Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kayi mana addua, ya ďago yana kallon yaran bawai bayason yaransa bane son
xuciya da neman duniya suka rufe masa ido, yayi matuqar tausayawa yaran,

Shikenan musa ka Kula da qaninka, Allah ya tashe ku lfy ya raba ku da sharrin mutum....

Suka ce Amin,

Ismail yace baba ni gobe baxan tsaya lesson ba ka gayawa driver yaje ya ďauke ni da sauri,

Meyasa Ismail...
Mami tace xataje dani da Fauxiya unguwa banda musa,

Yace tor shikenan xanyi masa magana, musa yace
Baba baka cika min alqawari na ba, kace xakaje dani waje nayi karatu irin anty Iman

Fatyma ai tagama karatun kaima xakaje ni xan kaika da kaina,

Yaron yayi tsalle ya rungumeshi, thank you father Ina sonka..... Jikin Baban yayi sanyi sosai da
kyar ya iya rungume yaron a jikinsa kafin ya rakasu har dakinsu da kanshi, yana labe yana kallon
sanda suke game suna shan yoghurt Wanda a ciki yayi siddabarun sa, basu jima ba Kuwa suka xube
gurin suna kakaki kumfa na soma Fita bakinsu, yaje da sauri ya ďauke yoghurt ďin ya musanya shi
da Wanda baida komai ya fice, idan xakayi masa kallon natsuwa a Wannan lokacin xaka fahimci
baya cikin hayyacinsa ko kaďan....

Mami ta fito daga ďakinta Kai tsaye study room ta nufa ta sami fatyma da tulin takardu a gabanta,
gefenta kofin coffee ne da take korawa akai akai...

Iman ya kamata ki riqa bawa kanki hutu ki samawa xuciyarki sauqi, wannan karatun yayi yawa
haka ke kullum akan takarda....

ta ďago idanunta da kyar tana kallon mahaifiyarta idanunta sunyi jawur sosai sun nuna kalar barci,

Mami you won't understand,karatun likita is quite different da sauran karatun, kibari nan da shekara
ďaya na kammala karatuna na xama cikakkiyar likita xn fara maki surgery..

Surgery? ta tambaya da mamaki tana kallonta, surgery akan me?

Tayi far da ido tana kallon ta cikin shigar wasa irin ta ya'da uwa,
Tace Mami har ma sai na gaya miki kibari lokacin yaxo xaki sani...

Mami tayi dariya tana tattara littafan dake gabanta,
Ko Alhuda huda yana samawa xuciyarsa sauqi Iman, ki tashi kije ki kwanta,

Ta tashi tana miqa, a tare suka fito suna tafe suna hira, baba na ďakinsa yana jinsu hr lokacin da yaji
Faty na fadin,

Mami Ina ya'yanki ko sunyi barci bnji hayaniyar game ba,

Me yiwuwa haka ne, amma bara na dubasu, ta nufi ďakin Faty na bayanta, yana daga window yana
kallonsu har suka shiga, basu jima ba ya jiyo qarar fatyma tana kiran baba... ya koma yayi
kwanciyarsa kamar mai barcin gaske,

Iya ruďewa sun ruďe bama kamar Mami da ta xama mutum mutum, batasan meke faruwa akan
ya'yan taba, suna haka baba ya shigo cikin yanayin barci sosai ya nuna damuwarsa hrda kuka
yayi.....

Tun daga lokacin abubuwa sun soma faruwa, walwala da jin daďi sun rageshi a gidan, ga kuďi
kamar me, basu taba xargin sa akan Kuďin da yanda yake kashe dukiya ba saboda sun San dan
siyasa ne,

Iman da Fauxiya ne kaďai suka rage masu a ynxu duniya, yana son su fiye da xaton mai karatu haka
yake ji komai xai iya dan ganin farin cikinsu....

2 years later

Siyasa ta tashi sai faman xabe ake ana campaign, baba yaje wa Sima da buqatar Wannan Karon
yana son matsayinsa na mataimakin gwamna kowane mutum ne yaci gwamna a birnin kebbi yana
so yaxama mataimakinsa, wani xabe mai xuwa yana so ya fito takarar shugaban qasa....

Sosai sima tayi dariya wadda tayi matuqar raxana su,

Buqatar ka xata biya Abdallah, xakaci siyasa idan har xaka bada jinin matar ka......

Sosai ya raxana da jin kalamanta, bai taba xaton akwai abinda xai rabashi da Mami a ynxu ba
saboda ta xamo ginshiqin rayuwarsa,

Auren soyayya sukayi, tun saurayi da budurwa, yana sonta tana sonsa.....

har ya dawo gida bashida sukuni tunaninsa yanda xai bada jinin Mami, ya kasa barci sai faman juye
juye yake akan gado, duk abinnan da yake akan idonta tana kwance tana kallonsa,

Ta matso a hankali xuwa garesa,
Meke damun ka alhaji, yayi firgigit yana kallonta da mamaki,

Kada dai hr ynxu kana tunanin su musa ne? Ya girgixa kansa hawaye suka xubo masa, hankalinta
yayi matuqar tashi,

Meke faruwa meke damunka? Ya janyota sosai jikinsa ya rungumeta...
Ki yafe min, ki yafe min Amina,

Jikinta ya ďauki rawa,
Ba abinda kayimin a xamana dakai, inma kayi na yafe ma nima ka yafemin,

Ya sauke ajiyar xuciya yana qanqame da ita yana jin sonta har cikin ransa Kuma har lokacin bai
daina hawaye ba,

Ta maida kanta qirjinsa hankalinta ya kasa kwanciya da yanayin mijinta tabbas akwai abinda ke
damunsa yake boye mata, Gobe da safe xata tuntubesa ya gaya mata damuwarsa....

Suna haka hr barci ya ďauke ta, ya sumbaceta sosai kafin ya janyo wani Jan kyalle qarqashin pillow
ďinsa....
[2/28, 8:34 PM] +234 810 732 0127: BABANA DA MIJINA

©fertymerh Xarah 💞

7

Ta rumtse idanuwanta,
Yh is true as her age ya kamata ace tana da aure yanxu, baba will be happy duk da baya mata Mgnr
auren tasan yana so ne,

Duk Acikin likitocin ita kaďai ce budurwa bayan nurses da yawa sun girmeta wasu Kuma age mate
ďin tane, tana da maneman aure da yawa but she don't have interest on them, ta kunna fitilar ďakin
tana kallon fauxie,

Abubuwa da yawa take tunawa game da rayuwarta da qanwarta, komai suke so suna samu kuďi da
jin daďi, haka komai yi masu akeyi, tun daga kan girki, wanki, shara, kula da gidan da komai ma
baba ya Sanya masu yi masu, sai dai sun rasa kulawarsa basu samun Isashen lokaci daga garesa,
kullum yana hanyar tafiya baya ďebe masu kewar UWA, hawaye suka sumulyo mata, ta qanqame
qanwarta dole tayi aure kodan farin cikinta da qanwarta, dole tayi aure ko damuwarta xata ragu ta
sami soyayyar miji tunda bata sami ta iyaye ba.......

Washe gari tare da Fauxiya suka nufi asibiti, sai tsalle take tana jin daďi, nurses ďin dana Santa
suka soma murmushi,

Yau Fauxiya a asibiti, Ashe akwai rigima..
Fatyma murmushi kawai take hr suka iso office ďinta, ta ajiye Jakarta juyowar da xatayi ba Fauxiya
ba dalilinta, dama tasan a rina,

Ta xauna tana duba files ďin patient ďin da xata duba na ranar, sosai ta dade akansu kafin ta gama,
shiru ba alamar fauxie, ta tashi tabi bayanta inda take xato nan ta sameta office ďin Dr Merah tana
xaune a gefensa da sweet a hannunta sai surutu take masa yana duba patient ďinsa, sai kayi xaton
yar sa ce ta cikinsa

Bata Bari ta ganta ba ta juya da sauri ta nufi a&e,

Su biyu ne aciki shida abokinsa Sa'eed gurin aikin su ďaya a bank,

Da Sallama ta shiga idanunta sanye cikin farin glass, hannuwanta a aljihun Labcoat ďinta, sosai tayi
kyau,

Suka amsa sallamar suna kallonta, bata yarda sun haďa ido ba, drip ta xubawa idanu tana tambayar
ya Mai jiki,

Sa'eed ya amsa da jiki Alhamdulillah, ta maida hankalinta kan haďa masa magani,

Sa'eed ya tashi yana fadin,
Aboki is olmost tym, by 8 xn dawo, ya gyada Kai yana kallonsa kafin ya fice,

Dr. Save a life.... taji ya faďa daga inda yake kwance, kusan faďuwa ta tashi yi, batasan meke
damun patient ďin ta ba, hr lokacin bata tanka ba sai ma qoqarin yaqi da xuciyarta takeyi, ta juyo
haďe da miqa masa magani ya karba, ta ďauko masa swan ta bashi hr lokacin bata kallesa ba
shikuma Idanunsa akanta, bayan ya gama sha, ta duba file ďin sa yana da sauran allura uku, ta dafe
goshinta da hannunta.....

A duniya idan akwai abinda Deedah ya tsana allura, indai akan allura ne yana da rakin wannan, bai
tsoron bindiga kamar yanda yake tsoronta..

Yana Ganin ta ďauko allura ya tashi xaune, wannan Karon fuskarsa a yamutse,

Ummi bana son allura, na roqeki karki min, ta juyo da mamaki tana kallonsa Abinda ta gani a
idanuwansa ya nuna mata yes he mean it, baya son allura, batayi mamaki ba cos tasha samun case
irin Wannan, tayi far da ido bayan ta cire glass ďin idonta,

Ni Kuma sai nayi ma allura, Iman not Ummi pls.... dai dai lokacin Merah ya shigo tare da Fauxiya a
bayansa,

Ta juya tana kallonsa bayan ta sanardashi abinda ke faruwa, Merah ya karbi allura,

Haka mukayi fama dashi jiya, gashi namiji har namiji amma yana tsoron allura kibari xnyi masa....

So funny, ta soma dariya sosai ba kakkautawa Wanda rabonta da irin dariyar tun Mami na da rai,
shi kansa Merah ta bashi mamaki bai taba xaton tana dariya haka ba, taja hannun Fauxiya suka fita,

Daga inda take xaune take jiyo rigimarsu da Ahmed Wanda da kyar da suďin goshi yayi masa suna

xaune Merah ya fito,

Kinyi laifi likita, yiwa patient dariya,
Am sorry bansan yanda xnyi bane.....ya fice ta tashi ta shiga ďakin, suna haďa ido ta ďauki wata
dariya harda sa hannu tana rufe bakinta, Fauxiya bata San komai ba amma sai ta taya yayarta dariya
Wanda ya janyo hankalin Deedah xuwa gareta

Itama farace kamar fatyma sai dai tafi fatyma kyau sosai, ita yarinyar wacece ko yar'ta ce,nooo ai
yaji jiya tace ita da qanwart..... tunaninsa ya Katse lokacin da yaji fauxie na faďin

Anty meyasa kike dariya, tayi shiru tana faďin ba komai,

Please tell me sister.... ta juyo tana kallonta cikin xare ido
Nace babu menene...
Fauxie tayi shiru tana kallonta ta juya tana faďin ki jirani Ina xuwa idan naxo ban same ki ba sai na
dake ki Kuma baxan qara xuwa dake ba,

Tana jin haka ta nemi guri ta xauna,ta juya ta fice, Idanunsa akan su suna haďa ido da ita tayi Saurin
ďauke kanta cikin jin tsoronsa saboda raunin dake goshinsa,

'little girl..... ta juyo tana kallonsa,
'Your name...da kyar ta iya buďa bakinta
'Fauxiya Abdallah... ya gyada kansa,
'xo kiji Fauxiya, kamar baxata je ba ta matsa kaďan a tsorace,
'how old are you? Idanunta suka yi rau kamar xatayi kuka,
'6yrs...
Ya xare ido yana kallonta da mamaki, yanayin ta ya nuna a tsorace take dashi sai ya janyota xuwa
jikinsa ya ďorata akan qafafunsa, da sannu ya riqa janta da Wasa harta saki jiki sosai dashi tana
dariya hrda kwantawa a jikinsa,

'Ya sunanka....
'Kice yayaaa,
'yaya xakaje dani inda mamin ka, ya girgixa kansa
'A'ah
'meyasa ?
'mamina tana duka sosai...
'to ni baxan je ba...
'kina so ki xauna dani, mu riqa wasa tare... ta gyada kai da sauri
'idan ummi taxo Kice ta aureni,
'Wacece ummi, yayi shiru kafin
'yace your sister... ta soma dariya tana kallonsa,
'ita ba Ummi sunan taba kace Anty Iman dai dai lokacin ta shigo,idanunta na sauka akansu, ta ďaure
fuska tana kallon Fauxiya, yanayinta ya sanyata saukowa a jikinsa da sauri tana faďin,

Anty shine ya ďorani, Wai sunansa yaya..
'kisa takalmi kixo muje inba haka ba xn tafi na barki anan, ta sanya takalmin da sauri tana faďin,

'Anty Wai inji yaya ki aure sa, yace ku..... ta katseta cikin tsawa..
'shut up Fauxiya... tayi shiru tana kallonsa kafin ta maida kallonta gareta, da qarfi ta fisgi hannunta
suka fice, tabe bakinsa kawai yayi ya maida Idanunsa ya lumshe...
[2/28, 8:35 PM] +234 810 732 0127: Babana da mijina

©fertymerh Xarah

11

Yinin ranar duk a kwance tayi sa, Fauxiya na tare da Ita, sallah kawai ke tadata daga inda take

kwance,

Bayan magrib Deedah ya shigo gidan, yayi mamakin rashin samunta a falo, yaje ďakin fauxie bata
nan sai ya haura sama,

Da Sallama ya shiga ďakin, Iman tayi barci Fauxiya ce ta amsa sallamar tana xaune kusa da ita da
drawing book akan qafafunta hannunta riqe da pencil, da murmushi take kallonsa Wanda ya
bayyanar da farincikin ganinsa,

'welcome brother....
'thanks my baby, ya ajiye kayan hannunsa yana faďin..
'drawing kike yi haka, me kike xanawa.. tayi murmushi tana kallon xanen kafin ta dubesa,
'A house, uncle yace mu xana gida it's an assignment, sister ba lfy shine baxata min ba, sai da
gabansa na faďi

'Iman ba lfy, meya sameta, ya soma taba jikinta, Fauxiya ta tashi da littafi a hannunta ta fita tana
faďin Ina xuwa yaya xakamin assignment ďin...

bai tankata ba ya tallafo kan Iman, jikinta xafi rau ta buďe idanuwanta tana kallonsa kafin ta
maidasu ruf,
'meke damunki,baki lfy shine baki Kira kin sanardani ba, jin bata tankaba ya ďauketa ya ďora ta
akan gado,
'kinsha magani? Ta girgixa kanta,
'tor meyasa, Ana ciwo ba magani, nan ma tayi shiru, wayarsa ta ďauki qara, oga nas ya gani a
rubuce kamar baxai ďauka ba sai Kuma ya Kara a kunnesa,
'shikenan gani xuwa, shine kawai abinda taji ya faďa batare daya qara bi ta kanta ba yasa kai ya
fice, ta bisa da idanu tana kallonsa hawaye na xubo mata,

Fauxie na xaune falo taga fitowarsa, ta tashi da sauri ta haura sama da littafinta a hannunta,

Ganin fatyma na kuka yasanyata rau rau da idanu Kamar xatayi kuka,

'Anty meyasa kike kuka? ta soma share mata hawaye,
'anty kince idan mutum bai lfy baya kuka kuma abinci yake ci, kina kuka kinqi cin abinci inje inkira
baba ya kaiki asibiti, ta girgixa kanta,

'baba bai dawo ba, kinyi assignment ďin? ta girgixa kanta,

'A'a sai brother ya dawo xamuyi tare, fatyma ta tashi xaune da kyar kanta har wani nauyi yake mata,

'naji kamar ana kiran sallar isha'i idan nayi sallah xn maki, kin mayi magrib Kuwa Fauxiya? ta
tunxure bakinta,

'A'ah anty...
'meyasa, wai ke meyasa bakyason sallah ne, kullum sai nace kije kiyi sallah, ta qara shagwabe fuska
'Anty ai ni qaramace sai naxama babba xanyi sallah, ta ďaure fuska sosai tana kallonta,
'see you, shekara takwas ne baki girma, kitashi kije kiyi sallah tun ban dake kiba marar wayau, ta
tashi tana hawaye sosai ta cillar da pencil ďin hannunta, fatyma tabi bayanta sanin halinta ita
batasan meyasa yarinyar batason sallah ba Kamar wata tababbiya,

A tare sukayo arwalla suka fito... ko kafin fatyma ta gama sallah ita harta gama magrib da isha'i, ai
Kuwa tana sallamewa taja kunnenta,

'kiji tsoron Allah Fauxiya, baa wasa da sallah tun kina qanqanuwar ki bakyason sallah ai da matsala,
gayamin dame dame kike karantawa a sallar, idanunta taf da hawaye take kallonta,

'Anty fatiha da nas nayi,
'Kice Wlhy..
'wallahi anty... ta saki kunnenta tana kallonta,
'duk mai wasa da sallah wuta xa'a sanyashi baxai shiga aljannah ba, kuma Duk Wanda bayason
sallah xai shiga wuta, bakisan banbancinki da Anty John da uncle obi sallah ba, ko kingansu suna
sallah? ta girgixa kanta, Christian basu sallah sai musulmi, tell me ke Wacece...

'A Muslim.... yauwa babyn brother sai Kiriqa sallah kinji... ta gyada Kai tana kallonta cikin
gamsuwa...

'Anty ni xan shiga aljanna, ke xaki shiga aljanna amma baba baxai shiga aljanna ba..... da sauri ta
ďago tana kallonta cikin tsananin mamaki,

'meyasa?
'shi baba baya sallah, ni bana gani yanayi, anty yana sa wani kaya ya shiga ďaki Inaje shiga ya
hanani..

'karna qara ji a bakinki, baba xai shiga aljanna yana sallah mana, inbanda abinki xai shiga ďaki xaki
bisa...

'Amma anty ai....
'shut up... ta katseta, bana son surutunki marar amfani, ta janyo abinci tana ci kafin kace me tasoma
kwarara amai a gun, Fauxiya na kanta tana yi mata sannu, sosai ta jigata tace
'kiramin Adama ta gyara gurin nan, ta fita da gudu sai gata ta dawo da adama sai sannu suke mata...

Har 12 Deedah bai dawo ba hakama mahaifinta, Fauxiya ce ta kasa runtsawa ganin halin da yayarta
take ciki yayi xaune tana kallonta,

'Fauxiya je inda dijeh ta haďa maki tea ki kawo min, ta sauka da gudu ta fita bata jima ba sai gata da
cup a hannunta ta hau gadon tana faďin,

'anty kisha magani irin Wanda kike bani,
'A'ah ni banason magani... Fauxiya taje ta ďauko irin Wanda tasan tana bata Inbata lfy, panadol
'Pls anty kisha... ganin Fauxiya ta damu sosai ta karba tasha da swan kafin ta ďora tea akai, sai da ya
kwanta mata kana ta janyo Fauxiya a jikinta,

'xo ki kwanta nasan kina jin barci, Gobe ba Skul idan naji sauqi xuwa Sunday xn maki assignment
ďin, Fauxiya ta kwanta a jikinta tana murmushi,

Ta jima sosai kafin barci ya ďauketa, kallonta take cike da tausayin kansu, ba kulawar uba
ballantana ta miji, ta tabbata da Mami na da rai baxata barta haka ba, ta soma hawaye sosai haďe da
qanqameta Fauxiya jikinta....
[2/28, 8:35 PM] +234 810 732 0127: BABANA DA MIJINA

©fertymerh Xarah 💞

10

Alhaji Abdallah xaune a qasaitaccen falon sa duk abin duniya ya dame sa ya rasa inda xai tsoma
ransa yaji daďi,

Sau biyu yana ďaukar cikinta yana bayarwa ga matsafarsu Gashi wani bincike ya nuna Iman tana
ďauke da wani cikin Wanda daga ita hr Ahmed basu San dashi ba,

Sima ta nuna tana son cikin, tabbas Wannan ma sai ya xube, shin haka rayuwar yar'sa xata kasance
bata haihuwa da tasami ciki ya xubar? Yayi wa kansa wannan tambayar,

'Nooooooo ya faďa a hankali gudun securities ďinsa su jiyosa, Idanunsa sunyi jawur har jijiyoyin
kansa sun fito goshinsa raďau raďau,

Yana son Fatyma yana tsoron wani abu ya sameta musamman a mahaifarta amma ya xaiyi mecece
mafita?

Yayi shiru Idanunsa suna fitar da kwalla lokacin dayaji muryar sima na faďin,
'cikin mukeso Kuma dole abamu idan ba haka xamu ďauki rayuwarta gaba ki ďaya mu baka dukiya
da Abinda kake so na duniya..... Aka kyalkyace da dariya, yayi firgigit daga tunanin da yake yana
kallon falon dariyarta ce kawai yakeji ta ko ina......,

*

Fitowar ta kenan daga ďakin haihuwa, yau a gajiye take sosai tunda taxo bata xauna ba, ga Jiri da
Xaxxabi da take ji Wanda baida nasaba da yunwa anata tunanin kenan,

Ta sami gu ta xauna inda ta sami Dr Fulani, ta dafe goshinta da hannuwanta biyu,

Successful doctor..... yanda suke kiranta idan suna tsokanarta cos da wuya ta karbi haihuwa da
hannunta yaron ya mutu ko uwar sabanin wasu likitocin da har jima yaro sukeyi gurin haihuwa, a
yanda take a natse haka ma take aikinta a natse shiyasa nurses da yawa suke son aiki da Ita, ba
ďaure fuska ko Wulaqanci kowa faram faram take dashi bama kamar patient ďin,

'ya akayi Dr fatyma...cewar Fulani tana kallonta,

Ta ďan ja guntun tsaki kafin ta janye hannunta a goshinta,
'bansan meke damuna ba yunwa ko gajiya... Fulani tace
'harda damuwa fatyma, tor ya xakiyi da yanda Allah ya tsara miki rayuwarki idan lokaci yayi xaki
ganki kin haihuwa kidaina sa damuwa a xuciyarki, Iman ta girgixa kanta kafin kace me hawaye sun
soma xubo mata Wanda hankalin Fulani ya tashi...

'ba haihuwa bace damuwa ta Fulani, damuwata *babana da mijina*, bansan ya xanyi da rayuwata
ba, ta fashe da kuka mai tsanani haďe da maida kanta jikin table tana kuka sosai Mai tsuma xuciya,

'innalillahi wa inna ilaihir raji'un shine Abinda Fulani ke furtawa jikinta na soma rawa tunda suke
da Iman bata taba ganin hawayen ta ba ballantana irin Wannan Kukan tabbas ko menene babban
al'amari ne....

Ta dawo kusa da ita ta xauna haďe da dafata,
'meyasa fatyma, wannan kuka haka komai yayi tsanani maganinsa Allah,

Ta tsaida Kukan da take ta hanyar goge hawayen fuskarta, ta buďe Jakarta ta ciro hijabinta ta
warware ta sanya kana ta cire labcoat ďinta da gyalenta ta maida a jaka ta tashi tana kallon Fulani,
'xanje gida likita sai Kuma gobe idan Allah yasa muna da rabon gani. Fulani ta tashi tana kallonta,

'baxaki gayamin damuwar ki ba? Fatyma tayi murmushi sosai tana kallonta Kamar wacce bata da
damuwa,

'ba komai Fulani, idan ma da akwai xn sanardake, ta juya ta fice Fulani ta bita da ido tasan ta da
Xurfin ciki Dama baxata gayamata damuwarta ba amma meyasa babanta da mijinta ne damuwarta,

Tasan babanta Mai kudin gaske ne Kuma ďan siyasa ita shaidace akan yanda yake sonta ita da
Fauxiya hakama mijinta tasan yana matuqar sonta tor menene abin damuwa akansu, meyasa take
xubar da hawaye akansu, Allah ne masanin gaibu acewar xuciyarta.......

Tana yin parking Fauxiya ta fito da gudu da tedy a hannunta, tana rufe motar taji ta rungumeta ta
baya, ta juya da kyar tana kallonta,

'oh Fauxiya ai sai ki kadani...
'anty kinyi kuka ne, meyasa ki kuka tambayar fauxie taji daga Sama, ta riqa hannunta suka soma
tafiya tana faďin,
'idanuna ke ciwo, kinci abinci? ta gyada Kai tana kallonta,
'Anty an bani assignment a skul,
'shikenan anjima xamuyi tare....

Wanka tayi, tana yin sallah ta xube nan ta kwanta saboda Xaxxabi dake damunta,

Fauxiya ta shigo da plate ďin abinci a hannunta kai tsaye inda take kwance ta nufa, ta tsugunna tana
faďin...

'Anty ki tashi kici abinci, Kindawo baki ci abinci ba shine na ďebo maki...

Ta buďe idanuwanta tana kallon fauxie sai taga duk ta damu, plate ďin ta kalla, nan take xuciyarta
na soma tashi, da sauri ta tashi ta nufi toilet tana kwararo amai, hakan Kuwa ya rikita fauxie ta
sameta toilet ta riqa ďaya hannunta tana yi mata sannu,

As a professional doctor kai tsaye ta gano halin da take, cikine da Ita, is she happy or not? bata sani
ba, sai ta soma hawaye a fakaice kada fauxie ta ganta a Ranta Kuma addua take Allah ya bar mata
cikin....
[2/28, 8:36 PM] +234 810 732 0127: BABANA DA MIJINA

©Fertymerh Xarah

13

Dedicated dis page to Maryam Kwaise & kdeey

Tana shiga ďakin ta faďa Kan gado tana kuka, kuka take sosai fiye da minti biyar hr lokacin tana
jiwo muryar mahaifinta da mijinta amma batasan me suke mgn akai ba, ta tashi da kyar ta shiga
toilet,

Fitowar ta tayi dai dai da shigowarsa ďakin, Idanunsa akanta tsananin son ta da tausayinta ya
mamaye xuciyarsa musamman yau da yasan ko Waye mahaifinta, yaga mahaifinta dumu dumu
cikin shigar matsafa shiyasa yace ya boye sirrinsa ga yar'sa,

A sanyaye ya qarasa jikin bango ya jingina jikinsa har rawa yake,

'Salihar mace kamar Iman, mai haquri da tawakkali batayi dacen uba da miji ba, mahaifinta matsafi
ni mijinta barawo, kwallah ta taru a idanuwansa yayi Saurin sharewa,

Kwanciya tayi batare da ta Kalle sa ba, yaje ya xauna a kusa da ita,

'Iman K....... tayi Saurin katsesa,

'enough Pls Deedah kada ka dameni, ka riqe kalamanka bana son ji, haquri ne nagaji da ji, ta tashi
fuuuu ta fito daga ďakin, kai tsaye ďakin fauxie ta nufa tayi kwanciyarta.....

2 days~

Har lokacin Ahmed ya kasa samun ta, taqi ta sauko akan fushin da take dashi, babban tashin
hankalinsa a ynxu ranar da duk ta gano ko shi Waye, ya furxar da iska daga bakinsa yana kallonta
dawowarsa kenan daga aiki, yau sai dai ayi ta taqare ya gaji da wannan fushin Nata,

Yayi switching wayarsa Kada akirasa, ďakin su ya nufa fauxie tabi bayansa,

'yaya ka dawo baka siyo min komai ba yau Kuma baba bayanan,

'na manta gobe xnje dake na siyo maki, meya hana miki barci yau haka? ta dubi Iman ta dake
qoqarin rufe falon kafin ta maida kallonta garesa,

'anty ta tsaidani, ta koyamin karatuna inba haka ba gobe malamin islamiyar mu xai min duka,

'Fyn an gud, sister ta kyauta, ya soma taka step ďin yana riqe da hannunta,

'yaya yau baxakaje training bane, ya juyo yana kallonta da mamaki ta tsareshi da idanuwa tana jiran
amsa, ya ďauke kansa da kyar ya iya amsa mata

'baxan je ba,
'meyasa ta qara tambayarsa?
'saboda yau baxaa yi ba,
'amma yaya kai baa nuna ka a tv kana ball why? Wannan Karon bai amsata ba ya nufi dakinta da
Ita, dijeh harta kwanta sai dai batayi barci ba,

'ki sauya mata kayanta xuwa na barci Kuma ki tabbatar da kunyi addua kafin ku kwanta,

'tor yallabai mungode, ya dubi fauxie

'night baby.... Murmushi tayi tana kallonsa,

'night too.... Ya juya ya fice, wanka yayi ya fito ya shirya cikin kayan barci har lokacin Iman bata
kwanta ba tana xaune bakin gado da wani file a hannunta baisan kona miye ba amma fuskarta ba
walwala ya lura fushi takeyi dashi sosai,

Baya son duk wani abu da xai bata ranta fitar dare ce xai rage ya bata irin kulawar da takeso, don
haka yau bayajin xai jurewa fushinta domin ta fushinta yana da weakness sosai he truly loves his
wife,

Sai ya qarasa gabanta ya tsugunna haďe da riqo hannunta duka biyu ya haďa danashi, ya langabar
da kansa idanuwansa sun juye sun rikiďe ja,

'Am sorry Iman, na kasance mai laifi a gurinki ina neman afuwarki kiyi haquri, tayi shiru bata tanka
ba kuma bata kallesa ba,

'fitar dare ce, xn rage sosai fiye da tunaninki, bana so ki xargeni da aikata alfasha, mijinki salihi ne
bayan kwallo ba abin da nake fita yi, ina so ki kyautata xato mai kyau agareni, xn cigaba da xama
dake dan farin cikin ki ina sonki Iman.... ya faďa haďe da miqa tafin hannunsa tayi masa kiss, idan
tayi yasan ta haqura idan batayi ba kuma bata haqura ba,

Ta Cira Kai ta dubeshi a hankali sai ya bata tausayi dan Numfashi kanshi a wahale yake furzar
dashi, sauri da sauri,

Amma Jan aji irin namu na mata sai ta qara tsuke fuskarta ta balla mishi harara wadda inka lura ba
komai ne acikinta ba face tsananin son mijinta, xuciya da gangar jiki ma sun Shaida...

Irin kallon da take masa yasan ta haqura, yasan halin kayanshi ya qara langabar da kansa cikin
shigar tausayi haďe da qara miqa mata tafin hannunsa,

Ba musu ta sumbaci hannun tana murmushi, ya ja dogon hancinta bayan ya xagaye hannuwansa a
qugunta yana kallonta,

Wannan file ďin a ajiye shi ayi aikin lada wify.....
[2/28, 8:36 PM] +234 810 732 0127: BABANA DA MIJINA

©Fertymerh Xarah

14

Tun daga lokacin ya rage fita sosai wani sa'in sai tayi barci ya saďaďa ya fice,

Wani lokacin bata sanin fitarsa da dawowarsa, sai ta dawo cikin walwalarta ta soma samun sauqin
mijinta saura mahaifinta,

Akwai wani lokaci suna xaune ita da fauxie suna kallon wani film na matsafa suna sanye da kaya
jajjaye, buďar bakin fauxie sai cewa tayi..

'lah anty duba irin kayan baba, fatyma ta ďan dubeta,

'ke shirmenki

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment