Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da g
ani an san sababbine, sai na fuske, na basar da maganar, munanan har yara
suka dawo break, malami ya shigo aka gaidashi anan yake tambayata ni baquw
ace nace eh, sauran yan clss sai dariya sukemin, araina nace wato rainin w
ayon hadda malamai akeyinsa, tun lokacin nayi marking din S/S master, hadd
a shi a yiwa students rainin wayo, haka dai har aka tashi makaranta zuciya
ta cike da qunci da tsanar birni da mutanen birni, bayan an tashima saida
naga tasku, sabida kowa anzo an daukeshi, wasu kuma skull bus take kaisu,
ni kuwa bansan ko inaba bare inje kuma bansan kowaba, haka na zauna jiki
n gate har 3:30 sannan yaya yazo ya daukeni, sister ya karatun dai? Ya nag
a fuskarki ba annuri ko skull din bata miki ba,?? Na turo baki wallahi yay
a ba skull din bace students dinne basuda kirki, hakafa duk inda na wuce s
unamin dariya, wai banyi iron ba shima ya kalleni ya kwashe da dariya, au

hadda kai yaya!?? to ke sister ai dole a miki dariya kin saka kaya haka kamar.....
ASHE KAINE MIJINA 15??
Na HAUWA M. JABO
Kamar wata zainb khalife ba tsari ba komai, ban san lokacin da na qyalqyal
e da dariyaba, wallahi yaya ka raina zainb khalifa, kuma ita ganin kanta t
akeyi wayayyiya tunda ta zauna qasar waje,har ma yanda takejin da yaruka k
ala kala.... ki barta shirmen banza takeyi, ni haushi take bani, kinsan ya
nzu wani abokina takeso,? Na gyalgyale da dariya, wallahi yaya duk sai na
gayawa gwagwo sharrin da kake yiwa yarta, ya harareni, kefa matsalar ki ke
nan yanzu sai kije ki fada,? Sosai kuwa sai in fada mata kana tsinar mata
ya, to ai abokiyar wasan muce, gwago ba abinda zatayi, heheheee, Kullum da
haka kake fakewa kana zagar mata ya.
Da hirar zainb khalifa "presenceszee" muka iso gida, ina abincina yunwa na
keji, yaya yayi salati, sorry sister Wallahi sam na manta ban baki kudin b
reak ba, mi kikaci,? Nayi mumushi.! Banci komai ba hasali ma da wata sis k
adee ta min tayi cewa nayi azumi nakeyi, Yaya ya zagayo ya dafa kaina, kiy
i haquri sister Allah namanta sam.! Laa yaya ba komai fa, ai nasan mantawa
kayi idan ba mantuwa ba ba yanda zaka barni da yunwa, yauwa kici abinci k
i huta anjima zamu je day to day shopping, idan kin kammala ki kirani......
ASHE KAINE MIJINA.16??
Na HAUWA M.JABO
Kammala ki kirani a waya sai muje ko, Ina qoqarin dura lomar a bakina nace
mishi to yaya, ya wuce, nici gaba da chin abincina ina baiwa innata labar
in rashin kirkin yan makarantamu, da kuma qawar da nayi sis khadee, da kum
a tsinar da yaya ya riqa yiwa Zainb khalifa a mota, inna itama dariya tamu
n, ai sai na hada yayanki aure da zainb khalifa muga qarshe tsiya, na kyal
kyale da dariya, wallahi kema kinsan inna zakisa kawai ya qara tsanartane,
dama haushinta yakeji, Allah sarki zainb nifa bana ganin abinda yaya yake
cewa tana dashi, kawai tanada dan Rawan kaine, inna tace nidai ba ruwana,
nayi murmushi, muna chin abinci muna hira har na kammala, inna bari inje i
n danyi bacci, inna ki tayar dani 4:30 pls, to Allah yakaimu,
Kamin biyar dagani har yaya mun gama shiryawa, har munshiga mota muka dau
ki hanya sai DAY TO DAY, gurin ya hadu Sosai, super market ne hade da res
taurant da kuma park a gurin, nidai kam fuskewa nayi kada a gane sabon sh
igace ni,amma Lallai gurin ya burgeni matuqa na sha magani ga shigar da n
ayi nasan qaryar yan birni Su nunan dressing, ina tsosta minti na a hanka
li, irin nima yar birnin nan dan na kula birni yan rainin wayone Sai Su

nemi Su min dariya wannan karon kuwa na shirya chin uban Su, "ni jabo ara
ina nace kaji naziah da zuwa birni Sai xancen cin uba" .......
ASHE KAINE MIJINA 17 ??
Na HAUWA M. JABO.
Munshiga day to day, munyi shopping, kayan make up, ba qara kwasowa da t
uraruka kala kala da Su chocolate ba abinda bai siyamin ba, muna fitowa c
ikin ikon Allah na hadu da Sis khadee sunzo siyayyah,itada wani hand some
guy, araina nace kar dai Saurayinta ne, dan yanayin yanda naga yana bata
kulawa ko motsi tayi a kan idon sa sai kuma Suka burgeni, naziah wannan
shine ammar shi xan aura Insha Allah, ta wani lumshe ido ta kalle shi, s
hi ko wawan Sai murmushi yake, tace wannan fa ko dai shine angon namu,tun
i yaya ya daure fuska, na kalli yaya naga yasha magani no yayane fa....!!
Ta dan sosa kai irin taji kunyar nan, ta gaida yaya na gaya ma yaya it
ace wacce ta min mutunci suka gaisa da yaya, yadan saki rai, mu dan kebe
da ita ke mutuniyar ai na dauka wannan kamu kikayi guy haka har guy, uhum
mm kina tare da ammar dinki kina kallon wani, tayi dariya aike ba'a tsaya
wa guri daya ne, har na fara joules naga saurayinki xaifi my ammar, mita
gani kuma tace kai ammar dina fa qarkene araina nace wannan yarinya da sa
urin sabo take, muka danyi tadi muka sha ice cream tare daga baya mukayi
sallama muka wuce, muka dawo gida cike da farinciki.....
Kwanaki sun shude, watanni sun haura shekaru sun jaa qaba, nida sis khad
ee mun zama daya, mun zama qawayen juna, fiye da tunanin mutum dan kuwa
komin ta yayi kama dana fatima na, mun zama abinda muka zama a skull,am
ma nafita wayo, duk wani neman magana ni nake turata tanayi amma ita ba
ta ganewa kuma bata ganeba, idan akazo in fuske a mata bulalarta, koda
tace ni na turata ba wanda yake yarda sabida kowa yana min kallon waliyi
ya dan ba mai ganin koda murmushi na bayan ita...
Duk wannan shaquwar tamu da nihal kusan shekara biyu amma tunda nake sau
daya na taba zuwa gidansu, sabida yaya baya bari, hattana qawaye baya b
ari inayi barkatai, bare zancen samari,
Nihal ta roqi yaya da kanta, akan ya barni inje gidansu, haka kuwa akayi yay
a ya barni amma bazai kainiba sai dai in shiga motar kasuwa sabida yana da a
iki sosai a office, ban damuba coz inason fita, na shirya tsab na musu tsara
ba, na nemi motarda zata kaini unguwarsu, saida na fito na fuskanci garin ak
wai hadari sosai, na sami mota na shiga sai unguwarsu nihal, kofar rini.....
.

ASHE KAINE MIJINA.18 ??
Na HAUWA M. JABO.
Unguwar su sis khadee kofar rini, ina isowa unguwar hadari ya fara tasowa
tare da iska, duk wanda yasan hadarin Sokoto yasan yanda yake da iska mai
hade da qasa a ciki, idona suka cika da qasa, har bana ganin gabana sosa
i, unguwar ba kowa, tayi shiru sai qarar itace da suke kadawa kakeji, kow
a ya shige gidansa, iska akeyi sam bana ganin gabana, sai samun kaina nayi
cikin qaton ramin kwata tsundum, Subahanallahi..... na fara swimming a kw
ata,mai uban wari ga kaina da ya bugu, haba ga ruwan sama an farayi kuma d
a qarfi, na tabbatar da idan ruwannan sukafi haka qarfi wucewa zasuyi dan
i, na tabbatarda kuma mutuwa ta tazo, dagyar Allah ya taimakeni na fito ra
min nan, ruwa kamar da bakin gwarya, na fito amma na baro jakata jikin kwa
ta, kuma gashi tace idan na iso in kirata, dan ban gane kwatancen da tamin
i ba gashi wayar na cikin jaka, jaka kuma na cikin kwata, sai qaqa....!!
ga ciwon kai buguwar da nayi, nasan ba taxin da zata daukeni haka dame dam
e da kwata in bata mishi mota, nasan ko na sami mota banida ko kwandala, h
aka naja jiki na rabe jikin gate din wani gida, ina tsaye sai ga wata mota
tazo music ne yake tashi sosai, saida suka iso kusa dani suka tsaya suka
kwashe da dariya, nadago na kallesu, bance komai ba ba bakin musu tsiya, s
ukayi horn aka bude musu suka shiga gidan, araina nace dole in bar nan gurin
Dan yaran gidannan da alama basuda kirki dagani yan iskane, na duba gabas
da yamma ba mafaka sai nan, sai kawai na haqura har a qare ruwan kunyar du
niya ta isheni, jikina duk kwata, ga ciwon kai ya tsananta har na kasa tsa
yuwa na tsuguna, ruwa yaqi zaqaitawa sai......
ASHE KAINE MIJINA 19 ??
Na HAUWA M. JABO.
Yaqi tsaqaitawa Sai na yanke shawarar bari in daure in dan shiga ruwannan
idan kwatar jikina ta wanke, my be zan samun abin hawa, na miqe kenan k
awai sai jiri ya kwasheni na fadi a gurin sumammiya, kaina ya qara bugun
gate din gidan,kikaji gwall, maigadi ya fito ya ganni a hakan ya shiga y
a kira matar sa aka taimaka masa ya shigo dani daga ciki, shida matarshi
suka taimakamin har na farfado na dawo hayyacina, amma bana gane komai k
uma ban san inda nake ba, matar ta ciremin kayan kwata ta daurayemin jiki
na ta saka min wasu tsummakaronta,ta bani dan paracetamol da panadol na k
ora, bayan kamar awa biyu na fara farfadowa, na gane inda nake, suka tamb
ayeni sunana da komai na musu bayani, muna cikin magana najiyo muryar sis
da wani namiji a waje
Uncle wallahi tun kamin afara ruwa tacemin ta fito, gida, kuma batasan nan

gidan ba, na kira wayanta yafi sau dubu baya shiga, kataimakeni dan allah
uncle, kinsan Allah, wallahi ba inda zani gwanda ma ki haqura ki kama ka
nki ke idan ma kika qara min maganar wata anan sai na babbalaki....
Tabbas muryar nihal ce kuma ni take nema, nace ma matar maigadi, gurin wacca
n yarinyar nazo, tanajin haka tayi wuf ta tashi, ta qwala mata kira.. sis k
hadee.! Sis khade!! Ko ta waigo ta wuce abinta, sista khadi kizo ga nazia an
an, ba shiri ta waigo ba shiri ina take rabi??.....
ASHE KAINE MIJINA 20
Na HAUWA M. JABO
Ina take rabi!!!???
Gatachan dakina, mi takeyi a dakin ki kuma da gudu ta qarasa, tana ganina
ta rungumeni, duk da warin kwatar bai saki gashinaba, amma haka ta rungu
meni tana kuka,kin bani wahala naziah, ta janyo hannuna muka shiga daga
cikin gidansu, dagyar nake tafiya, ga sanyin da nakeji, mun shiga gidan k
enan, bamu kai parlour ba naji murya daga baya ke ina kika samo wannan al
majirar??
Sis khade dai kam ko waigowa batayiba bare ta bashi amsa,! Yaci gaba da ma
gane, ke badake nakeba, wallahi idan nazo gurinnan sai na babballaki, haba
uncle ba girmankabane wannan abin da kakeyi, da talaka da mai kudi duk Al
lah yayisu,kuma ai wannan naziah dina ce fa.!! Kece naxoon taki almajirac
e amma kuma akwai diri, dayake duk kayan sun manne min a jiki shape dina y
a fito, najuyo na kallashe, fitsarar ta motsa na kalleshi daga sama har q
asa na zubar, na hada da tsaki, sis khadee ta kalleni, haba nazia, qanin a
bbanmunefa, na fuske ko qanin abbankune ai baisan darajar mutaneba, koma m
iye ai uncle dinane, kamin ta rufe baki tuni naji saukar mari a fuskarta k
amin in ga waye nima ya kwasheni da nawa marin guda biyu lafiyayyu, saida
na gigice,Cowon kai ya qaru na bude ido naganshi gabana tsaye, kuuuut idan
na barshi Lallai ya daki banxa, nima nasa hannu na kwasheshi da irin nas
hi marin guda biyu lafiyayyu.......
ASHE KAINE MIJINA..?21
Na HAUWA M. JABO.
Mamaki ya kama sista khade, taga yanda na mari ganin mahaifinta, wanda yak
e ji da ita, kuma a gabanta a gidansu.!! Lallai koda uncle ne bahida gaski
ya dole ta nuna ma naziah kuskurenta dan gaba...!!
Sista khade ta kalli nazia tace, ke dama yar akuyace??? Wacce batasan dar
ajar na gaba da itaba?? Wallahi da nasan ke butuluce da bazan taba qawance
da yar qauye irinkiba.!!

Mamakin duniya ya cika nazia dama haka sista khade take mara mutunci to b
a gyaleta zanyiba, wata zuciyar tace ki gyaleta gidansu kikaxo, sista kha
dee sai masifa takeyi, inda take shiga ba nan take fitaba, zuciya ta rufe
naziah uncle yayi Sokoko yana saqa Wulaqancin da xai mata, ni kuma ga m
ugun jirin da ya qara tasomin ga sanyi inaji ga yunwa, na dunqule hannu n
akaiwa sista khadee wani wawan nushi, kuma na kamata da duka baki, sai ji
ni, unle yana tsaye riqe da kumatu yana dada kallon wai almajirace zata m
ishi wannan wulaqanci yana chi gaba da saqa sharrin da zai mata kuma yasa
a ma danginta wulaqanci, sai ganin yayi ana kokowa, tuni ya hanbare ni a
wurgar dani gefe, ina miqewa na kama hanyar dana ga na biyo mun shogo na
samu na fita gidan nakama hanyar titi kamar mahaukaciya, ga warin kwata
gashi ina layi kamar yar maye, gashi banida ko kwandala na shiga taxi, in
a tsaye idona sun fara rufewa naji qarar mota gabana, sai jin nayi yace i
na zuwa na fada mishi unguwarmu tuni ya bude min nashiga........
ASHE KAINE MIJINA. 22
Na HAUWA M. JABO.
ya bude min nashiga, ina shiga motar ban qara sanin inda nakeba, suma nayi
mi nayi Allah masani, sai farkawa nayi na ganni a wani makeken gado an sa
ka min ruwa, na bude ido a hankali, na jujjuyasu bansan inane nan ba, nayi
qoqarin tashi amma nakasa tashi kaina yayi nauyi, naduba sai naga ashe ru
wa ake qaramin, iya tunanina gidan su sista khadee ne tunda daga chan nafi
to, my be faduwa nayi aka maidani chan.! Kawai sai na daure fuska dan kuwa
banason ganinsu. Banason taimakonsu, banason duk wani abu daya shafesu, i
na kwance sai ga wani saurayi gajere fari ya shigo, ina ganinsa, na fara s
urutai, miyasa kuka maidani gidanku, miya dameku da lafiyata da ciwona?? K
umaidani gaidanmu banason ganinku ko kadan, haka nayita surutai ina qoqari
n cire drop dinda aka sakamin sai naji ya riqe hannuna, na daga ido na kal
leshi baice min komai ba saima bina da ido da yayi ina balaee na, naso in
ci gaba sai kuma na fasa sabida kaina yayi nauyi Sosai ihun da nayi.. nama
ida kaina, na rufe idona, bacci mai nauyi ya qara daukeni banfarka ba sai
tsakiyar dare, abin mamaki.........
ASHE KAINE MIJINA.?23
Na HAUWA M JABO.
Abin mamaki gajerin qaton da na gani daxu shine na gani kwance a gefena ya
na sharar bacci abinshi, dayake qadon qatone Sosai, kuSan gadon ya cika da
kin, har yasa ko gurin sallah babu, na tashi ina dube dube ga dukkan alama
nan dakin mazane, amma sista khade ta cuceni maimakon ta kaini dakinta sa
i ta ijiyeni anan? Dakin uncle dinta Wallahi nida ita har abada ta xubar m
in da mutunci yanxu idan yaya da inna suka ji na kwana daki daya da qato m

i xasu kalleni,.....!!??
N qare tunane tunane da bala'eena cikin xuciya, nayi niyyar in tayar dash
i ya kaini gida amma kuma na fasa, na dago kaina na hango qofa biyu naje
a hankali na murda daya najita gam a kulle na murda ta gefenta sai ta bude
na leqa sai naga ashe toilet ne, ko nayi wanka bnida tufafin sakawa gwand
a in haqura nayi fitsari nafito, raina duk a bace, ina dubawa naga ledar D
AY TO DAY, kuma ledar ta clothes ce sai na buda ina dubawa naga tufafi da
brush da duk abin buqatar mace hadda pad ko sista khadee dan uban tace mi
shi bana sallah ohon mata!!!??
Na dauki ledar na shiga bayi na kulle nayi wanka da yake kaina adaure yake
, amma dai gashina anyi sama dashi hakan ya bani damar wanke gashina tsab,
nayi wanka kamar ban taba wankaba, ga ruwan da zafi Sosai, duk sanyi da k
asalar da suka rage naji sun tafi, nayi brush, amma yunwa ta addabeni, na
saka kayan top ne da jeans, nafito kamar baniba, amma zuciyata cike da hau
shin su sista khadee, ina fitowa naji ana kiran sallah, na tuna inna tace
kada inkai maqreeb.......
ASHE KAINE MIJINA.24
Na HAUWA M. JABO.
Kada inkai maqreeb, naje na tayarda wannan gajeren yana wani mutsuke ido,
mlm ka tashi kaje ka kira sista khade akaini gidan mu ko a budemin qofa
inje gida... na fada cike da qadara, wani kallo yakemin, kallon baisan al
qiblar maganataba, kallon mi kike nufi??, ya tashi zaune, amma kya bari g
ari ya waye sannan akaiki gida ko,?? wane gari zan bari ya waye? Yace Ba
kiji ana sallar asuba bane??Asuba!?? Dama asubace ba maqreeb ba?? Kuka ya
kubucemini ba tare da nasaniba, miyasa sista khadee tamun hakane? Miyasa
zata bari ihar in kwana gidansu kuma ta ijiyeni a dakin uncle dinta??
Lallai khadija ba qawar kirki bace, wannan duk araina nakeyi, na dago na k
alli mutumin nan,na rasa irin rashin kunyar da xan surfa mai, kawai, nace
uncle to sista khadee ta gayawa inna da yaya ina gidansune??, sabida inna
tace kada in kai maqreeb gashi har gari ya kusa wayewa?? Yayi kasake yana
kallona, kayi magana mana uncle, yaji dadin sunan data kirashi dashi, har
yana maimaitawa a fili uncle.!!! amma kuma shi wacce sista khadee ce take
fada haka, Lallai idan yagaya mata baisan sista khadee ba wannan rudaddiy
ar zata daga mishi hankali fiye da na yanxu, amma zai lallabata har gari y
a waye sai ya mata bayanin komai, da sanyin murya yace ki zauna in miki ba
yani, kinji sister na, da jajayen idona na dago na kalleshi jin ya fadi s
unan da yaya yake kirana dashi, sai na sami kaina ina maibin umurninsa, na
zauna girmn kai ba nawa bane na xauna.,........

ASHE KAINE MIJINA 25
Na HAUWA M. JABO.
Na zauna, kiyi haquri zuwa wayewar gari zan gaya miki komai, kinji? na da
ga kai alamar shkenan ba komai, na zauna jigun, chan natuna banyi sallar ko
azzahar bare magreeb gashi har an kira asuba, na miqe naje na dauro alwula
nazo nayi sallolin da suka hau kaina bayan na kammala nayi sallar asuba na
yi addu'a Allah ya fitar dani wannan qangi da sista khadee ta jefani, ya ts
areni da sharrin uncle dinta,!
Anan zaune bacci yayi awon gaba dani ban farkaba sai guraren tara na safee,
ina farkawa na duba bashi ba labarinshi, na tashi na murda qofa najita kul
le gam, ga BF nan an hadamini an ijiye mini, wasu zafafan hawaye suka ganga
ro a kumatuna Lallai sista khadee ta cika yar iska! Wato haka zata min ko?
Ba wata mafita illa in danne abincina in barwa Allah ko na mutu in tafi cik
i da nauyi.!!
A bangaren iyayen nazia kuwa tunda inna taga an kira maqreeb bata dawo ba t
a kira wayar nazia, tana ringing amma ba'adauka, tayi ta kira har ta qufula
ta daina kira ta dauki alwashin idan ta dawo zata gane kurenta, shiru naz
ia har qarfe goma bata dawoba, sai hankalin inna ya fara tashi, ta dauki wa
ya kena zata kira yaya hafeez sai gashi yazo, kasan fa har yanzu nazia bata
dawo ba!??, haba dai,? Allah kuwa! Kuma nayita kiranta bansametaba, to bak
i kira qawar tataba? Eh ban kiraba, to bari in kirata.
Saida ya kira sau uku ana hudu aka daga, batayi maganaba shi ya fara sall
ama aka amsa mishi sama sama, yanxu inna take gayam nazia har yanzu bata
dawoba! Kuma tace gidan ku xataje kamar yanda kika roqa na amince ta taf
i, tace Nazia kuma?? Ai batazo nan ba!! What???.......
ASHE KAINE MIJINA.26
Na HAUWA M. JABO.
What..!!!?? Eh batazo ba nace, ai kuwa tun safee tafito gida tace zatazo g
idanku, kamar yanda kika buqata inna ta barta tazo, hmmm to kuwa banan taz
oba, sai ku kira wayarta kuji ina yarku take.! Ban..... yaji ta katse waya
bata ma saurari abinda zai ce mataba, ya juyo yayiwa inna bayanin abinda
khadijar ta fada hankalinsu duk ya tashi, suka fito aka fara chigiya ungu
wa unguwa har kofar rini unguwar su sista khadee saida akaje nemanta, amma
bata ba labarinta, gashi dare yayi, haka suka kwana zaune, ga wayarta na
ringing amma ba'adauka guraren asuba ma wayar saita daina ringing hankali
ya qara tashi, tunda asuba yaya ya koma police station aka kai hotonta ana

cigiyarta, aka kai gidan tv gidan radio jarida duk aka baza ana nemanta,
amma har guraren 12 na rana ba ko karenda yace ya ganta,
Tana zaune ta tanqware gafafu, taji ana murda qofa, tuni ta miqe tsaye tana
jiran shigowarsa, yana kunno kai dakin da sallamarsa da murmushin sister h
ar kin..... sai saukar mari yaji a fuskarshi, kai mahaukacin inane da xaku
kawo gidan maxa ku ijiye, idan ita khadijar yar iska ce to ni ba yar ita ba
ce kuma ka gaggauta maidani gidn mu...!!! ya dago da sauri ya kalleta, ya
daga hannu zai mareta kome ya tuna kawai ya sauke hannunsa,ya dunqule hannu
rai bace ya mata wani kallo ya wurga ledar da ya shigo da ita ya ja qofa y
a kulle ya tafi abinshi, sai tafara dana sanin hukuncin da ta mishi, tafara
Allah wadai da zuciyarta,da kuma rashin kunya irin tata, miyasa ta mishi h
aka?? Lallai bata kyauta ba gashi ya tafi ya barta,jiya ta mare shi yauma t
a mare Shi, itako haka xata qare da dukan maxa..!!!!?
qeqe idonta ba kuka ba alamunsu ta miqe ta janyo ledar Abincine take away gu
da biyu komai dai guda biyu, da alama da nashi da nata dasu drink da ice cre
am duk a ciki, ta bude ta sa abincin gaba amma ta kasa chi tayi tagumi ta t
ashi tayi sallah azzahar tananan zaune har la'asar tayi sallah taga cikinta
ya fara ihu, ta janyo abincin taci ta qoshi,a haka bacci yayi awon gaba da i
ta.......
ASHE KAINE MIJINA..27
Na HAUWA M. JABO.
Gaba da ita har dare yayi bashi ba labarinsa guraren sha biyu ta dauko abinc
in dazu, dayan da ya rage ta chinye, shiru shiru har bacci ya dauketa bata f
arka ba sai guraren biyar, bashi ba labarinsa, amma kuma ya ijiye mata ledar
BF.
hakadai wasa wasa har saida Nazia tayi kwana hudu a gidannan bata qara gani
n saba, kuma kamar aljani sai tayi bacci yake kawo mata abinci abin yana da
ure mata kai, yau ta dauki alwashin bata ba barci, har kusan maqreeb ba'a k
awo mata abinci ba, data gaji da jira sai ta dan gyangyada baccin da tashin
ta duka minti hudune amma har ya kawo abinci ya fice abnshi, tunani kala ka
la takeyi, ta fara tunanin ko ta daina cin abinci ne, wata xuciyar tace ki
danne abinki ko kin mutu kije da nauyi..
Duk tayi wani iri da ita ammafa bata rameba ko kadan dan kuwa bata wasa da
abinci saidai akwai alamar tashin hankali tare da ita,
Iyaye anyi sanarwa har an gaji bata ba labarinta, anje gun malamai suna t
a addu'a anata sauke qur'anai Allah ya bayyanata amma shiru.. sister khad

ee kuwa bata ma san cewa har yanzu ba'aga nazia ba, hankalinta kwance tan
a al amarrunta, ko a skull da andauko zancenta sai tabar gurin batason za
ncen, bata San xancen batanta akeyiba, su kuma sauran sun dauka haushin r
ashin qawane yakesa bata zama cikin mutane musamman da ake cewa garin zuw
a gidansu ta bata..
Yaudai baxanyi bacci ba sai naga aljanin da ke ijiyemin abinci,baccin qary
a nayi ya dauka nayi bacci ko minti uku ba'ayiba naji ana buda qofa a hank
ali bayan ya bude sai kuma ya tsaya kamar bayan minti daya sai aka turo qo
fa ina jin ya turo qofa nayi zubur na miqe dama akan dadduma nayi baccin g
efen qofane........
ASHE KAINE MIJINA..?28?
Na HAUWA M. JABO.
Qofane, yana Shigowa na miqe dan Allah uncle kayi haquri.!!! da abinda na
maka dan Allah ka kaini gida, aranshi yace dama batayi bacci ba??.
Ya tsaya bakin qofa ya toge, ina tsoron in shigo ki mareni! Ko ki dakeni d
an nakula bakida lafiya!! Naji xafin maganar amma na Shanye yaci gaba idan
haukar taki baxata motsaba in shigo, kuuuuut dan na mareShi xaicemin mah
au kaciya, na daqo na kalle shi namai kallon raini har na hada baqar magan
ar da xan yaba mai, kawai na sunkuyar dakai kayi haquri uncle.....
Yashigo dakin ya zauna, ya kalleta ashe ganin da yake mata a camera ba hak
a bane duk ta firgice a camera kuwa yana ganinta kaman lafiya lau,
Yana xama ta fara jero mai tambaya...
Miyasa ka ijiye ni anan??
Mi kakeso in maka??
Baka tsoron Allah ne??
Ko kai ba musulmi bane??
Baka tunanin halinda iyayena zasu shiga??
Is ok.... ya katseta, da daga mata hannu kansa na kallon qefe, ta dago ta k
alleshi, ki natsu kiji mi zan gayamiki!! Na farko Idan na fara magana kada
kiyi magana sai na qare, kinajina? Eh naji!! Ya juyo ya kalleta tausayinta
da yanda ta bashi amsa ya kamashi , lokaci daya sonta da sha'awar kusantart
a ya kamashi, ya hade yawun dole, gashi ta wani mishikyau, tufafin sa ne a
jikinta top da wando, yayi sauri ya kawar da kai, ya miqe tsaye idan har ya
kuSan ceta bai mata adalciba, dan kuwa yayi niyar keta mata mutunci ladar
mari da ta mishi amma kuma tausayinta ya rinjaye shi, ya miqe anjima zan mi
ki bayani, zatayi magana, mi nace miki?? Ta tuna yace kada tayi magana, ta
kalleshi taga idonsa taga ya kada yayi jaa, sai taji tsoro, ya fita, mamaki
ya kamata yanda ya sauya lokaci daya, taci abincin tayi sallar tana nan za

une sai gashi ya shigo, abin mamaki bai kalli ko gefenta ya zaune ya juya m
ata baya.....
ASHE KAINE MIJINA??29
Na HAUWA M.JABO.
Ya juya mata baya, yafara da cewa ranar assabar na dawo daga kasuwa sai n
aga kamar kina neman taxi, sai na tsaya in rage miki hanya dan unguwar na
san ba'acika samun taxiba, abinda ya bani mamaki yanda idonki ya

Please Login or Register in order to submit comment