Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wargi. Duk girman shekarun ta wata rana sai an shigaa rabiyar fadañ su da tsofaffi kawayen ta .

"Marka magana nake miki ...." Najan Isubu ta sake cewa da marka. Cikin muryar ban lallashi da neman afuwa.

"Yo ai shiru nayi ki tsara yadda komai zai kasance tunda jikar ki ce. Ai sai yadda kika ce."

Najan Isubu ta dan kakaro yake kawai. Ta juya ta kalli umma hadiza da ke tsugunne daga gefen wata kwalla .

"Haba ni na isa? Ni din gaba da shirme, Ai abunda kika yanke dole abi shi Marka... Kawai dai so nake ki duba zancen Na'Ateeku a mizanin tunani. Sam Na'Ateeku ba tsaran auren Waheedah ba ne marka."

"Sannu. Nace sannu zabiya mai dalilin aure. Ita din wacece da har zaki ce Na'Ateeku ba tsaran aurenta bane iyye? Fin karfin sa tayi? Ko kuwa usuli ta fi sa. Allah na tuba astagfirullah Na'Ateeku kaf unguwar shurah akwai wanda ya ko kamo dan yatsan sa ne a usili? Mutimi dan mutunci da dangi masu dattako. Kar ki manta kakan sa da ya haifi gyatumin sa shine mai unguwar shurah. Sannan mahaifiyar uwa ta sa kakanta kani ne ga dagacin fandau., Sannan kanin sa da suka fito ciki daya chiyaman ne ke kanki kinsani. Sharbacecen kwaltar data miqe sambal ai shi yayi mana. Ya kuma kawo tuqa tuqa (borehole) Da haqa rijiyoyi. Bacin nan shi kansa mai rufin asiri ne. Shago shaqe da kaya na kayan masarufi. Sannan ke kanki kinsan yanada shagon chajin wayoyi da sayar da kati. Ki gayamun tsakanin shi da ita wanene ya kere wani? Na'Ateeku duk yar daya tsayar a unguwar nan yace yana so wallahi auren sa zatayi. Iyayenta Kuma su zuba ruwa a kasa su sha dan farin ciki , Aikin kawai."

Marka ta karasa fada hade da hambale taliyar da ke cikin hannun ta . Najan Isubu ta sauke katuwar ajiyar zuciya. Ta juyar da kanta ta hango Waheedah dake tsaye a bakin kofa hawaye daya na bin daya . Tausayinta ya sake dabaibaye zuciar Naja. Cikin sanyin jiki da muryar roko ta sake cewa da marka,

"Duk abunda kika fada hakan yake Marka, Ban musa ki ba. Na kuma san kauna ce tasa kikeson ki hada auren nasu. Sai dai abunda nakeson cewa shine, Na'Ateeku yayiwa Waheedah girma Marka. Wallahi zaa cuceta idan har aka aura mata shi. Dansa na biyu Hashimu fa satin baya ya kara aure. Mata ta 3. "

"Sai akayi ya ya? Ai dan arziki shi yasan abun arziki. Yadda matan sukayi yawa ai dama kamata yayi maza su ringa aure su , Su cike gurbi. "

Najan Isubu ta sake gyada kai kafin ta zauna daga gefen Marka.

"Marka.... Rayuwar auren daa da yanzu ba daya bane. Tamkar yadda kukayi rayuwar auren ku da tamu wallahi ba daya bane. Hakama yanzu wannan zamanin ba a irin auren nan Marka. Zamani yazo da sauyi."

"Ni fa ban gane abunda kike nufi ba Najaatu. Gwara ma ki dena 'babaatu. Ahto!" Ta karasa hade da nanawa cinyarta duka.

"Abun nufi yanzu zamani ya kara wayar da mu. Ciwukan yanzu a baya baa yi su ba. "

"Uhmm Hu'uhm..." Marka ta numfasa tana gatsine gatsine.

"Allah Marka. Na'Ateeku bakiga yana da yara hudu ba marasa lapia shima.?"

"Bangane ba.. Yo sai me? Ba Allah ne ya doran su ba. Ina ruwan auren su da wahidin ya hadu da gamayyar rashin lapiar yaran sa?."

"Ina nufin Na'Ateeku a dauke zancen ya haifeta da sauran su. Abunda nakeson ce miki shine. Shi ma Na'Ateekun yana dauke da kwayoyin cutar sikila. Kamar dai yadda su Kamalu da Najeeb ke fama da ita."

Marka taja dogon tsaki data saurari karshen zancen Najaatu. Cikin takaici tace,

"Banji ba, Ban kuma gani ba. Karki manta da sherri dan aike ne, Dik inda yaje zai dawowa mai shi... Sannan ni me sunan Malam (Na lado) Bayada wata cuta.. Domin idan da yana da ita da yaran wajen sa'adatu ba sa yi lapia ba. Ita kuwa uhm uhm Hadiza, Da cutar ta tayi guzuri. Aka liqa masa ita ya aure. Ashe lullube maganar cutar jikinta sukayi. ."

"Kayya Marka ki dena cewa haka dan Allah .. Banda ishasshen ilimin da zan buda miki komai yadda yake. Amman Allah ya kai mu sati na sama. Wata kungiyar wayar da kan jamaa kan hanyar da zaa kula kar a fada halin qaqanikayi na ciwon sikila zasuyi taro. Da yardar Allah kuma dukkanin mu zamuje. Saboda har gwajin jini za'a yi ko kanada cutar duk zaa sanar maka. Hakama idan baka da ita."

"Kingama?"

"Kiyi hakuri Marka."

"Baki gama ba kenan. To kici gaba idan kin gama se ki tashi ki koma inda kika fito."

"Kiyi hakuri Marka. Ni kawai so nake ki janye zancen ki..."

"Aure babu fashi..."

"Nalado ka sa baki dan Allah. " Najaatu ta dubi nalado dake gefe yana katsar ruwan dake kasan tukunya na taliya.

"Me zance Naja..?" Ya amsa ta hadi da lashe bayan hannun sa.

"Yanzu ba zaka tausashi zuciyar marka ba ta janye zancen nan? Haba dan Allah."

Malam Nalado yayi shiru bai ce komai ba.

"Aure babu fashi. Yace dama inde zuciyar sa ta aminta da ita. To fa ko kayan daki yace shi zai yi. Ita kadai za a wanke akai. Saboda Allah meya fi wannan karamci? Na'Ateeku kyakkyawa da shi , Sambalele jazur da shi . Kina ganin matansa kowacce da kayanta maya maya. Sunyi 'bundun da su.. wallahi ance ba yunwa agidan sa. Duk sallah sai ya dinkawa matan sa turame maya maya. "

Waheedah dake labe tana sauraron komai. Kasa jurewa tayi. Dan kukan da take rikewa ne ya kufce mata ya shigaa sharara a idanunta. Cikin rawar jiki da baki ta fita tsakar gidan. Ta sukwane agaban Marka tana faman rokonta.

"Dan Allah Marka kiyi hakuri. Ki barni na cigaba da karatu na. So nake na zama ma’aikaciyar lapia Marka. So nake na bawa harkar lapia gudunmawa Marka. Dan Allah kar ki mun aure ki bari na cika burina. " Ta karasa hade da riko kafafun Marka. Hawaye sai dalala yake daga idanunta.

"Matsa kafin na hamb'are ki. Me sunan Malam kana jin maganganun da tsageriyar yarinyar nan take faada....?”


"Laàa. Ke yanzu Waheedah Markan kike gayawa haka?Uhm tab. Lalle. Kokari." Cewar Inna Sa'adatu matar Nalado ta biyu, Mahaifiyar su Zainab da su ke uba d’aya da su waheedah…..

#FARHATAL QALB
#FARIN CIKIN ZUCIYA
#ZAFAFABIYAR2022

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰

_*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
                     💞
_NA_


_NANA HAFSATU_
_(MX)_


_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_


_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_


_LAST FREE PAGE: 5_
_(SHAFIN KARSHE NA KYAUTA!)_


××××××


   "Haba Sa'adatu, Wannan ba girman ki ba ne wallahi." Najan Isubu ,  Ta fadawa Inna Sa'adatu haka.

"Yo ai gaskia ta fada.. Me sunan Malam kana jinta ko kayi kunnen uwar watsi?"

"Kiyi hakuri Marka... Ke waheeda baa ta hakuri." Malam NaLado ya tsawatar wa Waheedah.

Ita dai Umma Hadiza bata ce komai ba. Tayi zugum a gefe kanta a kasa.

      "Ummaaa kafaata, Umma kafata. Kafata ummah ..Wayyo, wayyo " Najibu ya shigaa maimaitawa yana mai dartse hakoran sa 

Marka taja tsaki, Umma hadiza ta miqe da sauri ta koma cikin daki wajen su Najib.

"Haba wannan wahala har ina? Ga wannan ga wannan. Gaskia da sake " Marka ta fada tana mai hararo dakin su Najibu

"Kai Marka ki dena cewa haka. "

"Kinga Naja ki fita idanu na. Ni dama tun da na kyalla ido na hango shigowar ki, Nasan tabbas wani katsalandan dinne ya kawo ki.."

"Kiyi hakuri Marka. Da yardar Allah komai ya kusa wucewa. Lokaci ne, Idan Allah ya nuna mana wucewar da sai kiga tamkar ba'ayi wannan tashin tashinar ba." Naja ta karasa fada idanuwanta akan Marka dake faman cin magani.

Can ta sake sakin wani dogon tsaki tana karkada kafafu.  Cikin kufulewa tace,

"Kin isheni da zubar lallami Najaatu. Har kina wani lankwashe kai kina jin haushin Sa'adatu. Yo ai gaskia Sa'adatu ta fadi. Yaran Sa'adatu babu abunda zamu ce da su agidan nan sai san barka da fatan samun nasarar Allah akan dukkanin lamuran su. Zainab da suke kusan sa'anni daya da wahidin ne sau uku mai nemanta ya kawo mana kayan abinci ga su nan idan karya nayi."

"Zancen ki haka yake Marka. Domin wainar yar tsalan jiya ma zainab ce ta sayo." Cewar Sa'adatu hade da kecewa da dariya.

"Wannan duk ba abun damuwa bane Marka.."

"Babbar damuwa kuwa Naja. Natsani safiya tayi dare ya maye idanuna su sake dora ganin su akan Hadiza da ahalinta. "

"Kash. Assha Marka. Ki bar cewa haka. Babu fa bawan da ya tsara rayuwar sa haka fyace wadda Allah ya rubuta. Kuma menene yan uwantakan da zumuncin idan har dan uwanka baya kyautata maka?"

"Ke Naja. Duk abubuwan da zaki fada ba tasiri zai yi a zuciyata ba don in gaya miki..."

"Kibar cewa haka Marka..."

"Dole na fada. Kinga wuya. Nan inda abu ya tokare mun yaki tafiya. ? Ba komai bane fyace bakin cikin da Hadiza da yaranta suke samun. Nagaji idan da gaban gajiya nayi..."

"Ya SubhanAllah! Ki dubi girman Allah Marka ki dena cewa haka, Dukkanin yaran nan fa jikokine. Haka kuma Allah yaso acikin jikokin naki zaa samu biyu marasa lapia "

"Marasa lapia? Nakasassu zaki ce. Masu tattare da kunci da 'dacin rayuwa."

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Marka!! Marka!! Ki dena cewa haka. Malam ka saka baki. Wannan ba dede bane."

"Ba ze saka ba Najaatu. Idan kin gaji da ji ki tattara ki fice mana daga gidah ."

"Kiyi hakuri Marka. Kawai dai gani nayi wannan maganganun dik basu taso ba."

"Dole ne ayita. Shi ya saka nace wallahi kwayar hatsi nawa hadiza dasu Najib ba zasu sake ci ba. Su dan kinibibi sunyi shabe shabe ga nakasassu da baza su fita su nemo ba. Ita kuma uwar tasu ta daure musu gaba ba zata tursasu ba. Kullum dan tsagwarar munafurci suna daka suna sakin numfarfashi. Ita kuma ta faake kullum tana gefen su ba zata fito cikin mata tayi shiqa ba ta samu kudin batarwa. Ragowar me lapiar kuma ta tsiri boko ba kakkautawa.  Ba zeyiwu ba wallahi. Su tunda maza ne suje can su karata ita kuma tinda macece dole ne a aurar da ita. Baqin jini ya mata katutu maza basa zuwa. An samu kuma Na'Ateeku yace yaji ya gani zai aure akan wane dalili zamu fasa? Bayan idan ta aure shi kakarmu ta yanke sa'a . Ita kanta Hadizan sai tafu jin nutsuwa da kwanciyar hankali... Wahala zata ragu. "Marka ta karasa fada tana gyade kai.

Najan isubu ta numfasa kafin tace,

"Kowane bawa da yadda Allah ya kadarta masa rayuwar sa, Wala dadi wala akasin haka. Rayuwar hadiza da yaranta haka Allah ya rubuta mata tata jarabawar. Sai dai fatan Allah yaba su ikon cinyewa yasa jinkirin alkhairi ne Aamin . Zancen nauyin dake kanta da yardar Allah yazo karshe. Domin na samo mata aikin wankau da yan kaude kaude a layin manyan can na shurah. Saboda haka zata sauke nauyin wasu abubuwan . Haka zalika itama Waheedan akwai abunda zaa sama mata ta dingayi bayan su Najeebu sun ji saukin jikin su. Don haka Marka ki ajiye zancen Na'Ateeku agefe yanzu."

"Na ajiye na zuba mata idanu ina kallonta? Ba dan mashinshini a kusa sai zuryar boko? To bokon yaci uwatas."

"Kiyi hakuri. Insha Allah kwanannan samari zasu fara zuryaa a kofar gidan nan. Komai lokaci ne. Mijin ta na nan kusa da yardar Allah. Wanda zai share hawayen ahalin gidan nan kai dama na kusa da ku baki daya. Insha Allahu. Kice Aamin Marka.."

Umma hadiza dake daki hawaye suka shigaa zirara a idanunta. Tabbas Najan Isubu aminiyar kwarai ce data san dattako take kuma yi musu madaukakiyar kauna marar misaltuwa.

"Marka, Sa'adatu, Malam baku ce Amin ba."

"Aamin Najaatu." Malam Nalado ya fada yana sosa keyar sa.

"Uhum.... Inji me ciwon baki."Cewar Sa'adatu hadi da yin kwafa ta juyar da kanta gefe.

"Aamin inda gaske ne hakan zai kasance ba karairaki bane da wucewar zance."

"Insha Allah Marka... Na'Ateeku abunda yasa ki kaga na kauda zancen  maganar sa akan irin lalurar su Najibu ce. Ta sikila da ake cewa amosanin jini."

Marka taja dogon tsaki tana kauda kai gefe.

"Ke wallahi Najaatu kin iya samun waje kiyi ta sakin ta."

"Allah ba karya nake ba Marka."

"Wohoho ni lauya zan ce ne banaso wallahi. Na'Ateeku ban taba gani ya kwanta ciwo ba. Zaki jajiba masa."

"Marka abunda nake nufi shine. Shima ai yanada iyali dake dauke da irin ciwon su Kamal. Ba wai ina nufin shine mai ciwon ba. Amman yana dauke da wasu sinadarai na ciwon wanda idan ba'ai gwaji ba kafin aure shine zakiga anata hayayyafan yara masu dauke da ciwon. Yanzu kai ya waye Marka... Sai anyi gwaji kafin ayi aure saboda gudun 'barakar ciwuka. Hakan yasa na ce miki ki bar zancen Na'Ateeku da Waheedah. Domin kulla auren su kan iya haifar da illoli da yawa astagfirullah. Ba tsumi babu dabara. Maganin kar ayi kada a so ma "

"Keda Naja kinada kale kalen balai wallahi. Allah shi kyauta "

"Wannan shine tushen gaskia Marka. Ba Na'Ateeku ba. Ko wani ne daban yazo neman auren Waheedah ko zainab dole ne kafin ayi auren suje suyi gwaji. Wannan shine babbar shawara da ma'aikatan lapia suka kafa. Don gudun bacewar rana. Azo ana danasanin auren."

Marka ta tabe baki hade da jan karamin tsaki.

"Gidan aikin da zataje ina fatan nima inada nawa kason acikin albashin nata.?"

"Duk ba zai gagara ba Marka. Kuma insha Allahu tare daku duk zamuje taron nan ayi mana gwajin."

"Uhm.." cewar Marka.

"Bari na tafi. Allah ya kiyaye gaba."

"Toh Najaatu. Agyada gidah."

"Gidah yaji."

"Ke kuma tashi kafin na hamb'are ki. "

Takarasa tana mai wurgawa Waheedah harara. Gaba daya maganganun Najaatu sai shawagi sike mata akai. Ta kaikaice kai ta hango ledar taliyar kakkaryawa da tumatirin gwangwani. Na'Ateeku ya sake fado mata arai. CikiN zafin nama ta mike ta shige kuryar daki .

Waheedah ta mike jikinta a sanyaye ta shigaa dakin su Kamal. Umma hadiza kuma ta tafi ta yowa Najaatu rakiya. A soro Najaatu ta sake kwantar da hankalin umma hadiza. Da karfafa mata gwiwar ta zage damtse ta fara aikin nan da karfin ta. Ko zata kwatowa kanta da yaranta yanci a idanun su Marka .........



Tab!!! Lamarin ga ya ta’azaara… Jama’a wannan karon zafafa da zafin su suka taso. Ga fa gidan Malam na lado nan mai dauke da iyali da kuma gyatumar sa Marka. Ya rayuwar waheedah Zata kasance acikin wannan littafi. Shin su wanene wai The Adams family?? Na tabo muku bangaren zayn Adams Nasser kuwa? Hmmm inji me ciwon baki… Lalle labarin nan yana tafe da wani salo na daban mai taka rawar gani a wannan zamanin namu… Gefe d’aya dauke labarin yake tafiya da zazzafar kauna marar algus…. FARHATAL QALB!!! Lalle FARIN CIKIN ZUCIYAH…..yanki ne dake take rawar gani a zukatan bil adam. Musanman zuciyoyi biyu da ke begen kaunar juna…. A stunning love story😘don’t afford to miss this chance💯👍🏾 Ku shigo a dama da ku dan ganin yadda tafiyar Zata kasance…. Zafafa biyar. Yan biyar masu baiwa. Hikima, Fasaha da tsarkakkun alqaluma 💯📍

Yadda zaku biya👇🏾👇🏾

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
_*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
                     💞
_NA_


_NANA HAFSATU_
_(MX)_


_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_


_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_


_PG: 6_
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment