sauran abokansa suma ransu a
bace,

Suka cigaba da Mgnr su,
ďayan yace ai ina haihuwar barawo kashe shi xnyi dan baida amfani, gwanda ďan siyasa da barawo,

Driver yace baxan haifi ďa in kashe shi ba sai dai na nema masu shariya, wani yanada dalilin xama
barawo kawai Allah ya shiryesu yasa su daina....

Ba Wanda yace Amin, sun iso gwadabawa suka sauke wannan mutumin da abokinsa, wadanda ke
tare da Deedah suma suka ce nan xasu sauka, sai akabar Deedah da driver kawai,

Su kuma suka bi bayan wancan mutumin ba tare da yasani ba sai da suka ga gidansa tukunna suka
shiga motar kasuwa,

Ahmed Kuwa sai da sukayi nisa a jeji kana ya tsaida driver tare da fito da bindigarsa sosai ya
tsorata cikinsa ya ďauki kuka jikin sa har rawa yake,

'kayi haquri bansan Menayi ba,
'banace kayi wani abu tunda baka xageni ba, ni barawo ne ka min adduar shiriya naji daďi, sauran
dakaga sun fita yan uwana ne sunbi waďancan mutane suga gidansu, ga wannan(ya bashi dubu
hamsin) driver ya karba jikinsa na rawa yana godiya tare da gode Allah da ba xaginsa yayi ba da
Yanxu sai dai ya kashe shi a Wannan jejin ba Wanda xai sani ya kashe banxa, shiyasa mutum ya
shiga motar kasuwa baisan mutane ba baisan wane irine su ba mutum ko Aljan ya xauna yana xage
xage.... Allah ya taimakesa amma yana tsananin mamakin wannan mutum ace barawo ne, idan ka
ganshi natsatse dashi shigarsa ta mutunci ba Kamar sauran abokansa ba, fari ne kyakkyawa dashi,
Allah ne masanin gaibu akan xamansa barawo yaja motar da qarfi yabar gurin.

A sokoto suka sake haďuwa, bayan sun gama fashinsu a wani company sunci nasara suka juyo
xuwa gidan wancan abokin wannan mutumin,

Deedah bai shiga gidan ba yana daga waje kasancewar dare ne, suka shiga suka masa dukan tsiya
suka fito kana suka nufi gidan wannan mutumin dayafi xaginsu,

Wannan Karon da Deedah suka shiga gidan dan yaji xafin mutumin Mgnr sa nayi masa yawo a
kwakwalwa,
_ba hasararra uwa kamar wacce ta haifi barawo_, da kansa ya harbi mutumin a qafa, ya rinqa
kururuwa yana neman taimako yar'sa mace ďaya daga cikinsu ya shiga yayi raping ďinta, Deedah
yasa belt ya xane mutumin sosai jina jina shi kansa jikinsa ya baci da jini ya sunkuya yana faďin,

'ka gane ko mu su Waye? Mutumin ya girgixa kansa, Ahmed yace

'Mune Waďanda Muka shigo Mota da kai ďaxu Muke xaune dakai kana xaginmu kana xagin
iyayenmu alhali Kuma kace barayin basuyima komai ba amma ka xauna kana xaginsu, Yanxu
barayin Sunyima Abinda baxaka taba mantawa idan ka shiga mota gobe sai ka xagesu da dalili
suka juya suka fice mutumin ya fashe da kuka sosai yana nadama, magana ma Jari ce......

A xaton Deedah koda xaije gida xai samesu sunyi barci tunda ynxu sundaina jiransa ga mamakinsa
yana shiga falon sukayi 4 eyes da fauxie da pencil a hannunta,

'lah anty jini a jikin yaya yaji ciwo, da sauri Iman ta juya tana kallonsa lokaci ďaya xukatansu na
buga shi na tsoro ita kuma na xargin jinin menene?
[2/28, 8:37 PM] +234 810 732 0127: BABANA DA MIJINA

©Fertymerh Xarah 💞

9

Dawowa daga labari ~~~

Tafito daga toilet bayan ta ďauro arwalla, inda yake ma bata kalla ba ta sanya hijab ďinta ta fara
sallah,

Deedah na daga kwance yana kallonta sai ya sami kansa da saukowa ya shiga toilet yayi arwalla ya
bi ta...

Bayan wani lokaci sun gama ta tashi batare da ta cire hijab ďin ba taje ta kwanta haďe da juya masa
baya, jikinsa a sanyaye ya tashi yayi light off yabi bayanta ya kwanta haďe da juyo da Ita, she is
crying....

'why Iman, meke faruwa? Ko motsi batayi ba illa hawaye dake qara xuba a idanuwanta... Ya cire
mata hijabin haďe da qanqameta,

'I hurt my Iman, kiyi haquri akan Wanda kike,i hurt you and I will change, I promise to change
Iman ya qara matseta jikinsa, har lokacin bata tanka ba illa qoqarin kwace jikinta da take yi,

Ya tashi xaune yana kallonta,
'why ol dis...., me Kuma nayi Yanxu, nayi tunanin mun gama mgn dake tun a falo, ta tashi tana
kallonsa sai Kuma taji ta kasa furta masa komai saboda bacin rai da damuwa, he knows it yasan
damuwarta duk baxai wuce fitar dare da rashin bata haqqinta ba, tor ya xaiyi shi kansa a ynxu baya
so yana nadamar xama barawo bayan ga aikinsa, idan yayi yunqurin barin aikin oga nas xai ďauki
mummunan mataki akansa kamar yanda ya faďa,

Kallonta yake yana observing da ido da xuciya, gaba ďaya yanayinta ya sauya ya nuna wata mace
dake axabtuwa da soyayya da sha'awa Mai yawa,

Amma kawaicinta da kau da kai ya rinjayi komai, tana haquri dashi shi kansa ya Shaida, ba kowace
mace xata xauna da miji haka ba shiyasa yake qara son ta, ya riqo hannunta Idanunsa cikin nata,

Baxan gaji da baki haquri ba, ki yafemin Iman, xnyi qoqari na rage fitar I promise you.....

*

Washe gari bayan ta tashi daga barci tayi miqa a hankali tare da koro addua,
_Alhamdulillahil lazee ahyana ba'adama amatana wa ilaihir nushour,_ ta miqa hannu side ďin

Ahmed taji sa wayam, ta buďe idanuwanta,
She is late, da sauri ta diro ta faďa toilet inda ta same sa ciki yana wanka,

A tare suka fito kowane ďaure da towel, ita iya cinyoyinta shi Kuma iya qugunsa, jikine dashi na
Manya Kuma qasaitattun maza,

dogo ne sosai Mai kyau sura ta ko'ina, a tare suke shirinsu, qoqarinsu kada suyi lattin fita,

Wardrobe ta buďe ta ďauko mashi baqaqen Spanish suit Mai haďe da farin tie, ta ajiye masa akan
gado kana ta soma shirinta cikin riga da zani na Atampha ta ďora labcoat akai da ďan qaramin gyale
tayi rolling, idanunta sanye da farin glass, lokaci ďaya suka gama shirinsu, yaja dogon hancinta in
appreciation ďin irin kulawar da take mishi,

'kinyi kyau dear Allah ya barmin ke, murmushi tayi haďe da manna mishi kyakkyawar sumba a qirji
ya qara rungumeta,

Yana riqe da hannunta suka sauko step dai dai lokacin da Fauxiya da mai Kula da Ita suka fito tana
ďauke da qatuwar school bag ďin ta, murmushi tayi lokacin da suka haďa ido da Ahmed,

'morning sister...
taje da gudu ta rungumeshi tana fadin
'morning yaya... ya ďauke ta yana murmushi haďe da Jan hancinta,
'morning my baby....

Dijeh ta gaidasu kana tayi waje da jakar Fauxiya,

A tare suka xauna akan dining table, Fauxiya baxata tsaya guri ďaya ba, idan taci na wannan ta
dawo taci na wannan da haka hr suka kammala suka fito su uku a tare,

Driver na jiran Fauxiya kai tsaye ta shiga motar tana ďaga masu hannu suma suna mata bye bye,

suka kalli juna haďe da yin murmushi ta shiga motar ta shima ya shiga tasa,

Tana gaba yana biye da Ita hr suka xo FMC birnin kebbi, sai da yaga shigarta kana ya juya tasa
motar xuwa first bank dama kullum sai ya rakata yaga shigarta asibiti yake tafiyarshi.
[2/28, 8:38 PM] +234 810 732 0127: BABANA DA MIJINA

©fertymerh Xarah

15

Jikinsa a sanyaye ya ďauke kansa batare da ya sake kallonsu ba ya nufi hanyar step...

Fauxie ta dubi fatyma bakinta a buďe,

'Anty kin tuna sanda kika je daukata Skul har kika sami anayima wani duka jini ya fito a jikinsa
ko....

'eh tor me akayi,
'anty sata yayi akayi masa duka, shima yaya sata yayi akayi masa wannan dukan...... Caraf akan
kunne Deedah ya juyo da sauri yana kallonta dai dai lokacin da Iman ta bige mata baki tana faďin,

'yi min shiru shashasha, mijina ba barawo bane,

Fauxie ta soma hawaye tana riqe da bakinta, Iman ta juya tana kallonsa kafin tabi bayansa, jikinsa
har rawa yake da jin kalaman fauxie suna isa ďakin ta fisgosa....

'kagayamin wannan jinin na miye, ina kaje? Cikin dakewa yake kallonta,

'Accident wata mata tayi da yaro a bayanta, sunji rauni sosai yaron dana ďauka ne jikina ya lalace
haka ya faďa yana qara kallon jikinsa,

Mata da rauni, nan da nan ta nuna tausayawar ta akan abin, ta soma cire masa rigar tana faďin,

'kayi abin kirki daka taimakesu, Allah xai taimakeka watarana, abinda mutum ya shuka shi xai girba
hairan ko shairan, muje kayi wanka, ya bita a sanyaye cikin tausayinta...

Fauxie na xaune tunxure da baki ta sauko, tana ganinta ta ďaure fuska tamau Kada ta đauki abin da
wasa

'ke nagane bakinki baxai taba faďin alkhairi ba, kince baba baxai shiga aljanna ba yau gashi kin
Kira mijina barawo why Fauxiya?

'Anty kiyi haquri .....
'Mtseww sai anyi mgn Kice haquri, tashi ki tattara colours ďinnan kimaidasu Kada gobe kixo kina
damuna,

Ta tashi tana haďawa bakinta a tunxure ta nufi hanyar step, ta juya tana kallon Iman bata kallonta
sai ta shige inda Ahmed yana xaune yana amsa waya, yana ganinta yayi Saurin katse wayar yana
kallonta,

'yaya Ina ne kaji ciwo? Ya ďaure fuska

'ban sani ba,
'please yaya kayi haquri baxan qara ba,
'nida kika ce barawo ne fauxie, ta tsugunna gabansa,
'Ni bance ba yaya, nace kayi sata ne Kuma anty tace Bakayi ba shikenan.... ya ďauke kansa cikin
mamakinta, ta tsaresa sai ya nuna mata inda yaji ciwo, shi yarinyar ynxu mamaki take bashi tana
girma tana wayo, ynda ya gayawa Iman haka ya gayamata,

'good Samaritan, ta soma dariya ta fice yabi bayanta da kallo....

Daren ranar bai je ko ina ba yana gida tare da fauxie duk assignment ďin ta shi yayi mata, Sa'eed
abokin Deedah yaxo Wanda suke aiki tare a banki, sai da yawa yakanxo taya Iman hira idan ya
sami Deedah baya nan, sai shaquwa ta musamman ta shiga tsakaninsa da Iman, yana tayata hira da
shawarwari akan xamantakewarta da Deedah na rashin xamansa gida saboda shi kansa baisan
taqamaiman inda Ahmed ke xuwa ba tunda 6 suke baro bank,

Shima Sa'eed yakan xauna yabaiwa Iman lbrn matarsa salima irin yanda take nuna halin ko in kula
dashi suna da yara biyu bata Kula dasu kullum tana kwance komai sai mai aiki, shi namiji ne Mai
matuqar son kulawa ga mace amma bai samu ba daga matarsa kamar yanda Iman ke buqatar
kulawar mijinta bata samu ba.....

A Wannan ranar bayan Deedah da fauxie sun gama assignment yayiwa Sa'eed Sallama sai da safe
suka haye shida fauxie sama yabar Iman da Sa'eed, can you imagine ynda xaka bar matarka da
abokinka saboda rashin kulawa,

Daga Iman har Sa'eed kallon mamaki suka bishi dashi, sunyi xaton xai xauna ayi hirar da shine
amma sai suka ga sabanin haka, Hakan yasa Sa'eed yayi mata Sallama ya tashi ya fice da makullin
motarsa a hannunsa dan baiga dacewar xamansa da Ita a Wannan lokacin da mijinta ke gida ba sai
dai yana matuqar mamakin Deedah irin Wannan mata kamar Iman dayake nuna halin ko in kula
akan ta, inama itace matarsa ba salima ba da ya more a rayuwa,

Da Wannan tunanin ya qaraso gidan, parking yayi ya ďauki laptop ďinsa ya shiga cikin gidan,
hayaniyar yaransa yaji agun mai aiki sai da yaje ya gansu kafin ya nufi ďakin salima tana nan
kwance da waya a hannunta,

Sallama yayi bataji ba hankalinta nakan waya, tsakin dayaja ya janyo hankalinta garesa kallo ďaya
tayi masa ya ďauke dubanta garesa,

'Ashe ka dawo, bai tankata ba ya nufi toilet,

wannan tambayar raini ce take masa idan da sabo ya saba, bai taba fita ya dawo tayi masa sannu da
xuwa ba ballantana irin tarairayar nan da mata ke yiwa miji yaji daďi,

Ya fito toilet ďin har lokacin tana kwance abinta ,

'Salima..... ya Kira sunanta cikin husky voice ďin sa,

Uhm... ta amsa batare da ta Kalle sa ba, yayi shiru yana kallonta da mamaki,

'idan abinci kake mawa yana Kan dinning kayiwa Indo mgn ta xuba ma ni Wlhy duk agajiye nike....

'aikin me kikayi duk yau bayan kwanciya, ke Wai sai yaushe xaki cnxa rayuwarki Kisan Abinda ya
dace ga rayuwar auren ki, ba Indo nake aure ba ke nake aure dan me Wai komai sai Kice Indo xata
min ke kina kwance.... ta tashi tana kallonsa,

'Bismillahi ai kadawo qorafi baxai qare ba indai kana gidannan, Indo dole nasanyata tayima tunda
yar aiki ce, aure na xo yi ba bauta ba Yakamata kadaina min faďa haka kana takurani xaman aure
naxo yi....

'tir da wannan xaman auren naki, indai haka ake xaman aure da nadaina shi Kuwa, ke baxaki bani
haqqina ba sai kin ga dama idan Ina a matse ne sai na biya kuďi sai kace ba mata na ajiye ba, baxaki
iya gyara gurin kwanciyar auren kiba sai mai aiki, baxaki iya kula da yaranki ba sai Mai aiki, baxaki
iya Kula da gidanki ba sai Mai aiki, abincima sai mai aiki wannan wace irin rayuwace har sai

yaushe xaki canxa ne.... taja tsaki ta tashi tayi ficewarta tana taunar cingam yabita da kallo kawai
yana girgixa kansa....

*

Xaman falon ya gundireta sai ta tashi tayi kitchen tana kiran adama,

Da sauri ta fito tana goge hannunta da tsumma,
'baki gama aikin bane har ynxu?
'nagama hajiya Ina gyara kifi ne gobe fauxie tace dashi xataje Skul,
'Hmmmm fauxie kenan ta gyada Kai ta fice,

Fauxie ta diro daga Saman gado tana faďin,
'bye bros gudnyt, yana xaune akan stool yana duba wasu takardu na gurin aikinsa, ya ďago yana
kallonta
'gudnyt baby.....dai dai lokacin da Iman ta shigo,

'kika ce da kifi xakije Skul Gobe,
'eh anty...
'ashe gobe kowa xai kyamace ki kenan, ki bari idan kin dawo kici inba haka ba xaki dinga wari
acikin friends ďin ki, ta juya tana kallon Deedah..

'Wai hakane yaya? ya gyada kansa alamar eh,
'tor anty Kice ta barshi sai na dawo,
'kije dijeh ke kaďai take jira ku kwanta daga nan sai ki gayamata,
'gudnyt anty,
'Nyt ta juya ta fice da gudu.......

[2/28, 8:38 PM] +234 810 732 0127: Babana da mijina.....

©fertymerh Xarah 💞

16

A hankali ta maida kallonta garesa shima ita yake kallo kafin ya taso xuwa gareta hannunta ya
riqa suka xauna bakin gado,

'kin canxa sosai Iman, naga sai haske kike yi miye sirrin.. ya faďa haďe da Kanne mata ido ďaya,
tayi murmushi tana wasa da yatsun hannunsa kafin ta dubesa idanunta sunyi rau rau kamar xatayi
kuka,

'cikine ka tayani addua ya tsaya, ya saki wani murmushi mai bayyana irin farin cikin da mutum
yake ciki ya rung xuwa jikinsa,

'Insha Allah xai tsaya, ina son yara sosai Iman Allah bai bani ba,

'nafika sanin haka muyi addua Allah ya tsaida wannan....... ya ja dogon hancinta yana murmushi
haďe da cusa hannunsa cikin rigarta,

'bari muji xai kai wata nawa a yanxu, ta soma dariya tana ture hannunsa ya kwantar da Ita......,

Washe gari sun gama shirinsu tsaf na fita aiki, a tare suka sauko inda suka sami Dijeh na rigima da
fauxie harda kukanta fafur taqi ta sanya uniform,

'barka da safiya hajiya... ta faďa tana kallonta cikin girmamawa,

'barka... Kukan me kike yi Kuma,

'taqi ta sanya uniform hajiya...
'why fauxie? ke meyasa kullum akaxo shirinki sai anyi rigima dake, cikin kuka ta soma mgn,
'Anty ni baxan je Skul ba xan biki asibiti...

Deedah yace amma baby jiya fa naji kina Mgnr xakije da kifi Skul har anty ta hanaki, tor ynxu me
xai hana miki xuwa Skul,

'yaya ni baxan je ba kace sister taje dani hospital, Iman taja tsaki ta fice tana fadin

'ba inda xanje dake... Ahmed ya karbi uniform hannun dijeh da socks ďin ta da takalmi kana ya
ďauke ta yafita harabar gidan da Ita,

Akan Mota ya ďora ta har lokacin kuka take hrda kiran baba,

Deedah ya Kira driver,
'idan sun tashi Skul by one ka kaita asibiti inda Iman xasu dawo tare,

'shikenan yallabai.... Ya dubeta,
'idan Kuma bakiyi shiru ba xnce ya dawo dake Kada yaje dake inda sister, tayi shiru tana ajiyar
xuciya, ya Sanya mata uniform ďin harda socks and sandals ďinta ya sauko da Ita daga motar,

'jira inxo, tana tsaye gurin yaje ya karbo abincinta da skulbag ďinta....

Yana tsaye gurin har suka fice tana yimasa bye bye, ya sauke ajiyar xuciya haďe da girgixa kansa
yana faďin Fauxiya rigima.

1:00pm

Ta fito daga labour room, tana tafe da waya a hannunta tana amsa Kira harta iso consultant,

'likita bokan turai acewar Dr Fulani,

Dr Umayma tace daga ina kike haka kina xufa , Iman ta xauna tana share gumi,

'daga Gynaec nake labour room, wata yarinyace qarama ga dukkan alamu bata isa aure suka yi
mata, she is too young,

Allah ya taimakesu sunxo asibiti da wuri da Babu mamaki sai VVF ya sameta,

Fulani ta dubeta tana faďin,
'uwar na raye,

'tana raye har yaron amma kam tasha da kyar dan dai da sauran kwanaki a gaba ne, inkin ganta
gwani tausayi early marriage,

'Umayma tace mutumin qauye kenan, ga maxan ba haquri,

Iman tace dan ma bakiga mijin ba babban mutum ne Wai shine Mai gari yana da ďan iliminsa
shiyasa Wai suka xo da Ita asibiti,

'ai Kuwa da ta mutu a banxa cewar Fulani dake cin samosa, Iman ta ďan dubeta,

'sister xn sami sobo.....

'yau Kuma sobo xakisha cewar Dr Umayma,

'Kinsan Mai ciki da Kwaďayi inji Fulani bayan ta miqa mata robar sobo, sukayi dariya dai dai
lokacin fauxie ta shigo da gudu ta faďa jikinta ta baya,

'miss you sister,

'Kada kisa na faďi bakiga mutane bane kin shigo ba Sallama, ta koma da sauri tana dariya,

Sallama tayi ta shigo tana faďin, gud afternoon anty Fulani & anty Umayma,

Suka amsa mata, fauxie rigima, taje ta xauna kusa da Iman tana faďin,

'Anty xn sha sobo...
'Fulani ta bata wani sobo tana faďin gashi fauxie kibar anty tasha nata, tana dariya ta karba,

'Tnkuuuu anty, ta juya tana kallon Iman,

'Anty shi baba baya shan sobo a battle ko cup yafisha a kwarya naganshi ranar yana sha ya ce na
fita d......

Nan take Iman ta kware saboda ruďewa ta shiga tari sosai ba kakkautawa.....

My wattpad Phertymerh1


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment