Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka kwaranyo mata tace "inna inkika tafi wazai dinga bani wani abin idan na nema , Hajiya ce ta kunce ɗaurin zaninta kana ta ciro kuɗi a lalitarta, sunkai dubu goma ta miƙawa Talatu da keta share idanunta da mayafi ,
Cikin farinciki ta karɓa tana godiya .
Hajiya tasan wuyar da Talatu kesha a gidan mijinta wata rana baya bada kuɗin cefane kokuma yace" ta auni masara ta kai niƙa babu kuɗin girkawa hakan yasa Hajiya take matuƙar tausaya mata amma bata cika nuna mata a fili ba sbda gudun wata rana ,
Hasali ma shine yasa takeson ɗaukar Tinene duk da ta zamo budurwa dan a ƙalla zatayi shekara goma sha huɗu ,
Hajiya nada tabbacin kakar baɗi ubanta zai ce aure zaiyi mata kuma gidansu haɗin zumunci sukeyi .
Hajiya ce ta ƙara kai kallonta ga Talatu tace " inada buhun masara a ɗaki dana wake kuma ga shinkafa nan rabin buhu akwai mangyaɗa , duk ranar da bakida kayan awo ga mukulli nan kizo ki buɗe ,
Wani sabon kukan Talatu ta ƙara fashewa dashi tana tunanin kowa ya rasa mahaifiya yayi kuka tabbasmahaifiya itace abin alfahari ga kowane ɗa kuma itace take sanin ɗanta yaci ko bai ciba dazarar taga bai ciba zata fasa cin nata ta miƙa masa ,
haka dai sukayi sallama jikinsu duk a mace Tinene kam murna ta cika zuciyarta burinta taje birni ta waye tadinga kalar tafiyar Diyana dan komai na Diyana birgeta yakeyi .
Hajiya na kulle ƙofar ta miƙawa Talatu mukulli takuma ce mata akwai dambun nama a kwallah ki ɗauka mukan mun fito.
[31/05, 12:42 am] Mom Islam Ce💃: 💘😭 💘😭
*GUGUWAR ZALUNCI*
PAGE 7 & 8

NA

Wattpad momislam2020
Facbook mom islam mon islam
Email:
Zainabhabibu@gmail.com
Whtsapp: 08141799224

To Inna Allah ya saukeku lafiya cewar Talatu , Hajiya ma dauriya takeyi haka dai akasa abubuwan da takeso suka shiga mota ,
Tinene ta ƙwalawa Talatu kira , tana matsowa tace " Talatu dan Allah ki gayawa Bashiru nayi tafiya , maketa Talatu tayi kana tace " bakida kunya ne kifa kintsu Tinene rayuwar binni ba irin tamu bace ki nitsu ina gaya miki , sallama suka kuma yi motarsu ta tashi zuwa garin shugaban ƙasa wato Abuja ,
Basuyi wata tafiya mai nisa ba dan basu fita a kano ba Hajiya ta tsayar da driver tana cewa" kai baka tsayawa mutane suyi fitsari ne ? ko kuma so kakeyi yarinya tayi a wando ,
Ayi haƙuri Hajiya driver yace yana parking ɗin motarsa a gefen titi fita sukayi tare da wani galan da suka ɗuro ruwa a cikinsa,
Hajiya ma fitsarin tayi suka dawo mota .
Fitarsu Kano keda wuya Tinene ta hango mai gasa masara shirin kuka tahau yi tana cewa Hajiya itafa yunwa takeji ,
Shidai driver badan uwar mai gidanshi ya ɗauko ba babu abinda zai hana baiyi musu magana ba ,
Hajiya ce tace " kai tsaya a siya mata wani abun tasa a bakin salati ,
Driver ne yace " Hajiya nan basu siyar da komai fa , Tinene ce ta karɓe da cewa ga mai masara can wlh ko ita nasamu ai ƴaƴan cikina sa barni na huta ,
Hajiya ce ta ciro nera ɗari tace " driver ya siyo musu ƴan uku hamsin ,
driver yasan babu hakan yasa ya ciro kuɗi a aljihunsa ya miƙawa mai masara dan yasan inhar yakoma bai siyo ba Hajiya zata iya tsigaleshi , yana miƙa musu ,ya tada mota .
Sunyi tafiya mai nisa sbda sun wuce garuruwa da dama , jin motar tayi shiru yasa shi leƙa wa ta mudubi , hamdallah driver yayi ganin mai damun mutane tayi bacci , cikin ikon Allah sai gasu a Abuja har sunkusa layin su , Hajiya ba taɓa zuwa tayi ba shiyasa tayi gum da bakinta ,
Horn ya shiga yi , mai gadi ne ya wangale get ɗin yana ɗaga musu hannu ,
Hajiya ƙarewa gidan kallo takeyi badan ta ɗan yarda da drivern nan ba da zata iya cewa gidan ƴan yankan kai ya kawota amma bari ta zuba masa ido tagani ,
Yana parking ya fito tare da buɗewa su Hajiya ,
Tinene tayi bacci Hajiya ce ta ɗaka mata duka a razane ta tashi takalli Hajiya sanan ta kalli ina suke , mutsuke ido tayi tace " alkur'ani da gaske ne nayi mafarkin gani a wata sabuwar duniyar Hajiya ce ta sharara mata mari kana tace " zaki fito ko zaki zauna ni gaba zanyi dan inama tunanin kamar ba gidan Alhajin ya kawomu ba sbda babu ko wulƙawar mutane sai tsintsaye , Tinene ce ta fito tana shafa kumatunta ,
Ta nufi gurin mai gadi , gaishe sa tayi kana tace " muna neman masu gidannan , mai gadi ne yace "ciki zaku shiga bazasu jiku daga nan ba amma kuzo muje ,
Sai da ya kaisu har bakin wata ƙofa mai glass kana ya ƙwanƙwasa ,
Da sauri ta fito jikinta sanye da kayan bacci da alamu bugun ƙofar ne ya tasheta ,
Tsawa ta dakawa mai gadi kana tace " waye ya baka izinin shigowa nan ?" durƙusawa yayi har ƙasa yana bawa Diyana haƙuri saboda kaf cikin ma'aikatan gidan tsoronta sukeji sosai ,
Kasancewarta mace mai wani irin hali wato ƙasai ta bugu da ƙari kwarjini , Hjiya ce tayi saurin leƙowa tana cewa " waye yake mgna Diyana da bata gane ko wacece ke magana ba kasancewar Hajiya na can baya mai gadi kuma yana kusa da ƙofar ,Tinenuwa kumatanacan gurin tsintsaye tana kallonsu ,
Diyana tace " nice nan Diyana ,
Ai da sauri Hajiya ta matso tana cewa kauce kibani guri iyayi yayi muku yawa ,in mutum zai shigo har sai an tambaya ,
tunda Diyana ta tabbatar Hajiya ce ta iso tayi shiru kamar ruwa ya cinyeta Allah ne kaɗai yasan irin abinda zuciyarta ke shirya mata,
Kutsawa Hajiya tayi tana tana sana'ar tata wato mita , shikam mai gadi ya wuce tuni .
juyawar da Tinene zatayi taga babu Hajiya ai da gudu ta ƙara taje ta tura ƙofar ta shige ,
Samun su Hajiya da momy da Diyana da Afreeda tayi suna zaune a kujera anata gaisawa , samun guri tayi itama ta zauna tare da cewa " ina wuninku , lpy momy da Afreeda sukace banda Diyana daketa yamutsa fuska , Hajiya kam anbaje akan kujera anata zubawa momy labari , Tinene ce ta kalli Diyana ta nunata da yatsa tace " kaka wanan ce tazo gidanmu hekaran jiya ko ?" eh Hajiya tace " ai wanan da kike gani bansan gadon waye tayo ba , sam batason mutane .
Momy ce tayi dariya kana tace " ai wlh Hajiya nima ina tunanin hali irinna Diyana amma inaga halitta ce kawai ,
Hajiya ce ta gyara zama tace" inason Alhaji yazo muje gurin wani babban malami ƙila tanada matsalar aljanu dan naga kamar ba ita kaɗai bace ,
Tuntsirewa da dariya Afreeda tayi tana kallon bakin Hajiya sai kai lomar shinkafa takeyi ita da Tinene ,
Kuma kai wata lomar Hajiya tayi tace " tun lokacin da tazo gurina naga take taken hakan , momy ce tac" to Allah yabasu haƙuri , amen suka amsa banda Diyana da haushi ya cikata ,
Cikin ranta tace wato wanan tsohuwar tun yanzu zata fara ɓatamin rai ko ?" to wlh mu zuba zata gane batada wayo ta miƙe tayi bedroom ɗinsu, da yamma bayan la'asar kowa ya shige ɗaki Hajiya da Alhaji ne a zaune sai Tinene dake ƙasa a gefe tana kallo a tv hango wani mutum tayi yana kuka da alamu wani abinne ya sameshi a shirin film ɗin ai itama tahau share hawaye tana cewa" Allah sarki hankalinsu Hajiya bai kai gurinba sai da taji anja mata ƙafa tayi ƙasa ,wani wawan ihu Hajiya tasa tana riƙe da gurin ,Tinene da tayi abun hankalin na gurin tv tana kuma kaiwa Alhaji shirin naushi ,
Kaucewa Alhaji yayi yana tunanin anya wanan yarinyar mai lafiya ce kuwa ?.
Sannu Hajiya dady yace " yana kallon ƙafarta ,
Fitowar momy da Diyana da Afreeda ne yasa dady cewa zoki ɗaga Hajiya da azama momy ta ƙaraso tana cewa mai ya sami Hajiya ? abinda ya faru dady ya gayawa momy , ji sukayi an kwashe da dariya ,juyawa sukayi dukkansu harda mai kallo , ba kowa bace sai Diyana da ta riƙe ciki tana dariya , dady ne ya ɓata rai kana yace " ke Diyana kinci gidanku dan bakida kunya Hajiyar ce abin yiwa dariya kina gani tana fama da ƙafa wanan sakaran takuma jibga mata naushi ,
Da gudu Diyana tayi ɗaki saboda wata sabuwar dariyar ce takuma kawo mata ziyara,
riƙe haɓa Hajiya tayi tace "Faɗimatu kingani ko kinga abin da nake gaya miki ko ?" to Alhaji tun wuri kayiwa tufka hanci tun kafin suyi mata illa ,
dady da bai fahimci abinda Hajiya take cewa ba yafara tambayar mai ya faru ,mayar masa Hajiya tayi kana ta ƙara da cewa " a gaggauta wlh .
Itadai momy batada bakin magana sai eh da eh , dady ne yafara yiwa Tinene faɗa yake gaya mata mutanen tv ba fitowa sukeyi ba kuma basujin mutane , shiru tayi kai kace ba ita ta aikata ba ,
Miƙewa Afreeda tayi ta nufi bedroom ɗinsu tinda comedy ya ƙare , da dare yayi bayan isha'i mai aiki ta jera musu abinci a dining , Hajiya tunda taga anan za'aci abinci tace " bata yarda ba a kawo mata nata ƙasa , babu mai yimata musu kaf ɗinsu momy ta sauko mata dashi akan faranti ,
Diyana bata fito cin abinci ba sai Afreeda da ta zuba farfesun kifi tana ci ,
ina daughter ?"dady ya tambayi Afreeda ,
Afreeda ce tace " tana bedroom tunda tayi sallah ta kwanta ,
Buɗar bakin Hajiya tace " ba dole kaga mutum kamar muciya ba babu auki saboda baici abincin gidansu ya ƙohi ba,
Kai lomar tuwon shinkafa tayi tana mita ,
Tinene dake zaune da shinkafa da miyar kifi a gabanta tace " Allah sarki Talatu ko taci hinkafar da kika barmata oho ,
Hajiya ce ta dubi Tinene tace " maza kiyi kici kije ki kwanta , Faɗimatu ki nuna mata ɗaki karta cika mutane da surutu ,
Miƙewa dady yayi ya yiwa su Hajiya sallama ya shige ciki .
Washe gari takama laraba Diyana da Afreeda zasuje bikin wata classmate ɗinsu ko wacce burinta tayi kwaliya ta kece raini kasancewar yarinyar wani babban ma'aikaci ne amma bai kai dadynsu Diyana kuɗi ba,
Kar mai karatu ya ɗauka shima mahaifin amaryar talaka ne , no yanada kuɗi sosai kuma babu wanda bashida labarin mahaifin amaryar harnyanzu ana damawa dashi ,
Sai dai shi mahaifinsu Diyana wani attajiri ne wanda ko shi bai san iya adadin dukiyarsa ba , kasancewar sa mai kuɗish sosai ,
Kayane anko suka ɗinka kala uku uku kowane ɗaya zaiyi 50k ɗinki kuwa anyi masa na 5k atamfa da less da material babu na kushewa a cikinsu ,
Yau akeyi ɗaurin aure , in suka tafi yau sai gobe zasu dawo .
Diyana ce ta kalli Afreeda tace " sis yanzu mai zamu kaiwa amarya a matsayin tamu gudun mawar kinsan dai in muka bata kuɗi ba karɓa zatayi ba ,
Afreeda na saka skirt da ƙyar tace " sis yanzu dai gurin momy zamu dan wlh nima kaina yayi zafi burina inganni a gurin bikinnan ,
ƙarfe huɗu duk sun gama shiri Maltina Diyana ta ɗauko a fridge kaɗan tasha ta riƙe ragowar a hanunta suka nufi bedroom ɗin momy .
Samunta sukayi tana sa kaya ,zama Diyana tayi a bakin gado ita kuma Afreeda ta zauna a kan stool dake gaban mirror ,
Kallonsu momy tayi da fara'a tace " harkun shirya ne ?" eh suka ce Diyana ce ta shagwaɓe fuska tace " mom munrasa abinda zamu kaiwa Khairat a matsayin namu kyautar , riƙe baki momy tayi kana tace "karku damu ga wani haɗin humra da turaren wuta da nasa aka yimin haɗinsa tun daga maiduguri so ku tafi dashi kawai duka inyaso zanyiwa Hajiya Falmata magana ta ajiye min in tanada ragowa , rungume momy sukayi suna godiya ,
Afreeda ce tace " momy bakice munyi kyau ba , dariya momy tasa tace " ai wanan kwaliyar taku ko maƙiyi ,
sukasa dariya dukkansu lokacin da suka kammala shiri ƙarfe biyar na yamma , sunyi kyau kamar ka sacesu ka gudu Diyana ce ta ɗora baƙin glass ɗinta a ido kasancewar ta ma'abociyar son sakashi amma Afreeda bata damu da sanyawa ba,
ƴar aiki suka aika kiran driver , sai gasu sun dawo a tare Diyana ce tace " driver sabuwar mota zaka fito da ita , kafin ta ƙarasa magana driver yace " to Hajiya angama insha Allah , fitowar momy taci karo dasu sai ga Hajiya nan ta ɓullo tana ɗingishi , wayar Diyana ce ta fara ring ko kallon Hajiya bata yi ba ta ɗaga wayar , Khairat ce take magana kamar zatayi kuka ,
Haba sis kufa ake jira a gurin reception ɗinnan pls kuyi sauri , Hajiya ce ta gyara tsayuwarta tace "yau naga duniya yara su koma kamar zabiyoyi jibeku ko kyau bakuyi ba ,
Afreeda da hankalinta yayi gurin shagali tace " bye momy Hajiya bye tana ɗaga musu hannu , ganin cikinsu babu wacce ta kulata yasata cewa " ke zabiya zoki tafi da Auta itama taga gari ,
Ai da gudu suka fice,
Suka shige mota sai gurin biki , sunyi tafiya mai nisa kana suka iso ƙawataccen gurin da idan ka ganshi sai ka rantse a ƙasar waje ne , iya tsaruwa gurin yayi, suna sauka a mota na hango wata budurwa batada jiki tana sanye da doguwar riga fara ta yafa mayafin rigar a kanta ,
da gudu tayo gutinsu Diyana tana faɗin barkan ku sists wato munce bamuson let sai da kukayi ko ? ga anty Khairat can taƙi sakin jiki wai dan babu anty Diyana , lumshe ido Diyana tayi kana tace "am sorry amaryar mu tayi haƙuri ganinan na ƙaraso ,
Afreeda ce taja budurwar mai suna Siyama sukayi gefe ita kuma Diyana ta shige ciki ,
Da shigarta kallo ya dawo kanta kowane saurayi mai ji da kansa ita yake kallo hatt MC ma ita yake kallo ,

Gashi dai kayane da kowa na gurin yasan tsadarsa da kyansa kuma ba wata fayattaciyar makeup tayi ba amma hakan bai sa sundena kallonta ba ,
Cikin sauri tayi hanyar da zata sadata da gurin zaman amarya,
Tun daga nesa Khairat tafara fara'a da dariya ɗauke a fuskarta , Diyana ma maida mata da dariyar takeyi tana tafiya ,
Batasan da mutum a gabanta ba ta bigeshi wayarta ta faɗi ƙasa ta watse gefe ,
A, zuciye ta ɗago kai ta waysawa wanda ta bige harara kana ta ƙara masa da mari ,
Baice komai ba sai shafa gurin da yayi kafin kace me hankalin kowa ya dawo gurinsu bodyguard ne guda uku suka yi kana da shirin duka ,
Matashin saurayin ya dakatar dasu yana huci .
Durƙusawa Diyana tayi ta cire sim ɗinta tabar wayar a gurin , ta ƙarasa gurinsu Khairat da taketa zubda hawaye tana kallon Diyana , zama Diyana tayi takai dubanta ga Khairat da idanunta sun fara ja tsabar kuka ,
"afuwan amaryar mu cewar Diyana , Kamill wato ango da yanzu ya dawo gurin zamansa , kasancewar yaje bawa babban amininsa haƙuri ya dubi Diyana ,
yace "amma Diyana kinyi ganganci maiya kaiki kula wanan bawan Allahan?",
Lumshe ido Diyana tayi tace " Kamill sanin kanka ne bana ɗaukar raini shiɗin waye waye babansa ? shiii!!!, Kamill yace " karki ƙara magana ,
Ƴan matan dake gefe sai kallon Diyana sukeyi masu gulma nayi kowa yana ganin Diyana batada tarbiya wasu kuma daga can gefe , suna cewa ai gara da tayi masa haka ,
Maganin mutumin da bai ɗauki ɗan adan da daraja ba kenan ,
Shigowar Afreeda kenan taga anata nuna Diyana , kai dubanta tayi gurin da Diyana take zaune ,
ganin fuskarta babu walwalah yasata ƙarasawa da sauri ,
Ruƙo hanun Diyana tayi tace " my sis maiya faru ?" kiyi haƙuri kinga na daɗe ko ?" munje duba wata abaya ne da za'ayi yayi wanan sallahar ,
lumshe ido Diyana tayi kana takuma buɗesu tace " karki damu sis damuwata da ban kizo ki zauna ,
Khairat itama jikinta duk yayi sanyi , haka dai aka kira abokan ango da ƙawayen Amarya , farko sunan Diyana aka fara kira na biyu kuma babban aminin ango wato Kamill , sai da gaban Diyana ya faɗi , komawa gurin Kairat tayi ta raɗa mata a kunne cewar sis bazan iya rawa da wancan banzan ba.....!
[31/05, 12:43 am] Mom Islam Ce💃: 💘😭 💘😭

*GUGUWAR ZALUNCI*
PAGE 9 & 10


*AREWA WRITERS ASSOCIATION*

Sa sauta murya Khairat tayi kana tace " pls kiyi haƙuri kije na lokaci ɗaya nefa ,
Badan Diyana taso ba ta wuce ta nufi gurin da aka tanadar musu na rawa ,
Mc ne yasa mutanen gurin tafa musu , ya fara kwararo musu yabo , kaga matashin saurayi mai ji da kansa ƴan mata ma wawarka sukeyi , kai ku tafawa Alhaji Kamill ɗa ɗaya tilo a gurin mahaifinsa wato Alhaji Safiyan gidan kuɗi .
A zabure Diyana ta ɗago kai takai dubanta ga Kamill da shi hankalinsa ma ba a gurinta yake ba ta kawar da kai ,
innalilahi ragowar ta maƙale mata ma maƙoshi , tasani ubansa ba sa'an ubanta bane yafi ubanta dukiya hatta mahaifinta yana girmama Alhaji Safiyan kuma yafi mahaifinta suna kasancewar sunansa ya zaga ƙasashe da dama harda na ƙetare ,
Duk da shima ubanta sunanshi ya shahara amma ko kwatan na uban Kamill bai yi ba ,
Jiyo maganar Mc tayi yana cewa " an gaisheki babbar ƙawa aminiya kyakyawa kuma kuma fasihiya a fanin iya kwaliya kai kubata tafi , kowa yakama raf raf hankalin mutanen duk ya dawo gurinsu ,
mc ne ya bada umarni aka sanya waƙar da akayi ta biki , Kamill rawa yakeyi tsakaninsa da Allah matsowa kusa da Diyana yayi yace " ƴan mata ki taka man karki bada manyan mata har video akeyi fa , wanan sunkuyowar da Kamill yayi yana yiwa Diyana magana wasu abokan Kamill suka fara ɗaukarsu hoto aikuwa sun bada kala ,
Ɗan takawa tafara a hankali jikinta a sanyaye amma tanajin inhar Kamill ya kuma ɓata mata rai babu abinda zai hanata ci masa mutunci koda komai zai faru ,
tsayar da kiɗan akayi mc yace suje su huta , ran Diyana ya ɓacci sosai musamman da zasu sauko Kamill yakuma sunkuyawa yayi mata magana .
Khairat ce ta janyo Diyana tace " nagode sis nasaki abinda bakiso ko am sorry , rufe mata baki Diyana tayi da cewa " a'a sis karki damu wancan banzan ne ya ɓatamin rai badan haka ba da komai zai tafi normal,
ƙarfe 8pm an tashi anyi su yanka cake da hotuna, Afreeda ce ta kamo hanun Diyana tana cewa sis momy na kira wai mudawo gida okay Diyana tace ".
Bayan sun bawa ƙanwar Khairat abinda zasu bata sukayi sallama , kasancewar Afreeda ta kira driver yazo ya ɗaukesu , suna fitowa sukaci karo da Kamill yana waya yana murmishi , tsaki Diyana taja kana ta janyo Afreeda sukayi mota , wani killer smile Kamill yayi ya zura hannayensa cikin aljihun shaddarsa , ganin motarsu na shirin tashi ya koma gefe ya tsaya tare da ciro wayarsa , numbar bodyguard naga ya dannawa kira ko 3 mins ba 'ayi ba sai gasu nan sun taho sun tsa tsaya a gabansa tare da sunkuyar da kai ,
sukace barka prince yawancin abokansa da sunan suke kiransa amma ba kowa yasan da wanan sunan ba ,saboda wasu dalilai , haɗe rai yayi yace " kunga waccan motar maza kubita karku bari su gane okay sukace , cikin hanzari suka shige mota ,
Sukabi motar da yanzu ta fice daga harabar gurin.
Tafiya drivern nasu yakeyi cikin ƙwarewa ba kowa zai san yanabin wata mota ba kasancewar ko kwana motarsu Diyana batayi ba .
Tunda Diyana ta shiga mota tafara tuno abinda ya haɗasu da kamill a zahiri itama tanada laifi amma sam batason raini hakan yasata yimasa rashin mutunci ,sai huro hanci takeyi .
Afreeda ta lura da yanayin sis ɗin nata amma bata kulata ba kasancewar tasan halinta inta fiya shiga harkarta a time ɗin da take cikin baƙin ciki sukan iya ɓatawa su kuwana ma basu shirya ba ,
A haka suka isa gida babu mai cewa komai ,
Bata jira driver yazo ya buɗe motar ba ta fice zuciyarta nayi mata ƙuna ,
ko sallama batayi ba ta shiga palon ganin Hajiya da Tinene a palo yasata yamutsa fuska ta wuce bedroom ɗinta ,
Hajiya dake zaune ta riƙe haɓa tana jinjina lamari irin na Diyana ,
A fili tace " nikam wanan wace irin yarinya ce batasan darajar mutane ba , Tinene dake zaune gefen Hajiya tace Hajiya sufa ƴan binni basu damu da sallama ba ,
Hajiya ce ta ranƙwasheta kana tace " badai duka ba ita wanan mai zuciya kamar faɗa wuta bansan gadon wa tayo ba,
Sallamar Afreeda ce ta katse musu zance suka amsa tace " sannu Hajiya ,
Washe baki Hajiya tayi kana tace " ywwa ƴar albarka kun dawo lafiya ?" lafiya Afreeda tace" ta wuce ciki .
Kai tsaye bedroom ɗin momy ta wuce , da sallama ta shiga ta gaida momy , kun dawo sai yanzu ko ? momy ta jerowa Afreeda tambayoyi , am sorry mom wlh matsala aka samu amma yanzu komai yai normal ,
Momy dake kallon fuskar Afreeda tana nazrin ta tace " ina Diyana ?" tana bedroom ,
Kiramin ita,
Tom Afreeda tace " Afreeda na fita momy tashiga tunani tasan duk lokacin da ran Diyana ya ɓaci bata wai wayar kowa har ita ma to yau kuma maiya faru ?" batada mai bata amsa yasata zama gefen gado tana jiran shigowar Diyana ,
A' ɗakin Diyana Hajiya ce tsaye a bakin ƙofa tana balbale Diyana da masifa akan rashin ladabi , kuka Diyana tasa mai sauti dan a halin yanzu babu abinda zatayi zuciyarta tayi mata daɗi sama da kuka ,
Tafa hannu Hajiya tafara tana salati tace " to sharri zakiyimin ? shigowar Afreeda ne yasa Hajiya yin shiru ta juya bata ƙara magana ba .
Dafata Afreeda tayi kana tace " my sis momy na kira pls ki share hawayennan karki ɗaga mata hankali ,
To kona share hawaye mezan ce mata banison tasan irin target ɗin da na shiryawa wancan jakin dan wlh tunda yasani zubar da hawaye nima sai na wulaƙantashi , Afreeda ce tace " sis wai kina nufin Kamill ?" eh Diyana tace tana girgiza kai alamar tabatarwa ,
Wani marayan nunfashi Afreeda ta sauke kana tace " sis ki janye wanan maganar bazaki iya da Kamill ba mahaifinsa yafi dady komai hasali ma dady zai iya zama ɗan aikensa.....! wani mahaukacin mari Diyana ta sakarwa Afreeda tare da nuna mata hanyar waje,
why zaki ƙara ɓatamin rai kinada hankali kuwa ?" Afreeda ficewa tayi tana kuka a ranta kuwa cewa " tayi da badan tunda suka taso bata taɓa yiwa Diyana rashin kunya ba ,
Da yau sai sunyi dambe ,
ficewarta shine mafita,
Fitowa tayi daga sashin ta rufo door ɗin , mai gadi na hangota yafara miƙo gaisuwa dan jininsu ya haɗu da Afreeda kasancewarta batada wulaƙanci ,
Yanata gaisheta amma ko saurarar shi batayi ba , bai damu ba yasan hakan tana faruwa in tana cikin fushi bata cika magana ba ,
Gurin furannin gidan ta nufa tanata tsinkarsu tana jefarwa , miƙewa tayi ta dawo cikin gida ,
Samun momy da ƴar aiki tayi sunaya jera abinci a dining saita nutsuwarta tayi , kana tace " sannu da aiki momy, murmishi momy tayi kana tace " to ayi magrib azo aci abinci food is ready ,
sunkuyar da kai Afreed tayi tace " okay

Please Login or Register in order to submit comment