Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gobe zan kawo tawa ziyarar ta musan man a she bazansamu gatan kulani ba, kai Yaya ba fa haka nake nufi ba kazo mana wallahi Yaya nayi kewarka sosai, yaji daWin kalaminta yace ok nagode.

Rabee'a!
Mama takira sunan ta, tacigaba da faWin kifito kuyi Sallama kinshige Waki kina ta shewa keka dai a waya.

Ta datse wayan tace "to Mama ganinan ta fito cikin jin kunyar Mami wadda tace a,a Mama kibita ahankali, kika sani ko da sirikina take waya?.

Ta sunkuyar da kanta ™asa tana Murmushi, Fatima a zaure take cewa "Rabee'a wai ina Yaya Saif ne naga tunda mukazo bangan saba, Rabee'a tai Murmishi ta dube ta kamar yadda tai mata tambayar cikin raWa haka itama ta bata amsa da cewa"Yana Kano tunbayan dawowata gida yakoma".


Fatima ta rausayar da kai tace" Allah ya temaka".

"Ameen".

Kai Masha Allah kalmar da tafito daga bakinsa kenan sadda suka jero ita da Fatima sai yake ganin Fatima Mummunace a kan Rabee'ar sa.

Har suka Kara so bakin Motar cike da ladabi ya fito ya gaida Mama, Mama ta amsa tare da faWin "karka ™ara zuwa gidan nan katsaya a waje ai nan gidan kune dan anzama Waya".

yace" to Mama nagode"
Ya faWa yana Satan kallonta Sam hankalinta bai kansa suna cen suna magana ™asa ™asa sai faman Murmishi suke, yamike yace" ya isa haka Fatima suruntun na gida bai isaba?"

Sukai ido huWu da shi yayi mata wani irin kallo maicike da wasu sakwanni masu wuyar faWa, ta Wauke idonta daga nasa ta sauke wata ajiyar zuciya wadda sai da su Mami suka dubeta, wata kunyace takara rufe ta da kyar ta soma motsa Wan ™aramin bakinta tace "Munyini lafiya ya aiki?.

Lafiya kawai yace yana Murmishi yafaWa Mota yatayar suka shiga sukai Sallama kamin suka dauki hanya sai gida kowannensu xuciyarsa fes, Musan man ma Mami wadda tuni tagano Soyayya tsantsa da kauna a idon Rabee'a da d'an nata.
*********
Malam Hussain kam yaji sakon Rabee'a a gun Abokinsa inda yau yacaralle yadauki na gwagwa ansha kyau Sosai Matarsa tadubesa tace "Baban Haneef yau kuma ina zuwa ko dai yau Kanwata tayi kirane?".

Malam Hussain a kai wani Murmishi yace "kai Lauratu kina burgeni wallahi shiyasa nake alfahari da ke nasan bazaki juyamin baya ba wajen neman Aurena da Rabee'a ba shiyasa nake Kara baki waje na musan man a zuciyata, a yau zani zance wajen Rabee'a karo na Farko, yafaWa yaname lumshe idonsa, wani tuk'uk'in kishine yataso mata ak'ahon zuciyarta, a gabanta yake kiran sunan wata duk da dama indai tana son hira da shi tai tsaho to ta ambaci Rabee'a, wannan wata Kalan Rabee'a ce wadda ta sace min zuciyar mini?".

Lauratu meye kuma?

Muryasa kenan wadda tadawo da ita daga dankaramin tunanin da ya afkata, ta k'ak'aro Murmishi Wanda iyakarsa labbanta tace " To Malamina a dawo Lafiya ka gai damin K'anwata da kyau".

Zataji Insha Allah yafad'a tare da Sakai waje yanufi hanyar anguwarsu Rabee'a cike da farinciki ya shirya kalamai na banhakuri da nasiha da kalaman Soyayya irin na Ustazai.

Sai dai kash wata katuwar Mota yagani anyi Parking a kofar gidan ya hango Fararan Hak'oranta inda wani me mashin ya haska masa ita tana Dariya ta jingina da Murfin Motar, wani jiri ne yataso masa lokaci guda bai shiryaba shin waye wannan ita da tace ta daina Soyayya shin me ta mayar da shi soko ko me?
Ya kasa Matsawa ko ina itakam bata masan yanayiba yajuyane ko yakarasa yaji kuma wannan waye ko ko ya juya?...........!


To mai karatu nima bari na barku da Hussaini kutayashi alhini sanna kutayashi bashi shawara nidai nayi nan>Ø#Ý>Ø#Ý>Ø#Ý.

*Maman Khaleel*

*Šin kuce
'þ.*
NI KE DA GASKIYA

=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü

Na
Rabee'art Muhammad
(Maman Khaleel)

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.


Page 97

___K'afafuwansa sunsoma yimasa nauyi, a ransa yace yazama dole Rabee'a ta za6a ko ni ko me wannan Mota, yak'arasa cike da kwarin gwiwa wajen, Yayi masu Sallama, Arifullah ya amsa fuskarsa bayabo ba fallasa, yadubi Rabee'a wadda yaga ta sunkuyar da kanta kasa, kirjinta naduka tara-tara dan fargaba, Ya Malam Hussain zai mata haka ai tabashi no dinta, bayannan yanxu ita yazaitai da Arifullah dikda shid'in ba Sonta yake ba yana mata son kanwa da Yayan ta ne,har sukai musabaha Rabee'a batasaniba dan tayi nisa wajen tunani, Muryar Malam Hussain ce tadawo da ita dagon tunanin da ta afka, inda yake cewa "Rabee'a inba damuwa inason kiban aron minti biyu".

Da sauri ta d'ago kai tabisa da ido kawai, shikuma ya Matsa inda ya a je Frajen dinsa ya hau yahada kansa da gwiwa.

Rabee'a kam takasa ko Motsi, dik da son da take ma Malam Hussain amma kuma ta kasa koda Motsi ne kar Arifullah yayi fushi da ita.

Bakiji abinda saurayinki yafad'a ba, ai yakamata kiji da shi dan innine bazan lamunci hakaba, Malama kije kinmin tsaye a ka, Arifullah ya fad'a yana kauda kansa gefe.

tarasa bakin magana to meyake nufi da hakan? mekalaman sa suke nufine, in shine bazai lamuntaba, kuma gabadaya yacanza yawani sukurkuce kamar ba shine yanzu suketa nishad'i ba?

Ta soma tafiya ahankali har ta isa wajen da Malam, cikin siririyar Muryarta kamar mai shirin yimasa rad'a tace "Assalamu a laikum".

Yad'ago rinan nun idanunsa Wanda tuni suka canza launi daga fari zuwa jajaja, jin muryarta yasa zuciyar soma jin wani sanyi yaratsasa, duk da yana cikin wani yanayi natsananin kishi, amma bai hanasa yin Murmishi ba, ya amsa, tare da fad'in "Rabee'a Amaryar Mai rabo, shikuma wannan waye?".

Tace Malam munyini lafiya ya iyalin?

Tafad'a tare da kawar da tanbayarsa.

Yace "sudai lafiya nikam Sam babu", yafad'a tare da d'aga kafada.

Yaso bata Dariya amma ta dake tace" to Masha Allah".

Yace "ok bada muwa ni nasan yadda kika ajeni Rabee'a, nasan yanzu kindai na Sona, shiyasa kiketa min hanya hanya inba haka ba, meyasa kike kula wancan mutumin?".

Wai ke haryanxu bazaki daina san abin duniya ba haryazu iyayenki basu daddaraba a she Rabee'a?

Wani takaicine ya lullubeta tare da takaicin furucinsa, karar Motar Arifullah yasata saurin waigawa yafigeta da karfi yabad'a masu k'ura.

Wani takaicin ya kamata duk duniya bata da sama da Arifullah shine mutum na Farko Wanda yasamarmata farinciki yatemaketa lokacin da take neman temako, shine sanadiyyar samun lafiyar mahaifina, Motar kawai take kallo harya bar layin, tabbas ko ba'afadamata tasan tana son Arifullah so mai tsanani irin son da shikansa Malam Hussain baisamu kwatankwacinsa ba.

"Rabee'a inason sanin wannan waye kigayamin nasan matsayina awajanki".

Ta soma share hawayen da suka soma mata zarya a kumatunta, kamin tace " Shine Wanda nake So shine Wanda nake da burin Aura Wanda zai zauna dani batare da korafiba ko wata Mummunan fahimta ko yazargi Iyayena akan wani abu na da ban Wanda su Sam basuda masaniya kansa. "

Tanagama Fad'a tajuya tabarsa nan tsaye yana ta faman juya kalaminta, sai alokacin Yagane lalle baikamata yasaka iyayenta acikin kishinsa nababu gaira babu dalili, yadafa kansa shidakansa yasan yarasa Rabee'a bazata sauraresa ba domin yacima iyayenta zarafi akan kishinsa na banxa.

Da kyar yatada mashin d'insa ya bar layin xuciyarsa a cunkushe.

"Rabee'a kam tayi kuka sosai meyasa ita batada sa'a ne arayuwarta, to waima meyasa tafad'a ma Malam Hussain tana son Arifullah , shin shiyagayamata yanasonta, karfa tai saki nadafe tayi ba wan ba k'ani (wai karatun d'ankama) shin yanxu yazatayi ina zata sakanta taji dadi? ".

Haka tai ta kuka babu mai lallashi bacci kam yau sai dai b'arawo sudukkansu.

Dankuwa Arifullah a nasa ganin da gan-gan Rabee'a ta ce masa yazo gidan su dan tanunamasa iyakarsa to tabbas yau yagani, dama haka so yake dama haka mutum yakeji idan yaga Masoyiyarsa abin kaunarsa da wani kato can bashiba yakeji a zuciyarsa, meyasa bakafada minba kina son wani ba Rabee'a meyasa! Meyasa!!!.

Wata zuciyarsace tai saurin dawo dashi hayyacinsa na fad'in karka zargeta batada lefi kokad'an dan ita ba kafad'a mata kanasonta ba dan haka kome tama lefinkane, da ka fad'a mata da haka bata faruba, kanada daman yanxu da ka hanzarta kafad'a mata kana Sonta, inba haka ba kanaji kana gani wani can zai kwace ma ita, ko Uncle d'inka dan bashinan ne dayanzu anyi angama dan yana matukar Son ta shima, kawai malam indai kana Son ta to kacire komi kafito mata da zallar Son ta inko kaki, to sai dai ka dauki na annabawa wato hakuri.

Ya nisa tare da daukan shawarar zuciyarsa takarshe da tabashi yazama Dole ya da safe in Allah ya kai mu ya sanar da su Mami komi.

Tashi yayi yafad'a band'aki ya dauro alwala yasoma nafilfilu bayan ya idar yasoma koro addu'a samun nasara akan Allah yasa Rabee'a ta zab'eshi a matsayin Abokin Rayuwa kamin ya shafa, yabi faffad'an gadonsa ya kwanta yaja lallausan bargonsa.

(To sai muce Arifullah Allah yabamu Alkhairi Ameen.)

***********

Washe gari da safe Rabee'a ta tashi da wani matsanan cin Zazzab'i gawani ciwon kai Mai zafi da kyar ta iya yin sallah Asuba, tajawo wayan ta talatsa Number Yayana amma har tagama ringing =ØÝ ba'a d'aga ba, abinda Rabee'a batasaniba shine Arifullah a Mota ya bar wayansa shiyasa bai daga wayanba tun daren jiya take kiransa dan ta bashi hakuri amma yaki dagawa.

Mama ce taleko d'akin yau gidan su baiga sharaba sannan ko kicin bata shigaba, tana fitowa taga ne yau Rabee'a ba lauba, k'udindine ta ganta da mayafi ta k'arasa d'akin da sauri tana fad'in "subhanallah meyake da munki Rabee'a?".

Ta d'ago ta a hankali ta 6a goshinta tai tajishi zafi rau, meyake maki ciwone Rabee'a? Mama tasake furtawa cikin kid'imewa.

A hankali tasoma motsa dan k'ara min bakin ta tace " kai ne Mama "

Sallamar Babanta sukajiyo atsakar gida tadawo daga masallaci, da sauri Mama tace" Malam gani adakin Rabee'a bata jin dad'i".

"Assha! assha!! Subhanallah to sannu Rabee'a ya fad'a dai dai lokacin da yashigo cikin d'akin sannu Y'ar Baba bari nafita nasamo mata magani".
*******

Bayan yatashi ya fad'a band'aki ya salla wanka tare da d'auro alwala yafito yazura jallabiyyarsa mai ruwan madara ya fito yanufi massalacin unguwarsu a get suka hadu da Daddy, bayan sundawo ya koma d'akinsa yana shiga nefa na d'auke kayansu, d'akin yaza dind'in ya shafa aljihunsa yaji wayam, sai alokacinne ya tuna da wayarsa ashe tana Mota juyawa yayi yaje ya d'aukota Miss call =ØòÜ yagani wajen 79 kuma duk na tane......!

Maman Khaleel

Din kuce
'þ

NI KE DA GASKIYA

=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü

Na
Rabee'art Muhammad
(Maman Khaleel)
________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Saga Marubuciyar:

HABIBA
KISHIYAR ZAMANI

AND NOW =ØGÜ
NI KE DA GASKIYA

Da sunan Allah mai rahma mai jin k'ai.

Page 98

__Ya dunga juya wayarsa yana kallan no d'inta yakasa dauke idonsa akanta,ba shida wani abinda yahuce illa yakirata.

Yasoma Neman layin amma said dai Sam wayar hartagama ring ba'a d'agaba ,yasake kira a karo na Uku Mama ta hango hasken wayan Dan tana silent ne, tace ke a nata ma kiranki Rabee'a ko waye oho?.

Yayana tagani a allon wayar a tunaninta Saifullahi ne tad'agatace " Assalamu a laikum"

Jin Muryar yayi kamar ta Rabee'a sai dai wannan tafi ta ta girma kadan,yalumshe idonsa tare da wata irin faduwar gaba a hankali yafurta "Was alaikumussalam Mama an tashi lafiya?".

Murmishi tayi jin Muryar Arifullah ta amsa da " lafiya lau yasu Hajiyar taka?".

Cikin kosawa dayaji abinda yasamu Babyn sa yace "duk lafiya suke Mama,Um ......am....Mama....Rabee'a tana kusa kuwa?".

Yafad'a yana Sosa kai kamar tana kallonsa .

Murmishi Mama tayi kamin tace" gatanan amma bata jin d'ad'ine zazzabi ne ya lullubeta gatanan kwance ".

"Subhanallah Mama yaushe ne ciwon yakamata?.

Inji Arifulla ya fad'a cikin sauri.

Mama tace ka kwantar da hankalinka insha Allah zuwa anjima in tasha magani zata warware dan Malam Yaje wajen liti me chamis ya had'amata magungunan kaji?".

"To Mama Allah ya sawake yasa Kaffarane ya fad'a tare da kashe wayer sai Faman juya ta yake yanata faman safa da marwa hankalinsa da ruhinsa suna wajen Rabee'a da yakulle idonsa ita yake gani Sam yarasa sukuni ,koda yaje sashin Mami Dan gaidata take tanbayarsa me ke damunsa,cemata kawai yayi Bakomi jiya bai samu bacci bane saboda wani aiki da yayi jiya",bakinsa yaji kawai yana zuba ma Mami karya abinda baisaba ba,tadubesa tace "ok Allah ya taimaka adai dunga rage aiki anasamun isasshen bacci".

Yayi Murmishi to Mama, wai yaushe Dady zai dawone nakosa yadawo,

Tadubesa cike da kulawa tace " asatinnan zai dawo insha Allah, ya akayi akwai maganane?".

Yasoma Sosa kai yana Murmishi yace "Um Mami dama kan Maganar Yarinyar da nake sone" .

Mami tak'ara gyara zama cike da farin ciki abinda tadade tana Rokon Allah kenan yau gashi lokaci yayi Arifullah dakansa yau yake maganar Aure,tadubesa kamin tace "to masha Allah a ina sirikar tawa take?".

Yasoma shafa lallausan gashin kansa Wanda yake kwance luf akansa Wanda yake samun gyara akai akai yawani kwanta kamar na mace,yace " Mami yarinyarkice ai Allah yasa ma kubani."

Mami tayi Dariya tace Muhammad Arifullah fad'amin wata y'ar tawa kakeso inji in zan iya aurama".

Kansa na k'asa yace "Mami bawata bace Rabee'a".

Aran Mami tasbihi take da godiya ga Allah da ya amshi addu'ar ta ,cike da firin ciki tace Masha Allah, Allah yasa Alkhairi Allah yasa kuma a yi damu.

"Ameen Mami"

Bayan sun d'an ta6a hira wadda tashafi Rabee'a,an an ne yake shaidamata rashin lafiyar Rabee'a ,in da Mami, tasoma fadin to ka hanzarta kalekata kaduketa ka kaita Asibiti ya dubata kaji.

To Mami zan yadda kikace.
yamike yace "Mami bari natafi daga can nawuce Office kar namakara ".

Yafada yana kallon agogon da yake daure a tsintsiyar hannunsa.

To Allah yatsare a gaidata kamin muzo dubiya.

Mami ta fad'a tare da Murmishin Farin ciki.


*******

Rabee'a kam jin Muryar Arifullah yasata jin wani sanyi acikin zuciyarta akalla tasamu saukin rad'ad'in da zuciyarta take mata sai dai haryanzu kanta namata wani irin ciwo,fuskarsa kawai take son gani,kozata samun sanyi a cikin zuciyarta,tanaji Mama tana kwantar masa da hankali,Baba yashigo yana fadin kinga Maman su Liti bai budeba sai zuwa anjima yanzu ki tanbayeta da me take son karyawa?.

Mama tace to Malam tashafa mata kai kamar mai shirin rad'a tace" Rabibina sannu kinji mezakici kamin anjima Babanku ya amso maki Magani".

Ta danyi Murmishi badan tanason cin komiba Dan Sam batasan cin komi ko ganin komi in ba Arifullah ba,ganinsa shine samun kwanciyar hankalinta,amma dan ta kwantar da hankalin Mama tace "Mama a kawo min Masa ".

Mama tace to talek'a tagayama Baba ,baijima ba yadawo Mama ta amsa kadan naci nature kwanan nazame na kwanta.

Kamar daga sama naji wata Murya Mai dad'in saurara da sanyi a zuciya,ga kamshinsa Wanda yacika gidan gabadaya ,wani sanyi ne yaratsa zuciyar Rabee'a takara bude hancinta tana shakar Daddad'an turarensa,bayan sungama gaisawa da su Mama tare da tanbayar mejiki,suka amsa masa da sauki,Mama tai masa jagora hardakin .

Kara kulle idona nai kamar mai Bacci Mama tasoma dan jamin yatsa a hankali tare da Fad'in Rabee'a ga Yayanki nan yaxo dubaki.

Nasoma motsa jikina a hankali,Wanda yasoma birkita Malam Arifullah namike Sam na manta jikina babu wata rigar kirki,Mama tana tashina tai gaba abinta tana Fad'in zauna mana ga waje tanunamasa kan Dadduman dakin Rabee'a wadda dakyar tai Sallah a kai.

Kallonta kawai yake babu ko k'iftawa duk tayi wani fiyau da ita kamar ta dad'e tana jinya,to me yasameta haka?

Tanbayar da yake ta ma kansa kenan ,itakam ganin kallon nashirin yin yawa yasa tadubi kirjinta taga komi nawaje kamar babu komi ajikinta da sauri ta bud'e baki tare da kallansa da sauri taja mayafinta ta rufe jikinta.

Yayi Murmishi aransa yace kwana nawane zasuzama mallakina nayi yadda naso dasu,ganin kirjinta Wanda yacika da nashanu tam yakara tayar masa da sha,awa abinda bai taba jiba ,lalle yakamata nasamu me d'ebemin kewa ina bukatar mace kusa dani matuka yayi a jiyar zuciya,yalumshe idonsa ya bude a hankali,sukai ido hudu dashi inda yakamata tana Satan kallonsa,Murmishi yayi tare da Fad'in kalleni mana,ta kauda kai gefe tasoma wasa da zobenda yabata,"yayi Murmishi to ni Bari nagaidaki tunda ni baza a gaidaniba nazama sirikinki ko ,to ina kwana Y'anmata yajikin?".

Dariya taso kufce mata ta d'an turo baki cike da shagwaba tace" kai Yaya wai Y'anmata ni ka bari banaso".

"Dariya yayi tare da Fad'in nimakidaina Cemin Yaya" ya fad'a tare da kwaikwayon muryarta.

Tai Dariya tare da rufe fuskarta tace "To ina kwana Yaya ya su Mami?".

Yadubeta cike da sha'awar yadda take shagwaba komi nata burgesa yake ,ya amsa da lafiya lau suke, nikam balau dan jiya ke da saurayinki kunhaifarmin da wani sabon Ciwo anan d'ina".

Yanuna mata gefen kirjinsa ,tadubesa da sauri tana dan zare ido tare da Fad'in ciwo kuma yagyad'a mata kai,alamar " eh".

"Yanzu dai kishirya muje adubaki a Asibiti".

Kai Asibiti kuma Yaya ,aranta tace nikam nawarke dan ganinka shine magani kuma Alhamdulillah.

"Tunanin me kike daga an ambaci sunan AsibitiK'anwata?".

Ya fad'a tare da mikewa kiyi sauri ina jiranki a mota ,wannan Umarnin Mami ne ,tace maza nakai mata d'iyarta taga likita .

Yana kai wa nan yafita tare da Fad'in kiyi sauri kishirya zani office karkisa na makara.

D'akin Baba yakoma yamasa Sallama tare da Fad'in "Baba dan Allah zankaita Asibiti a dubata" .

To!to!! Madalla nagode Allah yasaka ma da Alkhairi.

Ameen Baba ba da muwa nan ya a je masa wasu kudi masu dan kauri sannan yamike yafito dai dai nan kuma Mama tafito daga D'akinta hark'asa Arifullah yadurkusa yace to Mama zan tafi amma dan Allah inason kai Rabee'a taga likita .

Mama tace "kai ai bakomi duk d'aya nadauke ka da kai da Yayan Rabee'a sai kun dawo Muna godiya a gaida Hajiya" .

A mota Rabee'a ta sa Mesa ya bud'e mata wajen mezaman banza takai hannunta tabud'e k'ofar takai kanta cikin Motar wani sanyayyen kamshine yadoki hancinta ta shak'a tare da zura sauran jikinta a cikin motar sanyin Ac da daddad'an k'amshin turaransa sungama cika mata ruhi ,ta jingina kanta a kujera ta lumshe idonta jikinta duk ya saki tarasa meyasa aduk sanda suka kasance tare takan rasa nutsuwarta,yadube a tsanake yace" yadai jikinne ?".

Ta bude idanunta a hankali tasauke su a kan kyakkyawar fuskarsa yasakar mata wani yalwataccen Murmishin inbakeba....!

Tako so tagane yaren itama,tamayar masa da martanin Murmishin tace" um amma da sauki".

OK Allah ya sawake ko My K'anwas.

Yafada tare da rufe motar yatada Suka soma tafiya a hankali babu Wanda yakuma magana sai dai bugun zuciyoyinsu Wanda suke sauka kusan atare,ko wannan su da tunanin da yake a zuciyarsa,Rabee'a tunanin da take inama karsu rabu inama ta xamo matarsa uwa awajen ya'y' ansa, wai da ta ca6a.

Shikam addau'a yake Allah yasa takarbi soyayyarsa kar ta watsa masa k'asa a ido,wai in Allah ya mallaka min Rabee'a ya juyo ya kalleta yayi wani Murmishi lalle zansha gara.

Giwa Hospital ya shiga ya gyara parking yadubeta yace to bismillah ko in taimaka makin ne ?

Da sauri tace a,a zan iya nagode tare suka fito amota Kai Masha Allah abinda najiyo wata mata wadda take zaune a gefen wajen fulawa suna magana da wata dagani d'iyartace ,yarinyar tajuya inda Maman take kallo GASKIYA wannan dagani ango da amaryane danko sundace da Junansu Mama.

Maman tace kwarai ma kuwa dagani yarinyar kamar tanada shigar ciki.

Karaf a kunnen Rabee'a taisaurin duban bayin Allah dasuke ta sharhi akansu tai Murmishi, yace yadai kema kinji addu'ar da suke mana ko ,Allah Ameen.

Tace ni dai banjiba Yaya nadai tuna wani abune.

Tafada dai dai sanda zasu shiga office din Dr.Khaleel da sallama Arifullah yamurda kofar ,Dr.Khaleel Wanda daman yasan da zuwansu ya amsa masu sallama tare da Fad'in bismillah Rankayadade ,yamika masa hannu sukai musabaha kamin suka zauna ,Dr. Khaleel ya dauko file din Rabee'a yasoma budewa tare da Fad'in Hajiya meke damunki.

Rabee'a ta dubi Arifullah kamin tasoma fad'ama Dr.Khaleel komi.

Shikam tana fad'a yana rubutu har ta ga ma,Yad'ago kansa yace" bayan nan babu wata matsala?"

"Eh babu komi Dr.".

Wani guri ya danna ko minti daya ,ba ai ba sai ga Nursing tashigo cikin girma mawa ta gaidasu kamin tadubi likita tace " Sir gani "

Yadubeta yace kuje tare da Hajiya kiyi mata Allura sannan ki je phamecy ahada mata wadannan magungunan.

"OK sir."
Inji sister Rukayya,takarb'i komi kamin tadubi Rabee'a tace ranki shidade taso muje ko.

Rabee'a fa tunda taji an ambaci Allura fa idanuwanta suka soma raina fata,tadubi Arifullah yadaga mata gira alamar karfafamata gwiwa aransa yace akwai aiki akanka fa Arifullah domin Allah ya baka mace mai raki ya lumshe ido lalle wannan akwai aiki ranan haihuwa ,shikawai take kallo yanata Murmishi tadubesa tare da katsemasa tunani Yaya nafaji sauki kace tabar allurar kaji .

Tafad'a tare da wasu hawayen shagwaba.

Cike da burgewa Dr.Khaleel yadubesu yace to inafa ganin kanwar nan taka zata bamu matsala kasan yanzu tasamu dama can Baba me lallabamana ita kamin ai mata Allura.

Arifullah yanisa tare da Fad'in ok, yadubi Rabee'a cike da so yace" bakison kisamu lafiya ne Rabee'a?"

Tadubesa cike da wata irin shagwaba tace " Yaya to ai naji sauki fa .

Karon farko a Rayuwarsa na ta6a yarikemata hannu yamikar da itaba va Arifullah ba had Rabee'a sai da tai kamar zata shide saboda wani maganadisu da yake fixgarsu ga ba d'ayan su ,takasa yi mass musu har suka isa dakin Allurar cike da dabara Arifullah yasa Rabee'a a faffadan kirjinsa yana shafa mata baya a hankali ahankali,tai wani lamo da ita Rana wani sauke numfashi a hankali ,da ido yama Nurse din magana tazo tamata ,ai wata damka Rabee'a ta kaima Arifullah tana Fad'in wash!!!!!!!!.


Maman khaleel

Dinkuce
'þ
NI KE DA GASKIYA

=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü

Na
Rabee'art Muhammad
(Maman Khaleel)

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Daga Marubuciyar :

HABIBA
KISHIYAR ZAMANI

AND NOW=ØGÜ
NI KE DA GASKIYA

Da sunan Allah mai rahma mai jin k'ai.

Page 99

____ Wash! Yaya da zafifa,tafad'a tare da wasu hawayen shagwab'a,suka sauka akan Faffad'an kirjinsa,mulmula mata wajen yake a hankali tare da fad'in am sorry My Baby kiyi shiru anga kinji bazata sakeba kuma sai na mata hukunci indai tasake ,ya isa haka kinjiko,ya fad'a acikin kunnuwanta,har cikin ranta take jin wani sanyi yana ratsata tuno fa su ba maharraman juna ba ne yasata tasoma k'ok'arin zare jikinta daga nasa,sai taga d'akin ba kowa sai su kad'ai,tadubesa ta turo Baki tace kagani ko Yaya kasa Sister Rukayya taji kunya tabar mana words d'inko.

Yamike yaxo dab da ita yace" bake ba ce ba kinfiye rud'a mutum da wasu salonki mai sa mutum ya mance indayakeba,ya fad'ashima cikin wani salo Wanda shikad'ai ya iyasa.

Murmishi tayi kamin tace "nidai ka mayar da ni gida ,tafad'a tana tafiya tana d'an d'ingishi ".

"Wallahi ko kimike ko nad'auke ki cak nakaiki mota".

Ai tuni ta mik'e tasoma sauri ta nufi hanyar fita, Murmishi yayi kamin yace OK bajira ko nagode ,sai da yakoma Office d'in likita ya amso mata magani,kamin sukai sallama yanufo Mota,samunta yayi ta jingina kanta ajikin

Please Login or Register in order to submit comment