Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ita anjima"

tsaki yayi husna ta juyo ta kallesa


"ya sadeeq me ya faru ne?"

shiru bece mata komai ba ta maimaita har so biyu shiru dan hk ta tabasa a
furgice ya juyo

"Aisha"!!!

dasauri tamiqe jinsunan da ya ambata...

"wacece aisha?"

inda inda ya somayi

"su su sunan da dar zamusawa babynmu inkin haihu"
DOMIN KARANTA WASU NOVELS DIN ZIYARCI
www.hausaebooks.com.ng

zaro ido tayi tana kallonsa ya hadiye miyau yana gyada kai alamun eh...

"hmm ai nazata sunan watane can wlhi da nikadai nasan me zanmata wuqa
zancaka wa yar banza"

Zaro ido yayi a tsorace yana kallonta


"ynxu kina nufin inna kara aure seki kasheta"

"toh kaje ka kara auren mana ka gani..."

tafada tare da daukar laptop dinsa tayi hanyar kofa ya bita da kallo harta murda
handle din sekuma ta juyo tana fadin

"kuma zancen wata baby nina fadama banason haihuwa ba ynxu ba"

tana kaiwa nan ta fice daga dakin fuzar da iska yayi tare da jan tsaki....

Shatu kuwa batagana girki ba se to 8 fitowa tayi taajiye musu nasu ta dau nata
ta shige daki....kasa cin abincin tayi tana tunanin zancen esha...

"gsky dole na bi shawarar esha watoh ni be daukeni a matarsa ba saboda ya
rainamin hankalin sena kashe kwanaki bangansa ba..."

hk taira tunani kala-kala daga bisani ta miqe tayi sallahr isha karatu ta tsaya tayi
da addu'a se kusan 9 saura kafin ta soma shirin kwanciya..
toilet ta nufa tayi wanka ...


*sadeeq*

tsaki sadeeq yayi ya sauko daga kan gadonsa tare da rufe laptop dinsa fitowa
yayi daga dakin...

dakin husna ya nufa tana barci ganin hk yasa ya fitoh..har ya kai kofar dakinsa
ya tsaya dakin shatu ya kalla ya nufa dakin ahankali ya murda handle din dakin
cikin sa'a kofar a bude take...

yaba shiga yaji karar ruwa atoilet alamun tana wanka dan haka ya samu guri ya
zauna kan gadonta...kamshin turaren dakinta keta dukan hancinsa....

ita ko shatu tana fitowa daga toilet bata ma lura dashi ba daure taje da towel da
kadan ya wuce gwiwarta...
kallonta ya tsaya yi harta karasa gaban dressing mirror cream dinta ta bude ta
soma shafawa a hanunta...shiko gogon naka ya sake bakivse kallonta yake aransa
yana fadin

"kanar ba shatun dana dauko daga kauye ba"

fuskarta ta soma kallo da madubi aikuwa sukai idohudu da sadeeq..a razane ta
juyo ta na qoqarin yin ihu ya miqe da gudu har yana kokarin faduwa ya rufe mata
baki tare da riqe gashin kanta...kiciniyar kwace kanta ta somayiya hadeta da bago
ransa a bace..


"uban waya baki ikon fita dazu...har kina fita da guntun gyale ..koni baki
daukeni a bakin komai bane?

��
[2:19PM, 1/11/2017] Baby Afreen: ������
~*Ashe kishiyatace*~

_Na_

*Faty Afreen*

_In dedication to_
*�Abba gana�*

*14*


Shiru shatu tayi...cixon hanunsa tayi da ya toshe mata baki dasauri ya cire
hanunsa riqe matahanu yayi gam

"ka sakeni bakasan akwai zafi ba"

"baki bani amsar maganata ba"

shiru tayi kamar bazatace komai ba seta tuna da zancen esha dan hk ta runtse
idonta ta bude tare da fadin

"toh meyasa hkn ze dameka?bayan baka daukeni a matsayin matarka
ba...kwananka nawa rabonka da ka ganni?da ka daukoni daga gida hk kace wa
babana zaka ajiyeni inma matarka bauta?kuma da ka kawoni me kace min?cewa
kayi kayi alkawarin zakamin kome nakeso ko so 1 ka taba zuwa ka tmbyni me
nakeso ko akwai abinda nake bukata?"

tana kaiwanan ta fashe da kuka tana fadin

"inkasan bazaka iya adalci a tsakaninmu ba kafadamata ni ma matarka ce ba toh
ka sauwaqemin...kuma da kasan bakasona ai da baka yarda ka aureni ba tinda ba
wanda yasaka dole...tinda ka kawoni nan gidan ko yan uwanka basu san dani ba
balle****!!!!"

Bata karasa zancen ta ba ya daga mata hannu alamunya isa....shiru tayi taba
kallonsa...saketa yayi ya fice daga dakin yana fita tayi dariya


"wallahi inkayi wasa agabanta zan tona ma asiri..."

_2days later_

Zaune husna take tana chatting taba kallo dan ita aikinta kenan acikin
gidan...karar door bell taji ta kwallawa shatu kira akan tazota bude kofar....

Dija ce kawar husna...tana shigowa tabi shatu da harara...shatu ko bata bi ta
kanta ba tavwuce kitchen abinta...

dasauri dija ta karasa

"Laaa dija kece ai bansankina tafe ba..shatu kawomata ruwa"

daga can shatu ta amsa da toh

"ke dallah ki tsaya ki saurareni..wacece wannan "

"ohh shatu yar aikinace ai"

rangwashinta dija tayi akai


"husna bakida hankaline zaki ajiye budurwa irin wanan gidanki waiyar aiki"

dariya husna tayi

"ke karki damu ai inna samusu ido basa haduwa..dan ranar ma data fita tmbyt
yayi wai wacece ita"

"wallahi kishiga hankalinki inbakida hankali toh wallahi zasu miki hankali"

"dallah sharesu bakomai"

Dik zanceb da suke akan kunen shatu daje tsaye da jug din ruwa..

"Allah sarki husna dama mijinki be boye miki komai ba"
shine abinda shatu tafada a ranta kafin ta isa palon dauke da jug din ta ajiye
agabansu...

_Gidan su Esha_

"Hm kalla karki damu da husna ki riqe mijinki kawai kibishi akan yadda
yakeson gaba shi zeji jiki inbe fada mataba"


"toh kina fadan hk randa ta ganmu tare fa"?
"Toh inna ruwanki?ai a dadinki ne kema kisamu naki masaukin amatsayin
gidanki"

"tohni babbar damuwata shine yan uwansa fa basusan da zamana ba"

"mtsw kefa banzace ..shiyasa nace ki jashi ajikinki ahankali ki lallabashi yakaiki
kisansu"

murmushi shatu tayi sukai dariya suka tafe...

_Night_

Kwance husna take sadeeq na zaune tabata yayi yaga tariga tayi barci dan hk
ya sauko ahankali cikin sanda ya bude dakin ya fita dakin shatu ya nufa...
Ahankali ya kwankwasa... daga can tana kwance tayi tsaki

"ynxu mekuma takeso daddarenan hk?"

miqewa tayi ta bude
kofar dakin sadeeq ta gani a tsaye da sauri ta soma kokarin rufe qofar da sauri ya
riqe kofar

"Dan Allah shatu ki tsaya ki saurareni karki min hk mana"


"ai basona kake ba kuma baka damu dani ba dan hk ka tafi kabani wuri"

"dan Allah kiyi hkr mana kar husna ta fitoh ta ganmu hk"

"inna ruwana?ai gwara ta gane gsky dan nagaji da wanan abun"

sake qofar tayi ta juya masa baya ahankali ya shigo dakin tare dasa key a
kofar....kusa ya matso ya rungumota jikinsa..

"Shatu kiyi hkr nasan na bata miki amma insha Allah zan gyara"

Shiru tayi bata iya cewa komai ba sbd irin sa qonin da sadeeq ya soma aika
mata...kiciniyar kwace kanta tayi amma ta kasa.. nikuwa inna ganin hk na fice daga
dakin....

*washe gari*

_11:50am_

Zaune husna take a palo miqewa tayi ta nufi dakin shatu taba fadin

"yau meyasami shatu?bata taba kaiwa hk tana daki ba ko brk yau bata mana
ba"

taba shiga dakin ta ga shatu kwance se barci takeyi kokarin tadata ta tasomayi


"ke shatu meyasameki ne?"

"bkm tin jiya daddare jikina ya faramin ciwo shiyasa"

shiru husna tayi daga bisani ta fita segata dauke da cup na ruwa da maganin
ciwon jiki ta bama shatu....

shatu wuni tayi aranar kwance a daki itako husna kanar yadda ta saba komai
bata kauda ba agidan hk gidan ya wuni da datti sedai ta aika wajan umma aka
karbo mata abinci

��
������
~*Ashe kishiyatace*~

_Na_

*Faty Afreen*


.

_In dedication to_
*�Abba gana�*

*15*

*sadeeq*

shiru sadeeq yake na zuwa gida daidai nan hydar ya shigo fuskarsa dauke da
fara'a

"kaga Ango *husna* miji ga *Asma'u* shirin zuwa gida ake hk?"

"hmm gida zanje wlhi nagaji"

"ok nikuwa damau akwai abinda nakeso na tmbyk"

"kabari se gobe ynxu sauri nake"
"plx tambaya kawai zanmaka"
"ok inna jinka"


murmushi hydar yayi yana fadin

"gani nayi ka canja kwana biyu,inna tinanin akwai abinda kake boyemin"

dagowa yayi ya kallesa aransa yana fadin
"kodai na fadamasa ne?kaiii karna fada masa yasa dole se anfadawa su mama"

sunansa da hydar ya kira ne ya dawo dashi daga tinanin dayakeyi...
girgizakai ya shigayi

"bkm abokina baabinda nake boyema"
"shknan sadeeq intayi wari zamuji dan daga reaction dinkav ynxu ma mutun ze
gane"

shiru sadeeq yayi daga bisani hydar ya fice daga office din..ajiyar zuciya sadeeq
yayi ya tattara takardunsa guri daya ya fice....

Yana isa gida ya tararda husna tana kallo...

dasalamarsa ya shiga ta tarbesa cile da fara'a daga bisani ya zauna ta kawo masa
abincin da aka kawomata.....

Yajima azaune bega shatu ba yanata leqe husna kam hankalinta nakan tv

"husna wai inna mutuniyar taki ne?"


dasauri husna ta gyara zamanta tana fadin
"yauwa ya sadeeq ka shiga ka dubata kozaka bata wasu magungunan batajin dadi
dik yau baymta fitoh ba...."

shirucyayi na yan mintina ya miqe ya nufi dakin itako ta gyara kwanciyarta
tacigaba da chatting
....

Yana shiga yasawa kofar dakin key...ita ko shatu a zatonta husna ce... kamar
daga samata taji mutun kusa da ita ya rungumota....da sauri ta tashi ganin sadeeq
yasa ta bata rai....

"Meya kawoka nan?"
"kiyi hkr nazo dubaki ne..ya jikin"

"kaini lafiyata lau fa ka kyaleni"

"toh husna tace baki fita ba wai baki da lfy...kuma baki gyara ko inna ba ka palo
dik kaca kaca."

Murmushin takaici shatu tayi
"toh na gaji ne....ni ba yar aikin ku bace...gwarama ka kyaleni se nayi niya zan
gyara"

Sake baki yayi yana kallonta aransa yana fadin


"lallai shatu ta goge...yaushe ta iya magana hk"

gyara kwanciyarta tayi shiko ya kwanta gefenta yana shafa mata...kan kace me
barci yayi awun gaba da su....

Cikin barci yaji anna motsi kusa dashi...ahankali ya soma bude idonsa shatu ya
gani kusa dashi da sauri ya miqe kamarwani mahaukaci...yana fita palo ya ga
husna kwance itama se sharbar barcinta takeyi...

ajiyarzuciya y sauke kafin ya wuce dakinsa..

*washe gari*
_saturday_

Cikin shirinta na fita husna ta fitoh daga dakinta...shatu na gyaran palo ta
wuceta ta shige dalin sadeeq

"ya sadeeq na shirya zan tafi"

"toh karfe nawa zaki dawo senaxo na daukeki"


"bayan anyi sallar magrib"

murmushi yayiya bata kudi ta fice abinta tana zuwa palo ta iske shatu

"shatu xanje anguwa seda magrib zandawo ki tmby mijinakome yakeso seki
dafa masa"

"toh" kawaishatu tace ta cigaba da aikinta husna kuwa ta fice...

Shatu shiga kitchen tayi ta somawanke wanke tin najiya da batayi ba takeyi
tanayi tana tsaki....kanar daga sama taji mutun ya rungumota ta baya ihu tasa sbd ta
tsorata...

"ke nine fa"

ganinshine yasa ta kaimasa duka

"kaji yadda katsora tani kuwa?"

dariya yayi sukaita hira harta gama wankewanken yana mata dauraya....

Atakaice dai zancemuku aranar sadeeq da shatu sunsha syyy kamar dama
masoyan ne ko nace kamar dama sun saba...
har bayan isha sadeeq be dauko husna ba...ita ko can husna dataji shiru ta soma
kiran sadeeq yana ganin kiranta ya tina da zeje ya daukota nan ya shiga bata hkr
akan baya gida ne but ze biyo ya dauketa.


Haka rayuwa ta cigaban musu yau watan shatu 2 da zuwa gidan ..tin daga
lkcin dik bayan kwana biyu a dakin shatu yake kwana seda asbah inya fita
massalaci inya dawo seya wuce dakinsa...

*Wata ranar juma'ah*

��

������
~*Ashe kishiyatace*~

_Na_

*Faty Afreen*

_In dedication to_
*�Abba gana�*


*16*

*wata ranar juma'ah*

Husna ce ta fitoh daga daki da ear-pis akunenta tana jin krtu...

Zama tayi tasa wani indian film *Twist of faith* tacire ear-pies din tare dasa
wayarta a caji..zama tayi tasoma kallo...

Karar door bell sukaji nan danan ta miqe taje tabude kofa dija ce ihu tayi cike
da murna ta rungume dija...zama sukayi sukafara hirar yaushe gamo...

karar door bell suka kumaji..dija ce ta miqe taje ta bude...ummi ce gaishe da
dija tayi ta anasa ciki ciki...hk ma husna...

guri ta samu ta zauna su husna kuwa hira suke tayi abinsu...

ummi kuwa tsaki tayi aranta tana fadin

"mtsw wlhi badan mama ba banga me ze kawoni gidanan ba"


tana kaiwa nana sukaji anfitoh daga kitchen da gudu dikka suka maida hankali
agurin....shatu ce ta fitoh tana qaqarin amai dakinta tayi da gudu suka bita da
kallo....
husna kuwa ko ajikinta sema tabe baki datayi ta juya gun dija....

"yauwa kawata kina bani labari"
"dallah dakata...innace wanan yarinyarce kikacemin sadeeq ya kawota a matsayin
yar aiki?"

"eh itace me ya faru?"
"baki gani ba? cikine da ita fa?"

miqewa ummi tayi ta nufi dakin shatu dija ta rakata da harara

"hhhh lallai dija toh in ciki ne ma da ita daga can kauyen nasu ta kwasoshi
innaga...kinga mubar maganarnan"

hknan dija ta hkr da zancen badan taso ba...

*shatu*

Shatu taba shiga daki amai ta dinga kwarawa kamar zata amayar da komai na
cikinta....

Ummi na shiga ta tai maka ta batavruwavta kuskura bakinta ta dauraye
gurin...zama sukayi saman gadon ummi na mata sannu...sanda taga tadavsamu
sauki kafin ummi ta soma fadin


"sunana ummi kuma ni kanwar me gidan ce..ya akai bansanki ba?"

dasauri shatu ta dago ta kalleta
"ni me aiki ce"

"ok watanki nawa agidanan?"

"zankai wata biyu"

"Allah sarki...dama kin taba aurene yar uwa?"
"a'ah"
shatu ta fada atakaice

murmushi ummi tayi tare da fadin

"oh!!! toh wannan cikin nawaye shi kuma?"

atsorace shatu ta kalli ummi tare da rufe mata baki...

"kinga zo mu fita anan"

miqewa sukayi cikin sa'a da suka fitoh ba kowa a palon..kamar muna fukai
sukaita sanda har suka fice....gidan su esha suka shige mumy ta sanar dasu cewar
esha na daki...


"ahhh shatu sanunku da zuwa ...baquwa kikayi ne?

"eh kanwar sadeeq ce"

"ohhh bari na kawo miki abunsha"

miqewa tayi tafita se gata dauke da juice ahanunta...

nanfa ta zauna ...ummi ce ta fara fadin

"kin kawoni nan baki bani ansata ba"

shiru shatu tayi batace komai ba ...esha ce ta soma fadin

"meke faruwane tsakaninku?"

"kinga alamun ciki na gani a jikinta shinefa nake tmbyrt nawaye taqi fada"
acewar ummi

dasauri esha ta kalli shatu...

"CIKI!!! shatu ciki ne dake?"

dariya esha ta farayi ..kutashi muje asibiti...


miqewa tayi ta zari gyalenta suka fuce...
ummi kuwa asibitinsu sadeeq ta musu kwatance suje batare data fadamusu ba...

suna zuwa aka gwadata daga qarshe dai result ya nuna shatu na dauke da ciki...

kuka shatu ta faryi akan se an zubar da cikin

"Wayyoh esha ku ceceni ku xubar da wannan cikin"

tana kaiwanan jiriya dibeta ta zube aqasa...da gusu ummita juya ta nufo office
din sadeeq ko sallama babu ta banka qofar..ganinta yasa yamiqe

"ummi meya faru meya kawoki nan?"

"yaya kazo me me aikin gidanka ce ta suma tana da wai se an xubar"

cikintashin hankali yasoma fadin

"tana inna"
."tana waje"

cikin sauri suka fita suna zuwa suka iske esha tana kuka rungumecda shatu...

yana zuwa gun yafara zagin nurses din daje wucewa ba shiri suka dauketa aka
bata daki...


y

��

������
~*Ashe kishiyatace*~

_Na_

*Faty Afreen*

_In dedication to_
*�Abba gana�*

*17*


Ba shiri suka dauketa aka bata daki..iya gigicewa sadeeq ya gamayi abokinsa
hydar da ummi sake baki sukayi suna kallonsa abun mamaki yadda ya gigice akan
shatu...
*bayan wasu awowi*

DOMIN KARANTA WASU NOVELS DIN ZIYARCI
www.hausaebooks.com.ng

Zaune ummi take dija ta zaune saman dadduna alamun ta idar da sallah...

kallon shatu ummi tayi tare da fadin

"wai shatu kinqi fadamin komai akan abinda ke faruwa"

esha ce ta karbeta da fadin

"karki damu ummi zanfada miki komai ammafa ba a so mgnr ta fitoh..dik da
wannan cikin ze iya tona musu asiri"

shiru sukayi na yan mintina kafin esha ta zayyane ma ummi komai da komai...

Mamaki ya cika ummi ba abinda ya fado mata arai irin in mama tasan zancen...
murmushi ummi tayi tana fadin

"Allah sarki antyna..Allah ya raya mana cikinan...shiyasa naga yayana ya rikice
ashe babyn nasa ne"?


takarashe maganartacike da tsokana....

Sadeeq kuwa yana can office shima yabawa hydar labarin dik abinda yafaru
tsakaninsa da shatu..

"hmm ynxu kai sadeeq dik abinan kaqi fadamin....toh ynxu ya zakayi da ita?ko
zubar da cikin zakayi?"

"Kaii haba...na kashe dana.abinda husna ta kasamin...ynxu Allah ne kadai
yasan irin farincikin danake ciki...wallahi bavwanda ze kashen dana"

"toh seka dauketa kuje kufadawa mama..kokuma ka fadama husna"

"kaga kama bar xancenan muje na dubata naje gida dan kar husna tayizargin
wani abun"

miqewa yayiya fice bejira abinda hydar zece ba...

dakin suka shiga da sallama..nan likita ya shigotare da fadin

"dr.sadeeq ai kasan komai game da aikin basena fadama abubuwan da take
bukata ba..anma muje na baka list na magungunan da ykmt a bata...zaku iya tafiya"


fita dr. yayi sadeeq ya juyo garesu

"kushirya ku tafi gida zan taho da magungunan...ko hydar ze saukeku"

"a'ah nazo da motata zamu tafi kawai"
acewar esha

amsawa yayi da toh kafin a bi dr. hydar ya raka masa baya suka fice sukuma
kasan cewar dama basu wani zo dakomai ba su tattara suka tafi...

Suna isa qofar gida ummi da shatu suka sauka esha ta musu sallama ta qarasa
gida..

Ahankali suka shiga gidan suna shiga kwance suka iske husna tana
barci...shigewa dakin shatu sukayi

"zan fadama yaya sadeeq ya siyamiki waya in kinasonwani abun seki kirani na
kawo miki"

murmushi shatu tayi tana fadin

"nagode sosai ummi Allahya saka da alheri"

nan dai suka danyi hira kafin ummi ta fitoh tatafi gida...tana fita shatu ta fitoh
kitchen ta nufa ta soma dora abinci...


_9:33pm_

Ahankali sadeeq ya fito daga dakinsa cikin sanda ya leqa dakin husna yaga tayi
barci..fitowa yayi ya nufi dakin shatu...

"shatu!!ki bude nine"

ahankali ta miqe ta bude masa qofar ya shigo zama sukayi abakin gado shiru ya
ziyarcesu kafin ta soma fadin

"meyasa kaqi bari a zubar da cikintinda ba damuwa kayi dani bama balle abinda
zan haifa".
"Dan Allah kiyihkr karki min hk ...nadade inna jiran ranar da nima zan samu
nawa dan..nima nasamu me kirana da abba..

hawayene ya soma zuba daga fuskarta...hanunsa yakai cikita yana shafawa....

"gashi ke kin rufamin asiri . gashi zaki samamin farinciki"

kwanciya yayi saman kafarta...ita kanta jikinta yayi sanyi kansa ta soma shafawa

"shatu inna sanki nagode da irin taimakon da kikamin kin rufamin asiri nagode"

"kabari ya iisa hk...ni ynxu damuwata shine ya za ayi na haihu abinda na haifa
shima acigaba da boyesa?"


"insha Allah komai ze dawo daidai kafin lokacin"?

*1week later*u

Cikin sauri ummi ta ke juye alalen data sauke cikin kula....

"ummi inna zaki kai wannan alalen"
acewar mama

murmushi ummi tayi tare da fadin

"gidan yaya zankai...anty ce ta kirani wani shi take marmari"

washare baki mama tayi aranta tana fadin
"masha Allahhusna nada ciki shine basu fadamin ba...barinazo na fara siyan
kayan jinjiraye"

dakin ta shige fuskarta falda fara.ummi kuwa tana gamawa tashirya ta dau
hanyar zuwa gidan sadeeq


��

[3:16PM, 1/15/2017] Baby Afreen: ������
~*Ashe kishiyatace*~

_Na_

*Faty Afreen*

_In dedication to_
*�Abba gana�*

_godiya me tarin yawa gareku masoyana..kuma masoyan abba gana...inna
samun saqoninku ako yaushe...nagode sosai...inna miqa saqpn gaisuwata zuwa ga_
*Mr.sa'eed isah*(daga group din asykhaleel)


*sa'eed dan hajiya*(daga group din faty afreen novels2 )
*Afrah* (daga group din hausa novel lovers)

Nagode sosai da sosai Allah ya bar zumunci�

*18*

Ummi na isa ta tarar da shatu abakin gate se leqe takeyi...

"yauwa yar halak kamar kinsaninna tsoron shiga gidanan"
acewar ummi

dariya shatu tayi
"lallai ma se infadawa yanki kinkina tsoran gidansa"
"cabdi rufamin asiri"
Yadda zaku samu sama da 10000 KYAUTA daga kamfanin Google

Danna blue din rubutun kasannan ka gani

Google bonuses
dariya sukayi suka dantaba hira kafin daga bisani sukai sallama shatu ta koma
ciki...

_2mnths later_

"ya sadeeq niko innaso nama wata magana"


acewar husna

sadeeq da hankalinsa kekan system dinsa ya amsa mata da

"innajinki meya faru?"

"dama innaso na tmbyk cewar kasan yarinyarnan ciki ne da ita ko?"

wayincewa yayi kanar besan watake nufi ba
"wacece wannan?"

"shatu mana"

"wacece shatu?"

murmushi husna tayi tarecdajin sanyi a zuciyarta tinda mijinta yama manta da
shatu balle tayi zargin wani abun

"yar aikindaka kawo mana"

"ohhh kinsan dama dana daukota daga kauye aurenta ya mutu ne"

"ohh Allah sarki..toh seka maidata gida.."

"meyasa?"


"kafasan banason yara akan me xata haifamin dan da bansan ubansa ba
acikingida?"

"toh meye aciki husna ai taimako zakiyi...kanata yayi ma kifara siyan kayan
jinjiraye...sunan babana na za asamishi"

"cabdi wannanku tadama amma wallahi baza ahaifamin dan shege ba agidana
ba..kuma***"

bata karasa zancentaba ya dauketa da mari...cikin radadi ta riqe kuncinta dan ta
manta rabon da a mareta...

"ynxu sadeeq akanwancean abun zaka mateni?"

"inkika kara maimaita abinda lila fada senamiki fiye da hk....ke ba qin haifamin
yaran kikayi ba? kuma ita inta haihu anan zansamu yaron dazena deben kewa tinda
kekinka kasa"

kuka ta fashe dadhi ta fice daga dakin da gudu...shiluwa fuzar da iska yayi ya
kishingida akan gado idonsa na kallon sama...

*washe gari*
_morning_


Zaune husna take a palo ta dora kafarta daya saman daya ga sawun marin da
sadeeq ya mata afuskarta dakaganta kasan ranta bace yake...

Shatu ce ta fitoh daga daki gurin husna ta nufo...

"anty inna kwana"

"daban kwana agidanan ba zaki gani?"

shiru shatu tayi tana tinanin toh metama husna yau...

mikewa tayi jiki a sanyaye ta nufi hanyar kitchen...tsaki husna tayi aranta tana
fadin

"dole ma nadau mataki...kuma haihuwa zanyita kodan wanan yar banzar basu isa
su gajemin gida ba"

tana kaiwanan ta miqe ta nufi dakin ...dija ta kira bugu biyu ta dauka...

"Hello hussy yane"

"ke kizo gidana i need yuhr help"

toh dija ta fada ta kashe wayar...zarya ta farayi a dakin tana tinanin ta inda zata
bullo....


ita ko shatu tana shiga kitchen ta gyara ko inna ta yi wankewanke kafin ta
fitoh ta gyara palo

_1 hr later_

karar door bell sukaji dasauri shatu fitoh domin bude kofa harara husna ta
watsa mata...jiki sanyaye shatu ta juya ta koma daki...husna na budewa taga
dija...murmushi tayi tare da fadin

"shigo yar uwa"

zama sukayi akan kujera dija ta kalli husna tana fadin

"meyafarune?

"hmm akwai damuwa... shatu ce matsalata"

"metayi?"

Nan husna ta kwashe komai abinda ya faru ta fadama dija...

"cabdijan wallahi barin gidan zatayi "


"kinga ni ynxu damuwata shine nasamu ciki...kuma kinsan ahekaran jiya nasha
tablets dinan"

� "cabdijan tashi zakiyi muje musamu doctor kawai"

dasauri shusna ta miqe ta nufi hanyar dakinta tana fadin

"jirani bari na dauko gyalena"

Tana shiga ta dauko gyalensuka fice...

*Asibiti*

"gsky zan fadamuku tinda dai kika sha wa anan tablet din bazan iya cemiki
komai ba"

acewar likitan

dija ce ta amsa da..
"haba doctor...kataimaka mana dan Allah"

"gsky zan fadamuku i cant do any tin abt dis dole se kunyi hkr"


hawaye husna ta faryi batace komai ba ta miqe tsaye....

��
[3:17PM, 1/15/2017] Baby Afreen: ������
~*Ashe kishiyatace*~

_Na_

*Faty Afreen*

*A short story*

_In dedication to!_
*�Abba gana�*


*19*

Tafiya ta somayi ta fita daga office din dasauri dija ta bita tana kiranta.bata tsaya
ko inna ba se wajan asibitin

"husna kitsayakimin mgn mana innata mgn kin shareni.."

cak husna ta tsaya batare da tace komwi ba ahankali tajuyo tana kallondija cikin
fuskar tausayi tasoma magana....

"Dija kizo muje wani asibitin dan Allah..."

rikota dija tayi tare dafadin
"bkm husna karki sama kanki damuwa..kuma wannan yarinyar yar aikinki
cezaki iya korarta dik sadda kikaso batare da ya sani ba"

gyadaksi husna tayi tare da share guntun hawayen dake gangarowa..

Atakaicedai husna taje asibiti kusan hudu dik da na farkon biyar zance daya suke
fadamata..wani ma cewa yayi baya tinanin zata qara haihu sbd tasha kwayoyin sun
mata yawa sun affect mahaifarta...


kuka sosai husna takeyi da qyar dija ta rarrasheta suka koma gida....

suna shiga gidan husna ta fadakan kujera ta qara fashewa da wani kukan da
gudu shatu ta fitoh arkice tana tmbyr husna me yasameta...

wani irin ashar dija tama shatu ba shiri shatu ta juya hartana qoqarin faduwa...ita
ko dijaa fili cewa tayi

"shegiya dama kin fadi akasadan ya mutu"

ahankali shatu ta juyo ta kalli dija takalli husna kafin ta shige daki abunta..

"dija ynxuya zanyi?nariga na cuci rayuwata na cuci kaina"

ta qarashe maganarta tare da fashewa da kuka...

"kibar wannan kukan insha Allah komai ze daidaita"

"Taya zakice hk bayan munje asibitoci kusanbiyar amma dikka result daya...dik
ke kika jamin wallahi"

"yazakice nina jamiki? bafa kiga ni nasha maganin ba..kekika ce na baki toh na
baki kuma zakice nina jamiki"

*(Kunga yadda husna take..kawarta ta bata magani gashi mahaifarta ta samu
matsala..gashi ita ta mata wayau bata sha ba....hmm Allah ya shiryamu)*


"toh meyasa zakiban maganin bayan kinsan illarsa.?"
"kefa kikace bakyason haihuwa ko kukan yaro bakyason ji..shiyasa na baki
wanda ze miki aiki sosai"

ehu husna tayi tasa hannu akai tana fadin...
"wayyoh Allah na shiga uku"

shikuwa sadeeq a ynxu kome shatu ta bukata yana kawo mata batare da husna ta
sani ba.in yasan husna ta iyacin wani abun se ya siyo guda biyu...husna daya shatu
daya...amma dik abinda ake husna bata sani...

Kayan wasan jinjiraye kuwa sadeeq harya fara siya yana kawo ma shatu...esha
ma hk da ummi dasunga abunyara daya birgesu se su siya su kawo ma shatu..

shatu da husna kuwa mgnr kirki bata hadasu...husna ynxu batada damuwar data
wuce tasamu ciki itama... kusan dik bayan yan kwanaki husna setaje asibiti amma
disame result suke bata...

danhk kullun taje ta dawo setasha kukanta me isarta....
watarana da dadare suna zaune da sadeeq yasoma fadin

"husna meke faruwane?meyasameki naga kwana biyi kin canja"

shiru tayi tana tinanin abindazata ce ...canwata dabara ta fado mata..marairaice
fuska tayi tasoma fadin


"ni aynxu ba abinda ke damuna se yarinyarnan..."

juyawa tayita kama hanun sadeeq

"Ya sadeeq dan Allah ka naudata kauyensu nina hkra da me aikin zanyi komai da
kaina"

dariyar mugunta sadeeq yayi tare da fadin
"haba my husna kefa kikace ko agidanku bakya aiki se ynxu xakice kinhkra da
me aiki?"

"ehwlhi yaya na hkra"

"tohbaki isa ba tinfarko bakice hk ba...dan hk zamanta damaramagidanan"

kuka husna ta fara karshe ya fitoh ya baro dakin ya dawo palo dan bayasonjin
kukanta...

Abu kamar wuya yau cikin shatu watansa biyar (5) amma husna har ynxu
shiru..akulkun tsanar shatu ce ke qaruwa a zuciyarta...

wata ranar saturday husna na zaune a dakinta gaban dressing mirror tana
kwalliya ji tayi anturo qofa...


sadeeq ne fuskarsa dauke da murmushi ya qarasa lusa da ita itama murmushin
tayi

"zan danfita naje office ndw"

"ok shknan adawo lfy.."

Amsawa yayi da amin ta miqe har jikin motarsa ta rakasa..

baafi minti biyar da fitar sadeeq ba dija ta shigo...hira suka zauna sunayi
....shatu kuwa fitowa tayi daga dakinta ta nufi kitchen ...

"husna ynxu barin yarinyarnan xakiyi da cikin tinda kin kasa korarta?jifa yanda
cikin ya girma"

"dija nikaina narasa yadda zanyi wallahi"

wajan kunenta dija taje ta rada mata wata mgnr da nikaina ban ji ba...da husna
tayi suka tafa...

"shatuu!! zonan"

amsawa shatu tayi ta fitoh...tana zuwa dija ta miqecta dauketa da mari...husna ta
soma naushinta aciki nansuka fara dukanta ta ko inna suna fadin...

yau sesun kashe dandake cikin ...


suna cikin hk sadeeqcya turo qofa...

"HUSNA!!!" shine abinda sadeeq ya fada a gigice husna ta juya tana kallonsa
suka faraja da baya...

gurin shatu ya qaraso a rikice gani yayi harta fara bleeding...juyawa yayi ya
kama dukan husna ta ko inna daidai nan ummi ta shigo...

"wayyoh yaya karta mutu"

se alkcin ya juyo ya sunkuceta sukafita..dija da husna kuwa ya musu dukan
tsiya....har hancin husnana jini...

"husna kiga abinda mijinki ya mana wallahi ban yafe ba"

"dallah rufamin baki bake kika ja mana ba"

"mtsw husna ga shawa muje gidansu sadeeq ahk mufada mata abinda ke faruwa"

dasauri husna ta miqe tana dariyar mugunta...gyalensu suka zara sukafice daga
gida...


��
[3:17PM, 1/15/2017] Baby Afreen: ������
~*Ashe kishiyatace*~

_Na_

*Faty Afreen*

*A short story*

_In dedication to_
*�Abba gana�*

*20*

Shikuwa sadeeq betsaya ko inna da ita ba se asibiti dik yabi ya rikice daga shi
har ummi...


Husna kam adaidaita suka samu suka biyasa har qofar gida yakaisu....

suna shiga cikin zauren gidan husnavta fashe da kuka dija na riqe da ita ahk suka
qarasa cilon gidan...mama na tankadan garin tuwa tajiyo

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment