Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi sai abin ya so bata Dariya amma ta dake tace "haba Alhaji ya xakafadi haka? ".

"An
nace an fad'a Maryam kinaganin abun, Yaron nan ya rusamin Rayuwa yarusamin farin cikina da yanxu gobe war haka I na tare da Amaryata nagama tanadi gashi nasoma shan maganin karfin maxa gashi yaxo ya rusamin lissafi".

"Ta danyi murmishi tajuyar da kanta gefe tace ba ganiba Alhajina?"

"Ya wani jawota garesa oho dama hada baki kukai yaje yakashe masu yarinya? Haba ko ince Maryam ashe kinsan inda Usman yake da shi da yarinyar nan wallahi idan iyayen yarinyar nan suka ce mun yarinyar su wani abu yasameta to akul dinku ke da danki wallahi baruwana kinji nafadamaki iyakar GASKIYA dan motar da yafita da ita gata can yayi hatsari da ita kai yaron nan yajamin bala'i".

Hajiya Maryam wadda jikinta yasoma yin sanyi dataji abinda mijinta yace da bata damuba darasa Auren amma jin ya ambaci hatsari yasata da wowa haiyacinta karfa ace yarinyar Mutuwa tayi shine yagudu ya barsu cikin tashin hankali, nanfa tashiga tashin hankali mara misaltuwa takoma dakinta tasoma neman layinsa amma akashe, haka tai ta gwada number amma amma sai ace mata wayan akashe take. Takira duk wasu yan'uwa amma magana dayace bai xoba dataji haka sai tace to shikenan hala yana hanya dan yace xaixone ya dubaku, Alhaji Dalladi kuwa yakasa tsaye yakasa xaune dayaji karar waya sai gabansa ya fadi yadagoda sauri yadubi kiran saiyaga abokan kasuwanci ne, wasu kuma abokansa ne masuson suji meke tafiya akan Aurensa Wanda yasan koyasha giya wannan Auren ba shi, yana cikin tunanin ne sai ga kiran Abokinsa Wanda yamasa hanyar neman Auren, ya runtsa ido yace Allah kafitar dani daga cikin kangin da yaron nan yasani, yadaga tare da fadin"Hello"

"Alhaji muna kofar gidan ka, kafito yanxu kagayamasu inda yarinyar su kuka kaita dan wallahi danasan haka xakamin da ban ma hanyaba inji malam Musa.

"Alhaji Dalladi duk rashin mutuncinsa yana tsoran hukuma amma sai wata xuciyar tace meye anfanin kudi? Ai kawai kacema mai gadi ace masu bakanan, ko kakira Maryam kasan tana da tausayi baxataso acima mutunciba, tabbas gaskiya ne. Yafita yasamu Maryam ta hada kai da gwiwa yace kinganiko kinga abinda yaronki yajamana ko!!!.

Danjin cigaban labarin sai kubiyaoni gobe in mai duka Allah ya kai mu.


Daga Yar'uwar ku:

Maman khaleel
'þ
*NI KE DA GASKIYA*

=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü

*Na
*Rabee'art Muhammad*
*( Maman Khaleel )*
________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*Daga marubuciyar :*

*Habiba*
*Kishiyar zamani*

*And now =ØGÜ*
*Ni ke da gaskiya*

*Dedicated to : Yusuf Nuhu*
*Special gift to : Ibrahim Aliyu bros*

*Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.*

*Page 86 &87*

___"Kin dai ga a binda d'anki ya jawomana ko¿.
"ya gudu da yarinyar Mutane ,yanzu meye mafita¿, ga iyayen yarinyar nan a waje. "

Hajiya Maryam ta numfasa cike da takaicin maigidan nata domin duk abinda ya faru shi yaja shine ai mai budurwar Zuciya ai gashinan takai sa da dana sani.
shin waima Alhaji ya akai kuka hada Soyayya kai da danka?. "

Itama ta ai Ka masa da ta_ta tambayar, ba tare data amsa masa ta shi tambayar ba. Wani takaicine ya turnike sa a ransa yace lalle Maryam yau harni ta ke fada ma irin wannan maganar¿.

bahalin faWa ko k'orafi ko challenge kawai ki taimakamin yanxu da wata shawara.

Yanzu inje ko ke zaki?.

Ta dubesa yaso bata dariya dan ya tsorata ainun, nan da nan sai tausayinsa ya kamata.

Kunsan tausayi na Miji da Mata, sai kuma take ganin laifin dan nasu akan abinda ya ai kata bai kyauta ba, tace "Alhaji kai ya kamata kaje bakomi insha Allah, Allah zai bayyanasu kai masu bayani yaronka Shima bai dawo ba kaji Alhajina".

Ya nisa to Maryama nagode. haka yafita jikinsa ba kwari tare da bakin cikin sanin Rabee'a wadda tazo ta war gaza masu zaman lafiyan gida, a hankali ya bud'e get din Y'an sanda yagani Mota guda tare da Yaya Saif da Malam Musa Wanda sai zare ido yake, 'Yan sanda 2 suka fito hannun su d'auke da ankwa suka sa masa suka tasa keyarsa ba ko musu sai station.

"Mai gadin gidan yanufi falo da gudu ya na fad'in Hajiya sun tafi da Alhaji".

Da sauri ta mi™e tare da dafe kirji cike da razana tace" su wanene suka tafi dashi Garba?.

nan dai Garba ya mata bayanin yadda komi ya faru .
Kwanansa daya kamin aka gano station d'in da yake. Tambayar duniya an masa, amma amsa daya ce bai san inda suke ba, Alhaji Dalladi ya rame sosai dan ma Baba yace kar a dake sa, binciken duniya anyi ma Umar ba a gansa ba, Hajiya Maryam ce kadai tasan in da ya ke i ta ma ta hanyar Y'an gidan su, amma tai shiru bata gaya ma kowa ba, har ranan da Alhaji ya fito. Shima bata gaya masa ba dan gudun Sacin rai, tunda ita dai ya sanar da ita duk yadda Abun ya faru sai dai ya 'boye mata k'udirin sa na ya lalata Rayuwar Rabee'ah.

Wannan kenan

*************
Arifullah kwance ya ke yayi ruf da ciki a ma ke_ken gadon sa wanda yaji shin fida ta alfarma.

tuna ni ya ke shin ta ina zai soma ne¿ tabbas yana sonta, ya shafi kyakkyawar fuskarta wadda ta ke manne a jikin screen din wayarsa. sanda ya dauketa ran da xata koma gida tana Murmishi, sake shafa Hoton yayi , ina sonki Rabee'atu Ya Allah ka Mallaka min Rabee'ah tazamo Uwa ga yarana, Murmishi yayi mai tsada tare kai ma Hoton wani kiss =Ø‹Ü mai kyau ya lumshe ido ina ma mafarkin sa ya zama gaskiya? Ina ma ya bud'e idonsa yagan ta kusa da shi?

Ka kira ta mana kaji Muryar ta ko kaji sanyin zuciyar ka ya duba a gogon wayar sa yayi 11.50 pm anya batai bacci ba¿ tanbayar daya yiwa kansa kenan ba mai bashi amsa, kamin daga bi sa ni naga ya Matsa kira, kamar a mafarki taji k'arar wayar ta cike da tsoro ta farka bakinta d'auke da addu'a, tasoma motsa Hannunta ta kai in da tasa caji a gefen katifar ta Yar'sale =ØÞ wani Murmishi naga tasaki mai sauti tare da sauke wata nan nau yan a jiyar zuciya ta soma hada kalamanta Masu taushi kamin naji tace.....!


*To masu karatu kuyi hakuri da wannan na barku lfy daga y'ar uwar ku.*

Maman Khaleel
'þ
NI KE DA GASKIYA

=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü

Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel )

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 88 &89

Wani Murmishi naga tasaki mai sauti tare da sauke wata nan nau yan a jiyar zuciya ta soma hada kalamanta Masu taushi kamin naji tace "Assalamu a laikum Yayana"

Lumshe idonsa yayi saboda Muryar da tai amfani da ita tashige sa sosai bawani sanyi da ya ziyarci zuciyarsa.

"Hello Yaya kanajina? ".

Jinmuryar ta yasa shi da wowa daga shaukin da ya shiga, Yayi wani Murmishi mai sauti, kamin Yace "ina jinki K'anwata ya kike ya su Mama? "

"Lafiya lau Yaya,ina yini ya aikin da Mummy da Daddy? ".

"Yayi Murmishi Kinyi kewarsu kenan K'anwata? ".

"Eh mana Yaya da tunanin su Bacci ya daukeni Yaya nayi kewar Mumy sosai domin duk Wanda ya xauna da Mumy to tabbas ta shiga rai saboda kyawawan halayenta Yaya nayi kewarta sosaia".

Yace "Muma munyi kewarki sosai haka sukaita hira cike da farinciki da shaukin kauna, kamin sukai sallama, kowannan su xuciyarsa kal dan farin ciki, washe gari da safe ta tashi cike da wani kuxari aiki kawai take tana hasaso kyakkyawar fuskarsa wadda kullum take cikin annuri, tabbas dole Saudat ta rikice domin gaskiya shidin na da banne gashi da shiga rai ba kamar yadda ta xataba a baya, Murmishi kawai take wadda ita kanta batasan sanda take yinsa ba, Mama wadda tunda tafito take ta lurada yanayin Rabee'ah Ko mai yasata cikin farin ciki oho?.

Rabee'a takoma makarantar Islamiyyarsu inda tacigaba da karatunta Wanda ta mai da hankali sosai tunda acewarta ta a jiye Soyayya karatunta xataciga ba har Allah yakawo mata Wanda zai so ta tsakani ga Allah, a yaune kuma tasamu labarin dawowar Malam Hussain a bakin kawarta Aisha, wadda sai faman yaba kyau da kibarsa take tace"kai Rabee'a wallahi Malam yakoma kamar wani Balarabe, kece kawai a ransa har gida fa yazo yake tambaya ta wai kin yi Aure ko, sai nace masa aiko ba a yiba anfasa".

Kallon Aisha kawai take tana Murmishi tana ta kallon bakinta wadda take ta xuba kamar Y'ay'an kad'ayar da babu zaki har ta kai aya, kamin ta dubeta tace"Nagode sai dai ni yanxu Aisha Maza tsoro suke bani kuma bayan haka ma Malam Hussain ya manta dani ko kin manta da yanxu yana da Mat, wani xafi taji yataso mata a zuciyar ta sai take ganin ai duk laifinsane komi yafaru da ita shiya jawo dan da yafurta yanasonta da wuri da Alhaji Dalladi bai shigo Rayuwar su ba, wasu hawayene masu xafi suka gangaro mata a kyakkyawar fuskarta wadda ta kasa sanin ko nameye, "Aisha tai saurin fad'in meye kuma na kuka? "

Tasoma sa zaratan Hannunta tasoma share hawayen wadda itama batasan dalilinta na yin kukan ba, "Tace bakomi nima ban san kukan nameye ba kawai ni dai naga hawayen ne, "to ya isa haka inji Aisha".

Ko da tadawo gida sai tunanin hirar su ta karshe take inda yake cewa Rabee'a xanbarki badan raina yasoba, ina sonki amma yazama dole in barki gashi Iyayena sunmin mata Rabee'art zanbarki badan ina so ba sai dan babu yadda xamuyi ina maki fatan alkhairi a gidan mijinki..! ai baikarasa maganarsa ba nafada cikin gidan mu ina kuka mai cin zuciya, jin abin take kamar yanxu yake faruwa gawani kishinsa yanatasomata Sam baxan yadda da kai ba Malam Hussain karkaxo gareni kaje ka xauna da Matarka, nadaina soyayya, tana cikin wannan tunanin ne taji Muryar wani yaro yana kwala Sallama a cikin soron gidan tare da Fad'in wai Rabee'a tazo inji.........!


To Masu karatu ga Malam Hussain ya dawo ga kuma Gwarxo Arifullah shin wa zai dauka acikin gwarazan Rabee'a shin Waye kuma yazo neman Rabee'a?

Sai kubiyoni gobe in mai duka ya kai mu gobe.

Maman Khaleel

D'in kuce=ØLÜ
Comment and shire
NI KE DA GASKIYA

=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü

Na
Rabee'art Muhammad
(Maman Khaleel )

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Ina kuke masoyan gaskiya ina jinjina maku ina godiya da kulawarku gareni, Masoyan Arifullah sakon gaisuwa gareku ya d'aga maku Babban d'anyatsa=ØMÜ =ØÞ=ØÞ.

Wannan Page din nakine Fatima Abdurrahman ina godiya da kaunarkigareni na bibiyar wannan littafi tundaga Farko Allah ya bar kauna mai d'orewa Ameen.

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 90&91

Gabanta ya fara dukan Sakwarar Legas tare da tunanin waye kuma ita dai tasan tunda suka Rabu da Alhaji Dalladi bata karajin anyi sallama da ita ba da sunan anxo zance, Muryar Mama ta tsinkaya tana cewa" kai waye yake neman ta? "
"Um wani ne Mama nima bansan shiba yace dai inmasa iso wajenta".

Rabee'a dai tana jinsu taga in Yayantane zai kirata ne baitaba yo aikeba, "Rabee'a kixo kije kiga ko waye inji mama Tafada tare da fad'in je kace tana zuwa".

Yaron yace "to"

Tsaf take jikinta Sam babu k'azanta ta fito talek'a d'akin Mama ta shaida mata fitarta kamin ta nufi soron gidan su zuciyarta a cunkushe Malam Abubakar ne tagani tsaye abakin Baburd'nsa cike da mamaki kwance a fuskarta ta k'arasa, Shikam sai faman washe baki yake, Malam Abubakar Abokin Malam Hussain ne, to meyakawosa?

Muryar sace taziyarci kunnuwanta inda yake cewa "Barka da fitowa Tauraruwar taurari, mai rikid'a y'an maza".

Yafad'a yana Murmishi.
Itama Murmishin yak'e take Wanda iyakarsa la66anta, tace "kai Malam wannan kirari ai sai kasa mutane sukama bina da idanuuwa kamin sukawon hari".

Dariya yayi mai sauti yace" tab Rabee'atu dama haka kika iya zance?".

Tai Murmish "tace Malam munyini lafiya ya makaranta da iyalin? "

Tafada tare da kawar da nasa batun, domin takosa taji tatsuniyar da yazo mata da ita.

"Duk suna lafiya suna gaidaki".

"Ina godiya nima Malam".

Shurune ya ratsa wajen nawajen sakon goma kamin yakatse shirun da fad'in "yauwa Rabi nasan dai kinji labarin dawowar Abokina ko? ".

Tai kamar bataganeba tace "Malam wane kenan?".

Duk da yasan tagane nufinsa amma sai kuma tawaske da yimasa wannan tanbaya, Murmishi yayi yace "nasan Kinsan waye Amma Bari nakara tuna maki Malam Hussain nake nufi nine wakilinsa Inda nazo na ari bakinsa nacimasa albasa, wajen yada da, awar Soyayyarsa kamin yaxo gareki, Kinsan dai irin yadda yake sonki basai nakara fad'a ba mudai muna K'ara miko maki k'ok'on bararmu, ko da wani ma asashi a gefe Domin mune kan gaba, yafada yana Murmishi".


Wani irin hawaye ne suka xubomata tabbas da taso Malam Hussain amma yanxu batasan me yasa take jin haushinsa ba musan man ma matarsa wadda nasan yanxu suna sonjunan su sosai yana nufin zai raba masu sonne gida biyu sannan bakullum zata dunk'a ganinsa ba sai bayan Kwana 2 ta6 yanzu yadda gidan Malam Sallau haka zamuyi muyita fada kamar yadda Indo tafasama Habiba baki da muciyar tuwo, kema haka matarsa zata biyoki tadaki banxa, duk wadan nan tunanin tanayine a zuciyarta.

"Lafiya Rabee'atu Mekuma ya faru? "

kalmar dataratsa tsakiyar kwakwalwarta kenan, batasan sanda tace kuma Malam yana son Matar sa, nidai na hakura nabarmata shi, nima Allah ya bani mijina Wanda zamu zauna dagani sai shi, Tafada cikin wata irin Murya mai taushi gamida shagwaba.


" Yagane sarai kishine ke addabarta amma sai yadubeta yace to share hawayen kinji wallahi ni shaidane akan irin Sonda yake maki kuma zaki gani Idan yazo anjima kinji kidaina kuka dan Abokina bazaiji dad'iba idan yaga kina xubar masa da hawayensa masu tsada".

Tasoma share hawayen tare da fad'in "Malam ai acikin mu biyun dole yaji yafison wata ko? ".

Ya gyad'a kai "Eh hakane amma ke yake so ba itaba kinjiko".

Tai wani Murmishi to Malam naji nagode da haka sukai sallama yamika mata wata Leda, amma fafur tak'i amsa, "tace Malam nagode "

Tajuya ta nufi cikin gida cike da farinciki jincewa Malam Hussain dinta yana son ta, dantuni tasama kanta aya da tunanin cewa Arifullah yana son ta duk da cewa Arifullah yana cikin wani sashi na musan man acikin xuciyarta, sai dan kawai baxata samesaba sai dai tayi hakuri domin shidin mai tsadane sai su Saudat Y'ay'an manya, ba itaba y'ar talakawaba.

"Ka tai makeni karkabari ya yatafidani Yaya! Yaya!!..........!!!!!!.



kuyi hakuri da wannan ina godiya.

Maman Khaleel
nake maku fatan alkhairi muhadu gobe in meduka ya kai mu gobe
'þ.

Comments
and
Shire
*NI KE DA GASKIYA*
=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü

NA
Rabee'art Muhammad

(Maman Khalil) ________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 92&93

"Ka tai makeni karkabari yatafi dani Yaya! Yaya!! Yayaaaaa!!!! ".

"Binsu yake amma ya gaza cinmasu cike da wani kuxari ya ke gudu yana fad'in kai wayeeee?
Ka kyaleta Matana ne, shikam sai faman janta yake iya karfinsa bako wai waye bare kuma magana duk yadda ya so yacece ta amma a bu ya faskara, yanaji yana gani wannan mutumin yaja masa Baby, cike da firgici ya farka bakinsa d'auke da addu'ar mummunan mafarki yatofe ko ina na dakin kamin yakara maida kansa gefen damansa ya kwanta amma abin mamaki bacci ya gaza daukarsa daya kulle idonsa ita yake gani cikin hawaye tana miko masa zaratan Hannunta, ya mike ya zauna tare da fad'in ya Allah ka kare mu daga dukkan abinda zai damemu ya Allah katsaremun Rabee'atu na ya sa tazama mallakina ta zamo Uwa ga yarana yafada bayan ya ida Sallah nafila ya shafa kamin yakoma ya kwanta cike da tunaninta".

Dawuri yau ya shirya zuciyar sa yau a cunkushe take Sam bata masa dadi yayi kyau ainun cikin shaddarsa galila main ruwan Bula ya dauki hularsa Minister yadora akan sumarsa wadda take samun gyara akai akai ga sajansa Wanda ya kwanta yayi luf- luf a kyakkyawar fuskarsa ya daura wani tsadaddan a gogon sa ya daura asaman tsin-tsiyar hannunsa, Wanda sai faman daukan ido yake yakoma wajen takalmansa ya dauki takalminsa k'irar Italy kalan shaddar yafito sai faman kamshi yake yana taku d'ai d'ai, Arifullah kenan yaro dan kwalisa yaro mai tashe ga kuruciya ga Nera, cewar Mumy wadda take zaune a falo tafada acikin xuciyarta, sai faman Murmish take tare
NI KE DA GASKIYA

=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü

Na
Rabee'art Muhammad
(Maman Khaleel )

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Daga marubuciyar :

HABIBA
KISHIYAR ZAMANI
AND NOW =ØGÜ
NI KE DA GASKIYA

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.

page 94&95

Sai faman Murmishi take tare da fad'in"
Lale marhabin da D'angidan Daddy,wannan gayunfa kamar zakaje wajan surukar Daddy? "

Yasoma shafa k'eyarsa yana d'an Murmishi yakaraso Falon ya xauna kusa da Mahaifiyarsa ya soma gaidata, ta amsa tace "wai Arifullah yaushene zaka kaini gdn su Yarinyata ne wallahi nayi kewarta sosai".

tasosa masa inda yake masa k'ai k'ayi ya Murmusa yace to ko muje na ajeki agidan su, Fatima tafito daga d'akinta taji ana fad'in za, a ajeta takaraso cike da d'oki tace "Mami ina zaki? ".

Tai Murmishi tace" gidan 'Yata Yaya zai kaini".

Cike da farinciki tace" Yaya nima zani dan Allah kaji?".

Yayi Murmishi Yace "kai Auta Kinsan ina zata ne?"

"Eh" mana nasani wajen Sister Rabee'a mana Mami zataje ko Mamina?.

Mami tai Dariya tace "can zamu je kishirya ".

"Dama nasanarwa Daddy Kila muje gidan su Rabi asatin nan indai bakada aiki a wannan weekend din".

Fatima tai d'aki da gudu tana murnan yau zata ga Rabee'a da kyakkyawan Yayanta shiri take na kece raini tafito cikin wata doguwar Riga Marun wadda taji stone, sai d'aukan ido take, ta yane kanta da gyalenta tafeshe jikinta da turarukanta masu sanyi kamshi, ta d'auki takalminta mai tsini ta fito fes da ita, Mami tadubi yaranta aranta tace Masha Allah lalle Auta ma fa takawo itama.

"Mami nayi kyau?
Inji Fatima tafada tana juyawa a falon.

"Masha Allah kinyi kyau Auta, "yauwa Mamina nagode"

Ita kanta Mami tayi kyau cikin atamfarta k'irar Holland mai ruwan dorawa , Wadda akai Mata zanen Kore a jikinta, ta dauki gyale Shima Kore, tasa flat shoe kirar Italy kalan zanan atamfar, gawani kamshi tana fitarwa na Musan man, a mota suka sami Arifullah.

A mota hira kawai suke yanajinsu zuciyarsa fes farinciki yabiya wani Babban super makert yayi mata siyayya gamida kayan kwalam kamin yadauki hanyar Tudun Wada, suna shiga cikin layinsu Rabee'a, yayi parking a gefen gidan su , Mami da Fatima suka fito suka nufi cikin gidan Fatima nagaba duk takosa taga Rabee'a.

"Assalamu a laikum "
Fatima tafad'a acikin soron gidan su Rabee'a, gidan shiru dan Mama Bata nan ta shiga Barka mak'ota, kamar a mafarki tajiyo Muryar Fatima takara kasa kunnenta shin bagizo Muryar Fatima take mataba?

Sai da takuma jin Muryarta akoro na biyu, kamin tamike daga dogon tunin da tasava na Arifullah Wanda ko yaushe shine aranta sai dai kuma yamata nisa shi ba tsaran Aurenta bane, Malam Hussain shine dai dai ita, sai kuma ga muryar Fatima wadda ko a ina taji ta zata ganeta, tafito aikuwa da gudu Fatima tanufo Rabee'a tana murnan ganin ta, tarungumeta suna Murnan ganin juna,

Mami kam sai faman Murmishi take sun matukar burgeta, Rabee'a ta shiga jinin jikinta tana ma d'anta sha, awar Aurenta domin gaskiya sundace da juna, zataso taga yaran wadan nan taurari guda biyu kowa yana kayan kyau, Rabee'a ga tarviyya ga hakuri da girmama nagaba da ita gaskiya Rabee'a ta cancanci a sota,sai da suka dawo hayyacinsu daga Murnan ganin juna, cike da kunya ta nufi Mami tace sannu da zuwa Mami kushigo, takaisu d'akin Mama ta shinfid'a masu Darduma

Suka zauna takawo masu ruwa mai sanyi, Mami takarba ta sha kamin ta gaida Mami, Mami ta amsa tace ina Mamanku?

Tayi Murmishi tace" taje bayan mu barka tana hanya yanxu, zata dawo bari nadauko wayana nakirata".

Tana cikin neman layin Mama sai gata tana fad'in Aslm.

Bak'in takalma tagani nan dai takarasa ta shiga dagani babu tanbaya wannan itace Mahaifiyar Arifullah, nan suka yini suna ta hira Mami da Mama kamar daman sun san juna, misalin karfe biyar dai dai Yaya ya dawo, yakira ni cike da wani farin ciki nad'aga waya tare da fad'in" Assalamu a laikum Yayana .....!

Nabarku lafiya.

Maman Khaleel

Comments

and
share
*NI KE DA GASKIYA.*

=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü

*Na*
*Rabee'art* *Muhammad*
*(Maman Khaleel ).*

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.*

*Page 96*

___Ya lumshe idanuwansaa ya buWe su a hankali kullum muryarta kamar sarewa dan dadi shikansa baisan yana da muryar da yayi amfani da itaba wajen faWan " Amin wa'a laikis sallam ya ma'abociya kyau da Murmushi ya Tauraruwar Zarah mai haskake taurari Rabee'a da fatan kina cikin koshin lfy? ".

Wani Murmushi naga Rabee'a tana mai kwantawa a zuciyar masoyi Wanda yake da matu™ar wuyar futa a cikin zuciyar masoyi, tunda take akwai wanda ya iya kiran sunanta cikin Murya mai taushi irin Arifullah, bata gajiya da jin muryar sa, tasauke sanyayyar ajiyar zuciya wadda sai da Arifullah yadauke wayan a kunnensa ya lumshe ido, tace "lafiya Alhamdulillah Yaya Arifullah".

"Yau sai ga su Mami ko sunmaku zuwan bazata, Arifullah ya faWa".
Ai kam nagode ma Yaya naji daWin ganinsu,"Yaya ya Aunty Saudat?".

Duk da yagane sarai amma yace" wacece haka?"

"Haba Yaya Aunty Saudat fa Budurwarka fa nake nufi, tafaWa cikin shagwaS".

"Sam ni banida Budurwa me suna haka ni Budurwata sunan ta metsadane amma ita Sam batasan ina yiba nikaWe nake kiWana nake kuma rausayawa tare da rangaji".

Tayi Dariya tace "to dama Yaya ka iya rawa¿ tabbbb.

Shima Dariyar Yayi yace "um mana banyi rawaba ma sai ranar da Babyna taxo ta amshi Soyayyata tazo gidana wai a ranan hmmmm, kedai bari yanzu kina ina ne? ".

tace "ina Wakina"

"Ok " naga yamma nayi kice ma Su Mami sufito mutafi karna rasa jam'in Magariba".

"Kai daman kana ™ofar gida?".

Yayi Murmishi "yace tuntuni, nasan ko nace kizo Satamin rai zakiyi da wannan kunyar taki, shiyasa ma bansanar da ke ba".

A ranta tace Yanzunma bazan iyaba, amma tace "haba dai Yaya dane amma yanxu nadaina sai dai ina jin kunyar Mami sosai ta ganmu tare".

A binda Rabee'a batasaniba shine Mami tundazu taji komi dan yakirata ya shaida mata yakaraso,yace "ok nagode da har ina shirin cewa

Please Login or Register in order to submit comment