Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

menene gayamin bakada matsala ko kaɗan ,
Kamill ne yace " Abba yarinya nagani ...
Ragowar maganar ta maƙale masa a maƙoshi , masha Allah Abba yace " yana faɗaɗa fara'arsa , Kamill ko sai yanzu yakeyin asalin dana sani sosai .
Ƴar gidan waye ?" Abba ya tambayi Kamill ,
Ƴar gidan Alhaji Sani alherin Allah ce , Abba ne ya ƙara murmusawa yace " haƙiƙa wanan rana nake jira naji daɗi sosai nayi farinciki , ai mutumuna ne shiɗin babu damuwa komai zai dai daita kaidai kaci gaba da nemanta insha Allah auranku zai zamo alkairi ,
Kan Kamill a sunkuye baice komai ba yanata nazarin maganar da ya yiwa Abba , nasiha Abba yashiga yimasa akan halin rayuwa , daga ƙarshe Abba yace" ka kiramin Amina ,
ɓata rai Kamill yayi yace " tafice daga gidan zan shigo naga tahau mota driver ya jata, what..! Abba yace " yaushe ta tambayeni dahar zata fita , oky jeka idan mukayi magana da uban yarinyar zan kiraka , tom Abba Kamill ya fice ranshi ta wani fannin fess wanan makirar zatasha faɗa , ya fice daga gidan ,
Yana shiga mota maganar da ya gayawa Abba dakuma farincikin da Abba yayi akan maganar auran ba ƙaramin ɗaga masa hankali yayi ba ,
Tabbas Diyana bata cikin jerin matan da yakeso , sbda ita ɗin batada kunya ga rashin sanin darajar mutane ,
" Gaskiya nayiwa kaina da zuciyata rashin adalci Kamill yaketa nana tawa kamar bitar karatu ,
ikon Allah ne ya kaisa gidansa , yana zuwa yayi horn ba'a ɗauki lokaci ba mai gadi ya buɗe get ɗin da gudu tare da durƙusawa yana miƙa gaisuwa , ɗabi'ar Kamill ne in ana gaishesa ƙin daraja mai gaishesa , basajin daɗin abinda uban gidan nasu yake yimusu , amma babu inda suka iya shiyasa suke taka tsan tsan da duk wani abu dazai haɗasu dashi .
[31/05, 12:47 am] Mom Islam Ce💃: 💘😭 💘😭

*GUGUWAR ZALUNCI*

PAGA 15&16


bodyguard ɗinsa kuwa kowanne ya shiga tai tayinsa kasancewar oga baya wargi ,
Gashi yafita da ɓacin rai kuma ya dawo dashi .
Fitowa palo Alhaji Safiyan yayi , ganin Ameena na zaune tana danna waya , yasashi neman guri ya zauna , kana yace " meena yaushe zaki dena fita batare da izinina ba ?" waro ido Ameena tayi tace " ina zanje Alhaji ?"
Yanzu na aiko aka cemin kinfita a mota , buɗe baki tayi tasan babu mai yimata wannan sharin sai Kamill ,
Tarasa mai tayi masa ya ɗauki karan tsana ya ɗora mata ,
Hawaye ne suka fara zarya a fuskarta cikin she sheƙar kuka tace " Alhaji sai yaushe ne zaka dena kama maganar wanan yaron ,
Ina nake zuwa ?
Alhaji da ya ƙurawa fuskar Ameena ido yace " naji ya wuce amma kisanj Kamill ba yaro bane yakai time ɗin da zandinga shawara dashi so kin fahimta?"
Kawar da kanta gefe tayi dan intaci gaba da biye masa zasuyi babu daɗi '
Ita kuma batason musayar yawu da mijinta.
Bayan dady ya fito daga wanka momy ta temaka masa ya shafa mai ya sanya kaya , janyota yayi kusada shi suka zauna akan kujera ya kalleta yace " Faty mgnar da nakeson yi dake shine inason mahaifiyata ta zauna tare dani ,
Banison tayi nisa dani duk da akwai mai kula da ita a can ɗin ,nima inason samun nawa ladan , shafo kansa momy tayi kana tace " Habiby nima inason zaman Hajiya a gidannan ,
Ita da kanta ta matsa wai saita koma ƙauye tace " da aljanu a gidanan , nidai a iya sanina bansan dasu ba , amma bansan ko akwai ba .
Gyra zama dady yayi yace " ina tunanin harda rikicin tsufa .
Daganan suka miƙe tare momy ta kashewa dady ido tare da cewa , ga shayinka fa na shigo dashi , okay dady yace " ina zuwa yanzu zan dawo ya fice .
ƙasa ya sauƙo yana tunanin tafiyar mahaifiyarshi , samunsu yayi a palo zaune suna kallo ,
Zama dady yayi kana yace " barka da hutawa Hajiya ,
Ywwa barka Alhaji ya aikin naku ?"
Lpy lou dady yace " yana kallon Tinene da keta baza ido a tv " ke baki iya gaisuwa bane ?" sosa kai ta shigayi tana washe haƙora tace " hannu dai ina uni lpy dady yace " yana murmishi , ring ɗin wayarsa ce ta katse masa maganar da yakeson yi .
Ganin sunan mai kiran nasa yasa shi miƙewa da sauri ya haura steps zuwa ɗakinsa lokacin momy na toilet ɗinsa tana wankewa kasancewar bata yarda da ƴan aiki sudinga taɓa mata abinda ya shafi mijinta ba .
Zama yayi a bakin gado tare da amsa kiran ,
Sadda kai ƙasa yayi da alama da wani babban yake waya ,
dady ne yace " Allah ya temaki mai gida kuma Allah yaƙara maka lpy , daga can ɓangaren mutumin yace " wata muhimmiyar magana ce ta taso amma dole sai mun haɗu .
Cikin rawar jiki dady yace " to ko inzo me kawai ace kamarka ka shigo layinnan ,
NO. mutumin yace " karka damu dole nine zanzo buƙatar hakan ce ta taso karka damu.
Cikin rawar jiki dady yace " to da ƙarfe nawa zaka iso , mutuminne yace " bayan sallahar isha'i yayi ko ?" dady da fara'arsa yace " yayi Allah ya kawoka lpy ,
Sukayi sallama.
bayan dady ya ajiye wayar ne yafara tunanin mai zai kawo Alhaji....gidannan kodai yayi laifi ne , wata zuciyar tace " kazuba ido koma menene zaka gani Allah dai yasa alkairi ne .
Har momy ta fito daga toilet dady bai sani ba yayi nisa a tunanin Alhaji.... kamo hanunsa momy tayi kana tace " habiby ka zauna man amman dai lpy ko ?"
Da 'alamu na damuwa yace " faty baƙo zanyi maza kisa ƴan aiki su haɗa abinci mai kyau kamar kala biyar haka ,
Ok momy tace " kana ta fice , lokaci babu wuya jiyo kiran sallahar magrib yasa dady miƙewa ya yi alwalah ya nufi masallacin gidan ,
Bai dawo ba sai da akayi isha'i sanan ya shigo , babu kowa a palo ya haura step da sauri yana kiran momy , fitowa momy tayi daga ɗakinta , sai zuba ƙamshi takeyi tasa riga da skirt sun ɗameta amma tayi kyau , rungumota dady yai kana yace " Faty na kullum kamar ana sake maidake baby , shafa fuskarshi momy tayi tana dariya tace " to ya ka ganni nayi kyau ko ?"
Yana shirin bata amsa kira ya shigo wayarsa.
Sadda kansa ƙasa yayi tare da cewa ranka shi daɗe barka har kun iso ne ?"
Eh Alhajin yace " gani a mota anbuɗe min get na shigo ,
Dady na shirin ficewa da sauri momy ta taro shi ,
Maiya faru ne Faty ?"
Haba habiby baka gayamin maike faruwa ba nadai ga kana rawar jiki ,
Cikin alamar yana sauri yace " baƙo nayi kuma yanada muhimmanci a gurina, bugu da ƙari kuma kowane ma'aikaci nada burin ganin wanan bawan Allahn ya raɓesa sbda tsananin dukiyarsa dakuma goyon bayan manya daya samu ,
Riƙe baki momy tayi ,
Kana tace " to Allah ya jishemu alkairi ,
Amma shida kansa yazo har gidanka ?"
Ficewa dady yai batare da yabata amsa ba ,
Momy ta jimama zuwan wanan bawan Allahn daga ƙarshe dai tace " Allah ya tabbatar da alkairi ko me ya kawosa oho , ta koma bedroom ɗinta.
Dady na zuwa ya sami Alhaji ya fito daga mota yana zaune a wata farar kujera ,
Da sauri ya ƙarasa yana cemasa barka da zuwa ,
To tashi mu shiga daga ciki ranka shi daɗe ,
Miƙewa Alhaji yayi dady ya kaisa palonsa , palo ne daya ƙawatu da kayan alatu na zamani sai dai duk wanan ba komai bane a gurinsa kasancewar yatara gidajen da sukafi na Alhaji sani komai ,
Ƴan aikin ne suka fara shigo da abinci kala kala , ƴan aikin suna cikin shiga mai kyau drinks da abinci sunkai kala biyar .
kunun aya Alhaji ya zuba a cup kasancewar baya baƙunta akan abinda yake so ,
Bayan ya ajiye cup ɗinne suka gaisa tare da tambayar iyalai dakuma aiyuka ,
Bayan sun gama gaisawa Alhaji ya gyara zama tare da kallon dady yace " Alfarma nazo nema a gurinka ,
Cikin rawar jiki dady yace " har saikazo daka kirani ai .
Murmishi Alhaji yayi yace " a gurguje dai inason gayamaka abinda ya kawoni .
Dady da ya matsu yaji ko menene yace " to ina jinka?.
Masha Allah cewar Alhaji , yarona ne yaga ƴar gurinka yake sonta.
Nisawa dady yai kana yace " wacce daga ciki ?"
Diyana Alhaji yace " yana faɗaɗa fara'arsa.
Dady sai da ya jinjina sunan Diyana a zuciyarsa yasan inhar bata son mutum to ko inuwarsa bata raɓa garama Afreeda .
Alhaji ya lura da dady ya tafi dogon tunani ,
Baiyi masa magana ba saida suka dau tsawon mintuna kana dady yace " karka damu insha Allah bazai gagara ba ranka shi daɗe ,
Washe baki Alhaji yayi yana ganin alamun nasara ta bayyana .
Daganan Alhaji ya miƙe da niyar wucewa , rakashi har zuwa gurin motarsa dady yai Alhaji yace " to nanda kwana uku zan kuma dawowa inhar Allah ya yarda dakuma yarinyar banason aɗau lokaci mai tsayi , insha Allah kawai dady yace " dan bashida wata kalma dazai faɗa ,
Da haka dai sukayi sallama .
Zuciyar dady babu daɗi kasancewar bayason yiwa yaransa auran dole .
Bazai iya hana Alhaji Safiyan auran ƴarsa ba dan yayi masa abinda ba kowane zai iya yimasa ba.
Har aka buɗewa Alhaji Safiyan get dady bai motsa ba , saida ya jima a tsaye sanan ya shige ciki .
Momy nata tararradin dady ko lpy .
suna zaune a palo dady ya shigo Hajiya da kecin tuwo tana suɗe hannu tace " Alhaji ina ka shiga munjika shiru ga abincinka nan ko sai yayi sanyi zakaci ?
Ganin yanayinsa yasa momy shan jinin jikinta , a zuciyarta tace " akwai matsala , cigaba da magana hajiya tayi takuma cewa wai lafiya naganka haka ?"
Lapy lau dady yace " hajiya barin watsa ruwa ina zuwa ,
yana tafiya momy tabi bayansa .
Mtsw Hajiya tayi tsaki tare da cewa kwaji da tsohuwar gulmarku ni har zan tambaye shi abu yaƙi gayamin ,
kwashewa da dariya Diyana da Afreeda sukayi dan lamarin yabasu nishaɗi sosai.
Kunci gidanku wlh yarannan kun raina ni ,
Miƙewa sukayi kowacce bakinta a kunshe da alama dariya suke shirin yi akuwa suna isa kusada ɗakinsu suka saki dariya mai sauti ,
Tinene dake kokawa da ƙashi tazaro ido kana tace " wlh Kaka dariya suke yimiki , ƙwafa Hajiya tayi tana jiran shigowar dady.
kwance dady yake a kan gado idanunsa a sama yana tunanin maganar Alhaji Safiyan ,
Momy tayi tambayar harta gaji daga ƙarshe ta miƙe idanunta sun kaɗa sunyi ja zata fice ,
Miƙewa dady yai tare da ruƙo hanunta yace " matsalar nan ta shafemu duka ,
momy dake nazarin maganar dady tace " kanata magana baka faɗi mafarinta ba .
Dady ne yace " yazo nemawa ɗansa auran Diyana ne , kuma kinga duk abinda Alhaji Safiyan ya nema a gurina dole in bashi koda banida shi dole in nemo masa bare jinina yake nemawa ɗansa .
Jinjina zancen momy tayi ,wai hausawa sukace da kamar wuya gurguwa da auran nesa ,
To ai matsalar Diyanan ce akwai taurin kai ni kaina bata cika bin umarni na ba ,
Dama Afreeda ce to da sauƙi .
Haka dai suka dinga saƙa da warwara suka yanke shawarar gobe insha Allah zasu yiwa Diyana magana dakuma Hajiya .
Hajiya tagama zaman jiran fitowar dady shiru babu shi babu dalilinsa ,
Gashi Tinene nata rafka uban gyangyaɗi ,
Tashinta Hajiya tayi suka nufi ɗakinsu tanata mita harda cewa momy tsohuwar munafuka.
7:am Kamill ya tashi kasancewar yayi sallahar asbha shine ya koma ya kwanta , bathroom ya shiga yai wanka yana gama wanka yai brush tare da fesawa bakinsa mouth freshner ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa da wani kuma rataye a kafaɗarsa ,
Gaban mirror ɗinsa ya nufa yana ƙarewa kansa kallo ,
tabbas a ƴan kwanakinnan ya rame , amma wanan yarinyar ta cucesa maiyasa zai sa tunaninta a ransa cox shi ba ƙara bibiyarta yayi ba , ƙwafa yai a fili yace " da ƙafarki zaki tako har cikin gidana zakisha mamaki ,
Ɗauko mansa mai tsada yai kana ya shafe duk jikinsa da turaruka masu ƙamshi ya gyara sumar kansa ,
Ya miƙe ya nufi drower gurin ajiyar kayansa ,
Riga da wando ya jiro na jeans rigar pink color wandon kuma blue ,
Bayan yasa boxer ya sanya wandon da riga yakuma feshe jikinsa da turare , ya fito palo kunna tv yayi tashar mbc action ,
Hankalinsa sam ba gurin tv n yake ba amma duk wanda ya kallesa zaice tv yake kallo time table na abincinsa ya duba , yau farfesun kifi da soyayyan dankalin turawa dakuma shayi mai kayan ƙamshi kana da kunun gyaɗa za'ayi masa ,
Kasancewar sai ƙare shabiyu na rana yake breakfast yasa babu wanda ya shigo masa da safe
[03/06, 1:36 pm] Mom Islam Ce💃: 💘😭 💘😭

*GUGUWAR ZALUNCI*

PAGE 17 & 18

Yana tsaka da tunani wayarsa tafara ruri ,duba mai kiran yayi sai da yaɗan jinkirta dan kiran yakusa katsewa ya ɗaga tare da sallama ya langwaɓar da kai kamar yana kusa dashi ,,
Abba daga can ɓangaren yace " my lovely son ka tashi lpy ya hutawa , Kamill dake ɗan yamutsa fuska yace " am fine Abba ya aiyuka , lafiya Abba yace ".
Daganan Kamill yayi shiru , Abba ne yace " jiya naje gidansu yarinyar nan munyi magana da mahaifinta yace " insha Allah bazai gagara ba ,
Kamill da ko son jin sunan Diyana bayayi yace" tom Abba ,
Bakada lafiya ne ?" cewar Abba Cewa" Kamill yayi banajin daɗi ne ,
Subhanallah dady yace " kayi ka fito kaje hospital ,
Kamill ne yace " inada ragowar magani naji sauƙi ,
Alhaji bayason musu yayiwa Kamill sallama ya ajiye wayar .
10:am kowa ya hallara a dining domin karin kumallo inka cire Hajiya da Tinene dake ƙasa kan kafet a zaune suna nasu karin ,
Bayan sun kammala dady ya dubi Hajiya yace " Hajiya ya kike ganin maganar da mukayi ɗazu dake , tunda yanzu ga sunan ,
daga Diyana har Afreeda babu wacce ta fahimci abinda dady yake nufi ,
gyara zama Hajiya tayi kana tace " gaka gasunan ai kokuma ince gatanan ai ,
Komawa kan kujera dady yai Diyana na shirin barin gurin hanunta riƙe da waya dady ya tsayar da ita ,
Juyowa tayi batare da tace " komai ba , sanin dama ba magana zatayi ba yasa momy buɗar baki tace "haba daughter ana yimiki magana kin tsaya kamar kurma?" tahowa tayi ta nemi guri nesa da kujerar dady ta zauna tare da cewa gani dady ,
Yatsina baki Hajiya tayi kana tace " wlh bakida hali mahaifinki na yimiki magana kin wani tsaya kamar sa'anki ,
momy dai batada bakin magana ta rufe bakinta ,
Wata uwar harara Diyana ta dokawa Hajiya , cikin sauri Hajiya ta miƙe tare da saka kururuwa tana salati ,
Alhaji na gaya maka bazan zuna a gidanan ba ka matsa yanzu gashi wanan marar kunyar tana nema ta dokeni wlh kashiga tsakanina da ita tun wuri,
dady kam yarasa ta cewa ga damuwar Hajiya ga damuwar shi , shida Diyana ,
Hajiya kiyi hauri dan Allah zanyi mata magana amma yanzu mu samu mu kashe wutar dake gabanmu ,
Shiru Hajiya tayi tana girgiza ƙafa kamar mai jiran a taɓota .
Diyana " dady ya kira sunanta a hankali .
Na'am dady , Diyana tace " ta maida hankalinta gareshi ,
Alfarma nake nema a gurinki da fatan bazaki watsamin ƙasa a ido ba ?" jimm Diyana tayi kana tace " insha Allah dady bazan watsama ƙasa ba.
good Dady yace " nayi miki miji ......! Jin zancen tayi kamar saukan aradu ba ita kaɗai ba har Afreeda ma saida ta girgiza da jin wanan zance ,
Dady bai bari ya kaleta ba saboda kalonta zai iya sa zuciyarsa karaya ,
Yacigaba da cewa " haƙiƙa ina alfahari daku dakuma tarbiyar da nabaku nidai banida burin yiwa ƴaƴana auran dole ,
yanzu dai inason jin ta bakinki Diyana sbda ba wani ne zaiyi miki zaman auran ba , kuma zaman aure ba abin wasa bane zamane na har abada .
yanzu wace shawara kika yanke ?" Hawaye ne suka fara sintiri a kyakyawar fuskar Diyana babu sautin kuka sai zubar hawaye , tafa hannu Hajiya tashiga yi tana ni ƴasu sai kace " wacce za'a fillewa kai toni lokacin da aka yimin aure bansan kakanku ba ,kuma ban taɓa ganinsa ba sai ranar da yashigo dakina bayan an ɗaura aure ,
Dariya ce taso kuɓucewa momy dake zaune a kujera ta zuba tagumi, toshe bakinta tayi bata bari kowa ya gane ba ,
Bayan Hajiya tayi shiru dady ya kuma tambayar Diyana a karo na biyu ,
kalmar da ta fito daga bakinta ne yayi matuƙar firgita mutane kowa yayi mamaki.
Na 'amince dady na amince ta miƙe tayi bedroom ɗinsu da gudu hawaye na zarya a fuskarta , momy ma hawayen take sharewa kasancewar tasan Diyana ba har cikin zuciyarta ta faɗi wanan kalmar ba,
Liyafa dady yasa a shiryawa Alhaji Safiyan ta bangirma abinci kala2 .
Bayan isha sai ga kiran Alhaji nan ya shigo ,
Dady na ganin kiran ya miƙe jiki na rawa ya fice , samun Alhajin yayi a jingine a jikin motarsa kamar inda yayi rannan da sauri dady yace " haba Alhaji tashi mu shiga ciki dan Allah ,
Miƙewa Alhaji yayi tare da rufawa dady baya suka shiga palon dady ,
Bayan sun gaisa dady ya gabatar masa da abinci , kaɗan Alhaji ya taɓa kana yace " ya ƙoshi kai tsaye suka fara maganar ƴa'ƴan nasu , dady ne yace " na tuntuɓi ƴar gurina tace " ta amince ,
Kafin dady ya kai ga ƙarasa magana Alhaji ya faɗaɗa fara'arsa yana yiwa Allah godiya , cikin zuciyarsa yana cewa haƙiƙa duk da bansan yarinyar ba nasan yarona yayi dace duba da halin mahaifinta na cika alƙawari , masha Allah kowanensu yace " Alhaji ya dubi dady yace " a yanke dukiyar aure atemaka mana banason auran ya wuce wata ɗaya .
Dubu ɗari ma yayi Allah yasa ma dukiyar da auran albarka ,
Dariya Alhaji yasa kana yace " a haba zanbada 1 million ƴarka ƴata ce .
Nasani dady yace " karka manta Alhaji bawai naƙi bane amma mafi ƙanƙantar sadaki yafi daraja dakuma ƙarawa aure ƙarko , daganan sukayi sallama
Akan gobe zai turo magabata ,
dady na komawa bai zarce ko ina ba sai ɗakin mahaifiyarsa , ya bata labarin abinda ke wakana cewa Hajiya tayi " karka damu ka tura direba ya taho da ɗan uwanka hudu sai ya tsaya akan komai , dady yai farinciki yayiwa Hajiya sai da safe .
Duk wanan abin da akeyi Diyana batasan waye mijin ba ita dai ta amsa .
Washe gari abinka da masu shi ƙarfe biyar har ƴan uwan dady sunzo su biyu ,
Bayan sallahar isha'i baƙin dady sun hallara , aka bada dukiyar aure dubu ɗari biyar dady yaƙi karɓa amma sun turje sai da sukasa ƴan uwan dady karɓar kuɗin.
Suka sanyawa dukiyar Albarka tare da auran in an ɗaura , daganan aka saka rana wata ɗaya ,
Dady bai dawo cikin gida ba sai wajen ƙare 11pm na dare direct ɗakin momy ya nufa , tana sanye da sleeping drees wanda ya fito da ilahirin kyanta ,
Dady da yazo bata labarin abinda sukayi ai yama mance ya shiga toile ya yi brush kana ya watsa ruwa ya sanya jallabiya yabi bayan momy , niko nace asbha ta gari dady lol.
Washe gari dady ya dawo daga masallaci da asbha , ya sami momy da zaune kan sallaya tana karatun alqur'ani , saida ya jira ta idar kana ta gaishesa ,
Bayan sun gaisa dady yace " Faty jiya fa ankawo kuɗin auran Diyana wani uban faɗuwar gaba taji amma tarasa dalilin hakan , murmishin yaƙe tayi tare da cewa Allah ya sanya alkairi ,
Suka shiga wata hirar daban , momy ce ta katse musu hirar ta hanyar cewa " niko sunama waya da saurayin kuwa ?" dady dake nazarin maganar momy yace " to wayasani ko zatayi ai ba sani zakiyi ba , shiru momy tayi daganan kowa ya kama gabansa ,
Dady yayi ɗakin Hajiya dan ya gaisheta momy kuma ta shiga wanka ,
Zaune take itada Afreeda suna tattauna abinda ya faru jiya , Afreeada ce ta dubi Diyana tace " sis yanzu kin yarda da auran dole kenan bakima san mijin ba ?" karki damu my sis su dady nayiwa biyayya ina tausayin momy yanzu da ban yarda ba sai kiga Hajiya da dady sunkama jin haushinta , nasani itama bataji daɗin hakan ba , amma a yau ɗinan danaji ance wai ankawo dukiyar aurena , nayi danasanin cewa na yarda , ta fashe da kuka ,
Lil sis ban taɓa soyayya ba bansan ya ake yinta ba to yazanyi da mijin takuma fashewa da kuka mai sauti a karo na biyu ,
Rungumeta Afreeda tayi suka cigaba da kuka .
kira ne ya shigo wayar momy lokacin tana zaune a dining zasu fara breakfast , kasancewar ta shiga ta kira su Diyana ,
Allah ya temaka lokacin sungama kukan har sunyi wanka amma mai lura yaga idanunsu zai gane sun zubarda hawaye ,
Ɗaga kiran momy tayi tana dariya tace " haba mom Khady zan aiko su Afreeda anjima suzo su karɓa min , jinayi momy ta ce sai anjima tare da ajiye wayar , dady ne ya kalli momy yace " dawa kike waya?" murmishi momy tayi kana tace " da matar abokinka man Mom Khady ok dady yace "
Hajiya dake ƙasa ana cin farfesun kaza ta taɓe baki tana zabgawa momy harara , lol ko meye damuwarki ƴar tsohuwa oho .
Suna gama breakfast sukayi bedroom ɗinsu ,
Shigowa momy tayi riƙe da wata bag a hanunta ta miƙawa Diyana , amsa Diyana tayi tare da cewa meye wanan momy , momy ce tai murmushi tace " kwalabe ne zakiji komai idan kukaje amma karfa ku daɗe dan Allah ,
to sukace kowacce ta canza kaya , iri ɗaya sukasa riga da skirt na atamfa mai ratsin green and wite ba ƙaramin kyau sukayi ba musamman ma Diyana da kamar dan ita akayi atamfar ko ince ɗinkin ,
takalminsu kala ɗaya kai komai ma wayace kowa da kalar tashi suka fito tare da bag ɗin da momy ta basu suka nufi gurin driver , sbda babu wanda zasu aika ƴar aikinsu ta tafi garinsu gaida mahaifiyarta ba lpy , samun drivern sukayi a tsaye yana jiransu , motar da ya fito da ita Diyana ta kalla tare da yamutsa fuska ta lumshe ido , ta buɗesu kamar mai jin bacci tace " bazamu shiga wanan ba ka fito da sharon nafijin daɗin hawanta ,
Jikin driver na rawa ya fito da motar suka shige , mai gadi ya buɗe suka ɗauki hanya ,
suna cikin tafiya go slow ya haɗu , mutane kowa na tofa albarkacin bakinsa ,
Wata mota mai ɗan karan kyau ce ta fito daga wani titi da yayi hanyar gaban wato titin da su Diyana zasu bi ,
Ran Diyana ya ɓaci a masifa tafara tana shirin buɗe murfin mota tana cewa " wanan ai rainin wayo ne yaushene za'a tare mutane akan wanan banzar motar shi waye mai motar ? ta ƙarasa fitowa tana bam bamin masifa , wani bawan Allah dake kan mashin kana ganinsa zaka gane ya haifi Diyana dan a ƙalla yayi sa'an mahaifinta , yawu Diyana ta tofar tana ƙaƙarin amai , kai kuma waye da zaka zo ina magana kana magana , Allah ya baki haƙuri mutumin yace " tare da jan mashin ɗinsa

Please Login or Register in order to submit comment